Chapter 95 Reading Kanwar Maza Book 1 and 2 By Aisha Adam (ayshercool) Complete Hausa Novel READ HAUSA Novels

Kanwar Maza Book 1 and 2 By Aisha Adam (ayshercool) Complete Hausa Novel

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   95 / 128

282K to 285K   out of 382K words

yake yawonsa a garin gombe.

Ana haka yawo ya kai shi wani Wan ?aramin gari, nesa da cikin gari kaWan, ya kusa buge wata yarinya, ya yi ta bata ha?uri, ya kafe babur Win sa ya rakata gida.

Tun da ya haWu da yarinyar nan ya samu wurin zuwa, kusan kullum suna tare, ita kuma a lokacin yarinya ce sosai, yadda yake biye mata suna shirme, yake bin ta gona ya sanya ta saba da shi sosai.

Sunanta Bintu, ?ar wani babban malami ce a garin, shigaban manoma na wannan yankin, dan haka ya na da rufin asiri.

Babanta ya na ?aunar fura da nono, akwai wata riga da take zuwa sayo masa, duk juma'a, a titi suke haWuwa da Sharif, ya Wauke ta a babur su tafi cikin rigar nan, Bintu ta saba da su sosai, bafulatanar da take sayen nonon a wurinta, ta mayar da bintu kamar ?ar ta, haka Sharif ma sun saba sosai, dan kakar bintu ma yake ce mata.

Kwatsam aka je aka gaya wa baban bintu abun da yake faruwa, ya din ga yi mata faWa, aka hanata fita, hakan ya damu Sharif, ya kasa jurewa, ya bita har gida.

Yayyen Bintu suka kore shi, amma ya?i tafiya, sai da ya haWu da mahaifin Bintu, ya ce masa idan har son ta yake ya turo manyansa ayi magana.
Baban bintu yayi haka, dan ya kori sharif.

Sharif ya koma gida ya sakawa mai martaba rigima, shi fa baya son wannan jamilar, Bintu za a aura masa an ce ya tura iyayensa.

Mai martaba da fari ransa ya Saci, mai babban Waki ta taushe shi, ta ce dama ai so ake yayi auren, a fara aura masa bintun, sai ayi aurensa da Jamila, tun da dama shekara aka saka.

Matan mai martaba suka din ga ?anan maganganu, suna cewa ya na biye wa yaro, kimar sa na zubewa.

Ya tashi tawaga daga Kano, aje a yi masa bincike a kan Bintu, idan ba su da wani aibu, a nema wa Sharif aurenta.

Mai martaba ya ji daWin bayanin da ya samu, a kan Bintu da iyayen ta.

Da yawa sun yi mamaki, yadda kamar Wan sarki daga kano, zai auri ?ar talaka.
Aka yi shagali sosai, aka yi auren.

Daga Bintu har Sharif, yarintar su kawai suke zubawa, dan a lokacin ba ta wuce shekara sha uku ba.

Mai martaba ya tura mutane, da ban ha?uri a kan abun da ya faru, tare da tabattar wa waziri, idan lokaci yayi ba fashi, za ayi auren Sharif da Jamila.
Jamila da yayarta, da mahaifiyarsu, ba ?aramin tashin hankali suka shiga ba, dan haka suka din ga bin malamai, Allah ya tabattar da auren Jamila da Sharif.

Jin akwai wadda ake so Sharif ya aura, Bintu ta din ga murna, za a kawo mata ?awa.

Wasa? sai da Sharif ya shekara biyu, kan ya auri Jamila, yau ya bayar da wannan uzurin, gobe ya bayar da wancan.

Ana haka Galadiman wannan lokacin ya rasu, bayan shafe zaman makoki, mai martaba ya sanar da naWin Sharif a matsayin Galadima.

?a?an mai martaba da matansa, suka Waga hankalinsu, saboda gani suke rashin adalci ne, a bawa wannan yaron da ba shi da cikakken kai wannan babbar sarauta, bayan ga yayyensa.

