Author : Nazeefa Sabo Nashe Category : African Stories & Novels
wallahi, don kana saki na zan bayyana wannan vedion a duniya na rantse da
Allah ba Wanda zai hana ni, a yanzu ma idan baka amince ka yi min abinda nake so ba, sai na saki vedion
nan…” Kallonta yake sosai, yana taune lips ‘dinsa. Ya sunkuya daf da ita yana furta “Me kike so na Miki?”
Cikin wata irin murya da ta yi k’asa sosai. Safna ta ji muryar na nemar d’auke mata numfashi ga k’amshin
turaren da ya baibaye mata hanci, sai ta ji tana neman ta rasa hankalinta. Sai da ta yi da gaske sannan ta
fisgo muryarta da bata da amo sam ta furta “So nake ka saki matar da ka aura Jiya…..”
JIKAR NASHE★ ✍️HADARIN GABAS…..👌
32.
NAZEEFAH SABO NASHE★ ✍️
08033748387.
BRIGHT PENS SECOND BATCH
★★
Wani irin kallo yake mata,kafin Ya furta “Na saketa fa kika ce?” Ta ‘d’aga kai tana furta “Eh, ka saketa na
ce, idan Har kana son na rufa maka asiri…” Sai ya cije lips d’insa ya furta “Idan ina so ki tona fa?” “Kada
ka saketa, ka sha mamaki, wallahi a yau zan saki vedion nan.” Ya waro ido yana furta “Wai da gaske kike
za ki iya tona min asiri?” “Me zai hana?” Ta fa’da tana jijjiga jikinta… “Shikkenan, zan saketa, ba dai
matar da Didi ta aura min ba, ki je ki samu Didin idan ta amince min a yau ma ba sai gobe ba zan saketa,
don dama ba wani son yarinyar nake ba, sau ‘d’aya na tab’a ganinta kinga idan kika saka na saketa kin
taimaka min zama da abinda bana so…” Farin ciki ne zalla ya cika zuciyarta, ta dinga jin zuciyar na wani
irin kumbura tsabar murnar da take ciki. Ashe har yanzu ita take da Moddi ita Moddi yake so ba wata
banza ba can, ashe zata iya tursasa Moddibo Har yanzu. Sai ta samu kanta da b’acewar b’acin ranta, farin
ciki fal Ya cika zuciyarta. Sai ta mik’e kawai tana yafa d’an mayafinta ta fita zuwa sashen Didin. Moddi ya
bita da ido yana girgiza kansa. Lamarin Safna mamaki yake bashi, ta yarda take nuna son kanta tsagwaron
sa, in dai zata samu farin ciki ba ta k’i kowa ya rasa nasa farin cikin ba. Ji ya yi yana son yaga drammerr da
za’a buga da Didi da Safna don haka yaga bari Ya je, duk da idanunsa basa son ha’duwa da Didin ba don
komai ba sai don b’acin ransa da yake gani a idon nata, da gaske ya san Didi na jin haushinsa. Sai ya cije
leb’ensa hannayensa zube a aljihu ya nufi sashen Didin.
A zaune ya gansu, Fateema har a lokacin tana zaune hannayenta zube da k’uncinta. Sai ya ji tausayinta ya
mayar da kallonsa kan Amani da Imani da suka yi wani irin zuru zuru. Idanunsu Sun fa’da sun kuma nuna
alamun Sun ci kuka sosai. Ya zauna yana sakin ajiyar zuciya ba tare da ya yarda ya yiwa Didi second look
ba. Ba zai jure ba, ba zai jurewa yanayin kallon da take masa ba. Kowa Safna take kallo da take zaune
k’afa ’d’aya kan d’aya. Tana wurga musu wani irin kallo tana taunar chewingum. “Didi wajen ki na zo.” Didi
ta zuba mata ido ba tare da ta ce komai ba, don a Yanzu bata ganin lefin Safna komai ta yi Moddi ne ya
jawo mata. “Yauwa Didi, dama a kan maganar nan ne, idan Har ba so kuke maganar ta fita waje ba, ina
son Moddi ya saki matar da kika aura masa jiya….” Kowa ya ‘dago yana wurga mata wani irin kallo. Ta
