Chapter 7 Reading PRINCE KHAMAL Boyayyen Sarauta By Meerah READ HAUSA Novels

PRINCE KHAMAL Boyayyen Sarauta By Meerah

Author :  Meerah Category :  African Stories & Novels

Chapter   7 / 8

18K to 21K   out of 23.3K words

dad'e suna biyarta da gudu Amma basu kamata ba, tana cikin gudu tayi tuntub'e da wani dutse ihu ta kurma da k'arfi saida dajin ya amsa, kafarta taji ciwo sosai dalilin hakane ta kasa gudu, juyawa tayi taga wad'annan mutanen da suka biyota suna fad'a da wani mutum kasan cewar duhune yasa bataga fuskar shiba, sundad'e sunayi daga k'arshe dai wannan mutumin yasamu nasarar halakasu gabaki d'aya.

Tana nan zaune ta kasa tashi daga wurin da take, ganin mutumin tayi yazo wajenta ya d'auke ta yafara tafiya da ita, tsoro ya kamata sosai zuciyarta bugawa takeyi kamar ta tsage kirjinta.

Bayan wani dutse ya kaita ya ajiyeta, d'aure mata k'afar yayi tabar zubar jini, ahankali ya bud'e bakinsa yace "meyasa kika biyoni nan, bakisan wajennan nada had'ari bane"

Cikin farinciki tace "khamal dama kaine"? rungumeshi tayi tana murmushi tace "Alhamdulillah yau burina yacika", kallon sa tayi tace wlhi harna cire raina da sake ganinka arayuwata"

Murmushi yayi Wanda ya K'ara bayyanar da kyaunsa yace "ni Kuma haryanzu bancire ran sake had'uwa dake ba, saidai k'addara ta gifta tsakanin mu inaji ajikina burinmu bazai tab'a cikaba" "burinmu zaicika acikin kwanakinnan" ta fad'a tana kallonsa da k'aya taccen murmushi a fuskar ta, da mamaki yake kallonta yace "Afra kinsan me kike fad'a kuwa"? tace "nasan komai khamal, nasan duk abinda ke faruwa, Kuma a halin yanzu iyayenka suna nemanka, sunyi nadamar abinda suka yimaka, sbd na fad'a musu gsky cewa baka da laifi" cikin mamaki yake kallon ta yace "Afra ya akayi kikasan iyayena" murmushi tayi tabashi lbrn komai harda abinda ke tsakaninta da Nasir bata b'oye masa komai ba, khamal yayi mamaki sosai domin bai tab'a tsammanin Nasir zaiyi masa haka ba, domin shi ya rikeshi da zuciya d'aya a matsayin d'an uwansa Kuma aminin sa.

Baice komai ba sai kokarin mik'ewa tsaye dayakeyi, rik'eshi Afra tayi tace "khamal Ina zakaje acikin Daren nan"? Murmushi yayi yace "zanje na samo Miki y'a y'an itace domin sune kad'ai abinci acikin dajinnan" tace "a'a na koshi kadawo harda safe" yace "a'a kibari yanzu zandawo nasan kinajin yunwa, sbd nasan wad'ancen mutanen basu baki abinci ba" cikin mamaki take kallon sa tace "ya akayi kasan basu bani abinci ba"? tsayawa yayi Yana kallon ta yace "sbd Nima nayi zama a hannun su, basu tab'a bani Koda ruwa ba" ajiyar zuciya ta sauke tace " yanzu dai kadawo wlhi bazan iya zama a wajennan ba tsoro nakeji" jin tace tsoro takeji yasashi dawowa badan yasoba, zama yayi yana tsokanar ta,

Haka suka kwana cikin dajin ko wannen su cikin farinciki. washi garima haka suka kasance kowannen su cikin farinciki, a wajen suka yini da sunji motsi da sauri khamal zaisa Afra ta boye shikuma ya haye icce Yana kallon abinda ke faruwa acikin dajin.

Sunso fita Amma ba dama sbd kota Ina mugayen mutanen suna zagaye dasu..


