Author : NONE Category : African Stories & Novels
friends, i can even be ur sister...cewan hakan da sultana tay yasa taji raunattacen kuka mai yawa yazo mata itakanta bata san sqnda takara fashewa dq kukan sosai cikin tunowa da addanta inayah ba,...
gabaki daya sai sultana taji ta rude tana shirin budan baki zatay mata magana caraf sai ga ibaad yashigo ya tsaya cak daga kofa yana kallon su da wani irin murdadden murya yace "whats going on here?
da bala'in sauri sultana ta miƙe tsaye muryanta harna rawa rawa tace "nothing yaya...kawai fa magana nake mata shine naga tanata kuka..ni wlh banmata komi ba, bansan meya faru da ita ba..
fuskansa kamar na wanda bai taɓa dariya ba yace ma ayaanah "ke zo nan..da mugun sanyin jiki ta tashi tanata kkrin controling tears dinta kafin ta iso yay wuf ya jawota gabansa yace"kewai so kike na wanka miki mari ko?
a mugun tsorace ta girgiza kanta da sauri tana hawaye
yace toh uban meyasa kike son yin kuka, are u trying to sabortage ur treatment or what? kinga ina binki ahankli shine iskancinki yake dada karuwa ko?
budan baki tay cikin kukan zata bashi hqri cikin zare mata ido yace da Allah kirufa min baki, bana son ji, snn ki goge wann shegen hawayen naki kafin in fasa miki bakinki ynxun nan..
da sauri tafara goge hawayen sultana tay shiru jikinta na rawa rawa saiga nan maheer yana saukowa da robobin abinci..
kallonsu duka yayi yanamai karasowa yace meyeke faruwa anan?..pretty one are i okay..juyowa tay helplesly ta dan kallesa yace gama share hawayenki ki zoki kuci abinci da sultana saikuje daki tare kuyi bacci..
kai tsaye cikin iko ibaad yace "she is not eating!! bacci kawai zataje tay yanxun nan...ya kalle sultana a dakile snn yace" take the food for yourself, nd take her with you. inta sake bare baki kizo ki gayamin, saina mata shegen duka.. very stupid girl, uban waya yace miki anason jin kukanki...
yana fadin hakan ya haura sama yana jan tsaki..
wani hawayen taji ya kara sauko mata maheer baice komi ba ya mikawa sultana abincin snn ya bi bayan ibaad din da mugun sauri, ibaad na shiga dakinsa ko zama baiy ba saiga maheer din ya shigo fuskarsa adan dore yace"kaikuma meye haka zakana ma yarinya karama tsawa kana tsoratata"..and why wud u say she is not eating ahakan ne zata warke maka kafin sati biyu???
da bacin rai ibaad ya kallesa yace "you dont get it do you??maheer wallah am tired, nagaji, tun jiya yarinyar nan take bani ciwon kai while i was busy tolerating her amma batagani, daga tamin fitsari a atsakr daki sai takicin abinci, in kuma aka tursasata taci haka zata yi amai ta ɓata koina da kazanta, wai ciwon hauka ne? nifa kaga banason iskanci da sakalcin banza, yanxu fisabillah me ake mata datake yawan yima mutane koke koke
cikin lumshe ido da budewa maheer yace "dude she is just a child, just take it easy on her ko kaine akace sistrnka ta mutu snn qaddara ya raba ka da mum dinka rana tsaka wallahi bazakaji dadi ba bare wnn yar yarinya karama...
a mugun dakile ya kalle maheer din cikin jan tsaki yace "okay naji, ynxu sai a tsaya knn ana kallonta tana duk abunda taga dama?see...guy inkai zaka iya hakan fine, nide i won't tolerate that. i know is hard for her and she is sick, amma wnn dabiun datakeyi na koke koken nan bafa zai taimaka mata wajen warkewa a both side of her health nd grieve ba, dolene fa sai anbude mata ido if not babu abunda zai canza a condition na ciwonta saidai ma ta dada lalacewa..kaga ni, am soo tired wallah, bacci nakeji cos i have 2 more classes tmorw...kaje kawai kayi abunda ya dameka.
