Chapter 11 Reading Rayuwa da Giɓi Complete Hausa Novel READ HAUSA Novels

Rayuwa da Giɓi Complete Hausa Novel

Author :  BATUL MAMMAN Category :  African Stories & Novels

Chapter   11 / 42

30K to 33K   out of 124.8K words

neman da su ke yi masa.

"""Kamar yadda Wan uwana ya faWa maka gidan abinci nake ginawa. To sai na sami labarinka a wajen"

"mutane. Duk da ba haka ake so ba ance ka rasa wurin sana'arka."""

"""Eh. Amma yanzu ma haka wani waje zan je dubawa. Idan mun daidaita sai na kama haya."""

"Babu wani dogon tunani ko shawara Taj ya ce ""hayar kafi so ko za ka iya aiki tare dani?"""

"""Kai da baka gama gini ba Happy? Zai yi ta jira ne har lokacin?"" Kamal ya yi saurin katse shi."

"""Me ya kawo ku wurina tsakani da Allah?"" Abba ya tambaya da sakin fuska."

"""Aiki nake so mu yi tare amma wurin nawa da saura kamar yadda ya faWa maka. Ina so nayi recruiting"

"ma'aikata da wuri kafin na gama ginin."""

Kamal da ya yi zaton ganinsa kawai su ka zo yi sai yaji hankalinsa bai kwanta ba. Me yasa Taj yake neman

abin da zai ™ara nesanta shi da Alhaji? Ina shi ina aiki da wannan mutumin daga jin ance baya aiki?

Abba ya ™are musu kallo sai ya yi murmushi. Da alama shawararsu bata zo Waya ba don yaga irin kallon

da Kamal yake yiwa Taj.

"""Samari nagode amma ina mai baku ha™uri. Ina da mata da ´a´a huWu. Zama haka a yanzu ma yana"

"damuna balle kuma na wasu watanni. Sannan ina da ma'aikata biyar da har yanzu dani su ka dogara."""

KuWi Taj ya ciro daga aljihunsa da sauri.

"""Zan fara baka albashi tun yanzu kafin mu fara aikin."""

"""Happy!"""

Taj ya yi biris da Kamal. Shi kuwa bai barshi ba ya dubi Abba da kyau.

"""Kayi ha™uri don Allah. Bari mu tafi."""

"Taj ya Sata fuska ""Da gaske nake ina son aiki da shi Happiness."""

Abba sai ya nuna kamar bai ji haushi ba. Yana ´ar dariya ya yi musu godiya kawai ya tashi. Kamal kuma

ha™uri ya yi ta bashi sannan ya janye Taj su ka tafi. A mota kuwa kafin su isa gidan Ahmad anyi faWa kaca- kaca.

"""So kake Alhaji ya mutu da ba™incikin ka ko me? Kai yanzu rayuwarka tana yi maka daWi?"""

"""Kai baka ji komai ba da aka ce bashi da aiki yanzu?"""

"""Sai ka taimaka masa da kuWi."" Kamal ya ce har zuciyarsa."

"""Are you serious? Yanzu da aiki da kuWi wanne ya fi?"""

Da wannan cacar bakin su ka koma gidan. Don takaici Kamal ko shiga bai yi ba. A waje ya sauke shi ya tafi.

"""Masifaffe."" Taj ya furta yana harar motar."

*

Ikon Allah Zahra ta gani yau tun dawowar Salwa gida. Kwananta shida a Bauchi da aka yi musu gajeren

"hutum mid-semester. Abin da aka bayar da kwana goma har weekend ya kama shabiyu, a daddafe tayi shida ta dawo. ˜arya ma ta yiwa mamansu wai field work za su je. Da yake Agricultural Extention take karantawa. Nan kuwa kewar Taj ce ta isheta har tana neman zautar da tunaninta. Abin ba™inciki kuma"

shi ne tunda ta tafi ko sau Waya bai kirata ba. Ita ce ma da ta gaji tayi masa waya harda Wan ™orafi.

