Author : Nazeefa Sabo Nashe Category : African Stories & Novels
Ware
idonta tana furta “Me ka aikata Kiddo? Shi yasa tun ‘d’azu na kasa samun nutsuwa, me ka aikata na ce
maka.” Murya a can k’asa ya furta “Bakomai, ki zo please akwai matsala..” daga haka ya yi cutting kiran Ya
shige toilet daidai lokacin da Safnan ta bu’dewa Didin k’ofa. Didi tana kallonta cikin tashin hankali ta furta
“Ina Amani?” Safna ta rushe da kukan k’arya tana nuna mata wajen da ba zaka tab’a cewa d’aki ba ne don
ya saje da bangon wajen ba k’ofa. Didi ta ce “Ban gane ba, ina take?” Safna ta saka kuka tana furta “Ya
b’oye ta cikin d’akin sirrinsa, d’akin da yake ajiye tarkacen tsafinsa bayan ya mata fya’de….” A tare Didi da
Iman suka zube k’asa da alama dogon suma suka yi. Moddibo da bai San abinda ake ba, ya fito jikinsa
sanye da kayansa yana sake goge kansa. Ganin Iman da Didi a k’asa yasa ya ware ido yana kallon Safna, ya
yi kanta da sauri, yana furta “Me kika aikata musu?” Ta fincike hannunsa a wuyanta tana furta “Na gaya
musu abinda ka aikata, and so what? Wallahi ka sake ni sai na gayawa duniya abinda ka aikata, idan kaga
ban gaya musu ba ka saki matar da aka aura…” Bai bi ta kanta ba ya dai cije bakinsa Ya isa kan su Didi
yana shafa musu ruwa a fuska. Suka saki ajiyar zuciya a kusan tare. Didi ta kama hannunsa ta rik’e sosai a
hannunta tana furta “Ka gaya min Moddi, ka gaya min mummunan mafarkin da na Saba ne..” ya yi k’asa
da kansa hawayen idonsa yana zuba, Wanda shi kansa bai San dalilin zubar su ba, bai San a mizanin da zai
ajiye su ba. Ya matsa hannunta a hankali ya girgiza mata kai. Shigowar Umma T, da sauri ne ya saka shi
mik’ewa ya matsa daga wajen da suke… a fisge ta ce “Ina Amani?” Don burinta ganin Amanin ta kuma
tabbatar da ba abinda ya sameta. Ya cije leb’ensa kawai tunda Umma T taga haka ta tabbatar ya yi tsiyar
Ya aikata. Sai kawai ta sulale a wajen itama ta zauna cikin tashin hankali. Da muryar kuka take furta “Why
Moddi? Me yasa zaka saka mana ciwon da zamu kasa warke wa, Amani fa, Amani y’arka da ka haifa….”
Iman ma kukan take kawai. Shi kuma Uban gayyar ya yi k’asa da kansa kawai, shi ‘din ma ba wai yana
cikin sukunin zuciya ba ne, and bai san ta inda zai musu bayani su fahimce shi ba. Didi dai wani irin nishi
kawai take, hakan ya ankarar da shi Ya ‘dau waya ya kira Doctor. Amma kafin zuwa Doctor Didi ta ce lallai
sai an fitar da ita daga gidan Moddi ta daina ganinsa. Bata son ganinsa ta tsane shi. Umma T ce ta dinga
bata hak’uri ta saka aka mayar da ita ‘d’akinta amma still hankalinta baya jikinta, bata cikin nutsuwarta
hakan yasa Umma T ta sake shiga tashin hankali bata son Didin ta yiwa Moddinta baki. Suna shiga d’akin
ta rufo k’ofar ta saka Didi a jikinta tana sake kwantar mata da hankali. “Ki yi hak’uri Didi, Moddi a yanzu
addu’ar ki yake buk’ata, amma k’addarar auren Safna ne ta cilla shi cikin wannan halin.” Nan Umma T ta
shiga bata labarin abubuwan da da ita Didi bata sani ba. Didi ta dinga kallonta da wani irin shock ta furta
“Fateemah, me yasa kika b’oye min hakan? Me yasa a sanda na ce Miki me yasa su Magajiya zasu bar
gidan nan me yasa kika min k’aryar akan Moddi yafi son matarsa ne da su shi yasa zasu tafi sun gaji,
sanda kika bijiro min da maganar aurensu da kin gaya min hakan ai da ba wani ja zan amince, me yasa
Fateemah yanzu kin ga illar shirunki ko? Kinga halin da kika jefa mu a ciki ko? Burin Safna ya cika Moddi
ya kusanci y’ar cikinsa, ya b’ata mata rayuwa da wani ido zan kalli jama’a idan Safna ta tona asirin nan…”
“Ba zata tona ba Didi, ni na San Safna ba zata tona ba, abu guda ne dole a mata abinda take so dole
Moddi ya fasa auren da ya yi dole ya amince su rabu da matar, shine na San burinta, to za’a cika mata
burinta, in dai akai haka ina tabbatar miki ba zata furta zancen nan ga kowa ba, zata zauna matsayin
matar Moddi ita ka’dai as she wish…” Didi ta dinga k’ok’arin tattare yawun bakinta ta ha’diye da k’yar,
tana jin d’acinsa a mak’ogaranta. Zuciyarta na cigaba da bugu. Har ta sume bata sani ba. Allah ya taimaka
a lokacin Doctor ya zo. Ya yi k’ok’arin taimaka mata da duk abinda zata buk’ata.
