Chapter 3 Reading PRINCE KHAMAL Boyayyen Sarauta By Meerah READ HAUSA Novels

PRINCE KHAMAL Boyayyen Sarauta By Meerah

Author :  Meerah Category :  African Stories & Novels

Chapter   3 / 8

6K to 9K   out of 23.3K words

damu jakadiya kullum Yana zuwa nan danya gaisheni, kibari gobe da safe idan yazo sai abashi yasha"

Saurin Kama aikinta tayi danjin alamar motsin tafiyar mutum, jakadiya ce tafito daga falon gimbiya fulani..

Ci gaba tayi da aikin ta wata zuciyar tace ta taimaki wannan yazeed din wata zuciyar Kuma tace ke fita batunsu, meye ruwanki dasu keda ki kazo daukar kamal. Da wannan tunanin ta gama aikinta gaba daya......

Fitowa tayi daga part din gimbiya Fulani, ta fara dube dube acikin ma sarautar ko zataga Kamal...

Ta fiya takeyi bata San kowa ba batasan inda zataba, wasu bayi ne maza ta gani da alama fira sukeyi wuri ta samu nesa dasu ta labe tana binsu da kallo daya bayan daya Koda zata ganshi.....

Data ga Babu shi cikinsu saita Kara gaba, Afra tayi yawo sosai acikin masarautar har magrib tayi Amma bata ga khamal ba, haka ta hakura ta koma masaukin ta....

Washe garima haka tafito tunda safe Saida tayi yawon neman khamal kafin taje wajen aikin ta.....

Shiko khamal yanacen wajen Mai martaba bai fitoba tunsanda yaje gaishe she, sbd Mai martaba akwai shi dason fira, duk da khamal bayawan surutu gareshi ba Amma haka yake sake jikinsa yayi fira da mahaifinsa, saidai tunjiya yanajin wani bakon Al amari acikin zuciyarsa, domin bugun zuciyarsa ne yakaru Koda yaushe jiyake kamar Afra tana tare dashi, yanason bawa mahaifin sa lbrn Afra da irin sonda yakeyi mata Kuma yanajin tsoron bayyanar sirrin daya boye Wanda bayason kowa yasani....

"Prince khamal" Mai martaba ya fada Yana kallon khamal, "na'am daddy" ya fada Yana kallon sa, "inason ka daukeni kamar abokinka ba matsayin mahaifiba, khamal banason kadinga boyemin damuwar ka komai girmanta haka komai kan kantarta, khamal ka gayamin meyake damunka Danna lura dakai tunjiya kana cikin damuwa"

Murmushi yake yayi Wanda hausawa ke cewa yafi kuka ciwo, yace "ba komai daddy", kallon sa daddy yayi yace "yaushe kafara yamin karya, Yazeed" yafadi sunansa na ainihi babu alamar wasa a fuskar sa "kafadamin gsky meyake damunka"?

Ganin yanayin mahaifinsa yasan babu wasa a fuskar shi yace " daddy dama wata yarinya ce wadda mukayi soyayya da ita abaya shine nakejin kamar tana kusa dani"

Kallon sa Mai martaba yayi yace "wacece ita" nan khamal ya bashi lbrn Afra tun farkon haduwar su har irin korar Karen da Abba yayi masa lkcn dayaje gidansu...

Daddy ya tausaya masa sosai yace "wanene mahaifinta, kafadamin nida kaina zanje na nema maka aurenta akaro na biyu"

Gaban khamal yayi mugun faduwa domin yasan cewa zuwan Mai martaba gidansu Afra to tabbas allura ce zata tono galma " a'a daddy anriga anyi mata miji, har ansa ranar aurenta"

hawayene suka gangaro masa domin wannan kalmar daya fada bakaramin tayar masa da hankali tayi ba, kardai mgnr sa tazama gsky, idanko hakan ta kasance to tabbas zai iya hadiye zuciya ya mutu.......

Mai martaba bai Kara cewa komai ba sai binsa dayayi da kallon tausayi, lallashinsa yafarayi kamar karamin yaro......

Gimbiya Fulani tayi jiran shigowar khamal shiru bata ganshi ba har rana tayi babushi Babu alamar sa, haka ta hakura dole badan taso ba...

Sannu sannu Afra Saida ta share sati daya agidan bataga alamar khamal ba, Kiran Hashim tayi awaya tace ya Kara bincika mata koya fita daga gidan Dan haryanzu bataga alamar sa ba.

