Chapter 94 Reading Kanwar Maza Book 1 and 2 By Aisha Adam (ayshercool) Complete Hausa Novel READ HAUSA Novels

Kanwar Maza Book 1 and 2 By Aisha Adam (ayshercool) Complete Hausa Novel

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   94 / 128

279K to 282K   out of 382K words

koma gidansu yau ne, ko su na nan?"

"Wallahi yaya ban sani ba, amma dai ba na tunanin su koma yau, bari na kai mata wayar, yanzun nan ta tashi".

"No ?yaleta, idan ta dawo ki ce mu na yi masa sannu, Allah ya bashi lafiya, a gaida sabir".

Murmushi ta yi ta Wan Wago ta ce "To in sha Allah zan gaya musu, mun gode sosai".

"Zan shigo zuwa an jima, sai na duba shi".

"To yaya umar, Allah ya kawo ka lafiya"

Ji yake tamkar kar ya katse wayar, wata irin narkewa zuciyarsa take yi, da jin iya muryarta kawai. Mussman idan ta kira shi da yaya umar, ji yake tamkar ta fi kowa iya faWar sunan.

Kamar wanda aka yi wa dole, haka ya kaste kiran wayar, ya lumshe idonsa ya na haki, ya na gazgata zuciyarsa da babu tantama wannan shi ne so.

Girgiza kansa ya yi ya ce "Ya salam, why? Why? Abun da ban taSa yi ba, ni ko shirin aure ba ni da shi, ina zaman zamana meya aikeni" ya tambayi kansa. Gashi Abubakar ne abokin hirar sa, Abubakar baya nan, kuma duk da haka ma, ya san idan ya gaya masa dariya zai ta yi masa, abun da ba ya so, dan haka yake jin, zai iya jure koma menene.

A ?asan zuciyarsa ya ji kamar dama ce, da zai yi amfani da zuwa duba Adam, ko zai samu ya ga iman.

Rumaisa kuwa, takawa ya ga reaction Win ta, ta ?arasa wurinsa ta ce masa "Wai dama ka tashi, ina ammin?".

"Ta fita ita da Nusaiba" ya bata amsa.

Ta je ta zauna a kusa da shi, ta ce "To meyasa baka ce a kirawo ni ka tashi ba?"

"To yanzu ba ga shi kin zo na tashi ba".

"Ammi zan mutu, ki zuba mini ruwan sanyi, idan mutuwa ce hutu a gareni Allah ya sa na mutu, to ba in da za ka mutu ka tafi, sai na gama makaranta mai lilo" ta yi maganar farko tana kwaikwayon sa.

Murmushi ya yi, da sai da ha?oransa suka bayyana, ya ce "Rashin lafiyar ta wa ce, ta zama abun tsokana kuma".

"Wane irin wula?anci ne, ina magana da Wan uwana zaki zo ki zauna ki na wasu surutan banza?"

Rumaisa ta kalli Samha ta ce "Au dama Wan uwanku ne? To ni kuma ?arewar ?an uwantaka gidansa a kai ni na zauna, ke meyasa ba a kai ki ba? Me Wan uwa?"

"Shut up" yayi maganar yana matse mata baki.

"To ina ruwanta da ni, ba bu kyau wata ta kula mijin wata ba?" Kallonta kawai yake yi.

"To ina ruwana. ka ci abinci ne?"

Ya numfasa ya ce"Ammi ta bani, tun da tafiyarki ki ka yi, ki ka barni".

?an shiru samha ta yi, abun da take gani yanzu, ya sha ban-ban da wanda baba uwani take gaya mata, ?arya take yi mata kenan ko kuwa? Ta ce mata ba sa wani jituwa, amma alamu sun nuna mata, kamar sha?uwa a tsakanin su, babban tashin hankalin ta da fatanta, Allah ya sa wani abu bai taSa faruwa tsakanin su ba, ta kuma fuskanci rumaisan tantiriyar fitsararriya ce.

Ruma ta ce "To yanzu ya ka ke ji, da sau?i jikin?"

"Eh, Alhamdilillah"

"To sannu, ka tashi mu tafi gida"

Adam ya ce "Mu je gida ki yi yaya da ni, ba iya jinyata za ki yi ba"

Mi?ewa Samha ta yi, ta fice zuciyarta na zafi, a gabanta adam ya sakarwa wannan shegiyar yarinyar baki, wata banza da ita mara aji, balle mamora.

