Author : Meerah Category : African Stories & Novels
aikata irin wannan laifin da ake zarginka dashi ba, wlhi Koda zan rasa komai arayuwata saina fitar dakai acikin wannan halin bazan taba barin ana zarginka akan abinda baka aikata ba.....
Wayarta ta dauko tafara Kiran layin khamal, shiru ba'a daukaba, tunjiya take ta kiransa Amma baya dauka, wasu hawayene suka gangaro mata, kodai khamal yarabu da itane? Dafe kanta tayi, tafara tuna irin cin mutuncin da Abba yayi masa, da korar kare acikin gidannan, kuka tafarayi Mai daga murya, kamar mahaukaciya, umma ce tashigo dakin tana binta da kallo, abin duk ya daure mata kai, kodai Afra nada iskane bata saniba sai yau...
Hawa gadon tayi ta jawo Afra jikinta, tana cewa "lafiyarki Lau kuwa" kallon ta Afra tayi tace "umma khamal ya rabudani yaki daukar wayata tunjiya" tureta umma tayi cikin zafin rai tace ai haka nakeso Allah yakara tayi tsaki tabar dakin...
Afra tayi kuka a ranar kamar ranta zai fita, da kyar tasamu bacci yadau keta..
Afra tazama abin tausayi rabonta da abinci tunjiya, yauma bata da niyyar ci domin halin da take ciki Kamal daine zai iya fitar da ita aciki, gashi yatafi ya barta. Wasu zafafan hawaye ne suka gangaro a fuskar ta, bazan iya rayuwa ba idan har babu Kai khamal...
Wani tunani ne yado mata arai, tashi tayi cikin hanzari ta dauki mayafinta da key din motar ta tafice daga gidan...
Bata tsaya ko inaba sai kauyensu khamal, bakin garkarsu ta tsaya tana tunanin ta shiga kota fasa, saude tagani ta fito daga gidan rike da tulun dibar ruwa da alama rafi zata tafi.
Tana ganin Afra tsaye akofar gidan ta koma da gudu cikin gida, fadawa tayi akan Inna laure dake tsintar wake, "ke meye haka Kuma Zaki fadomin idan nibaki tuna Zaki iya jimin ciwo, aiya dace ki duba Dan dake cikin ki"
"Inna wannan yarinyar ce fa Yar birni nagani a kofar gida", "wacce yarinya Kuma?, Oh!! Ni laure wai meyasa Yan birni sukeda nacin tsiyane duk da ankori khamal din saita dawomin agida to mezanyi mata"?
"Inna shikenan ta rabani da khamal" saude ce ke mgn tanata faman kuka kamar karamar yarinya, Inna Dan Allah kidawomin da khamal wlhi bazan iya rayuwa ba idan Babu shi..
"Ke dallani matsa kibani wuri ai duk lafin kine da kinyi abinda boka yace aida haka bata faruba, kika kiyi kika je wajen wancen sha sha shan"....
"Wlhi Inna ba laifina bane nima naso na kwaci kaina Amma nakasa dan ya fini karfi"...
Gaban Inna laure ne yafadi ganin Afra tsaye tana kallon su Kuma duk taji abinda suke Fadi.
"Ke Kuma meya kawoki haka mayya anace, to karya kikeyi kurwar khamal tafi karfinki.....
Murmushi Afra tayi tana Kara shigowa cikin gidan, tace " dama ban taba yadda da wannan sharrin da kuka yimasaba, ayau asirin ku ya tonu Kuma wlhi saina fallasa ku abainar jama'a. Tana gama fadin haka takama hanyar dakin datasan na khamal ne tashiga, dube dube ta hauyi cen taga wayarsa, ajiyar zuciya ta sauke tare da murmushi, daukar wayar tayi tafice daga gidan ba tare da tabi ta kansuba.....
Ta bude motar ta kenan zata shiga ta hangi ado Yana tafiya, rufe motar tayi ta nufi inda ado yake..
Gaisawa sukayi cikin farinciki, Afra ta kalli Ado tace "Ado wai abinda khamal ya aikata gsky ne ko"?
Nisawa Ado yayi yace "nima banyar da ba kokadan, Ina zargin Inna laure da saude akan abinda yafaru, domin saude tana tsananin son kamal, Koda ace tabbas ya aikata to ba ason ransa bane tirsasasa akayi"
"Nima banyar daba Ado nasan khamal sosai a schl, bazai taba aikata irin wannan danyen aikin ba, Amma zan cigaba da bincike koma menene saina gano gsky, Kuma saina Nemo khamal duk inda yake afadin duniyar nan".....
