Author : Bintu Musa Category : African Stories & Novels
ai" sai lokacin ya dago yana kallon mahaifiyar tasa, a nutse yace "Da yardar Allah za'a gyara hakan" sai tayi murmushi sanin cewa a kaikace yake fada mata bazai iya bata yarinyar ba, ganin haka sai shima ya sake cewa "Inason ta taso cikin 'yan'uwanta ne su shaqu, a ganina ta hakan ne zasu samu hadin kai da junansu batareda sun wareta ba" kadan ya rage Uwah bata tabe bakinta ba saboda a yanda tasan matar d'an nata zuwa yanzu ma ta ware yarinyar daga cikin 'ya'yanta, sai kawai ta danne komai tace "Allah ya rayasu gaba daya" ya amsa da Amin. A daren ranan tasa aka maida Fadwan sashen nasu gurin Habiba ta cigaba da kula da ita.
Bayan sati biyu Papa ya shirya tafiya Abuja, a inda babban companynsu yake aiki. Tafiyarsa America yasa Abdulrazaq daya kasance daya daga cikin executive directors yake running a gurbinsa while Abdulrahman kuma yake running branch dinsu na Kano. Sai yanzu da dawowar shi Papan tasa zai cigaba daga inda ya bari dan shine President a Empire din nasu sannan Mai martaba kuma chairman gaba daya. A ranar da zai tafi sai da ya sake maganan kulawan Fadwan da Momma, suna zaune tana tsiyaya masa tea dinda hadimarsu ta kawo masa while shi kuma yana duba wasu takardun da zai tafi dasu gurin aikin. Sai da ta gama zuba masa sannan ya ajiye takardun ya karbi Khadijah dake riqe a hannunta daya, sai tace "Da ka fara da tea din tukunna" bai amsa ba ya cigaba da wasa da Khadijan, sai can ya dago yana kallonta yace "Fatima, fadamin ya zakiji in ace yau ba kya raye kuma aka rasa mai kula mana da Khadijah" sai ta hade girar ta cikin rashin fahimta, ya sake cewa "Ina miki kwatancen hakan ne da yanda har yau kika kasa karban Fadwa a qarqashin kulawarki" sai ta dinke fuska tace "Koda 'yan'uwanka basu kula dasu ba nasan nawa 'yan'uwan bazasu taba barin 'ya'yana a wulqance ba" ya sake danne komai sannan yace "Kika sani ko ita tafi namu 'ya'yan gata amma Allah ya rabota da kowa nata" sai ta dan juya kanta rai a bace ba tace komai ba, anutse ya sake cewa "All I'm saying is that, sai ka taimaki wani sannan Allah zai dubi naka a rayuwa Fatima, Think about it. Banason yarinyar nan ta taso ta fahimci tun tana da qarancin kwanaki a duniya kika gujeta da duk abunda ya shafeta, bamuda tabbacin me Allah ya ajiye mata a gaba, me zata zamo agaba, ko kuma wani irin kaddarar ce a harde tsakaninki da ita. Akwai mutanen da ko baka son kusancinsu a gareka sai Allah ya barsu a kusa dakai na har abada babu rabuwa, wanda babu yanda zakayi in baka so su ba. Ki fara taming zuciyarki tun yanzu a kanta in ba so kike Allah ya gwada ikonsa a tsakanin ki da yarinyar nan ba" da haka ya dauki shayinsa ya fara kurba amma har sannan bata juyo da kanta ba tana kallon Tv dake aiki a falon.
