ZARAH Domin Soyayya da Adalci by Maryerm Mukhtar

Author :  Maryerm Mukhtar Category :  African Stories & Novels

Chapter   6 / 8

15K to 18K   out of 23.8K words

kubama zuciyarku Hakuri"

"Nasan zakiji labarin yarinyar da Faisal zai aura,Zarah kiyi hakuri ya zama dole Faisal ya Aureta sbd umarnin da inna ta bada kenan,kiyi hakuri ki zauna da ita da Amana"

Zarah ta share hawayen dake fuskarta tace"dady Auren Yah Faisal koda yana nufin bak'in ciki na ne?"

Dady yace"koda yana nufin mutuwarki ne"

Zarah tamike tashiga ciki tana kuka.


*AFTER ONE WEEK*
Zarah na dining tana had'a kayan breakfast,Faisal ya shigo,ta kalleshi tace"ina kwana,ya amsa tare da cewa Zarah"

Ta d'ago ta kalleshi,ganin yanda kullum zarah ke k'ara ramewa sai idanunta daketa fitowa waje,hancita ya kara fitowa sosai,Faisal yace"Zarah meke damunki?"

Tayi dariyar ta kaici tace"toh yanzu har sai an tambayeni damuwata,kai kanka damuwace gareni,ta sake kallanshi tace"wai yanzu yah Faisal zaka iya aurena da gaske?"

Kallonta ya tsaya yana yi,tayi murmushi tace"Yah Faisal karka cutar da kanka,nasani bawai sona kake ba,tunda bakaso kafiso na tsaya iya kanwarka toh kayi yak'i da wannan auren,dan babu farin ciki a tare dashi"

Kasaba gabatar dani matsayin kanwarka,amma lamarin na shirin canzawa,yanzu zaka iya kallona a matsayin matarka?"

Yayah Faisal kasan nauyin da kalmar mata ke d'auka,kana ganin ya dace dani ko da wadda kakeso?"

Faisal ya girgiza kai yace"Zarah wannan shine karo na farko kuma na karshe da zakimin irin wannan maganar,kenan yanzu Zarah ko cewa nayi ina sanki A'a zakice min?"

Zarah tace"Yah Faisal bakaji kai kanka yadda kace ba,ai bakayi maganar kana nufin da gaske bane ba"

Faisal yace"Zarah ki Tsaneni ki gujeni ki daina yadda muna had'uwa dake a cikin gidannan,Amma bazan ta'ba cema maamaah banasan auren mu"

Zarah tace"wannan shine abinda ka za'ba ko?"

Wayarshi tayi kara ya fiddo,Abin mamaki Sarah yaga tana kiranshi,ya d'auka tare da juyawa ya tafi.

Zarah kuma tacigaba da Aikinta.

Cen kuma Faisal yake cema Sarah meyasa bata d'aukar wayarshi?"tace duk sadda zai kira tana aiki ne,shiyasa yanzu ta kira ta bashi hakuri.

Bayan kwana biyu su zarah sunyi hutu, aka asa ranar Zarah da Faisal da Sarah.

Zarah duniya tayi mata zafi,tarasa ta ina zata fara ma kukan.

Shikam Faisal har sun d'an saba da Sarah,amma ya lura da tana da wata matsala guda,shine yawo,duk sadda zasuyi waya zatace bata gida.

Zarah kam kullum tana d'aki sai aikin kuka,ana saura sati biyu bikin su Zarah suka koma makaranta.


Yaune Zarah taga Maamaah tasa anata shigowa da akwatina masu yawa,da alama na lefe ne.


By:πŸ‘Œ
Maryerm Mukhtar
[9/17, 5:28 PM] Maamah: πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›
*ZARAH*
for loveβ™₯and justiceπŸŽ“
πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

*_We don't just entertain and educate, we touch the hearts of readers_*

P.m.l

96\100

Writeen By Maryerm Mukhtar

DEDICATION TO Maryerm Mukhtar Fans Group

*Wannan page na masoyan Zarah ne wayanda basa jin haushinta*πŸ˜„



Zarah na zaune a bakin bishiya tayi uban tagumi,Khairat tazo ta zauna tare da cewa"Zarah tunanin me kikeyi haka?"

