Author : Meerah Category : African Stories & Novels
a jiyar zuciya ya sauke yace "bata mutuba saidai haryanzu babu tabbacin numfashinta zai dawo, domin idan ta sauke daya zata iyayin awa uku kafin tasake sauke wani, kuci gaba da yimata adu'a domin ita kad'ai take buk'ata a wajenku" Yana gama fad'in haka yayi tafiyar sa, Kamal kam awajen ya fad'i sumamme.
Gimbiya Fulani kuwa sai faman shige da fice take a wajen bokaye dan kada Afra ta farfado domin ta tabbata idanhar ta tashi to kashinta ya bushe domin banda rasa aurenta da zatayi saita fuskanci hukunci mai tsanani a wajen Mai martaba sbd sace Kamal datasa akayi tunyana karami.
Zaune take a wajen boka tanata faman sharar hawaye tace "ka taimakamin kada yarinyar nan ta farfado wlhi idan har ta farka asirina ya tonu kashina ya bushe" boka yayi dariya irin tasu yace "kidaina damuwa indai wannan ne angama zanbaki kullin magani Wanda zakije ki aza akan filon datake kwance akai idan har kika aikata wannan to ita da tashe sai a lahira" hhhhhhh "amma akwai sharad'i" cikin hanzari tace "sharad'in mene fad'i koma menene zanyi matukar bukatata zata biya" kallon ta yayi a natse yace " dole saina kwanta dake sannan aljanu zasusa hannu acikin wannan aiki" a razane ta kalleshi sai a lkcn taji warin dayakeyi maradad'i kauda kanta tayi tace "a'a boka kafad'i wani sharad'in amma ba wannan ba" a fusace yace "tashi kibani waje bazaki had'ani da aljanu ba" ya fad'a cikin b'acin rai, harta tashi tsaye ta fara tafiya Kuma saita tuna abinda zai faru da ita idan taki amincewa, da sauri ta dawo tace "na'amince matukar bukatata zata biya" wangale k'aton bakinsa yayi yana dariya jajayen hakoransa suka bayyana wad'anda suka koma wata kala sbd daud'a,
Tunda abinya faru tsakaninsu gimbiya keta faman amai sbd warinda ta Shaka wajen boka dakyar ta koma gida da kullin mgn daya bata, bayan komawarta ma aman bai tsaya ba tuntanayi sannu sannu harya galabaita ta tafita hayyacinta haka ta kasance cikin kunci da damuwa yau ta aikata abinda bata tabayiba tunda kuruciyar ta, gashi Kuma tarasa lafiyar ta.
Nasir ne zaune a garden abin duniya duk ya taru yayi masa yawa, yanzu shikenan andaura auren Afra da Kamal jiyakeyi aransa dama Afra ta mutu kowama ya huta wata kwallar bakin ciki ya share, duk abinda ke faruwa har yanzu Nasir ba tafi asibiti ba balle yasan halinda ake ciki, yana nan zaune yayi nisa cikin tunani yaji motsin mutum a kusa dashi, a hankali ya sauke idanunsa akan kausar datazo tanata sallama baijitaba, tana batun zama kusa dashi taga yayi saurin mikewa fuska d'aure, itama d'aure fuska tayi cikin kosawa da wulakancin da yake yimata tace "Yaya Nasir laifinme nayi maka haka dazaka tsaneni, menene laifina dannace inasonka? Me Afra tafini dashine? Yaya Nasir wlhi Ina matukar kaunar ka acikin zuciyata" "ya isa haka banasonjin wannan shirmen naki nace banasonki ko anaso dole ne" tsaki yayi yabar wajen cikin b'acin rai, itakam kausar ko ajikin ta acewar ta yanzuma ta fara sonshi Kuma duk hanyarda zata bi ta mallakeshi Koda baya sonta saitabi, tana nan tsaye wani tunani ya fad'o mata arai da gudu ta nufi part dinsu, tana shiga ta iske mahaifiyarta gimbiya Fulani kwance babu lafiya tace "umma sannu yajiki"? Ta amsa mata cikin kulawa da so da kauna domin tana matukar kaunar 'yarta sbd ita kad'ai ta haifa, hawaye kausar ta share cikin shagwab'a tace umma Nasir ne yaketa wulakanta ni dannace ina sonshi murmushi umma tayi tace "kingaji