Chapter 31 Reading Rayuwa da Giɓi Complete Hausa Novel READ HAUSA Novels

Rayuwa da Giɓi Complete Hausa Novel

Author :  BATUL MAMMAN Category :  African Stories & Novels

Chapter   31 / 42

90K to 93K   out of 124.8K words

neman albarka.

"Kayan abinci, kayan bu™ata na gida irin su sabulu da kuWin kashewa ga iyayensu. Duk masu aiki da masu"

kasuwanci suna contributing. A matsayinsa na babban namiji duk da cikin matan akwai waWanda

"samunsu yafi nashi, amma yana ™o™arin ganin ya yi bajinta. A haka kuma yake bawa Mamin dubu talatin"

duk wata.

"""Kai, Ahmad. Baka ce komai ba."""

Ya ma manta waya yake.

"""Allah Ya hore. Sai da safe."""

Ko minti goma basu yi da gama wayar ba ta sake kira. Ya san zancen ba zai wuce na kada ya dawo da

Salwa ba. Shi yasa ya™i Wauka. Zai kaita gida gobe in sha Allahu.

˜arfe bakwai da rabi Anti Zahra ta same shi a Waki wai Salwa ta fita.

"""Bangane ba. Ina ta tafi?"""

"""Ina ta tambayarta tana kuka. Da alama bata son tafiyar. Da ka ™yaleta."""

A harzu™e ya tashi yana ta faWa. Sai a lokacin Anti Zahra taji me yake faruwa. Ta ma kasa comprehending

wannan al'amari.

"""Don Allah kayi shiru kada Taj ya ji. Kwanansa biyu yana fama da zazzaSin nan mai zafi. Sannan ko babu"

"komai ka haWa uwa da ita. Mutumcinta abin karewa ne a wajenka komai rashin daWin da abin ya yi maka."""

"""Gidan wa zata da safiyar nan? Idan tana tunanin zan bita ne wallahi tayi kuskure."""

"""Naji. Ka san ba za ta wuce gidan ™anwar babanta ba ta Sheka. In ba nan ba kuma ™ila ta wuce Bauchin."""

"""Ita ta sani."""

Sai dare ya Wauki wayar Mami. Ta ™are masa tanadi kuwa. Shi kuma ya tsaya akan bakansa na cewa indai

Salwa ta dawo gidansa to Bauchi zai maidota. Ba zai zauna da mara kunyar da bai isa ya faWa mata taji ba.

Mami da taga ya™i tan™waruwa ta ha™ura.

"""Shegen yaro mai halin ubansa."""

***

A kwana biyun nan kullum Hamdi sai ta kira Taj. ZazzaSi ne irin wanda ya kan zo gama gari mai shiga gida

gida. Ita kanta tana mamakin yadda ta damu da ciwon nasa da kuma rashin ganinsa. Da Zee ta tsegumtawa Sajida halin da take ciki haWuwa su ka yi suna tsokanarta.

"Zee ta ce ""Salman Khan ya sallame zuciyar Hamdi."""

Ita kuma Sajida tana dariya ta tuna mata tsohon ™udurinta.

"""Ta dai gama cika bakin bata son namiji mai girki. Yanzu gashi nan mai gidan abinci ya hanata sukuni."""

"Da yake a wayar Zee ake ta bidirin, gajiya tayi da kare kanta ta tsuke bakin nan."

"""Aljannar mace dai tana ™ar™ashin ™afar mijinta. In kuma kuna ba™incikin kada na samu ne sai in ji."""

Sajida da Zee me za su yi kuwa banda dariya. Ashe rana irin wannan za ta zo musu a kurkusa haka basu

sani ba.

˜yalesu tayi ta koma kitchen wajen girkinta. Tana aiki tana tunaninsa. Yau ce rana ta uku tun zuwan da

ya yi ta kira masa Kamal. Wayar ma idan sun yi ba wani jimawa su ke ba. Gaisuwa ce da jin yaya jikin

nasa. Šan wasan nan duk ya daina.

