Chapter 29 Reading Rayuwa da Giɓi Complete Hausa Novel READ HAUSA Novels

Rayuwa da Giɓi Complete Hausa Novel

Author :  BATUL MAMMAN Category :  African Stories & Novels

Chapter   29 / 42

84K to 87K   out of 124.8K words

da motar ya Waga handbrake tare da canja giya zuwa 'P'. Ya juyo su ka haWa ido har

lokacin bata cire hannuwanta daga fuskarsa ba.

"Shan kunu ya yi ""Ki barni in ™arasa. Ba ke nake yiwa ba."""

Ita kuma ta marairaice masa

"""Don Allah kayi ha™uri to sai na fita."""

˜wayar idanunta yake kallo sai ta rufe idon.

"""Can I have that kiss now?"""

Zame hannuwanta ta soma yi daga fuskarsa ya janyota gabaWaya. Garin ya Worata a cinyarsa handbrake

ya sauka. Motar ta Wan yi gaba amma ba da sauri ba saboda giyar da ya canja. Rungume shi tayi ™am™am tana salati ta sanya fuskarta a tsakiyar ™irjin shi.

"""Wayyo Allah Abbana...Yaya..."""

Bata san lokacin da ya sake tsayar da motar ba. Hannunsa aya kawai taji a ™asan haSarta ya Wago kanta

sama.

"""Salwa bata da matsayi ko kaWan a wajena kinji."" Kai ta gyaWa a hankali."

"""Fitar da muka yi ba abin da kike tunani bane. Happiness ne yake ™o™arin fahimtar da ita ta ha™ura."""

"""Ai na yarda."""

"""Akwai wa™a da ta dace da irin wannan yanayin."" Ya Wage gira."

"""Kada kayi don Allah."""

"""Ke dai???"""

"""Bana so."" Ta turo baki."

"""Hamdi."""

"""Na'am."" Ta ce tana mai jin nauyinsa don ya™i sakinta balle ta koma mazauninta."

"""I love you."""

˜asa ta so yi da fuskarta don kunyar yanzu tafi ko yaushe. Sai dai Taj yaci alwashin yau sai ya rage wani

abu a kunyar nan ya tafi dashi gida. Shammatarta ya yi kamar zai yi magana taji saukar leSensa akan nata. He was so gentle amma ya kashe mata jiki har ta sake narkewa a jikinsa bata sani ba. Rungumeta yayi a haka kanta a gefen kafaWarsa kamar mai bacci. Shi kuwa wani irin contentment ya samu ds

nutsuwa a zuciyarsa.

Basu yi aune ba su ka ji ana ™wan™wasa gilas
in motar. Mutanen dake waje suna cewa ko lalacewa tayi

ko kuma mai ita wani abu ya same shi. Kamar ™ifta ido Hamdi ta koma wurinta tana raba idanu. Taj ya

kalli mutanen ya ga da wuya su fahimci matarsa ce idan su ka gan shi da mace. Kawai sai ya canja giya ya

yi gaba. Shi da Hamdi su ka haWa ido su ka kama dariya.

_Uwargida. I see you! SonSo Sis Juwairiyya_

RAYUWA DA GI�I 23

Batul Mamman

Har su ka ™arasa gida idan sun kalli juna sai sun yi murmushi. Abin da ya Waurewa Hamdi kai shi ne yadda

Taj har wani kawar da kai gefe yake irin na masu jin kunya. To ai ita ma kunyar take ji. Kuma ita ya dace ta dinga yin haka. Sai gashi kafin tayi yake yi. Gajiya tayi lokacin sun iso layinsu ta kalle shi.

"""Wai mene ne?"""

"Gefe ya kaWa kai yana wani rufe ido ""Awwnnnnn, ni ki daina tambayata. Kin fi ni sanin ko mene ne."""

Murmushin fuskar Hamdi Waukewa yayi. Ta soma harararsa.

