Author : UMMU AFFAN Category : African Stories & Novels
minti talatin yana gidan sannan yayi musu sallama kuɗi ya ajiyewa Baheerah ya fita, har wajen motarsa ta raka shi sannan ta koma ciki, ganin har an fara yayyafi gari na ruwa. Hurn yayi maigadi ya buɗe masa yana tafe yana tunanin wai a hakan Daddynsa yake so ya auri Baheerah tana da natsuwa da sauƙin kai amma shi yana mata kallo rashin tarbiyya sam baya jin Baheerah ta dace da tsarinsa. Ganin yadda take gudu a saman hanya ya sashi dallareta da fitilar motarsa, duk ruwa ya jiƙata har rawar ɗari take ganin yadda aka hasketa ta cure jikinta tare da ƙamƙamewa guri guda nan take ta fara hawaye, ƙura mata ido yayi kafin ya kashe hasken, har ya yi gaba sai kuma ya dawo ganin yadda ta tsugunna tana kuka ruwan nacigaba da dukanta. Tataah Ganin me motar ya dawo duk da bata san waye ba ta taso da sauri ta nufi motar, bata jira cewarsa ba ta shige ciki ta zauna kujerar gaba........
This book is not free. it's N300 via 0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
Stanbic bank. Then u show ur evidence of payment whatsApp number 08104335144
[8/29, 5:23 PM] Sadfat: *MU GANI A ƘASA...*
_Hot Love._
©FATIMA SUNUSI RABIU
UMMU AFFAN
*Page 17-18*
Ƙoƙarin cire hijabin jikinta take saboda jiƙewar da yayi sosai ya haifar mata da jin sanyi, ga shi ita ba shiri suke da sanyi ba yanzu ta fara ciwo, rigar sanyin dake jikinta ma ta jiƙe, hawaye kawai tacigaba da zubarwa kafin ta ɗago ta ce"Mu tafi ma...." Ai ganin wane ne bata san lokacin da maganar tata ta maƙale ba, tayi saurin yin ƙasa da kanta jikinta na rawa kamar ana kaɗa mata mazari. "Idan kin gama shirmen naki zaki iya fitar mini a mota" Gabanta ya kuma faɗuwa lokacin da ta waiga waje ta ga yadda ake ruwa kamar da bakin ƙwarya. "Ki fita nace!" Ya faɗa da ɗan ƙara, a gaskiya sai dai ya kasheta amma bata jin zata iya fita cikin ruwan nan, juyowa tayi cikin rau-rau da fuska ta ce"Kayi haƙuri"
Kau da fuska yayi daga kallonta, ganin yaƙi tafiya a hankali ta buɗe murfin motar, sai dai ruwan da taji ya feso mata ne yasa ta rufewa da sauri. Kuka ta saki, bin ta yake da kallo cike da mamaki, "Ke lafiya?" Ya tambayeta fuskarsa a ɗaure "Kayi haƙuri ruwa ake yi" Ta faɗa cikin kuka, bai sake kulata ba yaja motar, nannauyiyar ajiyar zuciya ta saki ganin ya fara tafiya cikin sauri ta sanar dashi unguwar da zata, bai kulata ba har suka isa, "Ga layin nan" Ta nuna masa da hannunta, kallon da ya jefeta da shine yasa ta saurin yin ƙasa da kai ta buɗe murfin motar don zuwa lokacin ruwan yayi sauƙi sosai sai yayyafi da ake, sai da ta fita a hankali ta ce"Na gode" Tare da rufe mishi murfin da mugun gudu ya bar gurin. Girgiza kanta tayi tare da gangarawa layinsu. Sosai ta shiga halin damuwa ganin yanayin da ta taradda Ummanta, duƙawa tayi saitinta tana girgizata "Umma! Umma!! Dan Allah Umma ki tashi" Idanuwan da Umman ke buɗewa yau a kafe ta gansu sai girgizata take amma bata motsi, da gudu ta fita tana kiran "Baba! Baba!!" Gwoggo ce ta fito tana jefa mata wani kallo ta ce"Lafiya?" Tana kuka sosai ta ce"Ummana ce bata lafiya ko motsi bata yi!" Taɓe baki Gwoggon tayi da cewa"Yoni ina ruwa na, ta mutu mana, shi kuma tsohon kin manta yayi tafiya