yana fadin hakan ya nemi waje ya zauna akan gadonsa yay shiru yanajiran maheer din ya fita ya bashi waje, for good five mins maheer baice komi ba, he was just trying to understand his point of view, cikin kyabe baki ahnkli yace"wann zafin zuciyar naka ai da soja kaje ba medicine ba,anyhow sha..i will see you tmrw.
kan ibaad na kallon gefe yace "naji, gudnite,..maheer ya gyada masa kai snn ya fita.
falon ya dawo, ya samu wajen shiru har sultana ta lallaba ayaanahn sun haura can sama izuwa dakinta atare. ya kama hanya zai je duba su kenan sai ga ammi babba ta shigo riki riki da wani leda datake kaffa kaffa dashi a hannu.,
kasar wuyansa ya amsa sallamarta yana kallon agogo almost 8.30 na dare ta dawo..
fuskansa ba asake ba cikin dauriya yace ina wuni mummy...
tsaki me kara taja mtcheww cikin watsa masa harara me zafi tace"aikin banza,.. daban wuni lafiya ba ai da bazaka ganni ba..and where is sultana
metaci yau?...ko ubankun bai kira farkansa ta ciyar masa daku bane wato ana jirana nazo nay muku girki ga boyi boyinku ko?..
shiru yay mata
wani tsakin ta kara jaaa zata haura sama dayan sashen domin taje taduba sultanan maheer yay saurin tsareta da cewa "mummy she is not upstairs..ibaad yanakan mata assignmt acan sashen baba.
tana juyowa tace "karya kakeyi munafiki...wani sashen baban naka?? toh yanxun nan mukay waya da safeera tace min ga babanka cann yaje can gidan sunakan tattaunawa a falonta da dan uwansa muhammad,
maheer ya dan sosa kai yace" ai dama bance yana nan ba, i just told u abt sultana dan karki bata lokcnki kije sama, dats all i know..maybe kafin ya tafine ya barsu acan
cikin katsesa da masifa tace "yabarsu acan? see..dont u stand here..go over der now, kadena barin min yata da katon namiji sukadai da sunan yana koya mata karatu...inku kun aminta da ibaad din naku nifa ban aminta da shi ba karyaje ya danne min yata ya cuce ni ehee just go up der nowww ka duba min lafyar yata..
da sauri yace yess maa.
hawa yay yadan buya awani waje yana ganinta tafasa zuwa dakin sultanan, tana wucewa sama sashenta ya sauke wani makudan ajiyan zuciya tareda jin reliev aransa dan yasan muddin tasan cewa ayaanah zata kwana a dakin sultana wani sabuwar rikici zaa balo da daddaren nan...
Ata fannin zainab arifah kuwa ranar gabaki daya bata sauko kasa ba kuwa har saida mahaifinta prof zayyanu ya dawo gidan da yamma..
yana zuwa kuwa kamr yaji jikinsa cewa babu lafiya sam yaki zama yahau bori yace ma maids marmaza suje akira masa yarsa ta sauko yana son ganin kyakkwan fuskarta..
koda maids sukaje duk taki ta kulasu, har saida mum dinta hajya hamida taje dakanta ta dinga buga mata kofar tana lallaminta jin ance babanta ne yake son ganinta yasa ta sauko sanye da pink dior riga da wando daya matseta kanta babu dan kwali tabaza sumanta har wuyanta ta taho kasan cikin daure fuska da kukkuni..
suna haɗa ido da babanta da gudu taje ta fada ajikinsa tanamai sake masa kuka mao cikke da shagwaba da sakalci
wani irin yagalgalata ya dingayi yana tambayarta abunda yake damunta ,dakyar ta dena kukan tafara gaya masa ai wata ce tazo da irin jakarta makranta ita gaskiya ko acanza mata wani jakan wanda babu wanda zai iya sayan irinsa ko acire ta kawai a school din amaida wani...
