Author : zallah Category : African Stories & Novels
abinda ke faruwa tun daga
dalilin barin Ruqayya gidanshi.
har zuwa yanzu. Mamaki ya kama Kawu ya rinqa
zuba
sallallami yana fada akan danyen hukuncin Kaka
da kuma wautar Jamilu, daga,qarshe yaiwa
Abubakar naisha da kuma fatan' alkhairi. Yasa ya
kira Rukayyar itama yai mata nasiha sosai
Ya so su kwans sai gobe su juya, amma
Abubakar ya ce a‘a, saboda zai je office.goben.
Kawu yasa RuKayya ta kwaso kayanta,“ ya
zubaSU mota sannan sukai gaba bayan yaima
kawu kyautan kudi masu yawa sannan suka
kama. hanya babu wanda ya kula wani, Ruqayya
ta gaji da kukanta har tai shiru. Bai ce mata ci
kanki ba har burci barawo yai awon gaba da ita
Basu iso Katsina ba sai karfe goma .saura 'da
yan mintina, maigadi ya bude_ mushi qofa ya
kutsa .motarshi a ciki kai tsaye gurin ajiye motoci
ya faka motar tashi sannan ya fito a gajiye yake
likis dan da kyar ma yake iya daga. kafa ya
budema Rukayya dake Zaune yana kokarin kaukar
ta ta farka a tsorace
gami da ture hannayen nasa Ya yi murmushi
sannan ya matsa yana fadar ., . ‘ "Ki fito mun.
iso" Ruqayya ta bata fuska tana fadar:
Ni wallahi bahu inda zan matsa ‘sai ’ka . maidani
gaban uwata
Abubakar yai dariya“ sosai kafin yace
”Wacece uwar taki kuma? Kidai ce kakarki me
sangartar dake, kuma yarinya ke da qara ganinta
qila sai kin koma wankan jego“ Rukayya ta
harare-shi tare da tabe mashi baki ta dauke
kanta ta turo mashi qeya.
Shi daria ta bashi don haka bata ga lokacin da ya
janyo hannunta ba sai dai ji tayi an sureta gaba
daya anyo waje da ita ; ‘
Rukayya ta soma shure~shure tana zillewa amma
bata kufce daga hannuwansa ba har$ai da ya
danganata da katafaren falon gidan wanda wurin
zilIe-zillenta tasa suka fadi akan‘tayils, amma duk
da haka nan bai saketa .ba, tana cikin
hannuwansa sai da ta gartsa mashi cizo a
hannuwan sannan ya sakcta ita kuma ta zabura
ta mike ta” kwasa aguje 'ta barshi, falon,
amma‘sai ta kasa bude qofar a bude take ba kcy
aka Saka ba k0 sakata ba amma ta datse Haushi
ya kama Ruqayya, ta rinqa jijjiga qofar da ko
gezau bata yi.
Abubakar yana kallonla ya mike yana dariya yai
shigewarsa kicin hankalinsa a
kwance
Hmmmm lol jama,a wai ya za,a kwashe da
kakalle ne idan har taji labarin habu yaje ya
dauke matarsa?
naku har kullum A,I,S KE CEWA i luv y'll
cont it
RIKON KAKA
CHAPTER 26
ya dora musu girki yau zuciyarsa fes take da
nishadi marar misali.
, Nama ne ya gasa sannan ya dafa
dankalin turawa da indomie ya gama komi tsaf ya
jera 'a dan farantin ya dauko kwalin 'Iemu guda
biyu tare da robobin ruwan Faro suma biyu ya
jera a saman (carpet) ya sameta ta hada kanta
da kujera kuka kawai take amma marar sauti sai
dai za' a iya jiyu shasshekarta
Abubakar ya ajiye tiren kayan abincin a gabanta
sannan ya raba gefenta ya janyota jikinshi’ ya
rungume yana kokarin lallashinta bata ture shi ha
amma kuma bata daina kukan ba
Abubakar ya dora kanta a saman. qininshi ya
Kara rungumrta yana fadar.
‘ "Kiyi haquri‘ don Allah ki daina kukan nan haka
nan kada kanki yai miki’ ciwo".
Yana maganar yana gyara mata gashin
kanta wanda ta turo kallabinta wurin kokawar
dazu.
