Chapter 5 Reading MURADIN ZUCI Zuciya Na Yaƙi A Sirri By Bintu Musa READ HAUSA Novels

MURADIN ZUCI Zuciya Na Yaƙi A Sirri By Bintu Musa

Author :  Bintu Musa Category :  African Stories & Novels

Chapter   5 / 9

12K to 15K   out of 25.8K words

my water broke" ya zare ido tareda juyawa ya kwala kiran Habiba da qarfinsa, aikuwa da gudunta ta qaraso dakin su Imam na biye da ita dalilin jiyo qarar da mahaifiyar tasu tayi, da sauri Habiban ta rufe kofa sanin zasu iya shigowa sannan ta qarasa da saurinta tafara riqe Momman dake fitar da numfashi, ga wani gumi da ya fara jiqata tun ba'a je ko Ina ba, atake Papa ya hau tambayanta in zata iya tashi, ta gyada kai dakyar alaman Eh sannan suka hau dagata shida Habiban dan ficewa da ita zuwa mota, dan a bayyane yake haihuwar ce tazo gadan gadan.

A wannan yanayin suka isa asibitin a inda tun kafin su qarasa da ita ciki nurses suka taho da gadon daukanta akayi ciki da ita Papan da Habiba na biye dasu, sai da aka shiga da ita labor room sannan Papa yace da Habiban ta koma gida dan kula da sauran yaran tunda an barsu su kadai. Ranan wuni Momma tayi tana labor, ta azabtu iya azabtuwa kafin ta haifo 'yarta kyakkyawa me kama da ita. Bayan an shiryata aka miqo wa Papa ita ya rungumeta a jikinsa kamar ya maida ita ciki dan murna. Sai bayan Momma ta huta sosai zuwa 9 na dare sannan ya kira can gida Nigeria, sunyi murna iya murna barin ma Anti Aina'u data fara tunanin zuwa, amma sanin itama tana dauke da nata cikin yasa Papa yace mata A'a ba sai ta zo ba, a inda ya tabbatar mata da kuma sauran 'yan'uwansa akan sunanan dawowa cikin sati uku dan zuwa America a wannan lokacin ba abu bane me sauqi. A washegarin ranan Papa ya koma gida ya taho da yaran nasa har da Habiban zuwa asibitin, ganin Momma da Baby ba qaramin farin ciki ya sanya 'ya'yan nasu ba, suka dauki jinjirar fuskokinsu cike da yalwan murmushi kamar basu suka ce sunason namiji ba. Hankalin Papa na kan Fadwa har Habiba ta sauqe ta daga goyen da take a bayanta, nan ya dauketa sannan ya hau tambayan ko ta bata madaranta, ta amsa da Eh a ladabce duk Momma na kallonsu.