Zarah tace"Khairat tunanin irin butulcin da nake nunawa nakeyi,Khairat tace"mekike nufi?"

Zarah Tayi murmushi tace"Khairat inna ta tasoni gaba,tasani sai wulaqanci nakeyi cikin gida,kinsan me tasani nayi wai in har ina so ta barni nasha ruwa?"

Khairat tace"A'a

Zarah ta kalli Khairat tace"tun daga ranar da aka gayamin cewa ni ba yar gidan bace,inna ta hanani zaman lfy,tace min idan har na aurar mata jika,toh wlh sai ta sanar da duniya wacece ni"

"Ce min tayi muddin banyi abinda maamaah da Daddy zasu hana auren nan ba,wai har makaranta zata zo ta tona min asiri,Khairat sai kace ni nai ma kaina haka,ta duk'ar da kai tana kuka tare da cewa"khairat da irin wannan rayuwar wlh gara na mutu"

Khairat tace"dan Allah Zarah kiyi hakuri,komi yayi farko yana da karshe wlh,Zarah ta share hawayenta tace"yanzu yah Faisal kallon butulu yake min,kuma bana fidda ran Daddy ma haka yake kallona,amma wlh khairat nayi Alkawarin sai na hukunta iyayena muddin nagano su"

Sun san basu da buk'atata suka haifeni basu kashe ni ba,Khairat tace"uhm Zarah kidaina wannan maganar,kowane bawa da irin k'addararshi"

Zarah tace"Khairat Babu wulaqanci da inna batasa nayi ma Yah Faisal ba,nagaya mashi magana duk wadda taimin dad'i"

"Khairat Bakiji yanda nakejin kunyar abinda nake aikatawa ba,na yadda banasan auren da za'a had'a"

"Amma ko daga gidanmu aka fara rashin halacci ya dace nayi abinda na aikata?"

Khairat tace"ya isa Zarah,ai Allah yaga zuciyarki,idan Faisal mijinki ne babu tsimi ba dubara,dan haka kisama zuciyarki hakuri"

Wajen 5:00 Zarah ta dawo daga makaranta tana shigowa gida taga kawayen Maamaah su uku suna duba kaya,akwatuna ne cikin falon cike da kaya.

Zarah ta gaishesu suka amsa da fara'a,Zarah ta wuce ciki tayi wanka tasa kaya marasa nauyi,tana zauna gefan gado tana d'aure gashinta.

Ganin duk ma yayi datti,yasa ta yanke shawarar zataje gyaran gashi gobe salon.

Tana zaune Meenah tashigo da gudu tana fad'in Zarah Amarya,Zarah ta d'ago cikin mamaki tace"Meenah kece?"

Meenah tace"hmm Zarah kina d'aki,sai kace wata tsohuwa,Zarah tayi murmushi tace"kai Meenah baki abin magana"

Meenah ta zauna tace"Zarah Amarya toh ina Angon yake?"

Zarah tayi murmushi tace"ke kin cika surutu,Meenah tace"Zarah wannan wace irin rama ce kikayi?"

Zarah tayi murmushi tace"karatu ne ya maidani haka,Meenah tace"Zarah nifa har yanzu gani nake wasa ne batun aurenki da Yah Faisal"

Zarah tace"haka kowa zai gani,Meenah tace"amma fa ke yar gidan maamaah ce,wance uban lefan da akayi maki,duk ke d'aya"

Zarah tace"kema in kinaso sai ki d'auka,Zarah tasake da cewa"Meenah yasu Aunty Faty?"

