Author : NONE Category : African Stories & Novels
takejin ta tsanesa kamar mutuwarta.
kallon tsana take masa har ya karaso ciki ya dan rusuna ya gaisheta ta amsashi ciki, snn ya sanar da ita inda zaije nanma tay kamar batajishi ba, after few scnds of silence dan kansa yagaji da attitude inta yamiƙe shiru ya fice agidan yanaji tana binshi da tsaki tare da cewa Allah yasaka mutuwarka ce ta kiraka a tudun mayen yaro kawai Allah yasa gawanka ne zai dawo bakaiba.
..koda ya dauki mota ya fice haka maganan nan nata yarinka masa yawo akai cikin wata karamar toyota jeep da bappa zaidu ya bar masa zaiy tafiyar dashi, yana tukin ahnkli ya kira bappan zaidun awaya suka fara magana ya sanar da shi cewa ynxu zai wuce tudu wajen hajy mai tuwo, hira sukeyi har ya isa cikin anguwar rijiyar zaki inda family house dinsu yake dan ya amsho wasu sakonin da za'a kaiwa hjy mai tuwo daga wajen mahaifiyarsa ammi karama, kusan kaf gidan babu karya ammi karaman tafi samun karbuwa awajen uwar mijinta, dake ita tasan wani abu waishi nitsuwa, dattako, gata da biyayya da sanyin hali, tunda taji uncle moh yasanar da cewa ibaad kawai zasu tura wajen hajiya ayau din taje kasuwa tasiyo dukkan wasu abubuwan masu kyau datasan hajy mairon tana mugun so snn ta dafa mata abinci me rai da lafiya tay packaging insa a close basket dan yawuce mata dashi.
ganin hakan datakey na kyautatawa yasaka sumtimes har anty safeeran ma take gani tana daukar darasi, dan anty safeera is a calm young nd wise lady, a shekaru dai bazata wuce 35-36yrs ba duk dama babanta yana da kudi itama tana gama secndry din ta aure uncle mohd har suka samu first son insu mujaheed dayake sa'a da zainab arifah, sai yar autarta kulthum bayan nan ne ta koma karatu, she is curently studying msc micro biology amma a private university., duk duniya babu abunda take mutuwar kauna kamar mijinta uncle moh, shi mutum ne meison jin dadin rayuwa, he is all about this flashy rich guy life, kominsa is loud, tun daga way of life insa me aji, har sutura, kominsa me tsada kawai yake sawa, he is the finest nd the youngest engineer of the almansur's elders, ryt in his early 40s, shi farine sosai dogo mijin novel, mai cute red lips da kwantaccen saje, gashi da saurin fara'a, mutane suna yawan cewa dansa mujaheed yagado farin fatarsa ne sosai.
anty safeera can do anything to please him, wani irin soyayya na amana take masa, ganin ibaad agidan yasa sai itama tajeta sashenta tadan tarkato turaruka masu kyau da tsada ta bashi danta burge mijinta, agabansa tace asaka ma hjyn kayan nata tsarabar aciki.
lafiya lafiya ibaad yay musu sallama, uncle moh ya rakosa har gaban motar jeep in yanamai dada jadadda masa cewa in har ruwan sama ya tsaresa a tudu karyace zai dawo sabida akwai fatake masu kidnaping da barayi kawai yayi haquri ya kwana agidan hajy mairo inyaso gobe da sassafe sai ya dawo
sude babban burinsu shine ibaad ya samu yaje tudun ya gano musu asalin menene ke faruwa da mahaifyar sun acan, snn ya lallaba musu ita taji aranta cewa zata iya barin wajen ta dawo cikin kano ta zauna tare da su a gida.
gabaki daya tabi tahana yayan cikinta binta can tudu sukuma anan cikin kano hanklinsu sam baya kwanciya, sai tace sam za'a sace matasu in sukazo, saidai kawai ayi waya tsakanin ta da bappa zaidu da uncle moh akai akai, dake suna yawan tura mata kudi kowani wata ko cikin sati, prof zayyanu kam dama tun tuni ya dena nemanta kuma bata wani damu da baqin halin sa ba dan abune data saba dashi tun bai kai ma haka ba, ko surukanyenta da jikokinta ma knsu bata fiye kiransu ba sabida tsaro.
