Chapter 6 Reading MURADIN ZUCI Zuciya Na Yaƙi A Sirri By Bintu Musa READ HAUSA Novels

MURADIN ZUCI Zuciya Na Yaƙi A Sirri By Bintu Musa

Author :  Bintu Musa Category :  African Stories & Novels

Chapter   6 / 9

15K to 18K   out of 25.8K words

Gefe da babban building din su Papan kuma wani building ne da bai kai nasun ba amma ya tsaru shima iya tsaruwa sannan bana kowa bane face 'ya'yansu guda biyun nan, gini ne tsararre da Mai martaba yasa aka yisa musamman dansu ya kuma zuba hadimai masu kulawa da sashen, sai ya zamto Twins suna da nasu kebabben gidan wanda ko basu wuni acikinsa ba suna zuwa kwana acikinsa. A yammacin nan sun san sun dawo gida dan tun kafin aje ko'ina jama'a suka fara cincirindon zuwa sashensu, sanin za'a shigo dinne yasa tun wuri Papa ya ware daki daya dake cikin falo na farko na sashen Momman yasa Habiba kintsa kayan Fadwan anan, dayake suna da hadimai masu tarin yawa sai ya zamto ko Ina tsaf yake a gyare. Momma kuwa gaba tayi zuwa falonta na biyu kafin a dangana da makeken dakinta, sai ya kasance duk wa'inda suka shigo can falon nata suke isa dan Papa ficewa yayi zuwa nasa sashen daganan kuma ya wuce gurin Uwah.

A babban falonta ya sameta zaune da wasu qannenta da suke cousin suna magana, shigansa ya samu guri ya bisa kujera ya gaisa da mahaifiyar tasa, ta amsa da "Ma sha Allah, ya gajiyan hanya" yace "Alhamdulillah" sai ya juya ya gaishe da iyayen nasa dake zaune ta dayan sashen falon, daya da suke kira Baba Ladi tace "Sannunku da dawawo, kunsha zaman turai ba laifi" yayi murmushi kawai, sai ta sake cewa "Naji labarin har da wata 'yar ka dauko riqo daga can" yace "Eh Babah, Allah yayi ikonsa" kafin ta sake cewa komai Uwah ta katseta da fadin "Wato anan dai zakuyi gaisuwan barkan, ai kwa qarasa kuga 'ya'yan nasa" sukayi murmushi sai Baba Ladin tace "Zamuje Dada" ta kalli Papan tace "Allah ya taya riqo, ya bada ladan niyya, gaskiya kayi qoqari sosai" dayar ma tace "Sosai gaskiya, Allah yayi jagora" ya amsa da "Amin Amin". Sai da ya jira suka gama sauran maganganunsu da Uwah suka tafi sannan ya gyara zama sukayi sabuwar gaisuwa, nan da nan Hadimarta mai suna Laraba ta cika masa gabansa da kayan ciye ciye, yakai hannu ya dauki yankan kankana guda daya Uwahn tana kallonsa tace "Ya iyalin naka?" ya amsa da "Alhamdulillah, suna kintsawa ne" ta gyada kai sannan tace "Sai anjima zaka qarasa gurin Dattijon?" Yace "Eh yanada baqi yanzu" tace "Toh ba damuwa, anjima sai mu hadu acan din".

