Author : Maryerm Mukhtar Category : African Stories & Novels
da ita.
A mota yasa ta suka nufi hospital,zarah ta bud'e ido ta ganta a hospital.
d'aga kai tayi taga wani rike da ita,ta mike zaune,kallanshi tayi tace"waye kai?"
Yayi murmushi sannan yace"kiyi shiru bari agama dubaki sai muyi mgn.
Bayan an dubata sunfito daga hospital d'in,suna tafiya kan hanya yake cewa"miye sunanki?"
Tace"Zarah
yayi mirmushi yace"toh ni kuma sunana abdul,nine wanda kukaje gidanmu keda faisal sadda ya d'aukoki daga makaranta.
Tace"toh amma ya akayi kagane ni?"yayi murmushi tare da cewa ya bazan ganeki ba.
Tace"toh dan allah ka kaini inda na bar motana,koda ya lalace sai nakai gyara.
Yace"toh bari muje.
Sukaje motan ba abinda ya sameta sai dai ta d'an lotsa,suka biya aka tada wurin abdul yayi parking motarshi ya tuka tata.
*Garin Abuja*
Najib ne kwance kan gado yana wani mahaukacin bacci,da kaga irin baccin kasan bana hankali bane.
Karar da wayarshi tayi yasa ya mike ya d'auka,bayan ya gama wayar,ya mike ya shigo toilet yayi wanka ya shirya cikin wata shiga kamar d'an yare.
Yafito falo bakowa ya nufi d'akin mahaifinshi ya shiga,wata jikka ba'ka ya bud'e cike take da kud'i dolars.
Ya d'auki kud'i masu yawa ya maida ya rufe,fitowa yayi daga d'akin tare da kwalama mai aikin gidan kira.
Mai aikin yazo,yace"kai bazan dawo gida ba yau,dan haka idan dady yazo yace nadawo kace eh.
Mai aikin yace"toh
Ya fita ya shiga mota da gudu yazo bakin gate,ya kira mai gadin yace"idan dady ya dawo ya tambaya na dawo kace eh sbd yau ba gida zan kwana ba,idan kuma kace ban dawo ba wlh abakin aikinka.
*Garin Kaduna*
Wurin cike yake da manyan mutane dagani kasan babban taro ne na manya mutane,wata matace tashigo wurin wadda bata wuce shekara 35 ba.
Kyakywa ce sosai,duk wanda ya ganta yasan tayi kyau koda tana budurwa,bayan ta isa mazauninta ne,tamike tana gabatar da kanta.
Garin kano
Akan hanyar komawar su zarah gida,abdul ya duba time tare da cewa kai,time yayi,zarah tace"time din me?" yayi murmushi tare da cewa za'ayi fira da Haj.RAHAMA SHEHU agidan radio d'in kaduna.
Zarah tace"wacece ita?"yace bakisanta ba?"tace"eh
Yace"ita ce shugabar ilimi ta mata agarin kaduna.
By:π
Maryerm Mukhtar
[9/17, 5:27 PM] Maamah: ππππππππ
*ZARAH*
for loveβ₯and justiceπ
ππππππππ
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*_We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_*
P.m.l
51\55
Writeen by Maryerm Mukhtar
DEDICATION TO MARYERM MUKHTAR FANS GROUP
Tace"toh bari nima na saurari firan nata,har suka isa ba agama firar ba,yayi parking a kofar gidan su zarah ya fito daga motar yace"toh zarah ga key d'inki allah ya kara sauki koh"
Tayi murmushi ta amsa tare da cewa ngd,yace"bakomi"
Har zaitafi ya juyo yace"uhmm zarah pls kibani no d'inki, tace toh nan ta rubuta mashi ya tafi,mai gadin ya bud'e tashiga da motar.
Zarah tashiga gida bakowa falon ta wuce d'aki tayi alwalla tayi sallah,tafito falo again ba kowa d'akin maamah tashiga ta tarar tana sallah,tafito ta dawo falo.
Tana zaune faisal ya shigo,kallonta yayi yace"zarah meya sameki a goshi?"
Ta d'aure fuska tare da cewa bugewa nayi,yace"nasan wurin rashin jinki kikaji wannan ciwon"
Bata dai bashi amsa ba taciga da kallanta,maamaah tafito ta kalli zarah tace"zarah meyasa kika fitar min da mota?"
Zarah tace"maamah wlh kayan makeup d'ina suka kare,nace yah faisal ya kaini ya k'iya,toh shine na d'auki motarki nafita da ita.
