Chapter 3 Reading MURADIN ZUCI Zuciya Na Yaƙi A Sirri By Bintu Musa READ HAUSA Novels

MURADIN ZUCI Zuciya Na Yaƙi A Sirri By Bintu Musa

Author :  Bintu Musa Category :  African Stories & Novels

Chapter   3 / 9

6K to 9K   out of 25.8K words

ransa saida hakan ya bayyana akan fuskarsa, sai matar can din ta sake cewa "Ka fahimcemu Mr Kargi, bamu zo da tashin hankali ba aikin mu muka zo yi, yara irin wa'innan daman aikinmu ne na tabbatar da sun samu kulawan da suke buqata" nan Papa ya gyada kai ahankali, a turance yace "I understand...Miss??" tayi saurin cewa "Eva..It's Eva Hollaway, from Texas Department of Family and Protective services" ya gyada kai "Okay, Miss Eva..I understand" da haka suka mimmiqe sai ta juya tayi godiya a Momma da ta kirasun, a nutse ta amsa da "Thank you Miss Eva" Papa na kallonta, Har suka fice kuma taqi kallonshi sai sunkuyar da kai take tana wani ciccin magani.

Papa bai dauki wani dogon lokaci a station din ba ya gama cike ciken da ake buqata daga garesa, amma da aka nanu masa clip na record din matar da ta ajiye jinjirar sai da ya qame a zaune dan mamakin ganin motar da ta fito daga cikinta, kansa ne ya kulle ganin babu wani alamun talauci a tattare da matar duk da yanda ta rufe fuskarta, hasali ma irin motar da yake hawa tazo da ita sannan daga yanayin kayan da ya gani jikin yarinyar tun farkon ganinsa da ita ya shaida cewan duk inda ta fito babu talauci a ahalin. Anan suka sanar dashi plate numbern motan matar was not registered kwata kwata duk iya tracing din da sukayi, ya gyada kai cikin fahimta yana jin wani tausayin jinjirar na sake shigansa a wannan lokacin amma haka ya danne komai har ya gama abun suke buqata daga garesa a station din.
Kasancewan maghrib ta masa a nan din sai bai je social service office din ba, sukayi agreement da miss Eva dake tare dasu a station akan zai dawo washegarin ranan.

Fitowa sukayi a tare da ita tana riqe da Fadwan sannan ta nufi motan ta ta sakata suka tafi da ita yana kallonsu wanda hakan ba qaramin karya zuciyar sa ya sake yi ba. Ga tsananin bacin ran abunda matarsa ta masa wanda har sannan yana jin dacin rashin ganin mutuncinsa da batayi ba tayi abu gaban kanta batare da shawararsa ba, haka ya hadiye komai ya nemi taxin da zata kaisa gida. Da ya isa gidan yana bude falon Momma ta dago kai tana kallonsa sai ya dauke kansa ya nufi dakinsu dan yayi sallah, saida ya zo wucewa ta gabanta ta fara kokarin miqewa da kyar dan Habiba da twins basa falon, tana kallonsa tace "Baban Jidda i had to do what is safe for us, this is the only way and you're not making any effort to do so" sai ya juyo a nutse yace "Kinji nace wani abu ne?" tayi shiru tana kallonsa batace komai ba, ya juya tareda nufan dakin yana danne duk wani abunda ke taso masa a zuciya. Har suka zo kwanciya Papa baice mata qala game da abunda tayin ba, itama ganin haka sai taqi kulasa aganinta duk inda aka samu kwana biyu komai zai wuce, zasu dawo yanda suke a baya dan sanin da tayiwa mijin nata mai hakuri ne da kuma rashin riqe abu arai...Saidai abunda bata sani ba shine wannan karon tayi kuskure, ta kuma tura shi har zuwa maqurar da ya dau damarar nuna mata matsayinta na macen dake qarqashinsa.

