Author : Bilyn Abdull Category : African Stories & Novels
da matsanancin soyayyar da take masa, to ?arshen wayewa ma tun tana shekara biyu a duniya aka tafi da ita UK, ba kuma ta ta?a zuwa Nigeria ba sai a shekarun girma kuma a lokacin sukai aure. Takan ji ya mata kwarjini da cika mata waje a duk sanda yake a gabanta, wani lokacin ma tafi sakewa da shi a waya fiye da kasancewa a face-to-face....
Ê Ê Ê Ê ?agatan da yay ne cak ya katse mata tunani, kamar wata babyn wasa duk da kuwa ita ba ramammiya bace jikinta a mulmule yake da ?ar ?ibarta sai dai bamai yawa ba. Hannayenta ta zagayo a wuyansa tana mai kwantar da kanta a ?irjinsa. A haka ya shiga da ita cikin bayin ya dire cikin jacuzzi. ?asa-?asa cikin ra?a da wani salon soyayya irin ta manya yana wani kalar shinshinar wuyanta daya sakata lumshe idanunta tsam-tsam ya furta.
Ê Ê ÊÊ ÒKiyi amfani da ruwa mai zafi sosai zai daina taguwar Zak... Sarkin rakiÓ dai-dai nan ya sakar mata ?ar sumba a cikin kunne data sakata zabura. Yanda ta ?an?ame jikinta ya sashi sakin wani lallataccen murmushi na ganin dama, cike da takunsa na zarra da jarumta ya bar mata bathroom ?in gaba ?aya har lokacin da ?aramin murmushin a lips ?insa, ?yawawan idanunsa kuwa sun wani shige ciki sosai jan cikinsu yafi yanda suke akoda yaushe. Sai wani luuu yake da su yana bu?ewa a gajiye...
Ê ÊÊ Gaban mirror ya koma ya saka turare ka?an ya fice a ?akin gaba ?aya dan yana son zuwa gidan su Imran gaida iyayensa.....
<>><>><>>
ÊÊ
Ê Ê ÊÊ ?AUYEN BANKAURA
Ê Ê ÊRakwacammm!! ?arin bazata ya kara?e kunnen Umma dake tsakar gida tana aiki. Da sauri ta kalla ?ofar ?akin, tare da ?wala kiran sunan Nimrah da tasan tana ciki. Shiru ta?i amsawa. Umma tai ?wafa da fa?in, ÒNice nake kiranki kina min shiru ko, shike nan ALLAH ya baki sa'a na shigo ?akin nan jikinki ne zai gaya miki.Ó
Ê Ê Ê Tsulum ta fito jikinta fututu da garin tuwo ko fulawa. Suna ha?a ido da Umma sai ta fashe da kuka tana ?aga yatsa sama bayan ta lashesa akan harshe.
Ê Ê Ê ÊÊ ÒUmma na rantse bani nai miki ?arin nan ba, ?eran ?akinki ne......Ó kuka ya ?wace mata. Rasama abin cewa Umma tayi, kawai ta cigaba da kallonta. Itako tana ?ara ?arfin kukanta da rantsuwar ba ita bace ?era ne yay ?arin nan. Dai-dai nan Babanta dake bayi ya fito. ÒKaiya-kaiya lafiya dai kuwa? Uwa kin san bana son wannan shashancin kukan banzar fa. Mi akai miki?Ó.
Ê Ê ÊÊ Ran Umma a ?ace ta ce, ÒSai anyi mata. Ko ita tayi ai ta iya kukan iskanci. Kuma wlhy yau babu mai hanani dukanki a nan gidan. Fulawar mutane kika ?arar min daga kawowa ai musu mirjin taliya, bayan a sama na sakata saboda sanin halinkiÓ.
Ê Ê Ê Ê ÒNa rantse ?era ne, Baba kace karta dake ni, ai dai ?eran yafi ta kamo ta dakaÓ. Nimrah ce ke maganar cikin uhun kuka bayan ta rugo tazo jikin Babanta ta ?uya. Kansa kawai ya girgiza da fa?in, ÒALLAH ya shiryeki Uwa, al'amarinki ya fara bani tsoro, yanzu kiyi laifi amma tsabar sha?iyanci kice wai ?era ne? Shekaran jiya fa haka kika ?arar da mangya?a Inna ta hana a ta?aki da Kawunki Tanimu, yanzu kuma kayan mutane, sana'ar kike so uwar ki ta daina?Ó.