"""Ke!"""

A firgice ta kalli Yaya. Bata san tun yaushe take tsaye tana yi mata magana ba.

"""Jikin nasa ne har yanzu?"""

"Wayancewa tayi kamar bata gane ba ""wa?"""

"""Garinku in kin san shi. Wa ma za ki ce min?"""

˜asa ta kalla a kunyace. Fuskarta babu walwala. Yaya ta fahimci har yanzu a kwance yake.

"""Jiya dama Abbanku yake zancen zuwa a dubo shi. Zan sake yi masa magana yanzu in sha Allah a waya."""

Fuska mai tona asirin zuciya. A take fuskar Hamdi ta washe. Yaya ta kama baki tana salati.

"""Anya dama ba shirya maganar auren nan ku ka yi da Taj ba? Cikin ´an kwanaki kin zurma haka?"""

"""Ni ban zurma ba Yaya"""

"""Tsiwar ma ai naga ta ragu. Allah Ya yiwa aure albarka. Amma ki rage murna don ba dake zai je ba. Halifa"

"zai Wauka."""

"""Kai Yaya, ni yaushe na ce zan je?"""

"Dariya tayi ""nima wasa nake miki. Ai na san ko tayi aka yi miki za ki ce a'a."""

Bata ™ara magana ba tunda ta gane Yayan ma tsokanarta take yi. To ita har me tayi da ake mata wannan

fassara?

*

A Sangaren Taj abin da ya zata zazzaSin gajiya ne ashe combo ne na typhoid da maleriya. Ciwon da ya

manta rabonsa da yi. Shi ne ya yi masa rubdugu irin wannan. Kuma da yake zafi ake yi sai ya haWu goma da ashirin. Dalilin zazzaSin ne ma su Mama su ka tsahirta da sanya lokacin biki. Shirye shirye dai sai abin da ba a rasa ba. So su ke amarya ta shiga Wakinta nan da sati uku ko wata guda. A nasu shirin idan ta tare da wuri za su Sata shirin Alhaji. A ganinsu dama wata ukun nan da ya bayar ya yi ne saboda sanin cewa

da wahala ace Abba Habibu yana da abin da zai yi bikin wata ´ar nan kusa.

Sosai Ahmad yake bashi kulawa. Musamman bayan tafiyar Salwa. Fushin da ya fara akan yadda aka yi

mata dole ya kau da ya gaskata ita ce ta janyowa kanta.

Kamal ne dai tun ranar da ya kai shi asibiti ya ™ir™iri tafiya washegari. Ciwo ke neman kayar dashi kuma

baya son kowa ya sani. Haka ya tattara ya tafi asibiti. Mubina ta kwantar dashi. Magunguna tana iya

"bakin ™o™arinta. Bata so su fara dialysis domin ana kaiwa wannan matakin, transplant (dashe) shi ne best"

option Win da zai rage.

Ranar da ta kwantar dashi bayan ya zama stable ta kira Yaya Kubra. Dama kullum jiran wayarta take yi.

Tana gani kuwa ta bar ayyukan gabanta ta tafi asibitin.

"""Akwai shirin da ki ka fara yi ne Doctor saboda in san next course of action?"""

"Yaya Kubra ta gyaWa kai ""na fara bincike ta bayan gida. Wata questionnaire na ™ir™ira a google form nace"

"ta research Wina ce. Ita na tura a groups na family ake ta cike min. Harda families Win duka matan gidan mu. Kuma da yake da suna so far na sami mutum huWu that are rhesus negative."""

"Idanun Mubina harda ™walla ta ce ""Masha Allah. Amma dangin kusa ne?"""

"""Surprisingly daga dangin Hajiya na sami uku. Šaya ne a dangin Umma. Ai jinsi baya hana bayarwa ko?"

"Duka huWun mata ne."""

Mubina ta ce gender baya hanawa.