Anan sukayi sallama takama hanya tashiga mota tabar wajen.
Gida ta nufa cike da farinciki, afalo ta iske umma ta hade rai, itama hade fuska tayi tazo zata wuce ta gabanta taji tace "daga Ina kike"?
Tsayawa tayi batare da tajiyoba tace "daga gidansu nusaiba"
By
๐ Meerah๐๐๐
[3/15, 10:24 AM] Meerah ๐: ๐คด๐ป๐คด๐ป๐คด๐ป prince khamal๐คด๐ป๐คด๐ป๐คด๐ป
๐น๐น๐น๐น๐น
By
๐น๐น๐น
Meerah๐๐
๐น 08068971503
ELEGANT ONLINE WRITER'Sโ๏ธโ๏ธ
Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai
๐
ฟ๏ธ 1๏ธโฃ1๏ธโฃ_1๏ธโฃ2๏ธโฃ
Daki ta shige ba tare da ta Kara cewa komai ba, itama umma binta da kallo kawai tayi..
Akan bed dinta tafada cike da farinciki, murmushi ne take ta famanyi, Allah sarki khamal a yau nasamu hujjar da zan iya bada shaida akanka, Allah ya tsaremin Kai a duk inda kake, Amin...
Mikewa tayi ta nufi kitchen Dan samun abinda taci..
Lokaci tafiya yakeyi, ranaku na gudana, umma da Abba sai faman shirye shirye sukeyi.
Ita Kuma Afra duk abubuwa sunyi mata yawa gashi bincike takeyi a halin yanzu, dan ta San inda khamal yake, ta kasa samu wani lbr Mai dadi akansa, domin ta bayar da cigiyar sa, harda kyauta Mai yawa ga Wanda duk ya ganshi Amma Ba bushi Babu alamar sa.
Wadanda tasa nemansa sun tabba tarmata baya cikin garinnan, domin sun duba lungu da sako Amma basu ganshi ba...
Umma ce tashigo dakin tace "ki tashi maza kishirya ga Wanda Zaki aura nan yazo a falon baki" ficewa tayi ta barta nan zaune....
A jiyar zuciya ta sauke, mikewa tayi ta dau Maya finta rai bace ta fita..
Zaune ta iska shi Yana jiran shigo warta, da sallama ta shiga, kamar bazai ansaba, sai Kuma ya amsa cen ciki batare da ya kalli wajen da take ba...
Zama tayi a kujerar da ke kallon tashi, tana kallon sa, shima ahankali ya dago kansa cikin kosawa da kallon da take masa ya kalleta fuska daure
Murmushi tayi tace "naji dadin zuwan ka sosai Kuma a yanayin ka Dana kalla inada tabbacin burina zaicika"
Tsaki yayi yace "ba wannan ne yakawo niba tirsa sani akayi nazo Kuma nazo Dan haka Kinga tafiya ta" mikewa yayi yafara tafiya, batare da yace mata komai ba.
"Nagode kwarai, naji dadin zuwan ka, bari na rakaka" binsa tayi abaya har wajen motar sa, dakanta ta bude masa ya shiga, daga masa hannu ta dinga yi tana murmushi harya bar gidan....
Daki ta koma cike da farinciki, ba laifi shima ya hadu, Amma bazai taba Kai Kamal ba.
Wayarta ta dauko ta Kara Kiran wannan number kozata dace, haryanzu dai kashe wayar take, wani zafi takeji aranta tarasa dalilin dayasa khamal yaki bude wannan ledar data bashi. Kodai yagani kin kunna wayar ne kawai yakiyi?
Hawaye ne suka gangaro mata, khamal meyasa zakayimin haka? Kodai kadaina sonane shiyasa ka watsar dani??
Kuka takeyi sosai babban tashin hankali ta shine yau saura kwana uku a daura mata aure gashi Kuma khamal yaki kunna wayar balle tasan inda yake..
Tana cikin haka wani tunani yafado mata arai da sauri ta dauki wayarta da Kira wani course mate dinta, Kira daya yadauka.
