Author : Bintu Musa Category : African Stories & Novels
taimaka miki ki kwanta?" nan ma ta girgiza kai bata ce komai, shiru sukayi sai can yayi qasa da murya yace "Fatima, yarinyar nan itama batada zabi akan abunda ya faru da ita" sai sannan ta dago kai tana kallonsa tace "Ni bance laifinta bane daman, kawai bazan riqe yarinyar da bansan asalinta bane, ya kawai daga ganin yarinya a yashe zaka dauko ka qaqabamin nima inaji da kaina" sai yayi murmushi tareda kamo hannunta yace "Haba mana Binta na, ai ba lallai sai ke zaki raine ta ba, ga hadimanki dayawa da duk abunda kikace shi zasuyi, Ina laifi in kin taimaki yarinyar da batada gata ayanzu sai na Allah da namu, ki tuna fa muma ba dabarar mu bane ya bar mana namu 'ya'yan cikin gata kuma a gaban mu" sai ta kwace hannunta tana hade fuska tace "Ni ka daina dangantamin yarana da irin wannan maganganun, kuma ai ba mu kadai bane mutanen da zamu iya riqeta, akwai orphanages dayawa ai" Papa na kallonta yace "Then..Menene makomar yarinyar kenan? what if.." kafin ya qarasa ta fara qoqarin gyara kwanciya tace "Ni kawai banaso, nace banaso ana dole ne? naji yau ta kwana a gidan amma zuwa gobe bazan lamunci zamanta a gidan nan ba" da haka ta kwanta ta juya masa baya yana kallonta, can ya sauqe numfashi ya miqe ya fice. Dakin twins ya tafi a upstairs dan tabbatar da ko sunyi bacci sai ya samu Imran nata munsharin bacci abunsa while Imam na zane a takarda anan zaune kan upper bunk dinsa dake saman na Imran din, murmushi Papa yayi yace "Imam bazaka bar zanen nan haka ba kayi bacci?" sai ya dago kansa, ahankali yace "Saura kadan" yace "No son, it's late..ka kwanta haka nan sai gobe ka qarasa" da haka ya qaraso bakin gadon ya fara tattare masa takardun, sai ya dago takarda guda daya yana gani a zuciyarsa yana mamakin baiwar yaron a kullum in yaga abubuwan da yake zanawa kala kala. Sai da ya tabbatar ya kwanta sannan ya nufi switch din dakin zai kashe wutan yaji Imam din yace "Papa, cikin ya daina mata ciwon?" sai ya juyo yace "You mean Fadwa?" ya gyada kai ahankali, sai Papa yayi murmushi yace "Eh ya daina har tayi bacci, now sleep....saida safe" da haka ya kashe wutan sannan ya fice tareda rufo musu kofan..
Tunda ya koma dakin kwanansu Momma bata juyo ta kallesa ba duk da idonta biyu har sannan, har ya gama shirin baccinsa yazo ya zauna a gefen gadon bata motsa ba kuma idanunta a bude tana kallon wall din dakin ta bashi baya, sai ya juyo yana kallonta yace "Kinyi bacci?" shiru tayi bata amsa ba, qasa qasa ya sake cewa "Ya cikin naki?" nan ma tayi shiru, ganin halin nata ne ya motsa yasashi kwanciya shima ya juya bayansa yana jin zafin hali irin na matar aurensa.
Bintu ✍️
Paid Book (500)
8134692758
Fatima Musa Maina Opay
Shaidar biya: 08134692758
MURADIN ZUCI📖
Bintu Musa ✍️
Chapter 03
Free page..
