Author : Meerah Category : African Stories & Novels
zan zubawa yarima wannan gubar matukar zaku samamin hanyar da zan iya shiga part dinshi"
Ajiyar zuciya jakadiya ta sauke tace "indai wannan ne toba damuwa kibani nan zuwa gobe zanbi duk hanyar da zanbi danki shiga part din" fulani dai batace komai ba sbd ta yadda da jakadiyar ta 100%
Yana farkawa daddy ya kalleshi yace "son wacece wannan afrar ne datake son ta cutarmin da gudan jinina", murmushin yake yayi yace "Daddy itace wannan yarinyar wadda nabaka lbrn ta kwanaki" tashi yayi yana kokarin ficewa a dakin ummi tace "son ina zakaje Kuma kaida baka da lfy"?
Murmushi yayi Wanda ya Kara fito da kyansa fili yace "ummi naji sauki fa sosai lafiya ta Lau" itama murmushi tayi tace "duk da haka kadawo ka zauna zamuyi mgn dakai" baice komai ba ya dawo ya zauna, ummi ta kallesa tace "son kayi mana bayanin komai gameda yarinyar gobe insha Allah zamuje munema maka aurenta" gabansa ne yayi mummunan faduwa da sauri yace a'a basai kunje ba sbd tariga tayi aure"
A jiyar zuciya Nasir ya sauke jin furucin khamal lallai dolene ya tashi tsaye idan ba hakaba yanaji Yana gani zai rasa Afra.....
By
Meerah💞💞💞
More comments more typing
[3/30, 1:44 PM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal 🤴🤴🤴
🌹🌹🌹🌹🌹
By
🌹🌹🌹
Meerah💞💞💞💞
08068971503
ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️✍️
Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai
🅿️ 3️⃣1️⃣_3️⃣2️⃣
Zaune khamal yake tare da Baba sanusi a gidan sa dake cikin masarautar, sbd Baba Sanusi yace masa yana son mgn dashi shiyasa ya bishi gidanshi, kallon sa yayi yace "Yazeed inason ka tsaya ka natsu akan abinda zan gaya maka, khamal na yarda da tarbiyyar ka halayenka da dabi'unka, inason kasan da cewa wannan masarautar tanada ka'idodi, dole ne ga duk Wanda zaizama sarki a sameshi da nagarta, wannan masautar batayi sassauci ba ga duk wanda yake shirin zama sarki kuma aka kamashi da laifi wanda zai iya zubarwa da masarautar nan mutunci, hukuncin da akayanke akansa shine kora domin bazai gaji sarki ba Kuma 'ya 'yan sama bazasuyi sarauta ba, kaji wannan kadan kenan daga cikin hukuncin da aka tana darwa wanda ya aikata wani mummunan laifi, sannan bin doka wajibine ga kowa musamman ma sarki dole yabi doka Koda kuwa shikad'aine d'ansa"
Khamal kam jikinsa yayi sanyi sosai duk da sanyin ac dake ratsa ko Ina a falon bai hanashi yin gumiba muryar Baba Sanusi yaji yana cewa "khamal inason kafadi gsky gobe komai dad'inta komai d'acinta kada kaji tsoro" khamal kam bai iya cewa komai ba, sunjima a wajen Baba Sanusi yana kara masa karfin gwaiwa, da bashi shawar warinda suka dace dashi, daga hakanan sukayi sallama.
A bangaren gimbiya fulani kuwa jakadiya tagama komai Afra kawai ake jira ta kaiwa yarima abincin sa na dare, babu b'ata lkc ko ta shirya tsaff saidai kuma tanajin matsananciyar damuwa, har zata fita ta tunada gargadin da Nasir yayi mata akan karta kuskura ta bayyanawa Kamal kanta idan kuma taje to tabbas zai gayawa kowa abinda khamal ya aikata, gabanta ne ya shiga dukan uku uku nan take tsoro da fargaba suka kamata, Kuma ba damar taki cika umarnin gimbiya fulani, jiki ba kwari ta dauki bakin abinda take shafawa a fuska ta saka nikaf ta fita..