Mai martaba ya yi burus, kuma bayan naWin sarauta, aka Waura masa aure da Jamila.
Maimakon Bintu ta damu kanta, ita murna take yi, shi uban gayyar ne yake ta takaici, dan har ga Allah ba ya son jamila, ga wannan sarautar da aka bashi, ya na da shekaru ashirin da biyar. Jamila ta ?udiri aniyar, Waukar fansar abun da aka yi mata a kan Bintu.

Rayuwa ta cigaba da garawa, son da Sharif yake yi wa Bintu, ya sanya mai martaba da mai babban Waki suma suke son ta, saboda tana da tarbiyya da nutsuwa.
Hakan ya ja mata ba?in jini a cikin facalolinta. Da an yi maganar sirikai, sai mai martaba ya ce "?a ta bintu".

Sharif da kansa yake koyawa bintu karatu, daga baya ya sakata a makarantar boko.

Sai dai ba ayi shekara da auro Jamila ba, abubuwa suka fara sauyawa a gidan.

Jamila ta fi Bintu wayo sosai, dan ta ba ta shekara biyu ma, kuma ta rayu a gidan wazirin daura, hannun yayarta, dan haka ta san abubuwa, da munafunci na gidan sarauta. SaSanin Bintu, da neman ilimi kawai ta taso ta na yi a gidansu, dan ita a gidansu ma, ba a banbance Wan wannan Waki da wancan.
Dan haka da bin malamai, da makirci, Jamila ta fara haWa Sharif da Bintu faWa, kuma ta din ga shishshigi a wurin facalolinsu, tare da nuna musu ita ta Allah ce, Bintu ba wayo sosai, sai dai ta yi ta kuka.

Tsawon shekaru uku, da aure, sannan ta fara al'ada ma a gidan miji, wataran ta je garin su, ta tarar yayarta ta yaye jaririyar da ta tafi ta bari tana goyo, mai suna laila, ta saka rigima sai an bata ita.
A duk lokacin da ta je gida, sai ta je rigar nan, wurin Ade, wato bafulatanar nan, idan har ta je kamar kaka da jika, za ta tarar ta ajiye mata tsintsiya, man shanu, da sauransu, kuma ita ma Bintu da na ta alkhairi take tafiya ta yi mata.

Bayan ta dawo da laila, sharif bai ce mata komai ba, dan ya na son yara shi ma, mai babban Waki ta bata hadima, Uwani, domin ta din ga tayata kula da yarinyar.

Sai dai ba Bintu ba, Jamila ma ba ta taSa ko Sari ba, suka kasa zaune suka tsaye ita da ?an uwanta, Bintu kuwa ko a jikinta, sabgarta kawai take da karatun ta.

Ana haka mai babban Waki ta rasu, wanda hakan ba ?aramin tayarwa al'ummar masarautar hankali ya yi ba, mussaman Sharif da Bintu.

Kwatsam Bintu ta din ga rashin lafiya, babu ?a??autawa, duk ta rame, Aka kaita asibiti aka tabattar ta na da juna biyu. Saboda tsabar ?uruciya da murna, Sharif ya je ya gaya wa jamila, wai ta taya su murna.
Aikuwa ta ?wafe abun nan a ranta, da alwashin ganin bayan cikin, a cewarta tun da aka fara auren Bintu, sai t jira ta fara haihuwa. Dan muraran jamila ke nuna wa Bintu ?iyayya.

Dan haka maimakonsa bin malamai, Jamila ta fara shiga bokaye, da tsubacce-tsubacce iri-iri, domin ganin bayan cikin nan.

Allah mai jarraba bawa, sai da Bintu ta yi Sari uku a jere, kowanne sai ta sha wahala kamar ba ta rayu ba.
Hankalin Sharif ya tashi sosai, ya damu, mai martaba ne ke kwantar masa da hankali, ya saka ake yi wa Bintu rubutun Alqur'ani.

Sai a karo na huWu, sannan cikin ya zauna, sai dai ta azabtu saboda laulayi, dan ?arshe ba dan Sharif ya so ba, aka mayar da Bintu gida, ya din ga jin haushi, dan ba ya son ta yi nesa da shi, hakan ya sake ?ular da jamila, ta yi amfani da duk wata dama, ta asiri, wurin Wauke hankalin Sharif daga kan Bintu, tun da ta je gida bai taka ya je dubata ba, sai da ta haihu, aka aiko.

