Author : Nazeefa Sabo Nashe Category : African Stories & Novels
biyo baya ba ruwana, don abinda na gaya Miki
iya gaskiyar kenan har cikin raina…bana son na jawo muku magana zan iya samun y’ar ko waye na sauke
mata abinda nake ji…” Zuciyarta ta ji ta buga amma sai ta cije ta fice da sauri. Bata yi niyyar gayawa Didi
ba, amma ganin kallon Didin take mata yasa ta kasa samun nutsuwar yi mata k’arya. Shigowar Moddi ce
ta saka su d’ago da kai dukkansu. Yana kallon Didi ya furta “Didi kina da lemon tsami, yanzu na tambayi
wani abokina ya sanar da ni shine maganin matsalata…” Didi ta d’ago tana masa kallon k’urilla bai wani
damu ba ya zauna daf da ita yana rik’e k’asan cikinsa ya kwanta rigingine yana cizon leb’e. Takaici da wani
bak’in ciki ne suka saka Fateemah sakin baki tana kallonsa. Bata San rashin kunyar Kiddo har ta kai haka
ba, ta tabbata ko bai fito Ya gayawa Didi abinda yake
Ji ba, Didin da kanta zata fassara abinda yake nufi. Didi wani guntun murmushi ta saki ba tun yanzu ba, ta
San Moddinta ya girma kuma
Lafiyayyen namiji ne. Kitchen ta shige ta ha’da masa Lemon tsamin har da gishiri ka’dan sannan ta fito ta
mik’a masa tana lura da kallon takaici da Fateemah take wurga masa. Hakan yasa ta sakin murmushi tana
furta “Ki bar shi Fateemah, lokaci ne yazo haka girman yake ai, a wajen su Maza.” A zafafe Fateemah ta ce
“Wallahi Didi iskanci ne, da kuma ya raina ni ni da ke, Ya jewa Dijatu da wannan maganar mana idan bata
ci ubansa ba, rashin kunya k’iri-k’iri, shi dole sai ya nunawa mutane ya balaga, a d’aki fa Ya saka ni yana
gaya min wai mu aurar da shi kada ya janyo mana abin kunya….” Didi ta d’an yi dariya tana furta “Allah
y’a hore abin auren, idan Allah ya hore Ai sai a yi auren, Don gwara auren da yaro ya d’ebo maka abin
magana…” Moddi ya turo baki ya yiwa Fateemah gwalo ta kuwa sake hassala hakan yasa ta furta “Ai sai
ka yi auren, idan kana da sana’ar da zaka kula da matar.” Ya mik’e yana ce mata in dai abinci ne ai Didi
zata bata.” Ya fita daga d’akin saboda jin wani yanayi a jikinsa yana buk’atar tsaftace kansa. A zauren
gidan ya juyo siririyar muryarta tana sallama. Ya amsa sallamar yana kallonta da k’waryar nonon da ta
Saba kawo musu talla a kanta. Aa usual yau ma jikinta tas kamar ba wacce tazo daga rigar fulani ba. Ya
bita da kallo tun daga sama har k’asa sai kuma Ya d’auke kansa fuskarsa a d’aure Ya kalleta yana furta
“Zubo fura ki kawo min d’aki na, ke y’ar riga….” Ta yi wal da idonta kafin ta saki murmushi tana bin
bayansa da kallo wani farin ciki na cika zuciyarta a karo na farko Moddi ya mata magana cikin kwantar da
murya ba hantara da kyara, ko dai Allah ya amsa addu’ar da take yawan yi ne? Ko gidan bata shiga ba ta
durk’usa cikin rawar jiki ta fara dama masa furar mai da’din gaske. A bakin k’ofar sa ta tsaya tana furta
“Fillo ga furar…”Cikin wata irin murya ya ce “Shigo Malama…..
JIKAR NASHE★ ✍️HADARIN GABAS……👌
24.
NAZEEFAH SABO NASHE★ ✍️
08033748387.
BRIGHT PENS SECOND BATCH.
