Author : zallah Category : African Stories & Novels
min alqawarin ba zaka taBa kulata
ba, ba zaka taBa kusantar ta ba
matsayin mace"ba. Abubakar yai murmushi, ya
lakacc mata
hanci yana fadar. "Nayi sarkin kishi". Suhailat tai
murmushi cike da jin dadi,
Abubakar ya yunkura ya mike da ita a jikinsa.
Muje. mu karya kada yunwa ta kama mu".
Suhailat dai batai magana ba sai dai murmushi.
Rukayya ta gama duk dokin da' zata yi,
' tana zaune bacCi barawo ya sureta ba ita ta iya
farkawa ba sai ana kiraye-kirayen sallar la'asar.'
Ta mike tana faman murza idanuwa, tasha
,bacci matuka.
Wata irin yunwa ta bijiro mata saboda bata karya
ba, a dole tayo .falon gidan Suhailat ‘ da
Abubakar 'suna baje a tsakiyar falon saman
kafet ‘Abubakar na kwancc ya tada kansa “da
da filon kujera suhailat na kwancee kanta a
saman qirjinsa suna kallon (laptop)
Gaban Rukayya ya yi wata mumnunar faduwa har
ta kusa faduwa saboda tsoro, ta datse bakinta
saboda ihun da ya nemi kufce
mata. Su duka suka zubo mata idanuwa sai
faman makyarkyata take.
Abubakar ya yunkura ya tashi zaune, ya daka
mata tsawa
"Ke Uwar me kika fito yi kika zo kika
tasa mu gaba kamar kin sami talabijin? Me kike
kallo?“ ~ Rukayya. ta hau rawar murya, "Um.“
Dama...dama... yunwa nake ji ne shi yasa abinci
zanci". .
‘ Suhailat ta ce, "Abinci, ki ka bamu ajiya?
Tantiriyar mara'kunya, k0 dai kinzo kigag. abinda
muke tunda laben da kike bai miki ba?" Abubakar
ya ce, “To sai kizo ki wuce ga Sauran. abinci can
saman (table) kici, kuma idan kin gama ki
kwashe kayan ki kaisu kicin ki wanke
ai dai kina jina ko?"
Rukayya ta daga kai alamar ce, sannan 'ta wuce
simi-simi ta gefensu, Suhailat ta watsa mata
harara har da jan tsaki, tace
Sakarya, bakauya kawai. Allah wannan
da ganinta za tai iyayi". Abubakar dai bai ce
komai ba, ya koma ya kwanta ya ci gaba da
abinda yakeyi
Rukayya taje gaban (table) tana mazurai, shin
zata zauna ne koko zatA diba ne
ta wuce? Bata da amsa, don haka ta 'dauki filet
da cokali ta dibu-iya yanda zata iya cinyewa ta
zauna a qasa tanaci sai kace wacce aka tsare sai
faman tutturawa take hannu baka hannu kwarya.
Abubakar dake kwance ya; hangota dirshan a
kasa kamar wata almajira ya tabe baki ya dauke
kansa.
Tana gama cin abincin.ta mike ta kama tattara
wurin, sai data gama sannan ta dauka ta nufi
hanyar fita.
Abubakar ya ‘ watso mata kira, "Ke
mahaukaciya! 'Gidan wa zaki kai?"
Rukayya ta tsaya tana mazurai, sai da ya sake
maimaita mata tambayar sannan ta ce '
"Fita zanyi in wanke" . Ya ce," Ke, zo ki wuce
dallah nazo nuna
miki".
Rukayya ta dawo ta tsaya sai faman walqita
idanuwa take, sai da ya nutsa yasha iska tamkar
ba zai tashi ba, nauyi ya ishi ‘Rukayya
saboda‘kayan dake hannunta, sannan ya tashi ya
nufi hanyar kicin ba tare da ya tanka mata ba.
Sai da ya shiga kicins din yana tsaye yana jiranta
yaji shiru, sannan ya leqo.
"Ke uwar me kike anan tsaye?" 'Rukayya tai
saurin binshi, bai ce ta sauke*' kayan
hannuntaba, ita kuma tana tsoron ta. saukc tai
laifi “haka-ya shiga nunnuna mata yanda ake
amfani da kayayyakin na‘urorin dake kicin din
gaba daya, sannan ya ce
"Muje'kuma (toilet) in nuna miki".
