Author : UMMU AFFAN Category : African Stories & Novels
godiya tayi tana ɗagawa na motar hannu wanda da alamar zaiyi sa'an Kakanta. Bayan wucewarsa Ruhaima ta ƙaraso riƙe da jaka tana taunar jingam. "Gwoggo Lafiyarki da farar ranar nan a waje da muciya, ɓarawo kika ji anawa ihu halan?" Wani kallo ta aikawa Ruhaima na kin raina min hankali, irin kallon da kuwa bata taɓa yi mata irinsa ba, taɓe baki Ruhaima tayi tana niyyar shigewa ciki kamar zata bangajeta. Da sauri ta dakatar da ita "Kin ga tsaya ƴar nan, da kika fito baki ga gilmawar Tataah ba?" Baya Ruhaima ta dawo tare da zaro ido kafin ta ɗaure fuska "Gwoggo ba dai kin yiwa yarinyar nan abin da yasa ta gudu daga gidan nan ba? Wallahi idan har haka ne bazan ƙyaleki ba" Kallon mamaki Gwoggo ke bin Ruhaima da shi "Ke kina da hankali kuwa? Kin san da wa kike magana?" "Ƙwarai ina sane Gwoggo ba eh Gwoggo! Gwoggo Zainabu!!" Ta ƙarashe da tsiwa da chono baki gaba. "Ok na gane na ɗauka ko kina tunanin da Bilkisu kike magana ne" Wani kallo ta mata har ta juya zata shiga ciki ta dakata jin uban hurn ɗin da aka bugo musu. Sai da gaban Gwoggo ya bada wani rass! Ganin Baheerah da Hajara sun fito, nan take ta fara sunsunne kai, ganin haka yasa Ruhaima tukare bakin ƙofar dan taga alamar Gwoggon bata da gaskiya. Ai kuwa ta kalleta magana can ƙasa ta ce"Ruhaima me yasa ke ba ƴar rufin asiri bace, dan Allah ki matsa kar su ganni idan sun shugo kice musu bana nan" Jin haka Ruhaima ta ɗaga murya "Sannunku da zuwa bayin Allah, ai nan ne gidansu Gwoggon ga ta nan!" Hmmm ji Gwoggo tayi ina wuta ta jefa Ruhaima tabbas tayi da nasanin kwatanta musu gidan da yanzu hankalinta a ƙwance ba a zo takura mata ba. Dole ta juyo ta tare su da fara'a jagora tayi musu har zuwa cikin ɗakinta, duk suka zazzauna, ruwa leda ta kawo musu guda biyu ta sake zama "Ina wuninku Hajiya ya kuka baro Hajiya babbar?" "Lafiya ƙalau" Baheerah ta amsa a takaice ta ƙisa taga Tataah. Ganin bata da niyyar nuna musu ita ta ce"Gwoggo ina Tataahr ne?" Shuru tayi minti biyu sai kuma ta ce"Halan kuma ta ɗirka muku tsiyar ne? Wannan yarinya hali sak na uwarta babu inda ta barta komi nata na gado me, babu gidan aikin da za a kaita bata baro abin faɗa ba, mu kanmu a gida haƙuri muke da mugun halinta, dan Allah Hajiya kuyi haƙuri babu abin da muka mallaka a garin Habuja duk ƙarya ce, gidan nan ma aronsa aka bamu mu zauna ko sisi bama biya uwarta ta daman baƙin halinta ya hanata zama lafiya kowa baya faɗin alkhairi akanta sai mugun halinta shiyasa take kwance ciwo shekara da shekaru ko kare bai taɓe zuwa ce mata sannu ba, shi kuma uban ya tafi ƙauye ganin kaka tayi ya ɗan samo mana hatsi ita kuwa Tataah sai dai Allah ya shirya wallahi ko kwana gida bata so yin, yanzu haka batun da nake muku kwana biyun nan bata kwana gida ba" Sai ta fashe da kukan munafurci har da shassheƙa ta ɗaura da cewa"Haka ake gayar mini irin manyan motocin da ake sauketa da dare idan tayi niyyar kwanan gidan kenan, to nayi faɗan