Chapter 20 Reading Abunda Ke Boye Complete Hausa Novel READ HAUSA Novels

Abunda Ke Boye Complete Hausa Novel

Author :  NONE Category :  African Stories & Novels

Chapter   20 / 88

57K to 60K   out of 262.2K words

sun dauke agogonka sunyi sadaki dashi kenan kuma sun baka yarinya ka karba aayanan ta zama matarka kenan ai...


yace awani addinin ne ta zama mata ta..wann fa ba aure bane hajiya dan wallah bai dauru ba inkuma baki amince da hakan ba gobe sassafe ki kiramana malami yazo nan yamiki bayani kiji, ni badon walakanta yarinyar da ciwo danaga anayi ba da saidai su kasheni awajen amma babu abunda zai saka in kawota nan dan babu abunda ya hadani da ita..

wani irin harararsa tay kmr ruwan idonta zai duba kasa tace "tokai yanxu saima a dauke ayaanan abaka kyauta kuma ka karba? yarinya wankakkeiya kyakkawa, me ilimi, da asali wacce harka mutu bazaka same kamarta ba,karka ga juma yay maka bozonta ka dauka ko shi yana dakai ne, toh wallh wallahi barikaji kakanta da kakan kanta hanshakan malaman addinin musulunci ne shikansa uban taawure hamshakin manomi ne me arzikin gaske ciwo da yaki ne ya cinyeshi mutuwa kuma ya raba taawure da gatanta har qaddarar aure yafado mata akan juma. toh ka iye bakinka akan yar jikata ahtooh ayaanah tafi karfinka..

tunda tafara maganan wani irin kallo kawai yake binta dashi tana rufe baki yace "wann duk ke ta shafa nidai bana sonta. kuma bazan karbi wani aure ba. kawai kisan nayi akashe maganar nan tun anan. snn kisani ina da duk wani labarin abunda ke faruwa dake anan garin tun daga kan satar da ake miki har da yan ta'adda da kike case dasu kina kaiwa maganan auren nan gida wallah saina tona miki asiri dake da sana'ar taki duk za'a kwasheku akaiku gida inga ta tsiyar..

baki bude ta dinga kallonsa cikin tafa hannu ohhh ni mairo ashe har cctv aka saka min kenan toh uban waye ya gaggaya maka wann uban karya haka rayyanu har kuma ka yadda?wani case? ni har ina nagamu da yan kidnaping..

fuskarsa a dore yace "zaki sani...kinsan ni bana wann wasan. har police station zanje a dauko min file din cases dinki da yan daban garin nan harda wanda kike boye masu bappa

rushewa da kuka tay tafara maganganu masu tsananin ban dariya ko ajikinshi haka ya hade rai ya dinga razanata..da kyar dai suka gama case dinnan sukayi bacci.

washe gari kusan da asubah ta farka taga yadda ya cire rigarsa me qamshi ya rufeta dashi dan kartasha sanyi da uban sauro shikuma ahakan ya hakura ya kwana atakure duk data farka ta kallesa atakure sai taji mugun tausayinsa ya kamata sosai, tashi tay ta rufesa da rigar snn ta koma cikin asibiti taje dan tay sallah snn ta duba jikin ayaanah

samu tay ayanah harta farka but she is very weak dakyar ma take magana..ga yunwa ga gajiya ganin kanta kwance akan gadon da yar uwarta ta rasu shiya kara dawowa mata da radadin zafin mutuwarta sabowa.

dakyar hajya mairo ta sakata sukayi sallah snn tanemi ruwan zafi ta bata tasha tazauna ta dinga lallashinta tana tambayarta duk abunda ya faru dan gabaki daya so take tasake jin sauran labarin yiyuwar auren nasu da jikarta ibaad, Allah Allah take taji inhar ibaad amince toh bazata sake a raba auren nan ba kodan ta samu kwakkwan dalilu nawucewa da ita birni na har abada...


dagata dayan bangaren kuwa daga cikin zauren wani gida dake can can jeji taawure ta fito, wata yar tsohuwace agidan wacce koyaushe taawure ta haihu ita take zuwa tay mata wankan gida har tamata jinya sosai sabida tuntuni juma ya hana hajya mairo taka gidansa.