By

MeerahπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
[3/30, 1:44 PM] Meerah πŸ’ž: 🀴🏻🀴🏻🀴🏻 prince khamal 🀴🀴🀴



🌹🌹🌹🌹🌹🌹



By

🌹🌹🌹
MeerahπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
08068971503



ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️✍️



Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai




πŸ…ΏοΈ 4️⃣5️⃣-4️⃣6️⃣




Zaune suke bakin wani rafi, suna kallon yadda ruwa ke gudana, wurin yayi matuk'ar birge Afra, kallon ruwan takeyi ta mayar da hankalinta baki d'aya a wurin, shikuma khamal hankalin sa na wajenta, ya kulada yadda take kallon wajen, murmushi yayi ya d'ibi ruwa ya watsa mata, zabura tayi da k'arfi ta tsorata sosai, shikuma dariya ta bashi ganin yadda ta zabura, ita Kuma haushin dariyar da yake mata taji ruwa ta d'iba itama danta watsa masa, yana ganin haka ya tashi da sauri, itama tashi tayi, yana ganin da gaske watsa masa zatayi ya fara gudu tana biyar sa, sundad'e suna gudu a dajin Saida Afra ta gaji sannan ya tsaya, rungumeshi tayi tace "habibina ina matukar k'aunarka" kara rungumeta yayi yace "nima ina kaunarki habibaty, kallon juna sukeyi cikin shauk'in so da k'auna, sauke kanta tayi kasa tace "naji dad'in zuwa dajinnan, Yana birgeni sosai, sannan kuma gashi Kana kusa dani, inajin kamar muci gaba da zama anan" murmushi yayi yace "idan mukaci gaba da zama anan taya zamuyi aure? Kinsan fa na matsu banga munyi aure ba" da haka suka cigaba da hirar su cikin farinciki, gwanin sha'awa.

Abba ne zaune gaban Mai martaba suna tattauna yadda zasu sake neman y'a y'ansu, domin tunda basuga gawar suba basu yadda sun mutu ba, sun yanke shawarar nan da kwana uku zasu had'a rudunar jami ai domin a kaiwa wad'annan mutanen hari, Abba ya dad'e anan suna fira kafin yayi musu sallama ya koma gida (kaduna).

Kwance saude take rai a hannun Allah ta dubi Baba dake zaune gefenta tace "Baba kayi hakuri ka gafarceni na aikata babban kuskure arayuwata nabiyewa son zuciya da Kuma zugar Inna, na fad'a cikin tsaka Mai wuya, Baba dan Allah ka yafemin Kuma ka nemamin gafarar yayana khamal, na cutar dashi, Baba khamal bashi da laifi, cikin dake jikina banashi bane" kukane ya katse mata mgn, cikin tashin hankali Baba yace "bangane mekike fad'a ba, idan ba cikin sa bane cikin waye"? "Cikin Dauda ne" ta fad'a a takai ce

Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un Baba yake ta maimai tawa yace "Saude mekika aikata haka meyasa zakiyiwa d'an uwanki haka? Kin cutar dani Saude, kin rabani da d'anda nake masifar so arayuwa ta, meyasa zakiyimin haka? Me khamal yayi miki da zaki yimasa wannan k'azafin? Kin bani kunya saude wlhi kinyi abinda ban tab'a zato ba" cikin b'acin rai ya tashi da niyyar fita Inna laure tace "malam Ina zakaje haka cikin wannan yanayin"? Harararta yayi yace "bansani ba, nace bansaniba mutuniyar banza mutuniyar wofi, ki duba halin da kika jefa y'arki a ciki sbd kwadayin ki da son abin duniya, daga k'arshe kun rabani da d'ana yaro mai natsuwa da hankali da sanin ya kamata, meyasa idona ya rufe a wannan lkc? meyasa ban goyi bayansa ba? Laure wlhi ko kad'an baki cancanci zama uwaba, kin tarwatsa rayuwar y'arki da kanki, kin nisantani da khamal Wanda nafi so fiye da y'ar dana haifa da cikina" hawayen sa ya share, ya fice daga gidan cikin kunci da damuwa.

Kai tsaye wajen Dauda yaje yayi masa fad'a sosai, daga karshe dai Dauda yace "aiba laifinsa bane Saude ce ta kawo kanta wajensa saboda ya bata kudi" ran Baba ya k'ara b'aci sosai, gida ya koma ya iske Saude kwance kamar yadda ya barta yace "ke Saude me kikayi da kud'in zubarda k'ima da mutunci da kika karb'a a wajen Dauda"? Muryar ta na rawa tace " Inna ce tace nasamo mata kudi zatayi zubin a dashe Kuma bata da kud'i shiyasa naje wajensa ya taima kamin, yace bazai baniba saina amince da buk'atarsa, da fari ban amince ba Saida Inna tace naje na samo mata kota halin k'ak'a ne"

Tasss!! Tassss!! Karar saukar mari kakeji wanda Baba ya yiwa Inna Laura yace "kije nasakeki saki d'aya" Saude dake kwance cikin matsananci rashin lfy, nan take numfashinta ya sark'e kafin kace wani abu tuni rai yayi halinsa, innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un, yaude Saude ta amsa Kiran Allah, saidai muyi mata fatan dacewa.

