Chapter 126 Reading Kanwar Maza Book 1 and 2 By Aisha Adam (ayshercool) Complete Hausa Novel READ HAUSA Novels

Kanwar Maza Book 1 and 2 By Aisha Adam (ayshercool) Complete Hausa Novel

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   126 / 128

375K to 378K   out of 382K words

ya dawo, ko kuma yazo ya tarar ta tafi kano, an ga jikirta a birnin kano, tun da ba a kaita kano dan Allah ba, yanzu dalili ya samu dan haka babu mai hanata tafiya.

Nan da nan riga ta Wauka, an samu ?ar mairamu a raye, ashe kan ta mutu ta haihu, aka din ga zuwa ganin mai sunan baba da mahmud. Sun sha karramawa kala-kala.

Washegari da wuri Alhaji Aminu ya sauka a garin, tare da jin batun tamkar almara, abun da ya faru shekaru kusan goma sha tara baya, yaya za ayi ace, wai an ga ?ar mairamu.

Sai dai ya tsinke da lamarin, bayan saukarsa mai sunan baba ya nuna masa hoton iman.
Alhaji Aminu ya ce "Malam Umaru, amma ka kasa gaya mini wannan abu, duk da ban wani san mairamu ba, amma wannan kamarta Waya da ade, kuma ba shakka jininmu ce, yanzu meye abun yi?"

Mai sunan baba ya ce "Idan ba damuwa, sai mu taho da iman Win da amm...

Ade ta ce "Wane mutum, da ?afar nan tawa ko a ?afa zan taka na je kano, na ga Bintu"

Alhaji Aminu ya ce "Da wace ?afar? ?afa duk sai saura? Ki zauna a shirya tafiya, sai a tafi gaba Waya "

Nan ya sake warware musu irin zaluncin da jauro yayi musu, ya din ga haWa kai da ?an bindiga ana cutar da su, wanda hakan ya sanya da yawansu suka tarwatse, da farko basu gano shi ba, sai daga baya amma an ce sojoji sun kashe shi.

Da daddare takawa ya ceea rumaisa, ta zo su tafi su kwanta, ta ce "Ba zani ba gwaggo ta ce idan na biye maka wani cikin zan samu, kuma wallahi haihuwa da wahala"

Dariya yayi ya ce "Ai shikenan"

Gwaggo ta kawo wa ruma abincin dare, ta ce "Yau ba zaki bishi ba?"

"Ai na gaya masa kin ce bamu da kunya, kuma idan na cigaba da biye masa wank cikin zan samu da suri"

Gwaggo ta Wora hannu a ka ta ce "Rumaisa ba ki da hankali? Ki ka ce ni na faWa, ashe halinki na wauta na nan, da wani idon zan kalle shi? Wallahi dole in tattara kayana in bar gidan nan"

Ruma ta ce "Ashe kuwa zaki maimaita masa abun da ki ka faWa mini, dan sai ya bi ba'asi"

Ta samu Wan kwali ta kwaWawa ruma a baya ta ce "Shashasha uwar wauta, shikenan zai daina ganin mutuncina".

**
Mahmud ya kira Ammi a waya, ya ce "Su shirya, su haWu a wuri guda, suna tafe da manyan ba?i zuwa kano shi da mai sunan baba.

Ba yadda ammi ba ta yi ba, amma ya?i gaya mata ko suwaye, ya ce amma muhimmancinsu ya kai ace har mai girma wambai ko turaki yana wajen.

Ammi ta ce "Turaki baya nan, ya je Germany wurin galadima, jikinsa ya tsananta, sai dai wambai"

Mahmud ya ce "Ba?i ne masu muhimmanci, har mimi muna bu?atar ta a wurin" Ammi ta din ga mamakin wane irin ba?i ne kuwa haka?".

Da ta sanar da wambai kuwa, ya ce babu laifi, a jira ?arasowar ta su, aji wani irin ba?i ne, ya ce idan sun iso a kira shi.

Ammi ta sanya aka yi ta Worawa da saukewa, duk da bata san wane irin ba?i ba ne, amma akwai bu?atar ayi girki.