anan wajen tsohuwar taawure taji dukkan labarin yadda aka binne yarta inayah awalakance da irin zargin zina da juma ya laƙaka akan yarsun snn ta bata labarin komi daya wakana akan auren ayaanah tace mata ai wani kyakkwn yaro jarumi me mota shine ya tafi da ayaana.

taawure kamar zata zauce haka tay kukan rasa yayanta acikin wnn daren musmn ji datay an aurar da ayanah wa wani wanda batasan sa baa abubuwa sai suka taru suka mata yawa sosai

zuciyarta ya cika da neman fansa bata damu ko zata mutu ayau ko zatay rai ba saitaji ta gwammaci ma gara ace abata duniyar data zauna cikin baqin cikin sanin cewa inayah ta mutu snn ayaanah ta aure wani wnda basu sanshi ba batama san ta ina zata fara nemota ba.

ranar yadda taga rana hakanan taga dare, kuka kam batasan kalar wanda batay shi aranar ba, can da asubah da sukayi sallahn fajr tsohuwar tana dan runtsawa kadan taawure ta bar kan sallahya ta fice ta zaga ta dauko katon sandan bugun shinkafa, igiya, wuka, da roban kananzir da ashana idonta a bushe tabi hasken almuru babu shakka ko tsoro ayanayinta ta saita hanya sai gidansa.

as usual dake sune ata karshe karshen gari babu wanda yasan da zuwanta wajen da aka binne yarta ta wuce direct yadda taga kmr kasa aka shuhhure akan kabarin yasa ta sulale kasa ta fashe da wani irin kuka me balain tsuma ayayin da koinanta ya shiga karkarwa mai tsanani koinanta ya nuna alaman firgita da baqin ciki me tsanani, bude bakinta tayi da niyyar yima inayar addua atake sai kuma taji wani irin nakason zuci ya mamayeta.

daci da baqin cikine ya rinka bin jinin jikintta har izuwa sassan gabobinta sai tayi lagwas jikinta babu kwari sosai tamkar wata nakasashiya haka ta dawo, cikin yanayin rasa me zatayi da rayuwarta ta sulale kan kabarin rigib ta kifu a kan gwuwarta, sai a sann adduar yazo mata tanayi tana wani irin razanannen kuka mai tsananin tsuma zuciya da shiga jiki wanda bata shirya masa ba

kuka tay har saida baqin cikin abun ya ragu mata aranta snn ta miƙe jikinta na rawa rawa idanunta ya mugun rufuwa da baqin ciki da batun daukar fansa tana ganin kamr inta kyale juma tay makanta da y'ay'anta butulci,yadda ya mata asarar yaranta yau takejin ko ta kashe shi, ko tay masa asarar duk wani abunda yakeji dashi masu muhimmanci a duniyansa agabaki day. an eye for an eye
ji take...inhar bata lahanta juma ba gani take kamar bazata kai gobe ba itama..

da makaman yaqinta ta shiga gidan, aurensu shekara 12 kenan babu abunda bata sani gameda arziki da kuma rayuwar juma ba, gogan dama ba tashi yakeyi yay salla akan lokaci ba wata rana ma bayayi bare ma yau da akace za'a tattauna abashi a matsayi afadan majiya ya tabbata babban burinsa na zama namiji me daraja agarin majiya zai yau zai cika...

turakarsa ta shiga kai tsaye batay wata wata ba ta farmasa da dabara yana cikin baccin ta dauresa tam da jikin gadon tun daga kafa har hannaye da jiki irin daurin goron nan tay masa, tana gama kullawa kuwa ya farka a firkice zai magana ta watsa masa makahon mari snn tabi tasamai ihu tafara tsine masa da yarensu tana kuma zaginsa ayanayin da ya mugun bashi tsoro...

tace mai bazai taba yin farinciki arayuwarsa ba, yadda ya binne mata yarta awalaknce shima haka yayansa agaba zasu zo su binneshi a walaknce, kuma inde tana raye bazai taba yin arziki ba har abada...