Zaune khamal yake a k'ayataccen falon sa, dumawa da kunci sunyi masa yawa, har cikin ransa yanajin kunyar yadda zai bayyanawa mutane cewa kazafi akayi masa bashi ya aikata ba, hawayen daya ke gangaro masa ya share, da sauri ya daga kansa danjin kanshin turaren Afra a cikin falon sa, tsaye ya mike yafara takawa zuwa inda take tsaye, ita Kuma mutuwar tsaye tayi ta kasa daga kafarta, muryar shi taji Yana cewa " Afra kece " ya fada Yana murmushi, har cikin ransa yakejin farinciki, hannu ya daga dan ya cire mata nikaf d'in.
A razane yaja baya da karfi ganin yadda fuskarta ta koma abin tsoro, tana ganin ya razana tace "khamal kada kaji tsoro nice Afra d'inka nice Afra, ganin sa kawai tayi yana kokarin zubewa a wajen, da sauri ta rikeshi ya fada jikinta ba numfashi, ta tsorata sosai da ganinsa haka, ihu ta kurma duk fadawan part dinsa suka shigo da karfi, Kama Afra sukayi suka sakata a kurkuku shi Kuma khamal aka wuce dashi asibiti.
Nasir yaji dadi sosai da ganin halin da khamal yake ciki domin shi a wajensa wata babbar damace awajensa, a fili ya furta, Allah ya kaimu gobe khamal tabbas gobe zaka fada cikin tarkona, wata mahaukaciyar dariya yayi irinta mugayen mutane idan suka ga alamar nasara....
Ummi najin halinda d'anta yake ciki da sauri tanufi asibiti, tana zuwa ta tarar likita na dubashi, dole ta hakura badan tasoba ta zauna jiran fitowarsa tana nan zaune saiga Mai martaba da gimbiya fulani har da Nasir da sauran fadawan sarki.
Likita ya tabbatar musu cewa lfy Lau yake torone kawai saidai yayi masa allurai masu karfi zai iya dadewa bai farka ba.
By
Meerah💞💞💞💞
https://chat.whatsapp.com/CdUQrjfQGnNKkl6cH8WwUL
[3/30, 1:44 PM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal🤴🏻🤴🏻🤴🏻
🌹🌹🌹🌹🌹
By
🌹🌹🌹
Meerah💞💞💞
08968971503
ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️✍️
Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai
🅿️ 2️⃣9️⃣_3️⃣0️⃣
Mai martaba yayi gyaran murya yace "Yazeed dole ne kagaya mana inda yarinyar nan take domin bazamu iya ganinka cikin wannan halin ba mu kyaleka" baice komai ba, fulani dake zaune a wajen tace "ni a ganina a kira wannan dattijon da aka samesu tare wata kila ya fadamashi wata magana game da yarinyar nan" gimbiya Nafisa tace "hakane gimbiya tunda munyi munyi ya fadamuna yaki, Kuma yakasa cire ta aranshi"
Mai martaba yasake kallon khamal a karo na biyu yace "son yanzu kana ganin matsayi na a wajenka da kima ta basu kai ka gayamin damuwar ka ba"? Jiki a sanyaye khamal ya kalli iyayen sa da Nasir dayake zaune a wajen tundazu baice komai ba, a hankali ya buda bakin sa yace "daddy ummi, ya kalli gimbiya fulani yace yace mamy banida kowa a duniyar nan a yanzu sama daku kune farinciki na, ku nake kallo naji sanyi a raina, idan ina tare daku to banida wata damuwa a rayuwa ta, tabbas kune kuka haifeni, yayinda wasu suka raineni, suma Ina matukar kaunar su a rayuwata sbd sunban kulawa sosai, sun Saida kadarorinsu dannayi karatu, sun sadaukar da farincikin su dannayi murmushi, ya kalli Daddy yace gobe zan fadamuku komai game da rayuwa ta, bazan boye muku komai ba"
Ummi ta kalle shi cikin so da kauna tace ni Kuma gobe zan bayyana maka wani abu Wanda zai sanyaka cikin dauwa mammen farinciki"
Kowa yayi murmushi dajin kalaman ummi Banda Nasir dayake ta faman hada gumi, tabbas dole yasan abinyi kafin gobe, itama fulanin danata tunanin da takeyi aranta domin tabbas dole burinta ya cika kafin gobe.....
