Author : Meerah Category : African Stories & Novels
ruwa ya watsa mata a fuska, nan take bakin ya wanke, murmushi yayi Yana kallonta yace "Afra kenan da kina tunanin zan kasa ganeki ne? Tun ranar Dana fara ganinki nasan kece na kyalike ne kawai dannaga iya gudun ruwanki, Afra meyasa kika gudu ranar daurin auren mu"?
"Nasir nasan nayima laifi Amma Dan Allah ka gafarce ni, wlhi zuciya ta tayi nisa a son wanin ka, bazan iya zama dakai ba amatsayin mijina"
"Kinsan baki Sona meyasa kika bari aka hada aurenmu, meyasa danazo gidan ku kika nunamin kulawa bayan kinsan basona kikeyiba"?
"Niba wata kulawa Dana baka, kawai dai ina ganinka ne na fahimci kamai baka Sona shiyasa naji dadi, harna nuna farincikina"
Hmmmmm "Afra kenan agabana kike cewa baki sona ko" kallon ta yakeyi cike dajin zafin kalamanta, batace komai ba "Afra " Ya fada Yana kallon ta "Ni inason ki" da sauri ta d'aga kai tana kallon sa " a'a ni akwai Wanda nake so", "wanene kike so Kuma meya fini dashi da har Zaki gudu ranar daurin auren mu"
Mutane ta tsinkaya suna tafowa wajen da suke ganin yarima ne da fadawansa yasa ta tsaya kallon sa danta ga wanene su gimbiya fulani keson kashewa, tunda nesa take ganin kamar khamal dinta Amma ta kasa gasgata hakan,
Kallon Nasir tayi tace "wanene wancen Kuma naga kamar wurinmu zaizo" juyawa yayi shima dan yaga wata mgn akansa, murmushi yayi yace "wannan shine magajin wannan masarautar" "magajin masarautar Kuma" cike da mamaki ta fada, "ehh sunan shi khamal Kona ce miki prince Yazeed, yadawo ne bayan tsawon shekaru da batansa tun yana jariri"
Taji dadi sosai dajin wannan mgn murmushi ne ya bayyana afuskar ta, Kara kallon sa tayi ganin yakusa kawo wane yasa tayi saurin b'oyewa bayan wata bishiya anan kusa dasu..
"Mekake yine anan nazo wucewa ne natsinke ka shiyasa na tafo" khamal Ya fada yanata faman dube dube kamar Wanda keneman wani abu "yarima lfy dai ko me kake nemane"?
"Nasir kanshin turaren Afra nakeji awajennan", "Afra kuma, wacece Afra "?
Kallon sa khamal yayi yace "wani yanki ne na rayuwata" ya fada Yana kallon Nasir "Kamal mgn fa mukeyi akan Afra ba akan rayuwar kaba"?
"Nasir bazaka gane matsayinta awaje na ne ba, Amma duk yadda kake tunani ta wuce nan"
Ajiyar zuciya Nasir ya sauke domin shi duk baya gane wannan yaren "kaga yarima mutafi kawai" Nasir Yafada Yana rike hannun khamal Dan bayason yaga Afra dake labe awajen, shiko khamal sai dube dube yakeyi, ganin haka yasa fadawansa suka ringa dube dube awajen, "wai me kuke nemane" Nasir Yafada Yana kallon su, wani ba fade yace "ranka yadade Nima naji kanshin turaren" k'wace hannun sa yayi yace kaga Nasir yi tafiyarka kawai zan zauna awajennan"
Nasir yace "yarima Anya lfyr ka qlau kuwa? Inaga kamar kanada shafar aljanu, bari naje na gayawa Mai martaba, harya fara tafiya khamal yayi saurin rikeshi yace "nifa lfy ta lau Babu abinda ke damuna"
To idan har da gaske lfyr ka Lau to mutafi dannaga alamar akwai aljanu awajenna, Nima tunda nazo naji kaina na ciwo"
"Nasir wacce hadima ce na tsinkeku tare kafinnazo nan" ajiyar zuciya ya sauke yace "yace wata yarinya ce nagani anan shine nace ta wuce tabani waje nan ba wajen zaman kuyangi bane"
Kamal bai Kara cewa komai ba, suka cigaba da tafiya..