girgiza k’afa tana furta “Haka nake so a yi, idan ba haka ba zan saki vedion nan wallahi a gari, don duk
abinda suka aikata jiya da y’ar cikinsa ina da recording d’insa, kamar na San akwai abinda Imam yake
aikatawa na saka k’aramar camera a d’akinsa ba tare da Ya sani ba, sai gashi kuwa ashe yana aikata
abinda nake zarginsa d’in. Didi idan baki sani ba ki sani akwai wani sirri bayan wannan da Moddi yake
aikatawa, akwai d’akin sirrinsa da baya bari kowa Ya shiga, idan kuma ya ce ba haka bane ya bu’de ku
shiga ku gani….” Wani irin kallo Didi ta zubawa Moddibo tana jin hankalinta yana sake tashi, da gaske
Moddi yana shirin bugar mata da zuciya. Moddin cikin takaici yake hararar Safna. Fateemah kuwa runtse
idonta ta yi ta dafe k’irjinta tana fitar da wani colorr numfashi. Amani kuwa ta dinga jin zuciyarta na
tsananta bugu. Idanunta akan Dadan tana son taga ko zai musa. Sai dai ko ‘d’aga kansa bai yi ba. Kan nasa
yana sunkuye a haka yake kallon kowa. “Tashi mu je ka bu’de min d’akin Moddibo, idan baka naso yau na
maka abinda baka tab’a zata ba…” Runtse idonsa Ya yi yana girgiza kai. “Ki yi hak’uri Didi, shigar ki d’akin
bashi da wata fa’ida, don Allah ki yi hak’uri.” Zubewa kawai ta yi akan kujera wannan karan sam ta kasa
togace hawayen da suke zubo mata… ta saki kuka sosai tana furta Ya Allah! Safna ta mik’e tana sakin
murmushi tana kallon Fateemah da ta zama kamar statue. Sai ta kai wayarta daidai fuskarta ta furta “Ke
kin san komai, kin san Moddi ya cusawa y’arsa k’aunarsa da sha’awarsa ta hanyar tsafi, kin ga abinda kika
gani a wayarta, sannan ga vedio, idan baku saka ya saketa ba a Yanxun nan zan saki vedion nan a tiktok
wallahi…..” Ta fa’da tana kunna vedion sannan ta shiga Tiktok. Da sauri Fateemah ta rik’e hannunta tana
furta “Moddibo saki Jameela saketa, Safna ta shirya tona mana asiri, ta shirya lalata mana sunan
family…” Moddibo ya kalli Fateemah. Ta ce “Ka saketa na ce.” Fateemah ta furta a tsawace. Moddi ya
lumshe idonsa yana furta “Na saketa…” Fateemah ta saki hannun Safnan tana sakin ajiyar zuciya. Idonta
na cigaba da zubar hawaye. Safna ta tuntsire da dariya tana furta “Ko yanzu nice da riba, na gaya muku
na zame muku k’arfen k’afa.” Ta fice tana cigaba da dariyarta, daga jinta ka san tana cikin farin ciki. Shiru
duka ‘dakin ya ‘d’auka baka jin komai sai sautin ajiyar zuciyoyinsu da suke yi a jere a jere. Didi ce ta fara
magana “Hankalinka Ya kwanta Moddi, ka saki matar da na aura maka, Duk abinda kake b’oyewa kuma
Ubangiji Allah ya tona maka asiri kwana kurkusa, idan kuwa na sameka a matsayin matsafi Wanda Ya yi
ku’di ta hanyar tsafi wallahil azeem ba ni ba kai, Fateemah ki zama shaida…” Fateemah ta lumshe ido
bayan jin sautin bugun k’irjinta Ya tsananta. A idanun Didi ta dinga ganin duk abinda ta fa’da gaskiya ne
Har k’asan ranta. Don haka ta mik’e zuwa gabanta ta durk’ushe murya a k’asa ta furta “Ki yi hak’uri Didi.”
Wani kallo ta mata da yasa Fateemahn ta ja baki ta tsuke tana matsa yatsun hannunta. “Kada ki ce min
komai Fateemah, duk abinda Ya faru ace kin b’oye min? Kin san abubuwa da dama amma kika rufe min?