A daren kowa ya hallara a Babban Falon Mai martaba dake sashensa, wanda anan ne yake gudanar da duk wani taron da ya qunshi iyalinsa da 'yan'uwa. Momma na riqe da Khadija ta shigo Habiba na biye da ita a baya riqe da Fadwa a nannade cikin towel. Imam da Imran daman suna gefen Mai martaba an cika musu gabansu da kayan marmari shi kuma yana kishingide da hannunsa daya kan tum tum pillow irin na gidajen sarauta. Sanye Dattijon yake cikin alkyabba amma madadin rawani akansa sai ya zamto hulace da ta zanu da adon irin na alkyabban. Papa dake sanye cikin nashi kayan sarautar shima yana zaune tare da Abdulrazaq sannan Abdulrahman dan Abdulmalik baya qasar shima a lokacin yana matakin karatunsa na Phd a Manchester (England). Samun waje Momma tayi a gefen matar Abdulrazaq din mai suna Maimuna ta zauna. Cike da nutsuwa Mai martaba ya fara gudanar da taron da addu'a, sannan aka gaggaisa, Momma kanta a qasa ta gaishe da surukan nata sannan Mai martaba ya dan miqe zaune, ganin haka sai Abdulrahman ya miqe tsaye tareda nufan Momman ya karbi Khadijah sannan ya kaita ga mahaifin nasu, karbanta yayi yana kallonta fuskarsa dauke da murmushi yace "Ma sha Allah, Sannu Khadija" Uwah tayi murmushi tana kallon jikar tata itama, sai da ya mata addu'o'i sannan ya miqata ga Uwah itama ta sanya wa yarinyar albarka sannan ta miqata ga Uncles dinta suma, sai kuma yace "Ina baquwar tamu?" duk mutan falon sai da sukayi murmushi harda Papan, Uwah tace "Ai da ita ake tafe daman" nan da nan Habiba ta miqe tareda kai Fadwan gurin Uwah, ta karbeta tana kallonta sosai, kasancewan ko'ina da hasken wuta a falon sai ya zamto idonta tar yake a bude tana kallon kowa, nan da nan idon kowa ya koma kanta suna kallonta, Uwah na murmushi tace "Ma sha Allah, kaga yarinya kamar ita tayi kanta" Abdulrahman dake kallonta shima yace "Ma sha Allah" sai Momma ta dago kai tana kallonsu, da aka miqa Fadwan gurin Mai martaba ya karbeta sai yace "Tubarakallah wannan Idanu kamar daman da shirinta na aurena tazo" sai duk mutan falon suka dara banda Momma, Maimuna da kuma Habiba. Uwah tace "Ai kuwa bazan iya kishi da wannan ba, inaa" sai Momma ta juya tana kallon yarta dake riqe a hannun Abdulrahman din amma idonsa na kan Fadwa, ji tayi kamar ta miqe ta karbeta ta bar falon amma tasan ko giyar wake tasha bazata fara kwatanta yin hakan ba ko da wasa, sai ta gyara zama tana duqar dakai cikin qunar rai, wato dagasken dai 'yan'uwansa zasu goyi bayansa akan daukan yarinyar, lallai bataga ta zama ba, lallai ne tasan ta yanda zata bullowa al'amarin tun kafin dare ya mata.
Ta bangaren Papa kuwa fuskarsa cike take da fara'a a wannan lokacin, dadin ganin yanda ahalinsa suka karbi Fadwan ya sanya masa farin ciki matuqa arai. Da Mai martaba ya mata addu'a har dashi aka amsa a falon shima yana kallon diyar tasa da har sannan idonta ke bude. Sai da aka miqata ga su Abdulrazaq sannan Mai martaba ya fara nusar dasu gaba dayansu game da ita, ya musu nuni da yadda da kaddara da kuma taimako a rayuwa, cikin girmamawa mutan falon suke amsa nasihar tasa, a tausase ya sake cewa "Wannan yarinya ita irin tata kaddarar kenan a rayuwa. Mafi kyawun riqon da za'a mata shine a alaqanceta ta fuska me kyau. Fada mata abunda ya faru da ita ba daidai bane, Inason dukkaninku ku zamo masu rufe wannan al'amari. Ban yadda wani ya tona mata wannan sirri in ba dolen hakan ce ta faru ba" duk suka amsa har Momma da Papa.

