Chapter 34 Reading Abunda Ke Boye Complete Hausa Novel READ HAUSA Novels

Abunda Ke Boye Complete Hausa Novel

Author :  NONE Category :  African Stories & Novels

Chapter   34 / 88

99K to 102K   out of 262.2K words

ta amince ta karbi wayar, ammi karama ta rakota har kofa snn ta fito ta mikawa mamanta wayar.. suna hade ido tace "baba ne yace wai inbaki.."yi tay kamr bazata karba ba taja wani dan banzan tsaki nurse hasina ta sa hannu ta karba ta saka mata akunne.

tsabar baqar kishi tana amsar wayar hawaye suka fara bulbulo mata a ido cikin salon makirci tafara masa bayani wai tazo ne ta zauna da yara a matsayinta na uwa ita batasan meyasa sultana tanamata ihu ba..
..duk yadda ta murda maganan da habaici da komi waidan ya kyaleta ta zauna yaki sam yace mata kawai taje gida inyaso zaizo sai suzo tare dashi

dakyar ta amince mishi zata bar wajen ta katse wayar jin zuciyarta na tafarfasa kamr zata fadi kasa haka tadinga jin jiri nurse hasinance ta janye hannunta da sauri suka fita waje..


sultana ta dawo da waya ita ta sanar da ammi karama cewa maman nasu ta koma gida..

batace musu komi ba har saida suka sha su ice cream da chops da maheer ya siyo musu snn ta fara musu nasiha game da muhimncin yafiya akan ammi babba musmn ma bangarem sultana dayanxu take gudun maman nata sosai tana mata kallon muguwa.

dakyar ta cire musu tsoronta aransu ta jajja kunnensu ta musu fada akan sudinga jin magana suna kiyayan abunda zaina bata ma ammin babban rai.

itade ayaanah damuwarta baifi taji ance awajen ammi karama zata zauna ba dan harga Allah data kalle ammi babba ynxu saitaji kmr duk abunda ya faru ranarne suka dawo mata kanta.

yau kusan kwana takwas kenan da mutuwar addanta haryanxu bawai abun ya gama fice mata arai bane, but she feel more nd more secured kwana biyun nan data kasance a karkashin kulawar ammi qarama..


har waje bakin gate nurse hasina ta raka ammi babba wacce ta fashe da wani irin kukan takaici tace "Wllh hasina har ynxu na kasa yrda cewar fatima tafini daraja a idon miji na nakeyi, kiga yar bura uba ta kirasa awaya tasashi ya koreni akan yara gani nake kamar mafarki nakeyi...

cikin jimantawa nurse hasina tace ai dama nagaya miki wallah fatima ta shanye shi tass danma bakiga jigilar dayake mata a asibitin nan bane shiyasa da tuni kin hadiye ranki kin mutu.

tace "aiko nagani yau..tunda ider ta bashi akaina kuma ya aikata..baki ji ynda xuciya ta ke min xafi ba, Kuma fa kojin magana ta baiyi ba ita kuwa tana gaya masa har ya dauka wllh ji nake kamar in banka ma asbitin nan wuta kowa ya huta..nurse hasina tace "Ba wani banka wuta kawata, ke kika fara bata chance ta kwace maki miji ta xama itace kan komai a rayuwarsa....yo uban meyasa zaki bari har ya koreki agidansa ...ai su maza insun gaji dakai babu abunda bazaka ka gani ba..

ahatsale tace "Duk ba wannan ba, nata bai tsaya min kamar yanda na yarinyar ya tsaya min a rai ba ..ni ki bani shawara ta ina xan fara, me kike ganin xan ma wnn yarinyar in huce takaici, ni dai baxan kasheta ba amma ina son abinda xan mata kisa ya fi mata alkhairi da shi, wllh na tsaneta, na tsani duk wani me son ya ganta kusa da shi ma, wallhi sai na tarwatsa rayuwarta duk dai akanta akamin wnn irin walakatacin..nida mijina da yarana amma wai wata macen ne take bashi oder akanmu?duk ba yarinyar ne ta jawo min ba...

nurse hasina tayi dariya tace "Ni fa ban wani jin yarinyar nan. minti nawa ne xa a kadata ta bar gidankin ma gaba daya, ita dai wnn yar iskan matar ya kamata ki fara tunanin ynda xa ayi da ita ba yar yarinya ba.

tace "To ni ta yarinyar nake tukun dan tafi kona min raina..dan wallah bana kaffara karya sukey bazasu dagata agaba na ba, haka akamin akan ibaad amma gashi haryau yaron nan na nanike min agida har anfi fifitashi akan yarana. hasina bazan fa yadda asake lakamin wata walakntaciyar creature a rayuwata ba.

