Chapter 15 Reading Rayuwa da Giɓi Complete Hausa Novel READ HAUSA Novels

Rayuwa da Giɓi Complete Hausa Novel

Author :  BATUL MAMMAN Category :  African Stories & Novels

Chapter   15 / 42

42K to 45K   out of 124.8K words

nasaba da tunaninta na komawarsa ga Wabi'ar baya.

"""To ko mu daina zuwa? In ya so lokacin da ka bar nan Win sai mu dawo?"""

"Allah Ya sani kamar ya ce eh, to amma nauyi da tunanin me zai je ya dawo a rayuwar su ³ar Ficika sai ya"

ce a'a. Yau kaWai da ya haWu dasu ya ga wani irin farinciki da annashuwa a tare dasu. Sun sake suna ta

aikin abin da su ka fi ™warewa wato girki. Har sai da ya yi tunanin me yiwuwa tun dawowarsu babu

wanda ya sami tarba mai kyau da mutuntawa sai yau.

***

Hamdi tayi kuka tun daga hanya har gida. Da ™yar ta iya labartawa Yaya abin da ta gani. Abba na

dawowa kuwa Yaya ta kawo zancen ita ma nata ran a Sace.

"""Yaya Habibu ka sani cewa bahaushe na cewa abokin Sarawo shi ma Sarawo ne. Yanzu duk wanda ya"

"ganka da mutanen nan zai yi maka kallon irinsu."""

"Da laluma ya dubeta ""Jinjin juya baya ba nawa bane ga wanda ya nemi taimakona. Duka duka yaushe"

"muka sami wannan rayuwar bayan haWuwa da yaron nan Taj? Ko har kin manta cin zarafin da aka dinga yi min akan neman shago? Duk unguwar da naje sai su ce kada yaransu su yi koyi dani basa so."""

"""Naji kuma duk na fahimta. Amma hanyoyin samun lada ai suna da yawa. Shigowar mutanen nan"

"rayuwarka a wannan lokacin da kake neman tada ™imarka a cikin mutane gaskiya ba zai haifi Wa mai ido ba."""

Ta sake faWi cikin fushi. Duk yadda ya so Sullo mata ta™i amincewa. Tsayuwa ya yi akan bakansa shi ma.

Yau dai Waya zai yi abin da yake jin ya dace ko ba zai faranta ran iyalinsa ba.

"""A bar maganar nan. Indai ³ar Ficika ne, ba zan kore shi ba."""

"""To ai shikenan. Allah Ya kyauta Sacin rana."""

***

"Yadda Salwa ta matsawa Taj da waya da messages a duk wata kafar da zai gani, haka Anisa ma take yi."

Gashi dai basu san da zaman juna ba amma kowacce ta matsa lamba.

Ita Salwa banda ™awa har Maminsu ta san irin soyayyar da take yiwa Taj. Da fari ta nuna rashin goyon

baya saboda Wan tsohon miji ne. Sai da taji ta kuma ga waye Taj a wani bidiyon girkinsa a youtube da Salwan ta nuna mata tayi mubaya'a. Matashi ne mafarkin duk wata budurwa. Burin duk wata uwa da take son ´arta da arzi™i. Ko da wasa girkinsa bai zo ranta ba balle ya dameta. Yana da kuWi kuma ta san asalinsa. To me ya rage?

"""Kada ki yarda ya manta dake. In ya tafi ki dasa kanki a cikin rayuwarsa."""

"""Ta yaya? Ko sau Waya bai taSa nemana ba da kansa."""

"Mami tayi dariyar manya ""wannan ai duk ba wata matsala bace. Ke ki dinga bibiyarsa. Gaisuwa safe,"

rana da dare. ³an abubuwan nan namu na mata ku baku iya ba. Sai a zauna sakato ana jiran namiji ya yi

"komai."""

"Salwa ta sunkuyar da kai ""Mami idan mace tana bin namiji fa wula™anta ta yake yi."""

"Taf...taji saukar duka a kafaWa. Rai a Sace Mami ta ce ""banda shashanci dama ai ba da soyayya za ki bishi"

"ba. Kulawa kawai. Ko kissar ma sai na koya miki?"" Ta harari ´arta."

"""Na fahimta Mami."""

"""Ko ke fa."""

Da haka Salwa ta kafa masa ™ahon zu™a. Waya da sa™wanninta babu wani abu da zai bada ita har yasa

"Taj gudunta. Yayana sama Yayana ™asa ne dai. Gaisuwa, bibiyar ayyukansa da yi masa fatan alkhairi. Tun"

yana sharewa har dai bisa shawarar Kamal ya soma amsa mata a mutumce.