The following day beyi qasa a gwiwa ba ya tafi office dinsu Eva da safe. Da isarsa ya fara neman izinin yaga Fadwan amma suka qi barinsa acewarsu hakan "It's not allowed" sai aka kaisa office din shugaban sashen a inda shima shugaban yayi kiran na qasa dashi a qaramin meeting room wanda a nan Papa ya sake musu bayanin duk abunda ya farun, bayan sun gama paperwork sai ya nemi magana da over roll shugaban nasu a office dinsa. Sanin co-operation companyn su Papan ba boyayye bane a Houston yasa shugaban bashi girman sa har da kawo masa ruwa amma bai sha ba, ya gyara zama tareda dan matsar da glass cup din gefe yace "What are the necessary requirements that I'll need to fulfill before adopting this child legally?".
Sai shugaban me suna Carl yace masa abune me sauqi tunda duk wani qualities din da ake nema na wanda zeyi adopting yaro shi Papan ya cikesu, kawai za'a bi legal paperwork ne for court approval amma kuma akwai abu guda daya, sai da consent din both married couple din which means sai lallai da amincewar ita Momman sannan za'a basu yarinyar, Jan aiki.
A farkon satin da ya fara going through process din ko bin ta kan Momman beyi ba ganin yanda ta manta da batun ma ta cigaba da rayuwar ta cikin kwanciyar hankali a gidan, duk yanda hankalin twins yake kan Fadwan more especially Imam haka ya danne in sun tambayesa inda take sai yace musu "Tananan lafiya". Habiba ma taji zafin uwargijiyar tata amma babu yanda ta iya balle tayi magana, haka ta cigaba da abunda ya kawota gidan tana ganin yanda Momman ta kama sabgoginta kamar ba uwa ba. Papa na iya kokarinsa na danne komai dukda tana ganin coldness dinsa lokaci lokaci dan abune da ya quduri niyya a ransa na sai ya bata mamaki akan abunda tayin. Zata sha mamakinsa matuqa.

A wani dare ya yanke shawaran kiran mahaifin sa dan sanar dashi duk da yasan ko bai fada masa ba abunda yake shirin yi din daidai ne. A lokacin da ya gama isar da bayanin nasa ta waya, sai Dattijon ya nutsar da muryarsa gurin cewa "Abu ne mai kyau hakan, kuma Allah zai muku jagora matuqar niyyarku akan yarinyar tsaftatacciya ce" yace "In sha Allah. Nagode, Allah ya qara girma" sai mahaifin nasa ya sake cewa "Mai dakin taka ce zata riqeta?" Ya amsa da "Muna shawara akan wannan din tukunna" sai yace "Yayi, Allah yayi albarka" ya amsa da Amin yanajin nauyin abun da yake shirin yi din na sauqa daga zuciyar sa.

Sati biyun da suka biyo baya ya cigaba da cukucukun adoption din tareda Eva kuma zuwa sannan suna barinsa yaga Fadwan in yaje office din nasu, atarin lokuta in aka kawo masa ita sai yaji kamar ya tafi gida da ita a lokacin, wani irin iko na ubangiji sai ya saka masa so da tausayin yarinyar matuqa aransa, da ita yake kwana arai most days saboda tunanin yanda batada kowa da kuma gata a wannan lokacin sai inda aka miqata. Da akazo batun lallai ana buqatan consent din Momma sai yayi confiding da Eva akan halin da yake ciki da me dakin nasa, itama taji ba dadi sosai amma cikin qarfafa gwiwa tace "Mr Kargi, Ina ganin soyayyar yarinyar nan a idanunka da kuma actions dinka, wanda hakan ya nuna min cewa Fadwa is safe with you, zata samu dukkannin gatan da muke fatan duk yaron da muka bada shi ya samu, abun da zakayi yanzu shine ka nemo qwararren lawyer da zai shige maka gaba akan hakan, Ina tabbatar maka da in process din ya tafi daidai ba sai matarka tayi signing komai ba zaka tafi gida da 'yarka" ta qarasa tana murmushin bashi qwarin gwiwa, godiya ya mata sosai yana jin dadin shawaran nata sannan ya bar office din. Da wannan Papa yayi wining case din a kotu a ranan Thursday, 15th of November. A yayinda qwararren lawyernsa da ya shige masa gaba ya jajirce sosai dan ba qaramin kudi ya zubar akan case din ba duk dan saboda suyi winning case din...And right there agaban su Ladan da sauran jama'an dake zaune cikin kotun Alkalin ya qaddamar da cewar Fadwa ta zama 'yarsa halak malak.