"Aslm Hashim kana ina yanzu" yace "ganin bakin aikina kamar yadda kika sani", "madallah, Hashim wani aiki nakeson nabaka Dan Allah"
"Wane aikine? Kinsanfa banida isasshen lkc", "karka damu Hashim zan ninkama kudin da zaka samu a wannan aikin da kakeyi"
"Ok wanne aikine"? "Zan turoma wata number yanzu ka bincikamin inda zaa sami Mai wannan wayar"
"Indai wannan ne karki damu aikinane yanzunnan zan bincika Miki", "ok to bari naturoma, saika turomin account number dinka"
Bayan ta turamai bada dadewa ba saiya kirata, " hello!! Hashim ya ake ciki"
"Na duba naga Mai wannan layin Yana cikin garin Zaria" gabanta ne ya fadi "Zaria" tafada azuciyarta batasan mgnr tafito filiba, saijin sa tayi yace "ehh! Acikin garin yake"
"Hashim bansan kowa ba a Zaria, Amma inason Dan Allah ka tayani bincike wanine nake nema", nan ta labarta Mai komai yaji tausayinta sosai
"Karki damu Afra inada wani friend acen zansa shi yabin cikamin komai" taji dadin mgnr sa sosai, kudi ta turamai 2.5million, Kuma ta tabbatar mai idan komai yatafi dai dai zata karamai, yaji dadi sosai, shiyasa yafara aikinsa Babu wasa....
Yau laraba baki na nesa Dana kusa sunzo domin halarta wannan gagarumin biki da aka shirya shi cikin kankanin lkc..
Afra kan sai safa da marwa takeyi a tsakiyar daki, domin tunjiya da sukayi mgn da Hashim bata karajin wani lbr ba awajensa, kota kirashi sai yace mata Wanda yasa aikin Yana cen Yana bincike har yanzu bai gama ba,
Hankalin ta ya tashi sosai, a haka ta share tsawon yina tana saurare Amma Babu wani lbr Mai dadi.
Washe garin ranar alhamis tunda safe ta Kira hashim kamar tayi kuka tace " Hashim gobene fa zaadauramin aure" murmushi yayi yace "karki damu Afra ansamu lbr Mai dadi" itama murmushi tayi cikin zumudi tace "angane inda yake kenan ko"?
"Ehh ya gayamin acikin gidan sarkin garin yake" dafe kirji tayi tace "gidan sarki Kuma"?
"Ehh ina tunanin kamar bauta yakeyi acikin gidan", "bauta kuma? Khamal dinane yake bauta awani gida" hawaye suka gangaro mata, cikin kunci da damuwa tace "Hashim yanzu taya zan iya fitar dashi acikin gidan"
"Hanya mafi sauki da zamubi, itace kema saikin shiga gidan amatsayin baiwa"
"What!!! Baiwa Kuma ni Afra nice zanje wani kazamin gida a matsayin baiwa" ajiyar zuciya ya sauke yace "matukar kinason khamal to dole ne kema ki zama baiwa a dalilin sa, Kuma fa ba a haka Zaki dawwama ba da zarar burinki ya cika to shikenan bauta ta kare"
"Shikenan Hashim zanje, inason ka tsaramin komai gamai da tafiyata, inson samune yau na keson natafi kafin gobe sbd taro zaiyi yawa agidannan"
"Ok zamuyi mgn dashi komai ake ciki zakaji kidai zama cikin shiri", "ok " nan sukayi sallama taci gaba da shirya kayanta,...
Shiru bataji komai ba game da Hashim har magrib tayi hankalin ta ya tashi sosai ganin yadda gidan nasu yacika makil da mutane na nesa Dana kusa, tun tana Kiran Hashim Yana cemata ta Kara jira harya daina daukar wayar ta, ta shiga damuwa sosai ganin yadda al amura ke tafiya, gashi tanason saka kayanta a mota Amma tarasa haryanda zatabi Dan gidan ko Ina mutanene.
Tanan tana jiran Hashim har 12:00am tayi bataji wayar sa ba, cikin tane ke kugin yunwa, fitowa tayi danta samu abinda taci, taga gidan shiru ba motsin kowa alamar sunyi bacci, taji dadi sosai da sauri ta koma dakinta ta dauko jakar kayanta ta fito cikin sanda Kar ajita,
Sannu ahankali ta bude motar ta tasaka kayan ta rufe, ta koma kitchen ta dibi abinci taci...
9:00am saiga Kiran Hashim yashigo wayar ta cikin hanzari ta daga Kiran "ki fito yanzu komai ya daidai ta ke kadai muke jira"
Tayi farinciki sosai, cikin hanzari tayi rubutu ga paper ta ajiye ta bude wayarta ta ciro layinta ta ajiye akan paper din ta dauki wayar ta da Maya finta ta nufi dakin umma....
"Umma zanje na tafo da wasu friends dina suzo biki Kuma basu gane gidanba", "to kiyi sauri karki dade kinsan baason amarya na yawo", "to umma yanzu zan dawo"
Da sauri ta bar gidan, tana fita ta Kira hashim a sabon layinta, Kira daya ya dauka "Hashim ganin a hanya yanzu zan iso.......
