Author : NONE Category : African Stories & Novels
umarnin karsu kara tsayawa akanta intana barci.
Tsaki mai kauri taja snn ta jefar da wayar akan gado adan dole tadaure ta dauki coffe din tasha kadan,snn ta aje shi ta dauki nutellan ta tafara sha،dan duk duniya babu wani abunda tafi kauna a rayuwarta sama da taga tana kwalliya, bacci, shan chokolate na karshen su kuma mafi muhimmancin shine zuwa "shopping".dan har gani take kamar bazata taba rayuwa in bataje shopinh ba a sati kusan sau goma ma zata iya fita shoping bai kuma dameta ba.
A kasaitacciyar yanayi mai daukar lokaci ta fada wajen wanka inda tay umarni ma maid inta elizabeth akan ta cikka bath tube da kumfa sann aka kawata wajen wankan da wasu irin flowing red flowers da kuma red candles da hot coffe.
daga yau har kullum haka ta umarce Elizabeth datana shirya mata wajen wankankart dan babu shakka tasan damuwa rta yadau hanyar gushewa dan arayuwa bata taɓa sanin wani abu waishi rashi ba, bare kuma kalmar qaddara,toh inma akwai qaddarar to nata qaddarar kenan na zamowa matar ibaad a future.
Bayan ta kammala wanka ta fito aka fara shiryata kanta nitse,ta saka white mcqueen maxi gown mai makahon tsada
Saukowar nata ma daban ne dan haka kowani masu aiki kusan shida ne suka matso kusa domin serving mata abunda zata karya dashi.
Ita kadanta ta zauna akan doguwar royal dinning table dinsu 45 mtrs long maicin royal chairs guda sha biyu, maids din dake a tsaye akanta tana zama suka fara aikin jejjera mata dishes kala kusan sunfi goma da uwarta hajya hamida tasa aka dafa mata da safen nan musammn dominta
Saida ta kammala karewa abincin kallo kafin da kyar ta samu ta tattaba abincin kan plate daya tanaci kmr wanda kwai ya fashe mata aciki can dai tamiƙe tsaye tareda ce musu sutattara sauran su zubar ta koshi.
daga inda take ta kwallawa mum dinta kira batajira amsarta ba tace "mum nikam na tafi shoping da driver, tana fadi hakan kuwa tayi ficewarta.
ba ita da dawowa ba sai wajajen karfe sha biyu na rana, jakar sayayya yakai takwas da masu aiki suka biyota dashi ciki, tabi ta daga wa kowa hnkli tun karfe daya aka fara mata spa har izuwa 2:30 kafin tay wanka aka zauna mata kwalliya wajen zaben kayan da zata sakama saida har taji elizabeth tafara cewa ga baƙon nata ya iso yana gate snn ta iya zaɓa.
wajajen 5pm na yamma ibaad sharp yay horn agaban gate dinsun dat took almost forever to open sabida scanning dinsa da masu kula da cctv cameras sukeyi kafin can dai suka budemai gate din ya shigo.
security ne aharabar gidan here and dere amma dake anriga an gaya musu wani yaro zaizo sai basu wani damu su tambayesa ba, calmy ibaad ya kashe mota ya sauko daga shi sai wayarsa
wani security yaxo suka gaisa daga nan baice masa uffan ya masa jagora suka shiga cikin gida...#surayyahms
share
08060712446
[28/10, 18:44] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: _ABUNDA KE ƁOYE...._
_Love And scandal💕_
*_Arewabooks@surayyahms_*
⏯️9️⃣
Door bell securityn ya danna within 2 mins wata maid sanye da torqouise colour uniform ta buɗe kofar tafito, suna hade ido da ibaad ta tsaya cak tana kallonsa cikin haɗiye yawu a fixge ta dauke idonta a nitse tace ma security "i will take it frm here. kai ya gyada mata baice komi ba yajuya yabarta tare da ibaad din awajen, cikin kare masa kallon rudewa ganin kamanin jini da prof a fuskarsa yasa tace "please come in ure welcome sir.."fuska ba yabo babu fallasa ibaad yace thank you gaba tay yana biye da ita abaya suna shigewa ciki aka rufe kofar gidan kirif.
