Chapter 20 Reading HADARIN GABAS Cin Amanar Iyali by Nazeefa Sabo Nashe READ HAUSA Novels

HADARIN GABAS Cin Amanar Iyali by Nazeefa Sabo Nashe

Author :  Nazeefa Sabo Nashe Category :  African Stories & Novels

Chapter   20 / 28

57K to 60K   out of 82.1K words

kasa fin k’arfin zuciyata ne….” Didi
ta dinga kallonsa idonta na zubar da hawaye sai kuma ta saka hannu tana share hawayen tana furta
“Allah na yafe masa, Allah kai ma ka yafe masa. Ubangiji ka shirya min shi….” Kifewa Moddi Ya yi kawai
yana saka kuka… jikinsa Har kakkarwa yake ya ji ya tsani kansa, me yasa shi ka’dai ne namiji shine kuma
yake son zama raunin mahaifiyarsa. Carbi ta mik’a masa tana furta “Ka yi ta jan Istigafari ba adadi, ka
kuma saka a ranka ba zaka kuma ba, sai Allah ya yafe maka, abu guda da zan gaya maka ba zan amince ka
auro min ita ba, don tabbas zata iya zame mana BARAGURBI. Bana son ka sake komawa wajenta, ka min
wannan alk’awarin Moddi. Kun aikata zina ko?” Ya cije leb’ensa yana d’aga mata kai. Sai kawai ta girgiza
kai tana furta “Allah ka taya ni kiwonsa, ka bashi mata ta gari da zata zame mana sanyin idaniya. Tashi ka
cire kayan jikinka ka kuma fita da su ka bada kyautar su don ba abinda suke sai k’amshin Humra da Ya
cak’ude da turarukan Bori.” Moddi Ya mik’e Didi ta bi shi da kallo tana sakin ajiyar zuciya tana kuma yarda
kayan suka yi Squeezing sai sannan ta dinga jin wani irin zafi a zuciyarta sai dai ta dinga dannewa bata
son ta sake zubar masa da hawaye balle Allah ya yi fushi da shi.
Kayan ya cire yana jin shima zafin a zuciyarsa amma sai dai me? Da zarar ya rufe ido Safna yake gani ba
kaya abin ya zauna daram a ransa. Ya rasa sukuni sai dai yana k’ok’arin rik’ewa Didi alk’awarinta bai sake
zuwa wajen Safna ba, bai sake nemanta a waya ba ko ta kira ba ya ‘dagawa. Sai ga vedion ta turo masa a
wane dare. Ya dinga kallon vedion yana jin takaicin abinda ya aikata a vedion ga Safna da ta manne masa
a rai take wahalar da shi…. Amma hakan ya dinga cijewa Don Didi kacokam ta mayar da shi parlornta
suna kwana tare. Cikin dare haka zata gan shi yana juyi cikin barci hannunsa dafe da mararsa yana ihun
kiran Safna. Anan Didi ta san sunanta ta kuma tabbata Safna ba haka ta bar mata yaro ba…




Hankalin su bai sake tashi ba, sai da Fateemah tazo mata da abinda ya dugunzuma zuciyatta ta kusa
bugawa. Suna gaisawa Fateemah ta kalleta ta kalli Moddi kafin ta cije bakinta ta ce “Didi, Moddi Ya ‘debo
ruwan dafa kansa, dole ya auri Wannan yarinyar Safna. Don ta turo min vedion da Ya dugunzuman
zuciya. Kiddo Har ya san ya je ya kusan ci mace? To ta rantse min idan bai aureta ba sai ta saki vedion nan
duniya ta gani. Za kuma ta ce fya’de ya

Mata…..” Moddibo runtse idonsa kawai Ya yi yana tunanin vedion kada Allah yasa Fateemah ta nunawa
Didi, sai dai addu’arsa bata amsu ba don hango waya ya yi a hannun Fateemah tana k’ok’arin nunawa
Didi….




JIKAR NASHE★ ✍️HADARIN GABAS……👌


25.



NAZEEFAH SABO NASHE★ ✍️
08033748387.