haka ta bugeshi da sanda tay masa jina jina, snn ta fice da kalanzir din tabibiye dakin ajiya da kan rumbunan abincinsa daya tara dumbin kayan abinci buhunai hatsi sunkai dari uku banda kananan shanya na su barkwano da gyada, waken suya da baqin cikin jin ya rabata da duka yaranta idonta a rufe ta bunka ma duk wani abunda ya tarana arxiki da wahalansa wuta ta kuma tabbata yakama sosai yana ci bal bal snn ta zubar da makamanta ta arce da mugun gudu tay hanyar tudu godiyan Allah da polisawa basu ganta ba harta isa gidan hajiya mairo agalabaice tana haki...


daga bangaren hajy mairon kuwa duk bataji dadi da ayaana ta gaya mata cewa ibaad bai amshi auren ba, hasalima cewa kawai yay zai tafi da ita amma bai furta da bakinsa cewa ya amshi aurenta ba wanda tun anan jikin hajy yqy sany ta san cewa dagasken babu aure. duk dama batay tsammanin hakan zai bata haushi sosai ba sai kuma taji kmr abun bai mata dadi aranta ba sam. kyale ayaanan tay akan ta huta bayan an idar da sallahn fajr awaje salun alun tafita taje tanemo musu malami, ibaad yana kofar masjid din yana zaune suna waya da bappa zaidu sai ga kirar mujaheed ma ya shigo, sun fara magana kenan basuy nisa ba wata nurse tazo har wajen ta kirashi akan anemansa acan ciki dakin ayaanah sallama yay da mujaheed din snn yabita suka wuce ciki kusan atare.

da sassanyar muryan sa yay musu sallama ayaana tanajin muryansa tay sauri ta lunshe idonta da alaman bata son ma ta kara kallonsa ita har yanzu mummunan tsoronsa takeji ganin yadda jiya ya tunkare babanta da kuma yan kauyensu da mugun taurin kai da jarumta har kuma ya kareta duk dama bata wankeshi da zargin zina da aka masa agaban kowa ba.

babu ko shakka tafi kowa farinciki data ji cewa shima jikar hajy mairo ne sai kuma ta bari akan cewa Allah ne kawai yake kareta daya turosa wajen shiya sa tafado ahannun na gida da ynxu batasan ma ya zatay da rayuwarta ba

dama kuma addanta tay mata alkwari akan cewa kota mutu bazata bari wani abu ya cutar da ita ba.. cikin wann yanayin hawaye masu sanyi suka dinga sauka maga daga cikin lunshashun idanunta, tanaji ibaad ya rusuna ya gaida hajiya mairo a mutunce kamr ba itace abokiyar fadarsa ta kullum ba, snn ya gaida malamin nann suka fara magana akan auren agaban kowa su hudun anaji ibaad ya sake maimaita ma malamin yadda auren ya faru.

acikin kankanin lokaci malamin ya warware musu bayani...

daga hajiya mairo, zuwa kan ibaad har ayaanan duk sunajin bayaninsa yace shi siffan daura auren a musulnci yana bukatar Ijāb da Qabūl wato bayarwa da amsa, nd it has to be a mutual offer & acceptance which must be done willingly. muddin ibaad baice “ya karɓa” with his own free choice ba, then auren bai dauru ba, musmn ba da akayi auren while he is still very much uncounsious, bada cikkaken saninsa ba, bada izininsa kona iyayensa ba, given by this alone auren bazaiyu ba ko shariance ne there is no real nikah. yace koda kuwa duk duniya ne aka taru aka shaida, a musulinci irin wnn aure still remain (invalid)
bayan haka Islam does NOT accept a forced marriage for either man or woman musmn while unconsious.

tsadadden agogonsa sa da aka nuna a matsayin sadaki shima malamin yqce ya haramta tunda bada izininsa ya miƙa musu ba daukawa sukayi bada saninsa ba,shima kuma za'a iya alaƙanta musushi da lefin masa sata.

malamin yace tunda auren bai dauru ba babu saki tsakaninsu sai dai "Faskh" wato annulment
Ma'ana auren ya haramta legally not bounded a shariance, snn a addininace dede yake da auren da ba'ayishi ba..
##idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*

