Chapter 111 Reading Kanwar Maza Book 1 and 2 By Aisha Adam (ayshercool) Complete Hausa Novel READ HAUSA Novels

Kanwar Maza Book 1 and 2 By Aisha Adam (ayshercool) Complete Hausa Novel

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   111 / 128

330K to 333K   out of 382K words

shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7.?? Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8.? Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9.? Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10.? Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11.? Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12.? Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13.? Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14.? Supplement na whitening/glowing skin*

*15.? Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*


Paid book ne, ? 500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu bu?atar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book Win. Kar ku manta da subscribing YouTube channel Winmu na Cool hausa novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ?anwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel Win*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please =?O?


*TALLA! TALLA!! TALLA!!!
*?AN?ANO DAGA LITTAFIN NAZEEFA SABO NASHE, MAI SUNA ?UDURAR ALLAH*

Ta Yaya zai zama jinina alhali ni na san bayan matana ban tab a kusantar wata mace ba? Ya furta kai tsaye yana kallon likitan da sakamakon gwajin yake hannunsa. Likitan yana jinjina kai ya sake furta  Tabbas Jaheed jininka don gwajin k wayar halittarku da komai ya tabbatar kai ne mahaifinsa kafin a kai ga haka ma ko Kamanninku da suka zamo kwabo da kwabo sun tabbatar da Hakan koda Ba a yi gwajin ba.

Shiru na tsawon lokaci d akin ya d auka kowa da irin tunanin da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da k wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab a rik ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi.? Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K UDIRAR ALLAH& .

(*Ina ma'abota karance-karancen litatafan hausa, na san kun santa, Nazeefa sabo nashe, tsohuwar marubuciya, da ta saba nishaWantar da ku, da WaWan litatafan hausa masu ma'ana da ilimantarwa, ya kuke tunanin wannan turka-turka, DNA Win sa ya kasance daidai da na yaron da bai taSa ganin mahaifiyarsa ba, haka zalika a iya saninsa tun daga ?uruciya har girmansa, bai taSa aikata zina ba? Ku kasance da Nazeefa sabo nashe, dan jin yadda zata warware wannan turka-turka a cikin littafin ?udurar Allah. Masu bu?ata kai tsaye za su iya tuntuSar ta a kan lambar wayarta 08033748387*)



Shiru yayi ya cigaba da kai lomar abinci bakinsa, suka tsare shi da ido suna jiran yayi magana.

Yaya Abubakar ya tashi zaune ya ce "Malam magana fa ake yi maka"

Mirsisi ya?i magana, ya cigaba da cin abinci, Aliyu dama ya daWe da gano yayan na su, ya afka kogin soyayya, magana ce kawai bai yi ba.

Sai dai ya gama cin abincin, sannan ya ce "Mama, ba Soye miki nayi ba, komai ya zo mini a bazata ne. Hasalima tausayinta da na ji ne, ya sanya na ji zan iya aurenta, amma kin san ni dai ban taSa kula ?ar kowa ba".

Aliyu ya ce "Wai wa ce ne?". Harar da yayi masa ya sanya shi yin shiru.

Mama ta ce "To, wai an ce turakin kano yana son ganinka, zai gana da kai, a kan maganar, kuma suna bu?atar ka fito ne"

Mai sunan baba ya Wan yi shiru sannan ya ce "Mama bani da abun aurenta yanzu, kin san komai a kanta, dan ina wurin lokacin da rumaisa ke baki labarinta.
An fasa aurenta da wani, kuma a yadda take gaya mini, shi ne karo na huWu, duk saboda waccan matsala, dalilin haka kuma, an ce wa mari?iyarta idan ba ta aurar da ita nan da watanni uku ba, ta mayar da ita in da ta tsinto ta. Magana ake ta shekaru goma sha tara da ri?onta, wurin wa za ta kai ta. Ban san ya aka yi na ji ina son na aureta ba".

Aliyu shi tausayi ma ya bashi, har yanzu bai gama yadda soyayya ce tayi masa kamun kazar kuku ba.

Mama ta ce "Na yadda da maganarka babana, kuma na goyi bayanka, dan shi Wa na kowa ne, yadda hajiya binta ke ri?e da rumaisa kamar ba sirikarta ba, kaWai ya isa na goyi bayanka. Kuma Allah ya sani tun kan haka ina ?aunar yarinyar nan sosai. Amma abun da nake tunani, kaga an saka bikin Abubakar, muna ta fama, gashi ka tsayar da gininka ana nasa, yanzu meye abun yi watanni uku sun yi kaWan".