Da wani irin hanzari ya cafki hannun Fateeman, ya damk’i wayar da take k’ok’arin nunawa Didin.
Fateemah ta wurgeshi da wani irin kallo kafin ta ciji baki tana furta “Ashe har yanzu da sauran kunya a
tare da kai? Ai da sai ka bari na nuna mata irin ba’dalar da kake yi.” Ya girgiza Kai idanunsa suna kawo
ruwa yana Jin Kansa kamar ya buga tsabar yarda ya masa nauyi. Duk iskancinsa ba zai so Didi taga
wannan vedion ba. Haushin Safna ya cika masa zuciya ya dinga jin zuciyarsa na wani irin tafasa. Didi ma
tashin hankalin ta shiga don a idanunta ya hango hakan. Sai dai bata bari hakan ya rinjaye zuciyarta ba,
balle ta sakar masa kalaman da zasu sake lallata shi. Sunan Allah kawai take ja a zuciyarta. Sunkuyar da
kai ya yi yana Jin gaba d’aya duniyar ta masa k’unci da zafi. “Tashi ka fita Imam.” Shine abinda Didi ta ce
don ganinsa yana sake hauhawar fushinta. Kamar Wanda yake jira da sauri ya mik’e ya fice da sauri don
hakan sai ya masa daidai. Kallo Didi ta bishi da shi. Kafin ta girgiza Kai ita ka’dai ta San maganin abin za
kuma ta yi shi nan kwana kurkusa ko ta huta da ganin takaicin Moddibo.




Yana fita bai zame ko ina ba sai gidan su Safna. Tunda ta fito ya ji zuciyarsa ta yi wani irin sanyi. Fa’dan ma
da ya yi niyyar zuba mata ya ji ya kasa. Wani irin soyayyarta mai zafi ce take fisgarsa. Murmushi ta sakar
masa ha’de da turo bakinta alamar kiss sai kuma ta hau waige waige ganin ba kowa sai kawai ta yi saurin
rungumarsa tana ja baya ta furta “I missed you dear, kawai kuma sai ka guje ni bayan ka gama jiyar da ni
da’dinka.” K’arfin hali ya yi ya tattaro dukkan nutsuwarsa ya gyara zamansa yana fuskantarta. Cikin
muryar da ta bayyana rashin wasa ya ce “Safna Why? Me yasa kika aikata abinda kika aikata?” Gira guda
ta d’aga masa sai kuma ta saki murmushi tana furta “Me na aikata Dear?” Ya sake tsare girarsa sosai kafin
ya ce “Vedion da kika turawa Tee, a ina ma kika samu numberrta?” Sai da ta yi dariya mai ha’de da
shashshek’a sannan ta yi k’asa da murya tana furta “A duniya na samu Imaam, na ga idan ba haka na yi ba
shirin gudu kake ka bar ni, ni kuma na shirya aurenka duk da ina ji a girme na girmeka da shekara guda,
amma haka zan aureka don ina son ka, ka yi min kai ne maha’dina. Na San dai zan sha fama a gida kafin a
amince na aureta Amma na amince zan d’au duk wani challenges matuk’ar zan cika buri na…” Kallonta
kawai yake kafin ya saki ajiyar zuciya har ta gama zubar ta sannan ta ‘d’ago tana kallonsa. “Ka amince za
ka aure ni?” Ta fa’da tana Kama hannunsa. Wani irin lumshe ido ya yi bai San sanda ya d’aga kai ba. Yana
furta “Sure..” wani irin ihu Safna ta saka bata San sanda ta kai masa Sumbata a baki ba… tana furta “Yes
wo…. Na San dole ma zaka amince.”
Sai da ya ‘d’au hanyar gida sannan ya dinga Jin kamar shawarar da ya yanke na amincewa Auren ta bai
dace ba. Kamar ya yi azarb’ab’i don wannan hurumin Didi ne. Amma sai ya samu kansa da rashin ganin
kuskurensa. Hakan ne ya dace. Safna ce zab’insa ita kuma ta dace da tsarin rayuwarsa…..




Sai dai bai san me su Didi suke shiryawa ba. A safiyar ranar Didi ta shigo d’akinsa hannunta d’auke da
dakakkiyar shadda fara k’al. Babbar riga da y’ar ciki da suka sha aikin har da hula da takalmi sababbi. Ta
mik’a masa tana kallonsa. “Tashi maza, ga ruwan wanka can Fatima ta saka maka a ban’daki.” Da sauri ya
dubeta yana kallon kayan hannunta. “Ina zamu Didi?” “Unguwa.” Ta furta masa kanta tsaye. Ganin
fuskarta ba yanayin wasa yasa ya mik’e ya nufi toilet d’in. Mamaki ya Kama shi ganin y’an uwansa duka
cike a gidan su da yaransu. Ya tab’e baki yana tunanin taron na menene ake yi? Wankan ya yi ya kuma
shirya tsaf cikin babbar rigar da ta masa kyau sosai ta sake fito da k’imarsa ta namiji cikakke duk da
yarintar fuskarsa bata b’uya ba. Yana fitowa suka saka masa gu’da a Kai. “Ma sha Allah ka ga angon y’ar
riga. Allah ya tabbatar da alheri yasa a ce gwara da aka yi…” Cak ya tsaya da numfashinsa yana zubawa
Jay ido cikin wani irin firgita ya ce “Y’ar riga kuma?” “Eeh, Y’ar riga In sha Allahu yau za’a d’aura muku
aure da ita, ita ta dace da kai. Na tabbata ba zata raina abinda Allah ya bamu ba…” Zuciyarsa ta dinga
wani irin bugu….