Tace"lfy qlau,ai cewa nayi nan zan taho wurinki,dukama Yah Faisal d'in baifi 4 days da zuwa kd d'in ba"

Zarah tace"ai dama kinyi zamanki can,dan nasan can zasuyi party,amma nikam babu abinda zanyi"

Meenah tace"tab wlh bazamu yadda ba,bikin Zarah guda,ace babu party,tab bari Yah Faisal yazo,Allah sai ya ware mana kud'i na daban"

Zarah tace"ke Meenah kefa kin iya surutu,kuma kinsan halinshi bayasan surutu,Meenah tace"kedai ki jira yazo mana"






By:πŸ‘Œ
Maryerm Mukhtar
[9/17, 5:28 PM] Maamah: πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›
*ZARAH*
for loveβ™₯and justiceπŸŽ“
πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

*_We don't just entertain and educate, we touch the hearts of readers_*

P.m.l

111\105

Writeen By Maryerm Mukhtar

DEDICATION TO Maryerm Mukhtar Fans Group

*Happy Birthday Aysha (Ummi Sarki)Dear Wish You All D best Of Life May Almighty Allah Shower His Blessing Upon u Now Nd Forever*😍

*Maryerm Mukhtar love you so much dear*πŸ˜„



Bayan an kira sallah magriba,Zarah tace"Meenah muje falo muyi kallo,Meenah tamik'e tare da cewa"yawwa kisamin firm mai dad'i"

Zarah tace"hmm damma kinzo bana cikin mood mai dad'i,da sai na baje maki firms d'ina kizab'a"

Suna zaune suna kallo Faisal ya shigo,basuma lura dashi ba,sai kamshin turarenshi da sukaji yana tashi,Meenah ta kalleshi tace"oh Yah Faisal ango,ai dama nasan wannan k'amshin turaren sai kai"

Yayi murmushi ya zauna,yace"Meenah yaushe kikazo?"tace"d'azu wlh nace bari nataho dan mufara shirye shiryen biki"

Faisal ya d'aga kai yana kallan Zarah yaga hankalinta baima wurin,kallo kawai takeyi,yace"yanzu ke Meenah ita amaryar batace tanaso ba,ai kinga kau babu party"


Meenah tace"kai Yah Faisal gsky bazamu yadda ba,party uku zamuyi,in aka had'a da dinner 4"

Faisal yace"toh naji kibari sai gobe idan kun yanke shawara keda sauran friends din nata,sai kumin magana"

Meenah tace"yawwa Yah Faisal,mik'ewa yayi ya fita,bayan ya fita Meenah tazunguro Zarah tare da cewa"ke yar rainin hankali,wato ke bazakiyi magana ba koh,sai ni uwar surutu"

Zarah tayi murmushi tace"toh ke kanki bakiji me kika ce ba,uwar surutu"

Sukayi dariya baki d'aya.

Washe gari da safe Zarah tana d'aki tana shirin makaranta,maamaah tashigo tace"Zarah gafa kayan lefanki bakizo kin gani ba tun jiya,Zarah tace"Maamah idan na dawo daga makaranta zan duba,Maamaah tace"gara dai idan kin dawo sai ki d'iba ki kai d'inki koh,Zarah tace toh maamaah"

K'arfe 2 Zarah tadawo daga makaranta,bayan taci abinci ta k'oshi,suna zaune d'aki Meenah nata danna phone d'inta.

Zarah tace"Meenah anjima da la'asar zamuje ki rakani na kai d'inkin kayana,Meenah tace"toh dan Allah daga can sai mu biya gidansu khairat koh"

Zarah tace"me zamuyi gidansu khairat kuma?"Meenah tace"kedai ki kaini magana zamuyi da ita ne,Zarah tace"toh shikenan gobe sai muje ki rakani salon"

Da la'asar Zarah ta shirya cikin black lace riga da skirt tayi masifar kyau,ko Meenah sai da ta yaba kwalliyar da Zarah tayi.