"""Idan mutum yaje gida baya son damu Salwa. Tunda ba daWewa za ki yi ba gara duka time Win ki ya zama"

"na family."""

"Ji tayi kamar ya faWa mata magana. Ta daure ta ce ""Ba ka cikin family Wina kenan?"""

"""In ji wa? Idan kin dawo zan baki wayata ki gani a yanzu zan chanja yadda nayi saving sunanki."""

"Zuciyarta ta harba da wani irin farinciki ta ce ""me za ka saka?"""

"""˜anwata Salwa. Yadda nake saving sunan ´an gidanmu. Manyan kuma ina saka musu Yayata"" Kuma bai"

"barta ta gama jin haushin hakan ba kamar shi ys kira ya ce ""bari na barki ki huta haka. Sai da safe."""

Azahar a Kano tayi mata. Tana zuwa gidan ko hutawa bata yi ba ta karSi girkin dare. Zahra tana ta faWa

"mata ta jira ayi la'asar amma ta ce gara tayi da wuri tunda tuwo ne. Daga nan ta haWa juice Win abarba, mangwaro da Wanyar citta saboda ta kula Taj yafi son fresh fruit juice. Da su ta taho tun daga Bauchi."

Bayan tayi sallar la'asar ta shiga Wakin Taj. Yana ™ullewa idan zai fita amma baya taSa zare key Win. A

cewarsa tunda masu gidan suna da kaya a ciki me yiwuwa za su bu™aci shiga idan baya nan.

"""Salwa me ki ke nema a nan?"" Zahra ta taho da sauri da taji alamun buWe ™ofar."

Tsintsiya ta sameta tana gyarawa Wauri. Tana ganinta tayi murmushi.

"""Anti Zahra gyara Wakin zan yi."""

Curiosity yasa Zahra ta Wan le™a. Baya bu™atar wani gyara na a zo a gani.

"""Yana gyarawa. Ki fito don yayanki sai da ya yi min warning akan bari ke ko mai aiki ku shiga Wakinsa."""

"""Yau Waya dai Anti. Ai gara ayi masa gyara sosai. Tunda baya gida zan yi sauri."""

Tafiyarta tayi ta soma da wankin toilet. A sink inda ya tara boxers da singlets da socks ta haWa komai ta

wanke. Sai ta bar masa a bucket yadda zai shanya idan ya dawo. Wankin ma ana yi ana rurrufe ido saboda kunyar da ta dinga ji. Šaki ya fito fes dashi don har bedsheet sai da ta canja masa. Bayan ta gama komai ta rura gawayi akan gas cooker ta wuce da robar turaren wutan da ta siya online. Tun Zahra na bin ta da ido har tsananin mamaki yasa ta koma cewa 'uhmmm'. Yau ko Wakin miji ne aka yiwa haka ai dole

ya yabawa matar balle wanda a iya saninta babu soyayya a tsakaninsu.

Ahmad ne ya fara dawowa gidan. Lokacin tuni Salwa ta gama har tayi wanka. Doguwar rigar atampa ta

saka da ™aramin mayafi ta zauna a falo tana ta ™amshi. Wannan karambani duk aminiyarta ce ta kitsa

mata. A cewarta da kyautatawa ake sayen soyayyar namiji. JindaWin yadda take kula da shi zai kwaWaita masa mallakarta a matsayin matar aure.

Wuraren ™arfe biyar da rabi Taj Win ya shigo da sauran fushin faWansu da Kamal. Sama sama ya gaisa da

Ahmad. Ya Wauki baby Aisha bayan gaisawa da Zahra. Salwa kuwa sai da tayi masa magana ya kula da ita.

"Ya dakata da tafiya ""Har hutun ya ™are? Ko dai kin dawo birnin da yafi ™auyenku?"" Ya ce da ita da zolaya."