cikin tsantsan nuna mataso da gata prof zayyanu yace matsalarki kenan princess
tace mishi ehh..yace toh shikenan..let me do sumting abt it ryt now..ciro wayarsa yay ya daddana ya bude dollar acct dinsa atake yay mata transfer $80k dollars..yace princess ga kudi ki saya duk jakar makarnta
daya miki..ita kuma yarinyar i will asked for her to be removed banason ana bata miki ranki kinji ko?? wani irin rungumarsa tay da karfi tana murna kamar ba itace ta dinga masa kuka yanxu ba..thank u soi much daddy..i love you i love you soo much...ure the besssssttt
wani irin fari zuciyarsa tay ganin ta tana murna sai yaji dadi aransa sosai, yay kissing inta a forehead so lovingly da murna tace "let me go nd oder it...and dad gobe zan rakaka 5 days conference dinka a paris..i wanna be by ur side..
cikin tsabar murna yace "as u wish my princess..
kissing dinsa tay agefen kuncinsa tace i love u daddy
..nn ta wuce sama tana wani irin murna sosai haka ya dinga kallonta yana murmushi harta bace ma ganinsa..
hajiya hamida taja wata kalar tsaki"haba alhaji yanxu akan jaka shine tay wann abun kuma ko scolding inta bazakayi ba ka sake daukan maqudan kudi ka bata tasaya wani? wann fa almubazaranci kake koya mata
yace keee? dagata min haba da Allah, kinfara kananan magana nan naki kenan ko. yata kenan mini fa in duk duniya tace tanaso wallahi saina bata bare kuma wani jakar banza
hajy hamida tace nifa ban hanaka bata abunda take so amma 80k$ alhaj yay yawa mana..stop making her a careless spender..ohon maka ai yarka ce..
yace "yeah yeah nd u stay out of it..zainab arifah is so sooo fascinating, jinina ne ajikinta, ke bakiga ma yadda taketa kkrin shiga harkan business dina tun yanxu ba?she is confident nd smart, she have potential to be a good ceo in d future nd i will make sure she is better than me .
cikin kyabe baki hajy hamida tace" kaidai akwai son zuga yarka..but, anyway she loves to impress you more than anything in her life..hala shiyasa tke kkrin koyan abubuwan dakake yi na business tun yanxu..
yana murmushi yace "i am soo proud of her.. tay murmushi tare da rage murya kasa kasa tace "is good ma da zata bika paris din dan dazu mukay waya da safeera tace min wann shegen mayen yaron data kwallafa shi arantan ya dawo...
atake mood din prof ya canza yace "really? to kema kiy shoru kartaji tafasa tafiyar nan cos i dont want her near him for now
Allah ma yasani wallah na tsane shi...banda darajar ubansa danake gani da ko mutuwa zaiy wallah bazai zo kusa da yata ba
hajy hamida tace hmmmm lets just keep quiet kasan zainab arifah da laɓe karma tanajin mu, ka tashi muje kayi wanka na hada maka special ruwan wanka..murmushi yay tare da ko waist dinta suna dariya ahaka suka haura sama atare.
fannin zainab arifah kuwa tana zuwa dakinta dama she already have this long purchase history with the LVs, dan haka atake ta kira private client consierge insu na can paris tay odering black colour rarest limited taiga leather special oder edition na LV bag pack, costing abt $79k (114million in naira) za'a kawo mata jakan in 5 days time can a hotel din da zasu sauka sa babanta in sunje. hqr saida tay hakan sann taji hankalinta ya kwanta sosai ta dau waya ta kira elizabeth ta hada mata ruwan wanka, tay wanka masu mata massage suka mata snn ta sauko kasa taci abinci ta koma dakinta taje ta zauna tanata karatu har saida tay bacci...she rarely pray sabida batama fara islamiya ba tukuna just few ayoyin sallah kawai ta sani guda uku falak da nasi da qul huwa as she was tougth by her father..
