Author : UMMU AFFAN Category : African Stories & Novels
ki manta kin ce a masallaci aka ɗaura auren ba tare da waliyan Aliyu ba, bugu da ƙari bai san matar ba kuma tun da ya dawo bai kuma maganar ba, wannan auren dashi da babu fa duk ɗaya ne, ba tarewa zatayi ba balle ki damu kanki, zamu iya abin da ma har abada bazai ganta ba yadda akayi auren a wulaƙance kuma ya saketa a hakan dama ba sanin juna sukayi ba" Sareenah ta saki wata ajiyar zuciya mai ƙarfi ta ce"Shiyasa nake ƙaunarki ƙawata kin san sirrin yadda zaki kawo mafita, na gode" Ta faɗa tana share hawayen idonta. "To ya yi ba komi kuma ai kin wuce hakan a gurina ki tashi kiyi wanka kici abinci ki kuma kwantar da hankalinki kamar kinyi baƙo ya mutu." Tana ɗan murmushi ta faɗa bathroom wanka tayi tazo ta shirya cikin doguwar riga ƴar kanti tare suka fito parlourn da Layla suka nufi dinning table Ammi ta ce"Layla sannu da ƙoƙari" Tana murmushi ta amsa da yawwa, Sareenah kuwa ko kallon Ammi batayi ba... AlhamduLillah ango Faruuk ya sami kwanciyar hankali tare da matarsa Hibbah suna gudanar da tsaftatacciyar soyayyar aure bisa koyarwar sunnar ma'aiki Annabi muhammad (S A W). Faruuk yayi wani ƙyau abin shi da ka kalle shi kasan ango ne, Hibbah tana kula dashi ko ince suna kula da junansu ainun. Mami tayi farin ciki da samuwar surika ta gari don Hibbah ta fito daga gidan tarbiyya. "Ai na ɗauka ba yanzu zaka koma ba!" Cewar Faruuk bayan Aliyu ya sanar dashi zai koma bakin aiki. "Hmmm!" Ya fesar da huci kafin ya ce"Daɗina da kai gwalishe mutum, to daman hutun sati ɗaya na ɗauka kuma na sanar da kai" Jinjina kai Faruuk yayi kafin ya ce"Me yasa ba zakayi transfer ka dawo aiki a ƙasarka ba ne? Kaje wata ƙasa da ba taka ba kana hidinta musu, ya kamata kayi tunani Aliyu" Kallon gefen baki ya mishi "Amma ai ƴan ƙasar ne suka koyar dani, shin mene ne laifina dan nayi aiki a ƙasar da su suka koya mini ilmin?" "Da laifi tunda kaima ƴan ƙasarka suna buƙatar jajirtaccen likita kamarka, musamman ma fannin da ka ƙware a kai" Miƙewa ya yi, "Kaga Malam sai anjima!" "Ya zaka tafi honey na kitchen kuma kasan dai kai ta shiga kawowa abinci" "Bana buƙata kuci kayanku, wannan ƴar yarinyar har wani girki ta iya, Faruuk kabi a hankali dai kar rawar kanka tasa ka illata musu yarinyar da bata isa komi ba" Mtsuww! Faruuk yaja tsaki "Wallahi Aliyu idan kana wani abin kamar ba likita ba, Allah ya shiryaka idan kai ka tashi aure ka auro sa'arka dan Allah" Aliyu na dariya ya ƙarasa harabar gidan ya shiga motarsa. Faruuk kuwa daman tun a ƙofa ya koma, kai tsaye gidan Mami Abuturrab ya wuce.
Mami ta sa Naanah ta kawo mishi abinci, sosai yaci don dama yunwar yake ji abincin Hibbar ne baya tunanin zai iya ci. Sai da ya gama suka gaisa da Mami ya sanar da ita gobe zai koma bakin aiki, gyaran murya tayi da cewa"Aliyu naji komi game da auren da kayi bayan kammala na Faruuk, amma baka tunanin neman matarka!" "Matarka!!!" YA ƙara nanata kalmar. Murmushi yayi "Mami ki bar wannan maganar wallahi kallonta nake kamar wasan kwaikwayo" "Aliyu auren? Auren ne kake kallo kamar wasan kwaikwayo? To idan bacci kake ya kamata ka farka, maganar aure ba abin wasa bane. Mata dai ta zama taka tun ranar da aka ɗaura aure sannan tarin haƙƙoƙinta ya rataya a kanka tun daga ranar don haka ka farka kasan abin da ya kamata" Sosai jikinsa yayi sanyi ya ce"In sha Allahu Mami zanyi abin da ya kamata" "Hakan dai yafi" Yana barin gidan kai tsaye ya nufi gidansu.