★★★
Kamar ba zata shiga ba, don zuciuarta wani irin bugu take yi, sai dai ta daure ta shiga ‘din. A zaune a
saman katifarsa mai tudun gaske d’akin sai zabga k’amshi yake don Moddi yana da tsafta baya shiri da
k’azanta kuma sam. Kallo ya bita da shi, kafin ya cije leb’ensa yana tunanin abinda zai aikata D’in daidai
ne, amma abinda yake ji ya shalle tunaninsa, Ya manta DIDI da kashedinta, ya manta da fa’dan da zata
masa ma. Ya dinga bin y’ar riga da kallo kafin ya saki malalacin tsaki ya furta “Zo ki zauna anan…” “Ta
zauna a ina Kiddo?” Fateemah ta fa’da don fitowarta daga gida kenan kawai taga kayan Y’ar riga da
takalmanta, ta San Moddin basa shiri da y’ar riga asalima ya tsani ganinta kullum hantararta yake yi.
Madadin amsa mata wani takaici ne Ya rufe shi ya lumshe idonsa kawai yana taune leb’ensa, banda ma
jaraba irin tasa me zai yi da wannna y’ar abar da baya mata kallon mace? Haushin kansa ya kama shi don
haka Ya cusa yatsun hannunsa cikin gashin kansa yana fisgar gashin da k’arfin gaske kamar shi ya masa
laifin. Fateemah a hassala ta finciki hannun y’ar riga da take tsaye tana ta rawar jiki da alamun tsoro
mabayyani a saman fuskarta. “Shashasha, me ya kawoki d’akinsa?” Cikin rawar baki ta furta “Shi ya kira
ni….” Wata harara Moddi Ya zuba mata hakan yasa ta ja baki ta yi shiru, jikinta na sake b’ari. Fateemah
ma harara ta zuba mata ta yi k’wafa tana furta “Da ya kira ki baki da wayo da zaki shiga d’akin maza?baki
son ko ya kake da namiji ba a wannan zamanin baka sakin jiki da shi, bare irinsu Kiddo da kunya bata ishe
su ba…” “Kada ki saka ta raina ni, wallahi b’allata zan yi.”
Moddi ya fa’da daga zaunen da yake fuskarsa a d’aure sosai. Sai abin ma ya bawa Fateemah dariya ta
furta “Raini na nawa kuma? Banda Wanda ka siya wa kanka, wallahi zaka zo ka samu Didi ka gaya mata
dalilin da yasa ka ja y’ar mutane d’aki….” K’asa k’asa ya furta “Dalilin ne yasa na ce ku yi mini aure…”
tsabar takaici Fateemah kasa amsa shi ta yi ta finciki hannun y’ar riga suka shiga gida tare wajen Didi.
Didi ta d’ago tana kallonsu kafin ta furta “Ke kuma fa, yaushe kika zo?” Sunkuyar da kai kawai ta yi tana
jan yatsun hannunta. Moddi da yake bayansu ya juya ya shiga parlor yana ji Fateemah na gayawa Didi
abinda ya faru. Didi ta zaro ido tana furta “Lamarin Har ya kai haka? Hasbunallah Wa ni’imal wakeel,
yaushe Moddibo ya koma haka? Ai shikkenan wuce ki tafi gida ni na San maganin abin, auren zan masa
da duk kuma yarinyar da tarbiyyar ta ta kwanta min a rai….” Yana jin haka ya yi saurin fitowa daga d’aki.
Yana muzurai ya ce “Not any girl Didi, ba da kowace mace Imaam zai iya rayuwa ba, na fi son y’ar gayu
mai tsafta wayayyiya y’ar boko.” Ta zuba masa harara tana furta “Shirmen banza da wofi, duk a lissafin
naka kuma Ban ji ka furta mai addini da iliminsa ba, mai kunya da tarbiyya…” Ya girgiza kai “Bagidajiya
kenan? Ai irin wannan yaran ba wayewa a tare da su, nifa nafi son wacce zamu buga Soyayya wacce ba
zata ji kunyarki ba, zata iya rungume ni a gabanki ta min Kiss….” Bu’de baki Fateemah ta yi tana kallonsa
Didi kuwa murmushi ta saki ta San Moddinta Ya kere nan, sam ba ya jin kunyarta sanda ya fara mafarki
ma ita ya fara samu ya gayawa, wai ya ga wani abu mai da’di a cikin barci ashe haka Mata suke da da’di
Didi musamman idan ka rung….” Didi ta yi saurin rufe masa baki tana furta “Wannan sirrinka ne Moddi,
kada na sake jin ka bayyana shi ga wani, alamu ne na ka girma kana kuma da lafiya…” Sai ya d’an yi
dariya yana rik’o hannunta yana furta Didi ko shine Jima’in da ake gaya mana a Islamiyya?” Didi bata ji