Ê Ê Ê Ê ÒBaba na rantse ?era n.....Ó
ÊÊ Bummm!!! Abinda Umma ta jeho mata ya daki bakinta. Ai data buga wani tsallen ihu ta zube ?asa saita fara birgima da fa?in wai Umma ta cire mata bakinta. Haushi ya ?ara turni?e Umma tazo kanta da tsumagiya ta fara zuba mata a jiki, da ?yar Baba ya kwaceta. Sai ga Inna ta shigo itama tana sababi, dan a duniya idan kana son ganin tujararta to ka ta?a Nimrah a gidan nan, shiyasa ma take wani iskancin da hujja. Maimakon taima Umma ka?ai fa?a sai ta ha?a harda Baba wai basa son Nimrah. Su dai ha?uri suka koma bata....
Da Nimrah Inna ta tafi sashenta, acan ta lallasheta ta bata nera ashirin wai ta sayo awara da kunu gidan Zinaru. Aiko da farin ciki ta ?auki kwano ta tafi, gidan Zinaru mai awara da gidansu akwai ?ar tazara ka?an, dan gidansu Nimrah yana cikin gidajen ?arshen gari, sune na ?arshe ma sai jeji babu gidaje a bayansu sai wasu ?auyukan. Har tabi ta cikin gari ta canja hanya ta koma ta bayan gida tabi wai tafi sauri. Tafe take tana shan majina da doke-doken abubuwa da karan dake hannunta. Wani lokacin ma har yara ?an uwanta idan ta gamu dasu sai dai kaji ta zuba maka duka, kafin ka rama ta zura da shegen gudu. Gata ?ar sirit babu ?iba sai tsayi.
Ê Ê Ê Ê Ê Ê Taje birtalin da zata fita a bayan gidan ta koma hanyar gari sosai ta hango wasu mutane zaune a ?asan wata ?atuwar bishiyar mangwaro dage wajen. Humm Nimrah neman magana ake gaya muku, sannan Nimrah fa?i ba'a tambayeka ba. Fasa tafiyar tai ta koma hanyar inda mutanen nan ke a mangwaro. Babu zato sukaji ?ar muryarta na fa?in, ÒSuwaye ku?Ó.
Ê ÊÊ Da wani irin sauri duk suka juya suna kallonta, sai mutum ?aya da bai juya ba sai ma runtse ido da yayi tare da jan hiraminsa dake kan wuya da sauri ya rufe fuskarsa alamar baya son ta ganshi, kuma tabbas ta sanshi ne shiyyasa yayi haka. A hasale wani zai mata magana na kusa da shi ya hanashi ta hanyar ri?e masa hannu ya matse. Murmushi yayi mata tare da fa?in, ÒYarinya miya kawoki nan?, mu ba?i neÓ.
Ê ÊÊ Fuska a ya yamutsa, maimakon kula zancensa na farko sai catai, ÒBa?i? A bayan gariÓ.
Ê Ê ÊÊ Sosai mamakin shegen wayonta ya bayyana a kan fuskokinsu. Wanda yay maganar dai ne ya sake mata murmushi. Ya ce, ÒEh zamuje ?auyen Garjalle neÓ.
Ê Ê Ê Batace komai ba, sai ma ido data zubama jakunkunan gabansu, sai kuma ta koma kallon wanda ya rufe fuskarsa. Ganin yanda ta zuba masa ido yasa wanda yay mata magana ?azun ?akko naira hamsin ya mi?a mata. ÒKinga ?ar Baba amshi wannan ki wuce gida kada a nemekiÓ.
Ê Ê Ku?in ta zubama ido, sai kuma ta girgiza kanta tana kamo gefen kallabinta da aka kulle ta nuna masa. ÒBana so, nima Inna ta bani zanje sayen awara neÓ.
Ê Ê ÊÊ ÒYauwa to maza kije ki sayo kada ta ?areÓ.
ÊÊ Harta juya zata wuce sai kuma ta dawo. Ta ce, ÒKai Baba to miye a wannan ?aton jakan da yawa? Wannan kuma miyasa ya rufe fuskarshi ko bashi da lafiya?Ó.
Ê Ê Ê Ê Babu wanda a cikinsu baiji kamar ya ham?are yarinyar nan ba. Amma dai wanda ke amsata ya daure ya ce, ÒEh baida lafiya. Jakun kuna kuwa mangwaro ne muka zubaÓ.
Ê Ê Ê ÒAi yanzu ba lokacin mangwaro ba neÓ.