Washegari tun da lokacin sallahn asuba yayi Papa ya kwankwasa dakin su Habiban dan jin lafiyan yanda suka kwana. Bayan ta bude sai ta sunkuya ta fara gaisheshi cikin ladabi sannan ta fito daga dakin domin bashi guri, da ya amsa mata sai ya shiga cikin dakin direct ya nufi gadon inda Babyn ke kwance tareda Jidda, bacci ya samu tanayi kamar ba ita ta tada musu hankali jiya da kuka ba, sai ya maida towel din ya rufe tareda gyarawa Jidda duvet dinda take lullube itama sannan ya juya ya fice daga dakin. A falon ya tadda Habiban tana jiran fitowansa sai yace "Ya cikin nata?" kai a duqe tace "Da sauki, bata sake wani kukan ba ranka shi dade" ya gyada kai sannan ya nufi upstairs gurin 'yan samarin yaran nasu. Tare da twins din yayi sallah anan falon suna biye dashi ya jagoranci sallahn dalilin rashin yawaitan masallatai a kasar a wannan shekarun. Har Habiba ta gama hada breakfast Momma bata fito ba, da Papan ya leqata ya mata magana ma bata kulasa ba sai ya dawo dinning area din suka cigaba da cin abincin da yaransa wanda suma a daddare suka gaisa da mahaifiyar tasu a wannan safiyar.
Habiba dai ita take tsaka mai wuya, fushin Momma uwargijiyar tata take tsoro matuqa gashi tasan ko giyar wake tasha bazata tsallake maganar Papa ba. To wa ya isa ya tsallake magana ko umarnin Yarima mai jiran gado bayan sarki Abdulfatah, sahun giwa ne ya taka na raqumi shiyasa babu yanda ta iya ta amshi kulawan jinjirar ta hada da aikinta na kula da uwargijiyar ta da tazo yi takanas a qasar.
Da Papa ya shirya fita gurin aiki ne Habiban ta sake tuna masa batun tufafin Babyn sannan ya sake shiga dakin dan dubota, nan ma ya samu ta koma wani baccin bayan Habiba ta bata madaran tasha kadan. Duqawa yayi idonsa akanta zuciyarsa na qara karyewa, sai ya kai hannu ya kama qananun fingers dinta duk bata motsa ba, wani irin nauyi yaji zuciyarsa nayi akanta, what a cruel world! This beautiful innocent child didn't deserve this, wane mara imanin ne zai yasar da wannan yarinya?.. Da wannan maganganun zucin ya miqe cikin sanyin jiki sai twins suka shigo dakin Imran na gaba suka qaraso bakin gadon suna kallonta. Sai Imran ya hau gadon ya kai hannu yana taba fuskanta yace "Papa bacci take har yanzu?" ya gyada kai yanajin nauyin yin maganan kar suga gazawarsa, sai ya juya yana kallon Imam ganin ya tsaya dan nesa da gadon idonsa quri akan babyn baice komai ba, dan murmushi Papan yayi sannan yace "Daga nan zaka gaisa da ita kuma Imam?" sai ya girgiza kai ya qaraso bakin gadon amma bai hau ba, cikin nutsuwarsa da ta zame masa jiki dukda yarintarsa yace "Papa ya cikin nata?" sai Papan ya amsa da "Ta samu sauqin, gashi har baccin ta takeyi ma" ya gyada kai bai sake cewa komai ba sai Imran dinne yake wasa da hannunta suna magana da Papan, sai da suka dauki lokaci a dakin sannan suka fice while Papan yayi kiran Habiba dake wajen Momma, bayan ta fito a hanzarce yace mata "Kayan sakawa ne kadai ya saura acikin abubuwan da take da buqatan ko?" tace "Eh ranka shi dade, da dai mayukan yara irin wanda kuka siyo kwanaki da Gimbiya" ya gyada kai sannan ya dauki qaramar jakansa dake dauke da takardun da zai buqata a wajen aikin nasa sannan ya sake leqawa dakin matar tasa suyi sallama. Tana hakimce a bakin gadon hannunta riqe da plate Habiban ta kawo mata nata breakfast din, ganinsa yasa jidda baro gurin mahaifiyarta ta qaraso garesa tana maqalqale kafansa, sai yayi murmushi tareda shafa kanta yace "Where is my little