"Kuma duk mai kula mijin wata, Wan wuta ne, kuma sai ya daina magana" ta yi maganar cikin Waga murya.
Samha ba ta ko juyo ba, ta yi gaba tana ?wafa, ba dan Adam ya auri rumaisa ba, da duk hakan ba ta faru ba, ta Wora zargin komai a kan sa, kuma ya kasa tsawatar mata.

Samha na fita, ya rungumo rumaisa jikinsa, tare da kwantar da kansa a jikin na ta.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, meye haka kuma, dan Allah ka cikani"

Bai ce uffan ba, ya ?ara lafewa, yana sauke numfashi.

Shiru ta yi, ba ta kuma ko motsawa ba, ta na jin bugun zuciyarsa a jikinta.

"Ita ma haka ka yi mata ko?"

"Ita wa?"

"Wannan matar da ta fita yanzu".

"Eh, tun da ba kya jin magana, ba zaki saita bakinki ba, idan ta zaneki shikenan" ya sake rungumeta sosai.

Cikin tsoro ta ce "Ba kyau fa"

Yayi ?ar guntuwar dariya, yanzu abubuwanta sun daina bashi haushi, akwai wayo wasu lokutan, wasu lokutan kuwa kanta a kwano yake, gashi dai ta fara girma, amma kamar ba mutum ba, har mamaki take bashi".

Ya kalleta ya ce "Wani al?awarin ki ka yi wa fulani?"

Ta numfasa ta ce "Ba yanzu zan faWa ba. Kuma gaskiya ka Wagani, ka yi mini nauyi, na ji da matsar hannun da ka din ga yi mini Wazu, ?asusuwana sai ciwo suke yi".

Bai Wagata ba, ya kwanta sosai a kan cinyarta, ya lumshe idanunsa.

***
A fusace Jamil yake sosai, ya dubi Jabir ya ce "Jabir, har ni wannan Yarinyar za ta yi wa fitsara, wai ba son fulani muke ba, kenan adam zuwa ya yi yana Sata mu a wurinta, abun da ya wuce ba ya riga ya wuce ba? Shikenan ba ni da zarafin bincike a kan ?ar uwata, ni da a tunanina, na lallaSata na samu wani abun daga bakinta, yadda ka san na harbeta na huta, ka ga iskancin da ta din ga yi mini?"

Jabir ya ce "Wai kai da na gaya maka halinta baka yadda ba? Kai ka ga zaryar da jami'an tsaro suka din ga yi tana asibiti, amma ta ?i magana, sai da aka kai ruwa rana, sannan ta yi".

"Ni anya ba fulanin ce ta gaya mata wani abun ba?"

Jabir ya ce "Ba tabbas, ka san halin Aisha bana tunanin ita ce, bari dai a yi sallar magariba, zan shiga na duba shi"

"Ka dai yi a hankali, ciwon nan nasa ne, ya tashi, ka san kuma sha?e mutane yake yi".

Jabir yayi murmushi bai kuma cewa komai ba.

Tamkar mai comedy, haka rumaisa take ta zuba, tana yi wa Adam shirme samfur -samfur.

Can kuma ta ce "Tashi, in Wauko maka filo, cimyata ta gaji, zan kuma je kitchen in yi girki".

Gyara kwanciyarsa ya yi ya ce "Ina jin releif a haka, ba zan tashi ba"

"Gaskiya cinyata ta gaji, duk jikina ya yi tsami".

"Mimi"

"Na'am basarake"

"Meyasa ki ka faWi maganar Wazu?"

Ta Wan yi jimm, sannan ta ce "Wacce?".

"A kan Mummy, kar ki sake makamanciyar wannan maganar,Idan maganar ta koma kunnenta fa? Zaki iya haddasa rigima, babu ruwanki da irin wannan abubuwan kin ji ko?".

Ta numfasa ta ce "Waye zai je ya gaya mata, ni fa ba ?arya nake yi ba, wata mata na gani tare da ita, gaba Waya ba kalar mutane ba, kuma da za ta tafi ta tashi ta bita k....."

Ya katseta ta hanyar cewa "Wannan matar tun ina da shekara bakwai a duniya nake ganinta, take azabtar da ni, ko ta Waure ni tamau da sar?a, ko ta din ga dukana da sar?ar, na yi mamaki da ka ce ki na ganinta, ban taSa gaya wa kowa ina ganin ta ba. Rumaisa wannan shi ne ainihin adam, kin ga abun da na din ga yi jiya, kamar mahaukaci, dan ma na daina duka da cizo kamar maye, zaki iya cigaba da zama da ni a haka, abokiyar gaba?"