A Parlour ya iske Ammi da Sareenah sai ƙawarta Layla, ƙarasawa yayi gaban Ammi ya zauna gefenta "Barka da gida Amm..." Dakatar dashi tayi ta hanyar ɗaga mishi hannu "Wanne sannu zaka mini bayan ka gama watsa mini ƙasa a ido, wallahi ka bani mamaki Aliyu banyi tunanin zaka iya aikata wannan shirmen da ilminka ba!" Ƙasa yayi da kai "Kiyi haƙuri Ammi ban yi hakan domin baƙanta muku rai ba, mutumin ne ya bani tausayi yadda yazo cikin masallaci yana roƙon a auri ƴarsa" "Mtsuww!!!" Ammi taja tsaki mai ƙarfi "Aliyu baka da hankali, yanzu wannan dalilin zai sa ka amince da auren ƴarsa baka san wacece ba? Ba kasan halinta da nasabarta ba? Mata nawa ne ake maka tallarsu akan ka auresu su basu taɓa baka tausayi ba ka amince sai wacce baka san wacece ba, Hmmmm faɗa ma ɓata baki wallahi ƙarya kake Aliyu!!" Da sauri ya ɗago yana dubanta sai kuma ya miƙe, "Daman zan miki sallama ne, wataƙil gobe bazamu haɗu ba don da wuri zan wuce" "Zaka wuce ina?" Ta tambaye cikin ƙaraji, kauda fuska yayi gefe kamar ba zai ce komi ba sai ya ce"Wajen aiki" Yana faɗa ya kaɗai kai ya fice. Sareenah ta saki kukan baƙin ciki yayin da Ammi ta miƙe tsaye cike da ƙunar rai. "Ku kwantar da hankalinku!" Muryar Layla ta sauka masarrafan jinsu "Taya? Layla taya na tambayeki? Kina gani fa kina jifa nikam naga ta kaina, wallahi tawa ta sameni" Sareenah ta furta tare da sakin wani kukan. Ammi dake huci kamar wata kumurcin maji ta ce"Dani Aliyu yake zancen, lallai Aliyu raini ya shiga tsakaninmu, yaron da ko ido bai iya ɗagawa ya kalleni a baya shine yanzu na gaya mini magana, hmmm wallahi zamu gani kuma mu gani a ƙasa dani yake maganar Kuluwa ce fa ya tarowa kanshi faɗan da bazai iya rabawa ba!" Layla wani murmushin ne ɗauke a fuskarta ta ce"Tun da nace ku bari, to ku bari ɗin ni nasan abin da zanyi. Wallahi idan har kun bada haɗun kai sai Aliyu ya raina kanshi sai ya dawo yana binku kamar raƙumi da akala." Ammi na sakin ajiyar zuciya ta ce"Ko wanne irin goyan baya ne zamu bada, matuƙar Aliyu zai auri Sareenah babban burin da nake son cikawa kenan a rayuwata." "To kamar angama" Layla ta faɗa duka suka bita da kallo...
This book is not free. it's N300 via 0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
Stanbic bank. Then u show ur evidence of payment whatsApp number 08104335144
[8/29, 5:21 PM] Sadfat: *MU GANI A ƘASA...*
© FATIMA SUNUSI RABIU
UMMU AFFAN
*Page 15-16*
Murmushi ta kuma saki tare da zama gefen coshin, suma suka bita tare da zaunawa. Ƙafa ɗaya ta ɗaura saman ɗaya ta ce"Hakan ba zai samu ba har sai Sareenah ta fara kwantar da hankalinta, sannan muje gurin mai gayya mai aiki da cikawa." Numfashi Sareenah ta sauke idanuwanta na kan Layla kamar yadda Ammi idanuwanta ke kan Laylar. Ammi ta ce"To Sareenah kina ji dai, ki kwantar da hankalinki maganar kuɗi kuma ko nawa ne zan iya kashewa akanki da samun cikar muradinki da kuma cika burina akan Aliyu." Numfashi me zafi Sareenah ta saki ba tare da ta ce komi ba... "Sannu Ummana" Tataah ta faɗa cikin tsantsar nuna kulawa. ''Kin wahala ko? Kiyi haƙuri idan na girma nayi aure zan kai ki ƙasar waje a duba mini lafiyarki ki sami sauƙi. Idan kuma mijina ba mai halin fitar da ke waje bane to zan kai ki babban asibiti a ƙasar nan domin samun babban likitan da yasan