"""Banda wa™a kuma harda irin haka kake yi?"""

"""Irin yaya?"" Ya tambaya kamar bai gane manufarta ba."

"""Meye wani awwnnn don Allah?"""

"Hannu ya kai ya shafa kumatunta ""Saboda ina son ganin wannan hararar da juya idanun naki. You always"

"look cute."""

"Murmushi ta soma yi ya kuwa sake cewa ""awwnnnn"" yana dafa saitin zuciyarsa."

Wannan karon dariya tayi. Irin dariyar da bai taSa gani daga gareta ba. Zuciyarta tayi fari kamar auduga.

"""Kin san wani abu? Zo mu shiga ciki kafin ha™urin Abba ya ™are."""

Bakin ™ofar gidansu ta kalla. Ai kuwa Abbanta ne yake Wan le™owa. Bai yi zaton za su yi dare ba. Kuma

sun iso Win ma ta™i fitowa. Shi ne ya kasa sukuni. Kada fa ta biyewa Taj al'amari ya kwaSe a gaba.

"""Zan kira ki idan naje gida. I hope ba da wuri ki ke bacci ba."""

Bata iya bashi amsa ba da ta hango inuwar Abban da gaske. Kamar an tsikareta ta fito da sauri. Tana

hango shi ya koma cikin gida ta bi bayansa. Taj ya yi murmushi kawai. Ya juya baya zai yi ribas ya yi arba da ledojin da ´an uwansa su ka ajiye mata. Parking ya gyara ya Webi yadda hannuwansa za su iya Wauka ya je ™ofar gidan yana sallama.

Caraf yaji Abba yana yiwa Hamdi faWan kada ta manta da maganarsu. Shi ba zai iya ja da Alh. Hayatu ba.

Jin sallamarsa yasa shi yin shiru. Hamdi kuma ta ruga ciki da sauri.

"""Taj baka tafi ba?"" Ya fito waje."

"""Sa™onta ne ta manta."" Ya nuna ledojin hannunsa."

"""Harda wahala haka?"""

"""˜anwarsu su ka yiwa. Bari na shigar mata dasu."" Taj ya wuce ciki kafin Abban ya ce shi zai karSa. Hakan"

zai zama raini ma.

"A tsakar gidan ya sake sallama, Yaya ta amsa da yi masa izinin shiga falon. Akan kujera ya ajiye ledojin ya"

ce da saura. Ta saki baki har yaje ya dawo. Lokacin ita da Abba ne a falon. WaWanda ya dawo dasu har sun fi na farkon yawa.

"""Mene ne haka Taj? Daga zuwa gaishe su kuma sai ka haWota da wannan kayan?"""

"""Babu ruwana Yaya. ³an uwanta ne su ka bata."""

Yaya dai bata jidaWi ba. Ta san kwaWayi ba halin Hamdi bane to amma za a iya fassara ta dashi ga wanda

bai santa ba in yaga kayan. Da dai bata karSa ba. Kiranta tayi ta dawo falon da sauri don kiran ta san na faWa ne. Kaya dama ta tafi cirewa. Wata free doguwar riga ta saka da hula a kanta.

"""Me yasa ki ka karSo kayan nan Hamdi? Tarbiyyar gidan nan kenan?"""

Dur™usawa Hamdi tayi a gaban kujerar da ya zube kayan tana ™are musu kallo. Ita kanta bata san sun kai

haka ba.

"""Allah Yaya ba ro™a nayi ba. Ba ma a hannuna su ka bani ba."""

Kusa da ita Taj ya dawo ya zauna a ™asa ya fara sauko da kayan gabansu.

"""Yaya yanzu abin hannun ´an uwana kike faWa a kai? Kin san da ro™a tayi nima ba zan yarda mu taho"

"dasu ba ko?"""

"Yaya ta ce ""Kada ka kare mata. Ai ta san irin abin da ya dace da wanda bai dace ba."""