By
๐ Meerah๐๐๐๐
Share and comments
[3/15, 10:24 AM] Meerah ๐: ๐คด๐ป๐คด๐ป๐คด๐ป prince khamal๐คด๐ป๐คด๐ป๐คด๐ป
๐น๐น๐น๐น๐น
By
๐น๐น๐น
Meerah๐๐๐
08068971503
ELEGANT ONLINE WRITER'Sโ๏ธโ๏ธ
Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai
๐
ฟ๏ธ 1๏ธโฃ3๏ธโฃ_1๏ธโฃ4๏ธโฃ
Tsaye ta ganshi da alama ita yake jira, parking tayi awajen, shikuma Yana ganinta ya zagayo ya shiga..
"Muje ko" ya fada Yana kallon ta, "tare zamuje kenan", "ehh tare zamuje zan tsaya harsai naga kinshiga gidan sannan nadawo"
Kallon sa tayi tana murmushi, tace "ngd kwarai Hashim Allah ya saka da alkhairi", "ba komai afra, ai dole ne na taimaka miki dannaga guy dinnan ya kamaki dayawa" ya fada ne cikin zolaya.
"Kaidai bari Hashim wlhi bazan iya jure ganin khamal cikin wani haliba, na dau alwashin taimakawa khamal Koda zan rasa komai arayuwata"
"Bazaki rasa komai ba Afra insha Allah Zaki iskeshi lfy ki dawo dashi lfy, iyayenki Kuma bana tunanin zasu iya fushi dake sbd tsabar sonda suke yimiki"
Hmmmm dogon numfashi ta sauke tace "kaidai bari Hashim iyayena sundaina sona tun lkcn da na kawo musu khamal amatsayin Wanda zan aura"
"Basu daina sonki ba Afra Kuma bazasu daina sonki ba, Afra inason kiyi nazari ki fahimci manufar iyayenki, suna sonki sosai, basu son ganinki cikin damuwa, Afra khamal bai dace da babbar yarinya irinkiba, wlhi nayi matukar mamaki daya iya ganin classic baby irinki yace yanaso, sbd ke ba matar talaka bace, ke Yar".........."ya isa haka Hashim" tafada cikinjin zafin maganar sa..
"Khamal bashine ya fara shiga rayuwata ba nice na shiga rayuwar sa, Hashim nice naga khamal nace inason sa ba shine yace yana sonaba".....
Hawayen dake gudana a fuskarta ta share "Hashim nice silar tarwa tsewar rayuwar khamal, nice sanadiyyar da yasa akayi masa sharri akan abinda bai aikata ba, bai taba aikatawa ba...
Khamal mutumin kirki ne Amma a dalilina kowa nayi masa kallon fasiki, khamal ya tashi cikin gata da soyayyar iyaye Amma a dalilina yarasa komai"....
"Afra me khamal yayi maki dakika aikata masa wannan abun"
"A'a Hashim wlhi ban shiga rayuwarsa ba dannaga ya tozarta, wlhi kaunar sa nakeyi tsakani da Allah, tunsanda na fara ganin sa, bansan haka abin zaika sance ba dana hakura da sonda nakeyi masa, sbd ganinsa cikin farinciki yafimin komai arayuwa"
Ajiyar numfashi Hashim ya sauke yace "Afra wai ya akayi kika samu soyayyar wannan guy din dannaga baya kula kowa a schl"
Murmushi tayi tace "wlhi nasha bakar wahala kafinna samu soyayyar sa, harna fidda raina, na daina zuwa wajensa sbd kullum naje baya kulani, idan inayi masa mgn ko kallo na bayayi.
Na dauki tsawon lkc Ina Kai kaina wajen sa Amma baya kulani, tun abokaina na bani shawara akan yadda zansamu soyayyar sa har suka koma cewa na rabuda shi, daga karshe dai mukayi fada dasu sbd na fahimci suna sone kawai surabani dashi..
Dana fahimci dai khamal bazai taba Sona ba arayuwar sa saina hakura na daina zuwa wajens, cikin ikon Allah sai gashi yazo wajena da Kansa, Ashe yawan nacewa Dana keyi a kansa da jure irin wulakancin da yakeyimin yasa Nima yafara Sona bai saniba Saida na daina zuwa wajensa ne yagane sbd ya shiga damuwa rashin ganina, nayi farinciki sosai wlhi awannan rana, tunda ga lkcn soyayya Mai karfi ta kullu tsakanin mu".....