matsalar ciwonki Ummana." Shuru tayi na wani lokaci kamar mai tunani sai ga hawaye "Wallahi Umma har na fara hangoki cikin lafiyarki fiye da ta baya, kina magana kina tafiya kuma komi na jikinki yana aikinsa sannan kina gudanar da dukkan ibadunki ba a kwance ba" Hawaye ne ta gani a idon Umman da sauri ta ƙarasa kusa da ita tare dasa hannu ta goge mata "Kuka kuma? Umma kin san abin da nafi tsana shine ganin hawaye na zuba a idaniyarki. Nan ta fara share mata tare da bata abinci taci, tana ta mata hira iri-iri domin zuciyarta ta kwanta. Washe gari da wuri ta wuce gurin aikinta saboda Hajiyar ta ce ƴar ta dake ƙasar waje zatazo suzo da wuri, hakan yasa tun huɗu na dare ta farko bayan ta ɗaura alwala tayi sallah raka'a biyu tayiwa Ummanta addu'a sai taje ta gabatar da duk aiyukanta na gidan kafin a kira sallar asuba tanayi wajajen shidda ta wuce gidan aikinta. Ta taradda Hajara tana ta aiyukanta sakamakon ita a gidan take kwana da sauri taje ta tamata bayan ta gaisheta ta amsa cike da fara'a da jin ƙaunar yarinyar a zuciyarta. Wajajen ƙarfe goma na safe suka gama komi sai da suka karya Tataah ta nufi ɗakin Hajara kwanciya tayi saman katifarta nan take kuwa baccin wahala yayi gaba da ita. Ƙarfe sha ɗaya na safiya jirginsu Baheerah zai sauka hakan yasa tun ƙarfe goma da rabi Hajiya da direba suke Airport. Lokaci na cika kuwa jirginsu ya sauka fasinja suka fara sakkowa, a hankali take sakkowa daga matattakalar benen jirgin, ƙyaƙƙyawa ce sosai fara tas! Kamar a tsaga jini ya fito, kana kallonta zaka gane tana da tsatso da larabawa ko turawa domin fuska kalarta da jikinta da ya nuna hakan, idan kuwa kaji muryarta zaka ƙara gazgatawa. Hajiya na hangota ta fara washe baki cike da farin cikin ganin tilon ƴar ta ta, ita ma da sauri ta ƙara so tare da faɗawa jikinta, sosai ta rungumeta duka suna cikin tsantsar farin ciki. "Mom barka ya kike?" Ta faɗa cikin harshen turanci "Lafiya ƙalau ƴata fatan kema haka?" "Ina lafiya Mom" Cikin mota suka shiga tare da ɗunguma Unguwar da suke. Har suka iso Tataah na bacci Hajara ce ta tarbesu cike da fara'a. Wanka Baheerah ta fara kafin tazo dinning inda taci abincinta cikin kwanciyar hankali sai yaba girkin Nigeria take yi Hajara sarkin barkwanci da zance sai biye mata take suna kwasar dariya, da alama Baheerah tana da sauƙin kai sosai. Sai misalin ƙarfe sha biyu saura Tataah ta farko, toilet ɗin dake ɗakin ta faɗa bayan ta kama ruwa ta wanke baki da fuskarta sannan ta fito direct ta nufi parlourn gidan. Zazzaune ta taddasu suna hira ƙarasawa tayi cike da natsuwa kafin ta zauna saman carpet tana musu sannu da gida, Baheerah ta ce"Wow black beauty, Mom wacece ita?" Ta furta idanuwanta akan Tataah. Hajiya ta ce"Ita ce mai kula da part ɗinki" Har lokacin idanuwanta akan Tataah ta ce"Okey gaskiya tana da ƙyau Mom kalar da ba a saya a kanti" Duka suka saka dariya. Hajara ta ce"Gaskiya ne shalelen Hajiya baƙi fantin Allah" Ita dai Tataah kanta yana ƙasa bata taɓa jin wanda ya yabi kalarta ba sai yau, duk wanda zasu haɗu kusheta yake da ƙyamar kalar tata amma sai gashi yau farar mace ƙyaƙƙyawa tana yabon kalarta. Baheerah ta ce"Wai ke bakiyin magana ne? Mene ne sunanki?" Har lokacin kanta a ƙasa cikin sanyinta ta ce"Tataah!" Baheerah dariya tayi sosai har da