Ga tausayi ya bata, amma hakan bai hanata yin dariya ba, ta ce "I tuntuni na sani, baba uwani ce ta gaya mini, idan ranka ya Saci ka na komawa kamar mahaukaci, har yaya Abubakar aka gayawa, kan ka aureni, wai kai maye ne. Sanan ban manta ba, kuma ina nan a kan baka na. Ai sai yanzu na gane ka na da Wan kirki kaWan, kar ka mutu sai na gama makaranta mai lilo"

Shiru ya yi jikinsa a sanyaye "Ba ki damu da ni ba sai lilo ko?".

"Kai fa ka gama addu'a ka mutu, kana mutuwa zan koma gida, idan na ?ara girma na auri Yaya Mahmud" ?uri ya yi mata da ido, sai kuma ya tashi daga kan cinyarta ya koma kan gado ya kwanta.

Ita kuwa madigar ko a jikinta ta yi nata wuri, dama ba ta son zaman wuri Waya.

Abun da ya tsaye masa a rai bai wuce, yadda rumaisa ta ce Baba uwani ce ta gaya mata, ya na komawa kamar mahaukaci ba, sai ya ji kimar dattijuwar ta ragu a idonsa, sai kuma abun da rumaisa ta faWa na ?arshe bai yi masa daWi ba.

***
Tamkar ya janyo dare, haka yake ji, ?asan zuciyarsa ya na fatan idan ya je gidan ya ga Iman.
Iman ma sai kaiwa take ta na komowa, ta na fatan Allah ya sa mai sunan baba ya zo.

Ammi kuwa da ta dawo, zuwa ta yi aka yi wa adam tofi, wurin malamin da take sawa ya na yi masa, ta karSo masa, sai dai ta bar shi ya Wan farfaWo har da fara'a ta dawo ta tarar da shi sai a hankali.
Sai ta yi zaton kawai jikin ne.

Haka nan iman ta tsinci kanta da yin kwalliya cikin doguwar riga, har ammi ta na tsokanarta, ko siriki za ta kawo mata.

Ta na nan zaune a falo, ta na danna waya, Sabir sai wasan sa yake yi a tsakar falon, gefe rumaisa ta na cin abinci, dan ba ta kuma komawa wurin takawa ba.

Jabir ne ya yi sallama, duk suka amsa masa, ya shigo cikin fara'a, "Autar Ammi da sirikar Ammi, Barkanmu da wannan lokaci"

Ba yabo ba fallasa, Iman ta amsa masa, rumaisa kuwa ta share shi.

"Ina takawan yake ne?" Iman ta nuna masa sashin Ammi, ya Wan tsaya ya kalli Iman ya ce "Bari in shiga in fito, zamu yi magana dear, kin yi kyau masha Allah"

Iman ta yi masa shiru, rumaisa kuwa ta kwaSe baki.

Ya na shiga ciki, message ya shigo wayar iman "Na zo" message Win mai sunan baba.

Da sauri ta tashi ta yi waje, a harabar gidan ta tarar da mai sunan baba, a cikin ?anan kaya yake, amma yayi kyau sosai da sosai.

Sai da ta furta Masha Allah, a hankali.

Unexpectedly ya Waga kai ya ga Iman, cikin zazza?ar muryarta ta ce "Sannu da zuwa yaya umar".

"Yauwwa sannunki" daga nan ta yi masa jagora, har ciki.

Ruma na ganinsa, ta tashi ta din ga tsalle ta na murna, amma ya basar da ita ya Wauki Sabir, da ya rarrafo wurinsa da gudu.

"Mai sunan baba, ba ka yi murna da ka ganni ba?" Kawai yayi mata murmushi, ya na sake rungume Sabir.

Ko da suka shiga sashin Ammi, Jabir na ganin mai sunan baba ya haWe rai, ya yin da takawa mamaki ne ya kama shi da ya ga mai sunan baba.

Suka gaisa da Ammi, yake gaya mata rumaisa ce ta ce masa magidanta ba lafiya, ya zo ya duba shi kan ya sanar da mama, dan za ta iya tayar da hankalinta.

