Author : Nazeefa Sabo Nashe Category : African Stories & Novels
tafi? Bayan ina
murna na samu aboki a inda ban san kowa ba. Ka taimake min mana nima fa musulmi ne.. ko baka son
lada?” Ya fa’da cikin gwamutstsiyar Hausarsa. Haka kawai Imaam sai ya ji ya amince da son kyautata
masa “Yanzu ya kake son a yi? Ni bana jin da’di ne ina son na je gida.” Cikin muryar tausayawa Alwan ya
furta “Oh Sorry, Amma pls mu yi exchanging number so that muna communicating..” Imaam bai masa
musu ba ya amshi wayarsa mai d’an banzan kyau ya saka masa numberrsa ya kuma yi saving da Imaaam
Moddibo..” Alwan ya kalli sunan yana furta “Nice…. Ni kuma sunana Muhammad Alwan. From Turkey
hope na samu d’an uwa.” D’aga kai Imaam ya yi daga nan ya masa sallama ya burga machine d’insa ya
wuce.
Koda ya koma gida bai wani kira Alwan ba ya ma manta da shi. Y’an biyunsa Iman da Amani ya yiwa wasa
ya shige d’aki.Safana ta bi bayansa ganin kamar baya jin da’di. Bai b’oye mata ha’duwarsu da Alwan ba ya
gaya mata komai. Murmushi ta saki tana furta “Allah yasa ha’duwar ta zama alheri…”
Da sassafe ya dinga jin wayarsa tana ringing. Yana dubawa yaga Muhammad Alwan ne sai da ya mik’e ya
zauna sosai sannan ya saka wayar a kunnensa “Morning” Alwan ya furta cikin nutsuwa “So ka tafi ka bar
amanarka da Musulunci ya baka, baka sake kirana ka ji ya nake ba na kira kuma baka d’aga ba.” Imaam ya
d’an saki ajiyar zuciya ya furta “Am sorry..” “No problem yanzu ina so kazo ka raka ni inda za ni pls!”
Kallon agogo Imaam ya yi ya furta “Ina zuwa aiki yanzu…” “please ka zo idan akwai yiwuwar ka samu
wani aikin da yafi naka sai kaga ka dace muna da companies a Nigeria and menene qualification naka? Ko
da yake sai kazo dai..” Ya fa’da yana kashe wayar. Safna da ta ji komai kasancewar wayar a handsfree take
ta mik’e da sauri tana furta “Alhamdulilah Moddibo ka maza ka shirya ka je ba mamaki wahalarmu ce
tazo k’arshe, dama aikin gwamnati bakomai a cikinsa sai wahala..” D’an kallonta kawai Moddibo ya yi ya
tab’e baki ya shige toilet ba wai don yana ji zai amince ya karb’i tayin da Muhammad Alwan ya masa ba.
Wanka ya yi ya shirya cikin k’ananan kayan da ya saba sakawa ya fito fes da shi sai zabga k’amshi yake.
Safna ta dinga kallonsa tana jin alfaharin kasancewarsa Mijinta. D’an rungumo shi ta yi tana shafa masa
wani turare da ba na komai bane sai na mallaka a kullum idan zai fita sai ta shafa masa sam baya kawo
komai a ransa don ta iya salo da kissa iri iri.
A parlorn su madaidaici ya zauna. Daidai lokacin da Iman da Amani suka shigo jikinsu a d’arare yaran
suna kallon Dahdansu da yake shan tea da k’wai. Yawu suke ha’diyewa don dai su ba shi aka basu ba.
Kunu ne da k’uli-k’uli kullum Mommyn take sakawa a basu kuma ta garga’di masu aikin da kada su
kuskura su fa’da k’arshe ma ta saka duk aka musu dabaibayi sai abinda tace suke aikatawa. Don haka ba
zasu tab’a bu’de bak’i su fa’da ba sai idan ta so. Idon Amani ya kawo ruwa tana kallon Dahda ta nuna
k’wan hannunsa. Da mamaki yake kallonta cikin tausayin yaran da kullum a fuskarsu zaka san su marayu
ne ba su da walwala sam sai dai idan Hajja tazo gidan ta kwana biyu. Ya ja hannunta ta matsa kusa da shi
ya furta “Zaki ci ne?” Ta d’aga kai. Shiru ya yi kafin ya d’ago yana kallon Safna ya furta “Yaran nan basu
karya ba ne?” Ta ware ido tana furta “In ji Uban wa? Ke dube ni nan baku karya ba?” Ido Dahda ya zuba
mata ya ce “In ji Ubana….” Ya gutsiro k’wan ya mik’a musu duka dankali da k’wan da suke cikin plate d’in.