har na gaji taƙi bari to ƴar kishiya kar ace dan ba ƴata bace na barta sakaka amma wallahi ƴar nan bata jin magana yanzu dai tayi mai kankat kwana biyu bata dawo ba daman ta saba hakan, fara aikinta gidanku ne kawai ta ɗan rage to yanzu abu ya dawo sabo, sai tayi sati bata dawo gida ba" Gwoggo tacigaba da kuka kamar gaske. Tuni ran Baheerah ya ɓaci zuciyarta kuma ta harzuƙa ta jin irin wannan munanan kalaman akan Tataah domin bata yadda ba har abada kuma bazata iya yadda ba. Miƙewa tayi idanuwanta har sun fara ja, da sauri Hajara ta miƙe tana riƙe hannayenta, ko kallon Gwoggo basu kuma yi ba suka bar gidan. Ruhaima ta ce"An dai ji kunya Gwoggo yanzu da girmanki kike ƙarya? Girma dai ya faɗi?" "Ruhaima waini sa'arki ce ko tsararki? Ni na aife ki ko ke kika aife ni?" "Kece Gwoggo amma kin shurgo ƙaryar ne da yawa, gashi har sun gane sun barki nan kile kamar kayan wanki" Mafecin dake gefenta ta wullawa Ruhaimar ta rufeta da ashar "A'a Gwoggo bani nakar zomon ba, rataya aka bani, kuma ɓatan Tataah bakiji nanin ba yacin nima sai na bi mata haƙƙi, haba dan Allah ƴar uwarmu ce fa" A harzuƙe Gwoggo ta tashi "Ki kamani ki kaini ga hukuma dan kaza-kazan ubanki, inda zan gane tabbas ƴar uwarki ce kenan tun da Bilkisu ta haife ki" Zatayi magana Gwoggo ta bita da muciyar hannunta da gudu tayi ciki... A ƙofar gidan Baheerah taci burki tana mayar da numfashi cikin ɓacin rai ta kalli Hajara ta ce"Hajara anya matar nan ba wata manufa a zuciyarta? Ni sam maganganunta basu da wani tasiri a zuciyata!" "Tabbas uwar ɗakina ai maganar gizo bata wuce ta ƙoƙi, kana jin wannan zancen kasan ƙanzon kurege ne" Numfashi ta sauke tare da cewa"Zanyi bincike dole, Tataah zata dawo gidan in sha Allahu, da nasan irin baƙin halin da take ƙunsa kenan gurin matar uba da bata zauna a gidan ba" Hajara ta ce"Bari kawai ai yarinyar zurfin cikinta yayi yawa" Kai tsaye mota ta dosa suna shiga ta bata wuta suka wuce..... "Wai yaushe zaka dawo da aiki anan?" Faruuk dake tuƙa motar ya tambayi Aliyu dake kujerar mai zaman banza idanuwanshi a lumshe. Girgiza kai Faruuk yayi ganin bashi da niyyar amsa mishi, "Amma tambayarka nake ko?" Bai buɗe idon ba ya ce"Ka bari idan ƙwailar matarka tayi ciki, idan zata haihu nazo amsar haihuwar na dawo aiki nan kenan!" Ɗan ɓata rai Faruuk yayi Aliyu ya raina Hibbah da yawa shi kam a rayuwa zai ga matar da Aliyu zai aura. "Kace nan da wata tara kenan?" Da sauri ya baɗe ido ya tashi zaune "What? Wannan yarinyar ce zata haihu nan da wata tara? Kana da hankali kuwa Faruuk?" "A'a ina tunanin da ni da kai duk bamu da hankalin, mu ƙulla alƙawari dai idan har nan da wata tara Hibbah ta haihu zaka dawo aiki a ƙasarka kuma jaharka" Ɗan dariya yayi baya son yin ta amma sosai ta ƙara mishi ƙyau har siririyar wushiryarsa ta fito, "Eh na yarda" Faruuk ma murmushi yayi nan take kuwa suka ɗauki alƙawari tare da tsayar da date. Filin jirgi ya kaishi, suna mota kafin lokaci yayi Aliyu ya ce"Daddy ya matsa min da ina dawowa