Paid Book 500
8134692758
Fatima Musa Maina Opay
Shaidar biya: 08134692758


MURADIN ZUCI 📖
Bintu Musa ✍️


Chapter 05

Free page


Bayan kwana biyu da gama zamansu na kotu sai department of child services din suka yi masa duk wasu cike cike na takardu da yake buqata akan Fadwan wanda bayan nan har asibiti sai da suka kaita tare dashi akayi mata duk wasu gwaje gwajen da ya kamata kuma Alhamdulillah sai results dinta suka fito "Disease free", ba qaramin dadi Papa ya ji ba more especially da ya ga genotype dinta was excellent. Da fari su Eva sun nemi zabinsa na canja mata sunanta in yanada buqatan hakan amma bai amince ba. Sai da akazo cike mata surname ya nemi su cire Kargi daga cikin sunanta su saka mata "Fadwa A. Abdulfatah" akan wasu dalilai nasa da bai bayyana musu ba, har Ladan dake zaune a gefensa sai da ya kallesa a wannan lokacin amma baice komai ba.

A kwana na uku.
Yana riqe da ita suka fito daga social service office din Eva na biye dasu, sai da suka qarasa ga motarsa sannan ya juyo ya fara godiya a Eva, tana murmushi tace "This child is lucky to have you, Mr Kargi" yayi murmushi "Thank you once again Miss Eva" da haka ya bude motan sai Ladan ya nemi yi masa rakiya sanin me zai tarar a gidan nasa, girgiza kai yayi yace masa "Ba damuwa, zan kiraka" ya qarasa maganan yana saka Fadwa acikin baby stroller da yayi attaching da car seat dinsa wanda takanas ya siyo guda biyu, daya nata dayan kuma na upcoming babyn da za'a haifa masa.
Bai dauki lokaci ba ya isa gidan sannan ya zagaya ya sake daukanta a hankali yana murmushi ganin yanda ko motsin tashi batayi daga baccinta. A compound din ya tadda su Imran na wasa da bingirar ruwa, Imran din na gudu Imam na biye dashi yana jiqashi suna dariya, ganin Papa da Baby hannu yasa suka nufesa da saurinsu, Imran yace "Papa, ka dawo mana da Fadwa?" ya gyada kai yana murmushi "She's back, as your sister" Imam yayi murmushi yafara kokarin karbanta sai Papan ya basa ita ya dora ta a kafadansa har da dan jijjagata kadan duk Papan na kallonsa, da haka kuma sannan suka shiga cikin gidan. Basu samu Momman a falon ba sai Habiba da take ta goge goge, tana ganinsa ta tsugunna suka gaisa sannan yace "Karbi yarinyar nan a mata wanka, akwai madaranta ko sai an siyo?" da sauri ta kalli hannun Imam ta kasa amsawa saida Papa ya sake maimaita maganan sannan ta amsa da "Eh ranka shi dade, akwai" da haka ta karbi Fadwan jiki a sanyaye tana hasko rikicin da za'a kwasa da uwardakinta.
Maganarta Dutse....Momma na zaune a bakin mirror'n ta Papa ya shigo dakin, ta juyo ta kallesa sau daya ta dauke kai dalilin har sannan suna 'yar sama sama da juna, amma ga mamakinta sai taga ya zauna a bakin gadonta yayi patting gefensa yace "Zo ki zauna zamuyi magana" asannu ta tashi sannan ta qaraso kusada shi din ta zauna. Saida suka dauki wasu mintuna sannan cikin nutsuwa ya fara jefa mata tambaya "Fatima, Inason ki fadamin ko da akwai abunda na rageki dashi a iya zamanmu?" sai ta kallesa tana hade fuska tace "Meya kawo wannan maganan kuma?" yace "Inason ki bani amsata" ta girgiza kai tana kawar da fuskanta, ya sake cewa "Akwai ta inda na sabo a zamanmu? ko ta furuci..ko kuma ta yanda nake mu'amalantarki da yasa kike yawan daukana ba'a komai ba" nan kuma ta dan ware ido tace "Ni yaushe na dauke ka ba ba'a komai ba?" "In akan maganan 'yar tsintuwar can ce yasa kake fadan hakan ai nayi abunda ya dace ne" cike da bacin rai yace "Kina nufin kin fini sanin abunda ya dace kenan Fatima?, ace Ina mijinki amma kullum maganata ce zata zamo abun tsallakewarki, abun takawarki yanda kika ga dama, a kullum ke sai kinyi qoqarin defying dina a duk abunda zance kenan" a zafafe itama tace "Ya Ina matarka zakace sai kayi forcing dina akan abunda banaso. Tun kawowar yarinyar nan gidan nan nace maka ka fitar da ita kaqi to ya kake so in maka in ban kira an fitar min da ita daga gidana ba" Papa baisan lokacin da ya miqe ba yana munata da yatsa yace "Baki isa ba Fatima, baki isa ki juyani yanda kika ga dama ba in kyaleki. Bamu gaji haka a gidanmu ba kuma baza'a fara daga kaina ba kina jina?" "Yarinya kuma gatacan na kawota gidan nan a matsayin 'yata halak malak sai inga abunda zakiyi. Ta zama 'yata da tayi taking sunana a bayan sunanta na matsayin ubanta sai in gani ko ni da ke waye yafi wani sanin abunda ya dace" da haka ya juya tareda ficewa a zafafe ya barta nan zaune bakin gadon a daskare.