Afra na ganin sun wuce ta lek'o tana kallon Kamal harya bace mata, share hawayenta tayi tace "Allah sarki masoyina Ashe Kaine magajin sarki nazo Ina nemanka acikin bayi"
By
Meerahπππππ
[3/30, 1:44 PM] Meerah π: π€΄π»π€΄π»π€΄π» prince khamal π€΄π€΄π€΄
πΉπΉπΉπΉπΉ
By
πΉπΉπΉ
Meerahππππ
08068971503
ELEGANT ONLINE WRITER'S βοΈβοΈ
Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai
π
ΏοΈ 2οΈβ£5οΈβ£_2οΈβ£6οΈβ£
Gimbiya Fulani ce zaune a falo itada jakadiya kowannen su cikin bacin rai, gimbiya tace "Anya yarima yasha gubar nan kuwa"?
"Ranki yadade hadimar da tabbatar min cewa yasha gubar, ranki yadade atunanina gara akoma wajen boka ya koma bada wani mgn"
Gimbiya tace"Kije kikara karb'o wani, a wannan karon banason a samu matsala" tashi jakadiya tayi don ta cika umarnin gimbiya..
A bangaren gimbiya Nafisa kuwa, jakadiya tayi yawo a cikin masarautar Amma bata ga Afra ba, haka ta koma ta sanar da gimbiya.
Gimbiya tace "shikenan jeki kawai gobe zansaka fadawa sunemamin ita duk inda tashiga..
Afra na kwance bisa tsohuwar katifar dake cikin dakin, da sauri Dije ta shigo dakin tace " Hajara yanzu naga jakadiyar gimbiya Nafisa na nemanki" a tsora ce Afra ta kalle ta tace "na shiga uku, Dan Allah Dije karki fadamata Ina nan, wlhi banason komawa gida" kuka tafarayi, Dije dai sai lallashinta takeyi
Washe gari Afra kamar bazata fita ba jiki a sanyaye tayi lullub'i ta fita Dan kar a ganeta, kamar yadda tasaba haka taje tayi aikinta tana dawowa akan hanyarta ta haduda fadawa su uku taji tsoron ganinsu sosai, binsu tayi sukaje kamar yadda aka umarce su..
Da sallama ta shiga falon, gimbiya Nafisa ita daice zaune a falon, durkusawa tayi har kasa ta gaisheta cikin girmama, ta amsa gai suwar ba yabo ba fallasa..
Nasir ne zaune a falon sa wayar sa ya dauko ya Kira Abba mahaifin Afra bayan sun gaisa Nasir yace "Abba naga anyi sanarwa jiya cewa haryanzu ba'aga Afra ba"
Abba yace "haka ne Nasir muyi nemanta ko ina Amma ba'aganta ba"
"Karka damu Abba insha Allah zan nemo ta duk inda tashiga" Abba yaji dadin maganar sa sosai, daganan sukayi sallama, murmushi yayi yace "Afra kenan wlhi dole Zaki aureni ko kina so kobaki so....
Kallon ta ummi tayi tace "Afra zan tambayeki banaso kiyimin karya idan kika kuskura nakamaki da laifin karya to zanyi miki hukunci Mai tsanani, ki gayamin menene dalilinki na zuwa gidannan"?
Sunkuyar da kanta kasa tayi yaukam zata fadi gsky koma mezai faru yafaru, "ummi dama nazo nan ne dannnn........ " Tayi shiru kunya ta hanata ida maganar,
"Fadamin mana" sukuyarda kanta tayi kasa tace " wanine nazo nema a gidannan" "wanene shi" ummi ta fada a takaice.
Cikin jin kunya ta fadawa ummi komai tsakanin ta da khamal Amma bata fada mata garga din da Nasir yayi mata ba ta daice bata son yasan tana cikin gidannan harsai komai ya daidai ta..
Ummi taji dadin lbr da Afra ta bata, saidai bazata ce komai ba sbd bata tunanin Mai martaba zai amince da sake kulla alaka tsakanin sa da mahaifin Afra...
Afra tajima a part din ummi, domin ummi taso ta dawo nan da zama ta daina bauta a gidan Amma taki a mincewa, haka ummi ta kyaleta badan taso ba,
By
Meerahπππππ
[3/30, 1:44 PM] Meerah π: π€΄π»π€΄π»π€΄π» prince khamal π€΄π€΄ π€΄
πΉπΉπΉπΉπΉ
By
πΉπΉπΉ
Meerahπππ
08068971503
ELEGANT ONLINE WRITER'SβοΈβοΈ
Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai
π
ΏοΈ 2οΈβ£3οΈβ£_2οΈβ£4οΈβ£
Suna fita daga dakin Afra dakin da aka kwantar da yarima suka je kwance suka tarar dashi, Baba Sanusi da Inna Khadija suka iske cikin shiga ta alfarma, domin bakaramar kyauta maimartaba yayiwa Baba Sanusi ba a ranar da akazo kirasu shida khamal, a wannan ranar ne aka saki Inna Khadija, a cikin masarautar Mai martaba yabasu kayataccen gida.
