Chapter 23 Reading HADARIN GABAS Cin Amanar Iyali by Nazeefa Sabo Nashe READ HAUSA Novels

HADARIN GABAS Cin Amanar Iyali by Nazeefa Sabo Nashe

Author :  Nazeefa Sabo Nashe Category :  African Stories & Novels

Chapter   23 / 28

66K to 69K   out of 82.1K words

bayan an d’aura ya gudu bayan ya yiwa matar saki guda.
Don haka ta dinga kallonsa, kallon da Har sai da Ya saka ya yi k’asa da kansa, a hankali ya furta “Ba zan
fasa ba Didi, ba abinda kike tunani bane.” Sai ta sauke ajiyar zuciya kafin wani murmushi ya bayyana a
fuskarta. Da gaske ta San wannan karan Moddi ba zai watsa mata k’asa a ido ba.. hankalinta ya kwanta, ta
dinga kallon su Fateema da suke tattara kayansu da na yaransu suna mata sallama. Idonsa a lumshe yake,
sam hankalinsa baya kansu yana can wata duniya da Ya yi zurfi a cikin tunaninta… sai da Fateemah ta
dafa shi ta ‘d’an yi magana da k’arfi a kunnensa. “Kiddo mun tafi, saura kuma ka je ka gayawa Safna
k’anwar Didi zaka yi aure..” Bai bu’de idon ba, balle ya bata amsa, alamun y’an miskilancin na kusa, idan
yaso haka yake sai ya cije ya k’i magana musamman idan zuciyarsa bata cikin sukunin yin

Maganar. Shafa gefen kumatunsa ta yi, sai kuma ta

Ja hancinsa tana furta “To Uban miskilanci, saduwar alheri.” Ya d’an murmusa kawai ba tare da ya bu’de
idonsa ba. Ya furta “Akwai sak’o a account d’inki, share it with Your sister’s” Ta k’asan ido yake kallonsu
duk suna ficewa…




Har ta kai k’ofa ta tuna bata yi sallama da su Amani ba. Sai kawai ta dawo zuwa ‘dakinsu na b’angaren
Didin. Jin kamar suna magana k’asa k’asa yasa ta tsaya ta lab’e tana jin su. Iman ta ce “Sha biyu na dare za
mu gudu, idan yaso ko garin su Mahmeey sai mu je.” Fateemah ta waro ido, kafin ta tura k’ofar ta shiga
da sauri suka ‘d’ago suna kallonta sai kuma suka sunkuyar da kai. Akwatin gaban Imaan ta kalla sai kuma
ta kallesu d’aya bayan d’aya gabanta na fa’duwa ta furta “Guduwa za ku yi?” K’asa suka yi da kansu. Jikin
Fateemahn a sanyaye ta zauna daf da su. Nasiha ta dinga musu da alk’awarin ba abinda zai faru In sha
Allah. “Moddi ba mahaukaci bane, na San ko giyar wake ya sha ba zai aikata muku komai ba.” Imaan tana
hawaye ta labarta mata komai. Wani irin waro ido ta yi a gigice ta mik’e ta koma parlorn Didin, da wani
irin duba take kallon Moddi Kfin ta furta “Imaam kana cikin hankalinka kuwa? Didi kin san abinda yake
shirin aikatawa?” Da sauri Ya kalleta a idanunta Ya hango da gaske abinda duk ta sani zata gayawa Didi, Ya
runtse idonsa kawai…..



Free pages Saura few pages fa! Ku hanzarta samba’do ku’dinku. 2118666253 UBA




JIKAR NASHE★ ✍️HADARIN GABAS…..👌
29.




NAZEEFAH SABO NASHE



08033748387.