Sukafito waje dai dai zasu shiga mota sai ga Faisal,cikin farar shadda an mata aiki da bak'i,ya d'ago kai ya kalli Zarah ganin wani kyau da tayi mashi yasa yace"My dear irin wannan kyau haka"

Zarah taji kalmar wani iri saboda bai ta'ba kiranta da wannan sunan ba,Tayi murmushi.

Faisal yace"Ah gsky sai munyi pic irin kyan nan da kikayi,Meenah tace"Yah Faisal kawo phone d'inka in maku"

Ya mik'a mata,ya dafo mata kafad'a,Meenah ta d'auka,pic d'in yayi kyau sosai,Zarah duk kunyar duniya ta cika ta,cikin ranta tace"wai shi wannan mutumin bama yajin kunyar abinda yake yi"

Sukaje wuri wuri suka bada d'inki,daga cen suka wuce gidansu khairat,khairat taji dad'in ganinsu,sukayi magana kan party d'in da zasuyi.

Khairat tace"gobe da yake basu da lectures zataje ta fiddo anko na friends d'insu.

Washe gari Zarah sunfito zasuje salon,Maamaah tace"Zarah idan an gama maki salon d'in,ki wuce gidan matar nan mai gyaran jiki da gashi"

Munyi magana da ita,zata fara yi maki dilka,da turaren jiki,hatta gashinki zata ringa mashi turare har zuwa ranar bikin"

Zarah tace"toh maamaah.

Bayan sunfita Meenah ke cewa"uhm Zarah yar maamaah gyaran jiki da kai har na tsawon sati biyu,gsky ke yar gata ce"

Zarah tayi murmushi,cikin ranta tace"uhm kedai kawai ni kad'ai nasan yanda nakeji.

Meenah tace"Zarah zanso inga yaranku keda Yah Faisal,wai nasan kamar larabawa,ke kyau Yah Faisal kyau.

Ni nama rasa wanda zance yafi kyau,Zarah tace"nafishi kyau"

Meenah tace"ke wani lokacin sai inga kamar kin fishi,amma jiya da ya matso kusa dani sai naga kamar yafi ki kyau"



By;πŸ‘Œ
Maryerm Mukhtar
[9/17, 5:28 PM] Maamah: πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›
*ZARAH*
for loveβ™₯and justiceπŸŽ“
πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

*_We don't just entertain and educate, we touch the hearts of readers_*

P.m.l

106\110

Writeen by Maryerm Mukhtar

DEDICATION TO Maryerm Mukhtar Fans Group


*Kumin Afuwa Fans Dina ina Tunanin Zan Dakatar da Novel dinnan Sbd yan Matsaloli da Nake Samu Idan kuma da Rabon Zan cigaba da yin Book d'in Toh*

*Congratulation Aisha Garkuwa ina tayaki farin cikin kammala book dinki bandirawo Allah ya kara maki baseera Allah ubangiji ya kareki daga sharrin mai sharri Maryerm Mukhtar really love u so much*😘



Shirye shiryen biki kawai akeyi,kullum Zarah sai taje wurin Gyaran jiki.

Bayan kwana biyu,Zarah tafito daga wanka d'aure da towel jikinta,Meenah ta kalleta tace"Zarah gsky jikin ki yayi kyau,kinga har wani yellow kikeyi,Zarah tayi murmushi tace"Meenah ba dole ba,wannan kayan da ake shafamin ajiki"

Meenah tace"Zarah gashinki har shek'i yake yi,ke gaba d'aya ke kanki fatarki takama k'amshi,gsky ina ga idan zanyi aure nima nan zanzo tamin gyaran jiki"

Zarah ta zauna gaban madubi tana tsane ruwan dake fita daga kanta,Zarah tace"Meenah kinji yanda gashi na ke k'amshi,Meenah tace"ke dai bari,d'azu d'an kwalinki dana d'auka k'amshi kawai yake"

Zarah tagama shirinta cikin riga da skirt na Atamfa,ta zauna gefan gado tana amfani da laptop d'inta,Meenah tamik'e da sauri tare da cewa"ke Zarah yau ne fa zamu anso wasu daga cikin d'inkunan ki"

