Author : UMMU AFFAN Category : African Stories & Novels
nan zan dawo" "Tom Dad Allah ya dawo da kai lafiya" Da "Amin" Ya amsa tare da katse kiran. Bin wayar yayi da kallo yana tunanin me zai sa Daddy sanar da shi ciwon Baheerah? Tabbas ɗiyar amininsa ce amma bai taɓa kawo hakan a zuciyarsa ba 'Allah yasa ba sanar da su tayi abin da ta sanar masa ba" Mtsuww! Yaja tsaki idan ma sanar dasu tayi can dasu gada shi ba ruwan shi. Gado ya faɗa domin yana san ya more hutunsa na satin da ya ɗauka kafin a koma fagen daga, kusan sha ɗaya ya farko wanka yayi tare da brush ya nufi part ɗin Ammi dan ya gaisheta. Ba kowa parlour yasan da wuya ma idan ta tashi fita yayi tare da wucewa gidansu Faruuk can ya karya Mami ta ce"Wallahi gara kuyi-kuyi aure ko ma huta da ciyar daku" Ƙasa yayi da kai bai ce komi ba daman tasan da wuya ta tanka miskili kenan kafi mahaukaci ban haushi, bayan ya gama office ɗin Faruuk ya wuce can ya kusan awa uku sallar Azhar ta fito dasu bayan su idar yayi mishi sallama ya nufi hanyar gidan saboda miscalls ɗin Ammi da ya gani kusan biyar lokacin suna sallah ta kira shi. Yana hanya tun daga nesa ya hango kamar mutum na gudu a titi haka dai yaci gaba da rahowa hr zuwa lokacin da ya ƙaraso gab da ita a tunaninsa mahaukaciyace saboda yadda take gudu tana waugen bayanta, duk ƙoƙarin kauce mata da yake amma haka ta tunkarosa wani wawan burgi yaja daidai ƙafafuwanta ganin yadda ta zube masa a gaban mota ne yasa shi fitowa da sauri.
Ya daɗe yana kallonta ba tare da ya ce komi ba kusan na minti biyu, kafin ya koma motarsa baya yaja ya kauce mata tare da fusgar motar a sittin. Nannauyiyar ajiyar zuciya ta saki tare da bin bayan motar shi da kallo, ta daɗe a gurin kafin ta tashi jiki a sanyaye ta fara tafiya a hankali domin ƙafafuwanta ba kaɗan suke mata zafi ba, tunani ta fara ta nufi guda ko ta koma gurin Madam? Tasan muddin ta koma gida Gwoggo sai ta kusan kasheta da bugu, gurin Madam kuma tana tsoro karta koma Alhajin nan ya kuma kamata, wannan shi ake kira da gaba giwa baya siyaki, haka tana sharar ƙwalla ta nufi hanyar da zata sadata da gurin Madam domin ba wai gudun Gwoggo kawai take tsoro ba har da irin hukuncin da zata ɗauka akan Ummanta a yadda take ji da ka taɓa Ummanta gara ita ka mata ko mene ne. Taci sa'a baya gurin cike da ƙwarin guiwa ta ƙarasa. Madam na ganinta ta kamota da sauri tare da turata wani ƙaramin ɗaki. "Tataah kin san abin da kika yi, kin san wane ne wannan mutumin a ƙasar nan?" Tuni hawaye ya fara ambaliya a fuskar Tataah. Madam ta dubeta cike da tausayawa ta ce"Ya tafi amma ya ce ba zai barki ba sai ya hukuntaki, wallahi Tataah ina jin tausayinki a zuciyata a shawarce ki ajiye aikin nan" A hankali ta ɗago "Allah yasa haka shine mafi alkhairi, da mutumcina ya zube gara na bar aikin" Kularta ta ɗauko Madam ta zuba mata abinci kamar na kullum sannan ta biyata kuɗinta har da ƙari tare da mata fatan alkhairi, jakarta da babban hijabinta ta ɗauko sukayi sallama, tana tafe tana hawaye da tunanin makomar rayuwarta a gaba, shin ya gobenta zai kasance? Ta bar aikin da take samu suke ɗancin abinci a wani sau ɗaya ita da Ummanta yanzu ta bar aikin ya zasu kasance? Ga babban tashin hankalinta Gwoggo wanne irin mataki zata ɗauka idan taji ta bar aikin? Da wannan tunanin ta tare ɗan napep yau ko tayin bata da zarrar yi saboda hankalinta ba a kwance yake ba.