Duk nacin ruma da iman, a kan son sanin suwaye ba?in, ammi ta ce musu ita fa ba ta sani ba.

Duk suna falon mai sunan baba ya yi sallama, iman ta tashi da sauri ta ce "Hero suwaye ba?in?"

Ruma ta gwale baki ta ce "Su hero manya"

Takawa ya ce "Umar kun bar mu a duhu kai da ?aninka, ku muke ta jira"

Yayi murmushi ya ce "Yanzu za su shigo" ya kalli iman ya ce "My yellow, yakamata ki bani tukuici kan ki ga ba?in nan fa" yayi maganar yana jan karan hancinta, a gabansu.
Kunya ce ta ka??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????mata ta ce "To me zan baka?"

"Saniya zaki sai mini" gaba Waya suka hau dariya, Ammi ta fito ta ce "Mai sunan baba kun sauka? Ina ba?in?"

Mahmud ne yayi sallama, sai Alhaji Aminu a bayansa ya ri?o ade, sai ?annenta guda biyu.

Sakin carbin hannunta ade tayi, ta ce "Ade" da ?arfi.

Jiki na rawa saboda tsufa Ade ta Wago ta kalli Ammi ta ce "Bintuna"

Da sauri Ammi ta ?arasa ta ri?o hannun Ade, hawaye ya wanke mata fuska ta ce "Dan Allah gaske ne ba mafarki nake ba, Ade ke ce a gabana? Ade ba irin neman da ban yi miki ba"

Suka rungume juna ita da ita.

Alhaji Aminu ya ?urawa iman ido, ya ce "wannan ce ?ar ta mu?" Kamar sokuwa haka iman ke bin su da kallo.

Mahmud ya ce "Hajjaju ga ?an uwanki, mijinki ya nemo"

Jiri ne ya fara Wibar iman, saboda ba ta san mafarkin nan ya cigaja da yaudararta.

Umar ya ri?e ta ya ce "Iman, calm down mana menene"

"Dan Allah ka tashe ni daga baccin, kamar ba zai faru a gaske ba fa?"

"Ba mafarki bane ba fa" yayi maganar yana zama tare da ita, saboda har numfashinta ya fara sama.

Alhaji Aminu ya ?araso gaban iman, ya ri?e hannunta, ya ce "?a ta ba mafarki bane ba, mu ne ahalinki" bayan gama kukan ammi ta ce Aminu haka ka girma sosai? Iman ga Ade da nake baki labari, wannan su ne ahalin mairamu"

An sha koke-koke, ?an aike ammi ta tasa, aka kira wambai, sai dai yaji kunya da nauyin abubuwan da suka din ga yi wa Ammi da iman, a kan rashin sanin wacece, wanda hakan yana da ala?a da zigar Mummy.

Nan Alhaji Aminu ya gaya musu cin amanar da jauro yayi musu, da ?iyayyar garin da ya sanya musu, suka kasa komawa, balle su binciki abun da ya faru gaske ne ko ?arya.

Takawa ya ce "Tabbas wannan mutumin shi ne rumaisa ta zana mini, ta ce da wa yake kama? Na ce mata iman, ta ce a yanayin da ta ganshi ne ya sanya ba zata taSa cewa ta ga wani mai kama da iman ba, kasancewar sa mutumin banza, dan har tattaunawa da shi ta yi"

Iman ta rasa mai zata cewa mai sunan baba saboda murna, sai kuka take yi.

Bayan an nutsa, ammi ta saka aka kawo abinci, takawa ya ce "Shi da matarsa zai ci abinci, mai sunan baba ya ce shi ma haka. Mahmud ya ce "Ni za a yi wa gori? Sai in ci da ammina"

Haka suka wuni cikin raha da dariya, iman ta rasa in da zata tsoma dan farinciki.

Labari ya bazu, Mijin iman da Mahmud sun gano iyayen Iman.

Hankalin Mummy ya ?i kwanciya, sai da ta zo ta ganewa idonta, Ade ga jikarta, amma ta yi ram da rumaisa, saboda yadda yarinyar ta yi mata.

