Chapter 22 Reading HADARIN GABAS Cin Amanar Iyali by Nazeefa Sabo Nashe READ HAUSA Novels

HADARIN GABAS Cin Amanar Iyali by Nazeefa Sabo Nashe

Author :  Nazeefa Sabo Nashe Category :  African Stories & Novels

Chapter   22 / 28

63K to 66K   out of 82.1K words

bayyana ragwantakarsa a yau, duk da
kasancewarsa jarimi mai k’ok’arin b’oye damuwarsa Amma yau kam ya kasa, ya bayyana rauninsa a gaban
yaransa. Jikinsu ya yi sanyi, zafinsa da suke ji ya fara narke wa zuwa tausayi, tausayin da basu San
dalilinsa ba, basu San me yasa ba? Musamman Imani da ta dinga jin kamar taje ta rarrashe shi. Ya da’de a
haka yana hawayen suma suna nasu. Duk zafin da zuciyar Amani take yi sai ta neme shi ta rasa. Tsanarsa
da take ji ta gudu, wata irin tarin k’aunarsa ta sake ji a ranta soyayya mai zafin gaske da take jin zata iya
aikata komai saboda taga ta kawar masa da damuwa. Ta dinga binsa da kallo tana lumshe idonta jin
husky voice d’insa yana furta “Am sorry Ama…. It wasn’t my fault, zuciyata ce In sha Allah komai zai
zama labari duk da na San Nine silar afkuwar halin da nake ciki, Soon zan maku bayani Amma kafin nan
please keep this a secret….” Daga haka ya lumshe idonsa sai kuma ya fara tafiya da baya da baya. Amani
ta dinga kallonsa tana jin kamar ta tashi ta rungumoshi ta lallashe shi. Tana kallo ya fice ya bar musu
k’amshin sa a cikin d’akin. Sai kawai ta rungume pillow tana sake sakin kuka. A sannan take jin zuciyarta
bata mata adalci ba… Imani bata lallasheta ba don itama kukan take kanta a saman bayan Amani ta furta
“Sister, mu rufawa Dada asiri, a idonsa na hango ba laifinsa ba ne, da gaske yake ba laifinsa bane, ban san
wace kalar k’addara ba ce take bibiyar rayuwarku daga ke Har shi…” Bata mata magana ba, don ita
abinda ya dameta ya dameta, bakomai ba ne sai wani irin k’aunar Dahda soyayyarsa da k’iyayyar sa da
suka caku’de mata a zuciya ta rasa a wani muhalli zata ajiye Dahda masoyi ko mak’iyi, ko kuma Mahaifi?
A daren ranar kam basu yi barci ba, sun tashi sun yi Sallah kowannensu Ya dinga gayawa Allah
damuwarsa da son ya magance masa ita. Sai sannan suka ji sanyi, suka kuma samu sauk’in abinda suke ji
a zuciyarsu, bayan Asuba barci ya d’auke su.




Shirun da Didi ta ji basu fito ba, yasa ta gaji da jira ta kalli Fateemah ta ce taje ta taso su. Time D’in k’arfe
10:00 na safe. Da k’yar Amani ta bu’de nauyayyen idanunta da suka kumbura fiye da na Imani, ta zube su
a cikin na Umma Teey da take kallonsu cikin matuk’ar fa’duwar gaba. A kasalance ta ce “Me ya same ku?
Me ye haka? Me ya faru?” Lumshe ido Amani ta yi tana kokawa da hawayen da ya kasa tsayawa daga
idonta. Hakan yasa fargabar Umma teey ta sake yawaita ta zauna gabanta na fa’duwa sai dudduba jikinsu
take. “Ku gaya min mana.” Imani ce ta sauke ajiyar zuciya kafin ta kama hannun Umma Teey D’in. Tana
sakin ajiyar zuciya da k’ok’arin kawar da damuwarta ta furta “Bakomai fa, waccan matsalar ce dai ta
Amani har yau bata daina ba.” Umma Teey tausayin yaran ya sake kamata sai kawai ta jijjiga kai tana furta
“Soon, zata daina In sha Allah, ina nan ina addu’a, lamarin ne akwai sark’ak’iya. Ina so dai ku cigaba da
rufawa mahaifinku asiri Har muga abinda hali zai yi, kun ji?” D’aga kansu suka yi. Suna furzar da huci
kusan a tare. Umma T,ta ce ku tashi maza ku shirya Didi na can hankalinta yana nan, duk ta damu, kuma
daga yau ina son ku koma sashenta da kwana gwara kuna kusa da ita, Ya fi wannan zaman naku anan da
hankalina sam bai kwanta da shi ba.” Basu musa mata ba, suka yarda da abinda ta ce, don kam zamansu
anan su da kansu sun san bai kamace su ba.