*WATTAPAD @SURAYYAHMS*


*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*


#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025
[07/11, 18:44] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ⏯️1️⃣6️⃣Abunda ke ɓoye!
malamin yana kammala musu bayani cikin lumshe ido da budewa ibaad yafurta alhmdullh acan kasar wuyarsa yanajin wani sanyi na ratsashi taciki ayayinda ayaana kam batasan ma me takeji aranta ba, tagumi hajy mairo tay da alaman bata wani ji dadin bayanan malamin ba, shide ya gama bayani bisa haqqin sharia da kuma nassin musulunci, agabansu akay ma ayaanar wasu yan tambayoyi game da auren wanda dakyar ta iya budan baki ta amsasu, dama ajine ko ibaad ya amshi auren agaban iyayenta da bakin sa, toh da sukaji bai amsa ba, nan aka warware duk wani kananan confusion dake tsakaninsu a shariance batare da wani dogon ɓata lokaci ba.

acikin nitsuwa da girmawa ibaad din ya tashi ya raka malamin waje, suna ficewa hajy mairo tahade rai ta juyo da bambami tanata kallon ayaana

da kmr bazatace komi ba can cikin girgiza kai da rage murya kasa kasa tace "hmmm, ke kuma yannan ai dabaki nuna musu bakison auren nan ba, wann aure ai kariya ne agareko ayaanah, duk taurin kan rayyanu yana girmama nagaba dashi hala ynzu da malamin nan yasaka mana baki ya roqesa ya amsheki a matsayin matarsa kodan kisamu kibishi binni da cikakken lasisinki, inba haka ba dayuwar mahaifinki juma zai zonan yakafa wani kwakkran dalilin da zai karbeki ahannun taawure kuma dai kinsan duk wani kalubale da zaki sha ahannun jikana rayyanu bazai kai rabin dumbin wahala da kuncin rayuwa da zaki kwasa a garin majiya a hannun ubanki juma ba.

dan shiru aayanah tay kmr bada ita hajyn ke magana ba, a mind intq gani take harma yaushe ta isa amata aure bare har ta zaɓi ta zauna da ibaad da tuntuni banda kushe lamarinta babu abunda taji yanayi. hawayen ta na zuba ahankli cikin tunani taki cewa komi, iyaka yawan surutu da lissafe lissafe da hajy mairon takeyi akan hakan saiyasa tadinga jin rauni da mugun tsoro maihade da fargaban yuwar komawarta hannun juma yanamai kare lullumeta, ahnkli wasu sabbin raunattacun hawaye suka dinga fitowa daga cikin idonta cikin rasa abunda zatace mata ta dadayin shiru tana sauke ajiyan zuciya ahankli....

karar bude kofar yasa hajy juyowa katse maganan da sauri, caraf kuwa suka hade idanu da ibaad, wani irin kallo tamasa da shirin masa masifar akan kin auren dayay saidai ganin yanayin daure fuskan daya tunkarota dashi yasaka ta sauko kasa da tempernta suka fara magana cikin hankli ayanah tana hawaye tanajinsu, yadda haj mairon take raki tana kara fahimtar dashi kalar hatsarin da rayuwar ayaanah zai shiga in suka bari hakan ya jawo ta koma kauyen majiya, da irin sharrin tsafi da mugunta dake cikin kauyen, ce masa take duk runtsi duk wuya ayaana saidai inzata zauna ahannunsa dan bazata taɓa bari aji labarin cewa baya tare da ayanah amatsayin ma'aurata ba inba haka ba juma da mukarabansa akauyen majiya zasu tsafeshi tass koma su kasheshi.

tace inma bazai riketa wajensa ba dole ne kawai ya tafi da ita birni inyaso zata gaya ma danta zaidu, ko muhammadu ko kuma surkuwanta fatima su rike mata ayanahn acan. da wani abu aran ibaad ya kalleta bayabo ba fallasa yace "hajiya duk hakan dakike fada fa bazaiyu ba, yarinya da ubanta da uwarta a raye sai ke kice akaita wani waje tay rayuwa, nidai bazan sace musu yarsu in kaita koina ba...ita kanta hjyn fada yay mata yace koda take matsayin kakarsu yakamata ta dinga tuna cewa ba alaqar jini ne ya hadata da taawure ba, taawure yar rikontace, wacce ta sameta sanadiyar aurenta na biyu, dan haka bata da wani hurumin yanke musu wann babban hukuncin akan yarsu..

kusan musu suka dingayi da kakar tashi akan wnn magann duk saikaji ka rasa waye me asalin gaskiya acikinsu...