Zarah tace"eh haka ne, toh muje yanzu ko kuwa,Meenah tace"A'a muje yanzu daga nan har mubiya wurin mai k'unshi dazata maki kuma tayima friends d'inki"

Zarah tace"toh muje

Sukafito Falo,Meenah tace"wai ni rabon da inga Yah Faisal tun randa zamu kai d'inki,sati d'aya kenan"

Zarah tace"toh ai kinga tun safe yake tafiya aiki,bamu tashi ba lokacin,nima tun lokacin rabona dashi,amma naji maamaah tana cewa ya tafi kd yau"

Meenah tace"ya tafi wurin kishiyarki kenan,Zarah dai tayi shiru,Meenah tace"ke ina fata ba wannan duk'e duk'en kan zakije kina ma Yah Faisal d'in ba"

"Wlh sai kishiyarki ta k'wace shi,ke babu wani love da zaki nuna mashi sai jin kunya"

Zarah tace"ke Meenah Yah Faisal d'in zan nuna ma love?"Meenah tace"eh toh ba mijinki bane?"

Zarah ta girgiza kai tace"Allah ya sawak'e wlh,bazan iya ba,idan mijine ta rik'e nabar mata,Meenah tace"wai da gaske kike ko wasa?"

Zarah tace"kinga wasa a idona?"

Meenah tace"wlh muddin kikayi haka kin bani kunya,ai nayi zatan zaki yak'eta da surar da Allah yayi maki"

Zarah kalli kyanki,nifa na lura Yah Faisal mugun san yarinyar nan yake,saboda ji yanda yaketa zarya zuwa kd"

Zarah tace"toh ni karki ga laifina wlh,kigafa yanda nake da Yah Faisal,ke kinsan dole abubuwa sumin wahala"

Meenah tace"toh ke kika sani,idan kika saki wlh sai dai kizama yar kallo dan komi zaizo yafi k'arfinki"


Nan sukaje sukasha yawo wuri wuri,duk suka gaji,bayan sun dawo gida suna cin abinci Meenah ke cewa"Zarah wai yaushe kike gama karatu ne?"

Zarah tace"saura wata d'aya nagama degree d'ina akan low,amma kinsan sai naje nayi course d'in da mukeyi na wata shida"

Meenah tace"Ahh kice kin kusa zama original lawyer,Zarah tai dariya tace"toh da ban zama bane"

Meenah tace"toh amma Zarah lagos kukeyin course d'in kuma gashi zakiyi aure yanzu,Yah Faisal zai barki kije lagos kuwa?"

Zarah tace"toh ai idan banyi course d'in ba babu amfanin karatun da nayi"

Da daddare Zarah na zaune falo ita da Meenah da Maamaah,Daddy ya shigo fuskarshi d'auke da fara'a.

Maamaah tace"yau Alhaji naga kanata fara'a,yace"kedai bari,ina wannan abokin nawa?"wanda nace maki ta hanyarsu ake bada shcolarship,maamaah tace"eh nagane shi"

Daddy yace"toh shine yaba Zarah ta kardar shcolarship ta zuwa America tayo course d'inta na wata shidda"

Zarah farin ciki ya kamata,Maamaah tace"Ah to aikam gsky Zarah bazata amshi wannan shcolarship d'in ba"

"Ita da zatayi Aure,Daddy yace"A'a kibarta taje,ai aure baya hana karatu,bare auren ma nagida"

"Kibarta tafiya zatayi wlh,maamaah tace yaushe ne tafiyar?"