Yanzun ma bugun zuciyar tasa take yi. Musamman da Didi ta ‘d’ora hannunta a saman kafa’darsa hakan
yasa ya dawo daga tunanin da ya lula. Ya bu’de idanunsa da suke fitar da maik’on hawaye yana kallon
Didin. Itama kallonsa take. Tana furta “Tunanin me kake Moddi?” Ya ja ajiyar zuciya kafin ya girgiza Kai ya
ce “Komai ma Didi.” Didi ta jinjina Kai kawai kafin ta mayar da hoton y’ar riga ta ajiye tana dubansa ta
furta “Goben dai da wuri zaka kawo su Magajiya ko? Don Sam bana son zaman ka’daita. Sannan ina son
ka fita ka samo almajirai da zasu kwana suna saukar kur’ani a gidan nan. Don na lura sosai Moddi
lamarinka sai na dage da addu’a.” Ya jinjina Kai yana furta “Za’a samo Didi.” Cikin muryarsa take Jin wani
irin weakness. Ya mik’e ya fita daga d’akin a hankali. Zuciyarsa kuwa tunanin y’ar riga ne kawai a cikinta.
Yana fatan Allah yasa bata tafi da Jin haushinsa a ranta ba.
Da Kansa ya saka a samo Malamai ya kuma bi shawarar Didi bai gayawa Safna zancen tashin ba, sai a
kashegarin ranar. A d’akinta ya sameta fitowarta daga wanka kenan tana Shafa mai. Ya bita da kallo yana
mamakin wata irin k’iba da take sake yi Sam bata controlling jikinta. Ta ‘daga Kai tana kallonsa kafin ta ja
mayafinta ta rufe jikinta don ita kanta ba zata so ya ganta ba kaya ba. Gaba d’aya halittunta sun canja.
Gefen gado ya samu ya zauna kafin ya sauke idonsa kan ta ya furta “Ki shirya za mu unguwa.” Ta saki
murmushi tana furta “Tom, ka jira ni a waje, yanzu zan fito.” Bai sake kallonta ba ya fice daga bedroom
D’in. D’akinsu Amani ya nufa. Sai da ya yi nocking k’ofar sannan Amani da take tsaye hannunta rik’e da
comb tana taje kanta ta furta “Mama Talatu shigo mana.” Idanunta ya sauka akan na Dada da yake tsaye
yana kallonta da sauri ta janye nata idanun sanda yarda gabanta ya tsananta bugu. Shima janye nasa idon
ya yi yana furta “Ku shirya zamu tafi.” Ta d’an waro ido tana furta “Yanzu kuma Dada? Ai basu gama kai
mana kayan ba.” Bai amsa mata ba ya fice daga d’akin. Ta bi shi da kallo tana sake shak’ar k’amshin
turarensa. Sai kuma ta saki murmushi ita ka’dai tana tab’e baki fa’da take son yi da zuciyarta, amma ta
kasa yarda laifin na zuciyarta ta ne. Sanda Iman ta fito ta gaya mata Dada ya ce su shirya wani irin farin
ciki ne ya lullub’eta ta tsani gidan da duka abinda yake cikinsa, ta tsani Safna, tana fatan komawarsu
sabon gida yasa zasu koma da kowane bak’in ciki ba, banda ma maganar aurensu Didi ta dakatar ita da
zata fi so ta yi aurenta ta huta. Tsaf suka shirya cikin kyakykyawar shiga yau Amani ma hijab ta saka kamar
Imaan. Suka fito parlorn. Safna na ganinsu ta ha’de fuskarta sosai tana jin wani bak’in ciki. Kafin ta kalli
Moddi ta ce “Da su za’a ne?” Madadin amsa mata da baki, d’aga mata kai kawai ya yi. Ta saki wani
k’aramin tsaki tana hararar Moddin k’asa k’asa. Ta lura kwana biyun nan wani Izza yake ji Amma zata yi
maganinsa. Wata irin mota mai masifar kyau shiga. Tunda kuma ya fara driving bai ce komai ba. Baka jin
komai sai surutun Amani da Ya cika motar. Zuciyar Safna a tunzire take da Amanin sosai. Ga Moddi bai
gaya mata inda za su ba. Tafiyar sam bata mata ba, don haka kawai take jin gabanta na wani irin masifar
fa’duwa. Don haka cikin hassala ta ce “Wai ina za mu ne?” “Unguwa” Ya bata amsa ba tare da ya ko
kalleta ba. Sai ta ja baki ta tsuke a ranta take lailayo ashar tana zuba masa. Amani tana baya farin ciki duk
ya cikata jin Dada bai gayawa makirar matar inda za a ba. Da alama bata san ina za su ba, bata San ma za
su koma sabon gida ba. Hakan yana nufin akwai Daru kenan…