Babu bata lkc Hashim ya Kara bincikawa ya tabbatar mata da yana cikin gidan haryanzu, jikinta yayi sanyi sosai hartaso ta koma gida ta tuna da cewa guduwa tayi idan ta koma batasan irin hukuncin da zasuyi mata ba.

Zaune take cikin lambu tana wasa da furanni motsin mutum taji abayan ta, tana wai wayawa, ta dafe kirji da sauri, innalillahi mezan gani haka tafada cikin ranta da mugun tsoro a zuciyar ta.....

"Keee meya kawoki nan wajen ko Kinga wurinnan yayi Miki Kama da wajen zaman bayi" ajiyar zuciya ta sauke tana godiya ga Allah dayasa bai gane taba da yau kashinta ya bushe, taba fuskarta tayi taji bakin abinda ta shafa Yana nan baifitaba, shiyasa ma bai ganeta ba...

"Kayi hakuri dan Allah wlhi ni bakuwa ce bansan komai ba acikin dokokin gidannan, tana gama fada tabi ta gefensa ta wuce tana murmushin jindadi, yau bakin paintin nan datake shafawa ya ceceta....

Shi Kuma Nasir tsaye yayi Yana binta da kallo kamar yasanta Amma bakin abinnan data shafa yasa ya kasa ganeta, hankalinsa ne yakasa kwanciya, jiyayi yanason sanin kowacece ita, bin bayanta yafarayi, sannu a hankali hartaje masaukinta shiga dakin tayi shikuma ya koma cike da sake sake aransa......

Wanene Nasir?

Meyasa Afra taji tson ganinsa?

Kubiyoni danjin cigaban lbrn

Nice taku har kullum

MeerahπŸ’ž

More comments more typing πŸ’˜
[3/30, 1:44 PM] Meerah πŸ’ž: 🀴🏻🀴🏻🀴🏻 prince khamal🀴🏻🀴🏻🀴🏻



🌹🌹🌹🌹🌹



By

🌹🌹🌹
🌹 meerahπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
08068971503



ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️✍️



Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai




πŸ…ΏοΈ 1️⃣7️⃣_1️⃣8️⃣




A gefen iyayen Afra ko basu San Afra ta guduba sai gab da daurin auren, mutane har sun hallara..

Umma ce taji shiru bataji motsin Afra ba tunda tace mata zata fita gashi har rana tayi ko break fast bataga tayi ba, "zainab" umma ce takira ta, da sauri tazo, "umma gani"

"Jeki Kira Afra tazo taci abinci, "to umma" zainab ta fada tana tafiya dan cika umarnin umma.

Tana shiga dakin taga ba kowa, zama tayi tana jiran fitowarta daga bayi, a tunanin ta tashiga toilet ne, idonta ne ya sauka akan wata paper da sim card a saman, dauka tayi ta bude danta ga a binda ke jikin paper din, gabanta ne yayi mummunan faduwa ganin abinda aka rubuta a paper din, da sauri ta fito tana Kiran, "umma!! Umma!!

Afalo ta tarar da umma zaune tare da baki, Mika mata takardar tayi tana share hawaye,

Itama umma bakaramin tsorata tayiba da ganin halin da zainab ke ciki ba,

Jikin umma na rawa ta fara karantawa kamar haka...

Umma, Abba kuyi hakuri ku gafarce ni wlhi bazan iya auren wannan mutumin ba, zanje neman khamal duk inda ya shiga afadin duniyar nan...
Na barku lfy 😭

Umma na gama karanta wa tayanke jiki tafadi, mutanen da ke wajen sun rikice gaba daya, fadar irin tashin hankali da suke ciki bata lkc ne, ruwa suka yayya famata,

Bada jimawa ba ta far fado, kuka tafarayi Mai tsuma zuciya...

Afra karki tafi kidawo wlhi zangoyi bayan a auramiki Wanda kike so, umma tayi kuka sosai kamar ranta zai fita, cikin wannan halin ne ta kira Abba ta sanar dashi halin da ake ciki, shima dai sumar yayi awajen taron daurin aure, mutanen da suka halarci taron su suka yayya famasa ruwa,. Bayan ya farfado ne yasanar dasu halin da ake ciki..

Iyayen ango dashi kanshi angon ransu yayi matukar baci, musamman ma angon Wanda yaji yafara son Afra tun lkcn da yazo gidansu yaji ta birgeshi.

Dangin ango sunyi fada sosai a wajen, shidai abba baice komai ba Dan ta 'yarsa yakeyi babu ruwanai dasu tunda sune sukaja mai yarasa 'yarsa wadda ita kadaice 'yarsa aduniya 😭

Gida ya koma yabar mutane nan tsaye, masu zaginsa nayi, masu tausaya masa nayi.

