Mu Gani A Ƙasa Gaskiya Ba Ta Mutuwa by UMMU AFFAN

Author :  UMMU AFFAN Category :  African Stories & Novels

Chapter   4 / 8

9K to 12K   out of 23.2K words

kai lafiya" Ta faɗa tana katse kiran, kafin ta ɗago ta kalle shi "Abuturrab" Ƙyawawan idanuwansa ya ɗago tare da sauke mata su. Ƙwarjininsa yasa abin da tayi niyyar faɗa masa ya kasa fitowa "Ammi kin kirani lokacin ina masallaci ne" Ya faɗa cikin sanyin murya. Ta ce"Abin da kake baka ƙyautawa Amma tun da jibi Daddynku zai dawo ai ya gani da idanuwansa" Ƙara zuba mata ido yayi ta gane nufinshi ƙarin bayani yake so yafi ƙarfin ya mata maganar ne, ƙarin tsaki taja tare da faɗin "Yau baka kwana gidan nan ba, ina ka kwana?" Kasa dena kallonta yayi yana mamakin Ammi yo shi ƙaramin yaro ne da za a masa wannan tambayar ko bai kwana gidan ba balle ya kwana. Ya ce"Gida na kwana" Wani kallo ta masa na ka rainani kafin ta ce"Ƙarya kake Abuturrab jiya nice parlour har wajen biyu na dare amma banji shugowarka ba" Bata san sanar dashi parlourn ta kwana saboda taji dawowarsa domin kar ya zargi wani abu. Ɗan smile ya saki dan da wuya kaga yana dariya yafi murmushi, "Na dawo, da yake Faruuk ne ya sauke ni a waje na shugo" Ƙura masa ido tayi kafin ta taɓe baki. Bai ƙara cewa komi ba, ganin shurun yayi yawa ne ta ce"Kayi mini zugun dan Allah tashi ka fita idan baka da maganar yi min" Da mugun mamaki yake dubanta sai kace ba ita ce tayi kiransa ba, to daman me zai ce yana jiran ji daga gareta akan kiran da take ta masa. Miƙewa yayi ba tare da ya ce komi ba ya doshi hanyar fita "Kaji Alhaji zai dawo jibi?" Ta wurga masa tambayar yana gab da fita "A'a!" Ya amsa mata tare da ficewa. Cije leɓe tayi wani abu na taso mata a zuciya, ta fesar da huci me zafi tana gyaɗa kai kamar wata ƙadangaruwa.
Da sauri Sareenah ta miƙe ganin fitowarsa, kai tsaye ƙofa ya nufa "Am Yaya Ali...." Kallon da ya mata ne yasata kasa iya ƙarasa abin da zata faɗa fuww! Ya fita daga parlourn, jagab ta zauna zuciyarta na mata zafi kamar wuta. Wayarta da ta fara ringing alamar ana kiranta ta duba ganin ƙawarta Layla ce yasa tayi saurin ɗauka"Layla kina ina ne?" "Gani a hanyar gidanku" Layla ta bata amsa. Ajiyar zuciya ta saki tare da furta "Sai kin ƙaraso" Ta ajiye wayar direct bedroom ɗinta ta wuce ta huci, kusan minti goma Layla ta ƙara so, "Reenah lafiya kike ta faman kai kawo?" Kasancewar ƙawayenta Reenah suke kiranta, zaunawa tayi bikin bed bayan ta dubi Layla ta ce"Hmmm! Ke dai bari, wallahi yadda Aliyu ke wulaƙanta ni abin na damuna" Ƙarasawa Layla tayi tare da zama kusa da ƙawar tata ta dafata da faɗin "Wai kina nufin har yanzu Aliyu bai shugo hannunki ko bakiyi aikin da aka saki bane?"
