Author : Bilyn Abdull Category : African Stories & Novels
da ?arsa ?aya Raihana da bata wuce shekara biyu ba sukabi bayansa.
Ê ÊÊ Tun ana zaman asibiti da Yakura har rashin ku?i yasa suka tattaro suka dawo da ita gida, Gwaggo Laraba ma ta sulale ta tafi abinta, sai A'isha kawai da Innarta, ga yara har takwas dan yarinyar da Fauziyya ta haifa ma sai A'isha ke shayar da ita. A wannan halin A'isha ta ?u?uta ta saka Abdul-rasheed a Secondary school, ta fara sana'ar masa da safe. Sai kuma ?ananun tsogumin ya fara tashi akan zaman Inna, wai ya kamata ya tattara ta koma Kano, rasuwa shekara ?aya da rabi amma ta tare a gidan ?arta. ALLAH sarki Inna uwa mai dattaku, haka ta tattara ta wuce A'isha na kuka Yakura dake kwance komai sai an mata da yara nayi ta wuce. Tafiyar Inna baifi da wata guda ba Babban yayan su Abdul-rasheed ya lalla?o yazo wa A'isha da batun wai yana son ya aureta, dan su ha?u su ri?e ziri'ar Abdul-rasheed. Takaici ya saka A'isha rufe ido tai masa tass, wannan abu da tayi kuma babu bincike mutane da dangin Abdul-rasheed suka sakata gaba saboda shi ya juya maganar a baibai. Haka aka dinga zuwa har gida ana cin mutuncin A'isha, sai dai su ha?e kai da Yakura da bata ?oye ma komai ba suyita kuka. Ana tsaka da wannan rikicin jikin Yakuran ya rikice matu?a, A'isha ta dinga bin dangi tana neman taimakonsu amma kowa ya nuna bazai iya ba bai da shi. Sai kawai ta yanke shawarar saida gidan da suke domin takai Yakura asibiti. Abinda ya bata mamaki sai ga ?an uwan Abdul-rasheed sunyi uwa sunyi ma?aukiya, ?arshe ma Yayan nan nashi da suke kira da Yayan gandu daya ce yana son aurenta ne ya sai gidan. Haka ta share bata nuna ta damu ba takai Yakura asibiti, ta biya ku?i za'a mata aiki da tun farko likitoci suka fa?a rashin ku?i ya hana. Sai dai UBANGIJI mai hikima bayan yin aikin da kwana biyu ALLAH ya ?auki ran Yakura??.
Ê Ê ÊÊ Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, wato gigita da magagin tashin hankalin da A'isha ta shiga da Haysam mai ?an wayo a cikin ?a?an ?ata lokaci ne ma wajen zana shi. Dan Yakura haihuwar Haysam ne kawai batai ba. Amma komai da uwa take ma ?a ta masa. Haka tsakanin Yakura da A'isha zamane na amana da ba'a batun wani kishi. A ranar da Yakura zata koma ga ALLAH ta kama hannun A'isha dana Haysam ta jaddada musu ta bar musu amanar ?a?anta. Bata yarda A'isha ta bama wani su Ma'aruff ba a duniya koda ?an uwanta ne da suke uwa ?aya. Tace ta baiwa A'isha har abada, ta kuma bama Haysam dake matsayin Babban yaya ya koma Uba a yanzu. A haka ALLAH ya ?auki rayuwarta hannayensu ri?e a hannunta.