Ko da ta sauka ta biyashi tafi minti biyar tsaye ƙofar gidan kafin ta shiga jiki sanyaye. Ba kowa tsakar gidan hakanne yasa cikin sauri ta shiga ɗakin Ummanta, tana nan kwance kamar yadda ta barta da sauri ta ƙarasa tare da jinginar da ita jikin bango dan tasan ta gaji da kwancin "Sannu Umma!" Ta furta hawaye na zubo mata, ƙura mata idon da tayi ne ta gane tambayarta take yi me ya faru? Kukan da take dannewa ne yaƙi dannuwa ta fashe da shi amma a hankali domin bata san Gwoggo ta gane ta dawo gidan. Nan take ta fara ba Umma labarin abin da yw faru domin Ummar na jin komi amsawa ne kawai bata iyawa, sai gani tayi Umman na hawaye da sauri ta fara share mata "Umma bana so kina kuka, wannan yana ɗaya daga cikin tarin jarabawata kar ki damu" Sai ita ta dena hawayen domin Umma ma ta bari, hakan yasa ta jawo kular tare da buɗe abincin tasa cokali tare da kaiwa bakin Umma amma sai taƙi buɗe bakin daman daƙar take buɗesa kaɗan-kaɗan take ci, ganin hakan yasa Tataah cewa"Dan Allah karki sa wannan damuwar a ranki komi zai zo cikin sauƙi" Da ƙyar ta samu Umman taci sai ta rufe musu sauran da dare ta ɗauko na ledar da ta zuba da Farhan ya bata taci. A ɗaki tayi akwalar sallar azahar tayiwa Umma sukayi tare basu daɗe da idarwa ba aka kira la"asar duk suka gabatar.
Kwanciya tayi domin wani zazzafi ne ke damunta duk da yamma ce kasa ƙin kwanciyar tayi, baccin wahala yayi gaba da ita Umma nata kallonta har ta farka wajen shidda na yamma. Miƙa tayi tare da hamma fitsari take ji sosai hakan yasa ta ciro kuɗin da Madam ta bata ta ciro ta irga daidai wanda take bata kullum sauran ta ɓoye domin kuɗi sosai ta bata. Fita tayi ba kowa kamar ɗazun daman Gwoggo ko yaranta basu fiya zaman tsakar gidan ba, sun fi son rayuwar jin daɗi a rayuwarsu. Hakan yasa buta ta ɗauka tare da shiga banɗaki ta rage mararta, tana fitowa Ruhaima na shugowa cikin wata banzar shiga da bata dace da ita ba a matsayinta na musulma tana wani taunar cingam ji kake "Ƙas! Ƙass!! Ƙasss!!!" Tana gaba Tataah na bin ta a baya har suka shiga madaidaicin parlourn na Gwoggo. Ruhaima ta saki ɗan mayafinta wanda dashi gara babu a saman matsagaitan kujerun parlourn tana furta "Wash! Yau na gaji" "Sannu Ruhaima bari in kawo miki ruwa da abinci kici ki kwanta ki huta" Shugowar Tataah ne yasa Gwoggo ɗaure fuska tana bin ta da wani mugun kallo, da sauri ta zube "Sannu da gida Gwoggo!" Hannu ta miƙa mata "Ba sannu na tambayeki ba danƙa min" A sanyaye ta miƙa mata kuɗin, irgawa tayi daidai na kullum tare da cewa "Tashi ki fitar mini a parlour" Ruhaima ta ce"Gwaggo ki basu abinci na yau dan Allah" Da sauri ta juyo da cewa "Karki haɗani da Allah Baby bazan iya basu ba" "Tashi ki fita!" Ta daka mata tsawa, da sauri ta miƙe ta fita. Jiri take gani sosai tasan ciwon goshinta ne ya sakar mata da zazzaɓi ga gudun da tasha ɗazu, tana shiga ɗaki kuɗi ta cira tare da fita, tana tafe tana layi, gashi duk inda ta duba bata sami chemis ba, hankalinta ya tashi sosai ta nufo hanyar gida. Titi ta hau ba tare da ta sani ba, tun daga nesa yake danna mata hurn amma bata sani ba saboda yadda taji zazzaɓin ya fara hawar mata kai tafiyar kawai take ba tare da tasan inda take cilla ƙafafuwanta ba. Daidai ƙarasowar motar daidai zubewarta a gurin a sume, a furgice ya fito daga motar duk da yaga ba wai bugeta yayi ba amma yanayin da ya ganta da alamar tana neman temako shi kuwa Faruuk Allah yasa masa zuciyar tausayi ga fara'a dawowarsa daga wajen aiki kenan yau yayi yamma sakamakon wani aiki da yayi.