Yana shiga gidan a falo ya zube kamar kayan wanki, hawaye nabin fuskar sa, umma ce tazo kusa dashi tace "Alhaji shikenan munrasa 'yar mu, munrasa farincikinmu Dana sani daban goyi bayanka ba, Dana sani Dana goyi bayan 'yata, wlhi bazan iya rayuba idanna rasa Afra" kuka takeyi sosai, Abba dai baice komai ba hawaye ne ke gudana a fuskar sa, kallo daya zakayi masa kasan cewa Yana cikin matsanan ciyar damuwa...

Ahaka suka kasance cikin kunci da Dana sani, umma kullum fada takeyi Abba ne yaja mata tarasa 'yarta, shikuma Abba baya kulata Dan acewarsa duk halinda take ciki baike Wanda yake ciki ba......

Fulani ce keta faman safa da marwa a makeken falon ta Wanda yasami komai na more rayuwa, jakadiya ce ta shigo da sauri ta russuna a gaban gimbiya Fulani tace "ranki yadade prince Yazeed baisha abinda muka bashi ba"

A razane gimbiya take kallon ta "wannan wacce irin banzar mgn ce kika zomin da ita? Mutum daya ya gagareki, yau sati daya kenan kina yimin alkawarin zaisha Amma kinkasa cikawa"

"Ranki yadade akwai tsaro mai karfi a sashen yarima, Kuma idan yazo nan duk abinda aka bashi bayasha, Amma nasamo wata hadima wadda ke Kai abinci sashen yarima Kuma tayimin alkawarin zata zuba masa abinda muka bata"

"Kije ki gaya mata matukar bukatar ta tacika to zan mallaka mata duk abinda takeso "an gama ranki yadade"

Afra dai tana gefe tanajin su, sukuma basuma sanda ita awajen ba, jijjaga Kai kawai tayi, aranta tanason taima kawa wannan mutumin Amma tanajin tson abinda zaije ya dawo, addu'a ce kawai zata cigaba da yimasa Allah ya kareshi daga sharrin makiya na boye dana fili,

Saude ce ke zaune a tsakiyar gidan, ta hada uban tagumi, hawaye na gudana a fuskar ta, Inna laure ce tafito da d'aki tana bin d'iyarta da kallon tausayi aranta tace duk nice silar shigarki cikin wannan halin, kallon baba Sani tayi tace "mlm hukuncin daka dauka akan khamal yayi tsauri koma mezakayi masa baidace ka koreshi ba, Khamal baya da kowa a duniyar nan saimu yanzu Ina zashi wazai bashi wurin zama"?

"Ya isa haka laure banason ki koma yimin mgnr nan khamal dai ba d'ana bane, Kuma kema ba d'anki bane, Kuma hukuncin dana dauka akansa shiya zab'awar kansa shi"

"Mlm khamal fa d'ana ne kamar yadda saude take d'iyata haihuwarsa ce kawai banyi ba Amma Nina raineshe tun yana cikin zanin goyo, Kuma Ina kaunarsa kamar yadda nake kaunar y'ata saude" bai koma cewa komai ba ya fice daga gidan,

"Inna Dan Allah kidawomin da khamal wlhi bazan iya rayuwa ba idan Babu shi" dafa kafadarta Inna laure tayi tace "kiyi hakuri insha Allah bazaki mutuba khamal zai dawo gareki" share mata hawaye tayi tare da rungumeta, itama hawayen takeyi, harga Allah tana kaunar khamal kamar Dan da tahaifa a cikinta...

Bayan fitowar Afra daga sashen gimbiya Fulani, haka kawai taji yau tanason zagayawa cikin masarautar Ko zataga khamal, haka ta dinga yawo, harta giji ko alamarsa bata gani ba, wani rafi ta tsinka nisa da ita, haka kawai taji tana sha'awar zuwa wajen, takon mutum taji abayanta kamar ana binta, aiko haka dinne, wai wayawar da zatayi caraf suka hada ido dashi, ta razana sosai da ganinsa musamman dataga alamar wajenta zaizo, taso tayi karfin halin danne hawayen da keshirin zubo mata sbd tsabar firgici Amma takasa,

Kara sowa yayi ya tsaya daf da ita yana mata kallon tuhuma........


