Author : zallah Category : African Stories & Novels
su wurin maguji'.
Ta mike a tsorace
ta nufi dakin nasu'.
Ya tsai da ita, 'Tsaya ki tattaro dukkanin kayan
daudarki kawomani'.
Rukayya ta daga kai
Ta shige dakin, shi kuma ya wuce Washegari
yana tashi ya nufi dakin Kaka ya tashi rukayyah
tai shirin makaranta
Kaka tace kai babu inda zataje donka jini nan jiya
suka kamata sukaita bugu kamar jaka don haka
bata komawa
Abubakar yace,'ldanta zauna nan me zatai miki?
Nan makarantar allo ce kikai kane kane kika
hanata zuwa wao bugunta ake , sannan kuma
itama makarantar bokon sai ki
hana? To wallahi .ko kasheta za a rinka yi tana
dawowa sai taje har makarantar allon sai ta
koma“.
Kaka ta ce "Tunda dama ba qaunar ta kake ba ai
dole ka kaita inda za a kashe ta saboda
mugunta, haka kawai ka dauki karan tsana ka
dorawa yarinya, ka kaita a kashe ta don Allah,
idan an tashi a aiko mani da kai da qafarta gida".
Abubakar ya finciko Rukayyar dake kan gado ya
jata suka nufi kofa YANA FADAR. ’
”Ba za, a kashe taba amma fa za ta daku kamar
ikon Allah”.
Bai ji abinda take fada ba don har ya kai bakin
kewaye, ya zuba mata ruwa a bokiti ya bata ta
shiga wanka.
Tana fitowa ya mika mata kayan makarantar ta
saka, ya ba ta mai ta murza ya zaro Naira
hamsin ya bata, ya ce.
Maza ki wuce ki tafi, kuma zan biyo bayanki
yanzu, ki tsaya wasa k0 da labe ne kiga ' yanda
zanyi da ke. Kina dawowa daga
makaranta ki ka ci abinci ki ka hula, ana kiran
sallar azahar kiyi sallah ki wucc makarantar allo
idan ba haka ba wallahi kika bari na samu labarin
baki zuwa na lahira sai ya fiki jin dadi wuce ki
tafi. ‘ Simi-simi ta wuce, daga daki Kaka tace.
”Yanzu baka barin tai kalaci haka za~ ta wuce ta
tafi?” , Ya‘ce, "Bata yi, ga Naira hamsin nan na .
bata ta siyi abinci ta ci". ' -Kaka tace, "Indai
mugunta ce irin taka ai ta wucc da haka Habu,
yanzu haka zaka kora , min ita bata ci komai ba
salon tai karo da mayya k0 maye su lashe mini
ita?” » ‘ Abubakar ya e, ”Su hadiye ta idan ta
tafi". ‘ , “ " Kaka ta cc, ”Ba bakin ka ba, me
mugun baki. Insha Allahu aniyar ka sai ta bika". .
Bai tanka mata ba ya wucc dakinsa yai nasa
shirin ya fice ya tafi wurin aikin sa, amma 'yana
can sai da aka kawo mashi kashcdi wai Rukayya
tayi fada da wani yaro har ta cije shi a hannu ya
fasa. Ya basu hawuri sannan yaje
“Tana dawowa daga makarantar tana hutawa
akai sallar azahar ta fito zata tafi makarantar
allo
Kaka tace, 'Yanzu zuwa za: kiyi k0? Mugun yaron
nan ya hanaki zama lafiya, duk indayasan za a
zalunceki saiya turaki Allah Ya saka miki'. .
Jika
Haka ta wuce makaran allon,.a can sukai sallar
la‘asar, Sai biyar na yamma aka tasosu
Tana dawowa tasamu Abubakar na gyaran cefane
cefane ta giftashi zata wuce ya ce‘
.. ’Kezonan'. , ta dawo gabansa ta durkusa ya
dubeta sosai kafin yace ,‘Wato saboda bakeke
wankinba shi ,yasa idan kika dawo makarantar
baki canja kayan sune na zaman gida kuma sune
na
Yawo cikin gari ko?‘
Shiru ba amsa, ya ce "Tashi kije ki ciri kayan ki
kawo mani".