Daddy yace"nan da wata d'aya da rabi,maamaah tace"toh kenan da sabon auren Zarah zata tafi"

Daddy yace"eh mana dan kau bama zata tare ba sai ta dawo,ina so Zarah tazama cikakkar lawyer da k'ananan shekaru"



By:πŸ‘Œ
Maryerm Mukhtar
[9/17, 5:28 PM] Maamah: πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›
*ZARAH*
for loveβ™₯and justiceπŸŽ“
πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

*_We don't just entertain and educate, we touch the hearts of readers_*

P.m.l


111\115

Writeen by Maryerm Mukhtar

DEDICATION TO Maryerm Mukhtar Fans Group


Maamaah tace"toh amma da an bari Faisal ya dawo munji ta bakinshi koh,Daddy yace"Faisal ke iko damu ko muke iko dashi,Maamaah tace"toh Allah ya za'ba abinda yafi zama Alkhairi"

Ranar lahadi Faisal ya dawo daga kd,bayan sallar magriba Faisal ya shigo duk suna falo,maamaah tace"Faisal kaji batun tafiyar Zarah?"

Faisal cikin yana yi na mamaki yace"ina zataje?"maamaah tace"shcolarship babanku ya samo mata zata je ta America tayo wani course a cen"

Faisal ya kalli Zarah da fuskarta ta cika da jin dad'i,yace"maamaah yaushe ne tafiyar?"

Maamaah tace"nan da wata d'aya,bayan bikinka da sati d'aya,Faisal yace"toh kenan auren nada sati d'aya zata tafi?"

Maamaah tace"eh haka alhaji yace,amma kuma yace bama zata tare ba,sai ta dawo,course d'in na wata shidda ne"

Faisal yace"amma maamaah da anyi hakurin tafiyar nan,yanzu fa zatayi auren,idan kuma k'asar wajen akeso taje bayannan koni zan iya biya mata tatafi"

Maamaah tace"babanku bazai yadda ba,sai dai kayi hakuri,wata shidda kamar yau ne"

Maamaah tamik'e ta shiga ciki,Meenah ta kalli Zarah tace"ke Zarah naga alama dad'i makike ji koh"

Faisal yace"ba dole taji dad'i ba,tunda zata tafi tabar ganin dodo,ai nasan Zarah zataji dad'i,saboda zatayi nesa da dodo me cinye mutane"

"Amma ai bazama zatayi har abada a cen ba,zata dawo komin daren dad'ewa"

Faisal ya fice abinshi,Meenah tace"yanzu dan Allah bakiji kunyar abinda ya fad'i maki ba,wato yama gane gudunshi kikeyi"

Zarah tace"Meenah kar kiga laifina,kiga laifin inna da tasani ina gaya mashi maganganun da har yake tunanin gudunshi nakeyi"

Yau saura kwana biyar biki,Zarah ta kwantar da hankalinta yanzu,saboda tasan ba yanzu zata tare ba, suna ta shirye shiryen biki.


Yaune Zarah suke bikin Graduation d'insu,bata dawo gida ba sai 5,Zarah na cikin farin ciki sosai.


Yau labara,yau ne ake bridal shower d'in Zarah,tasa white dress tayi bala'in kyau,ko Faisal da ba ido da ido ya ganta ba,yana kd wurin sarah a pic ya ganta sai da yaga kyan da tayi.

Cen ma Sarah shi sukayi,amma da Faisal ya had'a pic d'insu wuri guda sai yaga Zarah tafi yin kyau.


Ranar alhamis akayi mothers day,Zarah ranar tayi kyau sosai,friday akayi kamu,amma babu event d'in da Faisal yazo,yana kd wurin Sarah suna shagalinsu cen.

Yau takama asabar,za'a d'aura auren gaba d'aya a cen kd,na Sarah aka fara d'aurawa,sannan na Zarah.

Kasan cewar aikin Faisal ya koma abuja,yasa a can zasu zauna,daga kd aka wuce da Sarah abuja,Faisal kuma ya dawo gida gab magriba.

Zarah sunata shirin yin dinner,yau ne Faisal zaije dinner da Zarah zasuyi.