BRIGHT PENS SECOND BATCH



Idanu ya sake warewa ganin Fateemah har ta fice daga parlorn ba tare da ya san me suke tattaunawa ba.
Ya sake lumshe idonsa ganin Didin kawai ta zuba masa ido, sai yaga kuma ta mik’e ta nufi d’akin da su
Amanin suke. Tura k’ofar ta yi jikinta a sanyaye ta zuba musu ido. Su ‘‘d’in ma kallonta suke. Ta zauna a
gefen gadon tana kallon akwatinansu sai ta saki murmushi kawai, murmushin da su Amani suka ‘dauka
na mamakin abinda zasu aikata ne. “Za ku gudu saboda Didi ta Gaza a wajen baku kulawa ko? Za ku gudu
saboda k’una tunanin zan iya bari a cutar da ku ko ni na cutar da ku ko?” Sai ta girgiza kai ta furta “In dai
ina raye ku saka a ranku ba abinda zan bari ya cutar da ku, ina son ku ina tausayin maraicinku.. ku k’ara
min lokaci komai yazo k’arshe, na san kuna da matsala Fatima ta gaya min komai, ina kuma kan bincike
akan abin duk Wanda yake da saka hannu a ciki Allah zai yi maganinsa. Komai yazo k’arshe Moddibo zai yi
aure jibi, da matar da nake tunanin ita zata zame masa alheri a rayuwarsa, matar da zata so ku taso mu ta
kuma sake dunk’ule zumuncinku waje ‘daya.” Farin ciki ya cika zuciyarsu gaba d’aya suna jin a ransu
kamar da gaske duk wata matsalarsu ta zo k’arshe. “Kada ku k’ullaci Babanku, bashi da laifi ko ka’dan son
zuciya ne ya shigo cikin lamarin… ku yi hak’uri kun ji.” A wannan gab’ar dai Imaan ta jita kawai ba don ta
yarda da abinda ta ce ba, saboda da kunnuwanta ta ji abinda Dadan yake fa’da a waya. Sai kawai ta ja
ajiyar numfashi ta sauke tana kallon idon Didin da itama ta zuba mata ido, tana son ta gayawa Didin
komai sai dai bata San ta inda zata fara ba, maganar ta girmi kwanyarta. Didi ta shafe kansu ta sake fita.
Iman kallon Amani take da idonta suke lunshe sai kawai ta samu kanta da Shafa gefen fuskarta Amanin ta
Ware ido tana kallonta a hankali ta furta “Menene?” Amanin ta girgiza kai kafin ta furta “Bakomai.” Duk
da akwai komai ‘din wani irin zafi take ji a zuciyarta Wanda ta tabbatar na Kishin Dada ne, sai dai tana
fatan aurensa ya zama silar yayewar matsalarta.