Abubakar ya ce "Ba dan halinsa ba, kuma tun da ban isa ya gaya mini abun da yake ciki ba, saboda halin da yarinyar take ciki, da kuma duba da muma muna da ?anwa, muna fatan albarkacin wannan jihadi da zai yi, Allah ya kula mana da ita, a duk in da take, da kuma la'akari da yadda mutum ya faWa soyayya, da har ta kai shi ga yanke hukunci, ba tare da shawara ba, ni yayansa wato hassan Win sa, zan yi magana da su baffa, a Waga bikina a fara nasa, tun da abun gasa ne, nayi sai yayi. Sai su tare a nawa gidan, ni na ?arasa nasa".

Mai sunan baba ya galla masa harara.

Abdallah ya ce "Auren mai sunan baba, zama bai kama mu ba, dole mu yin?ura abu namu maganin a kwaSe mu".

Yasir ya yi murmushi ya ce "Ni zan sai akwatin kayan lefe, guda shida in sha Allah"

Huzaifa ya ce "Ji banza, an gaya maka akwatin lefen ma, jagwal za a saya, kamar kayan jagwal Win da kake na wayoyi da computer, da hacking in ji rumaisa".

"Bana son rashin mutunci, kai ka san abun da nake da shi ne? Kwanan nan daga china zan fara yin order wayoyi, kai ka sani ai, jari nake tarawa, amma ni


zan sai akwatunan lefe, kai uwar me ka ajiye da zaman basir Win Winki, banda shegiyar ?arya da saSa al?awari".

Mama ta ce "To zakaru, ai kun ci kun ?oshi, dole ku yi mini faWa".

Umar ya ce "Duk na ji ta bakin ku, na kuma gode sosai, amma babu wanda zai rabu da wani abun sa saboda ni, kai habu ba za a Waga bikinka ba in sha Allah, ina fatan nima wannan Win ba zai gagara ba, zan ?ara ?o?ari".

Abubakar ya ce "Wai dan an haife mu lokaci Waya ni sa'anka ne? Bana magana biyu kai ka sani, gidan nan ya zama naka, dama kaine ?arfin ginin, ni ba gaggawa nake yi ba, ita ma haka in sha Allah ita da iyayenta za su fahimce ni".

Mai sunan baba zai sake magana mama ta ce "Ka riga ka Waukki aiki babana, idan ba hakan aka yi ba, ni ban ga mafita ba, garbatina Wan albarka, Ubangiji Allah ya ?ara haWa mini kanku, ya kau da abun ?i a tsakanin ku, a duk lokacin da abu ya tasowa Wayanku, na ga kun haWa kanku, ba ?aramin daWi nake ji ba".

Usman da tun da ake maganar bai ce komai ba sai yanzu ya ce "Mama duk jajircewarki ce ta kawo haka, Allah dai ya ?ara miki lafiya da nisan kwana".

Suka amsa da Amin, Abdallah ya ce "Mai sunan baba, idan abu ya taso maka, bamu yi maka ba, wa zamu yi wa? Sadaukarwar da kake yi domin farincikinmu ai tana da yawa, komai ka samu mu, kai ne wa, kuma kai ne uba, kowa ya kwaso matsalar sa, mai sunan baba, dan haka muna bayanka a kowane ?adami Allah ya iya maka yayi ri?o da hannunka".

Karar da ?an uwan nasa suka nuna masa, ba ?aramin daWi tayi masa ba, har sai da hakan ya sanya shi murmushi, kuma ya kasa Soye farin cikinsa.

***
Ko da labari ya iske dangin mahaifinsu Umar, sun yi murna, tare da tsokanar mai sunan baba, dama zai iya yin budurwa yayi soyayya.
Wan mahaifinsu ya ce zasu yi ?o?ari, amma abubakar ma ba za a Waga aurensa ba.
Sai dai yayan mahaifinsu ya jinjina lamarin auro ?ar gidan sarauta yana talaka.

Tare da shi da umar, da yaya Abubakar da ?anin mahaifinsu, sai mijin iya baffa musa da ya zo daga, suka je gidan turaki bisa jagorancin Mahmud kamar yadda ya bu?ata.

Sai dai sun ga karramawa, da mutuntawa da basu taSa tunani ba, turaki ya ?ara jaddadawa mai sunan baba matsayin iman, mai sunan baba ya ce ya amince.
Turaki ya tambayi ?an uwan mahaifinsa, a kan idan sun amince su ma, suka ce ai shi ne zai zauna da ita, kuma tun da ya ce ya ji ya gani, suma sun amince ai Wa na kowa ne, a tarbiyyar da umar yake da ita, sun san ba zai kawo abun da zai cutar da shi ba.
Baffa Musa wa ga mahaifinsu ya ce "Sai dai mu ma wani hanzari ba gudu ba, yaron nan maraya ne, bashi da ?arfi saka biki nan da watanni uku yayi kusa da yawa, ga Wan uwansa nasa bikin muke hari, muna fatan a ?ara mana ya zama watanni shida, gaba Waya ya mayar da hankali ne a kan auren Wan uwansa bamu zaci nasan zai zo haka ba".