ne?" Sosai kukanta ya tsananta, ta koma baya da gudu, faɗawa tayi jikin Umman bayan shigarta ɗakin, "Ki tashi Umma" Abin da take iya gaya kenan. Amma sam ko motsi Umman batayi, a ranar haka ta kwana jikin Umma tana kuka ko runtsawa bata iyayi ba, garin Allah na wayewa ta fita a rikice gidan moƙocinsu Alhaji Barau ta shiga, bakinta ɗauke da sallamar suna zaune parlourn suka amsa mata zubewa tayi a gurin nan take hawaye suka fara zubar mata "Me sunan wannan yarinyar me ya faru?" Matar Alhaji Barau Hajiya Sabuwa ta tambayeta kasancewar sunan ɗiyarta ta fari gareta shiyasa bata kiran sunanta. Cikin kuka ta ce"Tun jiya da dare da na dawo Ummata bata motsi" "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un muje gidan naku" Ta ɗauki mayafinta dake gefen kujera ta saka ɗanta na biyu Fahat yafi bayansu. Sosai Hajiya Sabuwa ta shiga tashin hankali ganin halin da Ummar Tataah take ciki. "Fahat maza gida ka kira me gadi kazo mu kamata asa a mota mu kaita asibiti" Ta faɗa cike da damuwa, har Fahat ya juya sai ya tsaya sakamakon maganar Gwoggo, "Ba zai yuwu ba, ai mijinta yana sane da halin da take ciki bai kaita asibitin ba dan cutarta ba ta asibiti bace, idan an kaita asibiti ma asarar banza za ayi don ba warkewa zatayi ba" Hajiya Sabuwa ta ɗago cike da tsananin mamakin jin furucin Gwoggon "Haba Zainabu wannan wacce irin magana kike? Baki ganin halin da take ciki ne?" "Ko wanne irin hali take ciki wai ina ruwanku? Shisshigi da ƙwalata da ƙwala kai a faranti kawai, to Malam ya ce kar in sake nabar wani ya fitar mashi da mata daga gida saboda haka kome zai sameta ba ruwan wasu aha" Gwoggo ta faɗa cikin zallar son zuciya. Numfashi Hajiyar ta fesar masu zafi cike da jin baƙin cikin kalaman Gwoggo, Fahat ne ya figi hannun Mahaifiyarsa cike da ɓacin rai suka bar gidan. Tataah ta kuma sakin sabon kuka sakamakon dangwashin da Gwoggo ta aika mata "Munafuka ƴar banza kawai, ke har kinsan ki kira maƙota saboda tsabar wulaƙanci da shegen kinibibi, ai na faɗa miki uwarki Balki a haka zata ƙare rayuwarta" Zubewa Tataah tayi gurin tare da ɗaura hannu a ka tana kuka, bayan fitar Gwoggo rarrafawa tayi gurin Umma tana sake sakin wani kukan cike da tausayin rayuwarsu, ganin kuka ba zai yiwa Ummanta maganin komi ba tashi tayi ta ɗauro alwala tazo ta dunga gabatar da sallar nafila da roƙawa Ummanta samin sauƙi gurin sarki Allah gagara misali. Ƙarfe tara na safe Gwoggo ta leƙo ɗakin "Wai algunguma ba ki tafi wajen aikin ba ne?" Kasa ɗago kanta tayi 'Wanne irin aiki kuma Ummana tana cikin wannan halin' Ta faɗa a zuciyarta, Gwoggo ta sake katse mata hanzari "Tataah magana fa nake miki, ko so kike kwana ɗayan nan da bakije ba ya jawo mana wata matsalar?" Tuni hawaye suka wanke fuskarta "Gwoggo kiyi haƙuri bazan iya barin Ummata cikin wannan halin na tafi aiki ba" "What? Ni nake magana kema kikeyi? Har wuyanki yayi kaurin ina magana kina yi? To maza ki shirya ki tafi aiki kafin na kassara rayuwarki, ƴar banza mai mugun hali na gado" "To!" Ta faɗa a sanyaye cike da tashin hankali, haka tanaji tana gani tabar Ummanta a cikin wannan mawuyacin halin, sai dai ko a gidan aikin ba ta samu wani natsuwa ba haka take duk a furgice Hajara da Baheerah