Da kayan ta bishi Abubakar ya watsa mata wani
irin kallo. _
"Ke wai me yasa har yau ba zaki hankali
ba, wai kullum'kina girma kina 'cin qasa?
ajiye tiren kwanikan muje”. Rukayya ta ajiyc
sannan ta bishi, duk wani abin da yasan bata
sanshi ba sai daya nuna mata, sannan ya dawo
da ita kicin din tai wanke-wanke. .
Har ya nufi hanyar fita ya waiwayo, "Au . na
manta ban miki kashedi ba, nasan halinki da
tsinanniyar amsifa da fadan tsiya, to wallahi
tallahi duk randa ki ka sake gigi ya kaiki kika
takali mata ta k0 kikai mata rashin kunya, kin
san halina sarai yarinya, zan iya abinda yafi haka
ma.
Sannan batun aikin gida, ki tabbatar da garin
Allah yana wayewa duk abinda kike ki saki ki hau
gyaran gidan nan, da kuma kuku ya shiga kicin ki
bishi kina kakkama mashi ayyuka da safe, rana
da kuma dare, ina fatan kin gane"
Rukayya ta daga mashi kai, sannan yaja kwafa
ya wuce. Ta raka shi da kallo har ya bace,
‘sannan ta dawo da kallonta akan tilin kayan
'wanke-wanken dake gabanta, taja wata .
nannau‘yar' ajiyar zuciya ta duqa ta soma wanke
wankcn.
Tana cikin goge-goge a kicin din Kuku ya shigo
ya dora abincin . dare, saurayi ne dan kimanin
'Shekaru talatin da fan wani abu, Bayerabe ne
amma Musulmi yaji Hausa sosai. '
Suna hada ido da Rukayya ya sakar mata
murmushi. .
' "Sannu 'yan mata, ashe na samu abokiyar aiki,
yaushe aka kawo ki gidan nan ne?" Rukayya
tamkar ba zatai magaba ba, ta ce.
' "Dazu".
Ya waro ido, "Daga zuwanki kuma ba za ki huta
ba har Zaki _ soma aiki?" Rukayya tai Shiru ba
tare da tayi magana ba, . don haka shima kukun
ya cigaba da abinda ke gabansa. ' . RuKayya ta
gama wanke-wanken, sannan
ta dauki doyar da kuku ya bata ta feraye masa,
ta cigaba da fira. Tana gama feran doyar ya miko
mata yanke-yanke, tana yi ba ita ta samu 'tabar
kicin din ba sai da ya gama girkin tsaf. ' Abun
ya‘zama jiki, kullum in zai yi girki sai ya kira ta,
duk wani aiki mai wahala ita yake bawa tai masa,
sannan idan an gama duk
lol rukayyah dai ta zama yar aiki karfi da yaji
naku har kullum A,I,S KE cewa asha karatu lafiya
sannan a dinga comment
RIKON KAKA
CHAPTER15
abinda akai amfani dashi ita yake barwa ta
wanke ta goge kicin din, safe, 'rana da daddare.
Tun Rukayya na jin wahala har ya kal‘ ga ta
saba. ‘
Tund da asuba Rukayya ta farka tai alwala tai
sallah, sannan ta koma baCCin asuba kamar
yanda ta saba a. kullum. Cikin barci taji an maka
mata wani uban duka a jiki tamkara mafarki, ta
zabura ta mike a gigice tamkar mai shirin fita
hayyacinta. ‘
.Suhailat ce tsaye a, bakin gadon tana" cikin
shiga ta alfarma, tai kyau har ta gaji, gashin kan
nan nata yasha gyara, yana zube > saman
kafadunta. Duguwar riga ce a: jikinta (miik
colour ) mai adon duwarwatsu bakake tun daga
sama har kasa sai daukar ido suke. Dan
'qaramin bakin ya sha janbaki sai daukar ido
yake. ‘ .
Ta. nuna Rukayya da siririn farin danystsanta
wanda yasha bakin lallr 'cikin tsawa tace
‘ ”Tashi ki fita munafuka kije ki gyara min
falulluka'na, wato ke har wani bacci koma saboda
samun Wuri. T0 idan ma kina _ tunanin barci kika
zo yi gidan nan to ki, gaggawar: sauya tunaninki,
don ko' yan aikin .‘dake cikin gidan nan sai sun
fiki hutawa da Jin
‘ dadi kinji na fada miki Tashi muje ki gyara
.min dakuna kinji na fada miki
wani irin tsoro da fargaba suka kama
'Rukayya ta zabura ta fice daga falon, ' ‘ .