Ê ÊÊ Ta amsa tana sake matsosu. Tsawa na ?azun ya daka mata dan ya kasa ha?uri, ÒKe wuce ki bar nan komu yanka ki mai shegen surutun tsiya, ?ar firit dake sai sa ido kamar aljanaÓ. Ganin ya ?are maganar yana jawo wani ?an icce a kusa da shi da gudu tabar wajen kuwa. Sai da tai nisa daga nesan tana hakki ta juyo ta ce, ÒKu! In ALLAH ya yarda sai kura ta cinye ku masu jajayen ido irin na fatalwaÓ.
Ê ÊÊ Daga haka ta sake zurawa a guje. Takaici ya saka wanda yay mata tsawar nan ciro wata ?ar mitsitsiyar bindiga ya saita ta. Cikin sauri wanda ya rufe kansa da hirami ya ka?ar da bindigar yana yaye hiramin da girgiza masa kai alamar karya aikata wannan kuskuren.
Ê Ê Ê ÊÊ ÒMi kake nufi ko kana da ala?a da ita ne?Ó.
Ê Ê ÒBabu ruwanka da koma ya nake da ita, ka duba mana yarinya ce ?arama dududu bata wuce shekara bakwai da wani abu ba. Sannan a tsarinmu bamuyi haka da ku ba ai. Babu cutar da yara, babu cutar tsoffiÓ.
Ê Ê Ê Ê ÒKai ba?auyen banza an?i abi dokar taka, kodan kaga mun biyo ta hannunka ne kake tunanin bazamu iya aikin da kammu ba. Kada ka manta ku?i muka biyaka kai mana komai. Sannan da kake kiranta yarinya ai a yarintar tata tasan rashin kunya ma manya ko. To na rantse maka duk inda naga yarinyar nan a garin nan sai na fasa mata kai kuwaÓ.
Ê Ê Ê Ê Da sauri mai hiramin nan ya kalla Ogan tawagar, kafin ma yayi magana ogan ya ce, ÒKaga manta da shi, babu abinda zai mata kasan shi dai da zuciyar tsiya. Kamar yanda mukai al?awari da kai tun farko babu canji, bazamu ta?a yara da tsoffi ba. Kai dai kaje ka fara mana aikin tantance yara mazan da muke so. Zuwa jibi ka tabbatar aikinka ya kammala zuwa dare zamubi gida-gida mu tattaresu waje guda. Ga kayan aikinka nan da ku?a?enka zaka iya tafiyaÓ.
Ê Ê Ê Kansa kawai ya jinjina, sai kuma ya mi?e. ÒBazan tafi da wa?an nan kayan ba yanzu, sai magriba zan dawo ?auka.Ó
Ê ÊÊ ÒBaka da case GogaÓ.
Ogan ya fa?a yana bashi hannu. Daga haka ya gyara hiraminsa ya zagaya wata hanyar ?adda kama ya koma cikin gari..........???
Ê ÊÊ (Lallai cakwakiya, to wanene wannan ??? Yaya batun wanda yace sai ya kashe Nimrah? Kuna ganin zai ?yaleta kuwa??????. Hummm kudai muje kawai, dan ba'a fara komai ba ma. Cakwakiya ce iya cakwakiya a cikin littafin nan??????????????).
_Zaku sameshi a wa?an nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER????- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ?asar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya??_
*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya: ??_*
*_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number ??_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number??_*
*+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu ????_*
*_Typing??_*
*_??KI?A A RUWA.....!!??_*
*_Bilyn Abdull ce ????_*
*_?????? ??????? ???????????? ?????????_*
_Da s?nan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._
_Chapter 39_
__________________
*_Kuyi hakuri dani, ni kaina bana gane kai na saboda uzurirrika da suka zagayeni wlhy. Amma ina sha ALLAHU ina gab da kammalawa na dawo da hankalina gaba ?aya kanku. Ina muku fatan alkairi gaba ?aya ????????????_*
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
.........Hajiya Nimrah kam dai koda ta bar wajen gidan sayen awara ta nufa, koda ta sayo yaran gidansu data samu acan gidan awarar sunzo saye suka janye ra'ayinta suka tafi tare ta cikin gari bata dawo ta bayan gidan ba. Ta samu Umma na murza taliya, dan wannan itace sana'arta. Tuni Bana ya sayo mata wata fulawar ta murza a maimakon wadda Nimrah ta zubar, wannan ma ta wasu ce take murzawa a yanzu. Nimrah ta zauna kusa da ita tana shan majina da bu?e kwanon awararta.