..nurse hasina tace "toh inhar haka kike tunani ki kwantar da hankalin ki ai wnn me sauki ne

...dada saukar da murya kasa tay tace "ke kuwa raihanatu kamr baki da basira why dont u just use a reverse physcology? kawata kinuna musu kin shiryu sosai, draw the girlbcloser nd spoil her...sai har ansake jiki dake wallah ki barar da yarinya
..zakima iya batar da ita ta shiga duniya kuma kifito kifisu yin kuka...ba yar kauye bace??my friend, u can send her back to where she comes frm inyaso intaje ta bata ma ahanyar garinsun ohon su kedai ki wanke kanki tasss tukuna kafin ki musu mai zafi..

ammi babba tace Allah ko kawata? tace ehh mana, yanxu dai ana jirana a nurse station amma inkika dawo zamuyi magana..da harara tace ba wani nan, ke din ce xan gani hasina...keda idan kika tafi gantalin ki ba sai an gan ki ba?

nurse hasina tayi dariya tace "Ai ynxu na daina yawace yawace a waje kedai anjima zamu hadu zan gaya miki salo salo da zakibi...

ammi babba tace Toh ni dai anjima xan taho asibitin nan dani zay zama kar ki fita don Allah...tace toh.. Daga haka suka rabu..

Bakin gate din asibitin ammi babba ta nufa ta kusa cin karo da ibaad shima xai shiga cikin harabar asbtin a mota..

wani ja baya tayi tana kallonsa baima lura ba yace sorry, bata iya ta amsawa ba har dai ya wuce ta yay parking ya sauko, ta juya ta bi shi da kallo ko kiftawa babu kasar wuyarta tace "munafiki tsinanne kawai
ji yadda yay wani kiba..." Tana tsaye tana kallonsa har ya iso inda take cikin ladabi yace"ina kwana mummy" wani irin dauke kanta tay kmr bazata amsa ba da tuna maganan nurse hasina kuma saita amsa shi ciki ciki...ta kuma cewa "dama gida zanje saika kaini gidan inyaso ka dawo daga baya mamankan ai ba guduwa zatay ba.

shide baice mata uffan ba yay gaba tabiyosa ta zauna agidan baya yaja ta suka wuce gida...

har ya sauketa ya juya uffan batace mai ba ta shiga gidan ta haura sama sashenta taga kmr yadda tabar gidan hakan tazo ta samesa ko wayatta ba adaga mata daga kan table ba.

tana cire hijab ajikinta ta watsar da shi snn ta dauki wayarta da is almost worn out of battery dan banda tarin missdcalls da text daga wajen zinariya da kawayenta bataga komi ba tangible akai ba

maza maza ta kira mai aikinsu saddiqa akan tazo snn ta kashe wayar ta jona a chargi tafada wanka, wanka na musmmn tay ta fito ta cancanda kwalliya ta saka wata arniyar brown code lace riga da zani, kafin nan mai aikinsun ta iso ta bata oder akan ta kalkale gidan ta gyara koina snn ta dafa musu abinci da zai ishesu yanxun nan.


ata dayan bangren kuwa koda ibaad yakoma asibitin mahaifyarsa batace mai komi gameda zuwan ammi babban ba duk dama yagaya mata shiya kaita gida face saida maheer ya dawo abakin sultana sukejin labarin cewa ai tazo tace tanason ta karbi jinya sunata shan mamaki aransu.