da boyemin kenan, ainadade da gane kina sonshi domin ko a fada mukaje kin dinga kallon sa kenan" sunkuyar da Kai tayi tana murmushi, umma tace "inda wannan ne ki kwantar da hankalinka domin Mai martaba yadade dayimin mgnr ni nace abari saikun kawo kanku da kanku" da sauri kausar tace "umma Mai martaba ya amince da aurenmu"? Murmushi tayi tace "ai tun lkcn da aka fasa aurensa aka daura tare dake awannan wajen bayan mahaifin Afra yayi tafiyar sa awajen daurin auren, amma akace kar afadamuku sai kunfahimci junanku da kanku, shine dalilin da mahaifin Nasir ya turoshi gidannan danku daidaita tsakaninku" wani ihu kausar tasaki ta rungume ummanta da karfi tace "umma yanzu ni matar Yaya Nasir ce"? Tana fad'a tana murmushi, itama umma murmushi takeyi tace "kwarai kuwa kindad'e da aurensa a kanki baki saniba shima bai saniba" d'aga hunnuwa sama tayi tace "Alhamdulillah ashe dama andaura muna aure duk irin wahalar da nakesha akansa", "ehh kausar Nasir mijinkine" da gudu ta shige bedroom d'inta tanata faman tikar rawar murna.
Afra kam saidai muce sauki sai awajen Allah domin kwana biyu ta share a haka tana kwance kamar matatta Abba da umma da sauran mutane duk sunfidda rai da farfado warta domin yanzu daga ummi sai mai martaba da Kamal ne kawai a asibiti sauran duk suntafi acewarsu gawace suke jinya, saidai shi Mai martaba baifaye dad'ewa idan yajeba, acewarsa tunda gimbiya Nafisa da Kamal suna nan toshi basaiya zaunaba,
Ummi da Kamal duk acikin dakin suke kwana kasan cewarsa babban dakine saidai basu faye yin bacci tare ba domin likita yace a kula da ita sosai, wannan dalilin ne yasa idan wani na bacci to wani na zaune yana kula da ita haka sukeyi, yau ummi ce kwance tana kwana shikuma Kamal yana zaune a kujera kusa da ita, daganan bacci b'arawo yayi awon gaba dashi,
A hankali ta bud'e idanunta nan take ta tuna duk abinda yafaru da ita har daurin aurensu, murmushi tayi takalli yadda yake bacci cikin natsuwa sannu a hankali tace "Alhamdulillah a yaunzu kazama mijina Kamal Ina sonka sosai, yunkurawa tayi ta tashi zaune dube dube tafarayi tana neman wayarta ta manta cewa tun acen daji ta barta cikin motarta, hankad'a filo tayi ko zata ganta awajen amma bata ganiba wani kullin mgn ta gani, d'auka tayi cikin rashin sanin komenene ta banye taga ba komai bane sai dakakken iccen Wanda aka aje a matsayin magani, gimbiya Fulani ta fado mata arai nan ta tuna da irin kullin sharrin dataso yiwa kamal, murmushi tayi tace zanyi maganinki Dani kike zancen, kugi taji cikin ta nayi mata gefe d'aya Kuma zafi takeji wajenda aka harbeta, dafe wajen tayi ta tashi ta shiga neman abinci, cikin saa ta ganshi saidai babu ruwa drinks ne kawai a frige, fita tayi waje kozata samu ruwa amma ina ma'ikatane kawai ke yawo acikin asibitin kowa yayi bacci,haka yasa dole ta hakura ta koma, zama tayi ta zuba abincin ta faraci, cikin bacci ummi kejin alamar motsin mutum kusa da ita a hankali ta bube ido, cikin bacci take ganin mutum zaune saidai bata ganin fuska domin tajuya mata baya, Kara bude idanunta tayi dakyau taga tabbas mutum ne ta d'aga kai taga Kamal yanata bacci a kujera, cikinjin tsoro tace wacece da karfi Wanda yayi sanadiyyar farkawar Kamal, lomar data debo takai baki ta jiyo ta hadiye tace "ummi nice yunwa nakeji" da sauri Kamal ya dubi gado yaga babu kowa yace "Afra kece" wata lomar takai baki ta had'iye sannan tace nice Kamal bari ingama cin abinci masifaffiyar yunwa nakeji..