Baba Sanusi ne zaune a fada a gaban Mai martaba yace "ranka yadade a ranar da prince khamal ya kwana gidana bai fadamin komai ba akan rayuwar sa ya dai cemin wadanda suka raineshi sun rasu"
Mai martaba yayi gyaran murya yace "sanusi inaji ajikina akwai lbr maradadi Wanda d'ana yake b'oyewa bayason musani, ni babban damuwa ta itace kardai a ce wani abune ya aika ta sbd kasan wannan gidan namu bama barin abin kunya komai kankantar sa, Kuma a ka'idar wannan masarautar dole ne Wanda zai gaji sarki yakasan ce nagar taccen namiji, dokace wadda muka gada tun kaka da kakkani cewa duk wani magajin sarki ya kuskura ya aikata wani abu Wanda zaisa kimar masauratar nan ta zube to wajibine a fitar dashi daga wannan masarautar, domin bazai gaji sarki ba Kuma 'ya 'yansama bazasuyi sarauta ba" 🤔 Mai martaba ya ida maganar ne hawaye na gudana a fuskar shi, yasake cewa "yanzu mekake tunani kenan idan akace khamal ya aikata wani abu Wanda zaisa a yimasa wannan hukuncin" kukane yaci karfin mai martaba sbd tausayi da kaunar danna shi..
"Kayi hakuri ranka yadade inaji a jikina yarima bazai taba aikata maka mancin haka ba domin yaron kirki ne duk da ba dadewa nayi tare dashi ba amma na fahimci yana da riko da addini sannan ga ladabi da biyyaya, sannan baya kula kowa musamman ma mata domin ko hadiman dakeyi masa hidima baya kulasu, ranka yadade insha Allah gobe zakaji alkhairi daga bakin mafi soyuwa awajenka, Kuma farincikin ka"
Mai martaba yaji dadin kalaman Baba Sanusi sosai, domin shima zai iya bada shaida akan yarima saidai bazai iya kareshi ba idan har wani mummunan abu ya aikata, sbd dokar wannan masarautar ce, babu wani sarki da ya isa yataka wannan dokar komai sonda yakewa d'ansa"
Zaune take tana kuka tana juya gubar data amsa a wajen jakadiya a hannun ta sbd tasamu ganin Rabin ranta, kuka takeyi sbd tsabar fargabar abinda zai faru da ita bayan taki cika umarnin gimbiya fulani, tana cikin hakane wani tunani yafado mata a rai da sauri ta tashi tsaye taje ta samu wani busashshen iccen sarbejiya ta daddake shi ta kulle a leda, taje ta zuba wannan gubar a cikin dankaramin toilet dinsu ta dawo ta zauna cikin farinciki..
Nasir ne nagani yanata faman safa da marwa acikin dakinsa sai faman kiraye kiraye yakeyi a waya saidai yahana na dauko muku rahoto domin ya kulle kofar, ta jikin kofar na tsaya dannaji meyake shirin aika tawa...
Da sauri na ga ya fito ya nufi dakinsu Afra, zaune ya iska mata, fuska a daure yace ki shirya gobe zamuje gidanku Kuma a giben za'a daura muna aure" yana gama fadar haka ya fice da sauri...
A jiyar zuciya Afra ta sauke tace lallai dolene na cika aikina kafin gobe, dolene na bayyana a gaban khamal kafin gobe...
By
Meerah💞💞💞
[3/30, 1:44 PM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal🤴🏻🤴🏻🤴🏻
🌹🌹🌹🌹🌹
BY
🌹🌹🌹
Meerah💞💞💞
08068971503
ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️✍️
Dasunan
Allah mai rahama mai jinkai
🅿️ 3️⃣3️⃣_3️⃣4️⃣
Washe gari Afra ta tashi da matsanan ciyar fargaba, da fuduwar gaba, a zuciyar ta takejin kamar wani abu ya faru da kamal ko yana shirin faruwa dashi, lkc guda ta rude tafita hayyacinta, gashi an tsare ta a kurkuku babu damar taje taga halin daya ke ciki, adu'a tashigayi tana rokon Allah ya kare mata masoyin ta kamal, wasu zafafan hawaye ne ke gudana a fuskar ta..