karfe daya na rana nay sharp mai aiki ta gama girke girken abincin ta zuba su a cooler duk akasa a basket ta shirya komi, kamar dai yadda aka bata shawara komi tanayi ne harda extra dan ta nuna musu cewa tay nadama tashiryu amma cikin ranta bakaramin tafasa yakeyi da bala'i ba..

bayan azhr bappa zaidu ya shigo gidan ya sameta tawani ci ubn kwalliya shikansa yasha mamakin ganin abubuwan datay duk ta dage tashirya maganan zuwa asibiti. bai wani ja dogon magana da ita ba yaje sashensa yay wanka ya shirya kansa cikin manyan kaya arnd 2 suka nufo asibitin atare, luckily enuf yau ibaad ne kawai yaje eatery ya siya musu abinci suka ci ammi karama bataje gida ta musu girki ba

...zuwan su ammi babba ya saka dakin ya zama very cold ita kadai take zuba makirice makrcenta. wai itace yau harda bawa ayaana abinci abaki, ana hira sama sama, kowa na ciki na ciki daga karshe bappa zaidu ya musu nasiha akabar komi a cewa ya wuce....

haka ta naninke ta zauna musu a asibiti itama har izuwa dare snn tasako mijinta da yaranta duka agaba suka koma gida...

kan Ammi karama sai ya daure kadan da irin sabon salon makricin datagani awajen ammi babban yau amma abun bai wani dameta ba sabida tasan duk tsiya kayan farau a farau yake karewa duk wann makircin bazaiyi nisa ba.

agidan ma haka tabibbi dakunan yaranta ta shawo kansu msmn ma sultana wacce dakyar tazo tafara sake jiki da ita har suka dawo daidai. abu daya ne kawai bataci nasarar sa ranar ba yadda tay tay su samu wani nitsuwar aure da bappa zaidu
adaren yaki mata sam yace mata ya gaji da ssafe kuma tun kafin ta farka taga wai harya fita masallaci tun ba akira sallahn fjr ba

da haushin hakan ta fito a sashensa taje nata dakin ta kimtsa kanta ta sake fitowa

yau ranar sunday ne dan haka daknta tay musu heavy breakft a gidan akaci snn tasaka mai aiki ta shirya nakaiwa asibiti,still haka yauma ta dinga zuba kwainaneda makirce mkircen habaici itadai ammi karama batace mata komi.

yau gbaki daya bai wa kowa dadi ba, musmn yadda tay babakere komi na ayaanah sai tace itace zatay, haka dai kowa ya zuba mata ido tanata wahala. a fuska sai ta nina tana farinciki da aka sakar mata komi amma ranta mugun haushi takeji dataga ammi qarama ta ja ajnta taqi cewa komi ta kyaleta tana rawan tana kidan abun bakaramin kona ammi babba yake ata cikiba, taso ace abun ya zama musu kamar comptetion akam miji sabida ta nuna ikon cewa itace fa mai yara da kuma miji,

sai kwata kwata bata samu fuskan haka awajen ammi karama ba banda ma kara sakar mata nauyin komi datay, dan yau sunday ko abincin safe data saba zuwa gida ta musu batay ba, yadda suka farka da ayaana wanka kawai sukayi suka zauna, aka kawo breafst dinkuma taci kadan ko ajikinta..

tsakanin sartuday da sundayn nan kawai bakaramin dawainiyar asbiti ammi babba ta dinga yi ba, tanayi ne danta burge ta kuma cusawa ammi karama baqin ciki amma inaaa abun baiya mata dadi dataga ba kulata akeyi sosai ba. ga kawayentanan agefe sai zugata suke tana zuba abubuwan bajinta tana kashe jiki ma bappa zaidu dan aji haushi amma harga Allah inta koma dakinta sai tay hawaye musmmn yadda ammi qaraman quietly ta dauke ido akansu tabi tacire hannunta a komi ta zuba mata ido kuma inta kawo abincin ko sau nawa ne arana haka zasu ci ita da yara