Katafaren Parlour ne mai wani irin girma da tsari dayaji Lumtsattsun kujeru na royal chairs golden and red colour. labulaye da chandelliers suma golden colour sai baza qyalli suke snn Duk wani abu daya ƙawata Falon ya zamto shima golden nd red colour dinne da wasu irin manyan turkish carpet, manya manyan Airmores da incence burners kusan kowani kusurwa suna aikin bada Dadaddan Qamshin turarruka na alfarma da kuma iska mai sanyi wanda already sanyin ma yakama falon takoina sabida wata irin dukiyace ta musamman aka narkashi acikin wnn falon.
Babu kowa acikin falon tasu ta farko wanda shine zai sadaka da babban falo na biyu wanda ya kasance falon zama daganan kuma har zuwa sashen cin abinci.
Ratsa dogon Falon tayi ibaad na biye a bayanta ta nufi kofar da zai kaita ainihin falon prof zayyanu na musamman tana isa dede wajen kofar ya budu ta tsaya cak anan tamasa alama akan da yakarasa shiga shikaɗai sabida prof already yana ciki, uffan baice mata ba cikin takunsa mai sanyi da aji ahankali yashige ciki ita kuma takoma gef ta tsaya daga nan tana jiran fitowarsa.
Katafaren falone na alfarma an masa kwalliya da dusty rose da wani irin cool black furnishings, wanda shirun da wajen yay tamkar babu kowa aciki banda qamshi da ƙarar ac dake tashi ahankali.
Ajiyar zuciya ibaad yay tareda ta sakin masa nitsatsiyar sallama ayayin da prof ya dago kai yanamai sauƙe ruwan idanuwasa akan ɗan yayan nasa.
Zaune yake cikin shiga ta alfarma jikinshi killace da manyan kaya wanda tuni tay bajintar fallasa siffarsa na kyakkwan namiji mai cikar zati,jarumtacce mai kuma cikar ƙirar halitta da dirarren siffar jiki. Kallon daqiqa biyu yayi ma ibaad din,ganinsa lafiyayyan yaro mecike da tsananin sanyin kyau da cikakkaer kwarjini me rikitarwa zak zak irinna mahaifinsa wanda hakan ya kusan rudasa atake, ji yay aransa inama ace Da Shine Allah ya bashi wnn darajar samun ɗa namiji dakakke irin wann ba babban wansun daya rasu ba.
saurin daidaita kansa yay cikin tattaro makansa nutsuwa da ƙarfin hali yanamai sakin masa murmushi adan dake har ya amsa sallamarsa tare da umartansa akan ya karaso ciki.
ibaad na karasowa ya tsuguna kasa daf cikin
nitsuwa ahnkli yace "ina wuni kawu, fatan na sameka lafiya?
prof ya karemai kallo sama da kasa cikin yanayin kamiya adan tsime yace masa lafya kalau, shiru ne ya dan ratsa kafin yace" Kaine babban ɗan marigayi ko? bayabo ba fallasa ibaad yace eh nine, prof ya gyada kai, but u can see the provocking jelousy nd envy wailing tru his eye balls, dan yafiso ace kowani abu mekyau a duniyan nan shine zai mallaka msmn yadda yaga ibaad yafara girma cikin nitsuwa izuwa hadadden namiji mai kwarjini da aji sai yakeji aransa inama ace danshi na cikinsa ne bana yayansa ba.
cikin kaucar da wann tunanin yace ohh babu shakka, i can see the resembelence, "wai har ku nawa ne ya haifa haka? batare da dago kai ba ibaad yace "mu biyu ne. prof ya kara zuba masa ido da mamaki ayayinda shiru yadan ratsa tsakaninsu sai can snn yace umm well, dats fair amma kuma dukanku maza ne? nasan da babanka bai rasu ba hala da ƴayansa sunfi haka yawa,..baima bar ibaad din ya amsa shi ba cikin yanayin mita yace" babanka shine babbanmu a ahalin nan amma bansan mesa yaje ya auro yarinya karama ba, uwarkun tana raye ko itama tabishi?..