Birkito da ita yayi nan take idanuwansa ya sauka akan fuskarta 'Tataah!' Ya ambaci sunan da ta faɗa musu ranar shi da Ma'aruf. Da sauri ya kinkimeta sai cikin mota inda ya tada ya nufi wani private hospital dake kusa da gurin, yana zuwa ƙara surarta yayi cikin asibitin nan take aka fara bata temakon gaggawa. Faruuk sai safa da marwa yake a harabar gurin ya kasa zama ji yake tamkar ƙanwarsa Nanaah da suke ciki ɗaya ce babu lafiya, kusan awa guda kafin Likitan ya fito da sauri ya nufe shi, tun kafin yayi magana Doctor ya ce"Kwantar da hankalinka ta farfaɗo, zazzaɓi ne me zafi na maleria sannan ciwon goshinta ma ya ƙara assasa mata zazzaɓin sannan tana da ulcer" Numfashi ya sauke a hankali tare da furta "Na gode Doctor zan iya ganinta?" "I Zaka iya amma ta samu bacci saboda mun mata allurar bacci tana buƙatar hutu sosai" Gyaɗa kai yayi tare da nufar ɗakin da aka kwantar da ita, tun da ya shugo idanuwansa ke kan fuskarta da tayi fayau sai ciwon goshinta da aka wanke mata shi ga allurar ƙarin ruwa liƙe a hannunta. Kujera ya jawo ta zaman masu jinya ya zauna har lokacin idanuwansa na kanta, kusan minti ashirin yana zaune gurin kafin ya miƙe da sauri jin wayarsa na ringing Mami ce ya ɗauka da sauri "Faruuk lafiya har yanzu baka shugo gida ba?" Yana ɗauka yaji muryar Mami na tambayarsa. Numfashi ya fesar ya kalli gadon da Tataah ke kwance "Lafiya ƙalau Mami wata yarinya na kaɗe da mota shine na kawota asibiti yanzu haka ina can" Kawai ya tsinci bakinsa da furta wannan kalmar. "Asibiti ya jikin yarinyar?" Mami ta tambaya a kiɗime "Ki kwantar da hankalinki ba wani ciwo taji me yawa ba yanzu haka an sa mata ƙarin ruwa ta samu bacci" "To Allah ya ƙyauta gaba, wanne asibiti ne?" Sunan asibitin ya faɗa mata tare da yanke kiran. Kusan minti talatin sai ga Mami tare da Nanaah sunzo hannunta riƙe da kwando da kulolin abinci. Kasancewar asibitin bai da wani girma sosai yasa tana shugowa basu sha wahalar gane ɗakin da suke ba. Bakin gadon ta ƙarasa bayan Faruuk ya amshi kwandon hannunta yana mata sannu, gabanta ya buga da ƙarfi ta ƙure Tataah da kallo kafin taja numfashi "Allah ya bata lafiya" Suka amsa da amin ya ce"Mami bare naje nayi sallah banyi magrib ba" Ta ce"Sai ka dawo" Fita yayi ya bar Mami da Nanaah ya nufi masallacin dake asibitin...