Maamaah tace"zarah bakifa iya driven ba sosai,maamah tasake da cewa me yaji maki ciwo?"
Zarah tace"bugewa nayi ne"
Nan maamah tama faisal magana kan kin kaita da yayi, shigowar dady suka tsaya da maganar,nan dady ke cewa gobe inna(mamanshi) zatazo"
Gaban maamaah ya fad'i tace"gobe?"
Dady yace"eh haka tace"
*Washe gari*
Zarah tatafi makaranta bayan sunfito daga lectures ne phone dinta tayi ringing,ta d'auka muryar abdul taji bayan sun gaisa yake cewa dama ya kirata yaji ya jikin nata,tace"da sauki sosai"
Zarah karfe 6:00 ta dawo gida inna na falo zaune,suna fira da maamaah.
Zarah tashigo ta kalli inna tace"inna ina yini"
Inna ta amsa ba yabo ba fallasa,zarah tamike tashiga ciki.
Bayan tayi sallar magriba tafito falo kitchen tashiga,ta d'auko lemu ta zauna kan dining tana sha.
Inna dake can falo tace"ke zara'u zo nan,zarah taje tace"gani inna.
Tace"d'aukomin lemun da kika sha,zarah taje ta d'auko lemun ta kawo ma inna.
Inna ta fizge tare da cewa haka kuke ma d'ana asarar kaya,yanzu tunda nazo gidannan banga faisal ya d'auki wani abu yasha ba sai ke"
Zarah tace"inna wlh yunwa nakeji,daga makaranta na dawo shiyasa"
Inna tace"oho rashin kunya zaki mani,ai dama idan bare ya samu wuri iskanci iri iri"
Muryar maamaah sukaji tana cewa"zarah zokitafi d'aki,zarah tajuyo tashige d'aki.
Maamah ta matso kusa da inna tace"haba inna ya kike shirin fiddo abinda muka rufe shekara da shekaru,inna tace"eh dole kice haka mana,dan wlh na lura ke kinma fison wannan zarah akan faisal"
Zarah da tashiga d'aki ta zauna tana tunanin wai meyasa inna take mata haka,sai kace ba kakarta ba,zarah tace"toh amma ai bata yima faisal haka"
Nan zarah taita tunanin zuci,washe gari zarah bataje makaranta ba,suna zaune kan dining zarah tafito.
Ta kalli inna tace"ina kwana,inna ta amsa cikin fushi,zarah ta gaishe da maamah da faisal.
Zama tayi,maamah tace"zarah me zakici?"
Zarah tace"maamah ni tea kawai zanshi,amma idan ansoya doya zanci"
Maamaah tace"ba'a soya ba amma bari nasa amaki,faisal yace"maamah nikam gobe k'osai nakeso amana"
Zarah tace"kai yah faisal wlh bana san k'osai,mudai gsky kar amana shi"
Inna tace"ke wlh kifta idona, faisal zai ce yana san abu kice bakyaso, tsaranki ne?"
Zarah dai tayi shiru tana kallan inna.
Inna tace"toh k'osan za'ayi gobe,kuma yanzu doyar da za'a soya maki wlh baza'ayi ba.
"Idan bakyaci ki bari,zarah ta turo baki tare da mikewa tatafi,inna tace"yal banza dole kiyi iskanci tunda kin samu wuri"
Faisal yace"inna meyasa kikema zarah haka?"inna tace ba ruwanka rabu dani"
Faisal ya mike ya tafi,maamah tamike tare da cewa ni gsky inna bakimin yanda nakeso,ya zaki ringa nuna banbanci a tsakanin yaran nan"
Inna tace"sbd faisal jika na ne,zarah kuma tsintatta ce"
Muryar faisal sukaji yace"tsintatta kuma?"
By:π
Maryerm Mukhtar
[9/17, 5:27 PM] Maamah: ππππππππ
*ZARAH*
for loveβ₯and justiceπ
ππππππππ
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*_We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_*
P.m.l
56\60
Writeen by Maryerm Mukhtar
DEDICATION TO MARYERM MUKHTAR FANS GROUP
*Amin afuwa rashin post din da banyi ba jiya*ππ
*Wannan page nakine ke ta da bance fatima naseer mss tieyeimah allah ubangiji ya barmu tare ina kaunarki sosai*β₯
*Congratulation Aunty Kausar(kausar love) allah ubangiji ya albarkaci aurenki allah yasa gidanki ne na har abada allah ya baku zaman lfy na tayaki murna sosai*πππ
*Ina mika taza'ayyata gareki feedo deedoh allah ya jikan mahaifyarki yasa ta huta allah yasa can tafi nan allah ya kara baku hakurin rashinta*
Maamah tace"faisal wuce kabamu wuri,yace"toh maamah naji inna tana cema zarah wai tsintatta,maamah tace"ba mgnr zarah muke ba wuce katafi"
Faisal yace"dama wayata na mance nazo na d'auka,maamah ta mik'a mashi ya tafi.