Khamal yana kwance haryanzu bai farfado ba daga nannauyan baccin dayakeyi, karfe 10:00am Daddy da ummi harda mamy da Nasir duk suna cikin dakin da aka kwantar da khamal suna jiran farfa dowarsa, wani bafade ne ya shigo ya faɗi kasa yayi gaisuwa ga mai martaba da gimbiya yace "Allah ya baka nasara yanzu wani mutum yazo yace yana son mgn dakai"
Batare da ɓata lkc ba mai martaba ya bada umarnin a shigo dashi, da sallama ya shigo ya faɗi kasa yayi gaisuwa kamar yadda aka saba a masarautar yace "Allah ya taimaki sarki nazone da wani babban lbr mara daɗinji", hawayen munafurci ya share, kowa ya matsu yaji abinda mutumin zaice, shikuma Nasir sai fama murmushi yakeyi, mutumin yace "Allah ya baka nasara wani mummunan lbr ne akazomin dashi shine nace bari nazo na sanar dakai halin da akeciki" cikin kusawa da sonjin lbrn mai martaba yace "kafadamin meke faruwa"
Mutumin yace "ranka ya dade wani mutum ne dazomin da lbrn wai prince khamal korar sa akayi daga kauyen su adalilin kamasa da akayi da laifin yiwa kanwar sa cikin shege ƴar waɗanda suka reneshi"
Innalillahi wa inna'ikaihir-raji'un kowa yake mai maitawa acikin dakin, tuni mai martaba tari ya sark'eshi daga nan ya zube a wajen sumamme.
Ummi kan kuka ba'a magana a wajen, harda mamy dake kukan farinciki, suma kannen khamal khausar da khairat da suka shigo daga baya sunji komai, suma kuka sukeyi sosai, Nasir kam ko alamun hawaye babu a idanun sa.
Koke koken da akeyi ne a wajen yayi sanadiyar farkawar khamal, yashiga damuwa sosai ganin suna kuka, dubawa ya karayi sosai baiga Daddy ba, a tunanin sa wani abune yasame shi shiya sa kowa ke kuka, shima babu ɓata lkc ya shiga rera kukan sa, ba tare da ya tambayi kowa ba abinda ke faruwa...
Likitoci sundade akansa kafin su samo numfashin sa ya dawo nomal, haka suka yini acikin a sibitin kowa sai kuka yakeyi, sai marece aka sallami Daddy, kai tsaye fada suka wuce domin Daddy yace kowa yaje cen yanada mgn, ciki ko harda mutumin daya zo da wannan mgn....
Bayan kowa ya hallara a fada, mai martaba ya umarce mutumin daya sake mai maita abinda ya faɗa, babu ɓata lkc mutumin ya mai maita kamar yadda ya faɗi a baya, gaban khamal ne ya shiga dukan uku uku kunya duk ta kamashi, tabbas yau itace ranar da yake gudu tuntuni, yauce ranar tonon asirinsa, muryar Daddy yaji yana cewa "khamal kaji duk abinda ya faɗa"? wani gumi daya taso masa a gushi ya share, aransa yace yau komai zai faru saidai ya faru zan fadi gskyr abinda nasani, "ehh Daddy naji abinda yace" ya faɗa kai tsaye "gsky ne ko ba gsky bane"? Daddy ya faɗa yana kallon sa, "ehh Daddy gsky ne amma.............. " daka tarda shi Daddy yayi yace bana bukatar jinkomai daga bakinka, ka tashi ka fice ka barmin gida bana bukatar ganinka acikin gidannan" yana gama faɗar haka ya tashi ya fice.
Ummi tasowa tayi tanata faman rusa kuka kamar ranta yafita, tace "khamal meyasa ka aikata wannan abun? meyasa ka aikata abinda zaiyi sanadiyyar nisan tani dakai?, khamal meyasa zakayi wannan mummunan aikin bayan kasan wannan masarautar ta yanke hukuncin korar duk wani yarima daya aikata irin wannan abin" kara rungumeta yayi yace "ummi ban aikata ba wlhi sharri akayimin" yana mgn yana kuka kamar ransa zaifita, sundaɗe a haka kafin khamal yayi karfin halin tashi ya nufi part dinshi, kayansa ya shiga har hadawa yana gamawa ya dauki jakar har yakai bakin kofa ya yatuna da kyautar da Afra tayi masa, da sauri yaje ya dauki ledar yana kallon ta yana mumushi, mota ya shiga ya tadata ya fara tafiya batare daya san inda ya dosa ba, harya fice daga gidan Daddy na kallon sa asaman bene, har cikin ransa yanajin zafin rabuwa da ɗansa, amma ba yadda ya iya wannan dokace yazama dole ya yanke hukunci kafin hukuncin ya dawo kansa, hawayensa ya share yace ina matukar kaunarka khamal Allah ya tsaremin kai a duk inda zakaje ...