Bayan shudewan wasu mintuna masu tsayi Ladan yayi sallama a dakin shida matarsa Zulaiha wadda yara ke kiranta da Mami, 'yar asalin Nigeria ce a inda ta kasance 'yar'uwa ga Ladan din ta fannin iyayensu har auren hadi ya shiga tsakninsu. Da fara'a suka qaraso sai Ladan ya dubi Momman yana mata sannu da jikin nata, sai Mami ta karbi jinjirar daga hannun Habiban sannan ta zauna a gefen gadon itama tana mata sannu sannan suka gaisa. Ladan kuma sai ya miqa hannu gurin Papa dake zaune a resting chair ya karbi Fadwa yana fadin "Kaga yarinya tayi wayo kamar ba ita ba" Papa na murmushi yace "Gaskiya, kullum qara wayo take" zama Ladan din yayi a gefensa sannan ya dan dunguri hancinta yana mata murmushi, kallonsa take qur da ido kamar ba jinjira ba sai kace mai haddace kamanninsa, bai bar murmushin ba yake kallonta sannan yace "An miki qanwa kema" Mami na kallonsu tace "Uhm, gaskiya ne" ta qarasa maganan tana juya kanta gurin Momma dake kallonsu Ladan din kawai. Sai da suka gama gaisawa bayan Ladan ya bada Fadwan ya karbi jinjirar shima yayi nasa addu'an sannan duk suka fice tare dasu Imam din kuma har sannan Fadwa na riqe a hannun Papa ya fitan, sai lokacin Mami tace da Momman "Ban taba ganin inda Iyaye suka fifita son dan wani akan nasu ba, kina ma da hakuri Maman Jidda" sai Habiba ta nufi toilet yin wani uzurin dan tasan kwanan zancen kuma, Momma ta dan gyara zamanta jin an sosa mata inda yake mata qaiqayi, tace "Hmm, kema kin ga abunda nake gani kullum ko" tace "Ai iya abunda na gani kadai ya isheni shaida Maman Jidda" ahankali Momma tace "Ashe dai bani kadai bace nake ganin rashin daidai a lamarin nan, Kinsan har hadani yayi da Anti Aina'u akan lamarin yarinyar nan, dan nace bazan riqeta ba" Mami tace "Haka Baban Kareem ya fadamin. A Ina aka taba yin hakan?. Tunda baki aminta da riqonta ba ai ba'a dole, bare ma D'an wani ai ba abun riqo bane sam, kar ma azo ga dan farin mutum da basu gaji da'a ba ko kadan" ran Momma na suya tace "Ina yin magana sai yace min tausayinta yake ji, akan ta babu irin maganan da baya ganin daman fada min, Idona fa ya kalla yace min ta zama 'yarsa da zatayi amfani da sunansa na matsayin ubanta sai inyi abunda zanyi, ki fadamin dan Allah ko dutse ne a qirjina bazan ji dacin hakan ba? A yanda Baban Jidda ya juya hali akan yarinyar nan shi yafi komai baqanta min rai, ba haka nasan mijina a baya ba Maman kareem, Yarima mutum ne da Idan nace banason abu to komin son da yake wa abunnan sai ya hakura dashi koda Uwah zata nuna baqin cikinta akai, ban taba tunanin akwai ranar da zatazo wai ni zai kalli Idona yace min 'Yayi abunda banaso din sai inyi abunda zanyi in na isa' Ni faaaa!" ta qarasa maganan hawayen na zuba mata tana sharesu, sai Mami ta kamo hannunta daya tace "Kiyi hakuri Maman Jidda, a gaskiya nuna miki cewan baki kai din ba shine mistake na farko da yayi, yarinya kuma dan kince bakyason riqeta babu mai miki dole ai" sai da ta gama share hawayen sannan tace "Maman Kareem ki bani shawaran yanda zanyi, wallahi Allah ne shaida banason yarinyar nan har raina kuma bazan taba sonta ba, da nayi tunanin harda hadin bakin mijinki aka daukota amma yanda Yarima ya juye gaba daya na tabbatar da ba sa hannun shi" sai Mami ta sauqe numfashi sannan ta girgiza kai "Ko daya wallahi Maman jidda, hasalima Baban Kareem ba yadda beyi dashi akan ya hakura da daukanta ba amma ya dage akan qudirinsa. Mijinki mutum ne mai addini sosai da sanyin hali ga kuma tausayi , kuma kiyi duba da irin gidan da ya fito, shiyasa hakan yayi tasiri sosai akan yarinyar. Amma kuma shi dan wani ba'a nuna masa so irin haka, duk inda akaje aka dawo nakan nan dai shine mai tausayinka" Jinjirar ce ta katsesu da kukanta sai Mamin ta miqa mata ita ta karba, sai da Momman ta dage riganta ta saka mata abincinta a baki ta karba sannan ta dago kai tace "Kinsan sau uku kawai ya dauki yarinyar nan, amma hankalinsa na kan waccan din ana kawota ya dauketa kina gani da ita ma ya fice riqe a hannu" sai Mamin ta dan tabe baki tace "Abunnan fa ke zakiyi tufka a lamarin tun wuri, ko sama da qasa za'a hada karki karbi yarinyar ko da kun koma can gida, zaki gani shida kansa zai bayar da ita riqo a wani gurin, ai saida kwanciyar hankalin matar gida ake samun nutsuwar tafiyar da kowanne lamura" Habiba da fitowanta daga toilet kenan sai ta dan tabe baki tana girgiza kai ganin yanda Mamin ke qara kunna wani wutar a zuciyar uwar dakin nata, amma babu halin ta kwabesu.