Haka ta mike ta ciro ta dawo da su a hannu, ya
ce
"Dauki bokiti gaya can da ruwa kisa ki wanke".
Gaban‘ta ya fadi don tundatake bata taba wanki
ba, shi ke yi mata da kanshi. Haka ‘ ta mike taje
ta soma wankin kayan, yana kallonta har ta
gama ya amsa ya shanya. . .. ’ Sannan ya ce "ki
wanke hannunki ki , xo ki yanka mani alayyahun
can da albasa". ‘ Rukayya ta dubi hannun nata
babu abinda ya yi amma har sai ta wanke ya ce.
' "K0 baki ji ba?"
, Haka ta wucc ta dauki buta ta wanke hannun
nata sannan ta je ta zauna tana yankan
alayyahun ya dora sanwar taliyar sa,tana gama
yankan alaiyahun ya ce
Jeki ki zuba" Ta tafi zata zuba cikin tukunyar .yai
saurin daka mata tsawa.
‘ "Ke banza, haka za ki zuba shi? Barbada mashi
gishin' ki sa ruwa ki wanke". ’
‘ Ta dauki uban gishiri ta maka yana kallonta ya.
ja tsaki ta zuba ruwa ta wanke ta tsane shi
sannan ya ce '
"Je ki zuba". ' "
Taje ta zuba ta rufe, ta dawo gabansa.
"Na gama".
Ya ce, "Jeki shi kenan".
take ta nufl daki don kar ya qara saka ta wani
aikin
*** ******* ***
Wata ranar Juma'a RuKayya tana . makaranta tai
fada da (monitor) din ajinsu wai ta rubuta
sunanta cikin 'yan surutu, malamin ya buge
su.duka Shine fA yana fita ta ' kama monitar da
kokawa' gata ba iya fada tai ' ba, tai mata, duka
sosai. Akaje aka fadawa ' (headmaster) yazo da
kansa da bulalar sa ya zane Rukayya: radau har
tai fitsari saboda .
.azaba.
Yana fita ta dauki jikkarta ta gudo gida tana
kuka, ta fadawa Kaka. Ta ce, "Ai k0 yau sai ya
san ya debowa
kansa masifa".
Ta dauki mayafinta ta ce "Muje inga matsiyaci". '
Ta ja gida ta rufe suka dauki hanyar
makarantar har office dinsa ta kaita, yana
zaune saman kujerar dake gaban teburinsa sai .
wani mutum dake daga can gefe suna
magana. '
Kaka ta sawo kai cikin office din ba k0 sallama,
ta dubi mutumin dske saman _kujerar gefe tace. '
"Malam wurinka nazo, zuwa nayi inji uban da
yasa ka sa bulala ka rinka laftar mani
jika kamar ka samu jakka, k0 k0 shi Habu din
' nc da ya kawo ta ya ce ka sa bulala kai ta
bugunta harta ‘fita hayyacinta tai fitsari? To kotu
zata rabani da kai, wallahi sai nayi shari'a da kai,
sai ka bani labarin dalilin bugar mani 'ya babu
gaira babu dalili".
Mutumin yace Yi hakuri baiwar Allah, bani ne
(headmaster) din ba, gashi nan, nima zuwa nayi“.
Ta ce, "Karka sake ka zage ni’da turanci wallahi
na gaya maka, nima ina da
jika kamar ka dan makaranta" ~ Saurayin ya ce,
"Ikon Allah, yi hakuri don Allah Hajiya" ‘ '
Ya mike ya bawa (headmaster) hannu sukai
musabiha, ya ce.
"Ni zan wuce Yallabai, zan kira ka a waya k0 mi
kenan". _ Ya wuce abinsa ya bar (headmaster) da
rigima. ‘ . Da yake kwararren dan boko ne sai ya
mike daga kan kujerar da yake ya ce.
"Hajiya zauna, bisimillah sannu da
_ zuwa, bari akawo miki lemu". Kaka ta zauna
tana fadar, "Karka kaWO mani komi, dan iskan da
ya bugi Jika kawai
nake nema, wallahi sai na rama mata ,kaji na
fada maka
Lol ran kakafa ya baci mai zai biyo baya mu tara
later
a zallah shared a profile .