Duk yinin ranar zarah na d'aki kwance,ringing d'in wayarta ya dawo da ita,ta d'auka muryar khairat taji tana cewa zarah gani a kofar gidanku,zarah tace"da gske khairat ko wasa?"
Khairat tace"Wlh da gaske.
Zarah tamike tafito inna na zaune sai d'aure fuska take,zarah tafita.
Shigowa sukayi tare da khairat,har zasu wuce zarah tace"khairat muje ki gaishe da granny d'ina"
Suka matsa khairat tace"ina yini,inna ta amsa ba yabo ba fallasa.
Ciki suka shiga,bayan kamar minti 10 zarah tace"khairat bari inzo,tamike ta tafito.
Kitchen tashiga ta d'auko lemu da ruwa tare da cups tafito zata wuce,inna tace"ke zara ina zaki dasu?"
Zarah tace"inna bakuwa nayi zan kai mata,inna tace"toh maida lemun ki kai mata ruwa ai ya isheta,zarah ta juya ta maida lemun tashiga ta kaima khairat ruwan.
Wajen 1:00 khairat tafito zata tafi,zarah tashiga da khairat d'akin maamah dan su gaisa,maamah na zaune bisa abin sallah.
Khairat ta gaishe da ita,tafito zata tafi maamah ta d'auko kud'i taba khairta suka fito.
Bayan zarah ta dawo daga raka khairat tashigo falo ta tadda faisal zaune shida inna suna fira.
Har zata wuce faisal yace"zarah an gama abinci ne?"
Tace"bari na duba.
Tashiga ta tadda angama had'a komi,tazo tace"yah faisal angama.
Zata wuce"inna tace ke zara'u anjima zaki min wanki kayana dana sa jiya sunyi datti,faisal ya d'ago kai yace"wanki kuma inna?"
Tace"eh ko bazatayi bane?"yace"amma inna ai naga zarah bata iya wanki ba,inna tace"faisal wlh zan kwad'a maka mari,ni zance ga yanda za'ayi kace bahaka ba"
Zarah tace"yah hakuri inna zan wanke maki,inna tace"kice ma bazaki wanke ba kigani"
Zarah tashiga ciki tana hawaye,faisal ya mike ya fita.
Da la'asar bayan zarah tagama sallah tayi wanka,tana zaune d'aki murja tazo tace inna na kiranta.
Tafito inna na tsaye a falo,ta kalli zarah tace"ga kayan ce kije can bayan gida ki wanke mani,zarah ta nufi hanyar waje.
Kayan kala biyu,zarah tafara wankewa abinka da wanda bai iya ba,kwata kwata basu fita ba,ta dai yi wanda zata iya ta shanya.
Bata gama ba sai ana kiran sallah,abinka da fari duk hanunta yayi jawur.
Tashigo ciki ta nufi d'aki tayi alwalla tayi sallah tana zaune kan abin sallah inna tashigo, ta jawo zarah da karfi tare da cewa ni zaki maida sakara,shine zakimin wankin yan duniya.
Zarah da idanta ya cika da kwalla tace"haba inna wlh wanki da nayi maki iya karfina nayi.
Inna tace"ke ni zakima rashin kunya,zarah tace"!nna wai me nayi maki duniya?"
Inna ta d'auke zarah da mari tare da cewa"kibari idan d'ana ya dawo zai baki amsar tambayarki inna tafita daga d'akin.
Zarah ta zauna tana kuka,bayan kamar 1hour zarah taji dady na kiranta da karfi.
Tamike tafita duk suna zaune,dady yace"zarah inna kikama rashin kunya?"
Zarah tace"dady wlh ba rashin kunya nayi mata ba,tsawa dady ya daka mata duk zarah tabi ta rud'e.
Dady yace"zarah bazan d'auki rashin kunya ba,kirasa wanda zaki ma haka sai uwata.