ne suka tambayeta me ke damunta, sai kawai ta ce musu bata da lafiya ne... Abuturrab yana tafe a motarsa yana jan tsaki da haka ya ƙarasa gida, kai tsaye parlourn Daddynsa ya wuce can ya same su tare da Ammi bayan ya gaishe sune yake sanar da Daddy yaje gidan su Baheerah ne, Ammi wacce ko da ya gaisheta amsawa tayi a daƙile jin abin da ya ce ta juyo a rikice. "Baheerah kuma! To me ya kai ka gidan?" Ta tambaya cikin sauri, bai ɗago ba Daddy ne ya ce"Aliyu jeka zamuyi magana" "To Daddy na gode!" Bayan fitarsa Ammi ta ce"Alhaji ya ina tambayarsa kuma ka ce ya tafi?" Gyara zama yayi "Dan Allah Saratu ki kwantar da hankalinki, Baheerah ɗiyar aminina ce kuma kin san da alƙawarin aure tsakaninsu da Aliyu" A fusace Ammi ta ce"Wannan ai zancen banza zancen yofi ne! Alhaji me kake son bayar da ni ne? Bayan waccen maganar ta auren gantali ta aka masa yanzu ma wata kake so ya aura bayan kasan son da Sareenah take mishi?" Girgiza kai yayi "Amma dai kin san bazai yuwu nayi watsi da maganar da mukayi da aminina ba domin yarjejeniya ce tsakaninmu tuni, ke kin san abin da ya faru a lokacin" "Ba wannan magana, don kowa nasa ya sani Sareenah har suma ta dunga yi da taji an ɗaura auren Aliyu waccen koron yanzu me kake so taji? Ko kashe mini ƴa kuke son yi ne?" Miƙewa Daddy yayi ya wuce bedroom yana cewa"Ni dai na gama maganata, bazaki raba mini hankali guri buyu ba" Ganin zai shige ciki da sauri ta ce"To mu gani a ƙasa...'' Shima juyowa yayi da cewa"Zaku gani kuwa!" Ɓam ya rufo ƙofar, zuciyar Ammi ta soyi miƙewa tayi tana zagaye parlourn Layla ce ta tuno da sauri ta koma parlournta ta wuce sama, wayarta ta ɗauka tare da kiran lambarta bigu biyu ta ɗauka. "Layla wai ya maganarmu ne?" "Ammi ki kwantar da hankalinki, yanzu haka aikinku ne akeyi, Aliyun ne yana da taurin kai shiyasa har yanzu ba a sami yadda ake so ba" Numfashi ta fesar ta ce"Layla yanzu haka maganar da Alhaji yake wai Aliyun ma wani auren zaiyi! Shiyasa hankalina ya tashi" "Wani auren kuma Ammi?'' "Eh wallahi shiyasa na kiraki ba shiri, hankalina a tashe yake bana son Sareenah taji wannan maganar mu kammala komi dan Allah sannan har Alhajin a ɗaure mini bakinsa dan na lura shima kamar baya son Aliyu da Sareenah" Ajiyar numfashi Layla tayi ta ce"To Ammi dole yau na koma gurin shi tun da wata sabuwar kuma ta ɓullo" "Shiyasa na kiraki da wuri kafin abin yayi nisa" "To ki kwantar da hankalinki shi da aikinsa yake tamkar yankan wuƙa kafin ayi ne dai" "To Layla na gode zan miki transfer ta account ɗinki" "Badamuwa Ammi" Sauke wayar tayi a kunne, sai da ta turawa Layla dubu hamsim sannan ta ajiye wayar tana saukar da numfashi, a fili ta ce"Wallahi Alhaji daga kai har Aliyun sai kun dawo tafin hannu na, daman a nan kuke aikina ne yayi sanyi yanzu kuwa na dawo da zafina na.... "Hajara lafiya Tataah yau ba ta zo aiki ba?" Baheerah ta tambayi Hajara yanayinta da ɗan damuwa. "Wallahi uwar ɗakina ban san dalili ba, sai dai kin san ance jiki da jini halan ko bataji daɗi ba ne, kin san yau da gobe sai Allah nima tun ɗazu nake maganarta a zuciyata, yawwa kuma jiya da tazo kin san ta ce mana bata lafiya" Numfashi Baheerah ta saki hmmm tare da cewa" Haka ne kuma, Allah ya ƙare mu da