Su Didi na fita Moddi ya zube a saman Otman chair da take d’akinsa. Goshinsa kawai yake durza yana jin
hayaniyar Safna a saman kansa. Muryarta a sama tana furta “Idan Har kana son na rufa maka asiri wallahi
sai ka yarda da duk shara’din da zan gaya maka…” ya ‘d’an bu’de ido yana kallonta kafin ya ja hannunta
Ya fitar da ita daga d’akin, ya mayar da k’ofar yana murza key ya furta “We will talk about it later….”
Sannan ya nufi secret room d’in da yake ‘d’akin. Zuciyarsa na wani irin bugu ya saka hannu Ya bu’de
‘d’akin. Ta ‘d’ago a fusace idonta ya yi luhu luhu gashin kanta a hargutse kamar mahaukaciya sabon kamu.
Ta zuba masa idanuwan nata. Tana sake jin wata irin wutar tsanarsa da take ruruwa a zuciyarta…. Da
wani irin hanzari ta wawuro side lamp da take gefenta gadan gadan ta kwa’da masa ita tana furta “Na
tsaneka, na tsaneka Dada, na tsaneka Moddi kuma ba zan yafe maka ba wallahi…….
(Na biya bashin na jiya, As we all know bana posting weekend sai Allah ya kai mu Monday. Ku cigaba da
payment into this account don book 1 daf yake da k’arewa. Kuma kaf labarin ba’a fara komai ba.
2118666253 UBA 500, aji na musamman 1k.)
JIKAR NASHE ✍🏽HADARIN GABAS……👌
31.
NAZEEFAH SABO NASHE★ ✍️
08033748387.
★★★★★
Hannu yasa inda yaji danshin ko bai duba ba, ya san jini ne, ciwo Amani ta ji masa. Ya cancanci haka ko na
ce fiye da haka a wajen ta. Don haka bai ji zafi ba, madadin haka ma tausayinta ne ya cika masa zuciya. Ya
lumshe ido bai damu da jinin da yake zuba daga goshinsa ba, burinsa isa wajenta kawai ta amince kuma
ya taimaka mata. Sai dai a idonta ya dinga hango tarin tsanarsa, a cikin idon ya hango zata iya kashe shi
saboda Jin haushinsa da take. Idanun Sun birkice zuwa wata color daban. Jingina ya yi da bango yana Jin
sautin kukanta yana kewaye kwanyarsa. Kuka ne da take yinsa da yake bayyana irin zafi da k’uncin da
zuciyarta take ciki. Idonsa kawai ya lumshe yana cigaba da Jin k’uncin zuciyarsa. Ganin tana shirin
shi’dewa ya yi saurin isa wajenta da niyyar kamata da sauri ta dakatar da shi ta hanyar sake rotsa masa
Abu a d’aya b’arin goshinsa. Bai damu ba ya yi saurin gocewa yana furta “Ki tsaya Ama… just wait, you
need help…” A fusace ta sake d’agowa sai dai idanunta basa gani sannan gangar jikinta ta yi rauni bata
da wani k’arfi sai na zuciya, don tana Jin zuciyarta kamar k’arfe tana Jin kuma zata iya aikata komai sai dai