"""Ba'a san inda rana za ta faWi ba. Ka daina wula™anta duk mai nuna damuwarsa a kanka."""

"""Kada ta sa rai ne Happiness."""

"Dariya Kamal ya yi ""kai ma kamar wani Wan yaro in kayi wani abin. Ai yadda ta zo maka a ™anwa haka za"

"ka je a matsayin yaya. Tunda baka so ta bijiro da zancen soyayya sai ka toshe ™ofar."""

"""Kamar ya?"""

"""Ka dinga bata labarin wata a matsayin budurwarka. Wataran ka ce ma tana gaisheta."""

"Girgiza kai Taj yayi kamar yana gaban Kamal Win ""ba zai zama cin fuska ba kuwa?"""

"""A ™anwa fa tazo maka. Kuma dai kayi mata hannunka mai sanda ta™i Waukar haske. Ba sai ka bita ba"

"kawai a tafi a haka. Ya dai fi akan ka dinga shareta wanda za ta fassara a matsayin wula™anci."""

A haka suke ta tafiya. Ya Taj da ™anwarsa Salwa.

A Sangaren Anisa kuma bai san wane tudu wane kwarin aka bi ba sai ji ya yi Amma ta tado masa da

zancen ko za su fara haWa lefe kafin su koma gida.

"""Lefe kuma? Na wa?"" Ya tambayeta kai tsaye babu mamaki a tare dashi."

"""Kada ka raina min wayo Taj. Ya ku ka yi da Anisa?"""

"""Anisa kuma?"""

"Amma ta Waure fuska ""Allah idan na sake magana ka ce min 'kaza kuma?' Sai ranka ya Saci."""

"""Yi ha™uri Ammana."" Ya yi mata murmushi."

Mayar masa tayi sai kuma ta sake shan kunu.

"""Ka san sau nawa Daddy yana yi min maganarku? Sai dai nayi ta kame kame saboda ka ™i cewa komai."""

Yadda su ka yi da Anisa da Hajjo ya faWa mata.

"""Ni na zata mun gama magana tunda ta fahimceni."""

"Yanayin Amma duk babu wani kuzari ta ce ""Maganar da aka fara daga sama ai a can ya dace a ™are ta."

"Me yasa ba ka faWa min ba?"""

Ya yi shiru. Ba zai iya ce mata yaga kamar tana so ba shi yasa ya kasa sanar da ita ba.

Anti da kanta tayi mata waya tana cewa wai ta kira tayi mata murna ´arta ta sami miji. Anisa da Taj sun

daidaita.

"Da murna Amma amsa mata da ""cewa zaki yi na cigaba da tari. Allah Yasa damu za ayi."""

"""Amin amin"" Anti ta amsa da farinciki."

Da su ka yi waya da Daddy ma zancen kenan. Har yana cewa idan su ka dawo da kansa zai yiwa Alhaji

magana. ˜udurin Taj na aure bayan ya koma gida ba abin a kawo ido a zuba masa bane. Dole su za su yi nasu ™o™arin a yanzu da Taj ya zama successful su mayar dashi gaban mahaifinsa.

Ya gama tsare tsaren hanyoyin da zai bi domin bawa Alhaji ha™uri ya janye fushinsa. Wanda hakan ya

yiwa Amma daWi sosai. Shi ne ta tayar masa zancen shi kuma ya nuna ba haka aka yi ba.

"""Ni yanzu ya kake so in yi Taj?"""

Ta ma rasa ta inda za ta Sullowa lamarin. Idan ta nuna bata so a yanzu da maganar ta fito daga bakin

kishiyarta da mijinta kowa ita zai zarga. Za a ce ita ce bata so. Sannan ga dukkan alamu ma dai gadar zare Hajjo take neman ko ma a ce ta ™ulla mata. Kuskure guda zai sa a ce tana gudun ´ar kishiya. Ko kuma a gorantawa Taj rufin asirin da aka yi masa. Ta san Hajjo sarai. Idan abu bai tafi yadda take so ba to mutum

ya shiga Wari ba ma uku ba.

"""Kasan me nake so da kai?"""

"Ya girgiza kai ""ko mene ne zan yi miki Amma."""

"""Kada ka nuna musu komai ta waya yanzu. Don Allah ko da wasa kada kayi abin da Anisa za ta sami"

"maganar da za ta kaiwa Hajjo. Idan mun koma gida sai ayi maganar a gaban kowa. Yanzu ko me zamu yi a waya babu mai fahimta."""