This book is not free. it's N300 via 0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
Stanbic bank. Then u show ur evidence of payment whatsApp number 08104335144
*MU GANI A ƘASA...*
_Hot Love_
©FATIMA SUNUSI RABIU
UMMU AFFAN
_GAWURTATTU BIYAR._🔥
https://arewabooks.com/u/ummuaffan Follow me fans.😍
*Page 7-8*
"Umma! Umma!!" Tataah ta furta da ƙarfi tare da ƙoƙarin miƙewa. Da sauri Mami ta ƙarasa tare da riƙeta ganin tana niyyar cire ƙarin ruwan da ake mata, "Ki natsu kina asibiti ne!" Komawa tayi ta kwanta tana sauke numfashi tare da kafe Mami da bata san ko wacece ba da ido. Tea Mami ta fara ƙoƙarin haɗa mata kafin ta tasota zaune ta ce"Sannu ga tea bari na baki" Ƙasa tayi da kai bata ce komi ba, Nanaah ta kawo ruwa aka ɗauraye mata baki kafin Mami ta fara bata tea ɗin daidai shugowar Faruuk. Ƙure shi da kallo Tataah tayi a ƙoƙarin gano inda ta taɓa ganin fuskar, can ta tuno da shine ya taɓa taimakonta ana ruwa ranar. Sosai tasha tea ɗin saboda yunwar da take ji kawai ta isa ta sa mata ciwo, farfesun kaza Mami ta zuba mata ai kuwa ta lashe tas! Ganin irin kallon da Faruuk ke mata yasata jin kunya sosai tayi ƙasa da kanta. Ummanta ta tuna da sauri ta ɗago "Ina so na koma gida" Kafin Faruuk ya ce wani abu Mami ta maganantu "Baki lafiya fa, ki bada addres sai Faruuk ya faɗo musu kina asibiti" Da sauri ta fara girgiza kai idanuwanta suka cika tab da hawaye ta ce"A'a ba sai yaje ba, dan Allah a sallame ni na wuce wallahi naji sauƙi" Suna maganar likita ya shugo "Ah me jinyata taji sauƙi irin wannan zance" Ya faɗa da alamar yana da barkwanci. Tataah ta ce"I Na warke dan Allah likita ka sallame ni gida zani" "Ai ƙya bari zuwa gobe ko? Bai kamata a sallame ki yanzu ba" Cewar likitan. Mami ta ce"Nima abin da nake faɗa mata kenan!" "Wayyo Allah! Ummata" Ta furta hawaye na zuba "Umma!" Faruuk da bai san kalmar ta fito ba sai jin sautin ya yi "I Umma, dan Allah ka mayar dani gurin Ummata" Ta faɗa tana hawaye domin bata jin zata iya kwana wani guri ba tare da Ummanta ba. "Likita kawai ka sallamemu, ka haɗa mana duk maganin da kasan ya dace" Faruuk ya faɗa idanuwansa na kan Tataah wacce tayi saurin ƙasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta. Likitqn kwance mata robar ƙarin ruwan yayi saboda tuni daman ta ƙare amma cire allurar, bayan fitarsa Mami ta ce Nanaah ta gyara musu kayan basket ɗin. Minti goma bayan fitar likitan Faruuk yabi bayanshi kuɗi ya biyashi na komi ya bashi magungunan sannan ya koma ya ce su fito su wuce. Gida ya fara kai su Mami ta tun da kallonsa da mamaki shi ɗinma kasa ce mata komi ya yi bayan isarsa bakin gate ɗin, ganin ba zai ce komi ba ta ce"Ai sanake gidansu yarinyar nan zamu fara zuwa muba iyayenta haƙuri ko?" Sosai yake jin kunyar Mami a bisa ƙaryar da ya mata cewa bige Tataah yayi amma ya daure tare da cewa "Ku shiga gida naga dare yayi ne Mami bari ni naje kawai" Ko da yayi maganar ya kasa ɗago kai ya dubeta, ba musu ta cewa Nanaah ta sauka suje, kallon Tataah Mami tayi tare da dafa kafaɗarta "Ƴata Allah ya ƙara lafiya kiyi haƙuri da abin da ya faru sannan ki gai da mini Ummanki" Gyaɗa kai kawai tayi kanta a ƙasa, bayan fitarsu yaja motar ya doshi unguwarsu Tataah. Tun da ya hau titi bai ce mata komi ba ita ma kanta na ƙasa burinta kawai sanin halin da Ummanta take, Faruuk bai mance layin ba domin daidai ƙofar gidansu ya tsaya, sai lokacin ya juyo ya kalleta. A sanyaye ta ce"Na gode Yaya