Chapter 6 Reading PRINCE KHAMAL Boyayyen Sarauta By Meerah READ HAUSA Novels

PRINCE KHAMAL Boyayyen Sarauta By Meerah

Author :  Meerah Category :  African Stories & Novels

Chapter   6 / 8

15K to 18K   out of 23.3K words

hankalinsa wajen ta, ita kadai ake saurare, mai martaba yace "meye alakarki dashi dahar kika jefashi cikin wannan halin"?

Tace "ranka ya dade yanxu xanbaku lbrn kamal tundaga kuruciyar sa" sunji dadin mgnr ta sosai hakan yasa mai martaba ya bada umarnin kowa ya koma cikin fada danjin lbrn kamal....


**** KHAMAL******




Khamal yaro ne mai kokari da hazaka tunyana karami, Baba Sani shine ya tsinci khamal a cikin daji, yaji dadin ganin yaron sosai, sbd Allah bai basu haihuwa ba shida matar sa Inna Laure, sun shafe tsawon shekaru masu yawa dayin aure amma ko ɓatan wata bata taɓa yiba, wannan ne dalilin dayasa sukaji dadin tsintuwar yaron a cewar su, suma yanzu sun zama iyaye, sun nuna mushi so da kauna tamkar ɗanda suka haifa da cikin su, sun sashi makaranta sbd sunga yanada kokari da hazaka, duk da cewa a kauyen ba wanda ya damu da yayi karatun boko.

Haka rayuwarsa ta kasance harya kammala karatunsa na primary, babu ɓata lkc suka biya masa yaje makarantar kwana (boarding) yana aji biyu ne Allah ya bawa Inna Laure ciki ta haifi ɗiyar ta wadda taci suna Saude, haka rayuwa taci gaba da tafiya har khamal ya gama secondry, bayan saka makon jarabawar su yafito, khamal yaci jarabawar sosai, bakaramin daɗi iyayensa sukajiba saidai suna son yaci gaba da karatu amma basu da zarahi

Saida khamal yayi shekara ukku da gama secondry sannan Allah ya bawa Baba Sani ikon samun amfanin gona mai yawa, sune yasaida harda ɗayan gonarsa, yacika ya biyawa khamal yayi karatu, inda ya karance bangaren (health).

A haka rayuwar sa ta kasance, yana gab da kammala karatu ni kuma na shiga skull din course daya muke karatu da shi, saidai shi ya kusa gamawa nikuma a lkc nafara, ananne Allah ya hadamu muka farason junanmu...

Bayan ya kammala karatunsa ne muka yanke shawarar yazo gidanmu danya nemi izinin aurena, saidai anyi rashin sa'a domin mahaifina yace bazai bawa talaka aurena ba, duk da haka bamu rabuba sbd muna tsananin son junanmu, domin kuwa har kauyen su nake xuwa muyi hira, a she kanwarsa Saude tana masifar sonsa tun tana boyewa harta fito fili ta fadamasa, yace mata shi yanada wadda yake so kuma ita xai aura, wannan furucin yayi matukar ɓatawa Inna Laure rai, daga nan suka dinga shiga bokaye dan khamal ya farason Saude, saidai hakan bata faruba domin nidashi kullum kara sonjunanmu mukeyi....

Inna Laure macece mai masifar son abin duniya wannan dalilin ne yasa ta dinga sa Saude karɓar kudin samari, da hakane tasamu ciki, inna Laure bataji haushin ganin cikin ba sbd tana tunanin wata damace suka samu wadda Baba Sani zai tirsasa khamal auren Saude, saidai basuci nasaraba domin Baba naji abinda ya faru saiya kori khamal batare da yayi bincike ba....

A yanxu haka nasan wanda yayi mata ciki, wani saurayinta ne mai suma Dauda, shiya fadamin da bakinsa cewa shine yayi mata ciki"

Dogon numfashi Daddy ya sauke lkc ɗaya yaji kewar ɗansa ta dawomai, meyasa shima ya yankewa khamal hukunci ba tare da yayi bincike ba......