"Hamdi ta sunkuyar da kai ta ce ""Ki yi ha™uri."""

"""Ni ya kamata na bata ha™uri. Na zata mun zama Waya ne ko ban aureki ba shi yasa ban Wauki karSar"

"kayan a matsayin laifi ba."" Ya yi wani iri da fuska yadda za a tausaya masa ""a zatona na kai matsayin da zan iya tambayar Halifa da yake ™arami abu idan ina so. Na Wauka hakan ne a wajenku ku ma. Kuskuren daga gareni ne. Ki yi ha™uri."""

Yaya dariya ta kama yi. Abba kuwa ya girgiza kai don dama ya san za a rina.

"""Anya Taj ba Satan kai kayi na zaSen aiki ba? Da lauya ka dace. Yanzu Fisabilillah wannan marairaicewar"

"duk don nayi maganar karSar kaya ne?"""

"Da rashin jindaWi kamar gaske ya ce ""To Yaya abin hannun ´an gidanmu ai baya cikin wanda za a yi mata"

"faWa a kai ko?"""

"""Baya ciki. Magana ma dai ta wuce."""

Ya kalli Abba dake yi musu dariya da Hamdi da kana ganinta ka san taji daWin ceton da ya yi mata a

hannun Yaya.

"""Gara dai na baki ha™uri kuma nan gaba duk mu kiyaye."""

"""Nace magana ta wuce Taj."""

"""Mungode. In sha Allah zan yi musu magana su ma kada su sake..."""

"""Ya Rabbi. Taj a bar maganar nan. Ni na fara kuma na janye."""

Yaya ta faWi da ta rasa yadda za tayi dashi ya yi shiru. Tashi ma tayi tace musu sai da safe. In ta biyewa

Taj sai ta koma basu ha™uri tana tumami a ™asa. Ai kuwa su ka sanya dariya harda shi uban gayyar. Yaya da Abba na mi™ewa ya Waga hannunsa yana kallon Hamdi. Bata kula da cewa basu gama fita ba ta tafa

dashi a hankali. Yaya na gani ta ™ara sauri. Abba yabi bayanta yana dariya.

"""Ai naga kayan amma ban ce komai ba saboda sanin halinsa. Da yanzu muna ™ofar gida yana kalallameni"

"yadda ya yi miki."""

"""Ka san Allah? Zuciyata fes nake jinta. Sajida da Zee duka mazansu su na son su. Hamdi kuwa nayi zaton"

"Allah auren rufin asiri ne. Ashe da gaske yake da yace yana sonta."""

"""Da kin tuna Yaya Hayatu sai in ce miki halinsu guda. Kaifi Waya ne. Kawai dai shi bashi da tsatstsauran"

"ra'ayin uban ne."""

"""Ita ma ja'ira anya bata son shi kuwa? Da tabi ta ™ulla masa kafin su haWu. Ban zata za a sami kanta da"

"wuri ba haka. Amma yanzu ko makaho ya san inda zuciyarta ta dosa."""

Abba jikinsa duk ya yi sanyi da irin murnar da take yi da kuma gaskata batun Hamdi na son Taj.

"""Uwar zamani. Kina nan kina zancen soyayyar ´a´anki."""

"Tayi dariya ""a uwar Waka ba. Da mahaifinsu."""

Zee ce ta tayata kwashe kayan zuwa Wakin Abba bayan tafiyar Taj. Tafiyar ma don dai kawai dare ya

soma tunda an idar da Isha'i. Ba don haka ba yadda ya soma samun kan amaryar tasa da sai abin da aka gani.

*

"Washegari kamar yadda su ka shirya zuwa gidan Sajida, Zee da Hamdi sun kammala ayyukansu na gida"

da wurwuri. Tsabar Wokin son ganin ´ar uwar tasu da aka hana su yi da wuri ko ´ar cacar bakin da su ka

saba ba ayi ba. Yaya zuba musu idanu kawai tayi. Sai gasu shaWaya da rabi sun fito cikin shiri.