Rukayya ta soma magana cikin kuka. "Na ce
baxan zauna ba ka maida ni gida, ka maida ni
amma kaki don dai ka kawoni in rinqa‘yi maka
girki da aikin gida. Na rantse da Allah ba zanyi
ba". Abubakar ya yi murmushi yana fadar. "'bama
sai kin rantse ba 'yar gidan kaka, indai kin
amince zaki zauna dani magana ta qare, ni da
kaina zan rinqa yi mana girkin da aikin gidan, kin
amince?" ' Bata amsa mashi ba sa dai ta sa
bayan hannunta tana goge hawayenta. Bai ji
haushi ba ya dago ta daga jikin
nasa yana fadar.
"Daga yanzu ma za'a fara abincin ma abaki zan .
. rika baki". .Ruqayya tai saurin zamrwa tana
fxmadar.
"Ka kyaleni inci da kaina matsa".
Bai matsaba ya kyaleta sai dai hannunta na riqe
da nashi haka ta zuba abinci da hannu guda.
yana kallonta tana cin ,abincin kamar
tanacin kashi. Bai damu ba har ta gama, sannan
shima ya dauki sauran yana ci.
Tsabar gajiya da kukan da tasha kafin ya gama
cin abincin har ta fara gyangyadi, don haka yana
gamawa ya tasheta ya nuna mata hanyar dakin
bacci. Bata musa ba ta mike ta tafi abinta. Sai
dai duk da barcin da : take ji sai da ta jima a
tsaye tana qarewa tsararren dakin baccin kallo
wanda ya gaji da haduwa, a zuciyarta ta rinqa
tunanin k0 gidan waye Abubakar ya kawota kuma
oho.
Tunda bata da mai amsa mata don haka ta nufl
(toilct) ta dauro alwala tai sallah sannan ta dauki
kayan barcin da ta gani a ajiye akan gado ta
saka.
Doguwar riga ce fara sol har qasa mai .‘siririn
hannu, Rukayya ta saka hular rigar akanta
sannan ta kashe wutar dakin ta haye kan gadon ,
tai kwanciyarta. Haka kawai taji zuciyarta ta
samu nutsuwa tunda taji Abubakar yace ba aiki
zata cigaba
dayi masu ba a gidan, don haka hankalinta
kwance bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ita. '
Abubakar ya gama shirinsa a Bangarenshi sannan
ya nufo Bangaren nata, ya samu sai kwasar bacci
take hankalinta kwance. Nan ‘ya hawo kan gadon
shima ya . kwanta, ya jawota jikinshi ya
tofesu’da addu'o'i sannan yaja bargo ya lullube
su. Washegari tunda asuba ya tayar da ita suka
yi sallah, ta Cika da mamakin ganinshi akan
gadonta, sai dai ganin Bai nuna wani (action) ba
akan hakan yasa itama tayi ta maza ta share
suka yi sallar asuba. Ya jata suka koma
'suka sake kwantawa, sai dai har bacciya
’ kwashe shi amma ita ta gaza runtsawa,
mamaki take da kuma al'ajabi wai yau ita ce
yaya Abubakar kwance daki daya, gado daya
kuma manne'da juna. Wannan wacce rana ce mai
Sa'a haka a wurinta‘? tunanin da take. kenan har
barci Barawo ya lallaBo ya dauketa
Ba ita ta farka ba sai karfe goma saura, ta juya
ta ganta ita kadai kwance akan gadon. Ta llaBa
ta tashi zaune tai ido hudu da ‘ wasu riga da
siket sababbi dal akan gadon, hakan na nufin idan
tayi wanka ta shirya ta saka. '
Tsam ta mike ta fada (toilet) din ake
. manne’ cikin dakin ta watso ruwa ta fito ta
zauna bakin madubi ta shirya,kwalliya tayi amma
ba wata mai yawa ba, ta mike ta dauki kayan ta
saka ‘
English wears ne riga da siket Bakin siket ne ‘
T,Shirt body hock mai dogon hannu. Ta dauki '
dan karamin mayaifinta ta' dora akanta, sannan
ta zira silifas na fata ta fito falon don tasamawa
kanta abinda zata ci.