Da irin wa'ennan maganganun Mami ta rinqa qara ingiza zuciyar Momma akan lamarin, ta rinqa dorata a hanyar da kwata kwata babu mabulla acikinta sai tarin kurakurai, kasancewan daman Momman tana neman abokin kuka yasa taji dadin yanda Mami ta kalli lamarin a fuskar da take kallo itama, har saida likita tazo duba Momman sannan zancen nasu ya tsaidu wanda hakan ba qaramin dadi yayiwa Habiba ba, dan abune dake bayyane akwai rashin tausayi a lamarin nasu barin ma Momman saboda tun ranar farko da tace a maida yarinyar waje cikin sanyin ta bata tsoro matuqa. Sannan bata tashi yarda da rashin imanin uwar dakin nata ba sai da ta fara hanata kula da yarinyar qarfi da yaji, wanda ita batasan dame zata fasalta zuciyar Momman ba saboda duk wanda zeyiwa jinjiri dan kimanin satikai horon yunwa toh lallai rashin imanin yakai maqura.

Cikin kwanaki biyu da suka biyo baya aka sallamesu suka koma gida Habiba ta cigaba da kula da Momma sosai, sai ta tsiri goyon Fadwan akai akai ta yanda ko kitchen taje yin aiki zata kunceta ta bata madaranta, ko kuma inta shiga gyaran bandakin Momman nan ma ta sauqota ta wanke mata sayin da tayi, kuma taga nutsuwar hakan a idon Papan sosai dan burinsa shine yarinyar ta samu kulawan da ya dace daman. A kwanaki uku da suka sake biyo baya kuma yayi waya da Mai martaba a inda ya sanar dashi sunan da yake son a sakawa jinjirar, sanin cewa mahaifin nasa zai sa ayi yanka a 'yar tasa yasa yayi shiru bai kashe wayan ba bayan sun gama magana, jin haka sai dattijon nasa yace "Kana da wani abun fadi ne?" a ladabce yace "Ina neman alfarman a hada musu yankan ranka shi dade" dan shiru Mai martaba yayi da fari kafin yace "Ba damuwa". Da wannan Mahaifin nasa yasa akayi yankan raguna da shanukai akayi sadaka, a inda Yarinyar taci suna Khadijah, Fadwa kuma aka bar mata sunanta. Cikin sati uku da 'yan kwanakin da suka biyo baya wanda ya kama new year suka hau fara shirin komawa gida.

Paid book 500
8134692758
Fatima Musa Maina Opay
Shaidar biya: 8134692758




MURADIN ZUCI 📖
Bintu Musa


Chapter 08

Free page

Tun ana sauran kwana biyar su koma Nigeria Papa yasa Habiba hada kayan Fadwa tsaf acikin jibga jibgan akwatunan da ya siyo mata guda biyu. Dan kayan da ya siya mata zuwa wannan lokacin bazasu dauku cikin madauki daya ba saboda tarin yawansu, wuni biyu Habiba tayi tana hade kayan guri daya sannan ta hau killace na uwar dakin nata dana Baby Khadijah, su Imam kuwa sun riga da sun hada komai daman tun kafin zuwan wannan lokacin. Da Papa yaga yanda Mamma ta hada komai nata kamar wanda bazata dawo qasar ba saida yayi mata magana "Fatima bazaki bar wasu ba? I want us to return during fall (Autumn season), saboda akwai sauran ayyukan da ban gama kammalawa ba anan" batareda ta juyo ba tace "Ni dai na gama zaman qasar nan babu abunda zai dawo dani zuwa nan da September kuma, babu alkhairi ko na misqala zarratan acikinta, zaman cikinta bai qareni da komai ba sai guzirin baqin ciki" ta qarasa magana tana sake tula wasu sauran kayan cikin qaton box dinta, yana kallonta yace "Wane irin maganane wannan kuma, kinaji fa maganan aikina nake miki wanda dole zan buqaci iyalina a kusa dani saboda dogon zaman da zan dawo yi" sai sannan ta kallesa tace "Wallahi bazan sake takowa cikin qasar nan kwana kusa ba. Nasani gaba kuma ko 'yan biyu za'a ajiye mana a kofar gida" tsayawa kallon juna sukayi sai can ya girgiza kai sannan ya nufi crib din da Baby Khadija ke kwance aciki ya fara kokarin daukanta. Tana tsayen take kallonsa amma ganin bai kulata ba yasa tayi kwafa ta cigaba da jera kayanta tana ayyana yanda zata bullowa alamarin in sun koma.