ibaad ya dago kansa ahnkli suka haɗe ido fuskansa adan daƙile yace mishi "she is alive. prof yay dan kwafa a shashance "tou hakan yay dai-dai alhamdullh tunda kuna da wacce zatana ciyar daku kai tashi muje ciki nagaji da wann surutun..ibaad yay shiru kamar baiji shi ba, har saida prof din yamiƙe yafara tafiya snn ibaad din ya mike tsaye shima yafara binsa abaya,
wani katafaren hallway suka ratsa, acikin izza prof yake tafiyarsa yana lallatsa wayarsa kai daga ganinsa kasan ba har cikin ransa yake son wnn yanayin ba, shidai kwata kwata baison yan uwansa na jini suna raɓar gidansa bare arzkinsa wnn karon ma babu yadda ya iya ne rayuwar yarsa tafi mai komi muhimmnci a yanzu
suna shigowa wani katon white hall mai tattare da babban dining area sai ga nan matarsa hajy hamidan tabude wani babban kofa ta fito amugun mugun kasaitance wani irin kwalliya tayi tamkar ɗawisu qamshin hadadden turarenta tuni ya bule wajen da qamshinsa, tana taku dai dai kmar bazata taka kasa ba, tasaka wani ubansun boubou na original shadda lace royal blue colour wuyanta da hannunta sunci uban su da gwalagwalai.
suna hade ido da ibaad ta tsaya turus tanata kallon yaron cikin fallasashen ruɗewa dan acikin ranta batay tsammnin wai harya girma ya ƙara kyau haka ba, tasan dai zainab arifah tana yawan zuzuta kyansa ita a mind inta she expects to see notin but a hungry local boy with no social class, dan rabonta da ganin fuskarsa tun ahoton haihuwarsa datagani awayar anty safeera.
cikin neman wakanta nitsuwa tay gyaran murya me aji tabi ta tsime batako musu sallama ba dake taga mijintan nakan amsa call kai tsaye ta shigo cikin dauke kai tayi kamr batagan ibaad a tsaye ba.
tana zama akan chair ibaad ya daga ido ya kalleta daga tsayen yace"ina wuni ? ranta a harde ta masa wani irin kallon sama da kasa me shaqe da rainin wayo muryanta ciki ciki tace "lafiya. snn ta dauke kai tay banza dashi, shima sai bai kara kallonta ba, shiru ne ya ratsa tsakaninsu dan wani mugun haushin yaron ne ya riketa kamr zai fasa mata kirji irin feeling feeling dinnan najin anrainata dake ta riga ta saba ana yawan mata fadanci ko mutum ya girmeta zakaga yana rusuna mata kai kasa sabida matsayi da dumbin ikonsu, yadda tagama raina ma labarin kyan ibaad wayo sai kuma tazo taga ya ashe ma wuce yadda take tsammani tun daga siffarsa har izuwa kan dressing insa me mugun dauke ido da uwa uba yadda dadin turarensa me aji ya kusa danne nata me matukar tsada.
shi mutum ne wanda iya tsaftarsa ne zai soma dauke maka hankali, he always look so smart nd very neat, shi baya son tula kayan sawa ajikinshi amma kuma sutura me bala'in aji yake yawan sawa.
prof ya gama wayarsa kenan ya kallesu duka ganin kowa ya dauke kai sai yay gyaran murya yace hajiya hamida wann fa shi ne dan gidan marigayi babban yayana late dr almustapha almansur.
cikin rolling ido ta juyo tanamaiyin kamar tuntuni bata ganesa ba, da wani irin yaken makirci tace ohhhhh ayya, Allah sarki ashe dan marigayi ne, gashi kuwa ya girma da kamannin mahaifinsa, gosh jishi duk ya zama abun tausayi toh Allah dai ya jikan babankan, ran ibaad yafara baci bt still ya kwantar da hanklinsa yace Amin. ido ta zuba masa ta kara kallonsa ita dai gaba ki daya ji tay kmr taƙi jinin yaron dan daga ganinsa tasan zaiyi girman kai yadda taga ya hade ransa baya ko murmushi, saida ta gama kare masa tanaɗi aranta sann tace Alhaji sai ku karasa dinning din i am sure we are all famished.. prof yace aa hajiya kinsan ni bawani son cin abnci da yamma nakeyi ba amma dai tou bakomi muje dai zan taɓa.
