Chapter 18 Reading Rayuwa da Giɓi Complete Hausa Novel READ HAUSA Novels

Rayuwa da Giɓi Complete Hausa Novel

Author :  BATUL MAMMAN Category :  African Stories & Novels

Chapter   18 / 42

51K to 54K   out of 124.8K words

shi don bai yarda da zancensa ba ko kaWan."

"""Duka wannan bai taso ba. Ku je gida. Nagode"""

Abba zai shige gida ³ar Ficika ya kamo shi da sauri. Duk sun manta dashi. Kwarwar da yake da ihu ma ba

sa ji saboda mahimmancin abin da su ke tattaunawa.

"""Simagade. au Habibu ashe baka da hankali? Ya Allah zai kawo maka agaji a lokaci irin wannan ka nemi"

ka watsa mana ™asa a ido. Ina mai tabbatar maka da cewa Sajida kai za ta Worawa alhakin rabata da farincikinta. Daga nan kuma bamu san halin da za ta shiga ba. Ni a tawa shawarar kawai ka bari su aure

"su duka."""

"""A'a Balarabe. Baka san komai akan yaran nan ba. Son zuciya a yanzu ita ce ™iyayya mafi girma da zan"

"nuna a madadin kyautatawar da su ke min."""

˜ofar gidansa ya ™arasa da sauri don ™irjinsa zafi yake. Sai dai ko rabin jikinsa bai samu shigewa ba ya

"faWi a wurin. ³ar Ficika aka sake samun abin yi. Ya Wora hannu a ka zai cigaba da ihu, Kamal ya daka masa tsawa."

"""Kada ka kuskura ka sake tara mana jama'a. Yi sallama ciki ka yi min magana da Yaya."""

"""To, to"" ya amsa kamar ba Wan cikinsa bane ya yi masa tsawar. Yadda mata ke ruWewa a irin wannan"

"yanayin, haka nasa hankalin ya gushe."

"Da Kamal ya juyo bai ga Taj ba. Ya fara tunanin ko cikin gidan ya shige, don yanzu komai aka ce ya yi ba"

"zai yi mamaki ba. Ya lura yana da taurin kai irin na Alhajinsu, sai dai kuma shi Taj ya haWa da Wanyen kai kamar wani Wan ta kife. Idan ya san abu daidai ne to kawai damn the consequences."

Horn Win mota yaji daidai ™ofar gidan. Ya le™a Taj ya fito a lokacin.

"""Mu kai shi asibiti."""

"""Ai ka bari a faWawa Yaya ko?"""

Bai ma yi wannan tunanin ba. Amma da yake ya san mahimmancin yin hakan sai ya gyaWa kai. Salatin

Yaya su ka ji su ka koma cikin soron.

"""Damuwa ce Yaya. Kada ki Waga hankalinki musamman tunda da mutane a ciki. Za mu kai shi asibiti."""

Šaga shi su ka yi Kamal ya ™arasa dashi motar. Taj kuma ya tsaya sakamakon maganar da Yaya ta fara yi.

"""³ar Ficika kuma ya ce..."""

Taj ya gallawa ³ar Ficikan harara shi kuwa bawan Allah ya girgiza kai da sauri.

"""Wallahi ban faWa mata komai ba."""

"""Me ku ke Soye min?"" Ta tambaya hankalinta a tashe. Dama bata ga abin da zai Waga masa hankali ya"

faWi ba. Bayan bikin nan shi ne babban farinciki da cikar burinsu.

Gani su ka zasu Sata lokaci sai kawai Taj ya ce ³ar Ficika ya faWa mata in sun tafi.

"""Amma don Allah ki bar maganar a wajenki kafin ya tashi mu san abin yi. Yanzu hankalin mutane ne"

"kawai zai tashi."""

"""To, nagode. Idan kun je asibiti ka faWa min. Sai na kira ™aninsa ya taho."""