RIKON KAKA
CHAPTER6
, Ya' kwantar da 'murya, "Ayi 'haquri Hajiya,ai duk
abin bai kai na haka ba tunda ni da Jikar taki ai
duka jikokin ki ne,kua zaki' iya‘ hukunta mu idan
munyi laifi, ‘ musamman idan ki ka same mu da
rashin gaskiya. Kiyi hauri kakata, ba a daki
qanwa -ta saboda zalunci ba, ‘sai don laifin da
tayi, ta
; kama shugabar ajinsu tai ta bugu Idan kika, ga
bugun da tai mats sai kin tausaya matA
. shi~yasa. Sanin da nai k0 ke ce kika ga haka
sai» kin daki jikar. nan shi yasa‘ na hukunta ta
saboda gaba amman kiyi haquri kaka Kalaman sa
sun Shiga Kaka don haka ta ~sassauta fadan
tace "Gaskiya kar a sake bugar min jika saboda
wasu yara can, marainiyar Allah ce uwarta da
ubanta duk sun mutu; ni kadai na rage mata. In
bacin yaya'nta ma da ba mai jin magana bané ai
daga yau bata Kara dawowa' ‘ makarantar". '
Ya ce, "A'a ayi hakuri, insha Allahu za a kiyaye"
ta mike, "To sai anjima, Allah Ya _ taimnka". '
Ya ce "Amin Kaka"
Ta tasa Rukayya suka ficc daga (ofiicc) din,
(headmaster) ya koma ya zauna saman kujerar
sa yana murmushi, ya ce. _
"Ho! Allah Ya raba ni da ke lafiya" (Duk wanda ya
girmama tsohon wani shima ’za'a girmama nasa
a gaban idonsa k0 bayan idonsa
Da yamma bayan Abubakar ya dawo
~ daga wurin aikinsa yaji labarin zuwan kaka
makaranta, yai ta fada
' "Haba Kaka, .yanzu in bacin kin hadu da dan
mutunci ai da Allah kadai Yasan
yanda za ayi. Haba! ki ta abu sai kace kanki farai
jika? K0 ina sai kin fito da halin ki
To, "To ubaba, zoka dakan sai in san kaji haushi:
inba dukana kayi ba ai ban ssn kaji haushi ba
Abubakar ya ce, "Ai burinki inji haushi in fitar da
ita daga makarantar, kuma ba zan fitar da ita ba
wallahi ta zo ta dami al'umma, gara ta zauna can
duk wanda taimawa a zane ta".
Kaka ta ce, "A daketa din ni kuma dukwanda ya
bugar min jika idan naji sai naje na rama mata
tabbas".
_ ‘ Abubakar yace, “To shi kenan ki rama mata
din, hukumar makaranta ta sa a kama ki, wallahi
kuma k0 leke ba zan leka ba" Ta ce, "In ka tashi
ka manta dani k0 kasa a rufeni har dan makullin
ya bats" . ' Abubakar yai dariya ya ficce abinsa
don yasan halinta idan ya cika ta yanzu ta sa
masa kuka, ya tafi ya yo cefancn abinci ya_
dawo ya kira Rukayya, ya ce "Maza kisa tsintsiya
ki share gidan nan, idan kin gama ki min magana
ya wuce dakinsa ya barta tsaye".
Ta sumBuro baki ta rasa dalili kwanan ‘ nan da
yake takura mata ba yanda ta .iya, dolenta ta
dauki tsintsiya.ta share gidan
sannan taje ta sanar masa ta gama. --
Ya fito yace, "Hada itatuwa ki hura wuta, ai dai
kinga yanda nake yi?"
. Idanuwanta suka ciko da hawaye haka ta je ta
hada itatuwan yana tsaye yana' kallonta ya ce.‘
~ . ."To sa sabulu ki wanke hannunki ki . dauki
tukunya ki dauraye ki~aza saman ’
wutar". Haka yai ta saka ta aiki daya bayan '
daya har sai da aka gama girka shinkafa' da miya
k0 tsinke bai taBa da hannun‘ saba
Yasa ta dibar masa nasa; sannan ya ce. "Daga
yau aikin ki kenan a gidan nan kullum, don na gaji
komai ni sai kace dan daudu a gida.