"Wallahi nayi sai dai my Aliy yana da wata kafaffiyar zuciya gani nake kamar magani baya cin sa" "Ƙarya ne!" Layla ta katse Sareenah ta ɗaura da cewa"Tun da asiri yaci Annabin Allah uban waye zai ce yafi karfin asiri? Tun da na wannan Malamin bai yi ba ki haɗa kuɗi akwai wani sai mu sake zuwa" Numfashi ta sauke "Ni wallahi har na fara gajiya da kashe kuɗi ba biyan buƙata" "Idan kin dena son sa shi kenan amma ai dole sai da kashe kuɗi idan ba a ci nasara a wannan ba ai a gaba idan da haƙuri juriya da jajircewa za a samu" "Haka ne kuma" Sareenah ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa "Tun da kikazo sai zuba muke bari in kawo miki ruwa" Tana faɗa ta fice.
Washe gari Tataah bata tashi da wuri ba, tun bayan sallar asuba da tayi ta koma, sanin cewa ba zata fita wajen aiki ba, kuma daman ba lafiya gareta ba ƙarfin hali ne kurum. Kwance take wajen misalin ƙarfe tara na safe, sai juyi take tana tunanin yadda zata iya wuni a gidan tare da Gwoggo da kuma tunanin abin da zata ce idan ta tambayeta dalilin barinta aiki, tasan wuya kam sai tasha, amma wuya bata kisa, cikin mutuwar jiki ta nufi hanyar kitchen bayan fitowarta daga ɗakin, har lokacin su Gwoggin basu tashi ba, hakanne yasa ta fara aiyukanta cikin kwanciyar hankali. Ta kusan idawa Ruhaima ta shugo, kallon sama da ƙasa tayiwa Tataah kafin ta kau da ka tare jawo ƙaramar tukunya ta kunna ƙarimin rishonsu ta ɗaura, Tataah na gurin tana aiki har ta gama tafa indomie ɗinta biyu da ƙwai biyu, ta zuba a plate tare da barin wata a ciki ta miƙawa Tataah, kallonta tayi sannan tabi rahowar Indomie ɗin da kallo, gyaɗa mata kai Ruhaima tayi alamar ta amsa, hannu tasa ta ƙarɓa tare da furta "Na gode." A hankali. Juye indomie tayi cikin ƙaramin plate ta ida komi da sauri ta shige ɗaki Ummanta ta ɗaya tare da bata taci kuwa sosai ɗan murmushi tayi da cewa"Umma kina san infomie naga kinci" Lumshe ido kawai tayi tana bin Tataah da kallo wacce taci ragowar indomie ɗin. Wuni tayi a ɗaki alwala kawai ke fitar da ita, haka Tataah ta ɗauki tsawon kwana uku tana huda ba tare da Gwoggo ta sani ba. Kwatsam yau ta fita alwalar sallar azahar Gwoggon ta fito sukayi kiciɓis, bin ta da kollo tayi a wulaƙance kafin ta ce"Ballaga gantalalliya yau kuma zaman me kike a gida" Gaban Tataah na faɗuwa ganinta bata yi tsammani ba, ƙasa tayi da kai kafin ta ce"Uhm...Uhmm...da...ma....daman ai...!" Duk cikin inda-inda take ta kasa ma furta abin da ya kamata duk ta ruɗe. Baba ne shima ya fito binsu yayi da kallo Gwoggo ta dube shi "Baban Sudees kana ganin gantalalliyar nan yau bata fita ba ko? Wallahi kuwa zata ga yadda ake gantalewa a gidan" Kafe Gwoggo yayi ta kallo wata tsawa tadaka mishi "Kallona na kiraka kayi ne Malam? Wallahi yau idan banji hujja me girma ba akan ƙin zuwanki aiki, sai na lahira ya fiki jin daɗi, da ni kike zancen!" "Kiyi haƙuri bana lafiya ne, shine Madam ta ce na dawo gida sai gobe naje!" Tataah ta tsinci bakinta da furta hakan domin mafita take nema.....