"""Wadda ta san ta tambayi mijinta ta zo ta wuce. Wadda bata tam """

"Hamdi ce ta fara cewa ""Innalillahi"" hannunta na sauri ta buWe jaka ta Wauko waya za ta kira Taj, Yaya ta"

ce ba za ta lamunce titsiye ba.

"""Tunda ku ka fara zancen nan ai saboda nauyin dake kanku yasa na hanaku wannan ziyarar ta rashin kan"

"gado da ake yiwa amare da zarar sun tare. Amma ban faWa muku izinin fita ya bar hannunmu ba?"""

"Idanun Zee harda ™walla ta soma ro™onta ""don Allah ki bari mu tambaya yanzu. Allah ni mantawa ma"

"nake yi."""

"""Ha™™un, ai kuwa sai a fara shirin tariyarku tunda zaman gida ya sa kun manta darajar da Allah ya yi"

"muku. ˜arshenta a waje ma idan wani ya yi muku magana sauraronsa za ku yi saboda kun manta."""

Zamanta tayi akan kujera tana kallon ´a´an nata. Babu wadda bata tunawa ta kira mijinta ta nemi izinin

fitar ba a™alla sau uku. Idan tayi magana sai su hau dariya suna tsokanar juna. Jiya da daddare har za ta sake yi musu tuni Abba ya ce ta ™yalesu. Indai basu yi da wuri ba to kira cikin dare ko da safe duk Waya ne.

Titse ne wanda maza da yawa basa so.

"""Yaya don Allah."" Hamdi ta sake ro™onta kamar tayi kuka."

"""Kun san babu abin da na™i kamar mutum ya dinga kira min mantuwa. Maganar nan mun yi yafi sau"

"nawa. Amma aka rasa mai aiwatarwa. Sai ku koma Waki ku kwanta. Hutun ma ai abin so ne."""

Waya Zee ta auko ta duba. Ita dai jiya da yamma a text ta tambayi Baballe. Tunda ta tura text Win bata

™ara dubawa ba saboda ta san in ya gani kiranta zai yi. Wurin da ya tafi aiki a Kaduna ™auye ne. Tana

dubawa kuwa sai taga ya yi mata reply. Izinin fitar ya bata da bayanin raunin network da ya hana shi kiranta tun safiyar jiya. Ihun murna ta kama yi harda tsalle.

"""Yaya ya barni. Allah ni an barni. Kin gani"" ta mi™a mata wayar don ma kada ta ™aryata ta."

"""Sai ki zo ki tafi. Allah Ya tsare. Ana la'asar ki fito."""

"""Don Allah ki barni in kira yanzu."" Hamdi ta soma yiwa Yaya magiya. Da ™yar ta aminci. Ta kira shi ya fi"

sau biyar baya Wauka. Hawaye kawai ta soma don wani irin abu ne ya sami wuri a ma™oshinta ya zauna.

Duk magiyarta kuma Yaya ta ce babu inda za ta. Duk da taji tausayinta amma ba za ta buWe ™ofar irin

"haka tsakaninta da mijinta ba. Wannan kuskuren na miji bai sani ba ko ya ce kada ayi, uwa kuma ta ce sai anyi ba da ita ba. Bata bu™atar wani ya faWa mata irin sa'ar da tayi da Allah Ya aurar mata da ´a´an lokaci guda."

Ganin halin da ta shiga yasa Zee cewa ta fasa fita. Yaya ta ce bata isa ba. Ha™uri ta bawa Hamdi ta tafi.

Ita kuma ta shige Waki ta sha kukanta ta more. Tun Yaya na Wan jiyota har taji Wif. Ta le™a Wakin ta sameta

ta du™un™une jikinta tana bacci. Ga shatin hawayen da ya bushe ya fito raWau akan hodar da ta shafa.