Paid book 500
Fatima Musa Maina Opay
Shaidar biya : 08134692758
MURADIN ZUCI📖
Bintu Musa
Chapter 10
Free page
A wannan tafiyar da Papa yayi sai ta zamo daidai da tafiyar su Mai martaba da Uwah zuwa saudiya yin Umrah. Sai da yayi wata guda kafin nan ya fara shirin komawa gida. Bayan ya sallama sauran ayyukansa ga qaninsa Abdulrazaq da yake zama da iyalinsa anan Abujan sannan ya tafi. Amma daren ranar da ya dawo sai da zuciyarsa ta tsinke da aka miqo masa Fadwa a hannunsa yana kallonta. Cikin sati hudu-sati hudu kawai yarinyar ta fita daga hayyacinta kamar ba jinjira ba, tayi wani irin bala'in rama har wasu quraje ne suka fito mata kamar na qyanda gashi babu alamun kula a jikin yarinyar kwata kwata. Danne ransa yayi ya riqe yarinyar baice komai ba, bayan an kawo masa Khadijah ne kuma yaga son kai irinna matarsa qarara a fasalin yaran nasa wanda a bayyane yake basai an fada ba. Duk wasu alamomin lafiyayyen jinjiri mai samun kulawa sun bayyana akan Khadijah amma akasarin hakan akan Fadwa, baiwar Allah sai idanun nata suka sake fitowa rauu dasu kamar wadda take zaresu da saninta. Dogon kallon da Papa ya yi mata ne abubuwa dayawa suka darsu a zuciyarsa a wannan lokacin, Amma sai ya danne komai a ransa. Cikin kwanakin da suka biyo baya ya tsananta saka ido akan lamarin yarinyar, anan ya lura da yanda matar tasa ta maida schedule din kula da Fadwan abun walagigi, bata tashi barin Habiban ta kula da Fadwan sai dare, kuma duk yawan hadimanta bata saki Habiban ba sai ya zamto aduk wunin ranar jefi jefi Habiban zata yanke wasu ayyukan nata taje ga dakin Fadwan ta bata madaranta. Gashi a wannan lokacin su Imam sun koma makaranta suma basa zama sosai, balle yanzu da ba a sashe daya suke zama dasu akai akai ba. Abunda yafi qona ran Papan ma shine yanda duk da dawowarsa Mai dakin tasa bata chanja yanayin kulawan yarinyar ba kodan ganin idonsa, It's so extreme that sai da ya fara tunanin anya akwai zuciya a qirjin Fatimansa da yake gani a yanzu kuwa.
A wannan tsukun su Mai martaba suka dawo daga Umrah. A ranar da suka iso da Momman taje gaishe da Uwah bayan ta baro sashen Mai martaba sai ta sameta riqe da Fadwan tasa an kawo mata ita, ganin yanayin kallon da Uwahn ke jifanta dashi itama sai da ta dan sha jinin jikinta amma da yake zuciyarta ta riga ta bushe akan alamarin sai ta maze tana gaisheta, nan take babu boye boye rai a bace Uwah tace "Fatima! Allah ya qara gyara miki zuciyarki dan ki samu rabauta da lahirarki, in ba haka ba rayuwarki da kallo, kuma halinki bai zamo abun koyi ga 'ya'yan da suka fito daga tsatsonki ba" nan take kuwa Momma ta fara kuka saboda yanda maganar ta dake ta kuma ta mata daci arai, ita me tayi toh?. Uwah ta girgiza kai sanin hawayen kada take gani a fuskarta dan ta sani ba gyarawan zatayi ba.
A zuciye Momma ta baro sashen Uwah ranan cikin qunan rai ta tafi direct zuwa falon mijinta ta samesa zaune da yaransa har Jidda na kwance a jikinsa, ganin haka sai yace da su Imam dake zaunen su dan bashi guri, sai da suka fice sannan ya kalleta amma baice komai ba har saida ta gaji da shirun sannan tace "Ka fadamin shin fina da yarinyar nan tayi a wajenku har yakai a fara zagina a bayyane saboda ita?" anutse ya girgiza kansa batareda ya nuna alamun bacin rai ko akasinsa a fuskarsa ba sannan yace "Ko daya Fatima, Fadwa kaman Khadijah take a gurina dan haka babu ta yanda zata fiki a gurina har abada, kin fi min ita. Sai dai abubuwan da kike mata yasa zan rabakin da ita kamar yanda kikeso din" kallonsa ta tsaya yi, sai ya kamo hannunta yace "Zan rabaki da itan, kulawanta bazai sake zama abun damuwarki ba har abada in sha Allah, sai dai zan AURO wadda nakeson ta kulamin da ita tunda