aure na da Baheerah ni kuma kasan ba wani kwanta mini tayi ba, ko da can abota ce tsakaninmu ba soyayya ba, amma Daddyna da Daddynta sunƙi fuskanta" Ɗan dafashi Faruuk yayi "Kayi haƙuri kayi biyayya zance, Baheerah bata da matsala kai kanka kasan tana da sauƙin kai kuma tana da shekaru irin na macen da kake buri me ilmi sosai komi yayi yadda kake fata kawai ka bada kai bori ya hau musha biki" Dukan wasa ya kai mishi "Daga neman shawara sai abin ya zama zolaya?" "Gaskiya na faɗa, buradinka tun muna yara. Sai dai Aliyu abu guda ɗaya har abada kar ka manta da nauyin wata a kanka *Jameelah* matarka ta sunna da aka ɗaura aurenmu rana guda" Gabansa yayi mugun bugawa sam mantawa yake da wannan auren sai idan an tuna masa, abin da mutumin nan ya bashi ya tuna tun da ya jefa drowwer bai ƙara bi ta kansu ba. Numfashi ya fesar mai zafi jin an fara kiran suna ya sauka yana ɗagawa Faruuk hannu. Faruuk bai tafi ba har sai da yaga tashin jirgindu sannan ya dawo hanyar gida. Ƙira'ar ƙur'ani ya kunna suratul rahman muryar Abdulrahaman Sudees, a hankali yake bin ƙira'ar ya gangalo unguwarsu Tataah ya hango hannu ana ɗaga mishi daga cikin ƙwalta. Gabanshi ya faɗi har ya wuce sai kuma ya dawo, baya hango komi Faruuk da shegen tausayi haka ya sakko a motar ya doshi gurin, sosai ƙirjinsa ya buga ganinta "Tataah!" Ya furta amma ina sam bata motsi, matar da ta ɗaga mishi hannu ta ce"Nima wucewa zanyi na ganta yashe a gurin kamar matacciya" Bai tsaya jin ƙarashen maganar ba ya sungimeta yasa a mota yaja da gudu ya bar gurin ko takan matar da ta tsayar dashi bai bi ba.
Kai tsaye asibitin Aliyu ya kaita wannan karon, wanda ya zuba ma'aikata suke aiki. Ana ganin Faruuk da sauri aka amshe su hannu biyu aka nufi emagency room da ita, a gurin ya zauna tare da dafe kan sa. Tunani ya faɗa akan Tataah, tabbas daga ganinta kasan tana cikin wani hali, girgiza kai yayi ya rasa mene ne dalilinta a wancen karon naƙin sanar da shi ainihin wacece ita, tabbas yana jin tausayinta a zuciyarsa kuma yasa a ransa idan har ta faɗa masa to zai temaketa iya kar iyawarsa, karo uku kenan Allah na haɗasu. Yana zaune nan kusan awa guda sannan likitan ya tabbatar da mashi da sun samu nasarar dawowar numfashinta, ajiyar zuciya ya saki tare da hamdala a fili. Miƙewa yayi ya leƙa ɗakin tana kwance na abin zuƙar numfashi ga ƙarin ruwa da ake mata, fuskarta ya kalla tayi fayau duk da bata da haske sai ramar da tayi sosai fiye da ta baya a yadda ya santa, girgiza kai yayi ya cewa likitan dan Allah a kula da ita sosai yana dawowa, ya ce"Haba oga, aka kula da wasu can bare ma balle na gida kuma" Murmushi kawai ya yi ya fice daga asibitin. Kai tsaye gidansa ya dosa, wannan karon bai san sanar da Mami domin bai san ta wacce fuska zata ɗauki maganar ba, so yake sai yarinyar ta farka ta sanar da shi komi yadda zaijewa Mamin da ƙwarin guiwarsa. Hibbah ta amshe sa sosai cike da farin ciki da tareraya irin ta masoya, sai dai ta lura yanayinsa ba yadda ta saba