sassan jikinta Sun k’i bata ha’din Kai. Don haka tana ji tana gani Dadan ya d’agata cak zuwa lallausa kuma
faffa’dan gadon. Zata yi masa gardama ya yi k’ura mata ido yana furta “Shsssh, relax.” Ta runtse ido kawai
tana Jin Amon muryar tasa a tsakiyar kanta. Muryar da da take son ji yanzu ba muryar data tsana saboda
ita. Wayarsa ya danna tana ringing Doctorn ya d’aga “Please ka zo railway akwai patient, come with a
nurse…” ya furta yana sake damk’e hannun Ama da take k’ok’arin fisgewa tana son ta mik’e. Tsuke
fuskarsa ya yi sosai ya ha’de rai yana kallonta ya furta “Ba zaki bari ba, me ye haka?” “Ka bari Dada ka
cuce ni. Wallahi na tsane ka, bana son kallonka kuma ma…” sai ta kuma rushewa da kuka. Fisgar leb’ensa
ya yi yana furta “Don’t forget bani na kawo ki ‘dakina ba, ke zan tuhuma me yasa kika zo? Me kika zo yi
min?” Sai ta rushe da kuka tana furta “Kai ne Dada, kuma ka sani Kai ne silar fa’dawa ta cikin wannan
halin kai kake tsafi da gangar jikina….” Turo k’ofar da aka yi ne yasa ta ha’diye sauran maganar. Ganin
Umma T ce yasa Moddi mik’ewa fuskarsa a ‘daure ya koma gefe yana kallon Umma T ‘D’in da tata fuskar
tafi ta shi d’aurewa, idanunta Sun yi jajir ta kau da Kai tana kallonsa…. Sai kuma ta cije bakinta ta fara
magana k’asa k’asa… “Fita waje Moddi.” Ya yi kamar bai ji ta ba kamar ba zai fita ba, sai kuma ya fitan.
Umma T. Ta nufi toilet ranta duk a jagule. Ruwa mai zafi ta ha’da mata sannan ta fito. Hannu kawai ta
saka ta mik’ar da Amanin tsaye. Da sauri Amanin ta saka k’ara ka’dan. Tausayinta ya kama Fateemah
amma ta cije tana furta “Wannan ne kawai gatan da zan miki, a yanzu kam Ban San me zan ce miki na
rarrashi zuciyarki ba, cuta dai Safna ta riga ta yi mana ita wacce ba Wanda zai iya warkar da mu.” Ta fa’da
suna shiga toilet ‘din. Towel k’arami ta mik’a mata tana furta “Ki cire kayanki ki shiga cikin ruwan can, shi
zai saka ki warware jikinki ya daina ra’dadin da yake.” Amani kamar ta zunduma ihu haka take ji. Don dole
ta runtse idonsa ta shiga cikin ruwan wani bak’in ciki na ratsata ta sha mafarkin hakan Amma ga mijinta
na halak ta sha mafarkin wannan ranar da yarda mijinta zai lallab’a ta idan hakan ta kasance, sai gashi
lamarin yazo mata a abinda zata kira mummunar k’addara. Umma T ta juya tana furta idan ya salamce sai
ki tara wani ki yi wankan tsarki. Amani ta lumshe ido hawaye suna sake zubo mata kamar da bakin
k’warya.