Kana ganin yadda take magana sai ta baka tausayi. Da gani hankalinta ya kai ™ololuwar tashi. Tana

dannewa ne kawai saboda mutanen cikin gidan.

*

Asibitin kuWi Kamal ya kai su amma ba wanda ´an gidansu su kw zuwa ba. Ana bu™atar file Taj ya buWe

musu na family. Aka shiga dashi ciki aka duba shi. Jininsa ya hau sosai shi da bashi da bp. Dole aka bashi gado ana jiran jikin ya daidaita. Drip aka saka masa da allurai sannan ya sami bacci.

Zaman jiran Abdul™adir ™aninsa Taj da Kamal su ka yi a Wakin. Kamal ya dube shi a tsanake.

"""Yanzu Happy duk abubuwanbda su ka faru da kai a gida ba su isheka ba? Kai da bakinka kake cewa za ka"

auri Hamdi. Auren ma gobe goben nan. Less than 24hrs. Har kana yiwa Abba ™aryar sonta kake kawai

"don kafi kowa iya rigima."""

"""Allah da gaske nake ina sonta Happiness."""

"""Kai Win? Ya aka yi ban sani ba?"" Ya tambaya don bai gaskata shi ba."

"Babu wani juya zance ya ce ""Saboda nayi tunanin za ka ™aryata duk wata niyyata ta janyo Abba Happy"

"Taj. Infact bana tunanin da ka sani ko zuwan farko ba za mu yi gidan ba in ka san waye babanta."""

"""Lallai ka iya ganganci. Banda Soye min da kayi da kuma kana can tayi saurayi fa?"""

"Taj ya yi murmushi ""wallahi a next flight za ku ganni."""

"""Da ni na ce ina sonta fa?"" Kamal ya yi tambayar idanunsa cikin na Wan uwansa."

"""In sha Allahu ma Allah ba zai jarabcemu da son abu Waya wanda mutum Waya ya kamata ya so ba."" Ya"

haWe kafaWunsa don tsigar jikinsa tashi tayi.

"""Next time kada ka Soye min abin da ya kamata na sani."""

Gira Taj ya Waga yana ´ar dariya ganin Kamal ya Wauki zafi da gsske.

"""Bros, faWa min gaskiya. Ba ka ciki ko? Kaga matar yara ce irina."""

"Fuska Kamal ya Waure amma da gani ya sauko ""Ji min mutumin nan. To meye marabata da kai?"""

"""Wata biyar mana. Kai fa kana cikin layin tuzurai."""

"""Baka da mutumci Taj. Ni ne tuzurun? Kai kuma teenager ko?"""

Taj ya gyaWa kai yana dariya.

"""Banda ™uruciya, teenager kamar ka ina zai kai budurwa kamar Hamdiyya?"""

"""Inda ake kai matan..."""

"""Ehemm. Ughhh"" Abba ya yi gyaran murya da ™arfi don ya katse hirar tasu haka. Yaga an kusa zuwa"

wurin da bai kamata kunnuwan uba su ji ba.

Kan sa su ka yi suna tambayarsa jiki. Da sau™i kamar yadda idanuwansu su ke iya gani. Ya ™ara yi musu

godiya sannan ya ro™esu da su bar maganar auren nan haka. Allah zai bashi yadda zai yi da iyalinsa.

"""Idan Alhaji ya amince za ka yarda a Waura goben?"" Taj ya tambaye shi kafin su fita. Shi ko a fuska bai"

nuna damuwa ba da Abba yake ta maganar su daina zancen.

Shi dai Abba ya gama gajiya da zancen. Sannan ya matsu su tafi saboda so yake ya fice ya koma gida su

shawarta da Yaya.

"""Me zai hana? Waye zai ™i jinin Yaya Hayatu ko ma in ce zuri'ar Alh. Sule?"""

Jin wannan ya kwantarwa Taj hankali. Ya san Alhaji ba shi kaWai bane shamakinsa. Shi kan shi Abba za a

sha fama da shi.