Suhailat taja wani dogon tsaki tabi bayan‘ ‘
RUkayyar ta sameta tsaye a falon nata sai
makyarkyata take suhailat ta wur’ga mata
tsintSiya,ta daki fuskarta ta ce
' "Ki maza ki share ki kakkabe ki" ki goge,kiJe ki
gyara min komai kamin kuku ya iso ku shiga
kicin" ‘ .'
Rukayya bata iya cewa komi ba har ” Suhailat ta
wuce‘, sannan ta ja wata irin ajiyar zuciya wadda
ke bayyanar da tsananin tsoron daya kama ta
Rukayya kenan ko ina bakinta ya tafi da tsiwa da
fada? Wadda rigima k0 ba tata 'bace 'shiga take
ta siyi fadan tai ruwa tai tsaki; amma gashi yau
babban fada ya' tunkarota tana‘ gocewa, k0 me
yasa‘? K0 da yake Hausawa na cewa k0 Baba da
Babansa '
Duk da rashin aiki irin na RuKayya da son‘jiki,
amma yanzu duK babu su, ta Saki jiki tana ta
faman aiki. Ta zama wata (Very silent), tai
(cooling) sosai tamkar ba ita ce mai shegen
surutu nan ba. Rayuwa kenan, duniya juyi~ juyi
wai kwarto ya da. ya fada ruwan zafi yace,
"Daminar bara ba irin ta bana bace".
*
Y‘au wata daya da zuwan rukayyah gidan
Abubakar, kullum cikin wahala take, bata da zama
sai cikin dare, don haka idan ta kwanta kamar
matacciya, ana asuba kuma zata farka ta fara
daga inda aka tsaya. Saboda wahalar datake
gidan k0 Bangarenta bata iya gyarawa bata taba
wanka ba, tun kayan da aka kawota dasu
sune a jikinta har yanxu da take ‘duqe tama goge
gogen na'urorin duke qaton falon gidan.
Abubakar ya fito daga falonsa shi da Suhaiiat
tana manne a jikinsa, yana sanye da kayan
ma'aikata a jikinsa, Suhailat na rungume da
jakarsa ta ma'aikata. Rukayya ta saci kallon . su
tai sauri ta dauke kanta daga kansu. .
Suhailat ta dubi Abubakar, "Au Dear, na manta
don Allah ( just five minute)".
Abubakar ya ce, "K0 minti daya 'kika qara sai dai
ki dawo ki samu bana nan".
Suhailat ta ce "Na yarda"
‘ Sannan ta kwasa da gudu gudunta ta nufi
falon da suka fito
Rukayya ta dauki bokitin da ta jiqa omo da mofa
ta gifta Abubakar,muryarta a raunane ta ce
"Ina kwana?"
Sai da ya matsa yana kakkare hanci kamar
wanda yaga wata Shara, fuskarshi a dagule ya ce
"Subhanallahi! Kina da hankaii kuwa? Dubi kayan
jikinki yanda sukai dakal-daqal, ke
ko warin jikinki bakya ji sai kace mai kuli kuli?
Mtsw!’ Allah Yai wadan wannan qazantar taki,
sakarya wadda'bata san ciwon kunta ba. Wallahi
kar ki sake na qara ganinki da wadannan kayan,
(stupid) kawai, wuce daga nan dallah”. . .
Rukayya ta, wuce simi~simi tana bin. jikinta da
kallo, ita bata ga wata shahararriyar dauda da tai
ba da har zai mata wannan cin fuska ba. ,
Hawaye suka ciko mata. a idanuwa, duk qazantar
da take ma ai 'su suka ja mata, aikin ‘gidan
kawai da take ai ba qaramin ' tashin hankali
bane.
Ta sa‘hannu ta ‘share hawayen da suka ' zubo
mata, ta duqa tana zubar da ruwan
Kamar kullum, yau ma tamkar marar lafiya
Rukayya ta wuni, ana kiran sallar la’asar sannan
ta samu lokacin shiga (toilet) ta samu tai wanka
tana fitowa ta samu mai ta shafa sannan ta Ciro
daya daga cikin Kullin kayanta ta
saka, ta fito don tasan yanzu kuku yazo su dora .