Fateemah tana fita daga toilet ‘din ta fita parlor, itama nata idanun hawayen suke zubarwa, da gaske tana
Jin wani irin ciwo a zuciyarta, sai take ga kamar Sun ci amanar mahaifiyar yarannan Sun ci amanar Y’ar
riga. Me yasa Moddi ya kasa hak’uri da aka hana shi auren Safna, ya turje ya dage sai da ta aurota ba tare
da amincewarsu ko na Didi ba? Y’ar riga suka so, suka kuma yi masa sha’awar zama matarsa ba don
komai ba sai don kyawawan d’abi’unta. Ta tuna ranar da suka je Kai kayan lefen aurensa, bai sani ba bai
San ana nema masa aure ba. Su kansu iyayen y’ar riga basu sani ba sai da suka je, a take a wajen
Mahaifinta ya ce ya basu aurenta, bai b’oye musu ba ya sanar da su y’ar riga bazawara ce ta tab’a aure,
sai dai auren da wata guda Mijin ya mutu ta hanyar hatsarin mota. Basu wani ji komai ba Sun San Didi ba
zata k’i ba suka bayar da kayan aka kuma saka rana sati biyu. Sanda suka sanar Didi ai y’ar riga bazawara
ce cikin murmushi ta ce “Shikkenan sai Moddi ya raya ingantacciyar sunna, Manzon Allah ma da
bazawara ya fara…” a haka aka nema masa auren, bai sani ba har sai ranar d’aurin auren da aka gaya
masa aka kuma sanar da shi da y’ar riga aka d’aura. A take a wajen ya tubure ya kuma rantse baya sonta
me zai yi da ita gashi an sanar da shi bazawara ce… “ ta saki ajiyar zuciya Jin taku a bayanta, hakan ne ya
dawo da ita daga duniyar tunanin data shilla. Idanu ta zubawa Kiddo ganin likita a bayansa. Fuska a
‘d’aure ta masa filatanci don bata son likitan ya fahimci abinda take fa’da… “Baka da hankali ne Moddi,
tona mana asiri kake son yi? To ba zai duba ta ba ka ja shi ku koma, tun kafin ranka ya b’aci. Oo walla
hakki…” ta cigaba da masifa da filatanci. Moddi dai yana jinta bai ce komai ba, ya ja hannun Doctorn
suka fice. Sai da taga fitarsa sannan ta ja ajiyar zuciya tana jin yarda zuciyarta ke zafi. bedroom D’in ta
koma suka sake fitowa da Amani da take taku a hankali. Sashen Didi suka shiga daf da asuba. Didi na
kwance ta dinga bin Amani da kallo kafin ta lumshe ido ta d’aga hannu alamar tana kiran Amanin.
Amanin ta k’arasa wajenta ta shige jikinta. A tare suka saki ajiyar zuciya da Didin suka kuma saki kuka a
tare. Didi ta dinga Shafa mata kai tana furta “Ki yi hak’uri kin ji Magajiya, sannan kuma ki yafewa
Moddibo duk da bai cancanci yafiyar a wajenki ba, na San da ciwo Amma don Allah kada ki fitar da
wannna sirrin don fitarsa kamar tonuwar sirrin ki ne, don Allah ki rufa mana asiri ki rufawa kanki asiri…”
Ama kuka Kawai take tana jin zuciyarta na zafi. Me yasa Didi zata ce kada ta fitar da wannan sirrin? Me
yasa bata son ta tonawa Moddi asiri? Akwai adalci akan hakan? Ita bata k’i ta tona asirin ba abu guda ne
ta San ba zata samu Mijin aure ba to sai me? Dama ita bata jin zata yi aure a duniyar nan. Fateemah ta
zauna a gefenta itama. Hannayenta ta kama ta saka cikin nata tana matsa su a hankali. “Ba wai don
Moddi muka ce ki rufa wannan maganar ba, sai don kan ki Ama.” Ta fa’da cikin murya mai cike da sanyi.
“Ki rufa mana asiri yarda daga ni sai ke sai Moddi Safna, Didi da Iman ne muka San maganar nan to don
Allah ki barta a iya mu ‘din, hakan shine alheri a wajenki.. kin ji My daughter?” Amani ta ha’diye wani abu
da ya tsaya mata a mak’ogaro kafin ta sake sakin kuka, bata jin har abada zata iya rufawa Moddi asiri,
dole sai ta sanar da duniya waye shi? Uban da ya yiwa y’arsa fya’de saboda son duniya. Fateemah ta
kwantar da ita a saman gadon Didin bayan ta tilasta mata shan maganin pain reliever. Shiru ta yi kawai sai
dai ba barci take ba, sak’a da warwara zuciyarta kawai take mata. Kiran sallahr da ake ne ya saka su Didi
mik’ewa daga zaman jigum da suke suka fara shirin sallah. Sai itama ta samu kanta da tashi ta yi
sallahr….