Murmushi kawai tayi. Ahmad ya girgiza kai. Dama tunda ta dawo da wurwuri ya san ba zai wuce saboda

taji cewa Taj ya kusa komawa bane.

Da Aisha ya shige Waki a kafaWarsa ya kwantar da ita a kan gado. Ya yi mamakin yadda ya sami Wakin.

Waye ya gyara? Komai an killace shi gwanin sha'awa. Ya shiga toilet nan ma ™amshi kawai yake tashi. Da sauri ya duba sink da ya tuna ya bar kaya da zai wanke sai yaga babu. Nan fa yaji wani abu ya taSa masa rai. Yana duba bokiti kuwa sai gasu a wanke an matse. Ya fiddo gajeren wandonsa Waya ya tabbatar dai a

wanke yake. Bai san lokacin da ya sake shi a bokitin ba. Ya Wauki Aisha ya koma falo fuska babu annuri.

"""Anti Zahra waye ya gyara min Waki ne?"""

Ahmad ya yi saurin kallon Zahra ita kuma ta nuna Salwa dake faman doka murmushi tana sunkuyar da

kai. Sau™in hali irin na Taj bai hana shi nuna Sacin rai ba kuwa.

"""Ke ki ka wanke min underwear?"""

"Idanun Zahra waje su ka yo. Ahmad kuwa bai san lokacin da ya ce ""underwear kuma?"""

Da me tambayar da kuma yanayin maganar Ahmad sai Salwa taji tsoro.

Taj ya murtuke fuska.

"""You shouldn't have. Next time please kada ki taSa min."" Ya du™a ya mi™awa Zahra Wiyarta sannan ya"

"dubi Ahmad ""Yaya zan Wan kwanta kafin magrib. Da headache na dawo."""

Shigewa ya yi ya barsu. Da Zahra taga irin kallon da Ahmad yake yiwa Salwa sai ta tashi tsam ta shige

Waki.

Ai kuwa kamar jira yake ya soma faWa.

"""Wannan wane irin rashin daraja kai ne haka Salwa? Are you crazy or what?"""

Kai ta sunkuyar tana kuka. Ba kuma na faWan yayanta ba. Fushin Taj da tsoron kada gwanintar ta tayi

sanadin nesanta ta dashi kawai take gudu.

"""Ba tun yau na kula kina son Taj ba..."" sai a lokacin ta kalle shi hankalinta na tashi. Ya taSe baki ""wanda"

"bai damu da lamarinki bane kawai ba zai gane ba."""

"""Yaya..."""

Tausayi ta bashi don ta soma kukan gaske. Amma hakan ba zai hana shi faWa mata gaskiya ba.

"""Kin san komai dake faruwa a gidanmu da dalilin zamansa a gidan nan. He is trying his best ya daidaita"

"da Alhaji. Kina tunanin soyayyar Taj dake, ´ar matar da ya saka zai faranta masa rai?"""

"A tsorace ta kalle shi ""Yaya ni meye laifina?"""

"""Salwa kin fini sanin rigimar Mama tunda a gabanta ki ka tashi. Ke shaida ce irin yadda ta fitini Abbanku."

"Abubuwan da take yi bana jin akwai wanda Alhaji bai sani ba. Tun da in naso zuwa wajenta hutu baya son bari saboda yana gudun kada na koyo abin da zai haWa rigima a gidanmu."""

"Hawaye ta goge da mayafinta. Da muryar da kuka ya gama dusashewa ta ce ""To ni yaya zan yi? Ba ni na"

"Worawa kaina ba"""

"""Kada ki yi komai sama da neman zaSin Allah. Sai kuma tsare mutumci da darajarki ta mace. Ke kin sani"

"da ina nan ko Wakinsa ba za ki shiga ba. Ba kuma don ban yarda dashi ba. Amma wankin underwear...haba Salwa? It was totally wrong."""