Ammi ta ce "Ruma ce ita ma da abun ta, ai ya warware, dan Allah kar ka gaya mata hankalinta ya tashi, ya ji sau?i.

Mutumin da ya zo dubiya, bai fi mintuna goma ya yi ba, kuma daga takawan har jabir bayan sallama da ya yi musu, babu wanda ya sake kulawa, ya yi wa ammi sallama.

Kayan ciye-ciyen ya ba wa sabir, sai dai sabir ya ?i yarda ya ajiye shi ya ma?al?ale shi.

Ya fita da shi a kafaWarsa ya na murmushi, murmushin ba ?aramin kyau ya yi masa ba.

Jabir ne ya biyo bayan sa, ganin Iman ma ta bi bayan mai sunan baba.

Ya Wan kalleta sannan ya ce wa Sabir "Ka je wurin antynka, ko da kai zan tafi babana?"

Iman ta yi murmushi ta ce "Baban mai sunan baba"

Murmushi ya yi, ya mi?a mata sabir da yake ta ihu, ya na sake mi?awa umar hannu.

"Ke iman zo ki wuce, ina son magana da ke, na gaya miki tun Wazu amma kin yi banza da ni, ki ka bi wani" Jabir ya yi maganar cikin umarnin da iman ta ji ya yarfata.

"Amma uncle J, ai gani na yi ka na wurin takawa ne, shiyasa".

"Shut up malama" yayi maganar cikin fushi da kishi.

"Meye haka? Yayana ne fa, me ta yi maka?" rumaisa ta yi maganar tana harar Jabir.

Magana yake son sake yi, amma mai sunan baba ya ?ura masa ido. Sai kuma ya yi shiru, ya ji ya kasa sake magana.

Rai a Sace ta wuce, ba ?aramin haushi? ta ji ba, dan tuni ta fara kuka.

Ruma ta ce "Mai sunan baba, bari na raka ka"

"No, ki je ki kula da mijinki, zan ce ki na gaishe su" ya juya ya fice, wani irin takaici ne ya kama mai sunan baba, ba ?aramin haushi ya ji ba, abun da jabir ya yi wa Iman, kuma ya lura da yadda yake shishshige mata tun lokacin bikin rumaisa, tabbas ba dan a gidansu yake ba, zai nuna wa jabir, ba a shiga shirgin sa"

A harabar gidan mai sunan baba suka haWu da Mahmud, Mahmud ya yi masa magana, mai sunan baba ya tsaya suka yi musabaha, sai dai ya yi ta kallonsa, ya na tunanin yanzu ya baro Adam a ciki, kuma dai ya san ba shiga sabgar juna suke yi ba.

Mahmud ya ce "Ba Adam ba ne, mahmud ne, amma ka na da ala?a da rumaisa ko?".

Mai sunan baba ya jinjina masa kai ya ce "Eh ?anwata ce".

"Kamannin na gani ai, sunana Mahmud"

Mai sunan baba ya ce "Babban suna, ni kuma umar"

Mahmud ya ce "Masha Allah, ka gaida gida, a gaida mama, duk ina jin sunanku a bakin ?a ta, bari na zo na sauke ka a hanya, fita zan yi" Umar ya jinjina kai, dan gaba Waya ya ji Mahmud ya burge shi, mussaman yadda ya yi masa magana kamar sun saba.

A Waki rumaisa ta tarar da iman, ta na kuka.

Ruma ta ce "Gaskiya kin ba da ni, wai shi waye Jabir Win nan ne? Ya san waye mai sunan baba kuwa? Ke ma kin wani zauna ki na yi masa kuka, ni ma ina da saurin kuka amma kin ga ina yi? Meyasa ba a yi wa Nusaiba abun da ake yi miki?".

Iman ta share hawayen ta, Sabir sai jijjiga iman yake yana cewa Iman, dan ya iya sunanta raWau, kamar shi ya raWa mata.

Ruma ta ce "Gidanku, Anty zaka ce ko Mummy"

Iman ta yi murmushi ta ce "Anty Nusaiba ta su ce, kuma ta na da bakin da idan aka yi mata za ta rama, ni bana son tashin hankali ne, baki ga komai ba ma, dan su Fauziyya sun daina zuwa ne, baki ga abun da suke yi mini ba".