ganinsa ba, bata ce komi ba ta haɗa mishi ruwa yayi wanka sannan suka fita dinning, a baki take bashi abincin tare da daɗaɗan kalamai na kwantar da hankali. "My luv lafiya kuwa? Naga yanayinka ba yadda na saba ganinka ba" Sai da ta tabbatar ya ƙoshi kafin ta jefo mishi wannan tambayar. Numfashi ya fesar tare da kama hannayenta ya ce"Hibbah wata yarinya ce da alamu tana cikin matsin rayuwa!" Ƙura mishi ido tayi gabanta na faɗuwa nan take kuma yanayinta ya sauya, kumallon matan ya motsa. Da sauri ya sake damke hannayenta "Kar ki saka komi a zuciyarki Hibbah Allah ya gani temakon yarinyar nan nake son yi" Nan ya bata labarin komi farkon haɗuwarsu ana ruwa da rashin lafiyarta ya kaita asibiti har zuwansu Mami tare da halin da ya ganta a yau. Da sauri Hibbah ta juyo dan ita ma akwai tausayi kamar mijin nata ta ce"Wallahi har naji ina son ganinta da jin tarihin rayuwarta" Murmushi yayi cike da jin daɗin goyan bayan da Hibbah ta bashi ya rungumeta tare da cewa "Na gode honeyna!" Duka sukasaka dariya, nan kuma zancen ya sauya kala, kinkimarta yayi suka koma bedroom aka lula duniyar ma'aurata. Hibbarsa tana saka shi farin ciki da iya ɗaukar ɗawainiyarsa, a kullum ya tuna da maganar Aliyu sai dai ya girgiza kai Gadanga kenan kusar yaƙi. Bayan sunyi wanka sun shirya, sallar la'asar ya fita yi ita kuma tayi tata a gida sannan ta haɗa abubuwa su abinci tea plate cup, faro da juice a babban basket yana shugowa ya ɗauka tare suka wuce asibitin... Tataah tun bayan da ta dawo hayyacinta ta fuskanci a inda take da sauri ta tashi zaune, duk da jirin da take ji haka ta tsige abin da ke hancinta ta tsige ruwan da ake ƙara mata ta sakko daga gadon asibitin. hijabinta dake gefe ta raruma ta saka, a hankali take takawa har ta fito daga ɗakin. Asibitin bai cika hayaniya ba da alama sai ɗan wane da wance, haka ta fara takawa har ta isa harabar asibitin, juyawa tayi gabas da yamma kudu da arewa, kafin ta fita gate ta ƙaramar ƙofa a hankali, domin me gadi yana gefe suna hira da wani mutumi sam bai lura da ita ba, shi kuma ɗayan mutumin ya ɗauka tazo an dubata ne ta koma, haka ta samu ta fice daga asibitin ta duƙa tafiya ba tare da tasan ina zata ba.......
*Mu tara a paid group, ɗungurungun, tarin amsoshinku mu tara acan ni bazan ce komi ba yanzu, magana guda ko gundarin labarin ba mu shiga ba tukun. Labarin rayuwar Tataah mai cike da tarin sarkaƙiya😥 Fesa muku abu kaɗan afkawarta cikin wata al-umma da ba tata ba, koya makomarta zata koma a cikin al-ummar da ta kasance addininsu ba guda ba? Amsar na gurin Ummu Affan, sannan wacece Jameelah sai kun biyoni tsantsar tausayi abin al'ajabi soyayya kulawa sai a rayuwar Tataah, ku biyoni muje zuwa kuɗin ba mai tsada ba ne.*
_Alƙalamin ƴar mutan Funtua Katsinawan dikko ɗakin kara Fatima Sunusi Rabi'u Uwar Affan._
This book is not free. it's N300 via 0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
Stanbic bank. Then u show ur evidence of payment whatsApp number 08104335144