Faruuk Allah yasaka da alkhairi" Daga haka ta fara kiciniyar buɗe motar, magungunanta ya ɗauko tare da miƙa mata "Ga magungunanki ki daure kina sha kamar yadda likita ya rubuta miki zaki gani sannan ki dinga cin abinci akan lokaci" Da sauri ta ɗago suna haɗa ido ta mayar da kai ƙasa tare da amsa "Na gode" Ta fita cikin natsuwa, sai da yaga shigarta kafin ya sauke numfashi ya tada motarsa zuwa gida. Dare ne dan kusan tara da rabi hakan yasa ba kowa tsakar gidan ko da yake ko da rana ba cika zama sukayi ba, direct ta nufi ɗakinsu, hannu ta sa ta kunna gulop ɗin ɗakin da a kashe ta iske shi kuma akwai nepa. Tar! Idanuwanta ya faɗa ana Umma don ba bacci take ba, da sauri ta ƙarasa tare da ajiye ledar maganin ta nufi Umma "Kiyi haƙuri Umma wallahi ina can ina tunaninki" Ɗagota tayi tare da ɗibar ruwa ta bata sosai tasha ruwan, hawaye taji ya zubo mata ina da ta kwana ƙila da sai dai ta dawo ta taradda gawarta. Abincin ɗazun ta ɗauko tare da bata, ƙin amsa tayi tana ƙifta ido, ta gane abin da take nufi tana tambayarta inda taje ne "Umma na fita sayen magani kaina na ciwo ban samo ba, na faɗi a hanya wani ne ya temaka mini" Ta sanar da ita komi tare da jawo ledar maganin, kuɗi ta gani a ciki bandir guda gabanta ya faɗi ta ciro kuɗin tana juyawa tana zazzaro ido, Umma ma kallonta take ta ce"Shine ya saka min cikin maganin wallahi ko sanar dani baiyi ba" Ciro magungunan tayi tare da mayar da kuɗin leda ta ƙulle zuwa tayi ta ɓoye dan tafi tunanin ko bai sani ba kuɗin shiga shiga dan shi magani ne kawai ya ce ta amsa hakan yasa ta ɓoye da ƙudirin duk ranar da suka kuma gamuwa zata mayar masa da kuɗinsa.
Abinci ta ɗauko taba Umma sai da ta tabbatar ta ƙoshi sannan ta ajiye ɗan ragowar dan ita kam a ƙoshe take, magungunanta tasha tare da gyarawa Ummanta kwanciya ita ma ta kwanta a ranta tana mai ƙara jin tausayin Umman nata wacce daga ƙwanciya sai zama shima zaman sai an jinginata da bango. Tunani ta faɗa akan temakon da Faruuk ya mata Maminsa da ƙanwarsa ta tuno abin su gwanin ban sha'awa sai ta tsinci kanta da sakin murmushi. Da haka barci ya kwasheta.. Aliyu pov.
Cike da ɗacin zuciya yake tuƙin bayan barin shi gurin, yaja tsaki kam yafi cikin masaki "Mummuna me baƙar fuska!" Ya faɗa tare da fesar da wani huci me zafi, shi dai yarinyar bata mishi ba bai san dalili ba, ranar ya ganta a gidan abinci yau kuma a titi tana gudu anya ma kanta ɗaya? Ya tambayi zuciyarsa kafin ya ɗaga kafaɗa alamar bai dameshi ba. Yarinya ƙarama sai shegen gantalin tsiya daman matsalar ƴan ƙauye su shugo gari kenan. Da wannan tunanin ya ƙarasa gida, bayan ya shiga yayi parking kai tsaye part ɗin Ammi ya wuce. Sareenah zaune a parlour taci kwalliya kamar wacce zata gidan biki "Sannu da zuwa Yay..." Katseta yayi ta hanyar ɗaga mata hannu kafin ya ce"Ina Ammi?" Fuskarsa sam ba alamun wasa. Muryarta har rawa take wajen furta "Tana sama" Domin Aliyu va dai kwarjini ba. Cikin takunsa na isa ya fara taka saman ta bishi da kallo cike da so da sha'awa namiji har namiji irin mijin da take mafarkin samu, a fili ta furta "Wallahi tun da ina sonka duk yadda zanyi sai nayi ka zama mallaki, bari ka zama nawa sai ka gane kurenka" Zama tayi tare da ci gaba da kallon da take gefe guda kuma tana chart a waya. A hankaki ya tura ƙofar bedroom ɗin Ammi bakinsa ɗauke da sallama, zaune take bakin bed tana waya, saman kujerar dake ɗakin ya zauna jin da Daddy take wayar "Allah ya dawo da