ranar monday kusan komi yay matan daban sabida kowanne yaro ya wuce schll, so a gida duk akayi breakfast, iyaka abincin asibiti kawai suka kawo asbitin ita da bappa zaidu tanata famar makale masa abu kadan tawani jinkina da jikinsa, har yagaji da yarantan tan yabarta awajen yawuce aikin shima.. duk a tunaninta yar kisisin datake yin yana taɓa ammi karama a zcya, sede kuma ina haryau bata gane komi ba, tun safen yau din ake rububin sallamar Ayaanah haka tay babakere ta amshi duk wani takardun sallama tana cike cike komi aka tambaya itace ke saurin amsawa, still ammi qarama ta kyaleta da kayan wahala tay nan tay nan, ita kuma tay xamanta a gefen ayaanah tanata chating abunta da bappa zaidu game da batun tafiyarsu conference gobe batare da sanin ammi babban ba. soyayyarsu me sanyi suke sha awaya, suna hirar aiki da wayo yanayi yana lallabata shikansa da tunanin ko ranta na baci ne da irin azarbabi da habaice habaicen da ammi babba takeyi itakuma nuna masa takeyi batamasan tanayi ba.

anty hauwace inta dan leqo zasuyi ta gasar jefawa kansu habaici da ammi babba, hanklinta sosai ya tashi data fahimce cewa kamr sunsan labarin halin datake ciki da zinariya, itade ammi karama batacewa uffan harsugaji suyi shiru.

at around 1am likita yazo aka sallamesu amma basu bar asbinta ba sai can wajajen karfe uku da saura da su ibaad suka taso a schll

duk da wann uban sanyin halin da ammi babba take nunawa ko kusa da ita ayaanah bata iiya daurewa tay zaman minti biyu, duk kuwa nasihar da ammi qarama take mata da dare amma stil itade tana jin mugun tsoron sakewa da ammi babba

tunda suka kamo hanyar gidan zuciyartta sai bugawa yakeyi

har dakin sultana ammi karaman kuwa takaita
ganin ta damu sosai yasa ta daure ta jira agidan har saida bappa zaidu ya dawo kafin nan tace musu zata koma gida.

duk wani shirin tafyarsu ya gama yana son ace shiya kaita gida dan su tattauna amma kiri kiri ammi babba tay ruwa da tsaki ta hana hakan yuwa, sai tabi ta nanike musu tay tama ammin godiyar makirci, karshe dai maheeer da ibaad ne suka rakata gida daga karshe a chat kawai suka karasa maganan su..

gobe by 9.30am jirginsu zai tashi tareda wasu officials maza hudu mata uku as the core reprenstative na sabon
kungiyar philantropism da suka budeshi. ammi qaramar itace president kusan dolene komi sai anyi da ita, shikuma bappa zaidu kamr matsayin uban gida yake ga kungiyar gabaki daya kuma baifiye son yana kyaleta tana tafiya me nisa ita dayabba.

yau ammi babba ta farka da wani irin farin cikin jin taci nasarar yaface mijinta ajikin fatima snn by now tasan kowa yagane inda ta dosa na sauya halinta musmmn akan ayaana.

abu daya ya rage mata shine ta amshi kudinta da aka mata asara a wann satin, sosai tashirya salo salo na makircin nuna kulawa kala kala ga ayaanah domin ta shawo kan bappa zaidu cikin sauki ya bata kudi tamaida ma zinariyar mace da ta sakota agaba wanda inbandan kawarta hajy ramatu tanacan tana nema mata alfarma ba da bata san ya zasu kare ba ahaka ma yanx kwata kwata bata fiye barin wayatta a on ba

aranta jira take inta amshi kudin ta biya, in 2-3 weeks intaga basu dauki yarinya agidanta ba zata aikata mugayen plans inta na batar da ita gabaki daya inyaso tafada wani duniyar ma baidameta ba dan tasa aranta cewa bazata taɓa rike ayaanah ba.

wani dan uban wanka taci da zimman yau zata fara nuna wa ayaana soyayya na musmn dan sabida ta samu karbuwa awajen bappa zaidu, tun safe kuwa tafara aikata haka taje ta tashesu lovingly sukayi wanka akazo akaci breakfat duka dinning table like one big happy family har sultanah suka wuce makaranta..