This book is not free. it's N300 via 0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
Stanbic bank. Then u show ur evidence of payment whatsApp number 08104335144
*MU GANI A ƘASA...*
_Hot Love_


© FATIMA SUNUSI RABIU
UMMU AFFAN


_GAWURTATTU BIYAR._🔥


https://arewabooks.com/u/ummuaffan


*Page 9-10*

Wani kukan kura da Gwoggo tayi sai gata ta shaƙe wuyan Tataah. Ƙarar azaba Tataah ta saki daidai ƙarasowar Baba yana ƙoƙarin ƙwatarta "Dan Allah Zainabu ki rabu da yarinyar nan" Wata bangaza ta tayiwa Baba sai gashi a gefe, ya yin da tacigaba da kaiwa Tataah duka ta ko ina, "Kiyi haƙuri Gwoggo!" Abin da Tataah ta iya furtawa kenan cikin tsananin wahala, dama gashi ba ta lafiya ga ƙarin dukan Gwoggo. Bata ƙyaleta ba sai da ta mata ligib kafin ta ce"Mu zuba ni dake, shege ka fasa ɗan halak kuma sai yanka, dan ubanki yanzu wake da isasshiyar lafiya wallahi duk wanda kikawa sannu zai amsa da kowa takanshi yake sai dai ta wani tafi ta wani amma kowa ba lafiyar nan gare shi ba. Har ni zaki faɗawa baki da lafiya shi ya sa kika ƙi fita aiki saboda ke ga isasshiya to nima bana lafiyar ubanki ma ba lafiyar gare shi ba kuma haka yake fita nima in fita ai daurewa kowa keyi dan yanzu a ƙasar nan dai kowa bashi da lafiya." Sosai Tataah ke kuka kanta a ƙasa ta kasa ɗagowa sai zubar hawaye da take, hakan kuwa ya ƙara ƙufular da Gwoggo ta kai mata wani mari wanda tsabar zafinsa yasa mata sakin fitsari bata san lokacin da ya fito ba. Duƙewa tayi a gurin tana kuka kamar ranta zai fita, tafin hannunta ɗaure akan kuncinta da ƙarfi kuwa ta runtse idanuwanta sakamakon wasu fararen taurari da ta gani "Shegiya me baƙar fuska da baƙin hali, wallahi gobe idan kika kuma zama baki fita aiki ba sai na illataki, wallahi sai na miki abin da ya taka wannan algunguma ƴar kaza-kazan uban can." Kan Baba ta nufa tana huci "Kai kuma munafiki zamu haɗu da kai, wai har ina mata hukunci kazo wai zaka tare ta?" Ummm tayi wani murmushin takaici kana ta ce"Kai game ƴa! Ƴar ma da kake ƙila wa ƙala akanta" Da sauri ya ɗago ido yana kallonta tare da girgiza mata kai bai iya cewa komi ba, dan mugun tsoranta yake ji. Fuuu! Ta wuce ciki tana huci kamar kumurci. A sanyaye ya dubi ƴar tashi "Komi yayi farko yana da ƙarshe da izinin Allah!" Abin da ya furta kenan yabi bayan Gwoggo. Wani kuka Tataah ta saki, sai da tayi mai isarta kafin ta wuce ciki, tana shiga Umma ta kura mata ido, saddar da kanta ƙasa tayi sam bata so Umma ta gane tana cikin wani hali dan kar ta sawa Umma damuwa a rai, gashi ba lafiya gareta ba... A yau Daddy ya dawo sosai Ammi tasa aka gyara ko ina ga abinci kala-kala da ake ta shiryawa na tarbarsa.. Abuturrab tun safe yana part ɗinsa yana bacci, wajajen ƙarfe sha ɗaya yaji wayarshi na ringing kamar ba zai ɗauka ba sai ya jawo wayar ganin Faruuk ne ya ɗanyi murmushi tare da amsa kiran "Anaci kenan lafiya zaka kirani da sanyin safiyar nan?" Girgiza kai Faruuk yayi daga ɓangaranshi kafin ya ce"Dalla Malam fito ina bakin gate" Gyara kwanciya Abuturrab yayi tare da cewa"Bacci nake kuma bana san takura please!" Ƙit ya katse kiran yana jan tsaki tare da ajiye wayar ya gyara kwanciyarshi yana sake naɗewa cikin bargo. Gabaɗaya yaci an yaye bargon da fushi ya juyo idanuwansa suka sauka a fuskar Faruuk "Lafiya Malam!" Ya tambaya a fusace fuskarshi ɗaure. Faruuk gyara tsayuwarsa ya yi tare da rungume hannayensa a ƙirji ya ce, "Tambaya kake ko neman sani? Abey Malam tashi muje, mutum ya duƙa bacci kamar wata mace saboda lalaci" Saurin yaye bargon da ya rufa ya yi ya tashi da sauri ya duro gadon yana jan tsuka "Mtsuw! Kai kasan kallo ɗaya aka mini an san jarumi ne ni" Yana