Ê Ê ÊÊ A wannan rasuwa A'isha ta sake tabbatar da lallai suna cikin halin shiga uku ita da wa?an nan yara har takwas, dan kuwa Yakura batai wata biyu da rasuwa ba Yayan gandu ya sake zuwama A'isha da batun auren da yay mata a wancan karon, da tace bata yarda ba yace to ta tattara yara ta bar masa gidansa, ya bata sati ?aya kacal. Hankalinta ya tashi, ta kira Jamilu autan su Abdul-rasheed ta sanar masa komai dake faruwa, harna sharrin farko da Yayan gandu yay mata, shima hankalinsa ya tashi, dan basu ta?a sanin gaskiyar zancen ba sai yanzu, amma sai yace su koma gidansa dan babu yanda zai yi tunda yayansa ne. Dan haka suka shiga tattare kayansu, abinda zai zama kaya A'isha ta saida shi, sai kayan sakawarsu da abubuwa masu muhimmanci kawai suka koma gidan Jamilu da zama. Sai dai ko wata basu cikaba sabon kalubale ya ?ullo daga matar Jamilu, dan ?iri-?iri ta nuna ita bata yarda da wannan zama ba. Taya tana amaryarya haihuwa ?aya (dan zuwa yanzu itama ta haihu) ace azo a cika mata gida da ?a?a. Rikici ita da mijinta A'isha taga aurensu na neman mutuwa ta shiga tsakani da ro?on Jamilu ya barta ta wuce Kano. Zai tada hankalinsa ta lalla?asa da nuna masa muhimmancin yin hakan. Badan yaso ba haka A'isha ta hau shiri, da taimakonsa da rakiyarsa A'isha da ?a?anta takwas tai bankwana da garin Bauchi ta koma garinta na haihuwa Kanon dabo....
Ê Ê Ê Ê Babu zato babu tsammani Inna ta wayi gari da ba?in Bauchi. Al'amarin ya girgiza mata zuciya, duk da kuwa kullum dama addu'arta ALLAH ya kawo ma A'isha mafita, dan tunda taje rasuwar Yakura ta sake tabbatar da Bauchi bazata zaunu ga ?ar tata ba. ALLAH sarki rayuwa, bayan shekaru goma sha shida A'isha ta dawo gidansu babu Abdul-rasheed a duniya. Tayi aure tana da shekara sha hu?u. Shekararsu goma sha hu?u da Abdul-rasheed, yanzu yana shekara biyu da wasu wattani da rasuwa. Haysam nada shekara goma sha uku da wasu watanni a duniya. Ja'afar da Ma'aruff nada shekara takwas, Bilal nada shida, Ummi nada biyar. Mommy nada hu?u da wata takwas, Ammar nada uku da wata hu?u, sai ?ar da Yakura ta haifa a ?arshe da taci sunan A'isha suna kiranta MiMi nada ?aya da rabi. A yanzu A'isha nada shekara talatin da ?aya ne cif a duniya.
Ê Ê Ê Inna ma ba mai ?arfi bace, dama Abdul-rasheed ne ke mata komai a yanzu, hatta da karatun su Bashir, dan tunda ya rasu suma su Bashir ?in karatun ma ya nema ta?ar?arewa sai da Nasiru ya shiga ya fita ya samar musu wani taimako sannan. ?ar sana'ar koko Inna keyi da safe yanzu, sai daddawa, da itace take ru?e su ita da su Tasi'u da yake ba zama suke ba a gida koyaushe suna ma makaranta ne a Zaria, yanzu ga A'isha da iyalanta sun ?aru. Lissafin ya canja ?warai da gaske. Ita kanta A'isha tunda ta shigo gidan take tattauna abubuwa a zuciyarta, da yanda rayuwa zata sake kasancewa. Amma dai tasan zama bashi yiyuwa, babban tashin hankalinta karatun yaran, duk rintsi bata fatan karatun yaran ya tsaya musamman Haysam dake jss 2 zai tafi jss 3 ne nan da ?an watanni. Haka taita lissafi tun a daren da suka iso Kano ko rintsawa batayi ba. Washe gari karatun ya fara mata maimaicin kansa a cikin ?wa?walwa. Ga Haysam tunda suka zo ya tsangwami kansa sai dai ka gansa zaune gefe shiru. Koda yake tunda Yakura ta rasu rashin maganarsa ta sake girmama fiye da bayan rasa mahaifinsu. Ya sake zama mara fara'a da yawan walwala.........???
_Rayuwa kenan, akowane motsi bawa baya rabo da jarabawa da sabbin ?addariri, ALLAH ya baki wuyan ?auka A'isha??._
_Zaku sameshi a wa?an nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER????- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ?asar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya??_
*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya: ??_*
*_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number ??_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number??_*
*+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu ????_*
*_Typing??_*
*_??KI?A A RUWA.....!!??_*
*_Bilyn Abdull ce ????_*
*_?????? ??????? ???????????? ?????????_*
_Da s?nan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._
_Chapter 23_
__________________
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Link na grp
07077532253
https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm
https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok
IMZEEDVENTURE
Duniyar kayan kitchen ?an yayi dake maida mata ?an ?walisa a gidajensu.
Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?
Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?
To shiga link din grp na Imzeedventure?????? Kisha mamaki??? idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!
Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi????.
IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ?yale-?yale ce da ?ayatarwa da mata sukafi bu?ata musamman ?an ?walisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.
Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ?in namu dai domin ganema idanunki.
https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.
Koki tuntu?emu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*
Muna da account aTikTok@imzeed _venture.
https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1
Karku bari ayi babu ku,?????????? Nima Bilyn Abdull tuni na antaya??
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
.......Ta shin farko ku?a?en da A'isha tazo da su na abubuwan data sayar a Bauchi ta ?auka ta saya musu abinci. Dan ta fahimci abincin dake a gidan ko cikakken kwana uku bazai musu ba a wannan yawan nasu. ?an sauran abinda ya rage kuma ta shiga lissafi da tunane-tunane, babbar damuwarta karatun Haysam, sam bata so karatun yaron ya tsaya koya koma baya. Duk da suma su Ja'afar sun fara a Bauchi, amma a ganinta nasu mai sau?i ne tunda primary ne. Inna da taga shirun nata yayi yawa ta ta?ata tana tambayarta ÒMike faruwa kuma? Ni bana son ganinki a wannan yanayin tayar min da hankali yake yi matu?aÓ.
Ê Ê Ê Ajiyar zuciya A'isha ta saki, tare da ?an murmushin ?arfin hali. ÒInna ba komai ALLAH kamar yanda na fa?a miki tun jiya. Shin Inna idan na saka kaina a damuwa maganin mi hakan zai min, ita dai damuwar bazata canja komai ba, ba kuma zata dawo min da Yakura da Babansu ba wannan duniyar ba, kafin su na rasa mahaifi faÓ.
Ê Ê Ê ÊÊ ÒHaka ne A'isha ki cigaba da addu'a kinji, komai na rayuwa ?addara ce daga UBANGIJI, bawa bai isa gujema ?addararsa ba, na ?an ?ana rayuwar rashin miji data ri?on marayu nasan ?alubalensa duk da basu kai naki yawa ba, sai dai tabbas nawa mai sau?i ne dan ban rasa tallafi daga dangin mahaifinku ba, Bilyamin yayi ?o?ari na ganin kun samu duk abinda ?a mai rayyayen mahaifi ke samu. Shiyyasa al'amarin dangin uban ?a?anki yay matu?ar ban mamaki da tsoro, ya kuma tabbatar min da zamani ya fara canja salon da muka sanshi, ace bawan ALLAHn nan ya ?are rayuwar samunsa akan hidimarsu amma yanzu ?asa ta rufe idonsa a ga?ar da sukafi kowa morarsa su juyama zuri'arsa baya, wannan wane irin rashin tausayi ne, wane irin zumunci ne? Musamman yayan nan nashi yafi bani mamaki fiye da kowa. Ko kunya baya ji yazo kuma yace zai aureki kamar dama yana jiran ya mutu ?in neÓ.
Ê Ê Ê Ê ÊÊ Hannu A'isha ta kai ta share hawayen da suke ziraro mata, fuskata da murmurshi mai ciwo tace, ÒBabu komai Inna, kansu sukamawa ba shi ba, shi dai dan ALLAH yay musu da zuminci, amma tunda sun nuna su bazasu ri?i bayansa ba ai babu komai. Suma kuma ai sun haifa, kuma mutuwar tasan gidan kowa. Shiyyasa al'amarin mutumin nan ya bani mamaki, kana yaya dan ?aninka ya rasu kazo kace wai matarsa ta aureka, har sai na auresa ne zai taimaki abinda Abdul-rasheed ya bari a duniya. Inna a zatona ai ana barin halak dan kunya, ai bashi yayansa ba ko Sufyan dake ?aninsa wlhy bazan iya aure balle shiÓ.
Ê Ê Ê Ê Ê ÊÊ ÒKibar she?ani, tunda yanzu kin bar musu garin sai yaci kansa shi da matan nashi masu zaginki su mahaukata masu kishin banza. ?a?a kuma mu ALLAH ya bamu yanda zamuyi mu ri?esu mu basu tarbiyya, ALLAH ya raya miki su ya baki tsahon rayuwar da zaku mori juna ke da su gaba ?ayaÓ.