BY

MEERAH💞💞💞💞
[3/30, 1:44 PM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal 🤴🤴🤴


🌹🌹🌹🌹🌹🌹



By

🌹🌹🌹
Meerah💞💞💞💞
08068971503



ELEGANT ONLINE WRITER'S ✍️✍️


Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai



🅿️ 3️⃣9️⃣-4️⃣0️⃣



Mahaifin Nasir ne ya fara mgn da cewa "da farko dai muna baku hakuri game da abubuwanda suka faru a baya" nan ya faɗa musu duk abinda ya faru tun haɗuwarsu da khamal har zuwan Afra har ɓatan khamal, basu ɓoye musu komai ba, daga karshe yace "munzo nan ne dan nemawa ɗanmu khamal auren Afra, idan ya dawo sai a ɗaura aure",

Abba ya ƙara gyara zaman sa yace "bakuyi laifin komai ba, duk abinda ya faru laifinane, nine na matsa sai anyi wannan auren, dan haka ina kara baku hakuri, kuyi hakuri da abinda ya faru, sannan idan har Afra tanason khamal to na bawa ɗanku auren ta" murmushi sukayi gaba ɗaya, mahaifin Nasir yace "muna godiya sosai Allah yasa hakan shiyafi alkhairi".

Mai martaba yayi gyaran murya yace "Da farko dai ina nemawa Afra gafara a wajenku, sbd duk abinda tayi tayi ne danta ceci ɗana khamal, nagode!! nagode!! sosai Afra Allah ya taimakeki fiye da yadda kika taimaki ɗana" murmushi Abba yayi yace " ranka yadade Afra batayi muna laifin komai ba, ko kaɗan bamu riketa a zuciyarmu ba sbd laifin mune, nine naso cutar da rayuwarta ta hanyar haɗata da wanda bata so,na gane kuskurena, wlhi a yanzu koda khamal ba ɗan kowa bane zan yadda na aura mata shi tunda shi takeso"

Nasir kam yaji haushin mgnr Abba sosai musamman wajen da yace bashi Afra ke soba.
Ummi tace " ina neman alfarma a wajenku, inason ku bani Afra na tafi da ita, idan khamal ya dawo sai tadawo ayi mgnr auren su"

Ajiyar zuciya Abba ya sauke yace "tabbas da nan da cen duk ɗaya ne a wajena banida matsala da zuwanta cen, saidai inason abari ta kammala kara tunta, idan ta kammala sai ayi mgnr auren su" mai martaba yace "ba komai ta zauna anan taci gaba da karatunta, sannan aure baya hana karatu haka karatu baya hana aure, ko bayan auren zata iya cigaba da karatunta"

Kowa ya amince da mgnr mai martaba, antsaida mgn cewa da khamal ya dawo za'a daura auren....

Da haka suka cigaba da hirarsu cikin farinciki, sun dade a gidan kafin sutafi, gidansu Nasir suka kwana, washe gari tunda safe suka nufi garin zaria.

Afra kam suna tafiya ɗakinta ta koma ta kira Hashim domin ita ta matsu basu tafiba tasamu taji halin da masoyin ta yake ciki, kira daya ya dauka da sallama, amsawa tayi a takaice cikin raunin murya tace "Hashim ya ake ciki" ajiyar zuciya ya sauke yace" Afra gsky akwai damuwa" gabantane yayi mummunan faɗuwa cikin tashin hankali tace "meya sameshi" saida yayi shiru na ɗan lkc yana tunanin yadda zaifara yi mata bayani,yace "Afra Khmal yana cikin tashin hankali, sbd yana cikin wani daji mai matukar haɗarin gaske, domin duk wasu mugayen mutane acikin dajin suke, sbd yana da wuraren ɓoyo, ba lallai neba ace khamal yana nan raye acikin wannan dajin, idan kuma yana raye to tabbas yana cikin mawuyacin hali".




By

Meerah💞💞💞💞
[3/30, 1:44 PM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal🤴🏻🤴🏻🤴🏻



🌹🌹🌹🌹🌹🌹



By

🌹🌹🌹
Meerah💞💞💞
08068971503



ELEGANT ONLINE WRITER'S ✍️✍️



Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai



🅿️ 3️⃣7️⃣-3️⃣8️⃣




Hawayen fuskar sa ya share yace "Allah sarki son kayafemin wannan laifin dana aikata, na kori ɗana, kuma farincikin, tabbas khamal kaine rayuwata idan babu kai to tabbas zan rayune tamkar gawa a cikin duniyar nan, kayi hakuri ka gafarceni na tabka babban kuskure a rayuwa ta" kallon Afra yayi yace "ngd sosai ƴata, ngd da irin kulawar da kika bawa ɗana, bazan taba mantawa da karamcin da kikayi muna ba, insha Allah zaki rayu tare da khamal, ni zantsaya muku komai rintsi, Allah dai ya bayyana shi" kukane yaci karfinsa ya kasa ida mgnr.