A falon ta_ hange shi daga shi sai
,singilet da wando three quatcr ya zagc yana
ta gogegogen Show glass din dake shake da
kayan turaren wuta
Rukayya tabi. falon da kallo, ya gyara k0mai
tsabtsab sai kyalli yake yana fitar da ni 'imtaccen
, kamshi
Rukayya ta tabe baki saman kujera ta zauna tana
kallonshi cike da al'ajabi, k0 da yake ba tun . yau
ta saba gani ba tun a kauye dama Abubakar
gwani ne wurin iya share-share wanke-wanke da
girki. ‘
Abubakar ya nufota tana kallonshi har ya Karaso
inda take, ya zauna kusa da ita yana‘ fadar,
'"Sannu da tashi my dear,in kawo miki abincin
nan k0 zaki hau kan table ne?" Sai da ta yamutsa
fuska kafin tace
"Anan zan ci".
Ya yi murmushi ya miqe yana fadar.
"An gama ranki ya. dace
»: Ya nufi dinning ya kwaso abin break din-daya
shirya ya nufo inda take. ya dora. tiren akan
center table sannan ya turi . tebirin zuwa gabanta
yana murmushi
"To bisimillah"
, Bai kuma jira abinda zata ce ba ya juya yai
gaba ya cigaba da aikin da yake
Rukayya ta jima tana kallon shi kafin ta mika
hannu ta bude kayan abincin, soyayyen dankali da
kifi ne mai hade da kayan lambu sai ' ‘ kuma
kunu. Rukayya ta soma ci tana mamakin shi
kuma a ina ya iya irin_ wadannan girKe-girken? ,
‘Anan inda ta gama karyawar anan ta zame
saman kujerar . ta kwanta tana kallon wani film
din~ India a qatuwar plasma din dake girkc 'a
jikin bango ta kusa rabin bango.
Kafin ta gama kallon barci ya dauketa ba itata
farka ba sai ana kiran sallar azahar.
'Ta mike taje tai sallah, k0 addu'a bata
shafa ba Abubakar ya shigo mata da abincin
rana. ,Mamaki fa ya qara kamata canjawar sa
lokaci daya na sakata cikin (compusing). ’Bayan
sallar isha'i Rukawa na kwance "a falonta babarci
take ba amma idanuwama a rufe suke, tunanin
Abubakar ne. yai mata
tsaye a zuciya, hidimar da yai mata yaudaya
kawai ta wanke mata zuciya, ta wanke dukkanin
bakin cikin da ya shafe shekaru
yana qunsa mata. Bata ji shigowarsa ba sai dai
taji an
riko hannayenta tareda sumbatar goshinta. Ta
bude idanuwanta a hankali tana
kallonsa, ya hasketa da murmushi kafin ya ce.
"Tunanin ya isa haka, ki tashi ki shirya
muje muyo (shopping) kiga gari". Dadi ya kama
Rukayya ta zabura ta mike cike da doki tana
fadar.
"Don Allah yaya daga nan mu biya
gidan Aunty Maimuna".
Ya noqe kafada' "Naqi wayon, wato muje ta
cigaba da koya miki yanda zaki qara guduwa'
k0?" Rukayya ta zar0 ido tana fadar.
"tab! Yaya wa ya fada maka ita tasa ni na gudu‘?
Wallahi ni nai tafiyata da kaina".
Ya ce, "To ai kin kyauta kinga yanzu nima ba zan
kaiki ba har sai kin fara sona kin daina guduna
. Ta langabe kai kafin tace to "To wai yanzu wa
yace bana sonka
Ya noqe kafada, “To idan kina sona 'din ai sai ki'
fada" Rukayya ta zame hannunta tai gaba tana
faman turo baki, Abubakar ya rakata da kallo har
ta shige sannan ya sami bakin kujera ya zauna
yana wani dan murmushi' wanda bai bayyana
hakoranshi. ba
Shiri sosai Rukayya tayi da wani rantsatstsen
lcshi (two c010ur) wato blue da brown tai kyau
sosai don hatta Abubakar sai ' da ya yaba..Ya
dauketa a‘mota.