_ Shekarar ki sha uku amma babu abinda kika iya
a aikace-aikacen mata, jikin ki ma ba ki damu da
gyaran sa ba balle na gida, , kullum kina, faMa da
qazanta 'da shegen muni kamar don ke aka yi
shi, Mtsw!".
' Ya wuce'dakinsa'ya barta tana ta faman
tukuki
"""""". """""""
. Lamarin Rukayya ya zama sai dai addu'a, don
ma Abubakar yana tsaye akanta
Wajen makarantar boko da ta all, idan kuma ta
dawo ya tisa ta gaba da aikin gida, yana zaune
yana bata umami haka zata yishi kotanaso ko
bataso
Kaka tai mitar tayi amma bai kulata, bai fasa
abinda yai niyya. Wani abin ma da gangan yake
saka ta don ya wahalar‘ da ita saboda ya lura
har yanzu bata yin hankali kullum abinta gaba-
gaba yake
Bakin ciki ya ishi Rukayya, Abubakar ya takuraWa
rayuwarta, bata da sukuni.
Yanda ya tsaneta itama haka take jin ta tsane
shi, musamman yanda yake nuna mata kyama.
‘kara'ra duk abinda za tai masa sai yasa ta
wanke hannu, idan k0 ta'na girki ta fyace ‘majina
sai yasa ta sa sabulu ta wanke hannu. Idan ta
shiga kewaye ta flto k0 tobai bari ta “qara taba
abinda za a zuba cikin abinci sai ta wankc
hannunta da sabulu k0me tai kuwa cikin
kewayen. .
' , Abun nan na ci mata tuwo a kwarya, haka
kuma take daurewa babu yanda zata yl,
duk duniya babu Wanda take jiwa tsoro irinsa; _
Ta ja wani gajeren tsaki yanda ba zai iya'juyo ta
ba, .ta ci gaba da tsane shinkafar cikin kwando
tana gamawa ta zubar da ruwar . tsane shinkafar,
sannan ta dauko mai ta zuba a tukunya, ta‘ zuba
jajjagen ta soya, yana soma soyuwa ta juya ta
dube shi.
' "Kamar yaya za a zuba ruwan?"
Abubakar ya dago kana daga karatun
jaridardayake, ya ce
"Wai ke wacc irin kwakwalwa gare ki ne? Komai
sai kin tamabayi yanda 2
Za a zuba‘? To ban sani ba, ki zuba yanda kike
ganin zai
isa Rukayya ta taBe baki ta wucc ta debi
ruwan ta tafi wurin tukunyar ta zuba, tana tsai da
ruwa .tashshin ya taso mata, sai atishawa wata
na bin wata. Abubakar ya mike da hanzarin sa ya
yo kanta cikc da takaici, ya cc. . . "Wai ke wacce
irin qazamar banza ce? Yanzu kina jin atishawar
ba za ki kauce ba k0ki tara rigar ki amma shi ne
za ki tofewa ; abincin da zamuci? To sai ki cinye
abincin" Ya ja tsaki ya balbalrta da harara ya
wuce abinsa, haushi ya kama Rukayya ta daure
ta ci gaba da. girkinta, ranar bai ci abincin gidan
ba. . Wa Shegari kuwa Rukayya cike take da
shi, sai ai ganin ‘nama me yawa za ayi falfcsu
yasa ta tsaki jiki taci gaba da aikin. ‘
_ Saida aka gama falfesun tas sannan Rukayya ta
bude da ‘niyyar' ta motsa, da gangan ta zabga
atishawa a ciki har sau uku don taga iYakar shi.
Takaici da haushi ya cika Abubakar, yace"Kinyi
dai-dai, kin kyauta, daman burinki ki haramta min
cin naman kuma kinyi nasara".
Ya karkace ya zaro dari biyar ya miqa mata. '
"Amshi, gashi kije ki siyo mani balangu na dari
biyu, tsire na dari, sai ki biya shagon dan Inna ki
siyo mani maltina guda"
Rukayya ta amshi kudin ta fice, tana jinsa yana
fadar.