Ê Ê ÊÊ ÒUmma kalla, Baba Zinai ta zubo min da yawaÓ.
Ê Ê Batare da Umma ta kalleta ba ta ce, ÒKin gode. Sai ki tashi ki cire wannan majinar da kike faman sha ki wanke hannu sannan kizo kici dan nasan a fitarki kaf tarkacen garin nan sai da kika ta?aÓ.
Ê Ê ÊÊ ÒToÓ.
Ê ÊÊ Ta fa?a cike da abin arzi?i ta tashi tayi duk yanda Umma tace. Harda ?ebo ruwa a mo?a cikin randarsu. Tazo ta ajiye ta kaiwa zaune. Kamar wadda aka tsikara ta ce, ÒUmma kinga ko, da zanje ta bayan gida nabi, a gonar Baban Zakiru naga wasu mutane da yawa zaune, idanunsu jajaye kamar na fatalwa. Hadda jakunkuna manya sun ajiye, wai sukace min ?auyen Garjalle zasu je......Ó
Ê Ê ÊÊ Kallonta Umma tai a karo na farko, sai kuma ta ?auke kai cikin rashin ?aukar zancen da muhimmanci ta ce, ÒTo uwar soki burutsu zaki fara ba?in surutun naki ba. A gidan uwarwa ake ganin wata fatalwa da rana. ?auki awararki kici bana son maganaÓ.
Ê ÊÊ Baki ta tura sosai, kamar zatayi kuka ta ce, ÒNa rantse da gaske nake Umma. Kuma har wajensu naje ma, har naga wani mai irin kayan......Ó
Ê Ê Ê Ê ÒALLAH idan baki min shiru ba sai na fasa maki baki, koki tashi ki wace wajen Inna in damuna zakiyi.Ó
Ê ÊÊ ÒMi kuma tayi za'a fasa mata baki? Bayan ?azu kika gama dukantaÓ.
ÊÊ Baba dake shigowa ya fa?a. Sannu Umma tai masa sannan ta ce, ÒTa isheni da surutu ne. Wai taga fatalwa ko a gidan uwarwa ake ganin wata fatalwaÓ.
Ê Ê Ê Shi abin ma dariya ya bashi, ya ka?a kai kawai yana ?ar dariyar da fa?in, ÒUwa sarkin magana, Zakanyar Kawu Tanimu, in dai zance ne a bar miki abinkiÓ.
Ê Ê Ê Ê ÒBaba banyi ?arya ba fa, kuma harda mai irin kayan......Ó
Ê ÊÊ Murfin kwano da Umma ta jawo ya sakata saurin dafe bakinta dan tasan ka?an daga aikinta ta kwaf?eta da shi. Shima Baba sai ya shige kawai yana murmurshi.. koda Nimrah taga Umma da Baba sun ?i sauraren labarinta na fatalwoyi sai ta surare ta koma sashen kakarta Inna. Acan ta fara bata labari, sai dai anyi rashin sa'a itama Inna ta kwa?eta batare data maida hankali a zancen ba ta ?auka soki burutsinta ne kawai data saba. Daga ?arshe ma korota tayi daga sashen akan ta tafi ta bata waje barcin zatayi. Daga haka Nimrah ta fice cikin yara suka kama wasa. Can kamar an tsikareta taba yaran labari suma, abinka da ?uruciya sukace ?arya ne, sai ta dage akan suje ta nuna musu. Aiko haka suka ha?a gayya suka fita bada sanin iyayen ba bayan gidan.
Ê ÊÊ Tafiya takanas babu ko gargada ta kaisu har wajen mangwaron nan dake cikin gonar Baban Zakiru kamar yanda ta fa?s, sai dai a yanzu babu kowa wajen mutanen sun tashi sai robobin ruwa da suka sha da takardun nama, wata ledar ma ba'a cinye naman ba. Haka sukaita tsincewa suna ci, suka tattaro robobin ruwan dana lemo suka dawo gida. Yawancin iyayen sun gansu da wa?an nan robobin ruwa dana lemo, amma sai basu tambayesu daga ina ba saboda a wasu lokutan kawunsu Tanimu kan raba musu dan su dinga zuba ruwan zuwa makaranta, shima kuma yana zuwa dasu ne daga birni.Ê
Ê Ê Ê Ê ÊÊ Da yamma gab da magriba Umma ta gama aikin tuwon dare. Ruwan data ?umama ta ?iba taima Nimrah dake ta damunta da surutu tana cin gya?a wanka. Ta shafa mata mai ta saka mata kaya. Tuwon Inna data zuba a langa ta saka a botiki ta tura gaban Nimrah ?in. ÒKi ?auki tuwon Inna kikai mata, sai ki dawo ga miyar nan itama zan saka miki a wannan botikin ki ?auka ni zan shiga wanka bana son a kira magriba, saura kuma dan ALLAH kiyi abinda ban saki ba, ALLAH bazaki bini gidan Malam ba in har kikai min wata ?ar nanÓ.