faɗa direct ya yi toilet. Zaunawa Faruuk yayi gefen gadon yana dariya, daman yasan za a rina Aliyu bai san a kirashi rago ko kalmar dake kace-ceniya da hakan. Kusan mintina sha biyar Abuturrab ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa, ɗayan kuma yana goge sumar kansa, gaban mirror ya ƙarasa ya shafe jikinsa da lotion tare da buɗe durowa ya ɗauko doguwar riga ta jallabiya me matuƙar ƙyau da tsada. Taje sumar kansa yayi yana kallon Faruuk wanda shima idanuwansa yana kanshi "Haufa Guy!" Faruuk ya furta yana miƙewa, ɗan tsaki yaja yayi gaba yana furta "Ko kuturu ne kai akan naci haka ka barni haka" Faruuk na biye dashi har suka isa parlour, guri suka samu tare da zaunawa saman sofa. Faruuk ya ce"Kana ɓata mana lokaci fa Ma'aruf ya ce idan mun fito a kirasa ba zai iya zuwa zaman jira ba" Ya ƙarashe maganar da tsokana, kau da fuska Abuturrab yayi ba tare da ya ce komi ba. Ganin haka yasa Faruuk saurin tashi daga inda yake ya dawo kusa da Abuturrab cikin taushin murya ya ce"Please Aliyu idan zaka ka taso, idan kuma mu wuce ne shi kenan" Ɓata fuska yayi kafin ya ce"Da wucewar ku kayi da yanzu kunyi abin da ya dace, Faruuk kasan halina bazan iya zuwa gurin kuchakan yaran nan ba har na iya abin da kake tunani" A fusace ya miƙe cike da jin ɗacin kalmar da ya kira "Matar da zan aura ne kuchakar? Na gode Aliyu!" Faruuk ya fita da sauri. Taɓe baki yayi tare da ɗaga kafaɗa irin ko ajikin shin nan. Faruuk na fita Ma'aruf ya kira suka wuce duk abin da ya dace sai da sukayi sannan kowa ya wuce gida, tun da bikin ya ƙarato hankalin Faruuk duk ya koma can yana san zuwa duba cikin Tataah amma hidimar bikin kanshi sosai ya ɗauki zafi da komi kusan shi yake yi sai Ma'aruf dake temaka mashi amma sam Aliyu ya zare hannunsa kami da sha'anin auren. Faruuk ko ta kanshi ba yabi, har zuwa yau juma'a da ta kama bikin, shagali sosai ake babu masaka tsinke a gidansu Faruuk duk kuwa da girmansa, don shi ɗin ɗan dangi ne sosai. Ko yau da ake ɗaura auren Faruuk bai bi takan Aliyu ba harkar gabanshi kawai yake don yaji zafin kalmar da ya yaɓawa matar da zai aura Hibbah ta kuchaka shikam a haka yake ƙaunar abarsa. Baiyi tunanin ma zai zo ɗaurin auren ba abin mamaki sai gashi cikin wata ɗanyar shadda tamkar shine angon. Duk inda ya yi kallonsa ake tamkar wani tauraro, saboda ƙyawon da yayi cikin wata ɗanyar shadda marun tamkar shine angon har da malin-malin, masallacin sosai ya cika da al'ummar Annabi, bayan idar da sallar juma'a ne aka ɗaura auren Umar Faruuk Hassan da amaryarsa Muhibbat Kabir akan sadaki dubu ɗari biyar. Ana cikin ɗaurin auren kafin a tashi akaji muryar wani mutum na furta "Assalamu alaikum jama'a ga duk wanda ke buƙatar auren ƴata *Jameelah* ni mahaifinta zan bashi aurenta akan sadaki ƙalilan kai idan ma baka da kuɗin a yanzu? To zan baka aurenta a sadaka!" Gabaɗaya gurin ya ɗauki shuru baka jin motsin mutane ballantana kuma maganarsu, jin kowa yayi shuru ne wasu hawaye masu zafi suka sakko akan fuskar mutumin. Idanuwan sa ne suka faɗa akan fuskar Abuturrab shima kallonsa yake cike da mamakin uba irinsa. Gani yayi mutumin ya ƙaraso gabansa tare da ɗago shi, wani ikon Allah sai yaji ya miki mutumin ya buɗe baki da ƙarfi ya ce"AlhamduLillah wannan bawan Allah ya amince zai auri ƴata Jameelah!" Gaban Aliyu ya wani bada sauti me ƙara kamar yadda Faruuk da Ma'aruf suke dubanshi cike da mamaki, a tunaninsu shi ɗinne ya furta haka dan basa tunanin mutumin haka kawai zai ce ya amince, gaban limamin mutumin ya kai Aliyu wanda ya koma tamkar mutum mutumi yana duban uban wannan ƴa tamkar me taɓin hankali. Sai lokacin masallacin ya kachame da surutu