Ana gobe zasu tafi su Ladan sukazo yi musu sallama tareda 'ya'yansu biyu wadda babbar suke kiranta da Kamila sai ma biyinta da shima ake kiransa Kareem wanda shekarunsa sukazo daidai danasu Imam. A wannan lokacin ma saida Mamin ta san yanda tayi ta dora Momman akan wasu maganganun da suka kebe a dakinta. Ladan kuwa da ya karbi Fadwan sai tausayinta shima ya kamasa na ganin za'a tafi da ita inda ko a mafarki batada wani hadi da mutanen dake rayuwa a qasar, can ya miqata ga Papan yace "Allah ya baku ladan riqonta ya kuma albarkaci rayuwarta da na 'yan'uwanta gaba daya" Papa ya amsa da Amin yana kallonta, dan a badini shima in aka tona zuciyarsa tausayin yarinyar yake ji a kullum, saboda har sannan bai cire rai da dawowar mahaifiyar ta ba, a kullum yana fatan suji sallamanta akan ta dawo karban yarta amma ya sani wannan mafarki ne da bai san ranar farkawansa ba.

Ranan da zasu tafi tunda sassafe Ladan din yazo sannan Papa ya kira musu Uber guda biyu, daya Ladan ya shiga dasu Imam harda Habiba dake goye da Fadwan, dayan kuma shi ya shiga tare da mai dakin tasa yana riqe da Khadijah suka tafi Airport. Isarsu basu dau wani lokaci ba yayi sallama na aminci da aminin nasa sannan jirginsu ya tashi. Wuni guda sukayi cur kafin suyi layover a Heathrow Airport -London na wasu qalilan din awanni sannan suka sake bin wani flight din da zai kaisu Lagos. Nan ma sai da suka kwana biyu a Lagos suna hutawa a Babban family house din su Papan sannan suka sake bin wani flight din zuwa Kanon Dabo, inda anan ne kuma zasu kai ga Masarautar Kumi dake garin Kano, babbar daula da karfin iko da dukiya yasa tayi qaurin suna a kaf fadin Nigeria a wannan lokacin. Sunan Masarautar Kumi babu lungu da sakon da bai zagaya ba tun a 18-hundreds har zuwa wannan qarnin da ake ciki, wanda sarki Abdulfatah yake jagorancin ta a wannan shekarun tareda 'ya'yansa maza guda hudu wanda uku suka fito daga dakin uwar gidansa mai suna Amina (wadda ake kira da Uwah) sannan guda daya kuma ya fito daga dakin Amaryarsa mai suna Aisha (wadda Allah yayiwa rasuwa shekaru biyu kenan) .
Sarki Abdulfatah dattijon mutum ne da ya kasance mai sanyi da dattako ta kowanne fanni, a inda wannan kyawawan dabi'un nasa suka sauqa har zuwa kan 'ya'yansa guda hudu da Allah ya basa, Abdulaziz (wato Papa) shi ya kasance na fari kuma Yarima mai jiran gado a wannan lokacin, sai na biyunsu Abdulrazaq da na ukunsu Abdulmalik sannan Abdulrahman da suke uba daya dashi kuma qaraminsu. Sanin hali da kuma irin tarbiyar da mahaifinsu ya tasosu dashi yasa Papa baiji shakku ko kadan akan daukan Fadwa ba. Hasalima yasani wannan shine hukunci mafi daidai da mahaifinsa zaiso ya yanke a wannan lokacin, shiyasa baya dana sani ko kadan akan daukanta kuma cike yake da yaqinin iyayensa zasu karbeta kamar yanda ya karbeta shima.