Kina tunanin gata kika yiwa Moddibo, y’ar cikinsa fa? Da kin gaya min tuntuni da abin bai kai haka ba ai,
baki kyauta min ba Fateemah kuma ina fushi da ke.” Fatima ta saka kuka tana kama hannun Didin ta furta
“Ki yi hak’uri Didi, Ban gaya Miki bane saboda bana son ranki ya b’aci, kuma sai da na ja kunnen Moddibo
na ce kada Ya aikata Amma sai da ya aikata, ni kaina yanzu ina jin zafin Moddibo fiye da tunaninki, komai
shi ya jawo Amma ta hanyar gudumowar Mace Mara imani, wacce take son Ya yi ku’di ko ta wace
hanya…” Didi ta mik’e tana furta “Ai ga ku’din nan ya samu, sai ta ci ku’din shi kuma ta cigaba da walagigi
da rayuwarsa…” ta shige toilet wannan ne Ya bawa Moddi damar mik’ewa zai fice Fateemah ta bi
bayansa da sauri. Jin motsin ta yasa ya juyo ta ja hannunsa “Mu je d’akinka, ka nuna min abinda kake
b’oyewa a d’akin sirrinka idan ba haka ba ba ni ba kai Moddi…” Ya ja ya tsaya, ba tare da ya cigaba da
tafiya ba, fuskarsa a tamk’e ya furta “Amma kin san ni ba yaro ba ne ko? 38 yrs ya wuce wasa na San
ciwon kai na, na San abinda zan aikata mai kyau ko mara kyau ko?” Fateemah ta dinga kallonsa cike da
mamakin furucinsa ya cije bakinsa yana furta “Tunda Ban bu’dewa Didi d’akin can ba, bana jin zan iya
bu’dewa wani don haka leave me alone….” Turus ta tsaya tana
Kallonsa. Eeh lallai da gaskiyar Safna da ta ce koma meye a cikin d’akin ba na alkhairi ba ne, tunda har
Moddi ya iya kallon k’wayar idonta ya gaya mata haka. Idanunta suka kawo ruwa tana ji Moddi ya rab’a ta
gefenta ya wuce. Sai kawai ta zame ta zauna a walk way d’in don bata jin k’afafunta za su iya d’aukarta.
Daga lokacin gidan bai sake zama lafiya ba. Safna ce take zuba mulkin ta son ranta, Didi bata bar gidan ba
don zuciyarta ta kasa amince mata ta yi nesa da Moddi. Addu’a take masa sosai kuma tana sawa a yi
masa. Yaran gidan suka daina walwala haka jama’ar da suke cikin gidan. Kullum Amani na ‘d’aki bata ma
fitowa balle ta ga Dada Wanda kallonsa yake k’ara wutar tsanarsa a zuciyarta. Sanda aka yi sati biyu da
abin sannan Umma T wani tunani yazo mata da sauri ta mik’e jin abin yazo mata a bazata. “Idan Amani ta
samu ciki fa?” Sai ta ji fa’duwar gabanta ta tsananta ta fice da sauri ta shiga motarta. Chemist ta je ta
samu maganin da ta tabbatar zai yi flurshing marar Amanin. Wanda ba zai mata illa ba.
Daga nan gidan Moddi ta je, duk da bata son shiga gidan don yanayin Didi baya mata da’di. Su kansu
Amanin da Iman basa cikin hayyacinsu. Duk da Didi ta matsa da maganar aurensu. Mahmud D’in Umma
Dee dai shi za’a bawa saboda har yanzu su basu San abinda Ya faru ba. Kuma wata hu’du kacal aka saka.
Ba tare da Moddi ya sani ba don ko sako shi a zancen yaran Didi bata yi. Kamar ko yaushe Didi da Iman
kawai ta samu a parlorn. Ta zauna tana gaishe da Didi. Ta amsa mata cikin yanayin da ta Saba. Tana nuna
mata wasu kayan kitchen da ta fara siyawa su Amanin. Ta gani ta kuma yaba. Sai ta kalli Iman tana furta
“Ina Amani?” Iman ta mik’e sai Fateemahn ta ce mata ta dawo ta zauna zan je na ganta da kai na.