Hamdala suka shigayi suduka itadai banda cin abinci babu abinda takeyi..
Kubiyoni a shafi na k'arshe insha Allah
By
Meerahπππ
Share please πππ
[5/12, 12:28 PM] Meerah π: π€΄π»π€΄π»π€΄π» prince khamal π€΄π€΄π€΄
πΉπΉπΉπΉπΉπΉ
By
πΉπΉπΉ
Meerahπππ
ELEGANT ONLINE WRITER'SβοΈ
Dasunan Allah mairahama Mai jinkai
π
ΏοΈ 5οΈβ£1οΈβ£ -5οΈβ£2οΈβ£
Saukowa yayi da saman kujera ya dawo kusa da ita yace "Afra nayi farincikin ganin farkawarki, alhmdlh Allah na godema" ya fada cikin nuna kulawa da farinciki, hannunta ya jawo ya sumbacesa, fuskar sa d'auke da murmushi, itama murmushi tayi tace "honey yau babbar ranace a wajenmu burinmu ya cika inacikin farinciki sosai" gyaran murya ummi tayi tace "to marasa kunya a gabana babu ko Kara" kallon Kamal tayi tace "tashi kabata wuri taci abincinta" sosa k'eyarsa yayi ya tashi sum sum a kunyace ya zauna, ita dai Afra batace komaiba sai murmushi takeyi tana kallon sa danya bata dariya, kasan cewar ummi bata kallonta tana bayanta..
Washe gari tunda safe asibitin ta cika da mutane domin duk Wanda yaji Afra ta farfado sai yazo, likita ya kammala gwaje gwajen sa ya tabbatar da samun lafiyar ta, babu b'ata lkc ya basu takardar sallahma, Abba yace abashi ita sutafi idan tasamu lfy sai ayi biki ta tare gidan mijinta, haka kuwa akayi Mai martaba da ummi duk sun amince, saidai shikam Kamal baiji dad'in hakan ba, wannan dalilin ne yasa yace zaibi Baba sani gidan sa danya kasance kusa da Afra.
Mai martaba ya yiwa Baba sani goma na arziki, duk da yaso yayi zamansa acikin masarautar Amma firr Baba sani yaki amincewa yace yafi son ya zauna acikin kauyensa, haka ko akayi tare suka tafi da kamal, duk abinda akeyi har yanzu Nasir da khamal basuyiwa juna mgn ba, Kamal yafita harakar sa gaba d'aya, tunda Afra ta bashi lbrn sa, shikuma Nasir haushin Kamal yakeji wannan dalilin ne yasa yaki zuwa asibiti Kuma da suka dawo yaki cemasa yajikinta, hmm wannan kenan.
Suna isa gidan Kamal yaga gida shiru babu kowa yace "Baba Inna bata nan ne? Ina Saude tayi"? Ya jera masa tambayoyi lkc d'aya, baice masa komai ba ya bud'e d'aki ya dauko tabarma ya shimfid'a suka zauna, saida yayi gyaran murya yace "laure dai tana gidan su munrabu, ita Kuma Saude Allah yayi mata rasuwa, innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un Kamal ya shiga maimai tawa, nantake hawaye suka wanke masa fuska, shima Baba yaji mutuwar ta dawo masa sabuwa, tare suka dinga kuka kamar wasu mata, sundad'e a haka daga k'arshe suka jajantawa juna tare da yi musu ta'aziyya, suna gamawa da sauri Kamal ya tashi ya nufi hanyar fita, dakatar dashi Baba yayi ta hanyar tambayar sa inda zashi, bai fad'a masa ba ya daice yanzu zai dawo, baijara yasakeyin mgn ba yayi gaba..