tay murmushi yawwa my darling ai kuwa dazance kar kayi haka
ta kalli ibaad da rainin wayo a kwayar idonta cikin rage murya kasa kasa inda tasan ibaad din zaiji tace "ohh ni hamida dama haka yaron yake abun tausayi, alhaj ya naga duk yunwa ne ajikinsa kasan me? kuje kawai kan dinning din zan sameku acan i need to check on our princess,
prof baice komi ba ya gyada mata kai tana barin wajen ya kalle ibaad wanda already zuciyar yarinta na raya masa akan kawai yaqi cin abincin ya tafi sai kuma yay wni tunanin kawai sai ya danne zcyrsa yabishi suka zauna akan dinning table din kusan atare.
nan ma shiru ne ya ratsa tsakaninsu har saida hajya hamidan ta dawo ganin ita daya ta fito babu zainab arifah yasaka tun bata zauna ba prof ya fara tambayatta inq yarsan take, fuska ba yabo ba fallasa tace "alhaj ka kwantar da hankalinka she is coming kasan dai yarkan sarauniya ce mai son kwalliya da tsafta, so she will be here in few minutes dai tacemin, cikin jin dadin hakan yace its awryt let her take her time she will alwys be the prize, atare sukayi dariya. shide ibaad baice musu uffan ba,
daga kan long luxurious table din ido kawai bazai iya kirga abincin da ake jera masa agabansa duk dan a nunasa nasa bambamcinsa da su.
abincin gargjiya har tuwon biski ta saka anyi wai a tunaninta ko yaron baisaba cin na yan gayu irrinasu ba, itafa komin arzikn ka inhar ajinku ba daya bane to A talaka kawai take kallonka.
sunfi 10min suna zaune ba ataɓa komi na abincin ba sabida suna jiran yarsu yar gata zainab arifa ta gama duk abunda takey snn ta karaso.
hirar business suka faray sama sama tsakaninsu ganin ibaad bamai son magana ba yasaka basuma tsomasa aciki ba.
after like 10 more mins tahowa zainab Arifah takeyi akan golden steps cikin shan qamshi tana taku kamar bazatay ba domin itakanta qamshin turaren data fetsa ajikin nata tsabar yawansu da karfin qamshinsu ji take kmr suna bugar da ita, daya bayan daya take dora kafafuwanta akan step, cikin tattalin kai
can saiga ta bullo ta wajen inda suke wanda tundaga sama ta zubawa ibaad dake zaune akan luxurious dining table din da aka kawatashi da ababen tabawa ido tanajin kamar mafarki takeyi, wani irin sabuwar farinciki takeji mai yawa na mamayarta har kwakwalwa data gansa.
Kasaitaccen sautin takunta shi yadan janyo hanklin iyayen nata bisa gareta dan tay masifar kyaune na kure hankli saide duk gigin zumudintan nan kuwa bata wani tula kayar tashin hankli ajikinta ba, doguwar riga slay queens gown styles marar hayaniya sosai tasaka ajikinta na babban atamfa original engila red colour snn ta cakkara dauri tare da zubo da sumarta kafadunta, cos at this young age already ta fara saka irinsu nails da curtex da gashin doki duk dama babu laefi itama din tana da dogon suma., cikin nitsuwa ta sauko cos she rmbers clearly cewa babanta yace mata kar tay rawan kai agaban ibaad, dan haka tay balain kkri wajen danne abubuwa dayawa na zumudin ganinsa dake yawo cikin ranta da zucyarta.
faduwa gabanta ya dingay har ta iso tana satar kallonsa, iyayen atake suka hau yaba kyanta kamar yadda suka saba, itakuma tana fmr shagwabe musu fuska, ibaad yadago kai kenan suka hade ido da ita, gabanta ne ya mugun fadi saikuma taji takasa motsi tabi takafe shi da kallo mai sanyi kamar bata taba ganin kyakkawa irinsa a duniya ba.
