Chapter 15 Reading Abunda Ke Boye Complete Hausa Novel READ HAUSA Novels

Abunda Ke Boye Complete Hausa Novel

Author :  NONE Category :  African Stories & Novels

Chapter   15 / 88

42K to 45K   out of 262.2K words

da kwaryan maganin datake hadawan a hannunta, tun ma bai tafasa sosai ba, cikin sauri ta rike kan inayah tana mata addua tana kuma sassaitawa zata kai mata baki kenan sai ga dandanko ya doka sallama daga waje yana lekowa taciki..

tun basu ma gane shi ba yafara daga wargajin muryansa daga kofar xaurensu yana cewa ba'a amsa sallama ne agidan nan? kai malam juma kai buzu juma salama aleku... waye yake amai haka..

taawure ta daga kai zata amsa sai ga juma ya fito fuskar sa a mugun dore yana kkrin kafa hularsa akansa ko kallonsu baiyi ba yasakai zai fita..

tunda taawure ta bawa inaya ruwan maganin sai aman kawai takey jikinta na wani irin kyarma kr kar kar ayanah ta riketa sosai tana hawayen itama

daga kofar zaure juma ko amsa gaisuwar dandanko baiyi ba yahaushi da masifar katsemai baccin da yayi da sallamrsa
shikuwa nan ya fafuko makirci ya soma gaya ma juma ai ya gamo da tawure ne ajeji ta debo magani shine yazo ya dubasu ko lafya

suna cikin wanga tattunawa suka kara jiyo sabuwan ihun inaya tana cewa wayyo Allah cikinta cikin matsancin yanayi mai rikitarwa ga ruwan maganin na fitowa ta baki ta hanci,

da wani irin mugun tsinkakken gulma da tsegumi dandanko ya kusa ture juma ya shigo ciki har suna rige rigen karasowa tsakar gida

jikin juma har na rawa yahau cewa kai kai kai lafiya kuwa innari meye haka kukam kun shigga uku da wanga kazanta wani irin ragoncin ne haka?

cikin katseshi taawure tace me gida ciwon cikintan ne ya tashi..

wani caraf dandanko yace ciwon ciki ne har shine take amai? kai taawure ki rika fadin gaskiya kode taciyo wani abu awani waje awajen maza?

banza tay dashi ta kyalesa da juma dayake tuhumarsa akan manufar maganansa, ita kam zage karfi tay ta dauke inayan cak takaita kan tabarma ta dan wanke mata jiki snnn ta shimfidata tana mata fifita ayanah kuma tuni ta dau tsintsiya da abun kwashe datti tafara kwashe aman tana gyarawa..

musu ya kaure tsakanin juma da dandanko dan har waje ya rakasa yana tuhumwr sa akan abunda yke nufi da yarsa

dake dandankon mugun annamimi ne sai bai fito fili ya gaya masa cikin shege yake harsasshe wa inaya ba, baqaqen magana da misalai na yan matan kauyen da suka taba gumtso cikin shege kawai ya dinga kafa masa misalin ciwon inayan dashi yanamai ce masa saishima yay hankali, dan yanzu haka sarakunan garin sunsaka doka muddin yarka ta mutu d cikin shege bazasu mata sallan gawa ba shureta kawai zasuyi a rami kamar dabba snn su binneta a walaknce dan karta lalata musu kasa da kazantan zina.

duk dama juma mutum ne mai kaifin tunani yakuma san halin dandanko da gulma da son yaɗa karya dan ya tada zanne tsaye saidai sosai maganganun suka fara taɓa mai zuciya dan yawancin zarginsa akan yaransa yana tsayawa ne akan su mazinata ne kuma abun kunya kawai zasu jawo masa

da wnn tunanin aransa yaƙi ma dawowa gidan kawai ya miƙa sawun kafarsa ya shiga gari neman abincin karyawa da zimman kafin ya dawo hala innarin ta dawo cikin hayyacinta zai hadasu duka yaci ubansu har sai sun amayo masa gaskiya game da ciwontan nan...#surayyahms
idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*

*WATTAPAD @SURAYYAHMS*


*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*


#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025
[01/11, 15:51] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: Susum writer:
_ABUNDA KE ƁOYE...._
_Love And scandal💕_
*_Arewabooks@surayyahms_*