pumpkin?" tana dariya tace "Mee Papa" da haka suka qarasa gurin Momman da idanunta ke kan plate din bata dago ba har sannan, saida ya zauna a kusa da ita ya umarci jidda da taje gurin yayunta sannan ya sake maida hankali gareta yace "How are you feeling?" a nutse tace "Na dauka samun 'yar tsintuwar yasa ka mantawa dani da kuma jininka dake jikina" madadin ya nuna haushin kalaman nata sai ya danne tareda dan yin murmushi yace "Jiya kadai dan ban bi abunda kikeso ba yaci ki zamo me fahimta ta Fatima, i thought ko bance ki kula da ita ba ke me jin tausayin tane, cikin sanyin nan akayi dumping dinta batareda tausayi ba, menene nata aciki, sannan menene laifi na dan na nemi kulawa da ita, ke kanki kin sani babu yanda za'ayi in fitar da yarinyar nan waje a jiya, in kaita Ina? Haba Fatima, Ina imaninki ya tafi?" sai lokacin ta dago kai tana kallonsa, nan hawaye suka fara taruwa mata a Idanu sannan tace "Wato dan na nemi kare mutuncin ka shine rashin imani, yarinyar da kana gani kasan 'yar qazanta ce, wane irin maganganu kake son jawo mana da mutuncin ka, daraja da kuma kimarka?" nan kuma ransa ya fara baci yace "Kina gurin ne da aka sameta ta hanyar qazantar, wai me yake damunki ne Fatima, da kike maganar kima da daraja kina tsammanin mahaifan nawa zasuyi alfahari da cewar na yardar da yarinyar ba tareda na bata shelter bane?" Tayi shiru bata basa amsa ba sai ya sake cewa "Zan zamo jagora bisa mulkin iyayena da kakanni da zan karbi ragama kuma ace tun yanzu bazan iya kwatanta jinqai ba me na zamo kenan? will you be proud of that man?" nan ma tayi shiru batace komai ba, sauqe numfashi yayi sai ya nutsar da muryarsa wannan karon cikin lallashi ya kuma fadin "Ki tayani mu samu ladanta koda na qanqanin lokaci ne Fatima, tunda baki amince da mu riqetan ba zan samo mafita tunda wannan ba qaramin case bane a qasar nan. But before that, please ki ban hadin kai mu kula da baiwar Allahn nan, gidaje dayawa acikin estate dinnan amma sai Allah ya kawota garemu, bamu san me ya boye a cikin lamarin nan ba" ta gyada kai nan ma bata amsa ba sannan ta cigaba da cin abincinta, ganin tayi shiru yasa shi yi mata sallama tareda miqewa ya nufi kofa ta bisa da kallo sannan ta dan tabe baki tana qara hade fuska.
Papa bai dawo gidan ba sai karfe sha daya na safen ya shigo gidan hannunsa niqi niqi da kaya. A dan gigice ya shigo falon sanadin jiyo kukan Fadwa da yayi tun kafin ya bude kofan, sai ya samu su Imam da Imran din tsaye a dan nesa da dakin da Fadwan ke kwance tana ta tsala ihu sun kasa shiga ciki. Da sauri ya ajiye kayan akan table sannan ya nufi dakin ya shiga nan ya sameta har fuskar nan tata tayi jaa abunka da farin fata, cikin hanzari ya dauketa dalilin wani irin tausayi da ta basa ya dorata a kafadansa ya hau jijjaga ta, baiwar Allah sai ta tsaida kukan ta fara ajiyan zuciya jin ta ajikin mutum, sai ya juyo yana kallon twins da suke kallonsa a bakin kofan, idon Imran tsuru tsuru dayake yafi dan'uwansa Imam din tsoro a tarin lokuta, da sauri yayi magana ganin yanda baban nasu ke kallonsu "Momma tace kar mu shiga" ya sake cewa "Imam ya shiga ta dakeshi" sai Papan ya kalli Imam din da ya sunkuyar da kai baice komai ba, da haka ya fito ya wucesu yana kiran Habiban, da saurinta ta fito daga dakin Momman tana sunkuyar da kai jikinta na dan rawa na sanin me tayi, amma kuma ba laifinta bane tunda itama uwar dakin nata ce ta umarceta da tayi mata wasu ayyukan tabar yarinyar, ganin yanda take a