Zarah tace"dady dan allah kayi hakuri,ya d'aga mata hannu alamar tayi shiru,d'aki zarah ta koma tana kuka.
Inna ta kalli maamaah tace"dole ku gayama yarinyar nan matsayinta dan tasan wacece ita"
Maamaah da ranta ya 'baci sbd tasan zarah bata da laifi,tace" na yanke hukunci dama tun jiya cewa zarah zata koma hostel da zama sbd naga zaman inna da zarah bazaiyu wu ba"
Inna tace"zama gidannan yanzu nafara ba gudu baja da baya"
By:π
Maryerm Mukhtar
[9/17, 5:27 PM] Maamah: ππππππππ
*ZARAH*
for loveβ₯and justiceπ
ππππππππ
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*_We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_*
P.m.l
61\65
Writeen by Maryerm Mukhtar
DEDICATION TO Maryerm Mukhtar Fans Group
*Wannan page na kune masoya na*
Murja salisu na'ikke
Maman xee
Asma'u a gifawa
Feenah
Juwairay
Teeymerh Nougat
Asmee
Maimunat Salis
Aisha jume
Zainab auwal
Zee sani
Fatima lawal stafe
Salma bashir babandi
Yar malam
Maryam bintu
Baby rahey
*Amin afuwa kunada yawq amma insha allah next page zan cigaba*π
Washe gari zarah ta d'an dauki kayanta kala biyu tafito zataje mkrnt,maamaah na falo zaune,zarah tace"maamaah zantafi mkrnt amma zan dan zauna a hostel na kwana biyu"
Maamaah tace"toh zarah amma ki kula da kanki,zarah tace"insha allah maamah babu matsala"
Bayan tashi daga lectures zarah ke cema khairat zataje hostel ta kwana biyu cen,khairat ta tambayi zarah dalilin da zataje hostel zarah tace bakomi"
Khairat tace"toh suje gidansu ta kwana biyun a cen.
Washe gari
Faisal ya shigo gida da safe suna breakfast nan yake tambayar ina zarah?"
Maamaah tace"tana hostel zata d'an kwana biyu,dady yace"zarah na hostel?"
Maamaah tace"eh
Dady yace"ba nace karki fara maganar kaita hostel ba tun jiya,maamah tace"ai ba zama zatayi cen ba"
"Takoma ne sbd ta samu saukin yin karatu zasu fara exam yau"
Dady yace"toh ya zama na farko kuma na karshe da zarah zata bar gidannan bada sanina ba"
Cen bayan su zarah sun dawo daga makaranta suna zaune falon gidan su khairat.
Abdul ya shigo,ganin zarah ya fara jin dad'i,zama yayi yace"Ah zarah kece nake gani ko gizo kike faramin?"
Tayi murmushi tace"nice dai,khairat tace"yah abdul kasanta ne?"
Yace eh kanwar friend d'ina ce,khairat tayi murmushi tace"yah abdul kwana biyu"
Yace"wlh aiki ya hanani yin zumunci,ina momy take?"
Khairat tace momy taje barka,abdul yace"zarah ya karatu?"
Tace"Alhamdulilah
Abdul yace"yau bazan tafi ba sai munyi mgn dake zarah,tayi murmushi tace"toh yah abdul"
Khairat tace"toh naga alama maganar da zakuyi sirri ce bari natashi,abdul yace yawwa kanwata kin kyauta kuwa"
Abdul yace"zarah nasan zakiyi mamaki da nace zamuyi magana,zarah zanyi magana kai tsaye dan gudun kar na 'bata lokaci"
"Zarah Ina sanki,aurenki nakeso nayi,zarah tace"toh ni yanzu bana da amsar da zan baka,amma kabani kwana biyu idan nayi tunani zan gayama khairat"
Abdul yace"zarah dan allah karki wahalar dani,kece mace ta farko dana fara cewa inaso,kuma ina so ki gayamin gsky karki min karya indai bakya sona"
Zarah tace"yah abdul nikam me kamin zance bana sanka,kawai dai kasan ba'aso ayi abu da gaggawa"
Yace"toh zarah sai na jiki.
Abdul sai wajen goma ya tafi gida.
Washe gari zarah suka tafi makaranta,bayan sun tashi daga exam zarah tace"zata wuce gida yau.
Gida zarah ta dawo tana shigowa faisal na zaune,ya kalleta fuskarshi d'auke da fara'a yace"zarah kin dawo,tayi murmushi tace"eh yah faisal"
Tace"ina maamah?"yace taje kasuwa,tace"owk bari naje nayi wanka nagaji"
Bayan tashiga d'aki take tunanin meyasa kuma yau faisal yake mata fara'a?"