1️⃣2️⃣
tafiya me dan nisa juma yay kafin ya samu ya shigo cikin asalin kauyensu ta majiya, lokcin daf ana neman wajejen karfe goma na safiya kai tsaye gidan da ake saida yar tsame da dan wake ya wuce batare da ɓata lkci ba yabiya aka masa hadin dafa duka na wake da danwake ga kuma yar tsamensa da zazzafar kokonsa agefe yana turiri..

saidai tunda ya zauna akan teburin gabaki daya saiyaji ya kasa taɓa abincin, lura da dabi'un kananan yan matan dake taya aikin saida abincin kawai yaketayi musmn yadda yagansu yara kanana suna magana da maza anyhow babu alamar kunya da kamun kai atattare dasu da kuma yadda suke muamala da duk wanda yazo siyan abinci. har cikin ransa kallon marasa tarbiya dama yake musu, suna giftwa agabansa gaba daya sai yaji hanklinsa na tashi , zantukan dandanko ne suka soma dawowa masa kai batun rayuwar yaransa ayanah da inayah, dan shide yasan acan tudu baisaka musu wani mutum yanamai bincike akan rayuwar taawure da yaransan acan ba sabida gani yay agidan hajy mairo me tuwo suke kuma hajiya ai matsayin goggonta ne sai baikawo wani zargi ko matsala da zai afku da tarbiyansu acan ba, saidai tunda yaji har dandanko ya fara kawo tsegumin ko hala wnn irin rayuwar banzan sukeyi acan saiyafara ji aransa kmr fa biri ne yay kama da mutum da irin ciwon ciki da amai da inayah take dayaki warkewa sam.

gidan hajy mairo gidan jama'a ne kuma yasan dolene hala yaransa suma suna hulɗa da mutane acan sosai, kasa hadiye kunun da ya kurba yay ya zauna shiru cikin tunani, cikin ransa yace toh wayasan ko dagaske ne innari takwaso masa abun kunyane suke raina masa hankali duk atake saiyaji yarasa meke masa dadi.

cin abincin yake tmkr na dole yana Allah Allah ya fita kawai ya fara bincike, can sai ya tuna cewa da akwai wasu fulaninsu nan nan majiya masu saida dabbobinsu acan tudu toh hala zasu iya gaya masa wani abu game da rayuwar yaransa.

bayan kamr minti 20 ya gama cin abincin tare da gudanar da duk wata lissafinsa,ya taso kenan zai fita sai ya lura kame yanayin garin ya fara sauyawa kamar ma haddari ne keson tasowa, hakan yasa bai wani bata lkci ba ya biya masu abinci kudinsu cifff snn ya nufi cikin anguwa agaggauce domin neman masu basa shaidoji


ata fannin taawure kuwa matsanancin damuwa da tausayin yarta inayah sosai ya fara hanata sukuni, dan banda kuka, addua, da wayyo wayyo cikina babu abunda inayahn take kanyi gwanin ban tausayi, ganin halin da inaya take ciki wanda tamkar magungunan data bata gabaki daya basuy aiki ba yasaka taawure tay shahada aranta tayanke wani babban hukunci na zaɓar ran yarta akan aurenta da juma..

wann ba tunanin me sauki bane, bakomi hukunci me dadi bane har a idon Allah

amma tasan in har batakai inaya tudu inda akwai likita sun same taimako ba hala yarta inayah zata mutu anan da ciwo kuma awahale, at same time cikin zuciyarta tasani inhar ta fice agidan taje tudu toh saki uku tabbas ya shiga tsakaninta da juma kenan rabuwa ta har abada..