Itama gimbiya Nafisa kuka takeyi sosai da kyar tayi karfin halin cewa "ranka yadade yanzu ba lkcn dogon surutu bane, kamata yayi kasa anemo munashi duk inda yashiga"

Batare da ɓata lkc ba mai martaba ya bada umarnin aje anemosa duk inda yake, haka akayi ko, fadawa da police duk sunbazu ko ina lungu da sako acikin garin zaria, saidai kashhhhh, ba'asame shiba, har ƙauyukan garin saida aka duba amma babushi babu alamar sa...

Mai martaba da gimbiya Nafisa sunkara shiga cikin tashin hankali mara misaltuwa, khairat da kausar ma sunzama abintausayi kallo daya zakayi musu kasan cewa sunacikin matsananciyar damuwa...

Afra taso ta koma gidansu Salim Amma ummi ta hanata zuwa, badan tasoba ta kwana a gidan cikin kunci da damuwa.

Washe gari haka kowa ya tashi a gidan bamai kuzari kowa jan jikin sa kawai yakeyi babu kuzari, shikan Nasir yana cikin farinciki sosai dan a cewar sa gara kowa yarasa, tunda shi Afra bata sonsa Kuma iyayensa sonce ko ita daice nace a duniya bazai aure taba, to shima khamal bazai aureta ba, hmmmm Nasir kenan kamanta da hukuncin Allah kenan.

Mamy kam tunda taga Afra taji dalilin zuwanta, hankalinta ya tashi sosai domin ta tabbatar sai Afra ta tona mata a Siri, gashi ta kasa ganinta balle ta roketa ta rufa mata asiri, itama jakadiya duk abubuwa sun da gulemata gaba ɗaya dabararta ta ɓace domin ta tabbata saitaje kurkuku idan asirinsu ya tonu.....

Afra ce zaune a ɗakin da ummi ta bata, wanda ke kusa da ɗakin khairat, tunani takeyi taya zata Nemo khamal? Nan take ta tuna da kyautar data bashi, da sauri ta dauki wayar ta tahau Kiran layin amma a kashe, mikewa tayi da sauri ta fita daga d'akin, a falo ta tarar da ummi da khairat zaune kowanne da tunanin da yakeyi.

Ummi na ganinta tace "ƴata kinfito"? cikin kulawa Afra tace "ehh ummi" shafa bayan kanta tayi cikin jin kunya tace "ummi inason naje part din khamal na duba wani abu" gyada mata kai tayi alamar tatafi kawai batare da tace komai ba, kallon khausar Afra tayi tace "khausar muje ki rakani mana" tashi tayi tabi bayanta suka tafi.

Suna zuwa kai tsaye dakinsa ta shiga ta hau bincike, amma bataga komai ba sai wayar sa dayake amfani da ita, "Aunty mekike nema ne? naga sai bincike kikeyi bakice na tayaki ba"

Murmushi tayi tace "wata leda nake nema wadda na bashi lkcn da zamu rabu dashi a k'auye" "leda Kuma Aunty wacce irin leda?, menene aciki"? Murmushi Afra tayi tace "wata babbar wayace aciki da kudin da zaiyi amfani dasu a hanya, shine na bashi danna dinga sanin duk halin da yake ciki, saidai haryanzu bai kunna wayar ba domin nakira wayar kashe shine nazo na duba koya barta a gida, gashi na duba ko Ina bangan taba"

"Karki damu Aunty yaya Yana matukar kaunarki bazai taɓa barin kyautar da tafito a wajenki ba, murmushi sukayi cike da kaunar junansu, part d'in ummi suka koma, suna zuwa ummi ta kalli Afra tace "daughter yadace ki koma wajen iyayenki kinemi gafarar su" sunkuyar da Kai Afra tayi tace "dama inason na koma amma nafison sai anga khamal sannan" murmushi ummi tayi irin nasu na manya tace "a'a daughter bazai yiyuba gobe insha Allah zamuje wajen iyayenki, nida kaina zan nema miki gafarar su sannan na nemi alfarmar abani ke kidawo nan har khamal ya dawo"

Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta, kunya duk ta kamata, ba tare da tace komai ba ta tashi tana murmushi, itama ummi murmushin takeyi, harda khairat dake kallon su ba tare da tace komai ba sai murmushi kawai.