Murmushi tayi ta kirata shagwaSaSSiya a zuci. Ta tabbata daga ita har Zee Win daga yanzu za su bawa

abubuwan da su ka shafi aurensu mahimmanci. Dama wani darasin sai uwa ta daure zuciyarta take iya koyar dashi.

Shabiyu ta gota Taj ya farka daga baccin da ya Wauke shi a dalilin ciwon kai da murar da su ka dirar masa

bayan ya dawo jiya. Magani ya sha amma baccin ya gagara. Sai bayan ya yi sallar asuba sannan ya samu ya kwanta.

Missed calls Win Hamdi da ya gani ya yi tunanin ba lafiya ba. Sai kuma yaga message tana ro™on zuwa

gidan Sajida. Ya kwatanta lokacin da ta kira da sanda ya gani. Yau akwai daru da alama. Yawan kiran ya san a matse take da tafiyar. Ko abinci bai nema ba bayan ya yi wanka ya fita saboda Salwa da ta kankane falon. Yau Happy Taj yana fin kullum cika. Idan ya shiga sai an gan shi kawai. Shi yasa ya yanke shawarar fara zuwa ganin Hamdi.

Zai kirata ya ce mata ya zo yayi sa'a Halifa ya dawo daga Tahfiz. Yaje ya gaishe shi sannan ya shiga ya

faWawa Yaya saboda Hamdi na banWaki tana watsa ruwa. Yaya ta ce a faWa masa ya shigo. Shi kuma gwanin sai da ya faWa masa wanka take yi kafin ya faWi sa™on Yayan. ˜ananan kaya ya saka shi yasa ya so zama a mota da farko. Tunda Yaya ta ce ya shigo babu yadda ya iya.

"""Ya na ganka haka yau? Ko ba ka jindaWi ne?"" Yaya ta tambaye shi ganin fuskarsa ta Wan faWa akan ganin"

da tayi masa jiya.

"""Mura ce ta saka min ciwon kai."""

"""Ai kuwa gashi naji muryarka ta canja. Allah Ya ™ara sau™i."""

Hamdi bata san yazo ba. Wata shirt mai gajeren hannu ta saka da zani ta fito ko Wankwali babu. Fuskarta

fayau sai idanu a kumbure saboda kukan da tayi. Babu abin da ke tashi a jikinta sai wani irin ni'imtaccen ™amshin body oils Win Scentmania. Gwaji kawai tayi tunda dama tun kafin fitarsu ta so sakawa amma sanin rashin dacewar haka a addinance yasa ta fasa. Wurin ™arfe goma na safe taga sa™on Yaya Kubra ta whatsapp. Ashe tun jiya ma ta turo. Bata yi mamakin ganin sunan ba saboda Firdaus ce ta zauna tayi ta

kiranta da lambobin ´an gidan tana mata saving.

Bayanin sirrin dake tattare da ™amshi ga matar aure ta turo mata wanda ainihin mai turarukan

Scentmania ta tura mata. A ciki ta gane ™amshi ba ™aramin tasiri gare shi ba idan ana amfani dashi ta hanyar da ya dace. Musamman idan mace tayi katarin sani da sayen body oils Win da ita dai Hamdi bata taSa jin ™amshi irin nasu ba. Har shawara take bayarwa cewa yana da kyau mace ta samu wani ™amshi da za ta yawaita amfani dashi wanda miji zai ganeta dashi. To ko makamancinsa yaji a waje ita zai fara tunawa ya sami nutsuwa. Gashi wai har classes tana yi. Sannan packages Win ba dai arha ba. Dole ma ta faWawa su Sajida idan ta huce daga fushin yau. Don tana ta hango su ana can ana raha banda ita.

(07065525409 - Scentmania by Sana)

A ™ofar falon ta tsaya don kads Yaya tayi mata magana akan idonta.