A zube a saman gadon ta ganta. Idonta a lumshe gaba d’aya ta fita daga hayyacinta kamar ba Amani y’ar
gayu ba. Ta saki ajiyar zuciya ta zauna tana saka hannunta kan gashin Amanin ta mayar da shi baya don ya
rufe mata fuska. Duk gashin a cukurku’de yake ba ya samun gyara. Amani ta bu’de lumsassun idanunta ta
zube su a kan Umma T ‘D’in. Sai ta mik’e a hankali don jikin duk ba k’wari ba wani abincin kirki take iya ci
ba. Gaishe da Umma T D’in ta yi data zuba mata ido cike da tausayi take dubanta. “Ama.. ba zaki cire
damuwa daga ranki ba ko? Sai wani ciwon ya same ki ko? Dubi yarda fa kika zama?” Amani lumshe
idonta ta yi kawai tana jin dama wani ciwon zai sameta har ya zama ajalinta da tafi kowa son haka. Hannu
Umma T d’in ta saka a bakinta, hakan yasa ta bu’de ido tana kallon tafin hannun Umma T D’in. Tablets ta
gani. Umma T ta ce “Bu’de ki sha, yanzu abin yazo min kada mu je ko kin samu ciki mu shiga uku, gwara
tun wuri a koro duk abinda yake cikin mahaifar.” Zuciyar Amani ta dinga wani bugu. Ta dinga jin a
zuciyarta tabbas da zata samu ciki ba abinda zai hana ta bar shi ba don komai ba sai don ta tonawa Dada
asiri, don ita Har a lokacin ba wai ta hak’ura ba ne, tana dai kallonsu suna budirinsu da son rufawa Dada
asiri, amma a zuciyarta tana jin ba afuwa tsakaninta Dada tilas Ya girbi abinda ya shuka. Ba zata so ta
samu ciki ba balle ta sake b’atawa kanta suna duk da a wautar ta hakan shine abinda ya kamata. “Ki sha”
Fateemah ta furta tana tura mata tablets ‘din. Sai ta sha ‘din zuciyarta tana addu’ar Allah yasa bata samu
cikin ba. “Ba zai miki illa ba, amma nan da 1 hour na San za ki fara bleeding Wanda zai
Zama period d’inki na San shikkenan mahaifarki ta wanku.” Amani ta lumshe ido kawai tana d’aga kai.
Umma T ta zauna tana mata nasiha game da Dada sai ta ji zuciyarta ta ‘d’an samu sauk’i. Sai kuwa ga
mararta tana mur’dawa ka’dan. Kamar wasa sai bleeding. Umma T, ta ce “To Alhamdulilah hankalina ya
kwanta. Sai maganar karatunku na gayawa Mahmud dole zaki fara karatu da zarar an fara next session a
Sky Line.” D’aga kai kawai Amani ta yi tana mayar da kanta saman pillow don ita yanzu bata jin tana da
wani buri a duniya. Sai da marar ta lafa mata sannan Umma T ta tafi gida.
A kwana a tashi zuciyarta ta fara sanyi, Har ta koma walwalarta kamar da, suka cigaba da soyayyarsu da
Mahmud, kan dole ta cusawa kanta son sa, don ko bakomai tana jin auren shine rufin asirinta. Duk da
bata San me zata cewa Mahmud a sanda zai kusanceta ya jita ba budurwa ba. Wani kallo zai mata shine
abinda yake ‘d’aga mata hankali. Dada tun bayan faruwar abin bai fiye zama a k’asar ba, ga wani arzikinsa
da yake sake bunk’asa kullum yana jirgi daga can k’asar zuwa can. Don haka sam bai San abinda ake
shiryawa na auren su da Mahmud ba, Didi bata gaya masa ba kamar yarda ta ja kunnen y’ay’anta akan
kada kowa ya gaya masa. Da Umma D, ta tambayi dalili sai ta ce mata saboda Moddi ba ya son a yi auren
nan kusa, ya fi son yaransa su yi karatu.” Da wannan ta kashe bakin Umma D, don itama yanzu ba abinda
take buri irin auren Mahmudu da Amani ba don komai ba sai don ku’din Moddi da take gani, Moddi ba
shi da magaji idan har Mahmud ya auri Amani ta San sune da riba. Haka Safna ma bata San me suke
shiryawa ba. Ita yanzu hankalinta a kwance yake tana samun ku’di irin ku’din da take so. Burinta ya cika
Muhammad Alwan ya cikata da naira. Ga Moddi ma yana sakar mata ku’di duk da bashi da lokacinta don
ya yi keeping kansa busy.
Ranar da Amani ta san tana da ciki a ranar saura sati biyu auren su, kuma a ranar Didi ta sanar da Moddi
zata aurar da su Amani. Runtse idonsa kawai ya yi yana mamakin abinda Didin ta ce sai dai bai furta
komai ba, don ba’a ba shi damar furtawar ba. Yana kallo ta mik’e ta fice daga parlorn sa. Sai kawai ya cusa
hannunsa cikin sumar kansa yana fisga ka’dan ka’dan…
Wannan shine abinda ya faru….