Paid book 500
8134692758
Fatima Musa Maina Opay

Shaidar biya : 08134692758



MURADIN ZUCI📖
Bintu Musa


Chapter 09


Free Page


Bayan kwana biyar da dawowar su Papan ya fara shirye shiryen gagarumar walima na sunan 'ya'yan nasa. Zuwa sannan labari ya karade ko Ina acikin Masarautar da wajenta akan batun ya dauko 'yar riqo daga America, duk da har zuwa wannan lokacin ahalin gidan basu yarda an bude zancen na cewar tsintar yarinyar akayi ba, sai mutane suka dauki zancen akan Papa ya taho da yar riqo ne, amma sanin daga gurin waye dinne kuma kowa ya kasa fahimta, duk qwaqwai din 'yan gulma a dangi haka suka fara hakura, dan ko Momma haka taja bakinta tayi shiru akan Fadwa dan abunda take binnewa a zucyarta kadai ya isheta. Ana gobe hidiman ne 'yan'uwanta Aina'u da Madina suka iso daga Abuja suma. Kasancewan isowar dare sukayi nan da nan Papa ya aika driver aka daukosu, bai shigo sashen ba har saida suka huta suna cin abinci, cikin mutuntawa suka gaisa sannan ya juya tareda nufan kofa ya fita sai Momman ta dan bi bayansa da kallo fuskarta a dinke, ganin haka yasa Aina'u ta ajiye spoon din hannunta tace "Banason wannan abun da kikeyi Binta, a bayyane yake abun naki ya fara wuce gona da iri" sai Momman ta sauqe riganta data daga tana shayar da Khadijan, sai da ta ajiye ta a gefenta nan kan kujera sannan tace "Ni me nayi kuma Adda?" Madina ta kalli Aina'un itama ta dan tabe baki bata bar cin abincinta ba, sai Aina'un tace "Kin fini sanin abunda kikeyi ai, ke abu baya wucewa a gurinki ne wai?" caraf Madina tace "Fisabilillah sai kar ta nuna bacin ranta bayan an mata ba daidai ba" nan Momma ta kalli Madinan tace "Ai ita Adda a kullum ko me za'a min a gidan nan bata taba ganin laifinsu sai nawa, bayan kuma a ko da yaushe ni ake duka sannan a hanani kuka. Meye nawa dan nayi kishin soyayyar mijina da ta 'ya'yana?" Aina'u na kallonta tace "Wannan son zuciya ne kawai Binta, ba wani kishin soyayya, kina magana kamar wadda mijinta ya qauracewa gaba daya a rayuwa" tace "A yanda muka dauko wannan hanyar ni dashi daf muke da shiga wannan fannin, Adda wai ni zai nunawa 'yar tsintuwa ta fini da 'ya'yana a idonsa" rai a bace Madina tace "Toh wai ni meya hanaki rabasa da yarinyar tun a can ne?" Aina'u ta banka mata harara sannan tace "Banason irin haka Madina, kema watarana in kina abu kamar kanki a kunce" Momma tace "Ai gaskiya take fada nima da nawa sakacin kuma zan dauki mataki nan bada jimawa ba dan bana hada soyayyar mijina da kowa bayan 'ya'yana a gidannan wallahi, ko Uwah haka tayi hakuri ta barni, dan haka baza'a fifita d'an wani data kasance bare akan 'ya'yana kuma akan Idona sannan nayi shiru ba" Ainau tace "Yanzun har yaushe ma ya dauko yarinyar da zaki rinqa yin irin wannan maganganun? Grow up mana, it's high time ki rinqa tantance abunda ya dace da wanda be dace ba" tana kallon Yayartata ta wani hade fuska "Menene abunda bai dacen ba? Dan nace banason yarinyar?" Aina'u ta amsa da "Eh mana! Toh in kikace bakyason ta kina son kiga shima ya qi yarinyar ne, ya kike so yayi da yarinyar toh in ke baki jata a jikinki ba" Madina tace "it's obvious ai Adda, sai ya bada ita a wani wajen daban tunda matarsa bata so. Simple" Aina'u dake jin ranta na baci da qannen nata tace "Banason Ina magana kina saka min baki Madina, wannan raini ne kina jina? In bazaki tayani mu dorata akan hanya me kyau ba sai ki rufemin baki" sai Madinan ta juya kanta tana hade rai, can kuma ta ajiye spoon din hannunta ta miqe sai Momman tace mata "Me kikeyi har yanzu baki koma gidan ba?, aure da saura wata biyu" saida ta zauna akan kujeran dake kusa sannan tace "Sai nan da sati hudu zan koma, mitan Mama dayawa wallahi, komai sai tayi fada akai" Aina'u tace "Sai kace bamusan halinki ba" sai Madinan ta kalleta tace "Adda ki fito fili kice in bar miki gidanki kawai" tace "Meyasa zance ki bar gurina Madina, kema kinsan duk fadan da nake miki suna bayan soyayyar da nake miki ne" Momma tayi murmushi tace "Madina duniya, da sai ince to kizo nan muyi zaman mu kawai" Aina'u tayi saurin cewa "Ai saidai bayan Idona zaku zauna guri daya a irin wannan lokacin, sai ta zauna ta tayaki uzzirawa mijin naki kenan" sai duk suka fashe dariya Madina har da kyakyatawa, nan kuma twins suka shigo tareda Kasim da shima yake sa'ansu, Imran na ganin Madina ya fara murmushi sai ta daga masa hannu da nufin suyi shake tace "My boyyy" yana dariya ya miqa hannunsa sai Kasim kuma ya zauna a gefenta. Idon Aina'u na kan Imam tunda ya shigo har ya zauna a kujerar dake dan gefe dasu yayi kwanciyarsa dan daman sun gaisa tun zuwansu, sai tayi murmushi tace "Imamu ana nan da hali dai" Momma ta juya tana kallonsa itama, tace "Sai ki rasa me yake dannewa a cikinsa da bazai fitar ba, ayi mutum sai dan banzan zurfin ciki" sai ya juyo yana kallonsu bai ce komai ba, Aina'u ta sake yi masa wani murmushin tace "Kaci abinci?" ahankali ya amsa da "Eh" ta sake cewa "Me yake damunka?" sai gani sukayi ya dan yi murmushi tareda girgiza kansa, Madina na kallonsa tace "Allah ya baki daya Adda Binta" nan ya miqe tareda nufan gurinta yace "Kai Anti" ta dan turesa tana dariya tace "Ni ka matsa min daga nan jare, kana ganina ai ka dauke kai" bai fasa kwanciyan a gefen nata ba sai ta kyalesa ta cigaba da hiranta tareda su Imran da Kasim.
Can suna zaune daya daga cikin hadimar Momman ta shigo Mai suna Laure dalilin kiran da uwar dakin nasu ta mata, sai da Momma ta gama lissafo mata abubuwan da zata mata sannan ta kalli Yan uwan nata tace "A kawo muku ita ne?" Aina'u tace "Jinjirar?" ta gyada kai sai Madina tayi saurin cewa "Mezamu mata in mun gantan Adda?" Kafin Momman ta amsa sai Aina'un ta dubi Laure tace "Ki kawo ta kinji" da haka Lauren ta amsa a ladabce sannan ta juya ta fice. Bata dade ba ta dawo falon dan sanar musu an kaita gurin Uwah, Momma ta tabe baki batace komai ba ganin yaransu na zaune dasu agurin. Suna cikin hiran Aina'u ta miqe a sannu zata shiga dakin Momman, dan itama cikine a jikinta na wata shida,
Sai Maimuna ta shigo falon hannunta riqe da yarinyar ta mai suna Sajida dake da shekara daya da wasu watanni, komawa tayi ta zauna da fara'arta dan sun san juna kuma suna zumunci da juna a Abuja. Maimuna ta qaraso ta zauna sai Twins suka mimmiqe har Kasim din suka fice. Saida suka gama gaisawa sannan Maimuna tace "Anti Binta sai hakuri fa, naji maganganu na tashi akan lamarin yarinyar nan" Momma tace "Uhm, kuma babu yanda aka iya dani ba, masu maganan sai su karbi riqonta ai ba laifi" Aina'u ta dan dafa kafar Momman amma sai tayi biris zata cigaba da maganan, nan da nan Aina'u tace "Ai dama sha'ani irin haka sai an hada da hakuri" Madina ta gyara zama tana tabe baki a fakaice, dan itafa tun kafin ta ga yarinyar ma taji ta fita ranta sanadiyar matsalan da yayarta ke samu akanta. Maimuna bata bar sashen ba sai da Momma ta fada mata kusan duk abubuwan da suka faru tun a Houston, Aina'u dai miqewa tayi daga qarshe ta shige dakin Momman dan tayi uzurinta, dan in ta cigaba da zama tasan tsaf zasu hau sama su fado itada qannen nata, kuma agaban faccala.