***

Salati Yaya ta fara yi kafin ta fashe da kuka. Zaune su ke a cikin wani Wan falo ™arami na Wakin Abba. Ita

"da shi da kuma Baba Maje, Inna Luba mahaifiyarta da kuma ™aninsa Abdul™adir."

FaWan kukan Inna Luba ta fara yi mata kafin ta koma tausarta.

"""Indai ku ka nunawa yarinyar nan cewa kun karaya na tabbata ciwon da za ta ji sai yafi na fasa auren."""

"""Yaron nan ya cuce mu"" cewar Abdul™adir."

"""Na dai cuce mu. Rayuwar da na zaSa ce ta zo tana bibiyar ´a´ana"" Abba ya faWi da raunin murya."

"""In ka amince kuma kana jin Sajida ba za ta ™i ba, yanzu zan kira Baballe ya zo gidan nan a rufe magana."

"Gobe ya auri ™anwarsa bakin kowa alekum. Ko kuwa?"""

Abba ya nuna farincikinsa da godiya.

"""Zan so haka. Amma Maje ka tuna lallai akwai ha™™i tsakaninmu da yaran nan. Aure ba a son yi masa"

"shigar sauri. Yanzun nan sai ya jagwalgwala abin da ake son gyarawa."""

"Baba Maje ya dage harda cewa ""indai ba kuma rowar ´ar za ka yi min ba ka amince kawai. Ba don ni na"

"haife shi ba amma Allah yaro ne mai biyayya. Ina sa rai in Allah Ya so ba zai bamu kunya ba."""

Yadda ya matsa Winnan sai Inna Luba ta ce a kira yaron. Ba a mayarda hannun kyauta. Kuma Allah kaWai

Ya san dalilin faruwar wannan al'amari.

Cikin farinciki Baba Maje ya kira Baballe a gabansu. Allah Yasa baya nesa sosai ya ce gashi nan zuwa. Ita

Iyaa da Siyama suna can wajen biki. Uwar ba™in hali kuma an tafi bikin ™awa kamar yadda ta shirgawa Iyaa ™arya.

Kowa ya yi zugum ana jiran isowar Baballe. Baba Maje ya takura masa da waya saboda basa son ´an biki

su fara dawowa. An gargaWe su lallai kada su wuce takwas a waje har amaryar.

Baballe ya iso hankalinsa duk ya tashi. Irin wannan kira da wayar bai saba dasu daga mahaifinsa ba. Shi

yasa ya dinga tunanin ko wani abu ne ya faru. Kafin ya iso sai da ya kira Iyaa yaji lafiyarta da ta Siyama. Ummi kuwa bata Wauki wayar ba don kada a ce ta dawo gida. Sam ba ya raga mata akan halayen da ta

tsiro musu da su a gidan.

Tiryan tiryan haka Baba Maje ya labarta masa halin da ake ciki a gaban kowa. Wanda shi Abba ya so su

"keSe. Don idan Baballe zai ™i, ba zai ji nauyin idanuwansu ba."

"""Baba don Allah ko za mu koma soro mu yi magana"" abin da ya ce kenan da Baban nasa ya matsa masa"

akan ya bada amsa.

Gabansa sai da ya Wan faWi. Yaran yanzu ba a ci musu laya. Ya gama yabonsa shi ne yake son watsa masa

™asa a ido.

"""Nan dukansu amsar da ka bani dole zan dawo musu da ita. Saboda haka gara ma kawai ka faWa a"

"gabansu."""

"""Baba don Allah"" ya faWi yana cije leSensa na ™asa. Shiru ba zai amfane shi ba a wannan lokacin. Shi yasa"

yake son faWa masa dalilin da ya sa ba zai iya auren Sajida ba.

"""Ka je ka saurare shi don Allah. Share ire iren waWannan abubuwan fa don mun isa su ne su ke zama"

"dalilan yaji ko mutuwar aure. Allah Ya kiyaye."" Inna Luba ta faWi tana nuna musu ™ofa."