tafa hannu ta ce"Tataah kuma? Wannan ai ba suna bane, wallahi sunan ma dariya ya bani" A hankali Tataah ta ɗago kallon Baheerah take wacce ke dariya duka dimple ɗinta sun lotsa kumatunta biyun, dariyar kanta ƙyau ta mana 'Lallai wannan ba ƙarin ƙyau ne da ita ba' Tataah ta faɗa a zuciyarta kafin ta ce"Yaya Baheerah da gaske Tataah ne sunana shi na sani" "Amma dai ba shine sunanki na asali ba" Ɗan shuru tayi sai kuma ta ce"Nima dai ban sani ba" Hajara ta ce"Tataah ƙuruciya na damunki" Ranar Baheerah ta sami farin ciki sosai haka kawai taji Tataah ta shiga zuciyarta jin ta take tamkar ƴar uwarta ta ciki ɗaya.... "Aliyu naji ance gobe zaka koma aikinka?" "I Daddy gobe zan koma" Ƙarasa shugowa Daddy yayi cikin parlourn ya ce"To tabbas ka shirya Baheerah ta iso kaje ku gaisa" Kauda fuska gefe yayi cikin biyayya ya ce"To Daddy" Juyawa Daddy yayi ya bar part ɗin gabaɗaya. Aliyu ya kalli jikinsa ta cikin mirror yaja tsaki a fili ya furta "Wai kamar ni ake son zaɓawa abokiyar zama, ai nayi girma da hankalin sanin komi na rayuwata amma ace har yanzu ban sami wannan ƴancin ba.
Duk juyawa sai ya saki tsaki, da wannan tunanin ya gama shiryawa, wayarsa ya ɗauko tare da kiran lambar Faruuk. Har ta ƙarace ɓurarinta ba a ɗauka ba, tsaki yaja jin zuciyarsa yake tazo ƙirji saboda takaici ƙara kira yayi sai da ta kusan tsinkewa ya ɗaga. Cikin wata irin murya da bai san Faruuk da ita ba yaji ya ce"Malam lafiya? A dunga sanin lokacin da za a riƙa kiran mai iyali please." Ƙit Aliyu ya katse kiran yana faɗin "Ɗan iska kawai, ko me zai yaga a jikin wannan yarinyar oho" Car key ya ɗauka saman mirror ya fita a sittin ko part ɗin Ammi bai leƙa ba. Saboda yasan gidan su Baheerah kai tsaye can ya wuce, Maigadi na ganinsa yayi saurin wangale gate domin duk wanda ya tashi a gidan yasan matsayin Aliyu a gidan tamkar ɗan gida yake in dai jama'ar gidan na ƙasar. Guri ya samu yayi parking a ɗan madaidaicin harabar gidan, Iyayen Baheerah masu dukiya ne sosai, mahaifiyarta baturiya ce hakan yasa mahaifinta komi irin na turawa yake babu tsarin fankaɗeɗan gida a matsirinsu komi na turawa suke. Cikin takun ƙasaitarshi ya fara takawa zuwa cikin gidan knowking yayi. Tataah dake kishingiɗe parlourn ita kaɗai ta miƙe, domin sosai take jin daɗin aikinta a gidan ba qasu aiyukan wahala masu yawa idan ka gama komi gar bacci zaka iya idan kana ra'ayi kafin lokacin tafiyarka, Hajiya ce kawai me ɗan matsala ita ma ba sosai ba yanayinta ne haka amma musulma ce sai dai bata da fara'a idan ka kalleta kai tsaye zaka iya kiranta mai zafi amma bata da faɗa sai ka shiga sabgarta. Da sassarfa ta isa ƙofar domin Hajiya na sama Baheerah tana part ɗinta Hajara kuwa tana kitchen. Cikin natsuwarta ta kai hannu ƙofar tare da buɗewa, mutuwar tsaye tayi gabanta na mugun faɗuwa lokacin da suka haɗa ido, da sauri ta janye hannunta a ƙofar, bai ce mata komi ba ya raɓa ta gefenta ya wuce ciki, har ya ƙarasa ya zauna Tataah ta kasa barin ƙofor, ba ƙarin shock ta shiga ba a hankali ta juyo daidai ɗago idanuwansa suka ƙara haɗa ido, sai duk ta daburbu ce"Hmm...hmmm.Hajiya tana sama bari na kirata" Tana gaya tayi saurin barin gurin. Taɓe baki yayi da ɗaga kafaɗa a ransa ya ce"Useless girl kamar na tambayeta!" Ta daɗe tsaye a sama tana mai da numfashi