at around past 5 ibaad ya kammala duk wata maganansa da uncle mohd snn ya shiga jeep din yakama hanyar anguwar tudu dake wata bangare ne me nisan gaske acikin kano wajen tafiyar awa uku ne da rabi sabida hanyar shiga garin babu kyau ko kadan
tun kafin ibaad ya dauko hanya, ata can bangaren juma kamr dai kullum, zuwansa wajen fulani jin labarin rayuwar da taawure takey a tudu bai kare masa ta dadi ba.
dan kuwa daga isarsa majalisan dattijai ya tarar da su kaca kaca anata raha, toh yay dasu aje gefe suyi magana amma sukaki suka bige da tsokanansa kamar yadda suka saba kullum. dakyar da wahala suka dan sauraresa suka koma gefen kai tsaye ya fara musu tambyar dake tafe dashi, dayan bafulatanin ana cemai sajo shi yafara ce masa ai wnn tsohon zance ne, yaran sa kam dama cikakkun yan barikine dan sun mugun shahara a anguwar tudu msmn ma inayah itace ma ake cewa gwarzuwar tudu.
hanklin juma sosai ya tashi da jin wann furuci, saida suka ganema cewa bada saninsa yaran suke karatu ba aikuwa su suka hau fede mai biri har wutsiya na batun karatun da su inayah da ayaana sukey, komi da komi saida aka gayama juma abaibai wanda tun bai bar wajen ba mazan dake wajen aka fara yaɗa labari nacewa juma cikakken lusari ne baida gindin haifan yaya maza gashinan ashema matarsa taawure tafi krfinsa akan harkan gidansa da yaransa taje tudu ta saka yaransa a makarantar kafuraye batare da izininsa.
ranar kamar kan juma zai fashe da feshin wuta haka ya kamo hanyar gidansa da gudu idanunsa sunyi jajizir ruwan saman nan da aka fara sabo kaf akansa ya kare...
yana dawowa gidan ya shiga turakarsa ya dau wata igiya ya cusa a wandonsa snn ya dau wata addansa mai kaifi akan yau xaima tawure dukan mutuwa snn ya sare kafafunta dashi..
hakanan yaci nemansu agidan har wajajen daya saura na rana bai samesu ba kuma kwata kwata bai kawo aransa cewa har taawure zatay tsaurin idon kashe aurensu akan ciwon inayah ba, adan dolensa yaje jejo ya nemo kasurkurmin magulmacin nan dandanko, sabida yasan duk tsiya abakinsa kawai zaiji labarin inda taawure takai masa yayansa,
haka ya bazama jejin kmr mahaukaci da kyar ya sameshi, dandanko dayaga juma wujiga wujiga sai yaki sam ya gayamai komi saida ya sha cikinsa yaji labarin asalin meke faruwa tukuna.
bayan yagama jin komi sann yahau kara masa wuta yana cewa aidazu ance masa anga matarsa taawure ta goyi innari sun wuce tudu da kayansu, snn yabi yace ma juma toh tabbas cikin shege ne inayah take dashi sukaje zubarwa a tudu awajen likitocin kafuraye, inba hakama ba, wani irin ciwo ne haka inayah takeyinsa da amai da rashin cin abinci da kuma ciwon ciki me tsanani..snn kuma ace duk saiwoin kauyensun nan ya kasa magancewa...
yace ma juma kawai dai cikin shege innari taje ta kwaso taawure take kokarin boyewa kawai yaje ya dau mataki sabida kar martabansa da kimansa ya kara zubewa a garin majiya.
hakanan ya kara pumpa zuciyar juma da zugi da kuma zargi harsaida yasaka ta karayin baqi qirin da mummunan fushi da kuma bacin rai, daga nan babu wani jira juma ya saɓi sandan sa da addarsa ya wuce garin tudu acikin yayyafi, ya iso around 2pm dede na rana lokcin jikin inayan yafara rikicewa
likita ya fito yana kkrin ceto ranta da taimako da ake bayarwa na emergncy sabida sun riga sun gano cewa chronic appendix ne yake damunta gashi bayan ya girma harma yafara ruɓewa acikintan dolene kawai amata tiyata aciresa agaggauce.