"""Yaya me za a dafa na dare?"" Tayi magana muryar nan na nuni da har yanzu ranta ba a sake yake ba."

Daga ciki Yaya ta amsa mata.

"""Abincin daren za ki Wora tun yanzu? ˜arfe biyu ma bata yi ba."""

"""Gara na gama tun yanzu."""

"""Ai fa yau tunda na hanaki fita sai abin da hali ya yi. To shigo ki gaishe da mijinki da jiki. Baya jindaWi."""

"Labule ta Waga tana cewa ""waya ku ka yi?"" Sai ta ganshi a zaune ya jinginar da kansa a jikin kujera. Ciwon"

kan ke neman dawowa harda zazzaSi. Da baya ta fara tafiya za ta koma.

"""Ina kuma za ki? Fita zan yi gidan Gwaggo Dela in duba ta."""

Ta gaban Hamdi ta zo ta wuce abinta. Tana fita tsakar gida ta ja kunnen Halifa akan kada ya shiga falo sai

Taj ya tafi. Dariyar sha™iyanci kawai ya yi. Tana jiyo shi ta ce

"""Šan banza."" A ranta kuwa gani take in ba wajen matarsa ba yanzu ina zai je in bashi da lafiya. Uwa ce"

dai tafi cancanta yaje ya narke mata da shagwaSa da rakin maza. To kuma babu dama.

Sai da Yaya ta fita daga gidan sannan Hamdi ta yarda ta ™ara kallon Taj. Yana daga zaunen ya nuna mata

kusa dashi da hannu amma bai yi magana ba. Ta juya ta kalli bayanta sai ta girgiza kai.

"""Please. Bani da lafiya fa."" Taj ya faWi yana lumshe idanu."

Shahada tayi kawai ta biye masa duk da kafin yazo da ta gama fushin rashin amsa wayarta da ya yi. A

hankali ta isa bakin kujerar amma ta™i zama. Ya mi™a hannu ya janyota gefensa.

"""Bani da ™arfin Waukanki saboda wani irin weakness da nake ji. Da tun daga bakin ™ofar zan taroki."""

Rumgumota yayi a gefensa. ˜amshin jikinta mai sanyi ya buge shi. Bai san lokacin da ya sanya fuskarsa a

tsakanin wuyanta ba. Ta fara no™ewa taga kamar ma angiza shi take sai ta ha™ura.

"""You smell..."" ya kai hancinsa bayan kunnenta ya ja numfashi ya sauke a hankali ""relaxing and sweet."""

Šumin da taji a fuskarsa dake bin wuyanta yasa ta daina mutsu-mutsu har ta tabbatar ba normal Wumin

jikin mutum bane.

"""ZazzaSi kake yi haka?"" Ta faWi tana janye jikinta don su fuskanci juna."

"""Uhmm."" Ya amsa da rashin kuzari ""harda kaina."""

"Juyawa tayi ta taSa goshinsa. Ya Wora hannunsa akan nata. Cike da kasala ya ce,"

"""Ba don bana jindaWi ba da na nuna miki yadda shigar nan taki tayi min kyau."""

Hannunsa dake tracing ™aramin hannun rigarta ta ri™e tana mamakin yadda yake tunanin wani abu

daban da zazzaSin jikinsa. Sake janyota yayi ya mayar da kansa kafaWarta yana ™ara rungumeta.

"""Ina zuwa."""

Fita tayi ta barshi. Ya runtse ido don kan nasa ba da wasa yake ciwo ba. Duk yadda aka yi zirga zirga da

rashin hutun kwanakin nan ke tambayarsa.

Abinci tayi niyyar kawo masa sai tayi tunanin babu lallai ya iya ci. Ta Wauko gasara ta dama masa kunu da

tsamiya kaWan saboda yaji daWin bakin. Da ta koma falon idonsa a rufe ta same shi. Ta zuba kunun a kofi ta zauna a gefensa.

"""Ya

29 / 42