Daga ™arshe rarrashinta ya yi da jaddada mata lallai kada ta ™wallafa rai akan Taj domin indai Alhaji bai

amince ba da wuya ya aureta.

***

Hutu yana ta daWi. Hamdi ta zaga gari sosai da Anti Labiba da yaranta. Basu da ´an uwa sosai a garin sai

abokan arzi™i. Shi yasa yawon nasu yafi ™arfi a wuraren sha™atawa da ciye ciye.

Wata rana sun dawo da yamma li™is Anti Labiba ta ce da Hamdi ta Wora abinci. Tayi tu™i ta gaji ga

bebinta na ta tsala ihu. Šaki ta shiga domin yiwa yarinyar tsarki amma har ta fito Hamdi bata Wora komai ba. Gyaran kitchen Win take yi saboda ana gama cin abincin rana su ka fita.

"""Hamdi baki ji na ce ki Wora jallof Win macaroni ba?"""

"Murmushin ys™e tayi ""Anti Labiba don Allah ki Wora. Duk wani yanke yanke zan miki."""

˜an™ance ido Anti Labiba tayi. Sai kuma ta tuna wata hirarsu da Sajida lokacin da ta zo mata zaman bi™i.

Tabbas ta faWa mata a duniya babu abin da Hamdi ta™i jini bayan namijin da ya iya girki kamar girkin kanshi. Ita duk abin da za ta Wora akan wuta mai suna abinci zuciyarta bata son yi. Ba kuma komai ya janyo ba illa tsohuwar ™iyayyar da take yiwa sana'ar Abbansu. Kuma fa da yake a wurinsa ta koya da

wuya ka ci abincinta baka yi santi ba.

"""Baki iya girkin bane ko me?"""

"""Idan na dafa ba lallai na iya ci. Don Allah ki Wora kinji Anti..."""

Sosai abin ya bawa Anti Labiba mamaki. Hamdi bata taSa yi mata ™iwar aiki ba. Ga iya sammako ta gyara

gida tun zuwanta. Amma fa duk cikin aikin nata bata taSa yin girki. Ita kuma Anti Labiba bata damu ba saboda mijinta baya son cin girkin mutane musamman a gida.

Abincinta tayi ta gama. Hamdi sai taji babu daWi don sai da aka matsa mata taci abincin. Bayan sun gama

ta bita Waki ta bata ha™uri.

"""Ni ban yi fushi ba. Kawai ina mamakin yadda aka yi ki ka zafafa akan harkar girkin nan."""

"""Idan ina yi sai Abba ya dinga faWo min a rai. Wallahi Anti Labiba bana son ganin shi a kitchen kwata-"

"kwata. Yanzu ma ina ta fatan Allah Yasa ya sami wata sana'ar tunda an karSe gidan abincin."" Magana take yi muryarta tana rawa."

Anti Labiba ta sa™ala hannunta a kafaWarta.

"""Nayi zaton kin daina abubuwan da ki ke yi da naga yanzu kullum sai kun yi waya dashi."""

"""Ni me nake yi?"" Ta tambaya da zumSura bakin."

"""Babu komai."" Ta shashantar da zancen ""snacks da pastries fa? Su ma kamar girki ki ka Wauke su?"""

"""Don ban iya bane amma ina so."""

"""Saboda basa cikin girkin da Abba ya koya mu ku ko?"""

Sunkuyar da kai Hamdi tayi a kunyace. Ita kuwa Anti Labiba sai wani tunani ya Warsu a zuciyarta. Ba dai

za ta ce komai ba sai ta tuntuSi ™awarta Hauwa gobe. Idan Hamdi tayi sa'a za ta koyi small chops da

youghurt from one of the best a garin Abuja.

***

Kwana biyu Taj ya yi baya zuwa site Win aiki. Idan Kamal ya zo sai ya ce kansa na ciwo. Abu ya taru ya

dami Kamal sosai. Lokacin tafiyar Taj na gabatowa amma ya sanyawa ransa wani abu daban. Shi kuma

yafi son ko zai tafi ya zamana aikin da ya rage ba mai yawa ba. Gara aci ™arfin komai a gaban mai wurin.