Da wani irin sauri suka dinga ci… har bai san sanda wata k’walla ta fara zubo masa ba.. Daga ganin yarda
suke ci ya tabbata yunwa suke ji. Sai da suka ci sosai sannan ya ha’da musu tea mai kauri suka sha. Ya
d’ago yana kallon Safna “As from today da yara na zan dinga cin abinci…” Safna ta ha’diye wani mugun
yawu tana furta “Haba dai kawai kuma sai mu zauna da su cin abinci su hanamu sakewa…” Ya watsa
mata wani kallo da ya sakata yin shiru bata shirya ba. Goge musu baki ya yi sannan ya bu’de lunchbox
d’insu abinda bai tab’a yi ba. Waro ido ya yi yana furta “What? Me
Ye wannan? da d’umamen tuwo za su makarantar?” Da sauri Safna ta waro ido kamar gaske hankalinta a
tashe ta ce “what a nonsense, wannan ai ba laifina ba ne laifin su Talatu ne bari a kira su a ji dalili….” Har
ta je bakin k’ofa ya jata baya da k’arfin gaske… ya wancakalar da ita saman kujera, idanunsa sun fito sosai
ya furta “Wallahi na samu laifinkine sai kin ga abinda zan miki. Don su nake nema na don haka dole a
dinga ciyar da su da cima mai kyau…” ya fita tsakargida yana k’wala kiran Mama Talatu da Inna Laraba.
Da sauri suka fito daga d’akinsu da yake gefen tsakargidan. Yanayin da suka gan shi a lokacin ya basu
tsoro suka furta “Baban yara lafiya?” Lunch box d’in ya cilla musu “Meye wannan? waye ya ce a zubawa
su Ama wannan abin su tafi da shi school?” Idanu suka waro suna kallon juna. Tsawar da ya sake saki ne
ya saka su saurin amsawa da rawar baki duk da Suna jin shakkar Safnan ba su fasa cewa “Hajiya ce ta yi
umarnin haka…” Ya juyo ya mata wani kallo da ya kusan sakata fitsari a wando. Bai yi magana ba illa cije
leb’ensa na k’asa da ya yi ya fice yana jan hannun yaran. Zuciyarsa na wani irin tafarfasa shi ka’dai ya san
hukuncin da zai yiwa Safna idan ya koma gidan yana jin k’arshen zamansu ne ya zo. Don ba zai laminci a
dinga zaluntar masa yara ba…
Safna tana ganin ya fita ta juya tana kallon Mama Talatu da Laraba. Ta k’unduma wani zagi kamar ba za
su yi sa’a da uwarta ba. “Ni kuke son ku kashewa aure ko? Wallahil azeem k’arshen zamanku a gidan nan
ya zo…” Haka ta dinga zaginsu tana ci musu mutunci ba su ce mata komai ba. Sai dai zuciyarsu fal take da
murnar tonuwar asirinta yau. Don kam Safna muguwa ce ta bugawa a jarida ba irin azabar da bata bawa
yaran Allah ne ka’dai ya yi da kwanansu a gaba. Sau tari daga su har yaran ba sa sake cin wani abinci
bayan wanda Zata basu da rana sai kuma garin Allah ya waye. Haka suna ji suna gani za su yi ta jin
k’amshin abu amma haramiyarsu. Ko idan Babansu ya kawo abu zai sa ta d’iba ta bi su k’aramin parlorn
da suke zama a tsakar gida da daddare ta shiga da kayan da’din ta ajiye ta ce kuma duk wanda ya ci sai ya
ha’du da fushinta. Wani lokacin Amani ce duk hanata da zasu yi sai ta ci tun bata iya k’unk’uni har ta fara
sakarwa Mommyn k’unk’uni kuma duk abinda zata mata ba zata yi kuka ba, sai dai ta yi ta cizon leb’enta
tana huci kamar yarda ta ga Dahdansu yana yi. Har tsarki da ruwan borkono ta tab’a yiwa Amani ranar ba
su yi barciba kuma duk kukan yarinyar ta hanasu su gayawa Ubanta… kai muguntar Safna garesu ba zata
k’irgu ba.. idan suka yi nufin gayawa Hajja sai su ji kamar an k’ulle musu baki sun kasa…
Suna kallonta ta shiga d’aki ta saka Hijab ta fito rik’e da jaka. Bata ko kallesu ba ta fice daga gidan. Suma
ba su damu ba don sun san ta saba fita idan baya nan don haka ba wani sabon abu bane a wajensu suka
saki ajiyar zuciya a fili suka fara tsine mata da son Allah ya tona mata asiri komai daren da’dewa….