Hmmmm "lallai na jinjina Miki Afra domin wlhi nayi mamaki sosai dana ganku tare, sbd kowa yasan khamal a skull baya kula kowa, Kai ko maza ma baya kulawa balle mata...
Amma kinsan wani abu? Kowa fa ya dauka cewa sbd kudin kune yasa khamal yake sonki, saidai ni abinda ya bani mamaki shine agabana ya taba wula kanta wata yarinya a skull sbd tace tana sonshi Kuma itama babbar yarinya ce kamar ke, kowa Yana ji da ita a skull din, Amma hakan baisa khamal yasota ba"....
Murmushi Afra tayi tace "zeeey kenan ai wannan kowa yasanta a skull din bata da kamun kai, shi Kuma khamal ya tsani ballagazar mace, wadda bata da natsuwa". ...
"Hakane Kuma domin khamal gsky kowa yasan shi a skull yanada kamun kai da riko da addini"
Da wannan firar suka iso garin Zaria, Kai tsaye gidansu abokin Hashim suka nufa, sun tarar dashi agidan sbd yasan da zuwansu,
Kai tsaye wajen mahaifiyar sa yakai su suka gaisheta cikin girma mawa, dayake dama abokin Hashim salim yayi mata bayanin komai tun kafin suzo, Amma bai gaya mata cewa Afra ba baiwar gaske bace...
Bayan ta basu abinci da ruwa sunci, tace "to 'yata tunda kunzo tashi zakiyi naje na hadaki da matar da take Kai bayi gidan sarki"... Jiki asanyaye ta tashi, wajen motar ta taje ta dauki iya abinda zata bukata acen tabar saura cikin motar, Salim ta bawa key din motar tace "ka ajiye min motar nan anan gidan zanzo na dauketa idan natashi bukatar ta"
Amsa yayi yace "insha Allah zan ajiye Miki ita bisa amana"
Kudi masu yawa tabashi, sanna ta ida turawa Hashim sauran kudinsa kamar yadda tayi alkawari, anan tayi sallama dasu ta tafi inda mahaifiyar Salim ke jiranta......
Babban gidane Wanda ya kunshi komai na more rayuwa tun a kofar gida zakasan cewa wannan gidan sarauta ne, Afra dai sai kalle kalle takeyi domin komai na gidan ya birgeta murmushi takeyi, sbd yauce ranar da zata hadu da masoyin ta khamal...
Wajen wata mata aka kaita da alama itace shugabar bayi acikin gidan, ta karbi Afra hannu bibbiyu sbd suna da bukatar bawai asashen gimbiya Fulani....
Babu bata lkc ko aka kaita cen a matsayin hadima wacce zata dinga tsaftace part din gimbiya Fulani.
Ana kaita ko gimbiya Fulani tace ayanzu zata fara aiki, Babu alamun tausayi kokadan afuskarta ....
Haka Afra ta hau shara da goge wurare, abinda bata tabayi ba arayuwar ta, saidai da nikaf tashi go, dan batason khamal yayi saurin ganeta tafi son tayi masa bazata......
Tana cikin aikine tajiyu murya kasa kasa ana cewa "ranki yadade boka ya tabba tarmin idan har prince Yazeed yasha wannan gubar bazai Kara numfashi ba aduniya....
Wata dariya gimbiya Fulani tayi, irin dariyar da mugaye sukeyi idan sukaga alamar nasara......
By
๐ Meerah๐๐๐
Share and comments fisabilillah ๐๐๐๐
[3/15, 10:24 AM] Meerah ๐: ๐คด๐ป๐คด๐ป๐คด๐ป prince khamal๐คด๐ป๐คด๐ป๐คด๐ป
๐น๐น๐น๐น๐น
By
๐น๐น๐น
Meerah๐๐
08068971503
ELEGANT ONLINE WRITER'Sโ๏ธโ๏ธ
๐
ฟ๏ธ 1๏ธโฃ5๏ธโฃ_1๏ธโฃ6๏ธโฃ
"Ni Fulani na rantse sainaga bayanka Yazeed Koda zantafi tsarara, yadda ban haifi namijiba agidannan Babu wadda zata haifawa sarki magaji"
Jikin Afra duk yayi sanyi, "innalillahi" kawai take maimai tawa, dama haka wannan gidan yake?
Tabbas zanyi iya kokarina bazan bari akashe wani Ina gani ba.
"Ranki yadade boka yace asawa prince Yazeed wannan gubar acikin abin shansa, gashi Kuma akwai tsaro Mai karfi a part dinsa"...
"Karki