tsoracen sai Papa ya fahimci wani abu, ya fara kokarin danne bacin ran nasa yace "Ya kika barta tana kuka, bayan na bar miki kulawanta" da sauri tace "Ka gafarceni yallabai, hakan bazai sake faruwa ba" sai ya gyada kai tareda sauqo da Fadwan daga kafansa yana kallon yanda ta fara kokarin komawa bacci, ya miqota ga Habiban yace "Ki mata wanka, ga kayanta can na kawo, ki tabbatar ta qoshi sosai kafin ta koma baccin, banason abunda ya faru yau ya sake maimaituwa" jiki na bari Habiba ta amsa da "Kayi hakuri yallabai ka gafarceni, bazai sake faruwa ba" sannan ta miqe tareda karban Fadwan ta nufi dakin kwanan su da ita, da dan hanzari Imam ya dauki kayan da Papan ya siyo wa Fadwan yabi bayan Habiban Imran na biye dashi da wasu a hannu suka shige dakin dukansu. Sauke numfashi Papa yayi yanajin bacin ran abunda matar tasa ta aikata bayan ko awanni uku masu kyau ba'ayi ba ya gama neman alfarman tallafinta gurin kula da marainiyar Allah, sai ya girgiza kai kawai ya nufi dakin nata aransa yana tunanin yanda halinta ke sake banbanta a kullum sabanin yanda ya santa baya.
Sai 12 ya shirya tafiya wajen aikinsa bayan ya tabbatar da Fadwan ta samu kulawan da take buqata sannan yayi sallama da iyalinsa ya fice, bayan ya gamo ayyukansa wajen 4 o'clock bai koma gida ba ya nufi gidan Abokinsa me suna Ladan dake living anan Houston din shima da familynsa, dan zuwa sannan duk tunanin da zeyi yayi akan lamarin nan and it's all leading him to one option, shine dole ya bada jinjira nan ga child services, dole yayi reporting ga police, duk yanda yake son yarinyar da kuma son samun ladanta dole haka zai hakura saboda jalala irinta matar da Allah ya hadasa da ita.
Paid Book 500
8134692758
Fatima Musa Maina Opay
Shaidar biya: 08134692858
From the writer of KUNCIN ZUCI...And now
MURADIN ZUCI📖
Bintu Musa ✍️
Chapter 04
Free page
Papa bai dade ba ya isa gidan Abokin nasa mai suna Ladan, wanda ya kasance citizen din qasar dalilin iyayensa da suka kasance Nigerian immigrants and living in the united states for a long time, a yayinda kuma abota ta hadosa da Papa tun samartakarsu a sanadiyar degree dinsu da suka yi tare a makaranta daya.
Iso Ladan ya masa zuwa dan qaramin garden dinsa dake backyard na gidan suka zauna bisa kujeru na shan iska sannan matarsa mai suna Zulaiha ta kawo musu abun sha ta kuma gaisa da Papan. Sun dau lokaci suna hiran rayuwa da kuma businesses dinsu a inda Ladan din yace dashi "Kargi is high time ka fara tunanin expanding cooperation dinnan naku zuwa Atlanta, there's alot of business potentials there, inda ni nakeda irin privilege dinka na rayuwa da wuya in zauna a guri daya haka sai dai wani ikon Allah. Duniyar matsawa take da gudu yanzu. There will come a time that zuwa America zai zamo abu mafi sauqi ga mutane unlike yanda ake wahalar samun zuwa yanzu" sai Papa ya ajiye cup din hannunsa ya kallesa "Abunda nake ta tunani yanzu haka kenan, in sha Allah zanyi maganan da mai martaba sai muyi shawara, dan kaga yanzu hankalina yafi karkata ga haihuwan mai dakina tukunna, da kuma passport din Babyn, amma zamuyi hakan da yardar Allah" Ladan ya gyada kai cikin gamsuwa sannan yace "Hakane, Allah ya sauketa lafiya" ya amsa da Amin suka danyi shiru while nursing their drinks, can Papa yace "Ladan, nazo neman shawararka akan wani al'amari daya tunkaromu nida iyalina, nayi tunanin iya tunani amma kaina ya kulle akan ta yadda zan bullowa lamarin" nan Ladan ya dan gyara zama yana kallonsa, sai