' Sai da suka gama yawon su saman manyan
titina. yana gwada mata 'manyan unguwannin
garin nan har sha daya sai data. gota sannan ya
kaita suka yo shopping din na kayan ciye-ciye da
lashe-lashe bayan sunci.
wasu can sannan Suka yo dakon wasu.
RIKON KAKA
CHAPTER 27
sai Sha ; biyu harda yan mintina sannan suka
shigo gidan. bacci ne kawai cikin idanuwan
Rukayya don haka ta bar Ahubakar yana sassaka
kayan firij ita kuma ta shige dakin baccinsu ta
watso ruwa tasa rigar baccinta cikin ta daure
gashin ta da ribon ya shigo. Ta madubi ta hango
.shi ya iso inda take bata san yanda akai ba sai
dai taji ya rungumeta ta buya ya miqa hannunshi
guda y; diuko kwalbar turaren cool water ya rinqa
fesa mata a jiki saidaya fesheta dashi sannan ya
ajiye turaren sannan ya jasu sukn fada saman
gadon dake bayan su, ya kashe wutar dakin
yaja bargo ya lullubc su. Washegari ita ita
takama Lahadi, ba aiki kamar jiya asabar, don
haka suna idar da sallar asuba suka koma suka
kwanta. Rukayya bata sake farkawa ba sai da Iaji
tamkar ana yamutsa ta ta bude idanuwanta da
kyar don ganin mai wannan aikin.
Abubakar yaja muta hanci yana fadar.
"A tashi haka nan ayi wanka a karya. ga ruwa
can: na hada miki". ' .a toilet ta fara juye juye
yace kinga wasa sai dai kiji ki cikin ruwan
wankan'. Rukayya tai surin tashi zaune tana
. ' kallonsa da idanuwanta duk bacci, Abubakar
ya miqa hannu ya janyota ta sakko daga kan
gadon, ya tisata gaba har sai da ta shiga (tOilet)
din ta kullo sannan ya juya ya fice.
' Rukayya bata bata lokaci ba wurin .shiryaWa ta
fito yau a tare suka karya don ta ‘soma sakin jiki
dashi. Tarairaya da lallashi .tare da soyayyar da
yake nuna mata ita tasa ta soma jin wata irin
sabuWar qaunarsa na shiga zuciyarta. Yanda
yake nuna tausayinta a fili abin har mamaki yake
bata, wai yau yaya Abubakar ne ya abubakar ne
ya koma' haka ya canza tamkar ba wannada
yatsaneta, ya hantareta ba. :
lallai Allah Ubangiji mai juya zuciya gashi yan'zu
ya juyo mata da zuciyar abubakar
gareta. Lallai a yanzu ta yarda'da maganar Aunty
Maimuna da take cewa, mai haquri yana tare da
‘nasara aiko ita dai taga nasarar. don ma zuciya
da taso ta rinjayeta daga farko lallai kuwa da tayi
'asarar da ya kamata azo mata
jaje don rasa namiji kamar Abubakar ba
karamin asara bace Da wannan tunanin har bacci
ya
dauketa a daren yau inda ta kwana da zummar‘
garin Allah na wayewa litinin zata riga Abubakar
tashi, ita zata yi komai ba,hidimar gidan ta hutar
dashi don harta . soma tausaya mashi. ' '_ _ Don
haka tunda suka koma baccin
asuba ita taqi ta koma tana ganin bacci ya dauke
shitaja jikinta ta fice kai tsaye‘ ‘kicin ta Hula nufa
ta dora ruwan zafi ta Zuba masu garin chitta‘da'
na‘a-na‘a,. suna ' tafasa ta juye a flask din
ruwan . Ta koma ta dayko dankalin turawa ta
fere tasa a tukunya ta dafa shi sannan ta. '
tsame shi tamai bula bula ba koyon girki
mukaxoba am sorry
Dayan ta gama tsaf sannan ta dauki komi la
jajjera su gwanin sha‘awa, sannan ta koma kicin
din ta gyara shi ta hada ruwan omo ta wanke
dukkanin abubuwan da tai amfani dasu ta kife ta
share kicin din ta goge ko ina da tawul sannan ta
janyo kicin ta kulle ta dawo falon tasa tsinlsiyar
laushi ta share shi tun daga
qasan kujeru har zuwa qarkashin sai da tabi ta
share. Sannan ta dauki mopprr ta hada
ruwa a bukiti ta goge tayils din tsab, k0 ina ya
dauki sheki.