dagata dayan bangaren kuwa ammi babba tana zuwa dakinta tay sauri ta kulle kofarta kirif harda saka masa key snn ta aje babban ledar data shigo dashi din akan gado, jikinta harna rawa rawa kmr wata marar gaskiya ta bude ledan tasaka hannu aciki, one after the oda tahau fitowa da shu'uman magangunan mata da akeyisun da laƙanin shirka da sihiri da suka karbo wajen zinariyar mace.
she was sooo convinced cewa karshen matsalar ta da mijinta yazo kenan, wani shu'uman ruwane aciki ta fito dashi daga kwalba tana kakkafa kaffa dashi dan kuwa ruwan dake cikin kwalban shine jagoran aiki,
zinariya ta riga ta gaya mata in har babu ruwan nan toh duka sauran concotion din data bata bazasuyi aiki ba, garin magani ne kala kala har guda uku da wani busashen jini anyi shi yawani kangare kamar konannen kilishi
zinariyar mace tace "har saita zuba ruwan kwalban nan a regular herbal tea dinda bappa zaidu yake yawan sha da safe while ruwan yana tafasa, snn ta tabbata yasha sosai kafiin nan sai tafara masa barbaden garin maganin akowani abinci da zata bashi har sai ya kare, shikuma busashen jinin a miya kawai zatana yankawa tana sawa har sai ya narke sann taje tabashi yaci.
zinariya tace mata muddin tay wnn abun daga ranar bappa zaidu zai mance fatima snn zaina jin magananta sosai kamarma itata haifesa haka zai dawo yana mata biyayya har akan gado, haka kuma still zai bude mata bakin aljihunsa, sai abunda taga daman deba daga kudinsa, ta tabbatar mata da cewa ko duka ribar busneses dinsa da salarynsa tace ya dauka ya bata duka haka zaidinga batasu batare da yacire ko asi aciki ba..
tsabar zinariya ta ci alwashi da wann hadin yauko sisinsu bata karba akan wann maganin ba,cewa tay suje sai sun gwada in aikin yaci snn sukawo mata kudinta 10million naira ne in cash. inkuma suka lalata aikin da kansu still zasu biya ta dan bata daukar asara.
ammi babba was very careful wasu abubuwn ma awayarta ta rubuta dan karta manta, abu daya ne ya rage mata dan tariga tasaba in sun samu matsala da mijinta irin haka batakai masa abun karyawa da safe, yadda tay masa borin hauka yau gani take kmr intakai mai shayin gobe da kanta bazaisha ba..
shiyasa tun ahanya ta gama lailaya hakan aranta kusan ma abunda yasa take neman sultana kenan, tattara duka magunguna tay ta aje su a very safe place acikin drawerta ta kulle da key, iyaka kwalba me dauke da muhimmin ruwan ne ta bari akan table, daga nan cire kayan jikinta tay tasss tafada wanka tafito ta kalkale jikinta da gyara snn ta saka wata shegiyr doguwar silk nity green colour irinna manyan mata...
lokacin already karfe goma saura ya karato zama tay agaban madubinta tana karewa kanta kallo tana baza wata irin shu'uumar murmushi da tunanin yadda zata baza baqar mulkinta akan bappa zaidu inhar maganin nan yaci. daga kan ibaad, har ayaanah duk ta sakasu a list din wayanda zata saka bappa zaidu ya walaknta su yaci musu mutunci kafiin ya musu korar kare a gida.
atake tafarajin wani farin ciki aranta tanajin cewa zuwa next week by now gidan nan daga ita sai y'ayanta babu wasu bare.
tajima tana zaune acikin wann tunanin har saida ta jira12pm yay yadda tasan duk tsiya mijinta ya dawo gida kuma kowa yaje dakinsa by now ya kwanta...
atafannin su sultana kuwa tunda takai ayaanah dakinta bisa umarnin ibaad gabaki daya ta kasa gane kan yarinyar, dan daga ta zauna sai kagata takure kanta agefe daya tayita kuka ahnkli har tana jan sheshheka me zafi, like sumtin is really eating her up nd paining her duk saika rasa meke asalin yawo akwalwalr ayanaah.