kunyarsa ba ta gaya masa shine, amma haramun ne aikata shi sannan Allah yana fushi da mutumin da Ya
aikata zina ma’ana kusantar Mace ba tare da an musu aure ba, don haka ka kiyaye Moddi ka bari ka samu
halaliyarka… haka ta zaunar da shi a matsayinta na Uwa bata b’oye masa komai ba, ta bu’de masa komai
ya sani sannan ta tsorata shi da kusantar koda rik’e hannun mace ne,balle wane sashe na jikinta, da zarar
ka aikata haka Moddi kamar ka shirya jefa kanka cikin zina ne da saninka don haka ka yi matuk’ar kiyaye
wa Allah ya shirya mana. Fateemah ta jijjjiga kai bayan ta sake wurga masa harara shi kuma ya mata
gwalo sai ta gefe shi da biron hannunta sannan ta fice tana furta “Didi siyar da gonar ki ta k’auye Ya
kamaki ko don ki yiwa Kiddo aure, idan ba haka ba kya ji wani labarin…” “Dole kuwa.” Didi ta furta kallon
Fateemahn “Ai dole na yiwa Moddi aure a kusa kusan nan, Allah dai Ya hore mana rai da lafiya.” Haushi
ya kama Fateeman ta fice tana furta “Ko da Uban me zai ciyar da matar?” Moddi da baya shiru ya furta
“Duk abinda Didi ta ci shi za mu ci, balle ma In sha Allah ba zan yi zaman banza zan dinga neman ku’di.”
“Kamar gaske?” Fateemah ta furta tana ficewa da hanzari don idan ta biyewa Didi da Kiddo sai ta kwana
a wajen bata gama kallon dramerrsu ba. Ita dai y’ar riga tana takure jikin Didi duk hankalinta ya tashi jin
za’a yiwa Moddi aure mutumin da take kwana ta tashi da shi a cikin rai… “Tashi daga nan ko na bugeki.”
Moddi Ya fa’da yana zuba mata harara. Da sauri ta tashi sai dai Didi ta ja hannunta ta mayar da ita ta
zauna, haka kawai take son yarinyar don tana da nutsuwa kuma Sam bata da kwarafniya ga Ibada kamar
ba daga riga ta zo ba. Amma bata san dalilin da yasa sam basa shiri da Moddi ba, don kar ya kira sunanta
yake kiranta da y’ar riga, Har sunan Yabi bakin kowa. A hankali ta gyara mata mayafinta tana furta “Uhm
uhm fa Moddi, ka yi fa a hankali don baka san inda rana zata fa’di ba.” Ya yi dariya sosai kafin ya furta ta
fa’di a gabas wallahi Didi, kada ma ki fara ta inama wannan yarinyar da ‘d’an k’ugunta zasu iya d’aukan
hidimata ji ta fa k’waila, ni nafi son mai manyan Abubuwan nan….” Da sauri Didi ta bu’de ido ganin inda
yake nunawa ta kuwa zuba masa dak’iwa tana furta “Fita daga nan Moddibo, Oh ni Mairo Allah ya
taimaki Uban Moddibo baya raye ba zai ga wannna rashin kunyar taka ba.” Ya k’unshe dariyarsa yana
furta “To idan ban fa’da Miki ba wa zan fa’dawa? Ai gaskiya ne ina zan saka wannan k’wailar?” Didi ta jefe
shi da ludayi hakan yasa ya fita yana dariya. Bai san kuma ya suka k’are ba.
Haka Safna ta cigaba da bibiyar rayuwarsa. Duk inda ya saka k’afa tana biye da shi, shima kuma hakan sai
yake masa da’di wata irin haramtacciyar soyayya Safna take koya masa ta inda sam baya iya guje mata.
Hot romance take zuba masa har ya rasa inda zai saka ransa. Ranar da ba zai tab’a mantawa da ita ba,
ranar da Safna ta ja shi wani hotel. Bai so zuwa ba
Amma ganin b’acin ranta k’arara yasa ba shiri Ya amince. Wanka Ya fesa ya fito sai zabga k’amshin turare
yake. A parlor ya tarar da Didi da Fateemah da su Jameela suna ha’da akwatinan Yabi akwatinan da kallo
yana furta “Didi wannan fa? Lefen waye?” “Na wani” Fateeman ta furta fuskarta a d’an d’aure. Tab’e baki
ya yi sai ya saka kai ya fice ganin har Safna ta fara zabga masa kira. Yana jin Didi na k’walla masa kira tana
fa’din Moddi addu’ar fa? Yau ka yafe.” Bai amsa mata ba ya fella da gudu don baya son Ya sake delay balle
ya b’atawa Safna rai. Didi kasancewr ta yi busy sai kawai ta k’yaleshi suka cigaba da abinda suke.