tun bayan sallahn azahr suke cikin wann tashin hankli anata kkrin stablizing din inayah kafin ace zaa nemo motar da zai kaisu cikin birnin kano dan amata tiyatar nan agagguce gashi lkcin ana wani irin kwaxa ruwan sama me yawa da kuma tsawa
duk da zafin ciwo wasiyar hakuri da neman yafiya kawai inayah take nema awajen taawure da ayanah dan ciwon ciki takeji mei tsananin ciwo da bazata iya fasalta azabansa ba,
anata rububin nan ashema kudin tiyatan nasu bai cika ba, gashi taawure bata da waya haka tafita tabar ayana ajikin inayah ruwa na dukanta duk abun hawa sundauke da kafa ta dinga tafiya cikin sauri tay hanyar police station neman hajy mairo dan tabata aron sauran kudin tiyatan agaggauce..
ficewarta a asibitin bada jimawa ba Allah yay ma mijinta juma isowa har cikin asibitn da taimakon wasu matasa dake yawan zama daf da kofar gidan hajya mai tuwo dake zaman saka ido dama suke sune suka dada tabbatar masa cewa tabbas taawure da yayanta suxo amma sunbi hjy mairo sunje asibiti tun da jimawa
ransa a matukar dagule ya farabibiyar kwatancen asibitin tun abakin matasan dayake tambaya yaji kusab kowa ana cewa inayah gwarzuwan tudu, shi duk ya dauka gwarzancintan nan a karuwanci ne da tsabar iya bin maza baisan gwarzuwan karatun qur'ani suke nufi ba.
zcyarsa baki kirin ya diro cikin asibiti, daf lokci ciwon cikin nata ya tsananta sai nasiha take ma ayaanah akan karda tay rauni koda ta mutu bata duniyan nan ta tabbata ta tashi tsaye tazama wata jajirtcciyar mace snn ta mata alkwarin zata cika ma mahaifyarssu taawure bban burinta naganin sunyi ilimi sun zama mutanen kwarai.
tsabar kukan da sukeyi rikeda hannun junansu in an intense emotional state basuma san sanda juma ya shigo kansu ba.
ji kawai sukayi ana huci daga bayan su ankuma zaro katon sanda kmr za'a je yaqi a mugun zuciye yana huci yadaga sandan sama zai bugashi akan nurses din dake tsaye duk suka saka ihu suka bar dakin aguje ganin sa gabjeje babu wacce tay gigin taresa. dayaga haka sai girman kansa ya kara hautsina yafara dirin masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba yabi ya haukata asibitin da zage zage
ayanah ta mugun tsorota, yadda kasan zucyarta zai fice daga kirjinta ya fice, amma haka ta cije ta ki sam tatashi ajikin inayahn tabi ta rungumeta tana kuka mai mugub karsashi wanda hakanne kawai yasaka bai kai musu dukan atare ba.
muryansa kamr zai tada asbitin yake kiran taawure kamr wani tabbabe yanamai zaginsu yanamai cewa inayahn karuwa tsinanniya kawai, yar bariki irin uwarta, yace wallh kinyi asara innari Ashe dama cikin shege kikayi kuke boyemin keda uwarki?? da yaren buzanci da fulatanci duk ya hada yana tsine mata dashi.
itade inayah kuka takey tana furta innalillah wa inna ilaihi rajiun....idonta a lumshe taki tace masa komi taki ta masa bayani bare ta bashi haquri..
..duk wani xafin xagi me tafe da amon muryansa dayake saukewa aknsu ji take kmr ranta yake zarewa dan zafi.
ayanah da tsabar tsoronsa ma bata iya masa magana ido da ido amma yau babu irin tsaurin ido da yaren da bata masa rantsuwa da bayani dashi ba.
tabi ta rungume inayah sosai tana kareta dagashi cikin kuka mai rauni, tanacewa baba ciwon appendix ne yake damun adda inayah ba cikin shege ba
hargagi yake ko ajikin sa kamar baijinta tanakan maganan ma ya ficokota ya tureta ya faffala mata maruka masu karfi, yaki sam yaji komi, shide yanaso ne ma yaga kawai ya gwada ma inayahn sandansa ya kashe ta,
dakyar likitan da wasu maza suka shigo suka samu suka rirrikesa snn aka kwace sandan daga hannunsa, ahakama sai zagin yaransan yakeyi kamar bashi ya haifesu, anfi minti ashirin ana wann hayaniyar da juma...