sunq cikin musun har tawuree tasamu isowa asibitin dake taje gidan hajiya bata sameta ba, tun daga kofar dakin ta tsaya cak tanajin bayaninsu sai jikinta yayi sanyi sosai musmn data gane kmr ansamo yarta ayanah, Allah Allah take ta shigo saidai yadda taji ibaad din yake tsagewa hajy mairo gaskiya akan alakarsu matsayinta na matar kanin uba ga taawure yasa ta dan dakata kadan

yace "sam shi bazai tafi da wata ayaanah birni ba, inma kareta sukeso suyi toh ta zauna mana agaban mahaifyarta anan, hjy mairo taci kuka, tamasa zagin duniyan nan amma ko ajikinsa,

duk ta dauka tsabar baqin hali ne da ra'ayin banza yasa yake ture maganan tafiya kano da ayanahn gefe yana nuna bayaso, batason harga Allah tun jiya ya riga ya shirya yin haka aransa ba. babbn burinsa shine yajawo wata babban yarjejeniya a tsakaninsu dan ya zamana tay saurin jin maganansa akan batun dawowarta gida, in return shikuma saiyace mata zai wuce da ayanah binni. kawai de so yake yaga yadaureta da jijiyar wuyarta, dan ta amshi dukkan bukatansa, hajiya mairo tsohuwa ce mai son rikici yasan saiyay da gaske kafin ya iya rabata da kauyen nan na har abada.

suna tsaka da wann musun ahnkli taawure tabude kofar tare da musu sallama sabida bata da wani dogon lokacin batawa ya zame mata dolene taje wani waje me nisa ta ɓoye kanta nadan wani lokaci sabida aika aikan da ta rattabawa arzikin juma..

tanayin sallama kusan kallo daya ibaad yay mata jikinsa ya bashi ko ita wacece, caraf kuwa hjy mairo ta juyo baki na rawa ta ambace sunanta tana hamdala a raunace suka dan rungume juna cikin fashewa da sabon kuka tana tuhumarta ina taje

jin muryan taawure yasaka ayaanah tay firgit ta bude idanunta da suka gama jiƙkewa da ruwan hawaye dan yadda taji ibaad yanata rejecting inta yadada sawa jikinta yay sanyi bana kadan ba, sai ta dada aminta dacewa duk duniya ne aka tsaneta, ba zallan babanta da yan kauyensu ba, ita de da alama kowa ne baya son riketa.

muryan taawure dataji yasa ta kara fashewa da kukan itama ta firgita tana cewa umma umma jikinta na rawa har zata diro kasa daga gadon ibaad yay sauri ya rikota ajikinsa da karfi duk da firgicin fushi data farayi masa bai saketa ba har kafin nan taawuren ta sake hajy ta karaso wajensu ta amshe a hannunsa ta rungume yartan tsamm da wano mugun karfin shauqi ta lullumeta kamar za'a kwace mata ita dan ko kadan batay tsammanin zata zo nan ta tarar da ayanahnta ba...

sosai nauyin datakeji a zucyarta ya dan ragu data rungume ayaanah..koba komi tay riba tunda ta samu yarta Alhamdullh

dake taji duk abunda suke fada tun a kofa bata kula bayanin aayana ba har saida ta fara gode ma ibaad tanamai sakamai albarka da ya dawo mata da yarta wajen hajy mairo

kalamanta masu sanyi sosai suka ratsashi, idanunsa suka ciko da ruwan hawaye, tausayin taawuren ya hanashi furta mata komi kai kawai yake gyada mata cikin sanyin jiki har snn yay excusing dinsu ya fice waje agaggauce ya nufi motarsa ya shiga yazauna aciki tare da kifa kansa akan stiring dan yay catching breath insa...

hajy mairo batay kasa a giwa ba ibaad yana ficewa kusan tass ta kwashe labarin yadda akayi da batun auren ibaad da ayaanah tagaya ma taawure, itama taawuren bata tsaya ba tagaya mata iya abunda taje tayi ma juma acan kauyen majiya amatsayin daukar fansa wanda hakan ya razana hajy mairo sosai dan ta jima da sanin cewa taawure mace ce mai kunya da dumbin

20 / 88