****

A daidai lokacin Safna na tsaye gaban Ramin data aikata komai, cikin tashin hankali take bin Ramin da
kallo tana cije yatsa. “Kan Uba!” Ta furta tana kallon yarda aka tone komai. Tashin hankalinta yana
hauhawa bata manta garga’din bak’in bokan ba, “Kada ki bari kowa ya san kin birne abin nan, idan har
wani ya gani tabbas kina cikin matsala. Zufa ta dinga zubo mata, ganin ko alamar kayan sihiran nata,
“Akwai Matsala Safna, duk wani sihirinki ya warware asirinki Ya kusa tonuwa!” Ta dinga jin muryar bokan
a kunnenta… jikinta na rawa ta zube a wajen. Zuwa ta yi dama a lokacin ta zuba rubutun da ya sanar
mata idan safiya ta yi taje ta zuba a kai. Sai dai taga wannan tashin hankalin. An tone Ramin an kuma
kwashe tarkacen Sihirin. Zafi zuciyarta take yi irin zafin da take jin da zata ga Wanda ya mata hakan, sai ta
kashe shi Har lahira… Idonta ne ya sauka akan hular Amani da zobenta… da sauri ta saka hannu ta
‘dauke su cikin zafin nama kamar wacce ake wa Gangi ta juya a zafafe ta nufi cikin gidan. Kai tsaye
d’akinsu Amani ta nufa ta tura k’ofar da dukkan k’arfinta. Idonta ya sauka a kansu suna yafa mayafi da
alama Sun shirya zasu fita daga d’akin. Ta watsa musu kayan a gabansu tana furta “Na Uban waye a cikin
ku?” Imani da sauri ta kalli Amani don ta San nata ne, hularta ce ta jiya data kwanta barci da ita… ta
waro ido ganin Amanin ta mik’e cikin taku mai nuna isa da rashin kunya zalla ta isa gaban Safnan tana
mata wani irin fisgaggen kallo, mai bayyana wulak’ancinta zalla… a gabanta ta tsaya tana sakin wani
murmushi ta nuna kanta tana furta “Na Amani Imaam Moddibo ne….” Safna ta k’ank’ance idonta cikin
na Amani, tsanar yarinyar na sake girmama cikin zuciyatta ta dinga jin tamkar ta shak’ota ta mutu, amma
idanun yarinyar a yau Sun razanata Sun kuma firgita ta. A idanun Amanin ta dinga hango rashin kunya
zalla da wani irin kwarjini da ba shakka idan ta cigaba da tata masifar Amanin zata iya tona mata asiri.
Zata iya fallasa sirrinta ta sanar da zuri’ar Lami’do wacece ita? Sai kawai ta cije baki, k’walla tana shirin
zubo mata. Ba k’wallar komai ba ce sai ta rashin sanin madafa, da rashin sanin abinda zata aikata… cikin
k’unar zuciya ta furta “Kin cuce ni Amani, kuma wallahi ba zan barki ba sai kin biya abinda kika aikata
min, sai na saka ki bak’i ciki fiye da Wanda kika sa min a cikin kwanakin nan zan mayar da rayuwarki
miserable…” daga haka ta juya ta fice cikin mutuwar jiki. Imani ta dinga kallon Amani a firgice ganin wata
irin da Amanin take hankalinta kwance kafin ta furta “Before ta yi making life d’ina miserable ni na mayar
da tata, matsafaciya kawai….” Juyota Iman ta yi a fusace tana furta “Ba zaki daina shiga sabgar matar
nan ba ko? Ba zaki fita hanyarta ba ko? Sai ta cutar da rayuwarki?” Amani ta dafa hannunta tana
murmushi ta furta “Wait and See, ba abinda zai faru sai alheri, In sha Allah sai naga bayan matar
nan….na tsaneta Imani, kuma ko yanzu na San burina daf yake da cika.”



Daga haka ta saka kai ta fice daga d’akin. Tana jin zuciyatta fresh kamar ba wata tarin matsala a tare da
ita.