ganin ya dauke kansa a kallo daya yasaka itama ta dauke kantan ahnkli cos she was lost in her tots for a moment dan batama jin me iyayen nata suke cewa kawai satar kallonsa ta dingayi harta karaso gefen baban nata ta nanike ata gefensa yarike mata hannu cikin tsantsan nuna mata soyayya da gata a fili, a shagwabe ta zauna daf dashi batace ma iyayenta uffan ba, tay cunen baki tanajin kanta a matsayin yar gata sangartacciya kuma ƴa guda awajen iyayentan wanda tasan zasu iyayin komi akanta a duniyan nan, yau yadda kasan danyen tuwo haka take narkewa jikin babanta. Tun data nemi waje tazauna acikin yanayin shagwaba batace uffan ba bare tay gaisuwa daga ta turo musu baki, sai tay rau da idanunta cikin tsinannen rigima.
hanklin ibaad gabaki daya baikansu jin yadda iyayen suka fara jajayya da ita wajen gaisuwa dan tun safe bata gaishe da iyayen nata ba.
yau sosai yakara lura da cewa zainab arifah din sangartacciya na kure hankali da tunani kalar wanda tsarin rayuwar banza ya riga yashige musu jikinsu sosai.
da kyar dai suka sakata tay gaisuwar harta gaishesa ya amsa atakaice kafin nan baban nata dakan sa ya bada oda masu aikin gidan dake akansu suka fara aikin serving dinsu abinci wanda gabaki daya wajen ya gamutsu da wani irin qamshi me shegen dadi ga nan dadadan aroma na garnished soups da gasashun namar kaji.
sama sama ake hira akan table din..shide ibaad sam ya kasa fahimtar kalar rainin wayo irin tasu cos all this traditional food tagabansa kawai ake tarawa hakama idan za'a samai abu a plate dinsa sai ancika plate din kamar sun ga mayunwaci ko mabaraci. shide tun da ya rike spoon yana jujjiya wa bai isa yace yayi loma yakai uku ma abincin ba..
prof ne yake magana time time yana kushe kokari, ilimi, da arzikin kowa cikin familyn su al-mansur, at same time yana dan sako labarin mahaifin ibaad din dake duk zuria shine kawai bai taɓa yin zuciya dashi ko ya rokesa kudi, ko wani taimako ba. hasalima badon shegen son zumunci irinna mahaifin ibaad ba da tuni prof ya raba kansa da zuriarsa sabida bappa zaidu da uncle moh sai suyi shekara fiye da hudu ma basu kulashi ba.
shi bawani cin abincin yqke ba kallon ibaad kawai yake yana cewa..."babanka mutum ne mai mutunci duk zuria shine kawai be taɓa nunamin baqin cikinsa ba,shi yasa nake jin kamar ba zaidace mubari zumuncin daya kulla da gidan nan ya yanke gaba ɗaya..
duk da prof baison zumuni bt he try to pursuade ibaad dan yaji aransa cewa zai iya amsarsa agidansa a mtsayin ɗa kodan albarkacin mutuncin mahaifinsa.
hajy hamida kuma tafi matsuwa datasan educational level din ibaad bawai dan zai mata amfani ba saidan ta samu wani makafar ci masa mutunci da kaskantar dashi in the future, she was highly expecting to hear some mediocre course. saidai tun ya ce musu medicine mbbs yake karantawa a jamiar Ado Bayero sai taji ranta ya baçi wann karon batama iya boye tsanar da take masa a fili ba..,
cikin furucinta na rainin wayo sai nuna mai take kamar bai kai ya karanta wann course din ba. sai tambayar ya uwaka tay ta haifeka take masa akan karatun. tanamai nuna masa karara cewa medicine yafi karfin brain insa like he cant just afford to be a doctor. tafara masa suggesting su hospitality managmnt, zoology, french, islamic, political science, library science, history, hausa e.t.c..shide ibaad bai iya raina babba amma tunda ya gane salonta na rainin wayone sai ya zamana da daddaya yake bata amsa me kaifi da nauyi wanda yasan hakan yana mata ciwo aranta sosai. duk courses din data kirasu mediocre saida ya gaya mata relevance insu a real life. ta dage masa wai saidai yabar medicine