. abincin dare. _ . , Suhailat tana zaune saman
daya daga
cikin kujerun dake zube a falon, tana sanye da , .
shigar shadda doguWar riga har kasa mai hade
da zanenta, ta sha ai'ki tun daga sama har kasa
sai daukar ido take, mai ruwan kasa-kasa da
ganin shaddar zata yi tsada. Tun daga kunnenta
har wuya har zuwa" ‘_ kafarta da yatsun
hannunta gwala-gwalai ne, " . sai walkiya suke.
Babu abinda yafl daukar . ' 'hankalin Rukayya sai
daurin kallabin dataima kanta, ta dora kafarta
daya kan daya da takalmi mai tsananin tsini a
qafar tana ta karkadawa. ’ ‘“ ' Ta watsawa
Rukayya wani irin kallo wanda ya .kusa ‘sata
makyarkyata, Suhailat tace. . ke zonan gaban
Rukayya yai wata mummunar
'_ faduwa, ta nufi inda Suhailat take zaune ’ ..
Bata ankara ba sai dai taji ta flsgota ta fadi qasa,
ta sa hannu ta dauke la da Wani
' gigitaccen mari har sau biyu.. ' Rukayya tasa
kuka tana faman rawar
jiki, Suhailat cikin tsantsar masifa ta soma
magana.
"Uban waye ya koya miki yin wanka a cikin gidan
nan? Wallahi sai kin fada min wanda ya kitsa
miki wannan".
’ Ta janyo Rukayya ta shiga duka tako' ina, tun
Rukayya na ihu har ta soma qokarin kwatar.
kanta.
Suhailal ta tsaya tana tafa hannuwa,
"Lailaha illallahu, kokawa za kiyi dani iye? '
Kokawa za kiyi dani na ce? To bisimillah”.
_Cikin kuka Rukayya ta ce "Wallahi -ba
kokaWa xa muyi. ba, kiyi hakuri don Allah.
Suhailal tace”Ai Allah yau sai kin fada min wanda
ya koya miki yin wanka da sauya kaya a cikin
gidan nan". ‘ Rukayya tace"Ai Yaya Abbakar ne ‘
Cikin kaduwa Suhailat= ta saketa tana maimaita.
"Abbakar, wane Abbakar din?"
"Yaya Abubakar, ai shi ne dazu zai fita ya...."tace
me? Dakin ki ya shiga? Ku kai ‘ me? ' Me ya ‘
shiga ku kayi‘?“ Cikin rudani da kaduwa Suhailat
ta jero mata tambayoyin da ita kanta bata san
ma 'anarsu ba, sai ma tsoratar da Rukayyar da
tayi da ganin yanayinta, ta rinka ja da baya cike
da tsoro. ‘
‘ ,Suhailat tace, “Dakata daga nan inda kike' ki
bani“ , amsar 'tambaya ta“. Cikin ’rudani Rukaya
ta ce, "Dazu da zai fita a _ falo ina goge-goge ya
ganni yace in wuce inje in canja kaya, kar ya
dawo ya sameni dasu a jikina".
Suhailat taja wata nannauyar ajiyar zuciya mai
karfi sannan tace ‘
‘ ’ "Wuce muje ki tattaro min duka kayan da kika
zo dasu gidan nan".
Ta“ tisa Rukayya a gaba suka nufi sashinta jiki
na rawa ta tattaro mata duka‘ yan komatsan da
tazo dasu, Suhailat ta dauka ta zubesu a qasa ta
bincike kayan, ta zaro mata
1page is missing
taje ta kona kayan," sannan .ta wuce sashinta,
kai. tsaye toilet ta fada ta sani
(scptol) da ruwan xai .ta Wanke hannayenta ,
sannan ta fito abinta. Bayan sallar magaruba
Rukayya na
kwance saman makeken gadon dake dakinta
tana. kallon t.v din dake manne jikin bangon .
.dakin, idonta ne kawai saman tv din, amma gaba
daya ilahirin hankalinta baya kai, xuciyarta
ta lula duniyar tunani
' ’ A .hankali ta dago kanta tana kallon kofar”da
taji an turo ,Suhailat ce ta shigo babu'
ko sallama, rukayyah ta zabura ta tashi zaune
sai rarraba idanuwa take . Suhailat taja ta tsaya
riqe da kugu kafin ta kallii rukayyah ta tabe baki.