Blue shiga Zarah tayi,tayi masifar kyau,Faisal ya kira phone d'in Zarah ya tambaye ta miye time d'in event d'in,amma sai ta gaya mashi wrong saboda bataso yaje.

Tace"karfe 10:30
bayan 9:00 dai dai aka fara event,wuri har ya cika anata shan music,Faisal ya iso,ganin party yayi nisa yasa ranshi ya 'baci ya gane Zarah wrong time ta bashi.



Bai tsaya ya shiga wurin ba,ya juya ya tafi,parking yayi a gefen titi yana mamakin abinda Zarah tamashi.



By:πŸ‘Œ
Maryerm Mukhtar
[9/17, 5:28 PM] Maamah: πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›
*ZARAH*
for loveβ™₯and justiceπŸŽ“
πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›πŸ›

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

*_We don't just entertain and educate, we touch the hearts of readers_*

P.m.l

116\120

Writeen By Maryerm Mukhtar

DEDICATION TO Maryerm Mukhtar Fans Group


Kusan 1hour yana tsaye gefan titi yana tunanin meyasa Zarah tamashi haka,cen kam karfe 11 suka tashi daga party,Faisal ya koma gida,bai tsaya shiga cikin gida ba saboda gidan cike yake,ya wuce d'aki.

Jin shigowar motoci yasa ya lek'o ta taga,Zarah ce tafito daga mota tana waya,Faisal yaga irin kyan da Zarah tayi,ba k'aramin burgeshi tayi ba,amma sai ya tuno da abinda tamashi,yayi sauri ya bud'e kofar d'akin ya fito.

Sunnan Zarah ya kira,tajuyo ya nufi inda take,yace"Zarah wai mike damunki?"menene a jikina wanda bakiso in cireshi"

Tace"Yah Faisal me kuma nayi,yace"look Zarah karki maida abin kamar bakisan menake nufi ba,Zarah saboda bakiso duniya tasan nine mijinki shiyasa kika bani wrong time,kika ce shine time d'in event"

Zarah tace"A'a Yah Faisal karka maida abinnan babba,naga kaima kd katafi wurin mtarka kukayi partyn ku,kuma ai kasan da cewa nima ina yin party a nan,tsawon kwana uku kana cen"

Toh naga bakazo wancen ukun da nayi ba,sai wannan na karshe,gara kawai insan bakazo ko d'aya ba"

"Ai dama abinda nake gudu kenan,nasan dama ga wadda kakeso danme za'a takura maka da batun aurena,zanga abu iri iri a zaman mu"

"Toh da yake Allah baya bacci,gashi ya b'ullo min da mafita,zantafi har na tsawon wata shidda,sai kusha amarci kaida ita,kuyi soyayyarku bamai hanaku"

Tajuya tatafi,Faisal da maganarta ta kashe mashi jiki,ya tsaya nan tsaya maganarta na mashi yawo a kunne.

Washe gari akayi walima,karfe 11:00 Faisal ya d'auki hanyar abuja.

Da daddare bayan kowa ya watse,daga Zarah sai Meenah,Zarah na kwance kan gado tana danna waya.

Meenah tace"Zarah da yanzu kina abuja kema,Zarah tace ai nagode ma Allah da wannan abin da ya faru,next week zantafi nima"

Meenah tace"amma naji ance bayan kwana biyu inna zata koma can gidan Yah Faisal da zama"

Zarah tace"toh ai dama nice bataso,tunda bana nan ai shikenan"


Washe gari
*Abuja*
Sarah ce kwance kan gado tana bacci,har k'arfe 11:00,Faisal ne ya shigo yana fad'in Sarah ki tashi hakanan,ta bud'e ido tana fad'in miye time?"

Yace"11:00 fa tayi,Sarah tace"wash wlh nai zatan 9:00 tamik'e tashigo toilet tayi wanka,tafito tasa kaya,Faisal na zaune gefan gado,Sarah ta kalli Faisal tace"bazamu d'an fita ba"

Faisal yace"haba wane irin fita

6 / 8