itama 'yatace Fatima, hakkin kulawanta ya rataya a wuyana kamar na sauran 'ya'yana, banason mu shiga hakkinta muyi laifi a gurin ubangiji" a sannu ta zare hannunta daga nasa cikin wani irin sanyin jiki, wani irin daskarewa jikinta yayi kamar batada jini, ganin haka sai ya sake nutsar da murya ya sake cewa "This is for the best Fatima, banason yarinyar nan ta zamo priority a sabanin dake shiga tsakaninmu, Ina sonki matuqa. Kisani wadda zata shigo bazata taba finki a zuciyata ba har abada" cikin diri tace "Just shut up Abdulaziz" ta miqe jikinta na wani irin rawa tace "Niiii !!..Ni zakayiwa kishiya akan 'yar tsintuwaaa! Ka rasa akan me ma zakamin kishiya sai akan 'yar da ka tsinto a yashe cikin sanyin Texas" kallonta yake quri baice komai ba, ta buga wani uban tafi tace "Qaryar me qarya ma, wallahi qarya kake Abdulaziz" sai lokacin yace "I've made my mind Fatima, kuma hakan shine zai zamo maslaha a tsakaninmu" muryarta na rawa tace "Wallahi karyane, maslahan banza da wofi! In maslahan kake nema ka dauketa ka bada ita a 'yan'uwanka su riqeta mana, ka kaita gidan Abdulrazaq mana, sai kace zakamin kishiya akanta" tayi wani qwafa mai qarfi tace "Gaskiya ne, lallai Abdulaziz" kawai ta juya a zafafe ta fice daga falon yana bin ta da kallo.
A daren ranar ya fadawa Uwah decision dinda yayi making. Kawai sai ta tsaya kallonsa taqi cewa komai, ganin haka sai ya dan nusar da murya "Ina ganin hakan ne kawai zai kawo mana maslaha, Inason Fadwa ta taso cikin gatan da duk sauran yaran namu zasu samu, kuma Fatima is not making any effort regarding that" sai sannan Uwah ta gyada kai cikin gamsuwa dan kowa ya kwana da sanin haka a gidan, sai kuma tayi murmushi tace "Ita wannan da kake son aurowa Yar Ina ce haka?" Yace "Bamu dade da fara magana ba.Y'ar gidan Muhammad Shettima ce" sai tace "Sarki Muhammad Shettima na Borno?" Papa ya gyada kai a hankali yana kallon mahaifiyar tasa. Sauqe numfashi tayi sannan tace "Hakan duk ba laifi bane, kuma dan ka qaro aure shima ba laifi bane. Allah ya tabbatar da abunda yafi alkhairi, in har hakan kana ganin shi zai dinke barakar gidanka, na baka goyon baya dari bisa dari. Allah yayi jagora" ya amsa tareda miqewa zai fice ta bisa da kallo abubuwa dayawa na mata yawo arai. Abunda ta dade tana jirane Allah ya nuna mata, dan ba shakka wannan matar tasa abokiyar zama ce kawai zata dusasar da kaifinta, tayi wa Abdulaziz kaifi dayawa. Kuma wannan decision da yayi making ba qaramin sanyi ya mata a rai ba, hakan na nuni da cewar d'an nata ya fara tsayawa tsayin daka a sama da matar tasa. Hakan jarumta ce a gurinta.
Saida suka idar da sallahn isha, Papa ya tabbatar Mai martaba ya samu zama a sashen sa kamar ko wane dare sannan ya samesa da maganar. A nutse Dattijon ya sauraresa yana kuma fahimtarsa. Sai da Papa ya gama maganarsa sannan Mai martaba ya nusar da murya "Banqi taka ba, amma banason ka gina yaqin da bazai taba qarewa a tsakanin yarka da mai dakinka ba. Zaifi dacewa ka qaro aurenka a domin kana da niyyan hakan amma karka kafa wannan yarinyar da hujja alhalin bata san komai ba. Zaka rufe ta da wani shinge ne mai hatsari da batasan ta Ina mafarinsa yake ba in ta mallaki hankalin kanta a gaba. Hakan kuma bazai taba haifar muku da d'a mai ido ba acikin ahalinka" Papa ya gyada kai cike da alhinin furucin mahaifin nasa. Yasani shima hakan ba qaramin tsana zai jawowa Fadwan ba, amma babu yanda ya iya ne, bazai iya zuba ido ana cutar da yarinyar batareda ya dauki mataki ba. Ya daukota dan ya bata duk wani kulawan data rasa sannan ya samu lada, amma abubuwan da suke faruwa a yanzu, bashi da tabbacin in ya bari aka tafi a hakan zai cimma burin daya daga cikin abunda ya lissafo.