Ê Ê ÊÊ ÒAmin Inna na gode. Sai dai Inna makarantar yaron Muhammad nan ita ke damuna yanzu, nasu Ma'aruff mai sau?i ne. Shi ko kinga Secondary yake aji biyu, nan da wasu watanni zai wuce aji uku, bana son ko baya ace ya komai balle karatun ya tsaya. Ga ku?in da suka rage min bazasu isa ai batun canja masa uniform ?in sabuwar makarantar da litattafai ba. Shiyyasa nake tunanin ko zan fara wankau ne Inna? Ko kuma naje gidan Iya Tabawa ta sama min gidan aiki?Ó.
Ê Ê Ê Ê Ê ÒWannan tunani ne mai ?yau A'isha, duk da harga ALLAH bana son irin wannan sana'o'in tunda duk na jigata jiki ne, wasu ma na kallonsu kamar ?as?anci ne, amma idan na hanaki banda hanyar wani abun bayan su, in ma ance sana'a sai da ku?i, mu kuma bamu da suÓ.
Ê Ê ÊÊ ÒInna nima baso nake yi ba, amma babu yanda zanyi. Dama dabarata anan idan na ?an yi kona watanni ne zuwa shekara in sha ALLAHU abinda aka ?an samu sai a fara sana'ar zai fi zaman shirun da jira a wajen mutane. Ni dai fatana duk su koma makarantar, na kuma share hawayensu kada suyi kukan rasa mahaifi kwata-kwataÓ.
Ê Ê Ê ÒTo ALLAH yasa mu dace, yasa haka shine mafi alkairi, yay ri?o da hannayenki, ya zama garkuwarki. Amma kafin a samu mafitar ita bokon zan kaisu wajen Malam su cigaba da makarantar allo tunda kinga acan Bauchin ma suna zuwaÓ.
Ê Ê Ê ÊÊ ÒEh Inna suna zuwa, hakan kuma yayi, dan nima bana son zamansu a gidan. ALLAH ya ?ara lafiya da tsohon rai mai albarka da amfani. Tabbas yau da bani dake Inna dana shiga ukuÓ.
Ê ÊÊ ÒBazaki shiga uku ba ?ar nan, domin kuwa UBANGIJIN daya hallicemu bai manta da kowa ba, fatanmu dai ya bamu dama da ikon sauke ha??in marayun nan da mahaifinsu ya hidimta mana da dukiyarsa da lafiyarsa sanda yana raye, muma ALLAH ka bamu ikon kwatantawaÓ.
Ê ÊÊ ÒAmin Inna.Ó
Ê A hankali Haysam dake tsaye ta jikin window yana saurarensu ya zame jikinsa yabar wajen. Cikin soro ya koma ya zauna, tattaunawar mahaifiyar tasa da kakarsa na dawo masa dalla-dalla. Yasan abubuwa ka?an da suka faru a Bauchi, amma ba duka gaba ?aya ba, domin Mammah bata bari su fahimci komai dake faruwa, dama shine mai shekarun fahimtar, koya ga wani abu idan ya tambaya sai ta nuna masa ba haka yake ba, idan ya matsa ma saita fara masa fa?a, dole yake yin shiru ya bata ha?uri. Daga nan kuma ya saki zancen kawai saboda gudun ?acin ranta.
Ê Ê Ê Ê Ê Hawaye masu zafi suka sakko masa a karo na farko, batare daya gogesu ba ya du?ar da kansa ?asa kawai suka cigaba da ?iga cikin ?asa. Ya jima a wajen yana tunani da iya abinda ?wa?walwarsa zata iya cu?awa da kwancewa, sai kuma ya mi?e ya fita a gidan. Ba yau ya fara zuwa Kano ba, sai dai idan sun zo ba yawo Mammah ke barinsu sunayi ba, idan ma zasu fita sai da ita, idan ko da Baba sukazo kwana ?aya ne kuma duk inda zaije tare suke tafiya shima ko Uncle Nasiru, Mammah kuma ta sanar masa yanzu Uncle Nasiru baya Nigeria ya tafi ?aro karatu ?asar waje. Ya ?an san wasu wajaje a anguwar, dan haka ya shiga zagayawa musamman inda kasuwa take ana ?an harkokin saidawa da sayarwa. Haysam akwai hankali da wayo da nutsuwa, shiyyasa Babansa ke kiransa yaro da hankalin manya. Sai da ya gama zagaye-zagayensa ya dawo gida, ya samu Mammah da Inna a tsakar gida suna hira, su Momy nacin abinci.