By

πŸ’ž MeerahπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
[3/30, 1:44 PM] Meerah πŸ’ž: 🀴🏻🀴🏻🀴🏻 prince khamal🀴🏻🀴🏻🀴🏻



🌹🌹🌹🌹🌹


By

🌹🌹🌹
MeerahπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
08068971503



ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️✍️



Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai



πŸ…ΏοΈ 2️⃣1️⃣_2️⃣2️⃣



Murmushi tayi cike da farinciki "ohh ni Afra meyasa ma na boye banfito nafada masa Ni dince ba, a'a bazai yiyu na fito a haka da wadannan kayan ajikina, ta dubi kayan da aka bata na hadimai, alhmdlh Allah nagodema daka bayyana minshi, Ashe shine ake cema prince Yazeed danaji jakadiya nafada, nan take ta tuna da kullin da suka shirya masa, da sauri tabar wajen, ta nufi sashen gimbiya Fulani, a guje take ko hanyar ta bata gani, jinkawai tayi tayikaro da mutum.

Saukar Mari taji a kuncenta "ke wacce irin dabbace haka zakizo ki bangaje ni"? Kausar ce take mgn cikin zafin rai.

"Kiyi hakuri ranki yadade wlhi ban kula dake bane" mtseew "taya Zaki kula dani bayan bakida hankali babu kwakwalwa akanki, banza, jaka, dabba" tana gama fadanta ta wuce, Afra dai batace komai ba, ranta ya baci sosai Amma ba yadda zatayi dole tayi hakuri, ci gaba tayi da tafiyarta, daidai kofar shiga falon ta tsaya tana tunanin ta inda zata fara, tabbas jakadiya ta bawa hadima wannan gubar Kuma gashi khamal ya koma part dinshi, tabbas idan banyi saurin dakatar dashiba zaisha wannan gubar, da sauri tabar wajen..

Gudu takeyi sosai harta kawo part dinshi tanashirin shigane dogarawa suka dakatar da ita, sukayi mata alamar ba'ashiga dakai, magiyi tashiga yimusu Amma Sam suka hanata shiga, haka ta hakura ta koma gefe ta zauna tanata faman kuka..

Bangaren khamal kuwa Yana komawa part dinshi kishin gida yayi ajikin kujerar dake cikin k'aya taccen falon, Nasir yaso yaja khamal da fira Amma Sam yaki daga karshema cewa yayi ya fita yabashi waje yanason ya zauna shikadai, jiki babu kwari ya tashi yabar wajen.

Hadimar ce ta shigo dauke da abinci da lemo ahannunta, ajiyewa tayi agabansa zuba masa tayi niyyar yi sai ya dakatar da ita yace lemo kawai yake bukata, tsiya ya masa tayi ta mika masa yace ta ajiye zai dauka, tana ajiyewa tabar wajen cike da fargaba..

Daukar lemon yayi zaikai baki kenan saiya ga photo Afra ya bayyana a fuskar tv dake jikin bangon dakin, sanarwar nemanta ne akeyi tare da aza makudan kudi ga duk Wanda ya ganta..

Cup dinda ke hannun sa ya fadi kasa ya fashe sakamakon rawar da jikinsa yafarayi, nan take ya zube awajen Babu numfashi......

Hadimar najin karar fashewar abu tasan maganin da ta zuba masane yafara aiki, da sauri ta lek'o ta ganshi kwance Babu alamar numfashi a tare dashi, murmushi tayi tace yau taka takare khamal saidai wani bakaiba, da sauri ta kwashe glass dinda ya fashe ta sauke lemon ta dauko wani ta aje awajen, nan take ta kurna ihu......

A guje fadawan gidan suka shigo, Babu bata lkc suka daukeshi suka nufi asibitin dake cikin masarautar dashi....

Afra na gefe tana ganin anwuce dashi nantake ta yanke jiki ta Fadi, itama daukarta akayi aka wuce asibitin da ita...

Bayan likitan ya gama duba khamal ne itama ya dubata....

Mai martaba ne tare da gimbiya Nafisa wato ummi suka shigo office din doctor, Mai martaba yace "doctor meya ke damun son ne? sbd bada dadewa ba tare muke dashi a fada, lafiya Lau yacemin zaije yayi wanka ya dawo, Kuma Babu alamar koda zazzabi tare dashi"

Ajiyar zuciya likita ya sauke yace "Allah yabaka nasara khamal yanacikin matsanan ciyar damuwa, tabbas akwai abinda yake so, domin Yana gab da kamuwa da ciwon zuciya, sai dai Kuma akwai wata yarinya da aka kawosu tare itama matsalar su dayace"

Hankalin ummi yayi matukar tashi, "likita kayi wani abu Dan Allah ka kubutar min da dana, shine farincikina" kuka ne ya katse mata maganar.