Da fitarsa ya shiga mota ya Kama hanyar kauyensu Inna laure, yayi sa'a kuwa ya tarar da ita a gida, tana ganinsa da murna ta tarbeshi itama maifiyarta da murnanta ta shiga tsokanar sa, shima yana mayar mata, inda sabo yasaba da zolayar kakarsa domin tunyana karami duk sanda yaje gidan saita tsokaneshi, Inna laure ta bashi hakuri harda kukanta domin harcikin ranta take kaunar sa, shima yana kaunarta sosai domin ta bashi kulawa a lkcn da yake bukatar kulawa, ta nuna masa soyayya a lkcn da aka nisantashi da mahaifiyarsa, wannan dalilin ne yasa bazai taba mantawa da itaba Kuma kome zatayi masa bazai gujetaba, yayi musu ta'aziyya sun roki juna gafara daga nan yace ta had'a kayanta yanzu zasu tafi, ba musu kowa ta shiga had'a kayanta domin tagaji da zaman gidan, ga masifar da iya uwani (mahaifiyarta kenan) keyimata akan korar Kamal datasa akayi akan fifikon data nuna akansa, iya uwani taji zafin abin sosai wlhi domin tana kaunar jikanta sosai, bayan ta shirya tsab tayiwa iya sallama suka fita, bakin kofar gida taga motar sa, ta wangale baki tana mamaki, tambayoyi ta shiga jera masa, baice komai ba sai bude mata gidan gaba dayayi yace ta shiga sutafi, ba musu ta shiga yaja suka nufi gida.
Gabanta na fad'uwa sosai sbd tasan halin mijinta sosai da kafiya idan yace bayason abu,
"Mutafi" kamal ya fada Yana kallon ta, ajiyar zuciya ta sauke tace "to" ya shiga gaba tana binsa a baya.
Baba na nan zaune kamar yadda yabarshi, Yana ganinsu ya mike tsaye cikin b'acin rai yace "Kamal meya had'aka da wannan matar kuma"? Murmushi yayi yace "Baba wannan inna tace fa" kallon Inna baba yayi cikin b'acin rai yace ta fice masa a gida, Kamal yace saidai su fita tare amma bazai iyazama acikin gidan ba idan har Inna bata nan, sundad'e kafin baba ya amince tazauna, daga k'arshe dai gidan yakoma kamar da, kowa na cikin farinciki.
Afra kam tasamu sauki sosai rauni ya warke har ansa ranar biki tare dana Nasir, sannu sannu lkc na tafiya ranaku na shudewa lkcn da aka aza yazo hausawa na cewa rana bata karya saidai uwar d'iya taji kunya, ba'a wani shagaliba abikin walima kawai akayi domin Afra ba mace bace maison hayaniya, da wannan dai aka kammala biki amarya Afra ta tare a gidan mijinta acikin masarauta yayinda kausar itama ta tare a gidan Nasir cikin garin kaduna, Nasir kam yadai d'auki zabin iyaye ne kawai badan yanason kausar ba, itakam kausar ta dauki aniyar zama Koda Nasir zaidinga wulakantata agidansa,
Kamal ya gyarawa Baba sani gida ya mayar dashi ginar zamani ya zuba musu kayatattun kayan more rayuwa, sunyi farinciki sosai da wannan.
Afra kam tasamu natsuwa da kwanciyar hankali acikin gidanta, Kamal Yana bata duk wata kulawar data dace, haka ummi tana bata kulawa daidai gwargwado.
Gimbiya fulani kam tuni ta rasu a dalilin ciwon kanjamau data kwaso wajen boka, khairat Kuma ta koma karatu a kasar waje, itama Afra acikin garin Zaria aka sama mata skull taci gaba da karatu, kausar kam ba laifi tana fuskantar rayuwa cikin sauki domin Nasir baya takura mata balaifi Yana sauke mata duk wasu hakkoki nata, a'lak'a mai karfi ta kullu tsakanin Inna laure da ummi haka Daddy da Baba sanusi, suna ziyartar junasu lkc zuwa lkc..
Tammat bihamdulillahi littafi ya cika da godiyar Allah, Ina mika godiyata ga Allah subhanu wata ala daya bani ikon kammala wannan littafi lfy
Ina Mika godiya ta gareku masu comments Allah yasaka da alkhairi Allah yabar zumunci.
Muhad'u a sabon littafina na gaba mai suna MENAHAIFA β οΈβ οΈ horo story
By
Meerahππππ
Share fisabilillah ππ