Jin haihuwar ya fi komai saka shi farinciki, ta haifi Wa namiji, sai a lokacin ya din ga murna, ya je garinsu, abun ka da mutan da, ko da wasa bai ga alamar ta yi fushi da shi ba, sai dai bayan suna yaro ya ci sunan Abdullahi. Aka Wauki soyayyar duniya aka Worata a kan yaron nan.
Watanninsa shida, yayi zazzaSin wuni Waya ya rasu.

Mutuwar nan ta girgiza Sharif, da ?yar aka shawo kansa. Still sai da Bintu ta sake Sari, sannan ta samu ciki ya zauna.
Da aka haife shi, aka saka masa Adam, wato sunan mai martaba, mahaifin Sharif. Ake kiransa da takawa, saboda gidan sarautar dabo ba a faWar sunan saboda girmansa, sunan mai martaba ne, kuma a lokacin Sharif ya yi wa Bintu srautar giwar galadima.

Jamila ba ta sake shiga tashin hankali ba, sai da ta ga, hankalin kowa ya koma kan Adam, ba a kansa aka fara yi wa mai martaba takwara ba, amma an fi nuna masa so, duk soyayyar da mai martaba yake yi wa Sharif ya mayar da ita kan Adam.

Adam na da watanni bakwai, wani cikin ya Sulla a jikin Bintu, da yanzu ake kira da ammi.

A lokacin laila ta tasa, ba shi da wata ?ar raino, sai Laila da baba uwani, idan baba uwani ta zo ta gama aikace-aikacen ta, sai ta tafi gida ta bar sauran hadimai, laila kuma ta cigaba da raino, dan Ammi ba ta iya komai.

Sharif duk ya shiga damuwa, yana murna zai sake samun ?aruwa, amma yana jin tausayin Bintu.

?annen Jamila na yawan zuwa gidan, su yi ta faWa da laila, ko su din ga cin zalin Adam, sai dai laila a tsaye take, ba ta da ha?uri, haka za su yi ta dambe, Ammi ta yi ta mata faWan ta rage faWa.

Wannan cikin shi ma ya tsaya wa Jamila, ta yi duk mai yiwu wa ta salwantar da shi, amma abu ya gagara, sai da aka haife shi, shi ma namiji.

Aka sakawa yaron Mahmud, sunan galadiman da ya rasu. Adam ba shi da wayo sosai lokacin, dan bai cika shekaru biyu ba, amma yana son sabon yaron da yake gani a wurin amminsa mai kyau, yana matu?ar kama da Adam da sosai da sosai, tamkar an raba kara biyu, duk kamarsu Waya da galadima.

Zigar facaloli, da soye-soyen zuciya, ya tunzura Jamila, ta rasa in da za ta saka kanta, ta din ga jin idan ta samu dama, tsaf za ta iya raba yaran nan da rayuwarsu.

A hakan, Sharif ya cigaba da tsaya musu, akan karatu, duk da ammi na fuskantar ?alubale, kowa ya juya mata baya, an fi tausayin Jamila, shi kansa Sharif gaba Waya ya canza mata.

Sai dai Mahmud ma, bai fi wata bakwan ba, ta sake fuskantar tana da ciki, dan idan ta haihu ta gama bi?i ba ta al'ada sai dai ta ga ciki.

Ayshercool.
08081012143

Paid book ne, ? 500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu bu?atar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book Win. Kar ku manta da subscribing YouTube channel Winmu na Cool hausa novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ?anwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel Win*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please =?O?



Hankalin Jamila ya yi mummunan tashi fiye da da, kasancewar idan mutum ya na aikata abu, gani yake kowa ma haka yake, ya sanya ta ce Ammi ce take yi mata asiri, ta hanata haihuwa, dan haka ta ?uduri aniyar wani abu a ranta, bayan yin shawara da Lubabatu, wato matar wan Sharif, wadda ta zame mata aminiya, a lokacin ita k???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?uma mijinta ba shi da sarauta, yarima ne kawai.

Sai bayan da suka bi gari-gari, yawon asiri, sannan Jamila, ta bijiro wa da Sharif cewar tun da ba ta taSa haihuwa ba, a bata Mahmud ko Adam, tun da giwa ta na wani laulayin, ba iya kula take da yaran ba, sai dai laila da masu aiki.