Fad'ar halin da Baba ke ciki b'ata lkc ne domin ya shiga cikin tashin hankali mara misaltuwa, itama Inna Laure ba bayaba domin idan kaduba fuska zakace tafi Baba shiga cikin tashin hankali.

Bayan anyi sadakar bakwai Baba ya shiga tunanin ta inda zai fara neman khamal, domin ya d'auki alk'awarin matukar yanada rai to saiya nemo khamal duk inda yake, ya nemi gafarar sa, yana zaune tunani ya fad'o masa da sauri ya tashi yasa babbar rigar sa da hula ya fita, bai tsaya ko inaba sai kofar gidansu Afra kamar yadda khamal yayi masa kwatancen gidan, baisha wata wahala ba wajen gane gidan kasan cewar gidane Wanda kowa yasanshi a gari.

Sallama yayi Mai gadi ya amsa Yana yimasa kallon sama da kasa, yace "malam wakake nema a gidannan"? Da sauri Baba yace "mai gidan nake nema ayimin sallama dashi dan Allah"

Kallon wulak'anci mai gadi yayi masa yace "kaga malam Alhaji dai ya gama bayar da sadak'a dan haka ka koma inda kafito" "Allah sarki yallab'ai niba sadak'a nazo nemaba, nazo nan ne dannayi wata muhimmiyar mgn dashi"mai gadi yace kaga malam Alhaji baya mgn da k'ask'antattun mutane irinka, kaga tafiya ta karka yadda na fito na tarar dakai a wajennan" Yana batun rufe k'ofar saiga Alhaji ya tako har get din, dan yana shirin shiga mota yaga maigadi na mgn da wani cikin d'aga murya, shine yazo yaga ko waye.

Baba na ganinsa ya zube k'asa yana sharar hawaye yace "ranka yadade kayi hakuri nasan ka gargad'e ni cewa karna koma bari d'ana khamal yazo wajen y'arka, kayi hakuri dan Allah ka taimakamin" ajiyar zuciya Abba ya sauke yace "meke tafe dakai" share hawayen sa Baba yayi yace "nazo nan ne danneman taimako, inason ka kataimaka ka tambayamin y'arka ko tasan inda d'ana yake"

Murmushi Abba yayi yace " wanne d'a kake mgn akai"? D'aga kai Baba yayi yalli Abba yace d'ana khamal nake tambaya" murmushi Abba ya sakeyi yace "ba naji lbrn cewa ka koreshi ba"? Baba yace "ehh ranka yadade nakore shi a kan wani dalili Wanda sai yanzu na gane gsky bashida laifi kazafi akayi masa, a yanzu na gane kuma inason na nemosa duk inda yake muci gaba da zama tare" Abba yaji tausayin Baba sosai, domin shima yayi nadamar korarsa dayayi a baya, saigashi a yanzu yafishi matsayi yafishi kudi yafishi komai na more rayuwa.

Abba ya cewa baba su shiga cikin gida akwai lbrn da zai bashi, haka ko akayi a falon sa suka zauna Abba ya bawa Baba lbrn komai duk abinda ya faru har yanzu da ake nemansu gaba daya, Baba ya jajantawa Abba tare da yimusu addu'ar fatan alkhairi daga k'arshe yace idan za'aje wannan dajin asanar shi, shima zaitafi..


By

MeerahπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
[5/12, 12:28 PM] Meerah πŸ’ž: 🀴🏻🀴🏻🀴🏻 prince khamal 🀴🀴🀴



🌹🌹🌹🌹🌹


By

🌹🌹🌹
MeerahπŸ’žπŸ’ž



ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️



Dasunan Allah mairahama Mai jinkai



πŸ…ΏοΈ 4️⃣7️⃣-4️⃣8️⃣




Cikin sand'a suke tafiya ahankali kada suyi motsi babba ajisu, bayan icce suka lab'e suna leken mutanen dake wajen zaune da bindigogi a hannun su, kallon khamal Afra tayi tace "honey yanzu haka zamuci gaba da zama acikin jejinnan" kwallar da take shirin fitowa ta gangaro a fuskarta, kayataccen murmushi yasakar mata yace "a'a bazamu cigaba da zama anan ba Allah zai kawo muna dauki, ki kula da kyau kada kiyi dogon motsi zamu jira anan idan suka wuce sai muje na tuno kyautar da kika bani aranar nan saimu Kira gida azo afitar damu" itama murmushi tayi tace "shikenan honey matukar Ina ganin wannan kykkyawan murmushin a fuskarka to bazan damuba Koda zamuyi shekara awannan wajen" murmushi yayi Wanda ya bayyanar da fararen hakoran sa ya Kara fitar da ainihin kyansa yace " kin tabbatar Zaki cigaba da zama anan tare Dani"? Gyad'a Kai tayi tare da murmushi a fuskar ta,