lafiya" "Amin" Hajara ta amsa taci gaba da aiyukanta, Baheerah kuma zame jikinta tayi tare da ƙwantawa saman kujerar da take kai, sosai take jin ba daɗi na rashin zuwan Tataah yau. Ta shaƙu da yarinyar jinta take tamkar jini da tsokar jikinta. Tana nan kwance har aka kira sallar azahar Allah sarki Tataah ce ta faɗo mata domin idan har an kira sallah taga tana kwance tana chating zata ce"Aunty Baby an kira sallah ki taso muje muyi!" Ɗan runtse idanuwanta tayi ji tayi kamar ita ce ke gaya mata a yau ma, kitchen ta shiga inda taji motsin Hajara ta ce"Waini Hajara baki san gidansu Tataah ba ne?" Barin abin da take tayi tare da dawowa jikin ƙofar ta ce"Uwar ɗakina ban sani ba, kin san yarinyar da sanyin hali ba komi nata take buɗewa ba." Wucewa Baheerah tayi domin jikin ta taji yana bata wani iri, ranar haka ta kwana babu sukuni. Washe gari ma har ƙarfe sha biyu Tataah bata zo aiki ba, hankalin Baheerah ya tashi sosai, sama ta hau gurin Mom ɗinta. Bayan ta shiga Mom ta kalleta "Baby lafiyarki ƙalau kuwa, naga duk kinyi wani sanyi" Shafa gefen fuskarta tayi "Lafiya nake Mom, dan Allah kin san gidansu Tataah ne?" "A'a me ya faru?" Tagumi tayi, "Mom yanzu baki san gidansu ba kika ɗauketa aiki?" "To taya zan san gidansu ni kuwa Baby? Sai dai ina da number ɗin wacce ta kawota aikin" "Yawwa Sweet Mom ɗan bani ko kira mini ita ma zata fi saurin ɗauka" Ba musu Mom ta kira lambar Gwoggo bugu biyu kuwa ta ɗauka "Hajiya Ina wuni!" Tun kafin Mom tayi magana ta gaisheta cike da ladabi. Baheerah ta ce"Mom ki tambayeta me yasa Tataah bata zuwa jiya da yau?" Tambayar Mom tayi mata bayan ta amsa gaisuwar, rawar baki Gwoggo ta fara "Eh....am...Hajiya kiyi haƙuri bata da lafiya ne" Da yake cikin ƙarar murya ta saka Baheerah tana ji, sai ta ce"Ki ce ta faɗi addireshin zamu zo ni da Hajara" Baki na rawa Gwoggo ta faɗa musu addireshin kafin suyi sallama, da sauri Baheerah ta sauka ɗakin Hajara ta shiga ta faɗa mata zasuje gidansu Tataah ta shirya sannan ta faɗa mata addireshin "Kin san wajen?" "Uwar ɗakina nasan dai unguwar amma layin idan munje sai mu tambaya" ''To badamuwa ki shirya nima bari naje na shirya" Wata riga iya guiwa ta saka tare da gyara gashin kanta me tsawo ta ɗaura ribon, har ta kai ƙofa sai ta tsaya tunowa da maganar da Tataah ta taɓa yi mata wata rana. "Aunty Baby ba dai a haka zaki fita ba?" "To mene ne don na fita haka? Kin san ban saba da rayuwar nan ba" Girgiza kai Tataah tayi ta ce"Ya kamata kam ki saba Aunty domin rayuwar nan da ta can tana da tarin banbanci, ke musulma ce ya kamata ki suturta jikinki idan zaki fita, mutumci mace shine tarbiyyarta kamalarta kuma shigarta, wani ko yaso yiwa mace maganar banza ya duba shigarta zai gane ita ba ƴar banza bace shiga na ƙarawa mutum kamala da mutumci a idanuwan mutane kuma shigarka ita ce mutumcinka" A wannan ranar sai da Baheerah ta canza kaya yanzu ma drowwer ta koma tare da janyo wata doguwar riga har ƙasa ta saka ta yane kanta da ɗan kwalin rigar, ita kanta sai tajita cikin mutumci ba kamar ɗazun ba. Ɗakin Hajara ta shiga ita ma ta gama shiryawa hijab ta saka suka fito harabar gidan, motarta ta shiga Hajara ma ta shiga tayi mata key tare da barin gidan a sittin......