Bai tsaya ko ina ba sai a harabar gidan. Safna ta dinga Ware ido tana kallon gidan da ya yi masifar tafiya
da imaninta. Sai dai gefe guda wani irin tsoro ne ya shigeta. Bata manta garga’din Bokanta ba. “Kada ki
sake ki tare a sabon gidan nan sai kin zo mun Miki aiki, idan ba haka ba komai ma zai iya faruwa. Aikinmu
da duk abinda kike tak’ama da shi zai warware…. Jikinta Har rawa yake da tuna hakan. Don haka da sauri
ta kalli Moddi ta ce “Ina ne nan? Ba dai sabon gidan mu ba ne? Ba dai tarewa muka yi yau ba?” Ya bita da
kallo yana mamakin sauyawar yanayinta. Madadin amsa mata sai ya saka kawai zai shiga gidan. Da sauri
ta ja hannunsa tana girgiza masa kai jikinta na rawa ta furta “Kada ka shiga Imaam, wallahi akwai
matsala, ya zaka kawo ni gida ba tare da sani na ba. Me kake nufi ko zuwa muka yi mu gani mu koma.” Ya
‘d’an janye hannunsa yana furta “Mun dawo kenan, akwai matsala ne?” Saura k’iris fitsari ya zubo mata.
Ta wani irin zaro ido tana girgiza kai ta furta “Me? Wallahi ba zan shiga ba, wannan ma ai rainin hankali
ne, ta ya zaka ce min na dawo gida ba wani shiri….” Ya ‘d’an k’ura mata ido kafin ya saki wani murmushi
Ya furta “Shiri? Shirin me zaki yi? Duk wani shiri na gama shi a gidan nan, akwai duk abinda za ki buk’ata a
ciki. Didi ma tun jiya ta tare…” wannan karan fitsarin sai da ya zubo. Ta runtse ido tana tuna sauran
maganar da ta zauna mata daram a kwanya. Ta haddace ta kamar karatu. “Barin Uwarsa ta zauna inuwa
d’aya da shi, ina tabbatar miki kamar shigar ki matsaloli ne ba matsala ba. Dole ki raba Uwarsa da gidan
sa…” Idan bata manta ba shine dalilin da yasa ta dinga zubawa Didi rashin kunya da rashin mutunci har
ta gaji ta tattara ta bar gidan. Sannan yanzu ya gaya mata wai Didi na ciki. Kai ina ai ba ma zai yiwu ba.
Gaba d’aya duk ta rikice hakan yasa Moddi ya tsaya yi mata kallon mamaki su kansu su Amanin kallonta
kawai suke. Har Moddi Ya k’arasa gabanta yana murmushi ya ce “Akwai sauran shiri ko?” Ya fa’da k’asa
k’asa sai kuma ya girgiza kai “Kin shigo kenan Safna. Idan kuma kika fita nan da kwanaki masu yawa ma
ba tare da izinina ba, ina tabbatar miki a bakin aurenki.” Ta ji wata irin hajijiya tana neman kada ita. Tana
kallon su Amani suka bi bayansa Amanin na sakin dariya k’asa-k’asa. Sai da ta dafa bango tsabar yarda taji
ana wujijjigata kada fa mafarkinta ya tabbata kada wannan gidan ya zame mata BAK’IN GIDA… ganin Sun
mata nisa yasa da sauri ta mik’e ta bi bayansu. Tana aikin turawa Malaminta Message. Hannunta duk
rawa yake… a haka ta isa babbar k’ofar da taga sun shiga. Inda anan babban parlorn da ya raba sassan su
da na Didi yake. Didin na zaune a saman kujera su Umma Tee zagaye da ita. Amani da sauri ta fa’da jikin
Umma Tee d’in. Duk murna ta gama bayyana a saman fuskokinsu. Suka d’ago suna kallon Safna da yake
tsaye kamar ruwa ya ci ta. Sai fidgeting yatsunta take. Didi ta saki wani murmushi tana furta “Maraba
lale, shigo mana Safna.” Wani abu ya dunk’ule mata a zuciya sai kawai ta juya da sauri ta nufi d’aya k’ofar
da ta tabbatar nan ne part d’inta. A zafafe ta mayar da k’ofar ta kulle tana sakin huci da wani irin Zare ido.
A tsorace take ta tsorata da komai ma, idan ba kallon tsoro ta yiwa Moddi ba, sai taga kamar kallon tsana
yake mata. Da wani irin hanzari ta fara kiran wayar Malamin nata. Bugu guda ya d’aga don shima yaga
message d’inta. “Safna kada ki shiga gidan nan, idan kika shiga komai ma zai iya faruwa, idan na ce komai
ina nufin komai, kada ki shiga….” Safna ta runtse ido tana furta “Na shiga Malam, Na shiga ka gaya min
ba abinda zai faru….” Daga d’aya gefen Malam ya ce “Akwai Matsala, idan zai yiwu ki fito yanzu tun kafin
abinda ake gudu ya faru….” “Malam ba zai yiwu na fito ba, ya ce idan na fito a bakin aure na….”
Muryarta ta tsaya cak ganin Moddi a tsaye a gabanta yanayinsa ya nuna ya ji duk abinda ta ce. Don
kallonta yake da birkitattun idanunsa da suka bayyana tsananin fitinarsa da rashin mutuncinsa, kamar
kallon farko da ya fara yi mata sanda suka fara ha’duwa. Hantar cikinta ta ka’da….