magiya da rarrashin duniya sultana tay mata amma takiyin shiru, kuma ko ta mata magana batacewa komi sai dai kuka, abun dik ya dame sultana har saida tafara cemata zataje ta kira yaa ibaad yazo kafin wani abun ya ragu har suka kwanta.
ahakama taki tasaka nity da sultana ta bata da kayan jikinta ta rakube agefen gadon tay lumui cikin takura jikinta waje daya...
bayan ta nitsu dakin was dead silent for a bit haka sultana tabar mata wutar bedside lamp din gefenta a kunne dan kar taji tsoro daganan hartay bacci ayaanah bata saka ranar runtse ido ba
12pm na dare na cikawa ammi babba ta fito cikin sanda gashi gidan yay wani irin shiru banda karar aircones babu abunda kakeji koina ya dau qamshi da sanyi sosai...
babban kitchen ta nufa tabude spicess scrolls, ta debo zallan herbal spices na hada tea din da mijin nata yafiso tahau shirya komi in d ryt quentity ta zubasu duka a empty tea maker snn tarufe shi witout adding any water da zimman da safe sultana inta tashi zatay masa tea din, sai ita takai masa tasan inde yarsace takai masa tea da safen dolene yasha.
wucewa tay dakin sultanan danta tasheta a bacci snn ta jadadda mata hakan, snn tace mata idan zatafara tafasawa ta kirata ita tazo ta sama mata ruwan, wai ahakan wayo tay dan tasan lokcin ne perfect time da zata iya zuba maganinta acikin sauki batare da ciwon kai ba
kai tsaye ta kulle kitchen ta fara tafiya har takai dakin sultanan tabude ahnkli ta shigo da mamaki taga bedside lamp daya a kunne, itakuwa ayanah tanajin motsin shigowar mutum tay maza ta rufe idonta tay kamar bacci takeyi
cikin sauri ammi babba ta kunna general wuta tana ganin mutum biyu ne akan gadon yartan babu jira ta isa wajen da zafin nama tawani irin janye bargon kasa, tana ganin ayaanah kusa da yarta akan gadon sai taji ranta ya harzuka yay baqi qirin....da har ta miqa hannu zata jawota kasa tay wurgi da ita sai ta tuna cewa she dont have time for creating a scene dat may cause her attention tafiso ne kawai tay focusing akan maganin nan.
tsaki me kauri taja ta dauke idonta akan ayaanah snn ta koma gefen sultanan ta zauna daf da ita gently frailing her soft hair da fingers dinta tana shafa mata fuska harsaida ta farkan da ita...
suna hade ido acikin gigin bacci sultana tace "mummy? ammi babba tay murmushin yake tace "yes my baby.. na tasheki ko?? sultana tanakan mutsuka ido tace "yess amma yaushe kika dawo gidan mumy shine kika tafi ko abinci baki ajiye min ba., jawota jikinta tay tana peting inta tace "toh sorry..keee ni ba wann maganan nazo miki da shi bama. kinaji na? sultana tace eh" jawota jikinta ta dada yi snn tace" autana inaso ne gobe da sassafe kije kitchen zakiga na hada miki komi a tea maker saikiyi ma dadynki tea dinsa ki kaimasa har sashensa ki aje. toh zakiga bansaka ruwa ba, daga kinfito just come nd call me first, zanzo nasaka miki ruwan ke saiki dafa ki zuba a flask dinsq kikai masa snn karfa kice masa nina taimaka miki kikay tea din kinji?
da mamaki a idon sultana tace "toh..toh mummy amma inyace meyasa nakawo masa faa..yafa san ban iya tea din ba.
cikin zare mata ido tace "kedallah bazai fadi haka ba kefa yar autarsa ce. bakiga wai fushi dani yakeyi bane. i just want to be good to him, shiyasa nakeso ke kikai masa tea dinsa na safen yasha kinsan dai