Babban Parlorn Didin taf yake da mutane. Wa’danda suka zo taya ta murna. Yau bakin Didi Sam ya k’i
rufuwa don a yau ne zata saka a kai ku’din auren Moddi. Auren da take ji idan ya yi shi dukkan
matsalolinsa da nasu za su kau. Tana kallon k’aninta Kawu Jauro ta furta “Duka a kai har ku’din har lefen
idan ta kama a basu Har sadakin bana son auren nan ya wuce sati biyu Jauro, ka gaya musu bama
buk’atar komai sai matar kawai.” Jauro ya ‘d’aga kai cike da gamsuwa. Amani kuwa gabanta ne kawai yake
fa’duwa haka kawai jin wai auren Dada za’a je nema. A da kam ta fi kowa son Dada ya yi auren Amma yau
sai taji wani abu ya dunk’ule mata a k’irji jin abinda Didi take cewa. Hakan yasa ta sulale daga cikin
mutane ta shige d’akinsu na sashen Didin tana shiga ta danno k’ofa. Zuciyarta na bugawa ta lumshe ido
tana jan Innalillahi a ranta don idan har ba mafarki take ba, ji take kamar kishin Dadan take, kishi mai
zafin gaske mai dagargaza zuciya da saka zafi a cikin zuciyar…. Ta runtse idonta tana furta “Ya Allah! Me
yasa ne?” Ta fa’da tana kwanciya saman gadon.
Iman kuwa farin ciki ne ya sakata neman idanuwan Amanin don su yi farin cikin tare ko ta hanyar kallon
juna ne, sai dai bata ga Amanin ba. Don haka ta mik’e zuwa cikin gida don neman Amanin a daidai
Sitroom da Dahda yake zama da bak’i. Ta fara juyo sautin muryarsa kamar waya yake, kamar kuma
magana yake da wani a kusa da shi… “Wannan karan fa na shirya da gaske nake zan aikata abinda kuke
so, zan cika muku burinku zan kusanceta……” Nimfashin Iman ne ya kusa d’aukewa tsabar tashin hankali
bata San sanda ta yi baya ba, don idan Har zuciyarta ta fassara abin daidai Furucin Dada yana nufin zai
kusanci Amani don cikar wani burinsa, Wanda ta tabbatar bakomai ba ne, sai SON DUNIYA…….



(wannan littafin book one ne free, book 2 and 3 paid ne. A biya 500 cikin wannan asusun 2118666253
UBA. Don cigaba da jin labarin Moddin Didi, da Amanin da Dahda. Wa ke da nasara tsakanin Amani da
Safna. Book 1 daf yake da k’arewa.)




JIKAR NASHE★ ✍️HADARIN GABAS……👌


28.




NAZEEFAH SABO NASHE★ ✍️

08033748387.