Babu musun komai, dan a lokacin ya na tausayin yadda take damuwa da rashin haihuwa, ya ce wanne take so a cikinsu.

Cikin ragon azanci, da ganin yadda ammi ta fi son Mahmud, fiye da takawa, saboda takawa na kowa ne, Mahmud kuwa ?arami ne, amma jamila ta ce Mahmud take so, a lokacin ko yaye shi ba ayi ba.

Ammi ta yi kuka, ta yi kuka, har wurin mai martaba ta je a kan ya taimaka ya karSar mata Wan ta, amma ya ce ta yi ha?uri, da ita da Jamila duk Waya ne, ta tausaya wa jamila, tun da ita ba ta taSa haihuwa ba.

Rashin Wan ta, ga laulayi, ya sanya duk ta jeme, ?arshe tana ji ta na gani, sharif ya tattara ya koma wurin Jamila, saboda ita kullum babu lafiya, ta daina cin abinci duk ta rame.

Da fari Jamila ta so azabtar da Mahmud ne, dan ta fara, kuma labari ya na iske Ammi, amma daga baya ta canza shawara, take ganin bari ta yi abun da har giwa ta mutu, zai fi yi mata ciwo, dan ta rama abun da aka yi mata, na fara auren Bintu maimakonta.

Dan haka ta koma nuna wa Mahmud so, a gaban mutane, da mahaifinsa, hakan ya saka kowa Addu'a yake yi mata, a kan Allah ya bata na ta ita ma.

Laila ce ke satar jiki, ta Waukko wa ammi Mahmud, ta kawo mata shi ta ganshi, duk yadda laila ta sha?u da Sharif, sai da yayi mata rashin mutunci a kan Waukar Mahmud ta kai wa Ammi, ya ce kyauta halak ya bawa Jamila Mahmud.

A haka Ammi ta haihu, wannan karon ta samu ?ar budurwa, ta yi ta murna, aka saka mata suna Khadija sunan mahaifiyarta, sai dai duk da haka tana kewar Wan ta, Adam tun yana kuka, yana tambayar ammi Mahmud, har ya daina.

Jamila ta toshe duk wata kafa, da zata sada Ammi da Mahmud, Ammi ta yi wa Sharif kuka, ta yi masa magiya a kan a din ga bari ta na ganin Wan ta, amma ya ce wai Jamila za ta tambaya.

Sai dai jaririyar nan ma ba ta yi tsawon rai ba, ta koma ga Allah.

Abubuwa suka yi wa ammi yawa, depression ya nemi kamata, amma a lokacin ba a waye da ciwon ba, aka mayar da ita gida, wai aljanu ke damunta.

Kamar wasa, Jamila ma ta samu juna biyu, wanda tun da ta same shi take iyayi, da sanabe da fele?e, ranar kwanan Bintu, sai galadima ya bata ha?uri, wai zai kwana da Jamila ba ta da lafiya.

Ammi ba ta taSa tanka masa ba, dan a lokacin ta mi?a wa Allah lamarinta, ta rungumi laila da Adam, ta cigaba da ri?on abun ta, gefe tana zuwa makaranta.

Facaloli suka din ga ziga jamila, suna ce mata uwar magaji, ai yadda aka tsallake yayyen sharif ya yi sarauta, haka? za a tsallake ?a?an bintu na ta su yi sarauta.

Sai dai Allah mai yadda ya so, tashin farko ta haifi mace, ta din ga ?unci tana ba?in ciki, kwanan ?ar uku ita ma ta mutu.

Nan ta din ga yaWa cewar, Bintu ce take bawa bokaye ?a?anta su cinye, shi ne wannan karon ta haWa da tata ?ar, tun da dama ?ar gidan malaman tsubbu ce.

Duk wannan abun da ake yi, Sharif bai daina ?aunar Wan sa takawa ba, sannan ya na Waukar Adam ya shiga da shi wurin Mummy Jamila, amma fa ba zai Wau Mahmud ya shiga da shi wurin Ammi ba, wai kar ta tayar da rigima ta ce sai an bata Wan ta. Shi kansa ya na mamakin yadda aka yi yake yi wa giwarsa wasu abubuwan kamar ba shi ba.
Iyayen ammi suka yi ta bata ha?uri, da nuna mata dama aure, sai an yi ha?uri ibada ne, ta yi ha?uri da Wan nan Allah ya bata wani.