"Likita yanzu menene mafita banason wani abu yasame shi" Mai martaba ya fada cikin matsanan ciyar damuwa..

"Allah ya baka nasara abu dayane zaayi masa Wanda zai kub'utar dashi, shine anema masa abinda yakeso tun kafin wani abu ya sameshi, sannan itama waccen yarinya tata matsalar tamafi tasa domin ita harta kamu da ciwon zuciya sbd matsananciyar damuwa"

"Wacece ita"? daddy ya fada Yana kallon likita, "Nima bansanta ba da alamar baiwace dannaga tufafin bayi ajikinta, saidai a yadda naga yanayin jikinta ko kadan batayi Kama da bauwa ba domin Babu alamar wahala koka Dan ajikinta"

"Zamu iya ganinta kuwa" Daddy ya fada Yana kallon likita, "ehh zaku iya zuwa tama farfado" tashi sukayi sukaje dakin da take..

Zaune take akan gadon hawaye nabin kuncinta, tana ganin ummi gabanta yayi mummunan faduwa, hawayen da takeyi tuni suka bace sbd tsabar tashin hankali..

Itama ummi kallon ta takeyi da sake sake azuciyar ta..

Saurin mikewa Afra tayi ta russuna kasa ta duke kanta Dan ummi ta daina kallon ta, gai shesu tayi cikin girmamawa kamar yadda taga kuyangi nayi.

Daddy ne ya amsa cikin sakin fuska domin shikan yaji yarinyar ta kwanta masa arai, dama khamal zai yadda daya hada auren su ..

"Kamar nasanki ko" ummi ta fada tana kallon Afra dake sunkuye a kasa, dago kanta tayi ta kalli ummi tace "a'a ranki ya dade kila da kamace kawai kika gani"

Hmmmm numfashi ummi ta sauke tace "ba Kama bace Ina tunanin kamar kece Afra wadda akaso Nasir ya aura"

Rassssss gaban Afra ya hau dukan uku uku cikin inda inda tace aaaa' aaaa rannnnnnki ya daddddde bani bbbace Ina gggganin kama ce kawai, Ni sunana Hajara iyayena a cikin wani kauye suke Wanda ke cikin jahar kaduna", (kauyen su khamal kenan )

"Nima Afra danake mgn acikin garin kaduna take", "ya isa haka gimbiya tunda tace ba ita bace ai shikenan, toma idan itace mezaisa tazo gidannan"? Daddy ya fada.

"Ranka yadade wlhi da kaga wannan yarinyar da zaka rantse da Allah itace anan, Kuma zata iya zuwa gidannan sbd batasan cewa Nasir Dan kanwarka bane"

"To shikenan koma dai menene ya isa hakanan, ko itace koba ita bace tunda harta zonan babu ruwanmu da ita, tunda ita ta kawo kanta aikin bauta anan"

"Amma ranka yadade atunanina yadace asanar da iyayen ta sbd dazu naga ana sanarwarta aginda television"

"Bazan sanar da kowa ba, sbd mahaifin yarinyarnan ya wulakanta mu awajen daurin auren, daga karshe ya tafi gida ya barmu kamar wasu wawaye awajen"

Yana gama fadar haka ya fice daga dakin, itama umma bin bayansa tayi.

Suna fita Afra ta lallaba tabar asibitin, gaba daya cikin tashin hankali.....



By

MeerahπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

Share plssss πŸ™πŸ™πŸ™πŸ™
[3/30, 1:44 PM] Meerah πŸ’ž: 🀴🏻🀴🏻🀴🏻 prince khamal🀴🏻🀴🏻🀴🏻



🌹🌹🌹🌹🌹


By

🌹🌹🌹
MeerahπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
08068971503



ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️✍️




Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai




"Wacece ke" ya fada fuskar sa babu alamun wasa, jikanta har rawa yakeyi sbd tsabar tsoro, shikenan yau asirinta ya tonu, idan iyayenta suka San inda take tabbas bazasu kyale taba,

Fuskar ta taji ya taba yanason ya share bakin data shafa , da sauri taja baya tace "ni hadima ce acikin gidannan bansanka ba ban taba ganin kaba ka kyale ni" tana k'okarin guduwa ne yayi saurin riko hannunta, tafiya ya farayi Yana rike da ita, taso k'wace hannun ta Amma ta kasa,

Bakin tafki ya tsaya yakalleta baice komai ba ya duka ya d'ibi

3 / 8