Afra na komawa daki ta dauki wayar ta tashiga Kiran Hashim, ring d'aya a nabiyu ya dauka da sallama, ansawa tayi suka gaisa cikin girmamawa, tace masa yasake bincika mata wannan number daya bincika mata kwanaki, nan ta fad'a nasa duk abinda ke faruwa, ya tausaya mata sosai aransa yace " Allah sarki Afra samun masoyiya irinki a wannan zamanin abune Mai matukar wahala, ya tabbatar mata da cewa zai bincika mata.

Washe gari Mai martaba da ummi harda khairat da khausar ne suka raka Afra zuwa gida, tare da sauran bayi, motoci biyar suka dauka sai garin kaduna, a gidan su Nasir suka sauka suka tafi tare da iyayen sa harda shi kansa..

Umma da Abba zaune suke a falo cikin kunci da damuwa, wayar Abba ce ta hau ruri ganin sunan Maigadi ne yasa ya dauka a kasalance, yace "kabarsu su shigo ko suwanene" kashe wayar yayi batare da yaji abinda Mai gadi zaifad'a ba.

Karar motocine ta cika gidan gaba daya, ganin haka yasa su umma fitowa Dan suga meke shirin faruwa, suna fitowa sukaga motoci sai shigowa sukeyi, galala suka tsaya suna kallon ikon Allah.

Afra ce ta fara fitowa da gudu ta karasa wajen iyayenta tayi hugging dinsu, Suma cikin farinciki suka rungumeta suna murmushi, "Afra inakika shiga kika barmu? Kiyi hakuri my daughter naso na cutar da rayuwarki ta hanyar had'aki da Wanda bakiso" Abba ne ya fad'a Yana share hawayen sa, kafin Afra tace wani abu karaf idanun sa suka sauka kan mutanen dake wajen, gabansa ne yayi mummunan faduwa ganin amininsa wato mahaifin Nasir, harda shi kanshi Nasir d'in, daure fuska yayi lkc guda yana shirin yin maganane idanun sa suka sauka kan Mai martaba, zaro idanunsa yayi cikin in ina yace "Afra wanene wannan mai Kama da khamal"?

"Ma haifinsane" ta fad'a tana kallon Abba, kunya duk ta gama Kama Abba, gaishesa yayi cikin girmamawa yace su shiga ciki, shiga sukayi kowannen su Yana yaba kyawon gidan da tsaruwar sa, tabbas gidan ya had'u iya had'uwa, ya wadatu da komai na more rayuwa.....



By

Meerah💞💞💞💞
[3/30, 1:44 PM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal 🤴🤴🤴



🌹🌹🌹🌹🌹



By

🌹🌹🌹
Meerah💞💞💞
08068971503



ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️✍️



Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai




🅿️ 4️⃣1️⃣-4️⃣2️⃣



Kuka takeyi sosai a ɗakinta, wanda yatayar da hankalin su umma dake falo zaune, da sauri suka shigo ɗakin, rungume ta umma tayi tace "daughter meya sameki? me akayi miki"? lkc ɗaya tajera mata tambayoyin.

"Umma khamal ne" tayi shiru bata ce komai ba, cikin tashin hamkali umma tace "meya sami khamal ɗin"? "umma waii......." tayi shiru takasa faɗar abinda Hashim ya faɗa mata, sau kuka takeyi, cikin ɗaga murya Abba yace "zaki faɗamuna gsky ko kuwa"? bata ɓoye musu komai ba ta faɗa musu yadda sukayi da Hashim, innalillahi wa'inna ilaihiraji'un kawai su umma ke maimai tawa, jikin umma duk yayi sanyi, hawaye nabin fuskar ta tace duk laifin kane Alhaji daka yadda anyi aurennan tun farko da duk haka bata faruba"