Cikin nutsuwa ya qara yin bayani ga mahaifin nasa. Sannan yasan a yanda Uwah ta karbi lamarin, ita zata sake tausasa masa Dattijon akan alamarin, dan bai manta ba alaqace mai kyau tsakanin mahaifin Binta da shi Mai martaban, kallon 'ya yake mata a koda yaushe. Amma sai Allah ya juya alamarin, dan bai bar sashen ba sai da suka fara maganan tsarinsa akan auren, nan ya fada masa bai son a dau lokaci.
Yaji sauqin nauyin zuciyarsa ganin yanda mahaifansa suka karbi alamarin, daya koma sashensa bai samu Momma anan ba kamar yanda ta sabar masa duk dare, kuma yasan za'ayi haka dan ya shiryawa duk wata fitinarta a wannan karon. Sai ya qara fita yaje sashen Twins dan wunin ranar tun safe ranbonsa dasu. A bakin part din nasu ya tsaya tareda gaisawa da dogarai biyun dake kula da gurin kamar ba basarake haka ya amsa gaisuwarsu, suka rinqa zubo masa kirari har ya shige. A Babban falon ya samesu bayan Laure ta zuba musu abinci da ta dafa musu ire ire daban sai wanda suka zaba. Imam na kwance a kujera yana zane a white sheet while Imran yana kallon Tv. Shigarsa Imran ya juyo yace "Papa barka da dare" yana murmushi ya qarasa tareda zama a kujera, Imam ya miqe zaune suka gaishesa ya amsa, again sai ya qara kai hannu ya dauki sheet dinda Imam din ke zane a cikinsa yana kallo a tsanake, yaso ya gane building din amma sai kansa ya kulle, sai ya kalli Imam din yace "What's this?" Imam ya dan matso suna kallo a tare sai ya kai yatsa yana nuna gurbin da bai gama sketching ba, yace "This has to go from here to the top" ya sake nuna wani gurbin "And from there, it goes straight to the outer layers of..." bai qarasa ba Papan ya sake kallonsa yace "Ina nufin building din Imam, Ina zan san outer or inner layers" ya qarasa maganan yana murmushi, sai Imam yayi murmushin shima sannan yace "It's JPMorgan Chase Tower" Papa ya dan hade girarsa in confusion da fari, sai can yace "Houston??" Imam ya gyada kai tareda kai hannunsa ya juya zaman sheet din a hannun Papa dan a kaikaice ya riqe ta shiyasa bai gane ba, aikuwa nan Papa yadan ware ido bayan ya fahimci zanen, sai ya sake juyawa ya kalli Imam din da mamaki, yace "Taya kas..." "How do you know it?" sai lokacin Imran yace "Papa you took us there, remember?" ya gyada kai yana sake kallon zanen. Har gobe baya jin zai daina mamakin abubuwan da Imam ke zanawa, it's just raw talent da Allah ya bawa yaron tun baije ko Ina a rayuwa ba. Sai ya sake cewa "But who taught you this?" Imam ya girgiza kai sannan yace "I just did it" shiru Papan yayi baice komai ba yana kallon d'an nasa. Anan part din yaci abinci tare dasu sannan ya tafi.