★ ✍️
Yana fita ya biya super market ya siya musu kayayyakin da’di da yawa sannan ya sauke su a makarantar
da suke zuwa. Irin private school d’innan ce mai sauk’in ku’di.. Suna sauka a machine d’in Amani da bata
shiru da bakinta ta kalleshi “Dahda kullum zaka dinga bamu k’wai da shayi mai madara… ka siyo mana
kayan da’di mu je da su makaranta?y’an ajinmu duka da kayan da’di suke zuwa, ba da tuwo da kwaki ba.”
Imaam sai da ya yi da gaske sannan ya amsa mata saboda yarda wata k’walla ta fara zubo masa “Zan
muku duk abinda kuke so Ama…” ya fa’da yana sumbatar gefen kumatunsu. Ya rungume su sannan suka
shiga aji. Yau zuciyarsu fal nisha’di ba rashin walwalar nan da suke zuwa da shi makaranta. Imaam ya bi
bayansu da kallo yana share k’wallar da take zuba a idonsa, ya furta “Allah ka yafe min…” cikin raunin
murya don sai ya tattara laifin gaba d’aya ya d’ora a kansa yana ganin koma me ya faru laifinsa ne da baya
bincika halin da yaran suke ciki musamman sanin da ya yi basu da mahaifiya. Kai tsaye zuciyarsa ta ba shi
shawarar ya mayar da yaran nasa gidan Hajja hankalinsa zai fi kwanciya.
𝒥𝒾𝓀𝒶𝓇 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★ ✍️HADARIN GABAS……👌
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★ ✍️
08033748387.
★★★★★ 1️⃣3️⃣
_*🔥BRIGHT PENS...🔥*_
2nd batch
Zazzafar tafiya mai abin ban mamaki, tawayen jerin marubuta huɗu a sabuwar tafiyar ta second batch.
*HADARIN GABAS*
Nazeefah Sabo Nashe
*ƘARFE A WUTA*
Ayushercool
*ZAYTOON*
Zee kumurya
*MUTALLAB*
Nimcyluv Sarauta.
Yawaitar kiran da Muhammad Alwan Yake masa ne, ya saka shi bai k’arasa gidan Hajja ba sai kawai ya tafi
direct wajen Muhd d’in, bayan ya yi waya office ya bada uzirin gaibu. Don bai ji a ransa zai iya barin aikin
sa ba. Madadin ya fito Muhd d’in cewa ya yi ya shiga d’aki ya same shi. Bai masa musu ba ya shiga in da
ya ce masa.
Tsaf d’akin sai zabga azababben k’amshi yake. Muhd ya nuna masa wajen zama “Please sit mana Imaam,
me yasa kake yin kamar bak’o.” Murmushi Imam ya saki karo na farko tun bayan ha’duwarsu ya zauna a
kujerar. Alwan ya cigaba da shiryawa cikin ha’daddiyar suit d’insa ya yi combing kansa mai kama da
gashin larabawa. Sai da ya gama ya kalli Juice d’in da ya ajiye masa da snacks ya mayar da kallonsa kan
Imaam d’in da alamar tambaya ya furta “Me yasa baka ci komai ba? Ko baka yarda da ni ba ne?” Girgiza
kai Imaam ya yi kafin ya tsiyayi lemon mai sanyin gaske ya kai bakinsa. Idanunsa akan Alwan da yake
sakin murmushi. “Nagode da ka sha, da baka sha ba akwai matsala….” Ya furta yana saka glass d’insa da
ya kasance bak’i wuluk. “Matsala kuma?” Alwan ba wani damuwa a fuskarsa ya d’aga kai yana furta
“Babba ma kuwa…” ya d’an ja fasali sai kuma
Ya furta “Ka san mu larabawa bama son mu yiwa mutum kyauta ya k’i amsa, sai mu ji ba da’di a
zuciyarmu.” Ya sake fa’da yana d’an sakin murmushi. dafa shi ya yi ya furta “Rashin shan da zaka yi zai
saka na ji a zuciyata baka amince da ni ba.” Sai sannan Imam ya saki ajiyar zuciya, amma sai ya samu
kansa da jin wani irin nauyi a kansa take ya d’an lumshe ido yana sakin ajiyar zuciya bai kawo komai a
ransa ba sai tunanin ko don yana cikin b’acin ran Safna ne.