Haka aka dinga shirin biki gadan gadan ba tare da Sun bari Safna ta sani ba. Sai dai a ranar ta fahimci
abinda ake shirin aikatawa don da tashin hankalin da take ciki yasa bata Saka ido a kan mutanen gidan
ba, mafita kawai take nema. Mafitar da zata wargaza kwanciyar hankalin zuri’ar Lami’do ta saka musu
firgici da b’acin ran da ba zasu tab’a mantawa da shi ba. A zaune take gefen gado hannunta rik’e da robar
rubutu ta tsurawa rubutun ido tana d’an murmushi k’asa k’asa. A hankali ta furta “Da gaske komai yazo
k’arshe kamar yarda Malam ya ce..” Sai kawai ta saki wata irin mahaukaciyar dariya… daidai lokacin
wayarta ta dinga ringing ido ta zubawa wayar tana jin wani irin matsananciyar fa’duwar gaba. Hannu na
rawa ta saka ta ‘d’au wayar ganin sunan Alwan da ya bayyana b’aro-b’aro a screen ‘D’in wayar. Tsinkewar
gabar da ta samu kanta a ciki ne yasa bata San wayar ma Upside down ta rik’e ta ba. Sai da ta ji muryar
Alwan yana furta “Kin kasa cika mana aikinmu, ga Mijin da kike so kamar ki Mutu yau ya miki Kishiya, yau
an ‘d’aura auren Mijinki d……” wani irin waro ido ta yi tana jin wani irin zafi tun daga k’asan zuciyarta
Har gangar jikinta. A razane ta ce “What?” Alwan Ya saki murmushi yana furta “Da gaske ya yi aure,
mahaifiyarsa ta masa auren Sirri, idan kina son kuma ya rabu da matar sai kin aikata abinda muke so, ki
saka ya kusanci yarinyar can ko ba ya so, ki yi musu vedio kice idan har bai rabu da matar ba zaki tona
masa asiri zaki saki vedion kowa ya san waye shi?” Murmushi ta saki wata irin nutsuwa tana shigarta.
Tabbas wannan ce shawara dama ko ba’a yi haka ba tayi niyyar ta saka ta tilas ya kusanci Amani don ta
b’ata musu rai kamar yarda suka saka tata zuciyar ciwo. Alwan ya katse wayar ya barta da tata wayar a
hannu. Da k’yar ta zame wayar daga kunnenta. Ta tuna a yau tana da damar da Imaam zai kusanceta sai
ta saki jin da’di a ranta,don a yau ne zata yi amfani da maganin mak’ale mata da Malam ya bata. Ya kuma
tabbatar mata in dai Imam d’in ya kusanceta ba zai sake marmarin wata mace ba da sunan aure… “Zan
yi amfani da maganin amma sai na gama da wannna matsalar.” Ta furta kanta tsaye. Wanka ta shiga tana
jin ba wani b’acin rai tare da ita duk wani shiri ta gama shirya shi a zuciyarta.
Ta gama wankan sannan ta shirya ta shiga kitchen. Favorite dishes d’in Didi ta dafa a gidanta su Mama
Talatu suna tayata cike da mamakin sauyawarta, ko dai bata son abinda ake ba ne a gidan.” Mama Talatu
ta fa’da k’asa k’asa tana kallon Inna Laraba bayan Safnan ta shiga store da yake cikin kitchen ‘din. Suka yi
shiru ganin ta fito still fuskarta cike da walwala tana kallonsu ta umarcesu su kwashi abincin su biyota
parlorn Didi da su. Haka kuwa aka yi Didi sai gani ta yi suna jera abincin a babban Dinning area d’inta da
Yasha adon carpet mai taushin gaske da pillows manya. Don Moddi bai saka mata Dinnig table ba ya san
bata so sai ya saka mata wani table irin na k’asan nan sosai Mara tsaho. Cikin mamaki Didi take bin Safna
data zauna a gabanta da kallo. Murmushi Safnan ta yi sai kuma ta sunkuyar da kanta idonta yana tara
k’wallar da ta k’irk’iro ta k’arya. Murya a k’asa sosai ta shiga bawa Didin hak’uri “Don Allah Didi ki yafe
min, In sha Allah ba zan sake aikata abinda duk na aikata a baya ba, na yi nadama kuma ina neman
afuwarki data yaranki Har ma da Moddi da y’ay’ansa gaba d’aya.” Didi cike da mamaki take dubanta ita ba
yarinya bace ta San wannan tuban na Safna bana gaskiya ba ne, da wani abu a k’asan ranta ba mamaki
yaudara ce ko kuma ta ji labarin auren Moddi take son ruguza shi ta hanyar makirci. Sai kawai ta saki
murmushi itama in dai Makirci ne gidan ta tarar yaushe aka haifi Safnan su da aka haifa zamanin da
makirai ma suka fi yawa, ba yanzu ba da mutane basu da wayon iya makircin ba ma. Hannu ta saka ta
dafa kanta tana sakin murmushi ta furta “Ai haka ake so Safna, tashin hankalin ai bashi da rana, Allah ya
yafe mana gaba d’aya. Wannan abincin dai yau ba zai ciwu ba don duk muna azimin Alhamis.” Safna taji
zuciyarta ta wani irin bugawa duk ku’din da ta kashe cikin abincin na asirin data zuba a cikinsa Sun tashi a
banza kenan? Kai ina wallahi da sake. Sai ta saki murmushi tana furta “Ai ba zai yi komai ba zuwa yamma
sai a yi muku warming ‘d’insa ku sha ruwa da shi, amma shi Moddin ai baya azimi.” “Shima yau ya
‘dauka.” Didi ta furta tana k’ok’arin danne dariyar da take ranta. Ta k’yale Safna a zuwan za’a ci abincin da
daddare.



Daga wajen Didi ta nufi sashen Moddibo, zuciyarta duk ba da’di wani irin zafin Moddibo take ji. Wato ita
zai yaudara ai kuwa zai sha mamaki. A zaune yake laptop a gabansa. Kallo guda ya mata Ya ‘d’auke kai. Ita
kuwa sai da numfashinta yaso d’aukewa tsabar kyau da taga Moddi ya yi cikin black shirt da farin wando.
Gashin kansa ya sha gyara sosai. Ta k’arasa kusa da shi tana nazartar yanayin parlorn da yake a gyare
tsaf-tsaf As usual Moddi baya son k’azanta ta sani don haka komai nasa yake zama very neat. So take ya
kalleta sai dai tun kallo gudan da Ya mata bai sake ba yana ta aikin tapping computer. Sai da ta gyara
muryarta wajen son k’wato tunaninsa da sanyin muryarta ta da take tunanin ta siranta sannan ta furta
“Wajenka na zo Imaan, I need your concentration….” Bai kalleta ba ya furta “All ears….” Ranta ta ji ya
sosu ganin abinda yake mata, Wanda da bai isa ba, bai isa ta yi magana ya shareta ba. Amma sai ta cije ta
daure b’acin ranta ta furta “ka yi hak’uri na amsa duk laifi na ina rok’on yafiyarka please!” D’ago kansa ya
yi yana kallonta sai kawai ya ‘dan saki murmushin gefen lips ya ja bakinsa ya yi shiru. Cak ta mik’e ta isa
gefensa ta shiga jikinsa a hankali ta furta “Da gaske nake, na yi regretting all my wrongs kuma ba zan sake
ba In sha Allah…” cikin idanunta yake kallo yana mamakin jin kalaminta, anya kuwa ta San irin laifin da
yake shirin yi mata. Sai kawai ya kama hannunta ya sumbata ba tare da ya furta komai ba ya mik’e ha’de
da d’age laptops d’insa daga wajen. “Ga abinci a parlorn Didi na kawo muku…” “Azimi” ya furta cikin
husky voice d’insa sannan ya shige d’akinsa. Bakinta ta cije sai kuma ta saki murmushi “Zaka dawo daidai
ne Imaam, zan baka mamaki.” Komawa ta yi parlorn Didi ta zauna ta sake a cikin su har tana jan Imaan a
hirar don kam bata ga fuska wajen Amani ba. Imaan ‘din ta dinga amsa mata a ‘darare don tsoron Safnan
take ji kamar yarda take tsoron ranta. Ban da Allah ya kiyaye tana dagewa da addu’a da tuni ta sakata a
mummunar hanya bata San me yasa a yanzu ma Safnan ta janye makaman yak’inta ba.