Har yazo kwanciya baiji shigowar Momma ba sai kawai ya tafi sashen nata. Yana shiga hadimanta suka fice duk suka bashi guri ya qarasa har bakin dakinta tareda tura kofar, amma sai ya jita a datse. Ahankali ya kwankwasa shima shiru bata amsa ba. Haka ya hakura ya nufi dakin da Fadwa take, nan ma Habiba ta fice ta bashi guri ya qarasa ciki, tana kwance acikin crib dinta amma batayi bacci ba dan ga feedernta nan akan wani stool Habiban ta ajiye alamun bata dade da bata madaran ba. A hankali ya sunkuya ya daukota sannan ya zauna a resting sofa dake dakin yana dan mata wasa da yatsansa a kumatunta tana kallonsa. Quri yayi yana kallonta cikin tausayawa, yarinyar abun tausayi ce, so vulnerable a hannunsa. Hamma tayi sai yakai hannu ya kare bakin nata da haka kuma idanunta suka fara lumshewa alamun bacci, sai ya danyi murmushi na sanin yawan baccinta. Madadin kuka sai yarinyar ta zamo me yawan bacci akai akai, maida ita yayi cikin crib dinta sannan ya lullubeta, saida ya mata addu'o'i sannan ya fice. Bai koma dakin Momman ba ya wuce bangarensa.
Paid Book 500
8134692758
Fatima Musa Maina Opay
Shaidar biya 08134692758
MURADIN ZUCI 📖
Bintu Musa
Chapter 11
Free page
Har garin Allah ya waye Momma bata rintsa ba, wani irin zafi da nauyi ta rinqa ji a zuciyarta kamar ana diga mata wuta. Babu abunda ke mata dadi a wannan lokacin, kuka kuwa ta yisa har ta gaji, ta kuma tsinewa jinjirar da duk ahalinta da suka ja mata wannan fitinar a gidan aurenta. Ita babu abunda yafi ci mata ranta irin wai akan yar tsintuwa za'a mata kishiya, akan yarinyar da ba'a san asalinta bama balle susan wacece ita. Indai haka ne toh tana jin har duniya ta nade babu ranar da zatazo Fadwa da abunda ya shafeta, bazata taba manta baqin cikin data qunsa ta dalilinta ba. Tun gari bai gama wayewa ba ta danna kira a Aina'u, a bugu na uku ta dauki kiran sai ta fashe da kuka me cin rai, hankalin Aina'un a tashe tace "Subhanallahi, Binta meya faru?" Momma bata bar kukan ba tace "Adda in nace banason yarinyar nan ko a gaba kar kowa ya kamani da laifi. Wallahi na tsani komai game da ita, ji nake kamar in kasheta in huta" da sauri Aina'u tace "Innalillahi, meya haka wai. Kanki daya kuwa, ki nutsu ki fadamin meya faru?" Cikin gunjin kuka tace "Wai akanta Abdulaziz yake ikirarin qaromin abokiyar zama, kishiya fa Adda, kuma wai akan yar tsintuwa" ta qarasa maganan wani kukan na zuwa mata da karfi. Shiru Aina'u tayi dan wannan batu ya daketa sosai itama, amma cikin dakewa tace "Binta kowa da irin kaddararsa a rayuwa, taki tazo a hakane sai ki zamo me karba ki godewa Allah, bawai kuma Ina bin bayan Abdulaziz bane, haqiqa dan kyautawa bai kyauta ba. Hakan da yayi kuma sake tabarbare lamuran yayi, duk da kema kinada naki kamashon kusan kashi saba'in acikin alamarin nan, na fada miki ki danne komai ki riqe yarinyar nan, ta hakan ne zaku samu maslaha tunda kin fahimci yanason yarinyar sosai, da ta hakan ne zaki qara janyo mijinki a jiki amma kikayi biris da maganata Binta, kika nuna ke kin isa kiyi yanda kike so babu mai tanqwaraki, Kinga irin kofar da kika bude yanzu ko, kinga irin matsalan da nake guje miki ko? Yanzu wa gari ya waya?" Momma ta share hawayenta cikin qunan zuci tace "Nida Yarana mun zamo abun banza agurinsa kenan? Kinason kicemin yar tsintuwar ta fimu a gurinsa kenan?" Aina'u tace "Ko daya, ni nasan bata fiku a gurinsa ba, amma laifinki anan shine. Tunda kikaga a karo na farko Abdulaziz bai bi ra'ayinki akan yarinyar nan ba sai ki sauqo ki karbeta, da shine zaman lafiyan naku, amma kika nuna naki taurin kan. Ta Ina kikaji ance Maza suna son macen da kullum tanason nuna ra'ayin ta ne abun fifiko akan nasu, Namiji ba'a masa