Ko da Daddy ya zo lokacin da za ayi mata send-off party na retirement basu nuna komai ba ita da Taj.

Lafiya lafiya yake waya da Anisa su gaisa. Idan bata kira ba sai ayi sati biyu bai nemeta ba. Bisa shawarar Anti da Hajjo da su ka kitsa wancan zance na amincewarsa duk da Anisan bata so haka ba take yawan

kiransa ko ta tura sa™o ta whatsapp.

Wata gomq sun ™are kamar ™ifta ido da buWewa. Duk wani shiri na komawarsu gida ya kammala.

Catering services Winsa na Happy Taj ne dai bai rufe ba. Duk lokacin da bu™ata ta tashi zai iya komawa ya

yi aikinsa ya dawo gida.

"Zuciyarsa a ranar da za su tafi tana cike da Wokin sake ganin Hamdi. Ba tare da saninta ba, duk wasu"

abubuwa musamman wanda su ka shafi samari yana sani a wajen ´an uwanta. Zee akwai surutu. Ita ke

faWa masa irin abin da Hamdi take yiwa samari idan sun zo.

"""Ni fa ina ganin kamar akwai wanda take so"" ta taSa faWa masa watarana."

"Murmushi yayi shi kaWai da ya ji muryar Hamdi tana cewa Zee ""gulmammiya, yau kuma faifaina aka"

"buWewa Salman Khan? Ki gama Yaya tayi mana shari'a don ba yarda zanyi ba."""

"Zee ta diririce, wayar da bata gama ba kenan ta tashi tana bata ha™uri."

"Ita kuwa kaza huce kan dami tayi. Mutumin nan na Abuja da bata san sunan shi ba ta riga ta cire shi a rai,"

tana kuma jin haushin yadda ya jirgata ta hanyar nuna kamar ya damu da ita.

***

Dogon tsaki mai madda da gunna Ummi ta saki a lokacin da Iyaa take duba katunan bikin Sajida da Yaya

ta kawo da kanta.

"""Allah Ya shiryeki Ummi. In Allah Ya so ba zan taSa aibata ki da bakina ba balle ki fi haka."""

"""Me kuma nayi? Yanzu mutum bai isa ya yi tsaki ba sai an fassara shi?"""

Tashi Iyaa tayi ta bar falon. Idan ta zauna tabbas za ta ™are da dukan Ummi da duk abin da ya zo

hannunta. Haka su ke ta fama tun bayan dawowarta daga makaranta. Ummi ta kangare fiye da

tunaninsu. Maganar aurenta da aka sa ran yi da ta gama makaranta tabi ruwa. Mijin dama na gida ne.

Duk shaiWancinta tana masifar son sa kamar rai. Zancen duniya da baya Suya sai gashi mahaifiyarsa da su

ke ´an maza zar da Baba Maje sannan ´ar mace da namiji da Iyaa ta zo har gidan neman ™arin bayani.

Yayinda Ummi take ta tsula tsiyarta a makaranta bata taSa tunanin akwai idon sani da za su iya kawo

zancenta gida ba. Sai gashi a hawan hawa maganar bullying Winta da haura katanga tana bin samari

yawo ta dawo. Maganar ayi ™arya ko kwaskwarima ma ba za ta yiwu ba. Dole su ka faWi gaskiya da ro™on

rufin asiri.

"""Maganar nan ba za ta taSa fita daga bakina ba in sha Allahu. Amma fa aure babu shi Fisabilillahi"""

"Baba Maje ya kalli ´ar uwarsa, sai dai bai ji haushinta ba sosai. Ko shi ne zai iya yin haka."

Washegari ya mayar musu da kuWin aurensu. Kayan kuma su ka ce a barsu. A ranar babu wanda ya

runtsa a gidan. Ummi kusan hauka tayi musu tuburan. Kuka da magiya harda barazanar tana son auren.

"""Kowa ya sayi rariya ya san za ta zubda ruwa. Ke ki ka ha™awa kanki wannan ramin. In kina da hankali sai"

"ki canja tsarin rayuwarki don gujewa maimaici."""

"Tana gunjin kuka ta ce ""yanzu Baba akan Wan daudu da ´arsa ka gwammace rayuwata ta zama haka?"

"Baka barni nayi jarabawa ba sannan auren ma ka kasa hana a fasa shi?"""