Yau da ya bar gidan Ahmad wucewa ya yi gidan Abba Habibu. Bai wahala wurin gane gidan ba. ShaWaya

na safe ta Wan wuce. Ya tura wani yaro ayi masa sallama da shi. Wata budurwa ba wadda ya gani a zuwansu na farko ba ce ta fito ta gaishe shi.

"""Abba ya fita amma yanzun nan zai dawo. Ba nisa ya yi ba."""

"""Ke ma ´arsa ce?"" Kamal ya kasa daurewa sai da ya tambaya. Ita da ta rannan da ya ri™e Zee aka kirata"

su na kama sosai. Kyawawan ´an mata ne masu nutsuwa.

"""Eh."""

"""Yaya sunanki?"""

"""Sajida."" Ta amsa masa."

Kujerar roba ta kawo ta ajiye masa a soron ta koma ciki. Kimanin minti goma a tsakani sai ga Abba ya

dawo.

Mamakin ganin Kamal ya yi sosai. Su ka gaisa sannan Kamal ya Wan rissina kai.

"""Na san za ka yi mamakin dawowata bayan yadda nayi a wancan zuwan namu."""

"""Babu komai. Allah dai Yasa lafiya."""

"""Alhamdulillah"""

Shiru ya kuma biyo baya har sai da Abba ya sake tambayarsa sannan ya yi magana. Da farko ya fara da

bashi labarin burin Taj tun ™uruciya da duk wani abu da ya biyo baya.

"""Wallahi ban hana shi don ™yama a gareka ba. Amma indai Alhaji ya sami labarin kuna tare bana jin zai"

"zai yafewa Taj."""

"Kallonsa Abba ya yi sosai yana jinjina kai ""to amma a ina mahaifin naku ya sanni."""

"""Soron Winki. Shi ma mutumin cikin gari ne."""

A karo na uku Abba ya sake ™urawa Kamal idanu na wasu ´an da™i™u sannan ya yi murmushi.

"""Yaya Hayatu ne mahaifinku?"""

"Da sauri Kamal ya kalle shi ""ya akayi ka gane?"""

"""Da gaske ku ´a´ansa ne?"" Abba ya kuma tambaya yana mi™ewa tsaye."

"""³a´ansa ne."" Ya faWi yana gyaWa kai."

"Jiki a matu™ar sanyaye Abba ya ce. ""Ka faWawa Wan uwanka kada ya sake zuwa gidan nan. Kai ma ka tashi"

"ka tafi."""

Kamal bai jidaWin yadda Abba ya koma ba. Da alama ba mutum bane mai son hayaniya. Amma jin waye

mahaifinsu ya canja yanayinsa. Hannu ya sanya ys fiddo dubu Warin da ya tanada tun a gida.

"""Ga wannan ka ™ara jari don..."""

"""Šauke kuWinka yaro. Bana so ko da wasa Yaya Hayatu ya yi tunanin da gangan na kusanci rayuwarku."""

Ciki ya shige ya bar Kamal ri™e da kuWin yana fargabar yadda za su kwashe da Taj idan ya sami labarin

zuwan nan nasa.

RAYUWA DA GI�I 12

Batul Mamman

Wannan shafin yana Wauke da tallan _LUCIOUSBITES_ gidan kashe ™walama. Mazauna garin Abuja ga

taku ta fito da kanta ba sa™o.

"Taron biki, suna, conference, seminar ko reunion ne? Ko kuwa sha'awar kashe kwaWayi ce ta tashi? To ku"

sha kuruminku. Hauwa aka luciousbites.ng ta fito domin fitar daku kunya a ko ina.

Domin ™arin bayani kuna iya tuntuSarta a kan wannan layi 08174821831.