duk sai ta rasa abunda ke mata dadi but the more ta kalli yanayin inayah sai taji rauni me tsanani ya kara rufeta

cikin wnn zullumin she waited for a while cikin da nisan tunani, can dai dataga garin ya fara hada hadari jikinta amatukar sanyaye ta miƙe tsaye tabi ta shiga dakinta, kallo daya tay ma dakin ta tuna ranar da aka kawota ciki tun aurensu na danye tana amarya, lokcin mijinta juma na sonta sosai, kai bazaka taɓa tsammanin cewa wani abu na tsana da cin mutunci zai shigo cikin rayuwar aurensu ba. wasu abubuwan inta tuna takejin gwiwarta yay sanyi, cikin rauni ta tsuguna adan wata kusurwa hawaye na zubo mata da tsananin karsashin zafin rusa aurenta da zatay ynxu aranta tayi kuka tay kuka sosai tagode ma Allahnta

dakyar ta iya bushar da zuciyarta tamiƙe tahau tattara duk wani savings inta na kudi da few kayanta na sawa ta sakasu a yar jaka saura ta daure su da tsumma,. tana gamawa ta fito da kominta a jakan snn ta daga ayaanah tadora mata jakan akai tace mata taje maza ta sako takalminta a daki ynxun nan snn ta fito su tafi,

ayaanah bata fahimci komi ba ta shiga dakin sun da kayan akanta tanamai lura da yanayin rauni da taurin rai dake kwance akan fuskar mahaifiynta wanda sosai ya bata tsoro da kuma fargaba. ta shiga ciki bada jimawa tazo ta samu tawuree har ta lallaba ta saɓa inayah abayanta ta daureta da zani kamr ba yar 12yrs ba, nishi me tsanani kawai inayahn takeyi batama hayyacinta banda ma dauriya irinna yaran buzaye da fulanin jeji da bazakace a age intan nan har zata iya daurema azaban zafin ciwon ciki datakeji ajikinta ba.

kafin kace wani abu taawure ta umarce ayaanah akan ta wuce gaba. kai tsaye suka fice agidan suka dau hanyar tudu, dan tsabar wahalan dataji inayahn takesha sai taji ko nauyinta bataji tafiya kawai take da sauri sauri kuma ƙarfin zuciya dukansu ukun suna ambaton Allah yanayinsu cikin rauni har suka isa garin tudu acikin kankanin lokci sai gasu kofar gidan hajy mairo mei tuwo..

lokacin kusan daf ake da karfe sha biyun rana amma dake hadari ya dan rufa sai wajen yay duhu da sanyi, suna isa taawure tay maza ta sauke inayah akan dakalin tsakar gidan dan izuwa ynxu inayahn tama dena yin motsi sai shure shure fuskarta yay fayau yay fari sosai, dan tsaban azaban datakeji acikinta wani dan uban nishi kawai takeyi idanunta sunyi farare soll sun jujjuya tay lagwas kmr lokcin mutuwarta take jira

ayanah tana aje kaya dake kanta tun taawure bata furta mata komi ba tay marmaza ta falfala da gudu ta fice kasuwa domin kira musu hajiya mairo me tuwo, daga nan kuma ko minti biyar da zama a dakalin basuyi ba inaya tafara jin wani irin sanyi sai kawai tafara ririike jikin taawuren tana shigewa jikinta sosai kamar wata mai ciwon nakuda tana nishi ahnkli kuma me nauyin gaske inda yake ciwo acikinta sosai yay tozo agefen dama ya kumbura

acikin matsanancin rauni baƙinta dake bari yahau cewa umma am, umma...ina ganin kamar mutuwa xanyi umma

atake idon taawure ya cika da hawaye tana juyowa idonsu ya sarkafe cikin na juna, ahnkli cikin nishi inayah me sauka tare da wani irin makodan hawaye tace "umma dan girman Allah kiy hkri ki yafemin musmn ma da aurenki da baba ya mutu yau a sanadiyata..umma dan Allah ki yafemin.. umma ki yafe min dan Allah karna mutu da wann shaidar akaina,.. kusan maganartan dakyar yake fita cikin nishi amma kuka take yi sosai taawure dake hawaye bata iya cewa komi ba ta rungumota ajikinta sai a sann ta itama fashe da kuka mai rauni itama inayahn sai ta kara fashewa da kuka sosai, ahnkl cikin lallami taawure tahau shafa mata baya tanacewa" yi ishiru abunki innari, ni bakimin lefin komi ba, ai danabarki ki mutu acan majiya gara auren nawa kawai ya kare..kinga shi mutuwar aure qaddara ne zanyi hakuri dashi, amma idan na barki kika mutu banyi komi akai ba hakan zai zama mini babban ciwo a rayuwata da zuciyata har na mutu baza yafema kaina ba.