"""Šan daudun ne kuma yake ta fafutukar ganin kin koma makaranta ba."" Ya ce da faWa ""amma da yake"

"kin daWe kina taSa mutumcin mutane Allah Yana yi miki talala yanzu ai kin ga ishara. Duk ™o™arinsa abu ya™i ci ya™i cinyewa. Ni kuma da hannuna ba zan sake kai ki wata makarantar ba."""

"Gidan da su ka barta basu tsira ba. A hankali ta tsiri fita yawo. Idan ta dawo ayi faWan, dukan da nasihar"

duk a bayan kunnuwanta. Shafawa idanunta toka kawai tayi tana abin da ranta yake so. Cikin watanni kaWan ta Washe fata ta koma fara tas. Ga magungunan da take sha na supplement masu ™ara wasu sassan jiki. Halittarta duk ta sauya ta koma wata daban. Duk inda ta ratsa maza ke bibiyarta suna kashe

mata kuWi. Wayo da dabara irin nata yasa ta™i yarda ta bada kanta. Amma fa tana bari su fanshi

wahalarsu ta hanyoyi daban daban. Hukuncin faWa da duka ya ™are. Sai nasiha da addua tsakaninta da

iyayenta.

Halin da ta shiga yana ci wa Abba da Yaya tuwo a ™warya. Gani su ke kamar sanadiyarsu rayuwar ´ar

aminansu ta gurSace. Yayinda su Baba Maje kuma su ke ganin dubunta ce ta cika. Halayen da take Soyewa su ka bayyana. Ba don abin da ta yiwa Hamdi ba da haka za ta yi ta ha'intarsu ™ila har gidan miji tana rayuwa biyu ba a sani ba.

Ummi ta sake Waura Wammarar watsa rayuwar Hamdi a duk lokacin da nata auren ya tashi. Kuma tsakin

da tayi ba komai ya janyo ba sai takaicin lokacin ramuwarta da bai yi ba.

***

Kimanin sati uku kafin bikin Sajida aka gama komai da ya dace a HAPPY TAJ. An kashe kuWi domin ™awata

"wajen yadda zai janyo mutane. Taj da Abba da kansu su ka dinga yiwa mutane gwaji idan sun zo neman aiki. Banda yaran Abba, sai da su ka ™ara mutane masu ayyuka daban daban a kitchen Winsu. Girki, wanke wanke, serving abinci, waiters, cashiers da masu yin fruit juice, mocktails da icecream. GabaWaya kitchen Win maza ne. Sannan ya nemi inda za su dinga sayen kayan abinci. Komai ya tafi cikin tsari."

˜annensa Bishir da Abba su ya dam™awa ragamar tabbatar da kayan bu™atar kitchen ba za su yanke ba. Sun daidaita da masu kayan masarufi na kasuwa akan wannan. Spices kuma na recipe Winsh za su dinga haWawa saboda haka raw Win kawai su ka nemi mai kawowa. Dankali da kayan miya kuma fresh masu kyau da tsafta daga wajen ™awar wata sister Winsu Rumanatu mazauniyar Jos (08065530483) za su dinga

saya. Ya zamana dai babu inda su ka bari haka nan.

Masu naman tsire ko gashi su ma interview da gwaji aka yi musu. Iyawa kaWai bata da garanti sai an

duba tsaftar mutum da ingancin kayansa. Haka kuma aka yi a Sangaren kayan fulawa. Saboda kawai Taj yana son Waukar Hamdi sai ya ce bakery Winsu mata za a saka.

Application babu kama hannun yaro. Da ™yar su ka zaSa don babu laifi a Kano akwai masu sarrafa fulawa

"daban daban da kayansu suke da inganci. Wata ™anwarsa da ta dinga zuzuta masa ™awarta Zahra wadda aka fi sani da Donutfairy (08065156303), dole yace a nemota. Ya WanWana doughnut, banana bread da youghurt Winta. A take ya nemi signing contract da ita tunda matar aure ce. Aka ™ayyade adadin abin da"

za ta dinga kawowa kullum da farashinta.

�angaren Kamal ma boutique ya tashi sai wanda ya gani. Garden da wurin wasan yara duka an gama

zuba ma'aikata. Ranar Juma'a aka yi sauka domin kore kowanne shaiWanci da neman albarka daga Allah. Sai kuma aka sanya sati mai zuwa a matsayin ranar buWe restaurant Win. Anyi ta sanya talla ta gidajen yaWa labarai da shafukan sada zumunta. Akwai discount ga mutanen da za su zo a wannan rana. Ga

kyaututtuka na yara domin za su yi gasa da wasanni.

Garin Kano ya Wauka. Ko ina ka zaga ana jiran ranar buWe Happy Taj.