Turaki ya ce "Babu laifi, kar ku damu. Ubangiji Allah ya yi mana jagora, kuma a hakan nan ma kawai, na yaba da tagwayen sosai, ba dan ance shi ma Wan uwan aure zai yi ba, ai da sai na bashi ?a ta, ai duk wani wanda ya fito daga tsatson ?a ta rumaisa, duk abun da yake so, in dai ina da shi zan yi masa.
Allah ya sanya musu albarka, ya nuna mana lokacin lafiya".

Baffa musa ya ce "Amin, ranka ya daWe tun da har an samu daidaito, ina ga ba sai mun ja lokaci ba kawo kuWin aure, ga kuWi mun taho da su"

Gaba Waya suka kalleshi, su dai sun san ba su yi haka da shi ba.

Ya karkace ya ciro kuWi, dubu Wari da hamsin, ya ajiye a gaban turaki.

Turaki ya ce "Masha Allah, Allah ya sanya albarka, to ba dan ba a shirya ba, ai da sai a Waura, mu bashi gidan zama, a wuce wurin ko malam umar?".

Mai sunan baba ya risuna ya ce "Ranka ya daWe ni yakamata na yi ?o?arin samar da mahalli".

Yayi murmushi ya ce "Babu laifi, Allah ya nuna mana"


Ko da suka taho hanya, Mahmud har gida ya kai su mai sunan baba, a gida suka sanar da mama ai an bayar da kuWin auren ma, mama ta ce daga zuwa tambaya an biya kuWin aure? Ta ce to sai a nemo kuWin malam musa a bashi abun sa, amma ya hau mama da faWa, a kan dan yayi wa ?a?an Wan uwansa abu, dan me za ta ce a biya shi.

Turaki ma wayar ammi ya kira, ya sanar mata su mai sunan baba sun bayar da kuWin auren iman, dubu Wari da hamsin, sun sanya watanni shida dai-dai.

Ammi ta yi mamaki, dan ita bata ta;a zaton abun a haka ba, ta ce to ba a basu komai na tukici ba, sun kawo kuWin aure.

Turaki ya ce su aika musu daga baya, amma sun zo da kuWin aurensu sun bayar.

Farincikin ammi ya kasa Soyuwa, ta nufi Wakin laila, da suke tare da rumaisa, tana ta koya mata abubuwa.

"Laila, rumaisa" suka Wago suka kalli ammi.

"Daga zuwa amsa kiran turaki, sun bayar da kuWin auren iman, an saka watanni shida".

Ruma tayi murmushi ganin yadda bakin ammi ya?i rufuwa.

"Au shine aka wareni, ban ma san za a kawo kuWin aure ba, iman yanzu ta rama ta ?wace mini yaya, dan na auri takawa"

Suka yi dariya, laila ta ce "Kaii Alhamdilillah, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ya sa za ayi da mu. Ni dai gayen ya burgeni ranar da na taSa ganinsa, so gentle".

Ruma ta ce "TaS, mai sunan baban ne gaye".

Ammi ta ce "Ya Ubangiji Allah ka sanya ?arshen matsalar nan ne ya zo, Allah ya sa kar a gaya masa wani abu da zai saka ya ce ya fasa".

Ruma ta ce "Ammi, idan kin ga ba ayi auren nan ba, sai ?udirar Allah.? Mai sunan baba ba zai taSa cewa zai fasa ba, sai idan ku kuka fasa auren, duk rintsi kuwa"

Ammi ta ce "Allah ya sa, bari ta dawo na gaya mata, Allah sarki ?ar marainiyata, Allah ya kaWe abun ?i".

?asan zuciyar ammi, tana ta yi wa iman addu'a Allah ya sa ta dace, dan yanayin nature mai sunan baba, tana bata tsoro, gani take kamar yanayin iman ya nuna tana son shi ba kaWan ba.

Da labari ya iske iman, da ta koma Wakinta sai da tayi sujudu shukur, sujjadar godiya ga Allah, saboda tsananin farinciki, haka nan a ranta take jin, sassauci zai samu a rayuwarta.

A irin kyan da Allah ya yi wa iman, zaka raina abun da aka bayar na kuWin aurenta, amma jiki na rawa ta kira mai sunan baba.

Sai da ta kusa katsewa sannan ya Waga.

"Yaya umar"

"Na'am".

"Ashe kuWin auren zaku kai, na zata kawai zuwa kayi ka amsa kiran da mai girma turaki yayi maka?".

"Na yi garaje ko, na kai kuWin auren ba tare da kim ce mini kin amince ko a'a ba. Tun da rumaisa ta ce mini, akwai wanda ki ke so".