sosai take a tsora ce tun ranar da ta fara ganinsa mugun tsoransa ya shiga zuciyarta, sai da ta dawo daidai sannan ta fara ƙwanƙasa ƙofar Hajiyar Bayan ta bata izinin shiga ne ta shaida mata tayi baƙo a waje sannan ta fito, sim-sim ta wuce parlourn kamar munafuka. Hajiya na sakkowa taga Aliyu ne ta saki fara'a, "Abuturrab yau an tuno dani kenan?" Ta faɗa cikin harshen turanci. Yana murmushi kansa a ƙasa ya ce"Sorry Mom aiyuka ne sukayi yawa" "Maganarka kullum kenan! To Allah yasa mudace" Gaisheta yayi ta amsa ba yabo ba fallasa, daman kuma haka yanayinta yake. "Tataah! Tataah!!" Ta ƙwala mata kira har sau biyu, da sauri ta fito daga ɗakin Hajara duƙawa tayi gabanta "Hajiya gani' "Ki kawowa baƙu abu ya motsa baki" Ƙanta a ƙasa ta amsa da "To'' Cikin sanyinta ta nufi kitchen. "Sannu da aiki Aunty" Tataah ta ce da Hajara "Yawwa Tataah" Ta amsa mata. Donut cake da chifs sai dambun naman kaza da drinks ta haɗa a saman triy tare da cup ta nufi parlour ƙirjinta na bugawa, center table ta jawo saitinsa tare da ajiyewa a sama, har ta juya Hajiya ta ce"Dawo ki zuba mishi idan kin gama ki kira Baby kice tayi baƙo" Da yake Baby Hajiyar ke kiran Baheerah. Ƙirjinta na bugun tara-tara ta dawo Hajiyar kuma ta haura sama, cup ta jawo tare da cika shi da juice zata buɗe dambun naman kazan ya ɗaga mata hannu, a rikice ta ɗago tayi tsaye jikinta na rawa gashi ta kafeshi da ido, shi kuwa fuskarsa na gefe. "Idan mayya ce ke sai dai kici kanki" Ya faɗa cikin wata siririyar murya da sauri tayi ƙasa da kanta dan har ga Allah bata san kallonsa take ba."Wai tsayuwar me kike? Ki ɗan bani guri ko naga haske mana, baƙa mummuna!" Da gudu ta far gurin hawaye na kwaranya a idaniyarta, ta daɗe tsaye bakin ƙofar Baheerah sai da ta goge fuskarta sannan ta shiga. Kwance take hannunta da waya da alama chating take, sallama Tataah tayi bata ɗago ba ta amsa mata sai dai fuskarta a sake take, kusa da ita taje ta zauna "Aunty Hajiya ta ce kije parlour kinyi baƙo" Da sauri ta ɗago "Baƙo!" ta maimaita sai kuma ta miƙe "Okey muje" Kallon shigar dake jikinta tayi, riga ce doguwa amma iyakarta gwiwa, yawancin irin shigarta kenan bata saka riga siket ko wando har ƙasa. Gyaran murya Tataah tayi "Amma Aunty baƙon namiji ne bai kamata ki fita haka ba" Murmushi tayi "No kar ki damu na saba da rayuwata a haka, zo muje" Ta doshi ƙofa, girgiza kai Tataah tayi "A'a ba sai naje ba Aunty" Dawowa tayi tare da kama hannunta suka fita. Tataah dai gabanta sai faɗuwa yake da haka suka ƙarasa parlourn. Shi kaɗai ne zaune, babu abin da yaci wanda Tataah ta kawo mishi, Baheerah na ganin Aliyu ne ta saki hannun Tataah tare da ƙarasawa da sauri kamar zata faɗa jikinsa sai kuma ta fasa tunowa da gargaɗinsa "Sannu da zuwa My Aliy!" Fuskarsa na kallon wani gefen ya ce "Yawwa" Zaunawa tayi gefensa "Kun gaisa da Mom?" "Eh" Ya bata amsa a takaice. Ƙara jawo center table ɗin tayi gabansa tare da fara ƙoƙarin buɗe masa "No karku buɗe na ƙoshi" "Haba dai Aliyu, bai kamata ba ace baka taɓa komi ba" Kallon kayan yayi, baiyi niyyar ci ba amma Baheerah sai da ta buɗe mishi komi ya ɗan taɓa kaɗan suna hira jefi-jefi. Juyowa tayi da niyyar kiran Tataah taga wayam, domin tun lokacin da ta saki hannunta ta ruga itama tayi baya da sauri ta bar parlourn. Kusan