Ansha hidima sosai dan 'yan uwan Momma sosai suka zo gurin taron daga Bauchi. Ganin yanda kowa in yazo yake tambayar jinjirar da aka taho da ita yasa Uwah ta aika hadimarta zuwa sashen su Momman aka taho mata da Fadwan dan ta matsar da ita daga idon mutane, dan har zuwa sannan idanuwanta a bude suke tana lura da yanda al'amuran yarinyar zai tafi a gidan d'an nata, saboda zuciyarta taqi aminta da cewar matarsa ta karbi yarinyar kamar yanda ya fada musu. Wunin ranar sai ya zamto ita ta kula da yarinyar da taimakon babbar hadimarta Laraba.
Har aka gama hidiman aka watse Momma bata nemi sanin inda aka kai Fadwan ba haka zalika ko da yan uwanta sun tambayeta inda Yarinyar take bata dogon zance akai.
Sai washegarin ranan su Aina'u suka fara shirin tafiya, sai da suka gama kintsawa tace da Madina "Muje muyi sallama da Uwah yanzu" da haka suka fito Babban falon sashen sai suka hadu da Papa da shima shigowarsa kenan tareda Abdulrahman a biye dashi, gaisawa sukayi dan rabonsu dashi tun daren da suka iso sai dai Momma taje sashensa sannan ta koma wajensu, sai gamuwar tasu tayi wuya. Da fara'arsa yace "Mun gode da hidima fa Maman Kasim" ya kalli Madina "Mungode Khadija" fuska a sake Aina'u tace "Ba komai mune da godiya, Allah ya raya zuri'a" yace "Amin, an kawo muku yar'uwartata kun ganta kuwa?" cike da waskewa tace "Eh mun ganta, Allah ya taya riqo ya bada lada", sai Papa ya amsa da "Amin summa Amin, ba dai ayau zaku koma ba" nan ma tace "Yau ne, zuwa anjima in Allah ya kaimu" sai yace "Okay Kamal zai kaiku" ya juya ga Abdulrahman dake bayansa yace "See to it please, yazo da wuri kar su jirashi" ya amsa da In sha Allah sannan su Aina'un sukayi godiya, Papan ya sake cewa "Agaishe da Honorable da Allah, mungode sosai" ta amsa sannan suka fice shikuma ya nufi nasa sashen. A falon Uwah suka sameta tareda wasu matan dattawa guda biyu, bayan sun gaisa aka kawo musu kayan ciye ciye sannan tace da Laraba ta dauko musu Fadwan. Da ta fito da yarinyar sai ya zamto Madina ce ta kusa da ita amma sai ta kafse taqi karbanta wanda yasa Aina'un miqa nata hannun da sauri ta karbi Fadwan dake nannade a towel tana bacci, da fara'a tace "Ma sha Allah, Uwah kinga yarinya tas da ita" fuska a sake Uwah tace "Sai Ma sha Allah" tace "Allah ya taya riqo yasa ta zamo cikon addinin muslinci" Matan ne suka riga Uwah amsawa sannan itama tace Amin tana lura da Madina da tace "Allah ya raya".