"""Amma fa Kamal A negative ne. Indai ba irin nasa ba kinsan sai dai O ko AB negative ko?"""

"""Dukkaninsu O negative ne. Yanzu su Alhaji ya rage su sani sai a tuntuSe su."""

"""Muje ki ganshi. Akwai Nephrologist da na fara magana dashi daga Port Harcourt. Idan an sami nasarar"

"samun mai bayarwa sai naji yaushe zai iya zuwa."""

Godiya Yaya Kubra tayi mata har ta rasa kalmar faWa. Mubina ta shige gaba zuwa Wakin da Kamal yake. A

hanya tayi ta nanata mata don Allah ta daure zuciyarta idan ta ganshi. Wannan yasa zuciyar Yaya Kubra ga tsinke tun kafin su shiga.

Mubina ce ta fara shiga da sallama. Yana kwance gaSoSi da fuskarsa sun kumburo sosai. Shi kaWai ya san

irin azabar ciwon da yake ji. Amsa sallamar ya fara da muryarsa can ™asa kawai sai ya yi tozali da Yaya Kubra. Ya yun™ura ya tashi zaune kafin ta ™araso.

Hannu ta Wora akan bakinta don kada tayi kuka mai haWe da ihu da taga yadda ya koma.

"""Kamal?"" Ta kira shi da rawar murya."

"Ya mi™a mata hannu, kwarmin idanunsa yana ziraro hawaye ta ri™e. A gefen gadon ta zauna su ka"

rungume juna. For the first time tun bayan ciwon nan ya same shi ya fashe da kuka mai ban tausayi. Duk

"wani ciwo, ™unci da damuwa da yake Soyewa ya bari ya nuna kansa a wannan lokacin. Shi Wan dangi yana ta fama da damuwa shi kaWai. Abin da gidansu basu saba ba."

Yaya Kubra tana kuka tana shafa bayansa da lallashi. Mubina kuwa ficewa tayi don bata son karyar masa

da zuciya fiye da halin da yake ciki. Mara lafiya baya son ganin rauni a tattare da likitansa.

Tsahon minti goma zuwa shabiyar kafin yaji sanyi a ransa ya daina kukan.

"""Kiranki tayi ko?"" Ya tambayeta yana nufin Mubina."

"FaWa ta soma yi masa ""Me yasa ka zaSi wannan rayuwar Kamal? Bamu da mahimmanci a wurinka? Ko"

"kana ganin ba za mu damu da lalurarka ba?"""

"""Irin wannan kallon kamar kina yi min sallama shi ne bana son gani. Wannan kukan zamu dinga yi kullum"

"har lokaci..."""

"""In sha Allahu za a dace. Ina nan ina bincike."""

"""Bata faWa miki cewa ko dialysis ba zai iya ri™eni na tsayin lokaci ba?"""

"""Na sani Kamal. You need a new kidney. And we'll find one in sha Allah"" ta share masa hawaye da"

hannunta.

Al™awarin ri™e masa sirri ya ro™eta har zuwa lokacin da za ayi bikin Taj. Sannan ™anwarsu mai shirin

haihuwa ko yau ko gobe ita ma ta sauke.

"""Me yasa? Wallahi ka san ba za ka burge Taj ba. Infact ni ba zan so ganin ranar da zai sani ba. Za ku yi"

"faWa Kamal. Za ku yi faWa sosai. Ko jiya da naje duba shi sai da yayi ta zancen wai ina duba maka magungunan allergy kuwa."""

Jingina ya yi da pillow don ya gaji da zaman. Ya yi ajiyar zuciya.

"""Na sani. Amma Happy zai tsayar da duka uzurin rayuwarsa ne. Zuwa yanzu kin san mutum ne mai sanya"

abu a rai. Amma kina gani saboda mu ya mayar da komai ba komai ba tsakaninsa da Alhaji. Kuma hakan

"fa ba ™aramin ciwo yake yi masa ba."""