na irin yadda Aliyu yayi shahadar wannan aure, su kansu limaman cike da mamaki suke, nan dai aka sa kowa yayi shuru kafin me ɗaura auren ya ce"Kana da sadaki a hannunka?" Mahaifin Faruuk ne wanda yaji tamkar an ɗaure mishi baki sai lokacinne ya iya cewa akwai kuɗi amma basu fi dubu ɗari biyu ba, Mutumi mahaifin ƴa ya ce dubu hamcin sun isa sadakin ƴarsa, haka Faruuk ya amsa gurin mahaifinsa aka bada inda nan take kuwa aka ɗaura auren Aliyu Muhammad Aliyu A.M.A da JAMEELAH Mahmud Abdullahi akan sadaki dubu hamsim. Abuturrab kallon mutane kawai yake tamkar wanda akawa asiri ko aka rufewa baki, ƙala ya kasa cewa har aka ɗaura auren inda mahaifin Faruuk ne ya wakilce shi. Faruuk ne ke masa wani kallo cike da al'ajabi "Angon Jameelah!" Yaji bakinsa ya furta daidai lokacin da Aliyu ya ƙaroso kusa da shi "Jameelah!" Ya furta ƙirjinsa na mugun bugawa da sauri da sauri, Mutumin nan kuwa na liƙe da Aliyu duk inda yaga yayi sai ya bisa, bayan angama komi aka fara watsewa mutumin nan ne ya kira Aliyu gefe, wata magana ya faɗa mashi da ni kaina ban jiyo ba sai wata ƙatuwar takarda wacce ko mene ne a ciki? Oho! Da ganan kuma sai ya nemi mutumin ya rasa, haka suka koma gida cike da al'ajabi. Anci gaba da gudanar da bikin Faruuk cikin farinciki ba wanda yasan da auren Aliyu sai wanda yaje gurin. Shi kuwa Aliyu tun da ya dawo gida bai kuma bi takan zancan ba, don duk a tunaninsa mafarki ne yayi ko kuma hasashe hakan yasa sam sai yaji ya manta da batun. Ƙatuwar takardar nan kuwa tun da ya buɗe durowa ya ajiyeta ya manta da batun ta.
Washe garin kammala bikin Faruuk ne, Daddy ya dawo sosai aka mishi tarba ta kece raini Ammi kuwa an ɗauki wanka na alfarma an shirya mishi abinci da nasha kala-kala. Misalin ƙarfe sha ɗaya na safe jirginsu ya sauka a filin jirgi na birnin tarayya Abuja direba ne yaje ya ɗaukosa, lokacin Aliyu na ciki yana bacci kamar kasa, har mamakin yawan baccinsa Faruuk yake yanzu domin ada ba haka yake ba. Daddy sai da yayi wanka sannan yazo yaci abinci Ammi sai nan-nan take dashi haka Sareenah cike da girmamawa take komi. Wajajen sha biyu na rana Aliyu ya shugo part ɗin cikin ƙananun kaya, tun da ya shugo Sareenah ke bin shi da kallo har ya sami guri ya zauna kusa da Daddynsa "Abuturrab!" Daddy ya kira sunansa. A hankali ya ɗago kai fuskarsa ɗauke da ɗan murmuahi ya ce"Welcome Dad!" Shafa sumar kansa Daddy yayi ya ce"Thank you Son! Fatan na sameku lafiya?" "AlhamduLillah Dad" Gyaɗa kai Daddyn yayi ya ce"Wai ya batun gurin aikinka? Ko kuwa sallamarka sukayi kazo zaman gida tsawon sati biyu?" "No Dad na amshi hutu ne saboda ina san na huta kuma ga bikin Faruuk amma AlhamduLillah jiya angama komi" "Ma sha Allah" Cewar Daddy ya ɗaura da cewa"Ummaru yayi aure saura kai kuma" Wani irin sauti ƙirjinsa ya bada tunowa da jiya an ɗaurawa Faruuk haka an ɗaura mishi" Girgiza kai ya fara a ranshi yana cewa"Ba haka bane, mafarki nayi" Daddy ya ce"Me yafaru ne kake girgiza kai kamar wani kaɗangare" Chak! Ya tsaya da girgiza kan tare da tuno abin da mutumin nan ya ce da shi...


This book is not free. it's N300 via 0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
Stanbic bank. Then u show ur evidence of payment whatsApp number 08104335144
*MU GANI A ƘASA...*
_Hot Love_


©FATIMA SUNUSI RABIU
UMMU AFFAN



*Wannan page ɗin sadaukarwa ne ga AMINATU SANI da kuma MAMAN YASEER da MINATU da HAJIYAR ALLAH, Comments ɗinku na sani nishaɗi Allah ya bar zuminci. Masoya littafin nan duk kuna raina ina ƙaunarku tamkar yadda kuke ƙaunar MU GANI A ƘASA... Tabbas kuna nunawa labarin ƙauna na gode.*


_YA KUSA FITA KASUWA, MAI BUƘATAR BUGAGGENSA 1K NE

4 / 8