Saura kuma ki tafi ki tsaya dambe k0 tsokanar
fada".
Zuciyarta tai fes, saboda muguntar da ta shirya
mashi Tana siyo naman ta sami
zauren wani gida ta bude ta tattofawa naman
yawu sannan ta nannade yanda ba zai gane ba,
tai dariya ta wuce tai gida.
Yana zaune tsakar gida saman kujera 'yar
.tsugunne, sai kaka wadda ke zaune saman~
tabarmar kaba, hira ake yi tana cin falfcsun
kamar duka kenan don da wuya a . gama hirar
abin bai zama fada ba.
Rukayya tai sallama ta kai mashi naman, ya
amsa ya ce ta dauko mashi flet ta nufi kicin ta
duko ta kawo masa.
* Ya ce, "Jeki daurayo min shi".
. “ Dabi‘ar da ke konawa Rukayya rai,kenan sai
dai babu yanda zata yi wankakkrn filet din amma
sai an sake daurayo masa.
Ta daurayo ta kawo masa, ya ciro hankicif cikin
aljihu ya goge fllet' din yana wani yatsina hanci,
ya zazZage naman cikin filet din ya Balle murfin
maltinar ya soma ci, yana ci yana Shan maltina
yana suburbudo . ” zance da alama naman na kai
masa karo
Rukayya ta zauna gefen Kaka suna cin falfcsun
naman, tana kallon yanda‘ Abubakar ke kwasar
naman har yana lumshe ido;
Dariya ta kwace mata sai kace wata zararra, ta
fashe da dariya har tana kyakyataWa. ‘
Abubakar ya tsaya da shan maltinar da yake
ya daddaure fuska.
, "Ke miye haka? Hauka k0 rashin hankali? K0 k0
mahaukata ne mu da zaki tisa mu a. gaba kina
kyalkyala mana dariya?" Rukayya ta guntse
dariyar saboda tsoron ‘ duka, ya ja tsaki ya ci
gaba‘ da cin naman sa.
Kaka ta ce "Ina ma laifinta harta iya yin dariya?
Haka kawai ka dauki karan tsana ka dorawa
yarinya, kai ta nuna mata tsana da Kyama haka
kawai, ai kaga naman yai mana auki, mu ci yau
har da safe a dunduma".
' Abubakar ya ce, "Ba komai, da dai inci abinda
qazamar yarinyar nan tai Wa atishawa
to gwara in zauna da yunwa, saboda tunda nake
ban taba ganinta tana wanke baki ba balle
yankan akaifa, kullum hannunta na cikin baki tana
taunar akaifa, sai tai shekara kanta bai ga kitso
ba wai nan sunan tana mace sai fama ‘ take da
muni cike da fuska"
Kaka tace "Barakallahu masha Allah, duk wanda
ya raina tsayuwar wata to ya hau sama ya
gyara, kai nan har kyau ka fita?"
Yace, "Ai kyan namiji aljihunsa Kaka" ‘" . Tace,
"Gafara can, ai dai aljihun bai isa ya siyo maka
kyan ba". , Abubakar ya ci gaba da cin namansa
yana fadar. "Maza dai ki kware saboda zafin
surutu, an kushc rabin ranki, masoyiyar ki. Kaka
tace "Fadi da‘ ihu ka qara da
' kururuwa" . Abubakar ya dukunkune takardar
Sannan ya wurga a Shara, ya shanye maltinar
yana faman gyatsa. Rukayya ta fashe da dariyar
da bata san
ta kwace mata ba. haushi ya kama Abubakar
ya zaro belt din wandonsa ya janyota daga gaban
Kaka ya soma dukanta, wai sai ta fada masa:
abinda takewa dariya.
Rukayya taji bugu ya ishe ta, tana kuka .. Tana
rokon sa yaKi ya kyale ta, Kaka sai zaginsa take
amma bai kulata ba. Da bugun ya isheta tace
“Tsaya don Allah in fada maka, wallahi naman na
tofawa miyau na kawo maka".
Abubakar yai saurin sakinta.
What!". ,
Ya fada hannunsa dafe da kirlji, ta ruga daki ta
rufe, Abubakar ya nufi wurin maguji yai ta kakare
kakaren amai, ya gaji aman yaqi zuwa,
idanuwanshi sukai jawur, ya nufi dakinshi.