Ta koma ta sa wani tsumma mai Iaushi ta goge
duk wasu abubuwa masu daukar qura dake falon,
sai data gama tsab sannan ta dauko boner har
guda biyu daya ta zuba turaren wuta ta jona‘ a
socket daya kuma ta kunna tsinsiyoyin kamshi
masu kyan gaske ta tsilstsira a jiki ta koma ta
dauko room freshner ta ruwa ta feshe dakin.
Ai kafin kiftawa da bismillah dakin ya kaure da
wani ni'imtacccn kamshi ta saki
labulayen ta goge sannan ta qara qarfin A.C ta
nufl sauran falukan suma duk ta gyara su kamar
na farko, da turare su da kamshi.
Karfe takwas dai-dai ta shiga (facin baccinta
shima ta gyara shi, ya wanko toilet‘sannan ta
watsa ruwa tana gamawa shima ta hada mashi
sannan ta filo. _
Kwalliya tayi ba wata mai yawa ba, ta saka baqar
jallabiyya mai hade da gyalenta, sannan ta nufl
kan gadon da Abubakar ke kwance ta rasa ta
yanda zata tayar dashi. can
dabara ta fado mata ta dauki fIlo ta rinwa‘ buga
mashi a kafa amma babu alamar Zai tashi.
Rukayya ta rasa yanda zata yi dashi, can dai ta
saduda ta hayo kan gadon tana dan
bubbugar filon da yake kwance akai tare da kiran
sunanshi
Caraf ya yi da ita, sai dai taji ta cikin jikinshi ya
kanannadeta da hannayenshi yana dariyaya ce ' .
"Wato na ma zame miki tamkar wani. dodo. k0?"
Rukayya ta girgiza kai tana’ Roqarin zamewa. '
ya Kara riqeta yana fadar.
"Ki tsaya kada ki jiwa kanki ciwo. tambayar ki
zanyi". ‘
Rukayya ta nuna mashi agogo tana Rukarin
zillewa, karfe takwas da rabi agogon ya nuna. Ya
yi saurin sakinta yana fadar,
"Kai-kai loakcin (office) ya kusa yi"..
Bai jirata ba ya Sauka‘da gudu-gudunsa ya fada
(toilet) yana faman yarfa hannuwa wai ya shiga
uku ya kusa makara.
Rukayya ta zauna bakin ‘gadon tana mashi dariya
har sai da ya shige sannan ta. mike ta yaye
zanin gadon ta canza wani mai ‘laushin gaske, ta
feshe Shi da (bed frcshncr) sannan ta bude
(wardrop) ta cirowa Abubakar kayan da zai saka.
Sannan ta flce abinta.
'A gaggauce Abbakar ya shirya yai break dinshi
ya, bata wata sabuwar waya rantsatstsiya, a
cikin kwalinta mai matuwar tsada, tsabar doki
Rukayyabata san lokacin da ta Runkame shi ba
tana murna.
Abubakar ya lakace mata hanci yana mata dariya
ya fice ya 'nufl wurin aiki‘abinshi. . Rukayya
kuwa wuri ta samu ta rashe‘a' falo ta rinqa
cskule-cakule a wayar tata tunda take a ' duniya
bata taBa riqe waya ta kanta ba sai yanzu, lallai
.Abubakar ya gama mata komai tunda ya hadata
dawayar salula.
Shi kuwa Abubakar tunda ya isa (office) din aiki
kawai yake amma zuciyarsa na kanta, duk abinda
yake qarfin hali ne kawai da jarumta, amma a
yanzu yana ji a jikinsa qarfin halin nasa ya kusa
qarewa. Yana son Rukayya so ba na wasa ba,
haka kuma yana sha'awar komi nata.