“Ka tashi mu je.” Ya furta yana dafa kafa’darsa Imaam ya mik’e a hankali ya bi bayansa.
Motarsa ya ce su shiga ya ajiye machine d’in nasa. Hakan kuwa aka yi. Direct cikin abinda bai fi mintuna
ba Imaam ya gan su a cikin Government House. Da mamaki yake kallon Alwan d’in. D’aga masa kai kawai
ya yi ya furta “Mu je, zan ga Governor na kai masa sak’o.” Jikin Imaam a sanyaye ya fito ya bi bayansa
yana mamakin wai yau shine zai ga Governor lallai ha’duwarsa da Alwan alheri ne.
A babban parlorn gwamnati aka saukesu inda gwamna yake gaisawa da manyan bak’insa. Mamaki bai
gama cika zuciyar Imaam ba, sai da Gwamna ya shigo madadin yaga Alwan ya mik’e ya kai gaisuwa sai
yaga ma Gwamnan ne yake daraja Alwan d’in. “Barka da sauka Doctor Alwan…” Murmushi Alwan ya
sakar masa yana firta “Nice to meet you excellency…” Gwamna ya d’aga kai yana sake sakin murmushi
sai kuma ya kai dubansa kan Imaam yana masa kallon rashin sani ko kafin ya yi magana Alwan ya yi
gyaran murya ya furta “A best friend of mine…” Gwamna ya saki murmushi yana mik’awa Imaam hannu.
Imaam ya d’an ji wani banbarakwai sai kuma ya dake ya mik’a masa nasa hannun shima.
Zai Mik’e ya fita ganin kamar tattaunawar tasu ta sirri ce Alwan ya saka baki ya kira shi. “Just sit, ba sai ka
fita ba.” Ya koma ya zauna. Yana kallon wani kallo da Gwamna ya masa sai kuma ya d’auke kai ya cigaba
da kallon Alwan da yake mik’o masa papers. “Zaka yi signing anan kamar yarda na fa’da maka, mun kuma
amince da buk’atarka ta ka sanya hannun jari a companyn da zamu bu’de anan, mun yarda zamu bu’de
babban companyn don cigaban arewa…” Murmushi da ya bayyana tsananin murnarsa gwamna ya saki
yana furta “Alhamdulillah… Nagode sosai ka mik’a min godiyata wajen Boss…” murmushi Alwan ya saki
yana furta “No problem Excellency..” ya mik’e yana mik’a masa hannu suka gaisa da tafawa sannan ya fice
a hanzarce bayan ya kalli Imaam da duk yabi ya zama kamr wani gunki a wajen. Murmushi ya saki ka’dan.
Ya dafa shi yana furta “Shall we?” Imaam ya d’Aga kai ya mik’e shima ya bi bayansa da d’an hanzari.
A mota kasa shiru Imaam ya yi sai da ya kalli Alwan ya furta “Dama ka tab’a zuwa Nigeria?” Murmushi
kawai Alwan ya sakar masa kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya saki ajiyar zuciya ya furta “Rabin
rayuwa ta na yi ne a Nigeria Abuja, shi yasa zaka ji na iya Hausa sosai, amma all my family suna Turkey, ni
na zauna anan ne saboda issue na business…” Imaam ya girgiza kai. “Ka san Turkish companies da suke
cikin k’asar nan?” Imaam ya yi saurin d’aga kai “Shi kuwa ya san Turkish group of companies duk wanda
yake K’asar nan Ai ba zai ce bai san wa’dannan companies d’in da k’asar nan take alfahari da su ba.
Kamfaninnika ne da suke sarrafa kayan masarufi iri iri na abubuwan amfani da furniture’s masu kyau da
tsadar gaske, a kwanan nan suke shirin bu’de companyn ha’da motoci. “Na familyn mu ne…” Ya ji muryar
Alwan a sama “Ni nake monitoring na Nigeria.” Da sauri Imaam ya juya yana kallonsa idan kuwa har ta
tabbata da gaske ne tabbas Alwan ba shi da girman kai kuma ya tsinci dami a kala. “Kana son ka yi
business da mu?” Imaam ya d’aga kai da sauri don ba zai bar kansa ya k’ulle ba. Murmushi Alwan ya saki
a zuciyarsa ya furta “Nice, hakan ya yi…” a fili kuwa cewa ya yi “Akwai shara’di… idan ka amince sai nace
maka ka godewa Allah ka kusa shiga sahun billionaires na Arewa…” Imaam ya ha’diye yawu yana d’aga
kai “Sharad’in me?” Sai da Alwan ya juyo kamar ba driving yake ba sai kuma ya juya yana cigaba da tuk’in
ya furta “I will tell you, but not now.”