BRIGHT PENS SECOND BATCH…
A gigice ta ja da baya da sauri, don bata son Dahdan ya ganta. Sai dai aikin gama ya riga Ya gama, don
tuni idanunsu suka ha’de da juna. Ta Ware ido tana toshe bakinta da k’ok’arin ha’diye kukan da yake son
taho mata. Sai dai ina bata da juriyar rik’e wannan kukan tuni hawayen ya kufce ya dinga zuba daga
idanunta… Mik’ewa Dahdan ya yi don isa wajenta da son ya yi mata bayani, sai dai ko kafin ya kai k’ofa ta
fice da sauri, bata son ganinsa ba kuma ta son jin ko wane kalami daga bakinsa. Ta ji komai ta kuma
amince Dadan matsafi ne, da gaske tsafi yake yi shi yasa duka abubuwan suke faruwa. Ashe hauka take
da take d’orawa Mommy Alhajin komai. Dahdan ne mai laifi shi ya yi silar afkawar Amani cikin wannan
halin. Ta mayar da k’ofar ta rufe Har da murza key sannan ta jingina da k’ofar wani irin kuka da bata tab’a
irinsa ba a rayuwarta ta shiga yi. Da dukkan k’arfinta take buga k’ofar da kanta tana furzar da wani irin
huci mai zafi. Daga k’asan ranta take jin wani irin zafi zuciyarta kuwa kamar ana tafasa ta da ruwan zafi.
Gangar jikinta idan banda tsiyayar da gumi ba abinda take yi. Duk da tarin sanyin A.cn da yake d’akin jin
ta take kamar tana cikin Oven, tsabar zafin da take ji na tashin hankalin da take ciki. Ta zube a gado
idanunta akan hoton mahaifiyarsu, kallon hoton ta yi kafin ta fisgo shi da k’arfinta ta shiga magana da shi
kamar wacce take cikin hoton tana jinta. “Me yasa? Me yasa Mahmeey kika Mutu kika bar mu? Me yasa
baki tafi da mu ba, kika barmu a wannan duniyar mai cike da maciya Amana da burin duniya? Mun
fuskanci k’alubale da dama kafin mu tashi mu kai yanzu, sai gashi a yanzu muna fuskantar k’alubalen da
yafi Wanda muke ciki, mahaifinmu Mahmeey, Dahdah yana shirin kusantar Amani y’ar cikinsa don Son
Duniya…” Sai ta sakè fashewa da kuka da k’arfin gaske, ta rungume hoton y’ar riga a jikinta. Ta da’de
zube a wajen cikin fitar hayyaci kamar wacce ta zare, burinta mutuwa a loakcin burinta ha’duwa da
mahmeey a can inda ba zata sake ganin Dahda ba, ba zata sake ha’duwa da duk wani k’alubale mai shirin
tarwatsa mata zuciya ba. Tana so ta Mutu sosai kamar yarda Amani take burin mutuwar itama. Bugun
k’ofar da ake yi ne yasa ta dawo cikin hayyacinta, sai kuma tabi k’ofar da kallo tana tunanin waye sai ta ji
muryar Amani tana kiran sunanta. A kasalance ta mik’e ta bu’de mata k’ofar. Idanu suka zubawa juna
gaba d’ayansu kowa yana jin wani irin ciwo a ransa, ganin halin da d’an uwansa yake ciki. Iman ta finciko
Amanin ta mayar da k’ofar ta rufe ta rungume ta da k’arfin gaske, a tare suka saki kuka sautin bugun
zuciyarsu yana k’aruwa. Jikin Amanin zafi zau da alama mugun zazzab’i ne ya kamata. Iman ta ja
hannunta zuwa bakin gadon ta zaunar da ita kafin ta mik’e cikin First aid box da yake gefen gadonsu ta
bu’de ta Ciro pain reliever ta d’auko table water ta dawo inda Amanin take. A baki ta zuba mata maganin
Amanin tana b’ata fuska ta sha maganin. Kafin ta zube a saman gado. Iman D’in ma kwanciya ta yi daf da
ita tana sakin ajiyar zuciya ta furta “Matsalar mu daga yau In sha Allah ta kau Ama.” Amanin ta ‘d’ago
tana kallonta da neman k’arin bayani. Iman ta d’aga mata kai “Dole zamu bar gidan nan a daren yau….”
Amanin ta zaro ido kafin ta lumshe su sai kuma ta ciji leb’enta bata ce komai ba. “Zamu wuce wajen
dangin Mahmeey, Har sai komai ya lafa, ina tsoron afkuwar wani abu da naji shi da kunne na yau, da
wani ne ya gaya min ba zan tab’a yarda ba…” Amanin bata bu’de idonta ba. Zuciyarta ce kawai take
bugawa da wata irin k’aunar Dahda mai zafin gaske… tana kallo Iman ta shiga ha’da musu abinda zasu
buk’ata. Har ta gama bata ce komai ba, tana jin abinda Iman ‘D’in ta yanke shine mai kyau…
Dahda kuwa tun bayan fitar Imani sai kawai ya lumshe ido Ya jingina da kujera yana jin kansa yana matsa
da wani irin ciwo. A hankali yake taune lips d’insa. Daidai lokacin Amanin ta shigo kamar an jehota a
firgice duk ta yi wani irin. Kallonta yake da mamakin yanayin da take kamar wata Mara lafiya. Zama ta yi a
gefen kujerar da yake kawai sai ta samu kanta da saka kuka. Bai ce mata komai ba har ta gama kukan da
ya tabbatar shine zai saka ta samu sauk’in ra’da’din da take ji a zuciyarta. Ta ‘d’ago a fisge ta sauke ganinta
a kansa kafin ta furta “Dahdah da gaske kai ka haife ni?” Shiru ya yi bai amsa mata ba, sai dai bai janye
idonsa daga kanta ba, ya furta “Kina tantama ne?” Ta cije leb’enta da k’arfin gaske kafin a fusace ta ce
“Ina tantama, idan Uban da ya kawo y’arsa duniya zai aikata abinda ka aikata, idan kuwa kai ka haife ni ka
cuce ni ka cuci kanka Dahda, ka gaya min me yasa ka aikata min haka, kuma waye Uba na don ban yarda