~Kaka tai ta masa dariyar mugunta, tace
“Anqi cin biri anci dila ba Ai tai min dai dai, sai
muga ta kyankyami“. :
. Tsananin Bacin rai bai barshi ya kulata ba.
Hmmmm lol
a zallah shared a profile .
RIKON KAKA
CHAPTER7
Wata ranar Asabar abubakar ya zowa Kaka da
zancen yana so ya ajiye aikin kamfani ya ci gaba
da karatunsa.
Kaka ta ce "A'a Habu, yanzu sai ka
ajiye dan aikin da kake yi ka tafl wani karatun
boko?"
. Ya ce, "Kaka karatun boko yana da amfane
tunda aikin kamfani banda tabbacin dorewar sa,
gara in ajiye in samu in ida hada digiri dina, tunda
dai Allah bai hana
mu abinda za a ci ba. Ni dai ki min addu'a kawai
nake so".
Kaka ta ce "To Allah Ya tsare, Ya ba
da sa'a, Ya shige maka gaba".
Ya ce, "Amin Kaka, haka nake so".
Lokacin da Abubakar ya jewa
Ogansa da zancen aje aiki ya ce
"Karkai gaggawar ajiye aikin ka Abubakar, yanda
aiki yake da wuyar samu a
Qasar nan, abinda ya Flye maka ka nemi alfarmar
kaje ka qarasa karatun ka
Akwai taimakon da muke bawa ma'aikatan mu
masu tafiya Karo ilimi, tunda wannan kamfanin
ba na gwamnati bane balle ace k0 ka tafl karo
karatu za a ci gaba da biyan ka albashi, ko ya ka
gani?"
Abubakar ya ce, "Hakan yayi YallaBai, ai ban san
da wannan tsarin ba, a gaskiya naji
dadi na gode Allah Ya tsare, Ya Kars budi".
Ya ce, ”Amin Abubakar".
Da wannan Abubakar ya baro kamfanin ya dawo
gida yaci gaba da buga-bugar. neman
(addmission) a Umaru Musa 'Yar Adua University
amma abin ya gagara uban gidan ' nasa da
kansa ya sama masa (addmission) din.
A gaskiya Abubakar ya yi sa‘ar uban gida na gari,
mai tausayin na Kasa da shi.
Ba, a jima ba Abubakar ya soma zuwa (school)
suka kaishi aji biyu saboda yana da kwalin N.C.E
dinshi.
Abubakar ya soma karatu gadan-gadan, shigar
sa University ya haifar masa da ci gaba matuka,
daga Dandagoro yake hawa: mota zuwa Umaru
Musa Naira hamsin ya dawo hamsin.
Zuwansa makarantar yasa ya Kara wayewa, ya
Kara gogewa, ya fita daban da samarin kauyen.
Sai ma ya kasance kamar koyon kwalliya da sa
kaya yake zuwa, k0 k0 ganin samarin birni da
yake ne a wankc a goge yasa yake ta ruwan‘
dunkuna? Kullum cikin yin dinki da siyen kananan
kaya yake, gayun ya bi masa jiki k0 yaushe za ka
ganshi a cikin hadin (to match) yake
Da kansbi yake shiga cikin gari ya harhado kayan
kwalliya irin na samari masu jida kansu.
Abubakar ya samu ci gaba sosai a rayuwa, sai
kuma daukar kai da jan aji
wurin Rukayya kuwa abin sai , hamdala, ta dai
rage yawan tsokanar fada,
Amman qazanta da rashin san kwalliya sai inda
ya qaru k0 kadan bata son moriya. Ko Kaunar
abinda zaisa ta motsA jikinta
Harta shiga aji biyar a (primary) a lokacin
Abubahr ya kammala digiri dinsa, aka tura shi
(service) Kaduna
Rukayyu tai matuqar jin dadin; tafiyar shi
(service) din nan, ta sami sakewa. Ta ida hargitsa
tum, babu mai mata fadan tayi wanka ko wanki
Hatts gidan ya ida qazanccwa, Kaka k0 bata
sata: bata : hana ta, duk