““ "
tace lallai samun wuri wato anxo birni ansha jar
miya har kinsan kixo ki miqe saman gado kina
kallo ko , to daga yau kin gama shi, shegiya
wayar dake hannunta ta lallatsa sannan ta kara a
kunne
hello sagir don allah kazo ” zaka cire min
na'urorin kallon dake sashin bakine don Allah yau
k0 gobe
Ta danyi jim kafin ta ce"Okay, to Allah Ya kaimu".
Ta kashe wayar, sannan ta ' dubi Rukayya. , ‘ .
‘ "To nayi maganin tsaffin idanuwa wanda duhun
gona ya riga ya kashe sai inga ta iyayi kuma.
Don na lura idan nai sake wata rana sai kin ce
dani zaki goga, don haka ke da gogewa sai dai a
lahira haka za ki qare cikin duhun'kai da‘ jahilci.
Ki tashi ki flto falo kuma dan uwan naki na kira".
"Mtsw!". ‘
Ta ja tsaki, ta balbadeta da harara
Jikin Rukayya ya kara sanyi tamkar mai
masassara, haka ta yunkura ta sauko daga kan.
gadon ta nufo falon kamar marar lafiya
. . Abubakar da Suihailat suna zaune saman
kUJera mal zaman mutum biyu, Rukayya ta
tsugunna a ..gabansu.
tace gani
Abubakar ya watsa mata, ‘ wani irin razanannen
kallon daya motsa mata hanjin cikinta
“Sannu, sannu marar kunya, wato kenan har jinki
kike wata tantiriyar marar kunya Hmm! Rukayya
kenan masu ilimi da wayewar kai ma sunyi sun
gama ballantana ke dake fama da ciwon jahilci
da duhun kai
K0 da yake ai ance dogo da hankali dama dacene
amma banyi tunanin ‘rashin hankalin naki har ya
kai kice zaki kokawa da iyalina ba. ‘ Ashe wautar
da sakarcin dake dankare cikin kanki sun‘wuce
iya sanina Wato duk nasihar' danai miki ashe ta
bayan kunnen ki tabi ta wuce bata shiga ciki ba
kenan? ‘ Saboda kina ganin kamar ban iya
daukar mataki akanki wato don na daina taba
lafiyar jikinki ko to kisani 'akan matata wallahi
zan iya jirkita miki kamanni in barki kwance
kinji na rantse miki wannan girman jikin naki da
kikai bazai hanani dinga jibgarki kaman allah ya
aikon ba
lol su abubakar manya
asha karatu lafiyaa zallah
RIKON KAKA
CHAPTER16
yace wannan ya zamo na farko kuma “na Karshe,
wallahi k0 kallon banza. kika sake kika Kara yi
mata na lahira saiya fiki jin dadi. Tashi ki bani
wuri!". ?
Ya daka mata tsawar da batasan sandata zabura
ta rufta aguje tai hanyar sashintaba, yaja tsaki.
"Mtsw! Zokalar banza zokalar wofl“. -. Ya dan ja
numfashi kafin ya maida kallonsa akan Suhailat. ‘
"Kiyi hakuri’ don.Allah, ki qara daddaure mata,
saBoda‘ yarinyar bata da wayau ko kadan, k0 can
haka take da shegen fadan tsiya, ga shegen karfi
kamar namiji, sai ‘ kace -ba mace ba. kibita a
hankali, ' kinga 'mahaukaciya ce, kar ta'zo ta
kayar min dake a” banza". suhailat ta watsa
'masa wani kallo mai kama da: harara, cikin sigar
zulaya tace ”Oh! Wato ni raguwa kakr dauka ta
kenan ko?," ‘ Abubakar yai dariya kafin ya ce'
”zaki hada karfin mutumin kauye Wanda ya saba
da cin‘dawa da masara da na
mutumin birni, wanda bai da abinci sai biredi da -
indomie?” Suhailat ta ce, “Allah k0?“
Ya ce, 'Da gaske idan kuma baki yarda
. ba na kirata tazo ku gwada naga wanda za'a
kayar".