"""Tsakanin uba da Wa ne wannan. Ina maganar Happy da Happiness. Sai ka shiryawa duk abin da zai biyo"

"baya."""

"""In ya ganni a haka kina tunanin zai iya yi min mita? Kuka kawai za mu zauna mu sha abinmu."""

Yadda yake maganar kai ka san akwai tsantsar tawakkali. Yaya Kubra a nan ta wuni har tara na dare

sannan ta tafi. Ta amince za ta yi shiru amma ba don Kamal ba. So take ta samu cikin dangin wanda idan ta bijiro da bu™atar ba zai ™i ba. Maganar neman donor ta hanyar gwamnati ba zai yiwu ba. WaWanda su ke kan list sun yi yawa sosai.

Tsakanin Kamal da Taj a waya sai ta whtsapp. Kamal ya cire simcard da sunan baya ™asar. Wai ya tafi

China odar takalma. Taj harda mitar me yasa bai faWa masa shirin tafiyar ba. Ya ce wanda ya bawa sautu ne ya sami matsala. Gashi kuma komai ya kammala. Ana bu™atar mai kaya. Abinka da rashin sabo da yi. Taj bai kawo komai ba ya yarda. Iyaka dai in suna waya ya dinga kiran wash wash kenan don kawai yaji

Kamal yana sannu kamar ya ari baki. Bai san ciwon Kamal Win ya ninka nashi ba.

***

"Kamar yadda Anti Zahra tayi hasashe, Salwa gidan ™anwar babanta ta tafi. Gidan da tun farkon karatunta"

baban ya so taje amma saboda Mami ta raina arzi™insu ta rufe ido ta ce bata san zance ba. Wannan

tafiya da tayi sai ta sami lasisin fita yadda take so tana haWuwa da Ummi. Gwaggonta kuma bata iya yi

mata magana saboda tsoron jarabar Mami.

Bayan bugun cikin da Ummi tayi mata sai ta nuna mata cewa tana jajanta mata rashin samun soyayyar

Taj. Ta kuma yi mata al™awarin za ta taimaka mata ta sami biyan bu™ata indai tana so.

"""Mamina ma ta gama komai har an fara maganar aurenmu"" ta faWawa Ummi da farinciki."

"TaSe baki Ummin tayi ""in an Waura muku auren kina tunanin kin yi nasara ko me? Mutumin da baya"

"sonki kuma igiyar auren tana hannunsa."""

"A tsorace Salwa ta ce ""kuma fa haka ne. Amma ba sona bane baya yi. HaWuwarsa da matar da aka aura"

"masa ´ar Wan daudu duk shi ya lalata komai. Da muna waya normal."""

A zuci Ummi tayi tsaki. Wannan Salwan irin matan nan ne da sakarci ya rinjayi tunaninsu. Gashi dai ta

san cewa ta girmeta amma irin shirmen da take yi da sunan soyayya ita ko da wasa ba za ta yi ba.

"""Ni naga sharrin ´ar Wan daudu. Akanta aka koreni daga makaranta sannan aka fasa bikina. Gidanmu"

"kowa ya tsaneni akansu. Wallahi da zan haWu da Hamdiyya Habib sai na rama abin da tayi min ko yaya ne."""

"Idanu Salwa ta zaro tana kallonta ""Hamdiyya? Ai kuwa ita ma sunanta kenan. Babanta yana aiki a Happy"

"Taj."""

"""Ni ban san a ina yake ba. Amma dai shi ma sana'ar girki yake yi. Kin ganta. A yadda suke matsiyata bana"

"jin ko iskar da mai Happy Taj yake sha™a ita ma za ta sha™a wataran."""

Hoton Hamdi ta nuna mata wanda ta samu ta Wauka daga wayar Siyama na ranar aurensu. Salwa ta

dinga sallallami gami da rantsuwar ita ce. Ita ma Ummi ta nuna nata mamakin ™warai.

"""Indai Hamdi ce nayi miki al™awarin zan bada nawa taimakon na raba su da masoyinki."""