Bayan tafito daga wanka tasake kaya tafito falo,dawowar da tayi falo ta tarar da inna zaune,ta d'anyi kasa da murya tace"ina yini inna,ko kallan idan zarah take batayi ba.
Faisal yace"zarah zoki zauna kibani labarin yanda exam d'inku ta kasance"
Inna tace"kai miye haka,sai wani janta kake a jiki,wai yaushe ma zakayi aure?"
Yace"inna ba yanzu ba,tace"wlh kayi kad'an bari babanka ya dawo dama akwai jikar aminiyata na nan ina so a had'aku aure"
Yace"what aure da wata wadda bansani ba,gsky inna kiyi hakuri banaso"
Inna tamike tace"wlh sai ka aureta kaji na rantse"
Da daddare bayan dady ya dawo yana zaune falo shida maamaah,inna tace"dama ina so zamuyi magana da kai,yace"toh inna ina jinki"
Tace"mata na samoma faisal wadda zai aura,maamaah ta mike tare da fad'in mata kuma?
Inna tace"eh
Maamaah tace"ai faisal yana da mata"
Inna tace"wacece ita?"
Maamah tace *ZARAH*
By:π
Maryerm Mukhtar
[9/17, 5:27 PM] Maamah: ππππππππ
*ZARAH*
for loveβ₯and justiceπ
ππππππππ
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*_We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_*
P.m.l
66\70
Writeen by Maryerm Mukhtar
DEDICATION TO Maryerm Mukhtar Fans Group
*Wannan page na kune masoyana*
Sumayya talba
Ummu humairah
Shema'u muhammad
Ummu humaira
Shema'u muhammad
Ummu shureim
Fauzia kabir
Fatima yusu
Ummuqura amin
Maman iman
Ummulqura amin
Hajara yusuf
M al.ameen
Sadeeqa
Mabaruka shinkafi
Fatima yusuf
Mufnah muhammad
Mareayumh
Ummu muhseen
*Amin afuwa kuna da yawa zan cigaba a next page*π
Inna tace"wace zarah?"
Maamaah tace"zarah ta gidannan,inna tace"jikana zai auri yarinyar da aka yada kuka d'auka,wlh bazan yadda ba,dady yace"inna dan allah ki nutsu muyi magana ta fahimta"
Inna takoma ta zauna,dady yace"wace yarinya ce kikeso ya aura?"
tace"jikar k'awata ce,kuma yarinya yace yar asali yar dangi,dady yace inna toh kinga zarah gidannan ta tashi,kuma kinga ita maman faisal tun zarah na k'arama take da burin ta had'asu aure"
Inna tace"toh ni ai wannan bai dameni ba,abinda kawai nasani shine faisal wadda na za'ba zai aura"
Maamaah tace"dan allah inna karki min haka,wlh tunda na d'auko zarah nakeda wannan niyyar"
inna tace"abinda kukayi ma wannan yarinya ya isa,basai kun aura mata faisal bane kunyi hallaci"
Dady yace"toh yanzu bama wannan ba,shi faisal ba lallai yaso yarinyar da zaki bashi ba inna,dan allah abi komi a hankali"
Maamaah ta duk'a kasa gaban inna tace"dan girman allah inna kibari faisal ya auri zarah,wlh inna zarah tana da hali mai kyau"
"Kuma bana tunanin faisal zaik'i zarah,saboda inna kinga akwai shakuwa tsakaninsu"
Inna tace"toh naji amma da sharad'i guda biyu,sharad'in na farko shine sai dai faisal ya auri mata biyu,zarah da yarinyar da nakeso,na biyu za'akira faisal gani gashi gaki a tambayeshi muddin yace bayasan zarah toh wlh babu wanda ya isa ya aura mashi ita"
Maamaah tace"inna dan allah ki janye maganar mata biyu,na tabbata zarah tafi duk wata mace da za'aba faisal"
Inna tace"idan abinda nace baiyi ba toh abarshi,amma kusani batun auren yarinyar da nakeso babu fashi sai anyi"
Maamaah tamik'e tafita ranta 'bace.
d'aki takoma tana kiran wayar faisal dan tana tsoran kar yace baya so,amma yaki d'aukar wayar.
Har karfe goma na dare faisal bai dawo ba,kuma tasake kira taji wayar a kashe,maamaah ta mashi text takoma ta kwanta.