🤔 *Me ya faru da Tataah kwana biyu bata zuwa gidan aiki???????*
_Duk wacce bata biya ma ta hanzarta domin shine na kusa da ƙarshe a free pages, …... Ake jira to, amma dai Hajiyata harkar girma kawai kar ki tsaya jiran a sato ki karanta wannan ƙaranta ce, kuɗin littafin nan daidai aljuhun kowa ne. Don haka ku biya ku karanta ba tsada Mommys Auntys and Sisters domin magana da marubuciyar kai tsaye 08104335144 nasan ba zaku bani kunya ba, ƴan facebook ma zaku iya magana kira ko whatsAp idan ma baki yin whatsAp zamu san yadda za ayi gi dinga samu Ummu Affan taku ce masoyana a ko ina kuke domin labarin yanzu muka fara._
This book is not free. it's N300 via 0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
Stanbic bank. Then u show ur evidence of payment whatsApp number 08104335144
[8/29, 5:24 PM] Sadfat: *MU GANI A ƘASA...*
_Hot Love._
©FATIMA SUNUSI RABIU
UMMU AFFAN
*Last free page 19-20*
"Ki tashi nace kiyi wanka!" Kuka take kamar ranta zai fita. "Ki tashi nace idan kuma irin bugun jiya kike buƙata, wallahi akan ki tozarta ni sai na miki wanda ya fi shi!" Ta ƙarashe maganar a fusace. Tataah tana jinta amma ko motsawa daga inda take ta ƙasa kuma batajin ko kasheta zatayi zata tashin, riƙe baki Gwoggo tayi cike da mamakin abin da Tataahr ta mata a yau, Ta ce"Wai ba da ke nake magana ba" A hankali ta iya ɗago rikitattun idanuwanta da suka daɗe da rinewa kimanin kwana uku da suka wuce ba wani haske a cikinsu sai ja da tarin damuwa "Gwoggo bazan iya tashi a nan ba, idan kika ga na tashi to nima ajalina ne ya riske ni" Zaro ido tayi "Ni kike gayarwa magana haka? Lallai kuwa yau idan bakiyi abin da nace ba za azo kam a kwashi gayar taki, dan wallahi kinji na rantse idan ban sabauta ki ba sai an kwashi gayar taki" A fusace ta fita ɗakin. Gaban Tataah ya buga da ƙarfi ƙirjinta ya dinga dukan tara-tara 'Tataah mene ne amfanin zamanki a gidan nan tun da Ummanki bata ciki?' Ta faɗa a zuciyarta, hawayenta ya tsananta zuba tunowa da tayi tun ranar da taga Ummanta kamar gawa Gwoggo ta tilasta mata zuwa gidan aiki ranar ana yin la'asar ta taho don ce musu tayi bata da lafiya, amma abin mamaki ko da ta dawo gida sai ta iske ɗakinsu wayau ba Umma babu dalilinta, abin da ya tada hankalinta matuƙa ta dunga kuka da kurma ihuw har Gwoggo sai da ta shugo,ita ma yanayinta ya nuna alamar kaɗuwa rashin ganin Bilkisun wato Umman. Sai ficewa tayi tun daga ranar Tataah ke cikin tashin hankalin kwana da wuni take tana kuka, washe gari bata je gidan aiki ba Gwoggo bata takura mata ba, sai ɗayan washe garin ta ce taje gidan aiki ita kuma ta nuna babu inda zata, shine ta duketa duka sosai duk da farfasa mata jiki, yanzu haka duk jikinta ciwo yake mata ga rashin barci. Tunowa da wannan kuma tasan Gwoggo zata iya fiye da hakan a hankali ta miƙe tana bin bango ta fice daga gidan, tayi nisa sosai taji jiri na ɗaukarta nan take ta zube a gurin a sume...Da muciya Gwoggo ta fito tamkar wata mahaukaci, ka rantse da Allah wani ƙasurgumin ɓarawon ne ta biyu amma sama ko ƙasa babu Tataah babu alamarta, ƙofar gida ta nufa tana cewa"Algunguma waje kika nufa? To wallahi yau ko uwarki Bilkisu ce zata dawo da lafiyarta ta bar hanani lakaɗa miki ɗan banzan duka da muciyar nan yau ko ni ko ke a gidan nan!" Bakinta tsukewa yayi sa'ilinta ta fita ƙofar gida taga babu me kama da ko Tataah a gurin, shuru tayi ta fara dube-dube amma bata, daidai lokacin aka sauke Ruhaima a wata ƙatuwar mota, kuɗi sosai taga an miƙa mata