Auren Papa da Momma hadi ne na Allah a sanadin iyayensu a inda masarautu biyu suka hade ta fannin aure. Momma ta fito daga daular Kubaya da ke garin Bauchi, 'yar sarkin dake reigning a wannan lokacin shima, su uku mata suka fito a dakinsu, babbarsu Aina'u sai Binta da Khadija wadda suke kira Madina sai kuma babban yayansu daya kabiru . Kasancewarsu 'ya'yan mace ta biyu a gidan sai hakan yasa mahaifiyarsu ta zamo mace mai babban buri a rayuwa, dan daga Binta har Aina'u da ta kasance yayarta saida kowaccensu ta shiga gidan gani na fada, a inda Aina'u take auren hamshaqin mai kudi a Abuja wanda kuma ake juya qasar dashi a siyasance, sai ita Binta (wato Momma) dake auren dan sarkin Kumi mai jiran gado. Daula da tarin dukiya ta sarki Abdulfatah da 'ya'yansa yasa mahaifiyarta ta san yanda tayi ta tusawa mahaifin nasu aqidar auren har ta isa kunnen sarki Abdulfatah, wanda shima yayi farinciki da kuma amanna da kasantuwar hakan har auren ya qullu tsakanin 'ya'yan nasu. A farkon tarayyar aurensu Binta ta kasance mace mai duqar dakai ga mijinta kuma tayi kokari sosai wajen boye halayenta na badini amma akace hali zanen dutse, da tafiya ta fara nisa nan kuma Abdulaziz ya fara gane wace irin mace iyayen nasa suka aura masa ta fuskar halayya.

Haihuwarta na farko mai martaba ya sa aka musu cuku cukun visa suka tafi United States ta haihu acikin garin Houston, inda ta haifo 'ya'yanta biyu maza masu haiba, na farin daya fito a mintuna ashirin na farko aka saka masa suna Imam sai na biyunsa Imran. Ya'yan da suka fito cikin gata ta kowanne fanni na rayuwarsu, ta inda Imran ya dauko kamannin Papa gaba da baya harda duhun fatarsa sai kuma Imam ya dauko mahaifiyarsu ta fannin hasken fatarsa. Papa bai taba jin yana alfahari da Momma irin na wannan lokacin ba, dan wannan kyauta da Allah ya basa ta silar ta ba qaramin farin ciki hakan ya saka masa ba, ya kuma dauki damarar zama da jure kowanne hali da mai dakin tasa zata bijiro dasu ko agaba ne. Dan Adam da samun waje..sai ya kasance Momma batayi duba da hakuri da sanyi irin na mijinta ba gurin wanzar da zaman lafiya a tsakaninsu, sai tayi amfani da kyawawan mu'amalarsa a gareta gurin baje kolin duk wani fitinarta akansa, amma a dukkan mafari dole ya kasance da qarshensa, dan karo na farko tayi gamo da wani bangaren halayya daga mijin nata akan jinjira Fadwa, kuma a karo na farko ya fara taka mata burki akan halin da ta sabarwa kanta dasu. Amma kunaga wannan soyayyar da yake nunawa Fadwan a gurin matarsa ba wata wutar yake sake cinnawa a zuciyarta ba? Shin hakan zai fidda da mai ido kuwa?...

Ba miqaqqiyar tafiya bace a wannan labarin. Sai mun hau tudu da kwari dangane da labarin Fadwa acikin wannan babban gida na sarauta a inda zamu gani shin da gasken zata kasance daya daga cikinsu, ko kuma zata rayu ne a qarqashin kaddarar da ta barota da qasar haihuwarta?

-------

Ranan da jirginsu ya sauqa garin Kano da yammaci suka samu motoci har guda biyu suna jirar isowarsu dan kaisu gida kuma duk a qarqashin umarnin Mai martaba dan mutum ne da yake daukaka lamarin 'ya'yansa ta fuska me kyau wanda kowa ya shaida hakan, kar ma azo batun 'yan biyun jikokinsa da yake matuqar so. Duk wanda yake kwana ya kuma tashi acikin Masarautar nan yasan soyayyar dake tsakanin Mai martaba da jikokinsa biyun nan wanda hakan har ya taba mahaifiyar su, shiyasa duk fitinar Binta a gidan kusan tarin lokuta mai martaba yana kauda kansa ne dalilin wannan 'ya'yan nata guda biyu, duk yanda Uwah take kwana da abun a ranta haka take hakurin zama da matar dan nata mai shafaffen ido.

Sai yamma lis motarsu ta isa shimfideden gate din da zai shigar da mutum cikin tanqamemen gidan, a inda gidan Papa yake nesa da sashen mahaifan nasa, dan tafiya ce mai dan nisa da aqalla zata dauki mutum 15 minutes in yana tafe bisa kafa ba abun hawa ba.

5 / 9