Dafa kafaɗar Afra yayi yace ki kwantar da hankalinki ƴata insha Allah zannemo mikishi duk inda ya shiga" kallon sa tayi tace "Abba dan Allah kabarni naje na nemoshi wlhi idan nazauna a gida zuciyata zata iya bugawa" Cikin mamakin ta Abba yace "Afra bakida hankali ne, taya zakice na barki kitafi cikin wannan dajin kina mace, to babu inda zakije, ni zansa a nemosa duk inda ya shiga, saidai banason kifaɗawa iyayensa halinda ake ciki domin na fahimci suna matuƙar sonsa, idan kika sanar dasu zaki iya jefasu cikin wani hali" wayar sa ya ɗauko ya kira police yasanar dasu halinda ake ciki, ya tabbatar musu idanhar suka samo shi a raye to zaibasu makudan kuɗaɗe, yana gamawa ya kalli Afra yace ƴata ki kwantar da hankalinki insha Allah zasu dawo dashi, sundaɗe a ɗakin suna lallaɓata har bacci ya ɗauketa, a ɗakin umma ta kwana tare da ita, tana kula da duk wani motsinta, shima Abba bawani kwanan kirki yayiba domin kusan ma tare suka kwana a ɗakin suna kula da ƴarlelensu...

Washe gari Afra ta tashi da matsanancin rashin lfy, ga aman jini datake tayi, da sauri suka dauketa sai a sibiti, likita ya dubata sosai, daga karshe dai ya tabbatar musu tanada ciyon zuciya, idan har ba'ayi mata abinda take soba to zuciyar ta zata iya bugawa, sbd ciwon yaci karfinta..

Yini ɗaya ta share harda dare kafin ta farka sbd magunguna da allurai masu karfi da akayi mata, washe gari da farkawar ta abinda tafara faɗi shine " Abba anga khamal" murmushin karfin hali yayi yace ƴata ki kwantar da hankalinki insha Allah khamal yana cikin koshin lfy, zai dawo gareki" hawaye na bin fuskarta tace " Abba dan Allah kabarni naje neman sa" tunawa yayi da mgnr likita badan yasoba yace "Afra idanna barki kije zakiyi farinciki"? da sauri ta amsa da "ehh Abba, zanyi farinciki sosai" tafaɗa tana murmushi, shima murmushi yayi yace "shikenan dakinji sauki zaki tafi" da sauri ta mike tsaye tace "Abba naji sauki fa lfy ta lau" da kallon mamaki ya bita yace "a'a daughter kibari ki kara jin sauki sai a sallamemu, likita ne ya shigo ya dubata yace jiki yayi kyau sosai za'a iya sallamar su, haka ko akayi Abba ya shirya mata tafiyar tare wasu jami'ai guda biyar, babbar damuwar sa shine haryanxu waɗanda suka je da farko babu su babu lbrn su, badan yasoba haka ya hakura dole ya barsu suka tafi...



By

Meerah💞💞💞💞
[3/30, 1:44 PM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal 🤴🏻🤴🏻🤴🏻



🌹🌹🌹🌹🌹



By

🌹🌹🌹
Meerah💞💞💞
08068971503



ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️✍️



Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai



🅿️ 4️⃣3️⃣-4️⃣4️⃣



Kwanan su Afra biyu da tafiya shiru babu lbrn su, idan aka Kira wayarta tun tana ringing ba'a d'auka harta Kai saidai aji wayar kashe, iyayenta sunshiga cikin damuwa sosai, Abba ya kira mahaifin Nasir yasanar dashi halinda akeciki, Mai martaba da kansa yazo kaduna ya jajantawa Abba yayi masa alk'awarin zaisa a nemosu duk inda suke.

Haka ko akayi Mai martaba ya tura mutane masu d'inbin yawa ciki ko harda fadawa da jami'ai saidai kash Babu lbr mai dad'i sun tarar da gawawwakin Jami an da Abba ya tura akan hanya wasu ko acikin daji Amma basuga Afra ba sunyi yawo sosai a cikin dajin Amma Babu alamar akwai wata rayuwa acikin dajin, da haka suka koma gida jiki Babu kwari suka sanar da mai martaba halinda ake ciki, aranan anyi koke koke a gidan, hakama gidansu Afra abin ba'a mgn..

B'angaren Afra kuwa aranar suna shiga cikin dajin suka tarar da wasu manyan y'an ta adda suka k'wace komai nasu suka kashe Jami an baki daya ita Kuma suka kaita wani bayan dutse suka ajiye ta, shugabansu yayi niyyar keta mata haddi Amma saiya fasa yace sukai ta su ajeyeta, tayi kuka sosai tayi musu magiya su kyaleta Amma fir suka k'i, dare nayi ta duba taga kowansu yayi bacci, a hankali ta dinga tafiya da sand'a tana ganin tabar wajen ta fara gudu, muryar wani taji yana cewa gatacen ta gudu aiko ba shiri ta K'ara gudu, sun

6 / 8