kara kankameta inayah tay tanata bata haquri dukansu suka taru sunata kuka sosai...

sunjima ahaka sai can kafin taawure ta share hawayenta tafara ma inayahn nasiha masu ratsa jiki akan tay hqri da ciwon nan jarabawa ce kawai da Allah ya aiko musu.

ayayinda ayaanah taje har kasuwa tana haqi, koda ta shiga shagon hajiya taci neman duniyan nan ma hajy mairon a shagonta amma bata sameta ba, hanklinta ya dada tashi, gata yar yarinya badon ma tanada rare beauty ba da babu wanda zai kula metake cewa, da kyar dai ta samu wata yarinya yar karama kusan age mate din addanta inayah anace mata Ruthy, kallo daya zaka mata kasan chirista ce sabida yanayin shigarta da kuma gashin doki dake kanta, she is like 12yrs old amma tana da girman jiki, ankawo ta shagon ne a matsayin sabuwar mai aikinsu wanda hjy mai tuwo ne taje ta daukota cikin satin nan agidan wata magajiyar karuwai dan kusan sau biyu kenan ana case nakkrin abusing in ruth sexually at dis very young age of 12yrs, sabida angane batada iyaye tsintar ta akayi a kwali anjefarta a kwalbeti, irin yaran nan da karuwai keyin cikinsu su haifa su zubar dasu a kwali..

hajy mairo tunda taji labarin ruth hakanan tay ruwa tay tsaki har saida ta kwato wann yarinyar daga shiga ukubar karuwanci a danyen shekaru a gidan magajiyan ta bata aikin shara da aika a shagonta dan kar acigaba da lalata mata rayuwa.

ruth din ne tazo tafara kula ayaanah sukayi magana harta gaya mata cewa ai hjy nacan police station suna case da mai anguwa yauma wata sabuwar case ne tsakaninta da wasu kidnappers aka bude

,..abunka da yarinta damuwar aayana kawai naga jikin addarta ne, haka ta sako ruth din agaba da magiya har sanda ta mata jagora takaita police station da kyar ma aka barsu suka shiga snn taga hjy mairo wanda suna hade ido rauni ya rufeta tafara panicking tana hawaye tana gaggaya mata cewa har sunzo da ita da mamanta da addanta jikin addanta yaki yay sauki.

ba agama rufe case da su mai anguwan tudu ba hajy tay maza maza taje ciki ta rokesu aka bata daman zuwa da dawowa aka bata 2hrs sabida case din nata da yan kidnappers kusnn babba ne so kawai ake a cimma wata matsaya yau basai ankai gobe ba.

ana basu 2hrs din nan hajya mairo tariko hannun ruth da ayanah wujiga wujiga suka kamo hanyar gida a abun hawa, tun daga zaure ta doka sallama suka samesu a manne da juna taawure ta tungume inayan ajikinta inayah tay lumui ta lumshe idanunta sosai ,

hjy nazuwa tadora idanunta akan yanayin inayah ganin yadda ta dawo wani iri kmr me kanjamau yasa ta fashe da kuka cikin kankanin lkci tafara raki tana salati tana sallamewa tana tambayar taawure meya faru cikin tashin hankli, tun ba amata bayani ba tasaka marmaza aka tada kura aka dauki inayahn abaya kamar yar tsana suka fito wqje wujiga wujiga aka sata abun hawa dukansu su hudun suka wuce da ita dan karamin Primary health care facility dake cikin tudun agaggauce.


suna isa cikin asibitin kuwa ruwa ya fara sauƙa kmr da bakin kwarya, da Allah ma yaso su yau akwai likitan dayazo daga cikin kano, duk dama sauri yake shima zai karkare aikinsa zuwa gobe juma'a zai koma cikin garin kano yanayin jikin inaya dayagani yasaka ya tsaya dan ya taimekesu

gurgura inayan akay a gado mai taya aka kaita har wani daki aka fara saka mata ruwa snn aka ja jininta aka fara mata yan gwaje gwaje ayayinda taawure da hjya mairo da ayaana da ruth suke tsaye likita yana musu tambayoyi,

ayaana ce tafi bada amsarsu sabida kusn komi na alaman ciwon addantan a idanunta ya fara..