Ba don ya so ba ya tashi su ka fita. Ransa duk ya Saci don Baballe bai saba yi masa haka ba. Yaro ne shiru

shiru mai sau™in kai. Tsayinsu kusan Waya don ma shi shekaru sun Wan dur™usar da shi. Fuskar Iyaa

ma'abociyar fara'a ya Wauko. Ga shi kyakkyawan matashi mai zuciyar nema. Banda aikin da ya samu ´an

watannin baya akwai shi da buga bugar neman halak. Bai san zama ko kaWan.

"""Ina jin ka. Kada ka ce min budurwa gareka. Tunda ban san da ita ba, ba za ta zama silar da za ka watsa"

"min ™asa a ido ba."" Baba Maje ya ce a kausashe."

"""Ba haka bane Baba"" Baballe ya ce a ladabce ""´ar uwarta nake so. Na Wan jinkirta faWa mata ne saboda"

"wasu dalilai. Gaskiya ba zan iya aurenta ba alhali ina yiwa ™anwarta so na aure."" Ya ™arashe kai a ™asa."

Gumi ne ya tsatstsafowa Baba Maje. Ya dubi ™ofar cikin gidan.

"""Dan™ari! To yanzu ya kake so nayi? Me yasa ku ke da zurfin ciki ne? Da na sani ko baka faWa mata ba ai"

"ba zan yi wannan karambanin ba."""

"""Idan zai bani ™anwar sai ka sanar da su Kawu a ayi auren goben a madadin na Sajidan. Sai a jinkirta"

"komai tunda ban shirya ba."" Baballe ya furta da hope Win baban zai amince."

"""Dama ko wace ai zan faWa musu. Ni damuwata ma ita Hamdiyyan za ta yarda ne? Ko ka manta yadda su"

"ka yi da Ummi a makaranta?"""

"Da sauri Baballe ya ce ""Zeenatu ce ba Hamdi ba."""

"""Wace Zeenatu kuma?"" Baba Maje ya ce don kansa ya ™ulle."

"Baballe ya yi murmushi ""Zee. Naga bata gama makaranta ba. Niyata zuwa ™arshen shekara idan ta gama"

"na san lokacin na Wan yi tari. Sai na gabatar da kaina."""

"Kamar Baba Maje ya make shi don takaici ya ce ""banza, kana can kana shiri wane zai shige tsakani sai dai"

"kaji ana batun an kawo kuWi."""

Shi dai tunda yaga kamar ya sauko sai ya kwantar da hankalinsa. Ciki su ka koma tare. Kowa ya zuba

musu ido. Baba Maje ya Wan rissina kai na jin kunyarsu ya faWa musu yadda su ka yi da Wansa.

"""Alhandulillahi ai duk gida ne."" Cewar Abdul™adir."

"""In kun amince dashi maimakon a fara kiran mutane ana cewa an fasa auren gobe, me zai hana a Waura"

"nasu. In ya so sai ta tare bayan ta ™are karatunta."""

"""Hakan ma ya yi. Bari su dawo daga wajen taron sai a faWa musu."""

In ji Inna Luba.

*

Banda gunjin kukan Zee babu abin da yake tashi a tsakar gidan. Sai da kowa ya watse sannan Inna Luba

ta kira su har Halifa Wakin Abba ta faWa musu. Sajida ko uffan bata ce ba. Tashi tayi da mutuwar jiki ta koma Wakinsu. Yaya za ta bita Abba ya hana.

"""Ki barta ta sami sararin yin kuka har taji sanyi a ranta."""

"""Ita kaWai?"" Ta share nata hawayen."

"""Wata damuwar tana bu™atar kaWaicewa kafin zuciya ta karSe ta. Idan tana bu™atarmu da kanta za ta"

"neme mu."""

Zee ya kalla da ta faWa kan kakarta tana kuka kamar wadda za a zarewa rai.

"""Shikenan sai a fara yi min aure bayan ina da yayye?"""