ayaanah ce ta fara jin daukewar numfashin inayah, ta mike da sauri jikinta na bari tayo kanta tun bata bude baki ba ahankli tajiyo kalmar shahadarta daya kufce mata abaki very faintly.,
akace wai duk inda malaikar mutuwa yazo sai iskan wajen yayi daban wani irin dimmm taji wajen ya dauke mata cakkkk, dan tunda tajiyo wnn numfashin ta na karshen taji kirjinta da jijiyon zuciyatta duka sun tsinke jikinta na wani irin rawa atake ta juyo sai kuma tazube aragwabe ajikin inayah tafara wani irin kuka mekara tana jijjigata tana kiran sunanta kamar tabbabiya..
da gudu likitan ya sake juma ya karaso wajen aka dudduba aka samu rai yay halinsa kowa yana furta innalillah aayana ta zube kasa tana kuka kamar ranta zai fita amma juma ko gizau baiji ba dan ya mugun tsanar asbiti da duk mutanen dake cikinta, anata batun yarsa ta rasu amma masifa yakeyi yana cewa sam cikin shege akazo zube mata tay mutuwar kafirci.
ran kowa saida ya baci a asibitin ko ajikinsa, shi mutuwar inayahn ma dadi ya masa gani yake data haifi shege agidan sa gara ta mutu, hakanan ya fizgo aayana waje, lkcin ana yayyafi sosai ya tsare adedeta ko ciniki baiyi ba ya cusata ciki yaciro igiyansa daga aljihunsa ya daure mata hannunta biyu da igiyan ajikin karfe ta cikin keke, snn ya koma ciki yanamai kara saukar musu da jakar balai yabi har kan gadon ya dauki gawan inayan akafadarsa, itama ya saka acikin keken, duka dashi da yaransa ya debosu agabansa suka kama hanyar garin majiya aganinsa sai ynxune ya cika namiji, snn zai nuna ma kowa tsananin jarumtarsa for once dai zaiyi abunda ya dace akan yaransa bisa tsarin al'adarsu ta kaka da kakanni dan martaban sa da kimarsa ya dawo.
lokacin ruwa aka farayi sabo kamar da bakin kwarya wanda shine yasaka har taawure bata samu abun hawan dawowa da cikaton kudin tiyatar data amso wajen haj mai tuwo akan lokaci ba
ko cikakken minti biyar juma baiyi da dauke yaransa ba ta iso asbitin wujiga wuijga kusab agigice jikinta yay jagwab da ruwa tazo musu da cikaton kudin tiyatar cass har tana haqi, tsabar tausayin data basu da kyar aka samu wata dattijuwar health worker data gaya mata cewa Allah yay ma inayahnta rasuwa snn gadai jahilci da haukar da ubansu yazo yay asibitin kuma ya tafi da duka yaransa gida ynxu
tunda aka fara mayar da maganan kusan kangare taawure ta suma daga tsaye har saida sukaga bata motsi snn aka bambamreta daga sudden shock din data shiga ciki aka samu itama bata ko motsi dan mummunn bugawa zuciyarta yay atake kuma ta suma aka bata gado ana kkrin reviving inta dan karta samu sudden heart attack due to shock.
tundaga hanya ayaanah take rabza kuka mai kara da karsashi, keken yana sauke su juma ya taso keyanta da haryanzu take rabza kuka kamar ranta zai fita wanda duk yawan ruwan nan da akeyi duk jejin saida ya dauka da karar kukanta, tanajin matsanancin tsoron abunda ke faruwa ga tsananin baqin cikin mutuwar addanta na dada gigita mata kwakwala tare da tsinka mata jijiyoyin zuciya..