A wurin siyar da motoci ya yi parking yana kallon Imaam ya furta “Mu je ka min rakiya, Allah yasa ka iya
mota ka ja min ita.” Imaam ya d’aga kai yana furta “Na iya..” ya jijjiga kai yana murmushi suka isa wajen
wata Honda accord mai masifar kyau bak’a wuluk. Ya yi ciniki ya biya ku’din ya mik’awa Imaam key d’in.
Imaam yana kallonsa ya furta na menene? “Na taimako na da ka yi, kuma kada ka ce min ba zaka amsa
ba ka san hukuncin hakan islamically..” Imaam ya saki ajiyar zuciya ya kuma kasa yi masa musu yana kallo
ya fita ya bar shi a wajen yana furta “Zan kiraka anjima zan je Abuja but zan dawo morning.” Ya lakace
hancin Imaam ya fita daga wajen yana murmushi ko bakomai burinsa ya cika. Imaam kasa motsa wa ya yi
daga wajen ya dinga kallon Motar da aka ce tasa ce ya lumshe ido yana mamakin Alwan da dukkan
alherensa daga ha’duwa jiya kawai? Ko da yake a arziki irin na danginsu ya san wannan bakomai ba ne.
Don haka sai ya ji ya samu nutsuwar zuciya ya shiga motar cikin matuk’ar farin ciki ya ja zuwa gidan Hajja
don ita ya kamata ya fara sanarwa….
★★ ✍️
Safna kuwa tun bayan fitar ta gida hankalinta tashe bata tsaya ko ina ba sai a gaban Malaminta. Yanayinta
da ya gani ya tabbatar masa ba lafiya ba. Ya san Safna ba tun yau ba ta amince da cewa shi ke samar
Mata da duk wani farin ciki.
Sun gaisa hankalinta a tashe ta sanar da shi dalilin zuwanta. Idanu ya zuba mata bayan duk ya gama jin
abinda ta ce ya furta “Akwai matsala Safna, dole ki tashi tsaye akan Mijinki don idan baki wasa ba kina ji
kina gani zai fi k’arfinki…” Tashin hankali ya bayyana k’arara akan fuskarta idan da abinda ta tsana a
sanar mata da Imaam zai rabu da ita. Ta yarda da aikin Malamin nan tun farkon ha’duwarsu da Imaam shi
ya mallake mata zuciyarsa da tunaninsa. “Akwai alheri ma da yake matso shi nan kusa, sai dai idan ba ki yi
da gaske ba zai ture Alherin akan wani dalili…” Ta waro ido “Malam hakane wallahi, don jiya ya ha’du da
wani mutum mai ku’di sai dai da dukkan alamu baya son tarayyarsu da mutumin Malam ina son ka kulle
bakinsa ya zama duk abinda mutumin ya umarceshi kawai ya aikata ba musu, ni in dai Imaam zai yi ku’di
kawai koma ta wani hali ne ya yi, ko na huta da gorin dangina na auri wanda ba shi da ku’di…” Malam ya
saki murmushi “An gama Safna, arziki kam Mijinki zai yi shi, amma a k’arshe fa naga wani duhu…..” “In
dai a k’arshe ne Malam duk daga baya ne, kawai a min aikin da zai yi abinda suke so ko baya so. Sannan
ka rufe min bakinsa tsaf kada ya dinga gayawa kowa sirrinsa sai ni ka’dai don kada ya je ya gayawa Hajja
ta hana shi ta cucemu.” Ta fa’da ba tare da ta bari bokan ya gaya mata duhun me ya gani ba.Malam ya
jijjiga kai ya cigaba da dube duben k’asarsa ya d’ago yana kallonta ya furta “Zaki iya birne bunsuru da
rai?” “Ba abinda ba zan iya ba Malam kai kanka shaida ne don na yi wanda ya fi wannan in dai akan
Moddibo ne….” Tabbas kin yi Safna ni kaina ina jinjinawa jarumtarki da rashin tsoro, don ma