Yana idar da Sallah ya nufi sashen Didi. Fuskarsa fayau kamar Wanda ya tashi daga zazzab’i. Fargabar jiya
ce kawai ta saka idanunsa suka fa’da ciki. A hankali yake taku hannunsa rik’e da counter yana matsawa a
hankali. Ya yi sallama cikin k’asa da muryarsa kafin ya tura k’ofar ‘dakin. Da sauri Amani ta runtse idonta
bata son ganinsa sam. Didi ma ‘d’auke masa kai ta yi, ta cigaba da laziminta tana fatan Allah ya rinjayi
zuciyarta daga tarin fushin da yake cikinta kada ta yiwa Moddibo baki. A kasalance ya zauna a k’asan
carpet d’in. Idanunsa a k’asa ya hau furta “Mun tashi lafiya Didi?” Shiru Didi ta yi, tana hak’ilo da
zuciyarta wajen ganin ta togace kanta daga samba’da wa Moddin zagi. Ya sake maimaitawa still bata
amsa masa ba har sai da Fateemah ta ji tausayinsa ta ce “Didi yana gaishe ki?” A fusace Didi ta ce
“Fateema kada kice min kina goyon bayansa? Kada kice min tausayinsa ki ke?” Fateema ta hau girgiza kai
“Ko ka’dan Didi, ai girman laifinsa ba zai bari a ji tausayinsa ba ko ka’dan, ai aikin gama ya riga ya gama sai
dai ai fatan Allah ya kiyaye na gaba…” Kallon Didi ta zuba mata ne yasa ta yi shiru sai kuma taga Didin ta
mik’e idanunta jajir a kansa ta furta “Moddibo!” Da sauri ya ‘d’aga kai yana mamakin Amon muryar da
tayi amfani da shi wajen kiran sunansa…. Bai san sanda ya samu kansa da furta “Ki yi hak’uri Didi….”
Kallon da ta masa ne yasa shi ha’diye sauran maganarsa. Kallo ne mai nuni da garga’di gare shi, a idanun
Didi yake hango yarda take jin haushinsa. Muryarta a fisge ta ce “Ba zan maka baki ba Moddi, ba zan ce
jeka ka gani ba, zan maka addu’a Allah y’a shiryeka, Allah ya dawo da kai kan tafarkin sira’dil Mustak’ima.
Amma ba zan iya zama a gidanka ba, ba zan iya zama inuwa guda da kai da matarka ba, zan tafi zan tafi
zan koma gida na idan ba ina so zuciyata ta buga ba ne, sai dai zan gaya maka zan aurar da yaran nan zan
aurar da marayun Allah, tun kafin mutane su farga su k’i aurensu, kuma tare da su zan tafi. Allah ya
shiryeka shine kawai addu’ar da zan maka.” Ta fa’di tana k’ok’ari sosai wajen ganin k’wallar ta bata zuba
ba. Moddi kasa cewa komai ya yi, to me zai ce? Yana kallonta ta fara shirya kayanta. Ya runtse idonsa
kawai yana son yi mata magana, irin maganar da zata kwantar mata da hankali, amma harshensa ya gaza,
Ya kasa bashi ha’din kai don haka kawai sai Ya kifa kansa a hannun kujera ya yi shiru kawai. Fateemah ce
ta katse shirun nasu ta hanyar furta “Amaryarsa fa Didi? Amaryar da aka ‘d’aura musu aure? Yaushe zata
tare?” Didi ta gintse fuskarta tana nuna Fateemah da yatsa ta furta “Ki shiga hanaklinki Fateemah, ki
kuma fita hanyata matuk’ar maganr Moddi ce zata ha’da ni da ke, bana so bana so ki sake jefa ni cikin
zancen Moddibo, Ya je ya yi abinda yake so, Ya aikata abinda duk abinda yake so, na daina ba shi umarni
tunda ba bin umarnin nawa yake ba.” Shiru Fatima ta yi bayan ta furta “Ki yi hak’uri Didi.” Moddi kuma ya
mik’e waya a kunnensa. Basu San me yake cewa a wayar ba don muryarsa ta yi k’asa da yawa. Fateema
dai ta bi shi da kallon k’asan ido, gefe guda na zuciyarta na jin wani irin tausayinsa.
A bedroom d’inta Ya sameta. Tana zaune hannayenta zube a k’uncinta. Ta d’ago tana kallonsa da sauri ta
janye idonta don ba zata jure kallon birkitattun idanunsa ba, Sun canja sun zama wata kala daban mai
razana zuciya… taku Ya yi na k’asaita ya shiga cikin ‘d’akin sosai. Idanunsa a kanta ya furta “Burinki Ya
cika ko? Sai ki gaya min kuma next abinda zan yi, bana son maganar nan ta fita, ba kuma wai ina rok’onki
ba ne, Aa umarni nake baki, idan kuma kin k’i…” sai ya ciza leb’ensa ba tare da ya furta komai ba. A
fusace Safna ta ‘d’ago tana kallonsa “Idan na k’i me? Na ce idan na k’i me zaka min Moddibo? Saki na za
ka yi ko? Na San shine abinda kake so….” Sai ta tuntsire da dariya “Saki na shine abu na k’arshe da zaka yi
regretting ‘d’insa a rayuwa