Ajiyar zuciya ya sauke yace " idan harkin tabbata to mukoma muci gaba da rayuwa anan" rike hannun ta yayi yajata alamar sukoma, da sauri ta rike hannun sa tace " a'a honey nafison mukoma gida sbd muyi rayuwar aure Mai cike da farin ciki, nakasance tare da wanda nake masifar so a rayuwata" murmushi yayi ya rungumeta yace "Ina matukar sonki Afra bazan taba iya rayuwa ba idan har bubuke a tare dani kinzamo jini da tsokar dake jikina, kasan cewa zama tare dake shine warwala da annurin da zai bayyana a fuskata da jikina baki daya, Afra bansan ta yadda zannuna miki godiyata ba, kin aje karatunki sbd ni kinbar iyayenki sbd ni kin sadaukarda rayuwarki duk sbd ni, Afra nayi miki alk'awarin kasancewa dake har karshen rayuwata acikin ko wanne irin yanayi, ke ta musamman ce a wajena bazan taba mantawa da halaccin dakikayimin ba" hawayene suka gangaro masa,

Hannu tasa ta share masa tana murmushi tace "kadaina tuna abinda yariga ya wuce habibina soyayyarka dake gudana acikin jikina bazata tab'a barina nayi nesa dakai ba, duk inda kashiga a duniyarnan saina nemoka koda hakan zaisa narasa rayuwa ta, gara na mutu a lkcn da nake kokarin taimaka maka dana zauna a gida ciwon sonka ya kasheni"

"Bazaki mutuba insha Allah, zamu rayu tare mu reni 'ya 'yanmu da kanmu" kallon juna sukeyi kowannen su cikin farinciki, suna cikin hakane Afra taji motsin wani abu a k'afar ta, da sauri ta duba, wata irin razananniyar ihu ta saki ganin maciji ya nad'e mata k'afa πŸ™„ da sauri Kamal ya riketa Yana kokarin guduwa da ita saiga mutanennan sun zagayesu kowanne da bindiga a hannunsa,πŸ€¦πŸ»β€β™€οΈ

D'auresu sukaye ga icce daya sukaje suka sanar da ogansu, yace abarsu nan d'aure har gobe a kashesu, haka ko akayi anan suka yini suka kwana daure, washe gari Afra ta kalli Kamal cikin mawuyacin hali domin d'aurin da sukayi misu ya azabtar dasu sosai, zuba kawai jini keyi a hannayensu da kugunsu da aka daure, tace " Kamal yau inacikin farinciki sosai a rayuwata" cikin razana Kamal ke kallon ta yace "Afra wanne farinciki kikeyi munacikin wannan halin"?

"Kamal ina cikin farinciki sosai yau sbd yaune zan mutu inatare dakai, yaune zanmutu kaina yana saman kafad'arka, Kamal inason naji kalma daya kafin numfashina na k'arshe ya fita daga jikina" hawaye yana zuba a fuskarsa cikin tashin hankali yace "Afra kidaina fad'in wannan mgn wlhi zuciyata bazata iya jure jin wannan kalaman naki ba idan baso kikeyi zuciyata ta buga a wajennan ba"

"a'a khamal zuciyarka bazata bugaba sbd Kai jarumine inada tabbacin hakan daga gare ka, Kamal kalmar danake bukatarji kafin numfashina ya fita itace kalmar daurin auren mu, dan Allah kada kabari a dauki gawata batare da andaura muna aure ba" 😭

"Ki daina fadin wannan mgnr Afra inaji ajikina Afra bazaki mutu kibarni ba, zamu rayu tare insha Allah" murmushi kawai tayi batare da tace komai ba tana kallon sa shima ita yake kallo, murmushi karfin hali shima yayi, shikadai yasan irin radadin da yakeji acikin zuciyar sa.

Suna cikin hakane saiga mutanen sundawo tare da ogansu, karasowa yayi wajensu yace "kune kuka gudu daga hannun mu ko Kuna tunanin zaku tseremuna ne, hhhhhhhhh wata irin dariyar mugunta yayi yace "shiyasa nacewa yarana kada Wanda yaje nemanku da kanku zaku kawo kanku a wajennan sbd duk dajinnan zagaye yake da yarana duk inda kukaje sai sunkama ku", hhhhhhhhh yana gama dariyar sa yace ku halbesu, yaje yasamu wuri ya zauna.