A bakin k’ofar D’akin Hotel D’in ya tsaya yana jin yarda zuciyarsa take harbawa, wai shine yau ya kawo
k’afarsa hotel? Anya bai ci amanar Didi ba. A tsorace yake amma idan ya tuna yarda k’irjin Safna yake a
cike sai yaji baya son barin wannan damar. Shi burinsa ko wasa ya yi da su Ya samu relief daga tarin
abinda yake ji a ransa. Ya d’an fusgi leb’ensa sai kuma Ya saka hannu ya murd’a k’ofar ya shiga. Sai da
numfashinsa yaso d’aukewa ganin Safna a kwanta rigingine ba komai a jikinta. Sai sakar masa murmushi
take tana lasar leb’enta. Ta mik’a masa hannunta Amma ya ja ya tsaya ya kasa matsawa kusa da ita.
Mik’ewa ta yi tana girgiza jikinta ta isa kusa da shi sosai. Sai da Moddi ya runtse ido tsabar yarda yake jin
wani yarrr a jikinsa ganin mace a gabansa ba kaya. Bai san kalar abinda ya ji ba abu guda ya sani ya kasa
controlling kansa a matsayinsa na mutum mai lafiya kuma matashi mai tashe balaga. A wannan daren ya
san Safna cikin wani irin gigitaccen yanayin da bai tab’a shiga cikinsa ba, bai tab’a zaton akwai irin abinda
ya ji a duniya ba. Sai da komai Ya lafa sannan tsoron Allah ya shige shi, ya dinga Jin tsanar kansa da
kunyar Allah da Didi ma gaba d’aya. Amma ya lura sam Safna ba abinda ya dameta ya kuma san ba shine
mutum na farko da ya fara saninta ba, don a bu’de take. Murmushi Kawai take saki cikin zallar farin ciki ta
sake d’anewa cinyarsa tana kama leb’ensa k’ok’arin tureta yake Amma ta kasa ba shi dama ta hanyar yi
masa ra’da a kunnensa tana furta “You are so sweet ango na, yau kam ka shayar da ni abinda wani namiji
bai tab’a shayar da ni ba, a yau na San kai ne maha’din Safna kai ka cancanta ka zama Mijina don ka zuk’e
min dukkan sha’awata, na yaba Imaam kuma ina fatan nan gaba ka’dan ka zama Mijina. Ashe duk sauran
maza Lami suke kai ne cikakken namiji kuma Ingarma.” Ta fa’da tana lumshe idonta a kunne ta sake ra’da
masa “I need more Imaam!” Ya yi saurin janyeta daga jikinta yana furta “Astagfirullah Safna ba zan iya ba,
ba zan iya auren matar da bata iya rik’e budurcinta ba Kamila zan aura…” wata dariya ta saki kafin ta
sake shigewa jikinsa ta furta “Kada ma ka fara wannan mafarkin Imaam, don kai ka’dai aka halicci Safna
duk macen da ta ce zata rab’eka sunanta gawa ina tabbatar maka, kada ma ka fara wallahi da gaske
nake…” ta fa’da Har da hawayenta sannan ta k’ashi wata zuma a harshenta da bai San ko ta Mecece ba
ta kamo
Nasa harshen ta cafka suna tsotson zumar tare. Sai da suka shanye sannan ta lumshe idonta a kunne ta
ce “Ka San zumar mecece?” Ya girgiza kai sai ta yi murmushi ta ce “Manta Uwa kenan, ka zama nawa
Imaam, ka k’addara a duniya ba kai ba wata mace har abada sai sai Safna, wannan kayan nawa ne ni
ka’dai…” ta fa’da tana jan mazugin wandonsa, da sauri ya ture hannunta yana jin kansa yana wani irin
sarà masa ganin yarda lokaci ya ja. Ya san Didi tana can tana nemansa. Kayansa ya d’auka ya zura don ko
wanka ba zai tsaya yi ba ya yi a gida. Burinsa kawai isa gida. Safna ta dinga binsa da kallo tana sakin
murmushi Har ya kai k’ofa ta d’aga masa wayarta tana nuna masa screen D’in wayar. Ta furta “Na samu
abinda zai ‘debe min kewa ko na tura maka?” Ya waro ido ganin vedion fasik’ancin da suka gama aikatawa