★★★★
An dawo labari…
Cikin dare Amanin ta dinga jin motsi a ‘dakin da take kwance a asibitin. Ba barci take ba hakan yasa ta
bu’de ido tana kallon mutanen da suka shigo cikin d’akin jikinsu sanye da black wears… fuskarsu a sink’e
cikin face mask. Tana kallo suka gudawa duka mutanen d’akin wata powder. Tana shirin ihu itama suka
busa mata… daga nan bata San me Ya faru ba. Sai bu’de idonta ta yi ta ganta a wani irin d’aki……
JIKAR NASHE ✍🏽
Saura 2 pages a gama book 1. Shine kuma free. Don samun cigaba ki tura 500 ko 1k don shiga aji na
musamman ta wannan account D’in. 2118666253 UBA.
HADARIN GABAS YANZU AKA FARA!HADARIN GABAS….. 👌
33.
NAZEEFAH SABO NASHE.★ ✍️
08033748387.
BRIGHT PENS SECOND BATCH
Ware idonta ta yi sosai tana duban babban bedroom d’in, da ya sha Kayan more Rayuwa masu
azababben kyau. D’akin banda fitar da wani irin sassanyan k’amshi ba abinda yake yi. Ta dinga bin d’akin
da kallo tana mamakin ina ne nan? Bata samu amsa ba kasancewar ba kowa a wajen. Ta mik’e tana jin
yarda kanta ya wani irin sarà mata kamar zai fa’do, hakan yasa ta rik’e kan nata tana cije bakinta ka’dan.
Ta koma ta zauna don ba zata iya tafiya ba, wani irin ciwon kai take ji ga mararta data matsa mata da
ciwo. Tsawon mintuna tana zaune a gefen tattausan gadon ba tare da ta San abin yi ba. Sai ta dinga jin
motsi alamar ana bu’de k’ofar d’akin. Ido ta Ware ganin wacca ta shigo. Mace ce cikin kamilalliyar shiga
sai kallonta take murmushi fal fuskarta ta furta “Kin tashi?” Madadin Amanin ta amsa mata sai ta d’auke
kanta, zuciyarta na wani irin bugu ta furta “Ina ne nan? Wa ya d’auko ni daga asibiti ya kawo ni nan?”
Girgiza kai matar ta yi tana furta “Sanin ba shi da wani amfani, don haka gwara ma ki daina tambaya ki
fuskanci abinda yake gabanki, Uwargida ta ce a yi Miki duk abinda kike so, mu lallab’aki tamkar sarauniya
don haka yanzu zamu cigaba da bin Umarninki…” “Uwargida?” Amani ta furta cikin sigar tambaya. Matar
ta sake sakin murmushi ta furta “K’warai kuwa, na San baki Santa ba, amma nan gaba ka’dan za ki Santa,
ta ce tana gaisheki ki kuma kula da kanki da abinda ke cikin ki, don a yanzu bata da wani abu mafi soyuwa
da ya zarce ke da ‘d’an cikinki a duniyar nan….” Hannu Ama ta saka ta Shafa cikin, zuciyarta na wani irin
wuntsilawa bata so ta gasgata abinda yake ranta, amma tabbas ko ta k’i ko ta so dole ta yarda Dada ya
siyar da ita, Ya kawo ta inda za’a tsafaceta a tsaface d’an cikinta…sai ta dinga jin wani irin takaici
zuciyarta ta dinga zafi. A zafafe ta kalli matar ta ce “Idan burinku d’an cikin, ku cire shi ku bar ni naje na yi
rayuwata kamar yarda kuke so…” “Ba hurumina bane wannan…” Matar ta fa’da tana sakin dariya. Sai
kuma ta jawo food warmers masu kyau ta shiga zuba lafiyayyen abinci a cikin plate ta tura gaban Amani.
Kallon abincin ta yi kafin ta furzar da huci. “Ba zan ci ba, ki d’auke daga gabana.” Bata bi tata ba ta fice ta
bar mata d’akin. Amani ta yi saurin mik’ewa zuwa bakin k’ofar. Sai ta tarar k’ofar irin mai thumbprint ce
dole ba zata iya fita ba komai zata yi. Hawaye ya zubo mata, a hankali ta zube a saman tattausan carpet
‘din tana sakin kuka. K’amshin abincin ya dinga rinjayar yunwar da take ji don haka bata San sanda ta ja
plate D’in ta fara ci ba. Ita kanta ta manta yaushe rabonta da abinci