JIKAR NASHE ✍🏽HADARIN GABAS…..👌
26.



NAZEEFAH SABO NASHE★ ✍️


08033748387.



BRIGHT PENS 2nd batch..




“Da wa kike waya?” Ya yi amfani da bu’daddiyar murya wajen tambayarta. Murya bata mata kama da ta
Moddinta da ta sani ba, wani ne wannan daban, da ya jirkita zuwa wata halitta mai furgutarwa gareta.
Bata tab’a ganinsa a wannan yanayin ba don haka razanar da ta shiga ba ka’dan ba ce. A fusacen Ya sake
cewa “Ba kya ji ne? Ki yi magana mana…. Ko sai na bayyana Miki wanene ni?” Ta ha’diye wani yawu
sannan cikin muryar da ta bayyana rashin gaskiyarta zalla ta furta “Da k’awata nake fa, da wa zan yi
waya.” “K’arya kike.” Ya fa’da direct yana kallon cikin idonta. Wata irin tsanarta yake ji a ransa. Ta sake
tsorata da yanayinsa don gani take zai iya kai mata duka. “Ka yiwa girman Allah ka kyaleni Imam me na yi
maka ne?” Cije leb’ensa ya yi sai kuma ya wancakalar da ita gefe yana jin idan har ya cigaba da tsayawa
kusa da ita zai iya zama ajalinta, a yarda yake jin zuciyarsa na wani irin zafi…. Da wani irin sassarfa ya fita
daga d’akin. Sai sannan Safna ta ja ajiyar numfashi ta shak’i iska. Kafin ta furzar da huci. Wani irin zafi take
ji a ranta. Ita yau Imaam ya yiwa haka? Ta cije bakinta wasu hawaye da ta tabbatar na bak’in ciki ne suka
zubo mata. Ta zauna tallafa da kumatunta tana jin tunanin da yake cikin zuciyarta shine kawai abinda ya
kamata ta yi. Ba dai burin y’an uwan Moddibo su tozarta ta ba, burinsu ya yi aure ya haihu zata biyo
musu ta yarda suke so. Wannan hawayen ta rantse ba zata zubar da su a banza ba. Da wani irin zafin
nama ta shiga kiran Lady boss. Bata wani b’oye mata komai ba, ta zayyano mata abinda ke faruwa. Cikin
mamaki Lady Boss ta furta “Kan Uba! Shi Imaam D’in ne ya aikata miki haka? To me ya shiga kansa?”
“Rashin mutunci, ko na ce Uwarsa da y’an uwansa suma sun je sun yi nasu k’ulunboton to wallahi
wannan karan na shirya musu zan tabbatar musu ni gaba nake da su a iya shege, zan b’ata musu sunan
dangin da suke alfahari da shi, da ina jin ba zan iya aikata abinda Alwan ya saka ni

20 / 28