sun iso gidansu babu takalmi akafara bare dankwali, haka juma ya turata akasa yabi ya kulleta adaki tareda gawan inayan snn ya fito waje ya wuce gari yakirawo mutane dan a masa shaidan binne yarsa da zaiyi bisa hukuncin al'adansu na kauyen, gashinan ruwa fa akeyi sama sama dake la'asr ya riga ya shigo ana neman kusan 4;45pm on dot amma hakannan magulmata da yan son ganin kwaf kwaf suka bazama yana bude kofar ya samu aayana tayita kuka harta sume tay karau ajikin gawar inayah dake dauke da fuskar murmushi.
wani irin shure aayanan yay gefe ta fadi akasa snn ya iyo ma maza biyu suka shigo, cikin masu fidda gawan inayahn dum mamaki ya rufesu ganin ynyin fuskarta da murmushi har suna tsammanin cewa ko ba mutuwa tay ba sabida wnnn hasken da fuskarta yay sosai kamar ba ita ba.
al'adace ya zamo basu yin jana iza wa wacce tay cikin shege agarin, dan haka juma ya sanar ya kuma nuna ma shaidunsa cewa yana Allah wadai da abunda ya faru da yarsa snn a shirye yake amata binnewar al'ada tunda cikin shege taje zubarwa.,
dakyar aka samu mata wanda suka mata wanka aka suturtata, ko kabari ba akaita ba kawai aka haƙa rami a bayan gidansan ta cikin jeji
normally bisa koyarwan addini ladubba ake bi ma saka gawa a rami ahnkli snn ta hannun dama amma koda sukazo saka inayah anata kabarin gungurata kawai sukayi sai suka shushhure mata kasa akanta har saida kabarin nata ya rufe......
(muna rokon Allah ya kare musulmi daga sharrin jahilcin wasunmu musulaman a duk inda suke, true life story, wata sabuwar makwafcyrmu christace baikai ko wata biyu haka ba data tataɓa furta min cewa ita babu abunda zai sakata taso musulunci ko tayishi harta mutu sabida musulmai mugaye ne, dalilinta nafarko shine babban yarta tabar christanci 2yrs back ta musulunta ta aure wani musulmi amma tunda ta shiga hannsa bakaramin tozarci da walaknci me tsanani takesha ba ga duka ga horon yunwa ga zagin cin mutunci, na biyu kuma awani kauyensu a jos tace mana da idonta tagan anyi ma wani mutum bawan Allah irin wannan walakntaccn binnewan da akay ma inayah, wai lefinsa shine shi tubabbe ne ba a musulnci aka haifesa ba, tace sanadiyar wann incident din mutane dayawa sunbar addinin. it was a sad reality in that remote villlage, it took alot of convincing kafin matar nan tazo ta fahimce mu harma tagane cewa ba haka musuluncin fa yake ba, snn zatama iya kaiwa kara kotun sharia dan akarbawa yarta yanci..kalubale garemu ne musulmai, addinimu bawai sai a fuska ko a baki bane. yakamata ace kyawawan halinka ko halinki shine zai fara bayyana kyawun addininki a duk inda ake, lets all make sure we set a good example of our religion no matter whom we are dealing with...bissalam)
*a saurare sabon Update ranar monday in sha Allah*
idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata
*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*
*WATTPAD @SURAYYAHMS*
*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*
#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025
[03/11, 21:06] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE BOYE..1️⃣3️⃣
ruwa akeyi sosai amma bashine yahana jama'ar kauyen majiya tahowa gidan juma kwansu da kwarkwartansu dan sugane ma idanunsu abunda ke faruwa da yayan juma ba. hatta wazirin sarkin buzaye saida aka dagosa da lemansa dan yazo yagani yakai rahoto gaban sarki...
agaban kabarin inayah inda suka gama shushhure mata kasa aka tayar da wani sabuwar hayaniya tsakanin fulani da buzaye, kowanne kabila tana kirga a wanne bangare ne akafi samun abun kunya, inda atake wazirin sarkin buzu cikin izza yake nunawa jama'a cewa dolene kawai juma ya amshi lefinsa snn ya tashi tsaye ya cigaba da daukar tsatsauran matakai akan iyalansa domin kare martaban al'adarsu da mutuncinsu na buzayen majiya, saƙo na farko da sarkin buzaye ya aiko shine marmaza akawo masa juma da yarsa ayanah a fadansa agurfanar da ita, snn a aurar da ita ma almajirin gonan