K’arfe shidd ta k’irk’iri ciwon cikin k’arya bayan da ta tabbatar ta aikata abinda take so successfully… Ba
wanda ya kawo komai Didi ta ce su tafi asibiti da Imaan. Suna zuwa asibiti Doctor ya tabbatar musu sai an
yi admitting Safnan. Iman taso guduwa gida Amma Safnan ta rik’e hannunta tana furta “Why? Idan kika
tafi wa zai zauna da ni, ki bari drip ‘din ya k’are mu tafi tare.” Haka Imaan ta hak’ura ta zauna ba don
ranta yaso ba.




Suna zaune a parlorn Didin Amani ne da Didin kawai. MODDI ya shigo sai ‘daukan ido yake fuskarsa cike
da walwala ya zauna a kujerar da take gefen Didi. Yana kallon Amani da take zaune tana kallonsa cike da
fa’duwar gaba. Wani irin take ji a duk sanda suka kusanci juna. Didi da farin ciki ta furta “Alhamdulilah Ya
ka baro amaryar?” Ya cire hularsa yana jingina da kujera idonsa a lumshe murmushin fuskarsa ya kasa
d’aukewa Ya furta “Tana gaishe ki, da kowa ma.” Amani taji zuciyarta kamar ta tarwatse don haka ta mik’e
kawai zata wuce Moddin ya ce “Ama…” ta juyo jin ya ambaci sunanta ledar hannunsa ya mik’a mata sai
kuma ya mik’awa Didi tata. Daga haka ya mik’e ta gefen Amanin yazo zai shige ya furta “Koma ki zauna,
Dodon naki ya tafi.” Duka jikinta ta ji wani irin yarrr jin yanayin sound ‘din muryarsa. Ta rik’e ledar a
hannunta kafin ta zauna cikin mutuwar jiki. Didi tana kallonta ta furta “Alhamdulillah yau buri na ya cika
Moddi Ya auri kamilar mace wallahi. Baki ganta ba.” Amani ta ‘d’an cije leb’e kawai. Didi ta saki tsaki “Wai
Uban me aka miki ne yau nake ganinki sukuku, ina lura koda aka sha ruwa ba wani abin kirki kika sha ba,
wuce ki je kitchen akwai fura a fridge dana dama Miki don na San ke gwanarta ce ki ‘d’auko ki sha a gaba
na.” Amani ba don tana so ba, sai don tana son Didin ta daina mata hayaniya a kai ta samu kuma ta barta
ta huta yasa ta shiga kitchen ‘din ta ‘d’auko furar ta kawowa Didin. Didi ta zuba a cup ta mik’a mata tana
janyo ledar da Dadan Ya bawa Amanin taga nama ne mai zafi sai Icecream a ciki da fresh milk. Ta furta
“To maza ki zauna ki sha komai, haba yarinya duk kin bi kin fige…” Dole Amani ta dinga turawa a cikinta,
komai ciki take yi cikin rashin kwanciyar hankali. Didin ma ta ja nata tana ci kaza ce da yoghurt. Amani dai
bata San ta kusa shanyewa fresh milk D’in ba ko don da gaske tana jin yunwa ne. Ta ajiye tana kallon Didi
ta mik’e “Zan je na yi freshen up na kwanta.” Didi ta fara kallonta da dishi-dishin idonta da take jin wani
irin masifaffen barci ta ‘daga mata kai. Tun kafin Amani ta kai ‘d’aki Didi ta mik’e ta shige nata d’akin
tsabar barcin da yake idonta. Amanin wanka ta yi ta kwanta rigingine tana jin yanayin da take ciki yana
sake k’arfi. Ta runtse idonta da k’arfin gaske tana hango Dada tana kuma jin muryarsa a kunnenta kamar
yarda ya saba zuwa mata a barci. Abu fa Ya fara zafi ga wani irin yanayi da take ciki kamar mai maye, ta
runtse idonta tana imagining abin wani irin feeling Mara misali take ji, a yanayin mayen ta mik’e daga ita
sai b’ingilar rigar barcin da take jikinta ta fice daga sashen Didin zuwa sashen Dada, ta ‘d’an walkway ‘din
da yake hanyar da zata sadaka da sashen Moddin…. Cikin mayen ta tura k’ofar parlornsa tana tafiya cikin
wani yanayi kamar ba ita ba ta shiga bedroom ‘d’insa. Jin ta take kamar a mafarki ba abinda take so irin
jinta a jikin Moddi yana aikata mata abinda take imagining bata cikin hayyacinta kamar yarda bata San
sanda ta kai kanta gadon ba ta kuma shige jikin Moddin…….