Ruma ta ce "Wallahi ko a kan bola aka haifeni, ba zan yadda da wula?anci ba, amma cika mini al?awarina. Meyasa papa ba sa shiri da daddyna, meyasa kuma ba ya shiri da ammi, Meyasa ki ke cewa kan ki, ?ar tsintuwa?".

Iman ta Wan yi shiru, sannan ta numfasa, a dai-dai lokacin da wani hawayen yake zubo mata.

***
ASALIN LABARI.....
1972 Kano state emirate palace, a zamanin sarki Adamu Abdullahi.

Masarautar kano na Waya daga cikin manyan masarautu, da ake ji da su a Nigeria, ba iya Nigeria ba hatta turawan mulkin mallaka, suna ji da wannan masarauta.

Sarki Adamu Abdullahi, mutum ne mai adalci, karamci da kuma yakana, kuma jarumi, hakan ya sanya soyayyarsa a zukatan al'ummarsa.

Ya na da tarin dukiya, ?a?a, barori da sauran hadimai.
Yana da tarin ?a?a, daga matansa da kuma ?war?warorin sa.

A wannan lokacin, ya na kimanin ?a?a goma sha tara, maza da mata, a cikin mazan Allah ya jarrabe shi da ?aunar Wan sa Muhammad, da suke kira Sharif, tun ya na iya Soyewa har ya gaza, yake nuna masa soyayya muraran.

A lokacin turawa sun kawo harkar karatun boko, wanda a lokacin dama sun tarar da hausawa da karatunsu na allo da tsangayu.

Galibi ?a?an sarki a wannan lokacin, suna da sarautunsu, a lokacin da suke ?allafa rai a kan sarauta, shi kuwa Sharif sam hankalinsa ba ya kan sarauta, ya fi karkata ga neman ilimi, na addini da kuma na zamani, da turawa ne suke koyar da su.

Sharif ya na da zafin zuciya, Mai marataba ne da mai babban Waki, wato kakarsa kawai ke iya sarrafa shi, kasancewar mahaifiyar sa ta bar duniya. A wurin mai babban Waki yake, sai kuma mahaifiyar Jafaru, wato turaki a yanzu, dan kamar uwa ya Wauketa ita ma.

Bayan ya kammala karatun sakandare, turawa suka ba shi gurbin karatu a ?asar Ingila, mai martaba ya ce bai san zance ba, babu mai raba shi da Wan sa, Sharif ya ?allafa rai a kan ya na son tafiya. Sai da mai babban Waki ta sanya baki, da wasu manya sannan ya amince.
Sai dai mai martaba ya na tsoron rayuwa cikin turawa, ga ?an?anin yaro kamar Sharif a wannan lokacin.

Bayan tafiyar sa, ya kammala degreensa na farko, a kan fannin tattalin arziki, ya ji daWin zaman ?asar waje, ba takura, babu kana tafe ana take maka baya, duk a hanaka sukuni da kaWaici, a cewarsa.

Da ?yar mai martaba ya saka aka dawo masa da Sharif, sai dai da ya dawo duk ya yasar da wasu al'adun, harkar gabansa ce kawai ta dame shi.

Ko zaman fada ba ya zuwa, idan ya shilla ya tafi na sa yawon, sai an ganshi.

Hakan ya fara damun mai martaba, ya fara tunanin yi wa Sharif sarauta, ko zai nutsu, sai dai ya na cikin yaransa ?anana.

Sharif ya tsiri cewa zai tafi master's gombe, nan ma sai da aka kai ruwa rana, mai martaba ya ce ya na da sharaWi, abokin sa wazirin daura, ya bashi ?anwar matarsa ya aura wa Waya daga cikin ?a?ansa dan ?arfafa zumunci, dan haka ya ce Sharif ne zai aure ta.

Sharif da fari ya ce "Shi ba ya son ta, daga baya saboda yana so karatu, ya amince, amma sai ya gama master's Win sa, mai martaba ya ce bai yadda ba, lokacin ya yi tsayi, wazirin daura ya ce a saka shekara, ba damuwa kan nan ta ?ara girma ita ma.

Ko da Sharif ya tafi gombe, ya samu abokai ya cigaba da rayuwarsa, yadda yake so, duk da mai martaba ya na turowa, ana saka masa ido a kan sa, duk da akwai manyan mutane da suke bibiyar sharif, saboda karamci ga mahaifinsa.

?alibai ba kowa ya san Sharif ba, yayi ta kashe musu kuWi, suna bin sa, har sabon babur ya saya,

94 / 128