bayan likita ya dau duk wani rahotonsu ya tafi dashi ciki nan hajya mairo tafara mita da masifa wa taawure kamar Allah ne ya aikota, akan meyasa tuntuni taawure bata dawo tudu sun nemi waraka ma inayah ba,

saidai koda taji taawure tahau furta mata labarin danbanzan duka da kuma tsauraran kalmomin da juma ya furta akanta tare da jarumtar datay yau na kashe aurenta danta ceto rayuwar inaya sai gabaki daya jikin hajya mairon yay mugun sanyi, atake kuma sao ta koma lallashinta tana bata hakuri.

lokcin ruwa akeyi amma ba sosai ba tunda sukaga likita yanata aiki baice musu komi sai suka dan samu sukuni aransu, har hjy mairo take basu labarin case inta da wasu mutane da aka samu rahoton cewa yan kidnappers ne kuma sunce zasu saceta, shine fa aketa case da ita har da mai anguwa akan zasu kafa vigilante group a kusa da kofar shagonta snn za'a basu daman rike bindiga sabida tsaro..

jin abun babba ne yasaka tawuree tace mata tunda jikin inayan ma da alaman sauki kawai takoma station agama case din in yaso in tagama ta dawo, da kyar dai hajy mairo ta amince da haka, koda zata tafi ita dayanta taje har ta dakin da aka kwantar da inayahn ta sameta wanda suna hade ido hawaye ya cika idonta tazo tadan rungumeta tayita mata adduoin samun sauki masu yawa tasaka mata albarka sosai.

itadai inaya sai cewa take ayafeta takuma gode tagode da irin kulawar da suka bata sai kuma tay murmushi me cike da hawaye me rauni.

ahaka dai da wann kalman har suka rabu da hajy maituwo dukansu suna zubar da hawaye ma juna at same time suna murmushi ma juna. hjy tana ficewa a asibitin tabi ta aje ruth a shago snn ta koma station agurguje da gunjin tausayin inayahn a zuciyarta

bayan tafiyar hajy maituwo ba da jimawa taawure tay zamanta a reception daga ita sai ayanah, sallahn azhar ne kadai ya dagasu lokcin kuma already ruwan saman yadan lafa sosai saidai wani sabuwar haddarin ne yake kan sake tasowa gashi har yanxu likita baice musu komi ba.



Dagata dayan bangaren at around 3:40pm na yamma ibaad ya bar school of medicine ya dawo gida agaggauce dan kansa har wani irin ciwo yake masa tsabar practical activities da yay a club dinsun yau.

tun 11am na safe ya gama normal school lectures, frm 12-3.30pm dinnan duk acikin club practical lab dinsu ya kareshi sun dukufa sunata practical kala kala akan major field dinsa na cardiology at an introductory level.

yana isa gida kai tsaye yahaura sama dama kuma dakinsa is always neat, wankansa kawai yay sharply yasan dake maheer bai dawo ba so baida wanda zai iya bata mai lkci, within few minute ya fito ya kintsa kansa anitse yasaka kananan kaya ajikin sa farin rigan raymond T shirt original cotton me dogon hannu da bakin wando suade da wata sleek sneakers yabi ya saka wata original black baseball face cap data masa mugun mahaukacin kyau kagansa kamar balabe except that he had this glowing yellowish body tone. shigarsa simple yet classy nd smart, bakaramin kyau yayi ba musmn da ya toshe idanunsa da fararen rayban spec da shirin zuwa anguwar tudu agaggauce dan yana so ya samu yajeshi ayau din nan dan komin dare yay makansa alkwari yaudin zai dawo gida dan yanada abubuwan yi a lab dinsun gobe sosai.

bayan ya gama shirinsa tsaf ya fetsa turarensa original dior souvage me sanyi snn ya fito ya dau jakar bayansa da wayansa yana tafiya anitse har ya same ammi babba a falo tana kallon indian wani series..

qamshin turarensa me aji ya saka ta tafara daga ido ta kalleshi itade duk ta kallesa kyaun fuskar uwarsa take gani dan haka

15 / 88