Mutun biyu suka saita bindiga, d'aya ya saitawa Kamal d'aya Kuma ya saitawa Afra, daga Kamal har Afra sun sadakat domin sun tabbata cewa yau itace ranar mutuwar su, wani mugun yawu suka had'iye da kyat suka rufe idanu suna jiran saukar alburushi a kansu.


Harbin bindiga biyu saukar alburushi biyu a lokaci d'aya, πŸ™†πŸ»β€β™€οΈ d'aya ya sauka a k'irjin Afra, d'aya Kuma ya sauka a bayan k'eyar wanda ya saitawa Kamal bindiga.

Sbd tsabar tashin hankali Kamal harda gutun hawayensa ya runtse idanunsa gingingin atunaninsa shine aka harba, Saida yaji ansake harba bindiga sannan ya bud'e idanunsa ganin mutanen nan yayi kwance cikin jini kowannen su ya fad'i babu rai, murmushi yayi azahiri yace "alhamdulillah Allah ya kawomuna dauki Yana fad'i yana murmushi, jin Afra batace komaiba yasa yakai dubansa gareta, lkc d'aya ya fita hayyacin sa cikin razananniyar K'ara yace " Afra! Afra! Afra! Afra kitashi kada ki mutu kibarni" Afra kam jini ke gudana tundaga kirjinata har kasa kamar an bude fanfo,


Da gudu maimartaba da Abban Afra harda Baba sani suka karaso wajen, sukuma jami'an da suka zo dasu sunacen suna gwabza fad'a tsakaninsu da wad'annan mutanen, daga k'arshe dai saura suka gudu aka Kama sauransu.

Banyesu akayi Afra kam babu alamar numfashi a tare da ita, jijjigata Kamal ya shigayi yana kiran sunanta yana kuka yana gunji saikace mayunwacin zaki ya dad'e Yana jijjigata kafin numfashita ya dawo sama sama kallon sa tayi cikin mawuyacin hali tace "karka damu Habibi kadaina kuka ina nan tare dakai Koda na mutu ruhina bazai barka ba"

"Afra kada kitafi ki barni wallahi bazan iya rayuwaba idan har babu ke, dan Allah kada kitafi kibarni " da gyar ta d'aga hannu ta share masa hawaye tace "bazan barkaba Habibi ina matukar sonka" kallon Mai martaba da Abba tayi dake tsaye suna kallon su tace Abba inason adaura muna aure a wajennan plsss" πŸ™

Haka akayi aka tattatara fadawanda ke wajen harda jami'ai Mai martaba ya fidda kud'i naira dubu d'ari uku yabawa baba sani yace ya biya sadaki sbd shine waliyyin Kamal yayinda Abba yayi waliccin Afra haka aka daura aure kowa na kuka 😭 ana gama daurin aure Afra tace Alhamdulillah ko yanzu na mutu burina yacika tana gama fad'in haka ta sauke ajiyar zuciya daga nan numfashinta ya tsaya cek......


Anan zan dakata saimun had'u a shafi na gaba insha Allah


By
MeerahπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

Share fi sabilillah πŸ™πŸ™πŸ™
[5/12, 12:28 PM] Meerah πŸ’ž: 🀴🏻🀴🏻🀴🏻 prince khamal 🀴🀴🀴



🌹🌹🌹🌹🌹🌹



By

🌹🌹🌹🌹
MeerahπŸ’žπŸ’žπŸ’ž




ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️



Dasunan Allah mairahama Mai jinkai




πŸ…ΏοΈ 4️⃣9️⃣-5️⃣0️⃣




Fadawane cike a harabar asibitin tare da Jami'ai kallo daya zakayi musu kagane cewa suna cikin damuwa.

zazzaune suke sunajiran fitowar likita, kamal kam yakasa zaune ya kasa tsaye, idanunsa sun kunbura sunyi ja sbd kukan dayayi kamar ransa zai fita, gabansa na tsananta fad'uwa domin shi ya tabbatar cewa Afra ta rasu Daddy ne yace sai ankawota asibiti.

Lokaci sai gudu yake awanni na tafiya abu kamar wasa ya d'auki lkc tunsuna jiran bayanin likita harsun fidda rai domin likitocin sunkasa yi musu bayani, duk Wanda ya fito a guje yake wucewa basuda lkcn mgn.

Bangaren Afra kuwa har dare likitoci na kanta sunkasa samo numfashinta ya dawo normal saidai yanzu an d'an samu cigaba domin bayan wasu awanni tana sauke numfashi guda, da wannan likitocin suka samu tabbacin bata mutuba.

Jiki a sanyaye likitan ya fito, da sauri sukayo kansa kowa da tambayar da yake yimasa,

7 / 8