Afra ko tana cen tana kuka tana faman bubbuga kofar kurkukun amma bawanda ya kulata acikin fadawan, a haka ta kwana har gari ya waye...
BY
MEERAH💞💞💞💞💞
[3/30, 1:44 PM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal 🤴🏻🤴🏻🤴🏻
🌹🌹🌹🌹🌹
BY
🌹🌹🌹
Meerah💞💞💞💞
08068971503
ELEGANT ONLINE WRITER'S ✍️✍️
Dasunan Allah mai rahama mai jinkai
🅿️ 3️⃣5️⃣-3️⃣6️⃣
Tana cikin bacci taji alamar taɓa kofar, da sauri ta mike tana fadin "don Allah ku fitar dani daga cikin wajennan, wlhi ba kashe shi nayi niyyar yiba" baice mata komai ba harya buɗe kofar yace ta fita, da sauri kuwa ta fita harda ɗan gudunta.
Tana fita bata tsaya ko inaba sai part ɗin khamal, tana zuwa taga ba kowa a wajen harda masu gadi duk suntafi, tayi tunanin yana fada, kai tsaye cen ta nufa, da zuwanta fadawa suka dakatar da ita suka ce hadimai basa shiga, sbd mai martaba yana ganawa da iyalin sa..
Badan taso ba ta hakura, waje tasamu ta xauna tanajiran fitowar khamal, wani tunani ya fado mata arai nan take ta tashi, ta nufi hanyar fita daga masarautar, tana cikin tafiya taji wasu fadawa na mgnr khamal akan abinda ya faru dashi jiya, wajen su taje ta kara tambayar su, cikin kwarin gwaiwa da son bada lbr suka fada mata komai, kuma sun tabbatar mata mai martaba ya kore shi...
Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un tayi ta nana tawa a bayyane, duk ta rude tarasa meke mata daɗi kwallar data taru a idon tane ta gangaro, taso ta danne raɗaɗin da takeji acikin zuciyar ta hartaje gidan su Salim amma ta kasa, kuka ta dingayi bakin rai hartaje gidansu Salim...
Tana zuwa ko ta iskeshi a gidan tare da mahaifiyar sa, hankalin su ya tashi sosai ganinta cikin wannan halin, tambayar ta suka shigayi, meyake faruwa? Bata boye musu komai ba ta sanar dasu halin da ake ciki, hakuri suka dinga bata harta daina kukan.
Dakyar momy ta lallaɓa ta tayi wanka taci abinci. Salim ne ya bata shawara akan taje fada ta sanar da mai martaba cewa khamal bai aikata abinda ake zarginsa da shiba, haka kuwa a kayi shirya wa tayi tsab cikin shiga ta alfarma, key din motar ta ta amsa ga hannun Salim, tana tada motar bata tsaya ko inaba dai fadar mai martaba sarki Ahamd Abdus-salam.
Shigarta gidan yayi daidai da fitowar iyalan giban baki daya ciki ko harda mai martaba, tsyawa sukayi cak suna kallon ta daidai wajen da suke ta parker motar ta, ta fito cikin takunta na kasaita da nuna isa, gimbiya fulani na ganinta gabanta ya shiga dukan uku uku, ko kallon ta Afra batayi ba dan bata da lkcn ta, wurin ummi ta wuce ummi na ganinta tazo ta rungumeta, su dukansu kuka sukeyi gwanin ban tausayi....
Mai martaba yace "meya kawoki gidannan? me kikazo nema"? hawayenta ta share ta kalli Nasir da tundaxu ita yake kallo yana hara rarta, kauda kanta tayi gefe kamar ma batasan yanayiba tace "Ranka ya dade, nazo nan ne a dalilin khamal, bansan cewa shi yarima bane saida na dade acikin gidannan ina nemansa" mai martaba yace "mekikazo nema a wajen sa bayan kin gudu daga gidan iyayenki, kenan kinxo nan ne danki kara lalatamin yaro ko"? a jiyar xuciya ta sauke tace "ranka ya dade khamal ba fasiki bane kamar yadda kuke tunani, khamal mutumin kirki ne, baya kula mata, baya shiga sha'aninsu, wlhi sharri akayi masa bai aikata ba, kuma nice silar shigar shi cikin wannan halin, a dalilina akayi masa wannan sharrin baijiba bai gani ba"......
Duk wajen kowa ya maida