Yana kaiwa tsakiyar falon yaji ta jawo hannun rigar sa da qarfi tana huci, ya juyo yana kallonta shima ransa na quna, cikin qwayar idanunsa take kallo tace "Wallahi bazan riqeta ba Abdulaziz, saidai ka zaba koni ko ita, kuma ayau ba gobe ba nakeson komawa gida na fasa haihuwa a qasar nan, ka maidani gida... ko zan haihu a jirgi yau bazan kwana a gidan nan yarinyar nan tana cikinsa ba" ta qarasa maganar qirjinta na hawa da sauqa. Shi mamakin qarfin halin ta ma yake matuqa, ace tana mace amma zuciyarta kamar ta mutanen fari wannan wace irin mace ce ita. A hankali ya zare hannunsa daga riqon da ta masa yace "Ba inda zakije daga gidan nan har sai kin haihu" sai kawai gani yayi ta nufi dakin da Fadwan ke kwance da hanzarinta kamar ba tsohon ciki ne a jikinta ba, ta tura kofar da qarfi tareda shigewa yabi bayanta da saurinsa, Imam ta samu a kusada Fadwan yana rainon ta kafin Habiban ta gama hado madaranta acan kitchen
A zafafe ta qarasa bakin gadon Papan yana qoqarin riqota amma kafin ta duqa ga Fadwan Imam yayi saurin yi mata rumfa akanta da nufin kareta, cikin bacin rai ta hau dukan bayansa Papa na riqeta tana fadin "Wallahi sai an fitar da ita daga gidan nan" bai tsaya sauraronta ba ya matsar da Imam din tareda daukan Fadwan zai fice daga dakin, sai kawai Momman ta fashe da kuka me qarfi tana fadin "Ni ka maidani gidanmu ni da abunda ke cikina tunda ka samu wadda ta fimu a wajenka" bai kulata ba ya fice daga dakin Imam yayi saurin bin bayansa suka nufi upstairs. Dakin boys din ya kaita ya ajiye ta a upper bunk din Imam dan Imran yayi bacci akan nasa, sannan ya juya ga Imam din yace "Ka kula da ita karta fado" ya gyada kai tareda hawa gadon, da haka Papan ya sake ficewa amma kuma sauqansa downstairs din sai bai samu matar tasa a dakin daya barta ba, ya juya zuwa dakinta tareda murda handle din amma yaji a kulle kuma yana jiyo kukanta acikin dakin. Habiba ce ta fito daga kitchen din jiki a sanyaye dan ta jiyo komai sai ya kalleta yace "Kije dakinsu Imam tana can, in kin bata sai ku dawo dakin naku" ahankali ta amsa da Toh sannan ta wuce saman ba kuzari. Har dare Momma taki bude dakinta ga Jidda ma ta tashi daga bacci tana kuka duk Papan na jiyosu amma ba yanda beyi da ita ta bude kofan ba taqi. Habiba ma tayi iya kwankwasawanta amma Momma tayi biris dasu, ganin har karfe takwas na dare bata bude ba yasa Papa dauko landline phone dinsu na gidan dan kiran mutum daya da yasan zata iya tankwara masa ita, duk