yanzu Amma fuskarsa kawai ake gani. K’ok’arin waftar wayar ya yi
Amma ta hana shi tayi sauri saka lock tana furta “Ko ka goge a wayar yana nan a email d’ina, don shi zai
zame min makami a wajen danginka na dole ka aure ni ko na sake shi a duniya.” Sai ta saki murmushi ta
taso a yarda take ta sake shiga
Jikinsa ta manna masa kiss tana furta “I need more….” Abubuwan da take masa ne ya saka shi sake biye
mata don ya kasa controlling kansa ji yake kamar Safna sarrafa shi take da remote. Baya iya k’in bin
umarninta ranar kam Safna bata sarara masa ba sai da ta ji ana Assalatu ya ware ido yana kallonta a
hankali ya furta “Didi Safna, yau sai ta kusa kashe ni.” Safna ta tab’e baki tana furta “Dido, don Allah ka
k’yaleni da wata Didi mu mori duniyar mu. Mu je mu yi wanka.” Haka ya sake binta toilet. Sai da ya yi
wankan sannan ta k’yaleshi ya saka cukurku’daddun kayansa da suke ta zabga k’amshinta ya fice da sauri
don baya son ta sake jan hankalinsa.
Tsoronsa bai sake girmama ba, sai da Ya isa k’ofar gidansu. Ya ji zuciyarsa ta buga da sauri ya saka hannu
ya buga gidan. Don Didi ta hana shi key D’in gidan ba don komai ba ta ce tafi son ta dinga jin shigarsa da
fitarsa don ta San lokacin da yake dawowa gidan. Jikinsa a sanyaye ya hau buga gidan. Kusan Minti Biyu
kafin Didi ta bu’de. A idonta ya hango rashin barcinta da tarin fatgabar da take ciki. Tsoro mabayyani a
saman idon. Sai ya ga ta lumshe ido ta kuma ja hannunsa ta mayar da gidan ta rufe. A tsakar gida ta saki
hannunsa sannan ta koma saman sallayarta ta tayar da sallah ba tare da ta furta masa komai ba. Kan dole
shima ya yi alwala yana tunanin Ya yi sallahr isha’i ko bai yi ba. Zuciayrsa ta tabbatar masa bai yi ba. Sai
ya samu kansa da jin kunyar Allah wace shagala ce ta same shi haka? Wani irin hali yake son jefa kansa?
Ya dinga fusgar gashin kansa. A haka ya yi alwala Ya tada sallah a gefen Didi. A kunyace yake sujjada. Idan
kuma zai rok’i Allah gafara sai ya ji bakinsa ya yi nauyi bai sani ba ko girman laifin da Ya aikata ne yasa
yake jin haka. Didi Har ta sallame Sallahr bata masa masa magana ba. Ta ‘d’ora a Azkar d’inta da ya zame
mata jiki. Jikin bango ya jingina bayansa yana lumshe idonsa haka kawai sai ya samu kansa da zubar
hawaye, da wani irin k’uncin zuciya yana ji a ransa bai kyautawa Didi ba, bai kyautawa irin tarbiyyar da ta
jajirce wajen bashi ba. Har gari ya fara haske bai bar wajen ba, kamar yarda itama Didi bata bar wajen ba
sai dai carbi take ja, tana kuma kallonsa a hankali idanunta duk sun ka’da Sun yi jajur. “Daga ina kake?” Ya
ji ta furta da wata irin tsumammiyar murya da bai San tana da ita ba. A razane ya ‘dago yana kallonta Ya
d’aga harshe yana shirin yi mata k’arya ta furta “Kada ka min k’arya Imamu, idan ka b’oye min ba zaka
b’oyewa Allah ba. Daga wajen Mace kake ko? Ka kai kanka wajen karuwai Ko?” Ta fa’di cikin raunin murya
idanunta suna zubar da hawaye. Kasa magana ya yi sai leb’ensa da yake kakkarwa Ya hau girgiza mata kai.
“Ki yi hak’uri Didi, ba karuwa ba ce matar da zan aura ce, don Allah ki yi hak’uri a kuma yi maganar auren
mu da ita a satin nan, ni kaina bana son sab’awa Ubangiji da nake, na