Ê Ê Ê ÊÊ ÒTo Umma, ALLAH ba abinda zanyi, dan ALLAH kada kice bazaki je dani ba, ina son na gaida Malam da IyaÓ.
Ê Ê Nimrah ta fa?a cikin tsalle-tsalle tana daukar botiki. Ita kuma Umma ta ?auki ruwan wankanta ta shige bayi tana fa?in, ÒIn da kinso ganinsu ai ?afarki tasan inda sukeÓ.
Nimrah da bataji mi Umman ta fa?a ba ta ?auki tuwon Inna ta fita cike da murna zasu gidan Malam, (Malam dai shine mahaifin Umma, babban malami ne a yankin kuma dattijon arzi?i da kowa ke girmamawa) koda Nimrah ta shiga sashen Inna babu kowa, dan dama ita ka?aice a sashenta tunda kishiyarta ta rasu sai dabbobinta. ?aki ta shiga ta ajiye mata kwanon tuwon ta fito, ta sake komawa sashensu ta ?akko miyar ma ta kawo. Harta juya zata tafi ta hango ?wayayen kazar Inna dake akurkin jikin katanga gab da fita a sashen. Kwana tayi ta koma wajen akurkin ta du?unna ta ?auki ?wai ?aya ta saka a botikin hannunta, sai kuma tayi ?an tsai kamar mai lissafin sauran ?wayayen, hannu tasa ta ?ara ?aukar ?aya, ta ce, ÒNi ?aya Umma ?aya. To Baba fa, shima bari na ?aukar masa, idan Inna taji harda shi akaci ai bazata dake shi ba tunda yayi babba sosai.Ó tana maganar tana le?a cikin akurkin duba wasu ?wan. Sai dai maimakon ganin ?wari taci karo da wata jaka. Hannu tasa ta jawo jakar. Tare da fa?in, ÒLah Inna har cikin jaka take ?oye ?wai, aiko saina ?ibawa Babana da KawuÓ. Tana maganar tana kici-kicin bu?e jakar, sai dai ta kasa. Abinka da yaro tana jiyo maganar Inna ta yayimi jakar ta jefa a botikin ta ?auka da gudu ta shige bayi, sai da Inna ta shigo ta shiga ?akinta Nimrah ta fito da gudu nan ma ta fice zuwa sashensu da wannan ?ar jaka da zato ta ke ita ?wai ne Inna ta ?oye a ciki.
Ê Ê Ê Lokacin da take shigowa sashensu Umma ta shige ?aki dan anata kiran sallar magriba. Anan tsakar gida ta ajiye botikin da jakar duka ta nufi ?akin gayama Umma takai wa Innar tuwon. Koda ta fa?a mata sai tace taje tayo alwala suyi salla su tafi. Cikin farin ciki ta fito, dan tasan koba komai zatayi wasa da ruwa ai. Sai da ta gama facaccalinta kuwa sannan ta tafi ?akin tayi sallar. Ta mance da batun ?wai taci tuwo suka tafi gidan Malam. Kafin su dawo ta ?ingire barci, sai goyota Umma tayi ma. Sanda Baba ke shigowa gidan ta jima da yin barci.
Ê Ê Ê Misalin sha ?aya na dare Umma da Baba sun gama cin abinci da hira Umma ta fito kaye-kaye tsakar gida sai ga Tanimu ya shigo sashen da sallama. Amsa masa tayi, tana murmurshi da fa?in, ÒA'a kawun Nimrah baka kwanta ba?Ó.
Ê Ê Ê Ê ÒWlhy kuwa ban kwanta ba Yaya, nace bari nazo nai muku sallama dan in sha ALLAHU gobe zan koma birni. Amma sai yamma zan wuce da safe dai zanje hayi wani ?aurin aure, daga can nake son nabi wasu abokanmu da zasu zo ?aurin auren suma daga birni.Ó
Ê Ê