"""Nagode. Ni kam alkhairi ne ashe ya kai ni Glory mall rannan."""

Ummi sai dariyar ya™e kawai take yi. Ita kanta duk fitinarta abin da Alh. Usaini ya tanadarwa Taj ya yi

mata hatsabibanci da yawa. Ta riga ta nuna masa tana tare dashi bata da hanyar guduwa. Haka kawai take tsoron mutane irinsa waWanda za su iya yin komai domin biyan bu™atarsu. Rashin kunyarta bata kai nan ba. Domin kuwa duk iya shegenta akwai abubuwan da take tsoron yi don kada su koma kunnen

iyayenta. Tunda Allah Ya kawo Salwa sai ta bashi shawarar amfani da ita don ya cimma burinsa.

***

Jinyar sati guda Taj ya yi kafin ya farfaWo sosai. Har ya faWa kuwa. Abba yaje duba shi har gidan Ahmad.

Kuma ya sami tarba ta mutumci daga gare shi. Wannan ya sake daWaWa ransa akan halin ´a´an Yaya

Hayatu. Da zai tafi ne Taj ya yi masa maganar Hamdi.

"""Abba don Allah ina neman alfarma a gareka."""

"""Indai zan iya in sha Allahu zan maka."""

"""Maganar rabani da Hamdi. Don Allah ka cire komai a ranka ka bimu da addu'a."""

"""Innalillahi..."" Abba ya ri™e kai ""faWa maka tayi? Ban san Hamdi da surutu ba wallahi."""

"Taj ya yi murmushi ""ba ita ta faWa min ba."" Ya tuna maganar da Salwa tayi ya ce ""Yaya Ahmad ne ya faWa."

"Amma ya ce kada na damu in sha Allah su Inna ba za su bari ba."""

"""Lamari na iyaye..."""

"""Allah bai bawa iyayenmu damar kashe mana aure ba. Musamman idan raba auren cutarwa ne ba"

"hanyar samun maslaha ba."""

"""Ina jiye maka yawan saSanin da kuke samu dashi. Hakan ba zai haifar da alkairi ba."""

"""Abba ina ™o™arin tsayuwa akan iyakar addini kan abin da ya shafi Alhaji. Duka abubuwan da yake fushu"

"dani a kai shi yake nuna amincewarsa sannan ya zargeni da rashin kyautawa."""

Shi dai Abba gani ya yi zai shiga tsaka mai wuya. Ya yi ta nunawa Taj illar dake tattare da zama cikin

fushin iyaye.

"""Don Allah ka nemi sulhu dashi kafin lokaci ya ™ure."""

"Muryar Taj a raunane ya ce ""na jima ina wannan amma ya™i bani dama. Zan cigaba da ™o™ari amma"

"Abba kada ka kuma sako aurena a ciki don Allah."""

"Tausayi ya bawa Abban ""na daina. Allah Ya kiyaye mana Sacin rana."""

"""A sunnar Annabi SAW? Inaaa, Abba ai sai dai lada."""

"Nauyi Abba ya fara ji tun kafin Taj Win ya je inda bai dace ba ya ce ""naga ka fara jin sau™i. Bari na tashi."""

Taj ya dinga dariya kamar ba shi ne yake kwance kafin zuwan Abban ba.

***

Inna tana falonta ana yi mata kitso aka yi mata waya. Ba™uwar lamba ta gani. Ta Wauka da sallama su ka

gaisa da matar da ta kira.

"""Na san ba ki gane ni ba tunda bamu zauna tare ba. Mahaifiyar Ahmad ce. Ahmad babban Wa namiji"

"wajen Alh. Hayatu nake nufi."""

Murmushi Inna tayi. Wannan ™alau take kuwa? A take ta cire wayar daga kunnenta ta karanto Ayatul

Kursiyyu. Šabi'arta ce haka. Duk abin da bata gamsu dashi ba koda bata aka yi sai ta tofe shi da Ayatul

Kursiyyu kafin tayi amfani dashi. Yadda Mami ta gabatar da kanta sam bai yi mata ba.