Ranar maamah bacci kasa d'aukarta yayi gaba d'aya,haka ma dady inna kam tasa ido tana so taga ko maamaah zata kira faisal d'aki.
Washe gari faisal ko ciki bai shigo ba ya fita,maamaaj tayi mamaki dan tasan faisal bai ta'ba yin haka ba.
Wajen karfe d'aya na rana faisal ya dawo,yana shigowa falo inna tace"ya tsaya nan bari ta kira maamah akwai maganar da zasuyi.
Maamaah tafito taga faisal zaune kan kujera,gabanta fad'uwa yayi tace"faisal ina wayarka?"
Yace"wlh maamaah ta fad'i tun jiya,maamaah tace kenan bakaga text d'in da nayi maka ba"
Yace"eh
Hankalin maamaah ya tashi zama tayi inna tace"faisal tambaya ce zamuyi maka,kuma amsar da kabada da ita zamuyi amfani"
Inna tace"faisal kana san *zarah*?"
Faisal ya kalli inna da mamaki yace"inna zarah kuma,zarah ai k'anwata ce"
Inna ta zayyana ma faisal komi,hankalinshi ya tashi,ya kalli maamaah yace"maamaah dama zarah ba kanwata bace ta jini?"
Maamaah da hawaye yake bin fuskarta tace"faisal ya zama dole na sanar da kai gsky,zarah ba kanwarka bace,adopting d'inta mukayi a ophanage home a garin *katsina*"
Faisal ya dukar da kai yana hawaye,inna tace"kabani amsata shin kana san zarah da aure?"
Faisal ya d'ago kai ya kalli inna yace"meyasa kuke min wannan tambayar,da wace fuska kukeso zarah ta kalle ku"
"Taya kuke tunanin zarah zata yadda da wannan maganar da batasan da ita ba"
Inna tace"kaga faisal amsa d'aya nakeso kabani eh ko A'a"
Yace"koda bansan zarah ba bana tunanin zan ce bana santa,dan haka ina san *ZARAH* kuma zan aureta"
By:π
Maryerm Mukhtar
[9/17, 5:27 PM] Maamah: ππππππππ
*ZARAH*
for loveβ₯and justiceπ
ππππππππ
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*_We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_*
P.m.l
71\75
Writeen by Maryerm Mukhtar
DEDICATION TO Maryerm Mukhtar Fans Group
*Masoyana kuna raina*
Asma'u A Gifawa
Asmina
Feenah
Saadatu umar sanee
Aisha jume
Hafsat adam
Rahmat al,ameen
Queency
Zeeewy
Litle bae
G princess
Mama sky
*Toh yau dai nagama lissafo masoyana wayanda nasani wayanda bansani ba kuma kuna raina ina tare daku ko yaushe*ππ€
farin ciki ya bayyana kan fuskar maamaah,tace"faisal allah yayi maka albarka.
Wajen 6:00 zarah ta dawo daga shcool,tashiga d'aki tayi wanka tayi sallar magriba,tana zaune gefan gado dafe da kai.
Murja tashigo tace"zarah wai kizo inji faisal,zarah tace"murja wlh kaina ciwo yake,kice mashi kwance nake kaina ciwo yake"
Murja takoma falo faisal na zaune,murja tace"wai kanta ke ciwo bazata iya fitowa ba"
Faisal yace"owk jeki.
Zarah na kwance dafe da kai faisal ya shigo,d'agowa tayi ta kalleshi.
Faisal ya had'e hannuwanshi tare da cewa"zarah ina so zamuyi magana,zarah ta ya mutsa fuska tare da cewa"yah faisal dan allah kabari sai gobe yanzu kaina ciwo yake"
Faisal ya tsaya yana mata wani kallo da manyan idanunshi farare tas,zarah sai taji duk kunya ta kamata,tace"yah faisal ya naga kana min wani kallo?"
Ya girgiza kai tare da cewa"zarah ke yarinya ce k'arama,maganar da zamuyi gani nake zata iya fasa maki zuciya"
Zarah tace"nikam yah faisal wace magana ce wadda zata fasa min zuciya"
"Kawai dai mubari sai gobe"
*Washe gari*
Zarah tunda safe tatafi makaranta,wajen 10 faisal ya shigo maamaah na falo yace"maamaah ina zarah?"
Tace"tatafi makaranta amma tace min yau 4 zata dawo,faisal yace"maamaah ya kamata yau a fad'ima zarah gskyr