Suna zaune gefensa, cikin girmamawa Baba Sanusi da Inna Khadija suka gaishesu, ummi da Mai martaba sunji dadin ganinsu sosai, sunjima zaune awajen kafin Prince khamal ya farfado.
Arfa na fita daga asibitin bata tsaya ko inaba sai dakinsu na kuyangi, gabanta sai faduwa yakeyi, Dije dake kwance saman katifar dake cikin dakin ta kalle ta tace " Hajara lfy kuwa na ganki duk a firgice" bata ida mgn ba saiga Nasir ya banko kofar dakin da karfi.
"Keee!! Fita kibamu waje" Yafada cikin bacin rai Yana kallon Dije, tuni jikin ta yafara makarkata sbd tsoro, da sauri ta fice daga dakin.
Kallon Afra yayi fuska daure yace "meye tsakaninki da Yazeed"? shiru tayi bata bashi amsa ba, tsawa ya daka mata da sauri ta kalle shi a tsorace, " nace wanene Yazeed a wajenki"?
Kauda kanta tayi gefe itama ta daure fuska tace "masoyi nane Kona cema mijin da zan aura"
A jiya zuciya ya sauke, aransa yanajin kamar ya shaketa sbd kishi, kallon ta yayi yace "bazaki aure shiba matukar Ina nufashi aduniya wannan alkawari nane" murmushi tayi Wanda hausawa ke cewa yafi kuka ciwo, tace "wlhi baka isa ka hana aurena da khamal ba, shinake so Kuma shi zan aura, a gabanka za'a dauramin aure dashi"
"Shikenan kije ki aure shi, nikuma nayi miki alk'awarin saina saka rayuwar Yazeed cikin matsananciyar damuwa, Kuma kisani wlhi duk ranar da kika sanar da Yazeed ko Mai martaba dalilin zuwanki gidannan nikuma a ranar zan sanar da mai martaba da duk bayin dake cikin gidannan cewa khamal fasiki ne, mai saka alkhairi da mugunta, zan fadawa kowa cewa khamal ya yiwa kanwar sa cikin shege, 'yar wadanda suka reneshi tunyana jariri, suka ciyar da shi, suka tufatar dashi, suka ilman tarda shi, suka nuna mishi so da kauna, karkiyi mamakin sanin wannan lbr danayi domin mahaifinki ya fadamin dalilin da yasa yaki aura mikishi"
Kuka Afra ta farayi tana rokonsa dayayi hakuri ya barta ta auri Wanda take so, Amma yak'iya yace dole ta aure shi koyasa Mai martaba ya kori khamal daga gidan, daga hakanan ya fice ya barta nan tana kuka...
Ummi ce zaune a k'aya taccen falon ta, ta kasa zama ta kasa tsayi, ita dai bata yadda da zuwan Afra gidan ba kota halin yaya tana sonjin dalilin zuwan ta gidan, babban abinda ke daure mata kai shine lkc daya prince khamal da ita suka yanke jiki suka fadi kuma likita yace duk abu gudane ke da munsu, to meyake faruwane? tabbas akwai wani abu, kallon jakadiya tayi da shigo warta kenan falon, amsa mata sallama tayi tace, "jakadiya inason ki binci komin wata yarinya acikin masarautar nan wadda aka Kai asibiti tare da Prince khamal", "angama ranki yadade" jakadiya ta mike Dan cika umarnin gimbiya Nafisa...
Khamal ne keta faman safa da marwa a dakinsa, hawaye na bin fuskarshi, shikade yasan irin radadin da yakeji acikin zuciyar sa, yanason yaje nemanta Kuma yana tsoron bayyanar sirrin sa a wajen iyayen sa, zama yayi a bakin gado yana tunanin inda zai samu mafita, tunawa yayi da kyautar da Afra ta bashi lkcn da suka rabu, da sauri ya mike tsaye yaje ya dauko ledar, murmushi yayi Yana bin ledar da kallo cikin farinciki, zama yayi yana shirin budewa saiga Nasir yashigo dakin, aje ledar yayi Yana amsa sallamar Nasir dake kokarin shigowa..