Suhailal tai murmushi kawai ta mike ta
janyo“wayarts dake ta faman ruri akantebir din
dake , gabansu.
Rukayya na shiga sashinta ta fada kan ‘ gado ta
soma rera kuka mai tsuma zuciya, kalaman
Abubakar sukai mata tsaye a makogoro' _ tamkar
.mashi, ji. take tamkar zata hadiye zuciya saboda
tsabar bacin rai da bakin ciki. ‘ Ada bata damuwa
da duk wulaqancin da Abubakar ke , mata amman
to amman yanzu mai yasa abin ke damunta?
Tambayar .da taiwa kanta kenan' wadda bata da
mai amsa mata ita. Tai saurin' zabura ta mike
lokacin da maganganunsa ke dawo mata.
wallahi akan matata zan iya jirkita miki halitta in
barki a kwance kinji na rantse miki kuma
don wannan qatuwar da kikai bazai hanini dinga
jibgarki kamar allah ya aikoni ba
Rukayya ta maimaita, "Katuwa kuma‘!" A sanyaye
ta nufi gaban dogon madubin dake tsaye a gefen
gado ta soma bin kanta da ,idanuwa. Ita kanta
sai da gabanta ya fadi, ta sa hannu tana shafa
wuyanta wanda ya ciko duk wasu rami' da gurbi
ya cike ldanuwanta suka dira saman kirjinta
wanda ya qara cika tamkar zai fasa rigar ya' filo.
lol
Gabanta ya fadi, to tun yaushe ta zama haka?
Ta dan karkata yana kallon kugunta da cinyoyinta
wanda suka qara budewa, sai dai har yau bakin
nan na nan kamar baqin zunubi
Rukayya ta koma tanara sharar hawayenta,
tabbas samun cima mai ' kyau yana gyara jiki
fiye da shan wasu kwayoyin magani.
Ko ina Kaka take yanzu? Idan ba zata manta ba
yau satin su shida rabon da su hadu tun ran data
kawota gidan gashi jin dadin
da take mata kwadayinsa amma ba a sameshiba,
‘ kullum tana cikin zubar da hawaye amma gashi
har wata kiba take, kota mece ce Oho. Ta bawa
kanta amsa.
Ga dukkan alamu Rukayya ta shiga shekarar cikar
‘yan matancinta, saboda ga jikinta nan ya nuna,
sannan ga tunaninta ya soma canjawa daga na
quruciya zuwa na masu hankali.
Tasa hannu ta share hawayenta sannan ta laluba
ta kwanta tana maida ajiyar zuciya, a haka bacci
barawo ya lallaBo ya sureta.
A kwana as tashi ba wuya wurin Allah, yau watan
RuKayya biyu a’gidan Abubakar, babu wani
abinda ta samu na cigaba illa wata irin natsuwa
da tazo mata, da raahin son magana, ga wani irin
hakuri. In zaka sa yatsa a bakinta ba zata iya
cizawa ba.
gurin qazanta kuWa sai abinda yai gaba, ~
' ita kanta tsamin jikinta ya takura mata
ga
atamfar dake jikinta har ta soma yayyagewa
don dama can taji jiki shiyasa ko aiki
take ta shiga kare-kare kenan, kada wani yaga
tsiraicinta. -
Yanzu haka aikin take ita da kuku suna girki, shi
ne ta dauki tawul din da suke goge~ goge ta
daura a kugunta a saman zanin jikinta, tana
aikinta. ‘
Suhailat ta leko kicin din, "Da Allah ku
saki wannan aikin, ina da baqi maza a hada masu
abin motsa baki, (just 10 minute) na baku". . , ‘
bata saurari abinda zasu cc ba ta juya ta. ' fice
Kuku ya dubi Rukayya cike da damuwa a
yanayinsa,kafin ya ce
"Gaskiya Hajiya tana da matsala, yanzu
maimakon ta bari mu qarasa abinda, muka dora,
a'a sai .dai mu sauke mu dora wani‘ Rukayya ta
tabe baki ba tare data tanka ba,taci gaba da
abinda‘ take. Shima ganin hakan yasa ya juya ya
soma abinda ke gabanshi, don yasan in ya biyeta
sai ya wuni yana maga’na bata bashi amsa guda
ba, don haja yaja bakinshi ya tsuke
Suka hadawa baqin kayan kwalama irin su
(snaks) kusan kala