JIKAR NASHE★ ✍️HADARIN GABAS…….👌


NAZEEFAH SABO NASHE★ ✍️


08033748387.




BRIGHT PENS SECOND BATCH




30.
Cikin wani irin hali da shi kansa ya kasa controlling kansa gangar jikinsa da zuciyarsa. Ruhinsa gaba d’aya
baya tare da shi, kamar a maye yake kamar kuma a buge yake a haka komai ya kasance, k’addarar
kusantar junansu a daren ta afku, cikin wani irin hali da su kansu basu sani ba, idonsa ya rufe burin juna
kawai suke…. Sai da ta ji shigarta jikinsa ya bu’de kuma abinda kowace budurwa ke alfahari da shi,
Sannan ta sake fita daga hayyacinta. Wani irin barci mai nauyin gaske barcin da su kansu basu San yaushe
ya ‘d’auke su ba…




A gadon asibitin wani irin fa’duwar gaba ne ya samu Safna. Ta dafe k’irjinta tana karanta addu’oin da ita
kanta ta san da wuya Allah ya amsa mata. Tana tare da tarin manyan laifukanta. Ta sani mai afkuwa ta
afku, ta cika burin Alwan gefe d’aya tana tunanin nata burin ya cika. Burin mallakar Imaam Moddibo,
ruhinsa dukiyarsa. Zata juya shi son ranta sannan zata yi amfani da wannan damar wajen threatening
danginsa. Ta lumshe idonta tana jin zafi a k’asan ranta Wanda ba na komai ba ne sai na tsananin kishi.
Yau Imam ya kusanci budurwa Ya ji d’and’anon budurwa zai gane tarin banbancin da yake tsakanin
budurwa da bazawara. Sai ta dinga jin wani d’aci a ranta. A zafafe ta fisge ledar drip ‘din da yake
hannunta sannna ta mik’e, idanunta akan Imaan da take zaune itama duk ta rasa nutsuwar, wani irin
firgici take ji a ranta. Ta kira wayar Amani yafi a k’irga ba ta ‘daga ba, ta kira Didi itama shiru. Ta kira
Umma Talatu ta tabbatar mata komai da kowa lafiya, kuma Didi Sun kulle sashensu balle ta kai mata. Sai
ta mayar da kiranta kan Dada shima still bai ‘d’auka ba. Haka ta gaji ta zubawa wayar ido tana jin fa’duwar
gabanta na sake k’arfi. “Tashi mu tafin da Safna ta furta shi ya dawo da ita cikin hayyacinta ta Ware
idonta kafin ta mik’e a hanzarce, don tafiyar ita tafi buk’ata, wannan yanayin da take ciki ba zai zama
bakomai ba, dole akwai abinda yake faruwa Wanda ba ta fata mummunan mafarkin da ta yi ya zama
gaskiya. Idan kuwa hakan ta faru bata jin zata yafewa Dada da Amanin kanta. Jiki a sanyaye take bin Safna
da take tafiya da k’arfinta kamar ba patient ba da kallo. Sai ta samu kanta da k’aryata ciwon Safnan…
zuciyarta ta tsananta bugu tana fatan ba wata kitimirmira Safnan ta shirya

23 / 28