Yasa hannu ya tallabe kansa cike da damuwa,
duk lokacin da ya kalli Rukayya yakan rasa
hankalinshi gaba daya, sigarta kawai takan nemi
ruguje‘ mashi lissafi. Lallai ya yi sa’a da
kasaitacciyar mace, sai a yanzu ne yake mamakin
kansa ta yanda har ya rinqa hantarar ta. Shin a
lokacin meke damun kwakwalwarSa da
idanuwansa da suka kasa ganin abinda ya dace
da shi? Wai har ya fifita Suhailat akan Rukayya,
yarinyar da in bacin kyan fuska babu mamora a
jikinta. Lallai shi ya gama wautar kanshi.
“Ya' ja tsaki mtsw! Kafin ya mike yasa hannu ya
lalubo wayarshi dake kan tebirs ya lallatsa lambar
wayarta ya danna mata kira.
(Ringing) daya, biyu na uku aka dauka. Rukayya
ta: mike a saman doguwar kujera (three seater)
ta danno mashi siririyar sallama a cikin dodon
kunne, sai da Abubakar’ yayi murmushin jin dadi
don har
’ 'tsakiyar kwanyar' kanshi maganar ta ratsa.
Ya kwantar da kanshi a saman makarin kujerar
da yake zaune, ya cigaba da jujjuyawa da kujerar
yana fadar.
"Ruky Darling, kinyi kewata kuwa?" Rukayya tai
murmushitare da lumshe ido ta
_ bude, kafin ta ce.
-"Sosai ma Yaya Abbakar, duk gidan sai ya yi
shiru da baka nan
Abubakar jinshi yayi tamkar a saman
gajiimare tsabar shauki, ya bude baki da kyar
yana fadar.
"To me za ki shirya mana kafin na dawo?"
Murmushi tayi wanda har ya jiyo sautinshi a cikin
wayar, ta ce.
"Wani spccial girki ne Yaya Abbakar me ‘ motsa '
kunne" Dariya yayi sosaikafin ya ce"Sai kuma me
qanwata? K0 shi kenan?"
‘ sai da tai wani fari da idanuwa irin na mai
neman mafita kafin ta ce '
"To ai ban 'san sauran abinda kake so ba
Abubakar ya ce "KeCe sauran, ke nake so
Rukayya, k0 ba zaki bani ba?" ‘
Ta ce "To ai kariga daka samu yaya Abbakar, me
kuma ya yi saura?"
Abbaakar ya ja numfashi kafin ya ce
' "Ai baki so na Rukayya, guduna kike shi yasa".
Tai saurin rufe baki tana dariya, ta ce
"Kai Yaya, tun yaushe na daina?" ‘
‘ Shima dariyar ya yi kafin ya ce"Da gaske kike
mata ta.? Ta jinjina kai tare da fadar, "Da gaske
nake mana,
Ya ce "To shi kenan, kice yau inzo gida da kwarin
gwiwa kenan matata tana maraba . dani. To'
amma ai min irin kwalliyar jiya a shafa min
janbaki da jan ido ta yanda da na shigo zan yarda
da lallai abinda aka fada min yanzu da gaskene".
RuKayya tana dariya ta ce, "Insha Allah Yaya, sai
ka dawo". ' Ya ce"To qanwata, me kikc so inyo
miki . tsaraba?" ., Ta danyi jim kafin ta ce, "K0
dami ma ka taho ina so". ' Ya ce "To Shi kenan,
sai na dawo“. Sukai sallama sannan kowa ya
ajiye ta kalli wayar _ Tsabar murna Rukayya ta
rasa irin . shirin da zatai na tarbar Abubakar,
tunda ' tayi la' asa: bata sake samun zama ba,
ita ce
shiga kicin ta hau shirya abincin da tasan zai yi
farin ciki dashi.
Abubuwa ne ta hada mashi sun kai kala hudu, ‘
sannan daga qarshe ta hada mashi (juice) din
gwanda da karas. '
‘ Ana kiran sallar magaruba ta gama komi ta nufi
(toilet) ta sharto wanka ta tare da
alwala ta fito, sai da tai sallah tana zaune tana
lazimi Abubakar ya shigo gidan. A gajiye yake
don ya sha aiki a (office), ya turo qofar bedroom
din nata ya shigo da sallamarsa, Rukayya ta dago
kai tana kallonsa bakinta dauke da murmushi. ’
Abubakar ya durkusa a gabanta ya dora
hannayensa akan jikinta yana fadar.
"Na gaji da yawa Ruky na, don Allah k0