*

Gidan Alh. Hayatu ya hargitse da shiryawa wannan rana. In ka duna status da stories Win ´a´a da jikokin

"gidan ds su ka tasa, gabaWayansu abin da su ke Worawa kenan. Sai kuma hoton Taj sanye da wasu fararen kaya na girki ya ri™e irin kaskon nan na zamani mai Wan zurfi da dogon mari™i a hannu Waya, sai kuma cokalin juyawa a Waya hannun. HarWe hannuwansa ya yi dasu irin yanayin tsayuwar Black Panther idan sun yi alamar Wakanda Forever. Yayi matu™ar kyau da kwarjini a hoton. ˜aryar mutum ya gan shi ya"

danganta shi da mace. Murmushin fuskarsa yafi komai tafiya da hankalin mai kallo.

"Yadda ake ta shiri da farinciki a gidan Alh. Hayatu, haka ma su Sajida su ke ta murnar wannan Waguwar"

"daraja da mahaifinsu zai samu idan ya fara aiki a Happy Taj. Har anko Abba ya yiwa ´a´ansa. Yaya kuwa nata kayan sun fi nasu tsada ma. Kowa ya yi murna banda Hajiya Hamdi. Gani take ba a rabu da Bukar bane an haifi Habu. Abbanta zai baro local ´an daudu su ³ar Ficika, ya koma hannun international Wan daudu wai shi Taj. Ita dai da tana da iko da ta hana shi wallahi. Har mamakin yadda kowa na gidan yake"

™aunar Taj Winnan take yi.

***

"Komai nisan dare gari zai waye. Bayan shafe shekara guda da ´an watanni, gobe ne ranar da za a buWe"

Happy Taj.

"Tunda aka saka rana Hajiya, Mama, Umma da Inna duk kawaicinta su ke ro™on Alhaji da ya yi musu izinin"

zuwa. Amsar da ya basu ita ce ba zai hana kowa fita ba amma idan sun tafi kada su dawo. Mama da Inna

har kuka su ka yi. Ya ce ai bai hana su ba. Kowacce tana da damar zuwa amma tabbas bai yarda su dawo

gidansa. Hajiya ta kai ™ararsa wajen Yaya Babba sai dai dattijon ya ce ba zai ™ara yiwa rayuwar ™anin nass

katsalandan ba. Har yau yana ganin laifinsa ne korar Taj da Alhaji ya yi.

Suna ji suna gani ´an uwansu da na mijinsu da ´a´ansu duk zasu amma ya yi musu shamaki. Walwala da

farinciki sai su ka yiwa gidan kaWan.

Taj bai fasa sanar da Alhaji duk abubuwansa ba kamar yadda Amma ta koya masa. Saboda haka duk wani

abu da ya danganci restaurant Winnan tamkar dashi ake yi. Har hotuna da bidiyo yake tura masa. Bidiyon ™arshe da aka yi kamar film na minti Waya da rabi shi yafi komai ™ayatarwa. An bi ko ina a wurin daga gate har ™urya. Ga ma'aikata da shi kan shi CEO Taj cikin farinciki suna ta aiki a wajen. Ya kwanta tun wajen tara na dare sai ya kasa bacci. Kewar Wan nasa tayi masa wani irin kamu. Ya yi kusan awa biyu

yana juyi a kwance ™arshe ya tashi ya Wauki mu™ulli ya fice.

Kowa ya yi mamakin fitarsa a wannan lokacin. Kamal zai bi shi Hajiya ta hana.

"""Wallahi kewar Taj yake. Ku rabu dashi. Bashi da aiki sai kallon waya. Rannan da kunnena naji muryar Taj"

"a wannan bidiyon da yara ke yawan kunnawa. Tunda girman kai ya hana shi dawo dashi gida sai ya yi ta wahala shi Waya."""

"""Hajiyarmu yau da kanki?"" Abba ya faWi da mamaki. Don ita bata da zafi kamar sauran matan."

"""Fita idona ni."""

Ta koma Wakinta ta kwanta. Sauran matan ma duk su ka watse. Inna ce da ta shiga Waki ta dinga addu'ar

Allah Ya daidaita lamura tsakanin uba da Wan.

To dai Alhaji bai zame ko ina ba sai Happy Taj. Shi da ya jima bai yi tu™i ba ko a jikinsa yau. Ga dare

amma haka ya fito ya tsaya a bakin gate Win. Ya kalli ginin da wani irin pride yana jinjina kai. Tabbas yana cikin farinciki. Taj bai lalace yadda ya

15 / 42