Bayan kwana biyu Uwah ta kira Papa zuwa sashenta da dare, ita kadai ya samu zaune riqe da Fadwan a hannunta tana jiran isowarsa, sai da suka gaisa sannan ta fara magana cikin nutsuwa "Ban kasance mai kai idanuna acikin gidanka ba sai wannan karon da yazama dole, da farko banyi niyyan saka hannuna a lamuran da suke tafiya da iyalinka ba amma gudun sai ta baci azo ana dana sani yasa zan yi magana" sai Papa yayi shiru yana sauraronta har ta sake gyara zama ta yi masa tambayan dake ranta tun dawowarsu qasar "Shin da amincewar matarka ka dauko marainiyar Allah'n nan kamar yanda ka fada mana?" da fari shiru Papa yayi sai kuma ya d'an sauqe numfashi sannan yace "Har yanzu muna fahimtan juna akai tukunna" sai itama tayi shiru tana kallonsa. Tasan za'ayi haka dan tun ranar zuwansu taga hakan shimfide a fuskar matarsa amma sai ta kawar da komai. Jin shirun nata yasa Papa yace "Babu matsala in Allah ya yarda, nasan zata kula da ita" sai ta dan hade fuska tace "Shine har aka gama waliman aka kwana biyu bata nemi yarinyar ba?, Yau kwana uku kenan jinjirar nan tana hannuna, ai ko ba komai sai ta biyo bayan 'yarta indai har ta karbeta a matsayin hakan" nan kuma Papa yayi shiru yanajin bacin rai na taso masa, ta sake cewa "Amma ba damuwa, yarinya dai in har riqonta zai zamo da mishkila sai ku bani ita in riqe

6 / 9