da yasan tsakiyar dare ne acan gida Nigeria amma haka ya danna kira ga layin da yasan zai samu yayar matar tasa mai suna Aina'u. A bugu na biyu mijinta ya amsa kiran cikin muryarsa dake cike da bacci sai Papan ya bashi hakurin tashinsa da yayi, yace "Ba damuwa Yarima ai kafi haka, mai dakin ta samu sauqa kenan" anutse Papa yace "Har yanzu da sauran lokaci, na kiraka bisa wani uzurin ne daban" sai yace "Ina jinka Yarima" nan Papa ya fara masa bayani a nutse duk da yanda kira yake matuqar tsada a wannan lokacin bai dameshi ba, burinsa daya a wannan lokacin shine yanda zai seta barakar da ta fara kunnowa a gidansa. Sun dauki lokaci me tsaho suna magana wanda iya adadin kudin da suka bata a wannan kiran in aka baiwa wani faqirin zai iya fitar dashi daga talauci na har abada, amma Papa baibi ta kan wannan batun ba har saida ya tabbatar ya isar da duk maganganun da suke bakinsa ga Alhaji Saminu mijin Anty Aina'u, a inda daga qarshe shima ya miqa wayan ga Aina'un ta cigaba da magana dashi Papan.
Jim kadan da gama wayan nasu aka sake kira sai be dauka ba ya tafi daidai kofar dakin Momma yace "Fatima ki bude kofan nan ga Maman Kasim akan waya zakiyi magana da ita" shiru tayi daga farko bata kulasa ba har saida telephone din ta sake yin wani qaran alamun kira sannan ta murda key din kofan tareda miqo hannunta ya dora mata a tafin hannunta sannan ta maida kofan ta rufe.
Momma bata dauki kiran ba sai da ta sake zama a bakin gado, aikuwa tana dauka ta fara cin karo da maganan Anti Aina'u a zafafe "Meye hakan kuma kikeyi kamar wata qaramar yarinya Binta?" tana shirin yin wani hawayen tace "Amma kinsan dai bai kyautamin bako?" Aina'u tace "To dan bai kyauta miki ba shine zaki bi lamarin ta kulle kanki a daki, da kikaje kan yarinyar dukanta zakiyi ko me?" "Kefa bakida hankali wani lokacin wallahi, ai ta nanata miki magana amma yana bi ta bayan kunnenki, banda ma Yarima yana matuqar sonki ai da baku kawo iyar haka ba da wannan banzan halin naki, toh wallahi tun wuri ki dawo hayyacinki in ba so kike in kira Mama ba a goben nan, ke har Mai Martaba zan kira yasan abunda kikeyi tunda ke baki isa a miki magana kiji ba, ki na abu kamar bakya tuna inda kika fito, meyasa ke kullum sai anyi ta miki bita akan sha'anin zaman duniya ne wai?" nan kuma Momma ta fashe da kukan cin rai, jin wai har iyayenta za'a kira akan abunda aka mata dole tun fari, jin ta kasa magana yasa Aina'un cewa "Ki nutsu ki san me kike yi Binta, dan

3 / 9