***

Da gaske ciwon kai ke damun Taj saboda bai iya sanya abu a rai ba. Ya so ™warai ya ja Abban Hamdi a jiki.

"Ba don neman soyayyarta ba, wannan da kansa zai yi ba ya bu™atar taimakon kowa sai Allah. Mahaifinsa yake son nunawa a rayuwa kowa da ™addararsa. Kuma a kowacce sana'a indai ba addini ne ya haramta ta ba, akwai mutumin banza da nagari. Don al'ada ta ™yamaci wani abu ba shi yake nufin yinsa laifi bane."

Sannan uwa uba akwai uzuri ga ´an Adam domin ba kowa ke dawwama cikin saSo ba.

A ganinsa rashin aikin Abban Hamdi wata hanya ce ya samu da zai iya sako shi cikin tasa sana'ar. Idan

Allah Ya sanya musu albarka kasuwa ta buWe Alhaji zai iya fahimtar kowanne bawa akwai hanyar

"arzi™insa. Sannan ko iyaye ba sa so indai Allah bai haramta ba sannan Wan bai kasance mai saSawa kowa ba, albarka za ta iya binsa duk inda yake."

˜arar wayarsa ce ta tashe shi daga kwanciyar da ya jima yana yi. Sunan Salwa da ya gani ya sanya shi yin

tsaki. Ita bata san gudunta yake yi ba? Har yau yana mamaki da bata yi tunanin kamar yadda mata ke killace kayansu na ciki haka kowanne namiji da ya san mutumcin kansa yake yiwa nasa ba. A iya saninsa ™iwa da rashin son aikin namiji ba zai sa ya bawa ™anwarsa sha™i™iya wankin ™ananan kaya ba.

Ballantana kuma wadda babu wani abu da ya haWasu.

Bari ya yi kiran ya katse sannan ya kirata.

"""Don Allah ka buWe min ™ofa na manta mu™ullina a ciki."""

Falo ya fito sanye da dogon wando na sanyi ruwan toka da farar shirt. Ya buWe mata jamlock Win ya juya

zai koma Waki sai ta kira sunansa.

Tun ranar da ta gyara masa Waki da faWan da Ahmad ya yi mata ta rage kuzari da karsashi a komai.

Fargabarta ita ce Sacin ran da ta gani tare da Taj da kuma shawarar da Ahmad Win ya bata akan ta cire

shi daga ranta. Da za ta iya da tun kafin ta zubar da ajinta ta cire shi ta ™arfin tsiya tunda ta fahimci bata

gabansa ta fuskar da take so.

Sake kiransa tayi da bai juyo sosai ba.

"""Ya Taj don Allah ka yi ha™uri akan abin da ya faru rannan. Na fahimci kuskurena."""

"""Ya wuce, kada ki damu."""

Fasa tafiya ya yi da ya tuna ™anwar Ahmad ai ™anwarsa ce shi ma. A matsayi guda duk su biyun su ke

zaune a gidan. Shi yasa yaga dacewar ya bata shawara.

"""Ko don gaba ki kiyaye irin wannan. Ba ni ba, ko Yaya ki ka wankewa undies bana jin za ki burge shi."" Kai"

"ta sunkuyar sai ya yi murmushi ""ku mata ba kwa son a taSa koda jakarku. So just imagine ace ni nayi miki wannan karambanin. Will you realy be happy that I helped?"""

Kunya maganar tashi ta bata. Ta rufe ido ta shige ciki da sauri tana mayar da numfashi. Da tunanin yadda

ya yi maganar a tausashe ta ™arasa Waki. Sai da cire kaya za ta shiga wanka ta kuma tariyo zancen sai taji faWuwar gaba. Shin magana ya yaSa mata ko kuwa ya sauko ne?

Domin tabbatar da matsayin maganar da sai ta tura masa SMS da yamma da ya fito falo suna hira

11 / 42