Iman a ranta ta ce 'Kai Win ne dai, kai nake so yaya umar'.

A zahiri ta ce "Ni ba wanda nake so fa"

Har cikin kansa ya ji shagwaSar da tayi masa, ya sake gyara zaman wayar sannan ya ce "To ya aka yi?"

"Bugowa na yi, na maka ya ka je gida, Allah ya ?ara buWi".

"Masha Allah, ayi ha?uri abun talaka na san kin fi ?arfin hakan"

Iman ta ce "A'a ban fi ?arfin haka ba, Allah ya yassare maka".

"Amin ya haiyyu ya ?aiyyum, thanks" ya katse wayar.

Nothing romantic mai sunan baba ya sani, kawai ayi abun da ya dace, dan soyayya in dai irin yadda Aliyu da Abubakar suke me
Jabir kuwa tamkar zai yi hauka, haka ya ji da aka ce, wai an kai kuWin auren iman, bai taSa tunanin da gaske yana son ta ba sai yanzu.
A baya matsananciyar sha'awarta ce take addabarsa, tun ranar da ciwonta ya tashi, yana nan shi ya Wauketa ya kaita mota.
A baya bai taSa tunanin jin son ta ba, saboda tana girmama shi a matsayin yayanta, shi kuma ?anwarsa, tun daga ranar da ya ga jikinta, ya sanyawa ransa lallai sai ya mallaki iman, ko ba komai, idan ka samu irinta a yaranka, ka samu kadara, saboda kyakywar bafulatanar yarinya ce.

Washegari, ammi ta bayar order yin girke? snacks, ta ce a kai gidansu rumaisa, ruma ta ce gida za ta je, ayi sabgar nan da ita, saboda wauta ta cewa Iman ta shirya, su tafi tare, laila ta ce ya za ayi ta je kai tukuicin kuWin aurenta, ban da wauta irin ta ruma.

Ammi ta ce laila da sidi sai su kai, sai su tafi da rumaisa, ruma ta ce ga Mahmud, ba sai sidi ya je ba.
Ammi har mamakin yadda Mahmud yake yi wa rumaisa biyayya take yi, duk abun da ta ce masa yayi, ko musu baya yi yake aikatawa.

Hakan kuwa aka yi, da shi da laila, da rumaisa, suka kai kayan nan, mama ta din ga mitar wannan kayan sun yi yawa, dan sun kusa kai Waya da kuWin auren, banda uban lemuka da naman kaji.

Laila sun gaisa da mai sunan baba, sai dai sama-sama, yaya Abubakar ne mai sakin fuska, sai usman sarkin tsokana.

Laila ta daWe a gidan, suna hira, take bawa mama labarin yanayin zamanta a canada, da iyalinta, take gaya mata a cikin watan, mijinta da yaranta suma zasu zo hutu.

Laila ta yi wa mama sallama, ta cewa rumaisa, za ta je ziyarar ?awayenta da ke Kano, idan Mahmud ne ya zo Waukarta, ko sidi sa biya su Wauke ta.

Rumaisa kuwa baki ya?i rufuwa dan murna.
Yasir ya samu ruma ya ce "Ke, zo mu yi shawara, nifa zan saiwa mai sunan baba akwatunan biki".

Ruma ta ce "Da wani kuWin?".

"Ke baki san na kusa fara shigo da wayoyi, da computer daga china ba, ni da abokina muke tara kuWin, yayansa ne zai tsaya mana, mama ma ta san zancen, amma a kuWin dole ni zan saiwa mai sunan baba akwatunan lefe"

Rumaisa ta din ga bayar da shawarwari, na arziki da na shirme.

Bayan la'asar, Mahmud ya dawo ya Wauki rumaisa, suka biya suka Wauki laila, albarkacin rumaisa, duk da ko a baya, laila da Mahmud ba a ga maciji, amma suka din ga hira yau sosai, hirar da ba su taSa yi a baya ba.

Jabir kuwa, Kasa jurewa yayi, ya Wauki mota, ya tafi gidansu takawa, wani irin kishi, da zafin zuciya yana ta azalzalarsa, ya shiga part Win su, sai dai kai tsaye da ya shiga babu kowa a falon, ya tafi Wakin iman.

Tana zaune a kan gadonta tana danna waya, kawai sai ganin mutum tayi a tsaye a kanta, yana huci.

Sai da ta tsorata, ta ce "Uncle J, lafiya kuwa?".

"Ban sani ba, tsohuwar munafuka, ni zaki yaudara? Wato dama wancan banzan talakan matsiyacin ki ke so? Ya rasa abun da zai kawo kuWin aurenki sai dubu Wari da hamsin, ko da yake babu mamaki, tun da kema tsatson tsiyar ce, ?ar masu kiwo ?afa

111 / 128