ya hau bashi labarin abubuwan da suka farun daga daren da aka ajiye musu babyn har zuwa wannan ranan, kafin ya gama maganan Ladan yace "Abdulaziz meyesa zaka saka kanka acikin irin wannan matsalan?" sai Papan ya dan hade gira yace "Bakaji me nace bane? Ce maka nayi fa har cikin compound aka ajiye mana ita, ya kakeso inyi? left her in this cold freezing weather?" Ladan ya sauqe numfashi yayi shiru na wasu sakkani tukunna, can yace "Ai lamarin qasar nan dinne, bakayi bama kamar jira suke balle issue irin haka ya faru? But you should've call the police Kargi, nan da Nigeria akwai banbancin mai matuqar yawa" Papa yace "Nasani, shiyasa nazo ka bani shawara ai, raina nason riqe yarinyar nan Ladan, wani irin protectiveness nake ji akanta banason ta fada wani mugun hannun wallahi, Inason riqeta in bata duk wani kulawan rayuwa ta yanda bazata rasa duk wani gatan da ake tunanin yara kamarta suke rashi ba" Ladan yace "Me matarka tace akan haka? ta amince da ku riqetan ne?" ya girgiza kai yace "A'a, as a matter of fact a ganinta na farko da yarinyar ta qi komai dangane da ita, can you believe har hana hadimarta kula da yarinyar tayi, haka na dawo gidan nasamu tanata kuka abun tausayi" sai Ladan yace "Toh kaga matsala ta farko kenan Kargi, dan wannan matsalace babba, the best idea shine ka bada yarinyar nan ga child services, tunda Fatima bataso babu ta yanda zaka taba jin dadin kula da yarinyar nan, Happy wife Happy home" Papa ya girgiza kai "Na dade bama fuskantar same angle nida Fatima, it's always the opposite Ladan, she never understands where I'm heading, yara irin wannan ba qaramin lada ake samu da riqonsu ba. Allah ya gani Ina tausayinta" sai Ladan yayi shiru yana kallonsa baice komai ba, ganin haka sai Papa yace "Amma tunda kaima hakan kace shikenan zan bada itan, addu'ana daya kar Allah yasa ta fada mugun hannun ko kuma ta taso cikin Christianity, Qasar nan ba ruwansu da wannan in suka tashi bada yaro, Allah ya dubeta duk inda take" a sanyaye Ladan ya amsa da Amin sannan suka koma wani batun daban.
Da wannan tunanin ya koma gida, amma abun mamaki yana dosar gidan nasa ya samu motoci biyu a fake a daidai bakin gate. A kallo na farko ya gane daya data kasance ta police daya kuma bazai shaida ta waye ba, duk yanda yakai ga taurin zuciya sai da yaji hantarsa ta kada, tunaninsa a wannan lokacin kodai neighbors dinsu sunsan me yake faruwa toh?. Da haka yayi parking a gefensu yana fitowa sai daya daga cikin polisawan ya qaraso garesa suka gaisa ya qara da "Sir, we need to have a few words with you" shima yace "Let's go inside then" da haka ya musu jagora zuwa cikin gidan suka shiga tare yana gaba.
A falo ya tadda Momma zaune kusada wata middle age woman wacce ke riqe da folders a hannunta tana nazarin bayanin da Momman ke mata, ta gefe dasu kuma Habiba ce tsaye riqe da Fadwan a hannunta ga twins tsaye a gefenta suma, sai bayan su Papan sun zazzauna matar ta kallesa ta fara magana cikin harshen turanci kamar haka "Matarka ta kira office dinmu akan yarinyar da aka ajiye muku jiya, shine muka zo saboda akwai buqatar zamu riqe yarinyar a hannun mu Mr. Kargi" sai police daya ya karbi maganan shima "Amma kafin nan munada buqatar muje station kayi cike cike, mun duba cameras na street dinku mun tabbatar ajiyeta akayi amma dole sai mun tafi dakai dan buqatar bayani daga bakinka" jiki a sanyaye Papa ya juya yana kallon Momma da taqi kallon idonsa, duk yanda yakai ga danne bacin