"Inna Luba tana shafa mata baya ta ce ""Ja'ira. Ashe kukan ba na ™in mijin bane. To ai da sau™i. Yayyenki"

"kuma ki sani kowacce lokacinta yana hannun Mahaliccinta kamar yadda naki yake."""

"""Mijin ma bana so Inna."" Ta ce tana ™ara sautin kukanta."

"""Bana son rashin hankali. Ihun da kike yi ma™ota za ki tara mana ko me?"" Yaya ta faWi cikin fushi."

Tana son Iyaa da Baba Maje a matsayin aminansu. Amma auren ne bata da tabbas a kai. Auren da aka yi

ta soyayya ma gashi nan bai kafin ayi ya tashi. Ina ga wanda ya yi kama da cushe? Duk son su yi aure da

"take yi, bata so a wula™anta su."

Hamdi ce ta ri™e Zee su ka koma Waki. A nan ta tarar da Sajida akan abin sallah. Kuka take yi amma babu

sauti. Sai kwararar hawaye kawai. Sau tari ma'anar sunanta tana binta. Mutum ce mai yawan kai

goshinta ™asa wurin Allah.

Zee daina kukan tayi ganin yayarta ta fita nutsuwa. Hamdi ta fita tayi alwala ita ma ta zo ta shimfiWa abin

"sallah kusa da Sajida. Ganin haka ita ma Zee sai tabi sahu. Sun riga sun yi sallar isha tun Wazu. Don lokacin shaWaya ma ta kusa. Al™ur'ani kowacce ta Wauka ta buWe inda ya samu su ka fara karatu. Idan ka gansu abin tausayi kuma abin sha'awa. Yayinda ta ´an uwan biyu ke nemawa kawunansu zaSin Allah da sassaucin abin da ya tunkaro su, Hamdi su duka biyun take yiwa addu'ar zaSin alkhairi. Tana fata"

kowacce ta sami aminci a ™addarar dake jiranta a gobe. Kuka kuwa idanuwansu ko gauta albarka.

Duk wannan abu wayar Sajida vibrating take da kiran Safwan. Ita kuwa tayi al™awarin sake haWuwarsu ko

jin muryar juna sai in sun haWu bisa kuskure. Ba za ta Wauka ba balle ace ta kasa ha™uri da wanda

babansa ya zo har gida ya ci mutumcin nata uban.

***

A Sangaren Taj yadda abubuwa su ka kasance sai addu'a kawai. Ro™on Kamal ya yi akan ya kai shi gidan

Yaya Babba ya ce babu ruwansa.

"""Ina son rabuwa da iyayena lafiya. Naga kai wannan is the last thing on your mind. Duk nasihar da nayi"

"maka bata shige ka ba."""

"""Don Allah Abba bai baka tausayi ba?"""

"""Ya bani, amma addua ce kaWai taimakon da zan iya yi masa. Da za ka ha™ura da auren Hamdi ni kuma"

"nayi maka al™awarin auren Sajida."""

"Haushin Hamdi da yake ji ya tuna, sai dai kuma wannan bai isa dalilinsa na ha™ura da ita ba. Wannan"

tsiwar yake son ™urewa da salon soyayyar da ya tanadar mata. Zafin kai kuwa ya yi imani da cewa bata kai shi ba. Zai gayyato ta cikin rayuwarsa su hau sama su faWo tare. Barinta ne dai ba zai iya ba. Domin duka wannan rigimar tasu bata kama ™afar son da yake yi mata wanda ya yi masa shigar farat Waya ba.

Bari ya yi sai da Kamal ya bar gidan Ahmad sannan ya fice. Ya kusa isa gidan Yaya Babba sai kawai ya

canja shawara. TaSo mai adaidaita sahun ya yi.

"""Don Allah ka yi ha™uri. Kantin Kwari zani."""

"""Malam lissafin kuWinka fa zai canja."""

Taj ya zura hannu a aljihu ya zaro dubu uku sabbi fil ya bashi.

"""Ko akwai ciko?"""