Kai ne ka haife ni ba…” Bai mata magana ba, Ya cigaba da kallonta yana fusgar leb’ensa kafin ya mik’e
tsaye. Wata drawer taga Ya bu’de ya zaro wani enveloped. Ya cilla mata a hankali ya furta “Your
answer…” Ya koma ya zauna yana furta “Komai kika gani jiya ke kika jawowa kan ki, shi yasa idan mutum
ya ce abinsa sirri ne baya son a gani, yana da kyau ka janye hankalinka daga kansa, Saboda baka San me
zaka je ka gani ba, yanzu da kika ga abinda ba a so ki gani ‘d’in ga situation d’in da kika jefa kanki nan, so
are you happy?” Daga haka ya koma ya zauna yana cigaba da kallonta, da kallon yarda hannunta yake
rawa wajen bu’de enveloped D’in. Hoto ne da wasu takardu. Hoton jarirai ne guda biyu rungume a
hannunsa yana nunawa Mahmeeynsu gefe guda kuma Didi ce da Umma T. Fara’ar fuskarsu ta kasa b’uya.
Y’ar riga murmushi kawai take idanunta akan jariran da y’ar k’walla a gefen idon nata. Ta San hoton don
haka ba bak’o bane a wajenta. Takardar ta tsirawa ido tana kallon sunan mahaifiyarsu a jiki da ranar da
aka haifesu. Sai kawai ta lumshe ido hawayenta na cigaba da sauka. Dahdah shiru ya yi yana jin wani
rauni a zuciyarsa, yarda yake jin zafin zubar hawayenta daidai yake da d’igar dalma a jikinsa. “Enough
Ama….” Ya furta cikin wata irin silent voice da take fita da wani irin magana’disu da yasa dole Amani ta
bu’de idanunta ta zube su a kansa… d’aga mata kai ya yi kafin Ya saka handky ‘D’in hannunsa yana share
mata hawaye. Zuciyarta ce ta dinga bugu madadin samun sauk’i a ranta sai ta dinga jin wani irin yanayi. A
firgice ta farka daga mafarkinta ta kuma ture hannun Dadan kafin ta mik’e da sauri, ta yi hanyar fita daga
sashen nasa, sam bata ganin gabanta…




Ya da’de zaune a wajen bayan ya janye idonsa daga kallon Amanin da ta fice a firgice. Ya sauke ajiyar
zuciya yana murzar goshinsa. Yarda yake murza goshin ji yake kamar yana tafiya ne da tarin damuwarsa.
Wani irin sanyi ya dinga bin sassan jikinsa. Nauyin da zuciyarsa ya yi ya dinga sauk’ak’e. A hankali yake
sauke ajiyar zuciya. Da gaske ya samu hanyar warwarar matsalarsa… Amma ta yaya? Ta Yaya zai amsa
tarin tambayoyin da ya hango a idon Imaan da Amani….. a hankali ya mik’e yana zagaye d’akin ya san
Imaan ta ji shi a wayar da yake magana, a idonta ya hango jin firgicin maganarsa, sai dai bata tsaya ba,
bata tsaya ya yi mata bayani ba, duk da shi kansa bai San kalar bayanin da zai mata Har kwanyarta ta
‘dauka ba. Don haka shirun shine yafi gwara ya ja bakinsa ya yi shiru kawai. Ya san shi mai laifi ne a wajen
yaransa, laifin da yake tunanin ba abinda zai goge shi, a idonsu yake hango tsanarsa lokaci guda kuma a
idon nasu dai yake hango tarin k’aunarsa, da tausayinsa. Da gaske shi abin tausayi ne, Safna ta mayar da
rayuwarsa akan irin tafarkin da take so, Ya amince ta yi winning a kansa…..




Cikin sanyin jiki ya koma sashen Didi. Rarraba ido yake a cikin tarin y’an uwansa ko zai hango y’ay’ansa.
Sai dai Babu su ba alamarsu. Ba wanda ya lura da halin da yake ciki. Don murna da zakwa’din aurensa da
suke yi. Ya d’an tab’e baki kafin ya zauna a daf Didin. Da jarumta sosai a muryarsa don son ya kawar da
yanayin damuwar da yake ciki ya yi magana. “Kun cika gidan nan da hayaniya, and kun sani bana son
hayaniya why all the noises don Allah ku tattara ku tafi, I need privacy ina son magana da Didi….”
Dukkansu da suke wajen sai da zuciyarsu ta buga. Basa son komai zai gayawa Didin ya ce Ya fasa auren,
zuciyar Didi ba zata d’auka ba zai raunata mata zuciya. Ba tun yau ake nema

Masa aure yake fasawa ba. Didi ma kallonsa take tata zuciyar tafi ta yaran nata bugawa bata manta wani
lokaci data nema masa auren ba, a ranar auren

22 / 28