Kallon sa Nasir yayi Yana murmushi Wanda hausawa kecewa yafi kuka ciwo domin shikadai yasan radadin da yakeji a zuciyar sa, "ya jiki" Yafada Yana kokarin zama kusa dashi, "naji sauki" khamal ya fada Yana kallon sa,
"Nasir meyake damunka naga yanayin ka ya cenza gaba daya, Kuma meyasa bangane ka asibiti ba har aka sallameni",
"Banajin dadin jiki nane" Nasir ya fada yana kauda fuska gefe, "meyake damunka? Meyasa bakaje kaga likita ba? kayimin bayani idan bakason zuwa asibiti saina dubaka a gida"
"A'a yarima rashin lfy ta baya bukatar ganin likita" dafa kafadar sa khamal yayi yace Nasir ka gayamin damuwar ka, ni Dan uwanka ne Kuma aminin ka"
Kallon sa Nasir yayi yace "yarima ciwon so ne yake damuna, na fada cikin soyayyar wata yarinya" murmushi khamal yayi yace "matsalar mu daya ce nida Kai, Nasir saidai Kai kanada damar da zaka mallaki abinda kake so amma ni banida wannan damar"
Gyara zama Nasir yayi yace "khamal tawa matsalar tafi taka sbd Kai wadda kake so tana sonka Amma ni bata sona, bata kaunata, wani take so daban bani ba"
"Nasir meyasa zaka fara son yarinyar da bata sonka"? Kamal ya fada Yana kallon sa, Hmmm "Kamal bazaka gane bane, lkc daya naji nakamu da sonta" ajiyar zuciya khamal ya sauke yace "me sunan yarinyar Kuma wacece"
"Sunan ta Hajara, itace yarinyar da aka fasa aurena da ita" kallon sa Kamal yayi cikin yanayi Mai wuyar fassarawa yace "Nasir karasa wazaka so sai wadda ta gudu ranar da za'a daura muku aure"?
"Kaga kamal mubar maganar nan nizan nemota duk inda take Kuma saina aure ta ko tanaso ko bata so" ajiyar zuciya khamal ya sauke yace " kana da babban aiki a gabanka" daukar ledar yayi ya maidata wajen da ya dauko ta..
"Kamal ya sunan yarinyar da kake so, Kuma a ina take"? Nasir ya fada Yana kallon sa "sunan ta Afra a kaduna take, munason junan mu sosai iyayenta ne suka hanani auren ta" "me yasa suka hanaka aurenta bayan Kuna son junanku"?
"Sbd ni talaka ne Kuma d'an k'auye, sukuma Mai kudi irinsu suke so" "haba khamal yanzu Kai babban mutum ne na tabbata matukar zaka koma tabbas zasu baka auren ta akaro na biyu"
"A'a Nasir bazai yiyu na koma wajenta ba sbd anyi mata aure"
Kallon sa Nasir yayi aransa yace ba'ayimata aure ba yanzu dai za'ayi mata, " ok ni zanje na kwanta bacci nakeji" Nasir ya fada, Yana kokarin ficewa daga dakin Yana murmushin mugunta.....
By
Meerahπππππ
[3/30, 1:44 PM] Meerah π: π€΄π»π€΄π»π€΄π» prince khamal π€΄π€΄π€΄
πΉπΉπΉπΉπΉπΉ
By
πΉπΉπΉ
Meerahπππ
08068971503
ELEGANT ONLINE WRITER'SβοΈβοΈ
Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai
π
ΏοΈ 2οΈβ£7οΈβ£_2οΈβ£8οΈβ£
Zaune yake a garden sassanyan isaka na kadawa tare da bugun zuciyar sa, da nesa ya tsinki fadawa na tafe dare da Afra wadda ya aika a kiramasa ita.
Zama tayi nesa dashi kadan, kallo daya zakayi mata kasan tana cikin bacin rai, murmushi yayi yace "amarya ta ba mgn"? Ko kallon sa batayi ba balle yasa ranzata bashi amsa, matsawa yayi daf da ita ya rike hannun ta Yana shafawa cikin so da kauna yace "Afra nasan baki Sona a yanzu inason kiyi hakuri ki bani damar mallakar zuciyarki ina tabbatar miki cewa wata rana zaki soni fiye da yadda nake sonki"
Wani kallon raini tayi masa tace " Nasir wlhi bazaka taba samun abinda kake so ba a wajena dan bana sonka bana kaunarka, ni d'an uwanka nake so Kuma shi zan aura, Ina tabbatar ma cewa baka isa ka hanani auren khamal ba wlhi" saukar mari taji a kuncenta cikin zafin rai ya mareta har Yana shirin kara mata wanine tayi saurin kaucewa.