Ê Ê Ê A'isha dake kallonsa kallo irin na tuhuma ta ce, ÒDaga ina kake Muhammad?Ó.
Ê Ê Ê Bai iya ?arya ba, amma baya son sanar mata abinda ke a cikin zuciyarsa, dan haka ya bata amsa kansa a ?asa. ÒMammah nan baya naje cikin kasuwaÓ.
Ê Ê Ê ÒCikin kasuwa kuma? Yin me to? Tun la'asar nake nemanka a gidan nan jiba har magrib ta kusa.Ó
Ê Ê Ê Ê Ê ÒKiyi ha?uri, nazo na fa?a miki na samu kuna magana da Inna shiyasa na fita kawaiÓ.
Ê Ê Shiru tai bata sake cewa komai ba, dan bata masa fa?a a gaban ?annensa koda ace ya mata kuskure, balle ma akan da?e kafin Haysam yay mata wani laifi da zata tuhumesa, yaro ne mai tsantsani da kiyaye ?acin ran iyaye. Kiran sallar da akai ce ta sashi tattara su Ja'afar suka wuce massalaci bayan sunyi alwala....
><><><><><><
Ê Ê Ê Tun daga wannan rana, rayuwarta ta canza gaba ?aya, A'isha ba uwa bace kawai, ta zama har uba, mai ciyarwa, mai kariya, mai ?ora ?a?a akan tafarkin gaskiya. Domin kuwa a ?oye ta samu aikin aikatau a wani gidan masu ku?i ta hanyar wata mata Iya Tabawa. Zata dinga zuwa da safe tayi ta dawo gida, da yamma ta koma ta ?ara yi ta dawo gida, ta za?i wannan yawon ne saboda tarbiyyar ?a?anta, ta fison koyaushe su dinga ganinta tare da su. Inna kawai ta san inda take zuwa, su Haysam kuwa sai tace musu makaranta ta samu ta manya a inda take zuwa ?in, Haysam yasan ba hakan bane ba, dan tun randa yaji hirarta da Inna yake biye da duk motsinta, hatta gidan Iya Tabawa da taje domin ta nemar mata wajen aikatau ?in ya sani, ranar yasha kuka da daddare sosai, tausayin mahaifiyarsu da ?aunarta suka sake cika masa zuciya, dan haka ya ?ara ?arfafa kansa akan nasa ?udirin shima dake ?oye a zuciyarsa game da taimakonta. A'isha bata tsaya a wannan aikatau kawai ba, a ?an lokacin da take dawowa gida bayan kammala aikin safe a gidan aikinta sai ta fara amsar wankau ?in mutane tanayi, bata damu da ?ananun maganar da mutane suka fara a anguwar ba, ta toshe kunnenta ta fuskanci rayuwarta. To babu mai taimakonsu sai gidan su Nasiru, da yayansa Zubairu daya koyama Abdul-rasheed ?inki, shima kuma zuwa yanzu iyalai sun fara masa nauyi dan matansa har uku, sai kawunta da tsufa ya fara kamawa, dan mi zata damu kanta da maganar fatar baki daga wanda basa taimakonta da komai. Da ku?in wankau ?in nan take saya musu abinci da ?an cefanen yau da kullum, dan duk wuya bata barin gida babu abincin da zai kai kwana biyu, ga yara har biyu tana shayarwa, dan ma Ammar ya isa yaye dan suna zuwa Kano babu jimawa ma ta yayeshi sai Mimi data rage.
Albashinta na farko da aka biyata a gidan aikinta ta maida Haysam makaranta da shi, da ro?o da neman alfarma harda kukanta ta samu aka sakashi js2 ?insa kamar yanda yake a Bauchi basu maida shi baya ba, suma su Ma'aruff da Ja'afar ta ?inka musu Uniform suka koma, sai dai su