dake bappa zaidu na shirin tafiyarsa bai fita agidan yau da wuri ba, haka tabishi har sashensa ta dinga kawo masa salo kala kala na soyayya wai danta nuna masa ta shiryu shide yanata mamakinta aransa musmnn datace mai zata gaya masa asalin meya tunzirata tay ma ayaanah duka ranar inya dawo. niyyarta shine ta shimfida masa karya kmr yadda tama maheer ranan, sai acikin karyanne zata tagabatar masa da asalin buqatun ta na bukatar karban kudin biyan asarar da tayi da wayo wanda tana da yaqinin inta lallabesa atake zai bata dan wnn kudin tasan bakomi bane awajensa.

shiduk bai gane wann salon nata ba but deeply in his heart yasan wann rawan jiki da kirkin datakeyi musu bazai wani daure ba.

Bayan duka yaran sun watse schll mai aikinsu siddiqace kawai take kulawa da ayaanah a daki, while ita kuma ammi babba tana taya bappa zaidun shiri harya gama yasaka wata dark navy blue very expnsive men voile data masa mugun kyau yayi adonsa yau bana kadan ba, yanata haba haba ya gaya mata zaiy tafiya sai aka kirasa awaya daga office sai gabaki daya yabi mance bai gaya mata ba har kuwa sukay sallama yafice agidan agaggauce, saida driver ya wuce dashi office yayi signing wasu muhimn files snn ya wuce airpot within like 5minute su ammi qarama da sauran team din duk suka taho jirgin 10am sharp ya lula da su kasar waje.


sosaii ammi babba ta shirya tarbansa yau da yamma, haka ta saka mai aikinsu taje kasuwa ta siyo musu fresh fresh manyan dakwulan turkey da spices tazo dakanta tay aikinsu tasha wahala har da kiran anty safeera koda zata gaya mata sunan spices da ammi karama take sawa dan tayish yay dadi kamar nata duk dan ta samu shigewa zuciyar mijinta da maganan karban kudin nan tayi ta huta da jarabar zinariya.

bakaramin wahala tasha kafin ta girka abincin yau ba ,dan saida akaje mata kasuwa neman spices din da ammi qarama take using a abinci kafin ta kammala wasu abubuwan, tay su fried rice, tasaka su hanta da kayanykin lambu, turkey dinn nan kuwa aka raba biyu daya aka soyasu, sauran kuma akay stew dashi dayaji lodin mangyada da maggi da uban barkwano.

kafin ma tagama aikin gabaki daya ta galabaita harma bata samu lokcin kula wata ayanah agidan ba. 1:30pm ta kammala komi ta shiga wanka tay sallah snn ta kwanta domin hutawa.

trout wayarta a kashe yake dan batason ta kunna bare zinariya ta ishsta da kira dan haka kwata kwata bataga text messg din da bappa zaidun ya aiko mata ba bayan har sun sauka a kasar waje.

baccinta ta shara me lafya ta farka wajajen uku saura ta samu har sultana ta dawo daga schll taci abinci tana zaune tare da ayaanah adaki suna hirarsu na yara, ta tsani taga sultana tana kawance da ayanaah amma kuma wnn karon babu yadda ta iya saita kyalesu, iyaka instructing inta kawai tay akan idan su maheer suka dawo daga schl ta kai musu abincinsu daki sabida tafiso ace yau ita daya zata tarbe mijinta akan dinning da uban girkin data shirya masa irinna ammi karama dan yaja santi suyi maganan kudi

tana gama instructing din sultana ta koma dakinta tacigaba da bacci batare da ta kunna wayartan harynzu ba

daga can kasar waje kuma a hotel daya dukansu suka sauka daga dakinsa saina ammi karama saina sauran mutanen ahaka ajere. wanda wanka kawai sukayi suka fito suka tsunduma hidimar daya kawosu tun around bayan asr.

ganin gidan was soo boring
yasa sultana tajawo ayanah suka fita can waje tabayan shades in gidan suka zauna agaban pool tanata bawa ayaanah labarin school dinsu, daga bisani sai taje kitchen ta debo musu dakwalan namomin turkey wanda aka soya har pieces uku manya tana kawo tabawa ayaana guda daya,

34 / 88