"Karkiyi tunanin ganin Ina lallabaki zaisa ki dinga fadamin maganar da duk tazo bakinki, to baki isaba Kuma bazan lamunta ba, Kuma wlhi duk lkcn da kakiyi kokarin hana aurena dake to wlhi sainasa mai martaba ya kori khamal daga masarautar nan" Yana gama fadar haka ya tafi yabarta nan sai faman kuka takeyi, tana nan zaune a wajen ta tsinki prince khamal tafe tare da fadawansa da kanwar sa khairat, da sauri tabar wajen tun kafin suganta.
Kamal na isowa wajen ya tsaya cakk Yana dube dube, khairat tace "yaya lafiya kuwa? Meyake damunka"? Kirjinsa ya dafe yace "khairat inajin kamar Afra tana wajennan" kallon sa tayi cikin rashin fahimta tace "yaya wacece Afra Kuma" baice mata komai ba ya fara dube dube lungu da sako, Suma fadawan neman ta sukeyi awajen, ita dai khairat binsu da kallon mamaki kawai takeyi..
Sun dauki tsawon lkc suna neman ta har wuraren da ke makwaf taka da wajen Amma babu ita babu lbrn ta, jiki a sanyaye ya zauna a wajen, kallo daya zakayi masa kasan Yana cikin damuwa sosai..
Tunawa yayi da cewa Afra ta b'ata yanzu haka ba'asan inda take ba, wasu zafafan hawaye ne suka gangaro a lallausar fuskar sa, lkc daya Kamal ya cenza gaba daya, wani zazzabi ne ya taso masa nan take jikin sa ya dau zafi, da kyar da taimakon fadawan sa da kanwar sa ya isa part din ummi....
Yana shiga dakin ya kasa zama ya kasa tsayi magana yakeyi a zuciyar sa, yanzu kamar ni Nasir ace wata mace ta kalleni tace wai bata sona, hmmmm wlhi Afra baki isaba dole Zaki soni, dole ki aureni, bazan taba bari ki auri wancen shashashan ba, wayar sa ya dauko ya daddana ya Kara a kunnen sa, gaisawa sukayi da mahaifinsa cikin so da kauna yace "Dad dama akan maganar wannan yarinyar da kukeson hada aurena da ita" banji abinda akace ba a daya bangaren naji dai yasake cewa "Dad wlhi nakamu da matsanancin son yarinyar nan, Dan Allah Dad kusake nema min aurenta a karo na biyu"
Cikin zafin rai naga yayi jifa da wayar da alama dai mahaifinnasa bai amince da bukatarsa ba.
Zaune ummi take tare da hadimanta sunayi mata fifita dayar Kuma tana ciremata b'awan ayaba tana mika mata, ganin prince khamal tayi fadawa sunshigo rike dashi, da sauri ta mike tsaye taje ta karbeshi ta rungumeshi tace "son meyake damunka jikinka yayi zafi hk" zaunar dashi tayi a saman kayatattun kujerun falon, ta kalli khairat tace" meya sameshi haka naga yanzu fa kuka fita dashi lfy Lau"?
" Ummi nima bansan meyake damun yaya khamal ba, daga zuwanmu fa garden yace yaji kanshin turaren Afra, yafara dube dube a wajen daga nan Kuma sai zazzabi"..
Jinjina kai ummi tayi ta fahimci komai, Amma batace komai ba, cewa kawai tafi fadawa suje su dauko mota a tafi a sibiti dashi, babu bata lkc ko aka tafi dashi cikin kankanin lkc likita yayi masa allurai daban daban, yajima yana bacci sakamakon allurar da akayi masa kafin ya farfado,
Gimbiya fulani ce tare da jakadiya sunata faman kulle kullen su ta yadda za'a sakawa prince khamal guba acikin abinci wadda boka ya koma basu, shawara sukeyi ta yadda za'a sake saka masa ita, Wanda yayi daidai da shigowar Afra falon, sunji tsoron ganinta amma dayake sunada karfin iko saisuka danne cikin tsawa gimbiya tace "keee meya kawoki nan a daidai wannan lkc"? Kara shigowa Afra tayi cikin izza da kasaita tace "nazo nanne danna taimaka muku, dazu naji Kuna mgn cewa zaku sake bawa wata aikin daban sbd baku yadda da waccen ba, to nizanyi, ni