Sai da ta gama sannan su ka gaisa da ita.

"""Dama naji shiru ne ina ta sa rai da wayarki amma baki kira ba. Nace bari ni na neme ki naji me ake ciki."""

"""Wace magana kenan?"" Tashi tayi daga wurin kitson ta koma Waki."

"""Auren Taj da Salwa. Alhaji ya ce baya son a wuce wata guda. Naga har an cinye sati."""

Azkar Win tunkarar shugaban da kake tsoron cutarwa daga gare shi Inna ta karanto wannan karon kafin

tayi magana.

(Allahummak finihin bima shi'ta)

"""Wane Taj Win wai? Nawa dai sati biyu kenan da aurensa. Bani kuma da labarin zai ™ara wani."""

Mami tayi kwafa a hankali tana raya duk za su zo hannu ne. Da ta san haka za ta yi mata tun farko ma da

ta karSo laya.

"""To ki tambayi maigidan naki. Sai mu yi magana daga nan."""

Inna ce ta fara kashe wayar. Ta dinga karanto addu'o'i. Me yasa duk wata rigimar gidan akan Taj take

kunno kai? Istigfari tayi da sauri sannan ta fita ta tafi Sangaren Alhajin. Dama yana gida. Girkin Umma ne. Inna tayi sallama ta shiga falon bayan Umma ta amsa ta iske shi yana cin abinci.

"""Alhaji me nake ji daga bakin tsohuwar matarka?"""

Karo na biyu kenan da Inna tayi masa magana babu kyautata kafazi. Yana namiji sai da yaji wanibabu a

ransa. Maganar Hajiya na neman tabbata da ta ce masa kada ya ™ure ha™urin Abu don mai ha™uri bai iya

fushi ba.

"""Wani abin ne ya faru?"" Ya tambayeta kamar bai sani ba."

"""Ka fini sani Alhaji. To amma ina so ka sani ka gama yi min hawan karkatacciyar kuka. Wannan juya min"

"yaro da kake yi ya isa haka."""

"""Haba Inna. In ranki ya Saci kada ki bari hankalinki ya gushe mana. Da mijinki fa kike magana."" Umma ta"

ankarar da ita don muryarta tashi take sosai.

"""Me ya rage min? Yau ko agola ne Tajuddin ai iyakar abin da mijin uwa da baya sonsa zai yi masa kenan."

"Wai ni matar nan za ta kira ta ce ya maganar auren Taj da Salwa?"""

"""Me?"" Umma ma ta Waga murya ba tare da tunani ba."

"""Ah to, kema kya faWa. Wai da Alhaji su ka yi magana."""

Ya fa manta da maganar nan. Duk a zatonsa idan Ahmad ya faWa mata yadda su ka yi za taji haushi ta ce

basa so. Daga ranar da su ka yi maganar ko tunawa bai sake yi ba saboda rashin mahimmancin zancen a wajensa.

"Umma ta dube shi ""Alhaji wai haka?"""

"""Eh. Mun yi magana da mijinta ya bawa Taj Salwa. SharaWina kenan idan ba zai saki ´ar gidan Habibu ba."

"In ba haka ba kuwa..."""

"""Kana son ya saketa kafin auren ya wuce wata uku ko? Ahmad, Wan halak ya faWa mana"" Inna ta ™arashe"

masa.

"""Tunda kun sani sai ku sa ya zaSi Waya. Na gama magana."""

"""Ahaf. Ai babban kuskurenka da ka bari aka yi auren nan Alhaji. Shi ne mai wuyar. Ko yanzu ba abin"

"mamaki bane ace Hamdi tana da juna biyu."""

"Ba Alhaji da ya kusa ™warewa da ruwan da yake sha ba, Inna ma zaro idanu tayi."

"""Kai Umma?"""

"""Auren yanzu da

31 / 42