Mai adaidaita ya saki murmushin da ya koma dariya.

"""YallaSai sai dai idan kuma sadaka za ka ™ara min akan wannan."""

Taj dake neman taimakon Allah sai ya ™ara masa dubu biyu.

"""Idan mun je in jira ka ne YallaSai?"

"""Da ka kyauta. Inda ka auko ni zan koma."""

*

Alh. Hayatu na zaune a cikin ofishinsa dake hawa na biyu a katafaren ginin store Winsa mai suna

Maitakalmi Enterprises dake kantin Kwari yaji ana ™wan™wasawa tare da sallama lokaci guda.

Muryar wani yaron shagon ce wanda ya kasance Wa a wajen wata da su ke ´an maza zar da ita.

"""Kawu dama..."""

"""Matsa na shiga"" Taj ya ce da Wan saurayin."

"Da sauri ya yi gefe, yayin da Alhaji ya tashi tsaye saboda gane muryar da ya yi."

"""Me ya kawo ka?"" Ya ce da kakkausar murya."

Yaron da ya nuna masa office Win don bai taSa zuwa ba tunda aka yi ginin sai yau ya kalla. Cikin sauri ya

rufe ™ofar ya bar wajen. Taj ya juyo ya kalli mahaifinsa sai kawai ya sauke gwiwoyinsa duka biyu a ™asa.

"""Alhaji na zo neman izini da amincewarka ne."" Ya faWi yana kallon uban."

"""Dama nayi wannan isar a rayuwarka ne?"""

"Zuciyarsa dokawa take da ™arfi saboda fargaba. Amma ya san cewa indai ya rasa goyon bayan Alhaji, ba"

zai taSa auren wadda yake so ba.

"""Ka fi ™arfin komai a rayuwata."""

"""Shi yasa ka zaSi barina akan ka ajiye burinka?"""

"Taj ya girgiza kai ""baka bani zaSi ba a lokacin da ka koreni Alhaji. Hukunci kawai ka yankewa kuskurena."""

Zuciyarsa hasala tayi. Šan nasa ya fishi gaskiya. Wannan ne ya Sata masa rai.

"""Rashin kunya ka zo ka yi min?"""

"""Ban isa ba."" Ya Waga kai daga dur™uson da ya yi ""aure nake so ka yi min gobe don Allah."""

"""Ka fara shan ™waya ne Tajuddin? Ni za ka tunkara da wasan kwaikwayo irin wannan?"""

"""³ar wajen Habib Umar ce. Simagade na Soron Winki."""

Yana gama magana ya rufe idanuwansa saboda jiran saukar mari daga Alhaji. Da yaji shiru na wasu

"da™i™u sai ya buWe idanunsa. Abu na farko da Alhaji ya fara ce masa shi ne,"

"""Me ka ke ta™ama da shi ne Taj? KuWin da kayi ne kake jin ya isa ka kawo min zancen banza irin"

"wannan?"" Ya nuna ™irjinsa ""Ni? Ni za ka cewa kana son auren Wiyar Habibu?"""

"""Bana ta™ama da komai Alhaji sai matsayina na jininka. Ka juya min baya a karo na farko amma Allah Ya"

tsareni daga faWawa rayuwar da kake guje min. Ba yin kaina bane. Ba kuma isarka bace ko tawa. Albarka

"ce kawai daga Allah wadda na tabbata kullum kana ro™a min."""

Kallon mamaki kawai Alhaji ya dinga yi masa. Yana kuma tuno kalaman Gwaggo na ™arshe ™arshe a gare

shi da take cewa Taj tamkar shi ne a madubi. Yadda yake haka ya haifo Wa irinsa. Duk lokacin da yake son

"ta™wara Wansa, to ya fara bari shi ma duniya ta tan™wara shi."

"""Shi yasa yanzu ma ka shirya saSa min saboda kana jin komai zai tafi yadda kake so?"""

"""Wannan karon ina jin tsoron idan ka barni

18 / 42