A kwana a tashi, ciwon ajali ya kama mai martaba, shi ma Allah ya karSi abun sa, al'umma shi ma sun ji mutuwarsa sosai da sosai, bayan rasuwarsa maimakon a naWa sarki a 'ya?an sa, sai aka naWa ?anin sa.
Hakan ba ?aramin fitina ya ja ba, dan sai da zumunta ta taSu.
Shi kuwa Sharif, ba sarautar ce ta dame shi ba, rashin babban masoyin sa mahaifin sa ya fi damun sa, kuma wanda aka naWa uba ne a wurin sa, dam tare suka rayu a wurin mai babban Waki kan ta rasu, shi yana Wan ?arami sosai, shi ne yake yi masa komai, kamar Wan sa, kuma idan ya kwaso rigimar sa shi ne mai taya shi, shawo kan mai babban Waki da marigayi, dan haka shi duk Waya ne a wurinsa.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, bayan wannan haihuwar da Mummy ta yi, sai da ta shekara uku, sannan ta haifi wata ?a macen, bayan sun gana Sata Ammi a cikin masarautar, da zancen ta na yi mata asiri. Sai dai ba haka ta so ba.

Ba wani armashi haihuwar ta ta, dan zuwa yanzu babu jinsin da giwa ba ta haifa ba.
Adam ya kai shekaru biyar, Mahmud huWu da watanni, hatta makaranta, Jamila ba ta yadda an saka su Waya ba da Mahmud, idan Adam da Mahmud suka haWu kamar su cinye juna, har Mahmud ya fara fita ya je sashin Ammi wurin adam, duk da bai san ba mummy ce mamansa ba, Ammi ta kama shi ta rungume ta yi ta kuka.

Baba Uwani ta yi ta bata ha?uri, ta Wauke shi ta mayar da shi, dan kar galadima ya shigo ya gani, yayi mata faWa. A irin haka Jamila ta fara amfani da baba uwani, ta bata kuWi tana sakata kawo mata rahoton abun da yake faruwa a sashin Ammi, duk da ammin na iya ?o?arin ta wurin kyautatawa baba uwani.

Wataran Adam ya shiga sashin Mummy, ya na neman Mahmud, kuma ya ga ?anwarsu, dan yana son yara. galadima na ganinsa ya yi murmushi ya tashi tsaye daga kashingiWen da yake yana cewa "Maraba da kai babana, abun ?aunata kuma magajina, galadima Wan galadima kuma jikan sarki, jikan manoma da malamai"

Sai da kirarin da galadima yake yi, ya bawa Adam Win dariya, wani dun?ulallen ba?in ciki ya tokarewa Mummy zuciya, galadima magajin galadima? Wato ita ko oho, wato har ma ya sa ran Wan sa zai yi sarauta, nan ta yi alwashin idan da ranta sai dai ayi biyu babu.
Tun daga nan ta fara turawa Mahmud a?idar tsanar Adam, wai babansu ba ya son sa takawa yake so, dan haka ya daina kula shi, shi ma ba son sa yake yi ba.

Labari ya iske ammi cewa, fulanin nan su ade sun tashi, Ade ta bar sallahun a gaya mata tashi ya kama su ba shiri, sun bar wannan rigar sun yi gaba.', za su koma mahaifarsu.

Ammi sai da ta je har rigar ta tabbatar wa da kanta, ta sha kuka sosai da sosai, yadda ta saba ta sha?u da Ade da ?an rigar, kamar danginta.

Rayuwa ta cigaba da tafiya, Jamila ta sake haihuwa, amma still ?a ma ce, sai da ta ji tamkar ta mayar ta ce ba ta so.

A wannan lokacin sarkin da yake ci, mahaifiyarsa ta na raye, dan haka ammi a wurinta take samun sassauci. Mai babban Waki ta wancan lokacin da ta ri?e shi, ita ma ba ita ta haife shi

95 / 128