Da yamma ammi ta ce ruma ta tafi gida, tun da jego take yi, takawa ya ce ta ?yaleta, duk tare za su zauna, su taya iman murna.

Mai sunan baba ma barin iman yayi a gidan, ya tafi gida dan ya huta.

Iman da rumaisa gami da nusaiba, sun kewaye Ade, sai dariya take basu, suna yi mata tambayoyi, har bacci ya kwashe su.

Takawa dama yana Wakinsa na sashin Ammi, fitowa yayi, kusan sha Wayan dare yana nunawa ammi wayarsa, ya ce "Ammi ina mimi, a taso mini ita"

A daren aka wallafa labarin kama Khalifa wakili a Mexico da cocaine.

Ammi ta ce "Bacci take yanzu, ka bari da safe"

Ya ce "Ammi ba zan iya jira ba, a taso mini ita dan Allah"

Haka Ammi ta je ta taso masa ruma, ya ja ta Wakinsa ya nuna mata.

"Ban gaya maka ba papa, duk wani azzalumi da ya fi ?arfinka, bai fi ?arfin Allah ba, ka zuba ido zaka ga yadda Allah zai WaiWaita azzalumai, yanzu ma ga ta in da Wan nasa zai yi takara, kuma wannan abun da aka kama Wan sa da shi, ya isa ya saka baban nasa ma su faWi zaSe".

Alwala takawa yayi, ya din ga salla yana godewa Allah, ko wannan tashin hankali ya isa hana wakili sukuni, Wan sa yayi laifi da ?asar da bashi da halin yin cuwa-cuwa.

Ruma kasancewar jiya ba ta yi bacci da wuri ba, ya sanya take ta bacci da safe.

Ammi ta saka aka Worawa ruma ruwan zafi.

Ade ta ce lallai a kai su su gaida iyayen mai sunan baba ma, Ade ta yi wa Ammi addu'a da iyalan ta da fatan alkhairi, bisa jajircewa kan ri?e amana.

Takawa ne ya je yana tashin ruma, ta buWe ido ta tashi zaune, ya ce "Ammi ta ce ki tashi haka, ki yi wanka sabuwar kakar ki ma tana nemanki".

Wani irin zilllo ruma ta yi tana haki, ta yakushi takawa a wuya ta fita da gudu daga Wakin, bayan ta ya bi yana kiran sunanta, ta baya ta Sulla in da ake girki idan da ba?i a gidan, ta kefa wani abu a cikin murhu.

Kan ya ?arasa wurin kuma ta faWi, cikin tashin hankali ya Wauke ta, ya kaita Waki, sai dai a sume take.

Ammi ya je ya gayawa abun da yake faruwa, hankali tashe suka nufi Wakin da take.

Kasancewar iman nursing take yi, ta dudduba ruma, amma babu wani abu da yake nuna akwai matsala a vitals Win ta.

A hankali ta yi juyi, ta ta da kai da hannunta kamar mai bacci, Ammi ta ce "Alhamdilillah, iman ku Waukko mp a kunna karatun Alkur'ani, ko wani abun ne ya sameta" iman ta jinjina kai ta aiwatar da abun da Ammi ta ce.

Mutane na ta zuwa ganin dangin iman, su Ade sai godiya suke yi musu na ri?e musu ?a.

Ade ta dame su da tambayar ina rumaisa, iman dai ta fito ta gaya mata halin da ake ciki.

Har kan rumaisa Ade ta je, ta dafa kan rumaisa ta ce "Wannan ai kamar shaiWanu ko sihiri"

Tun sanin da Ammi ta yi wa Ade, mace ce mai ibada da yawan addu'a, duk da kasancewar ta ba wata mai ilimi mai zurfi ba.

Ta dafa kan rumaisa tana ta yi mata addu'a, a hankali ruma ta ce "papa"

"Na'am mimi"

"Wata mage ce za ta sha maka jini a wuyanka, ta kasa"

"Babu wata magge fa, tsorata ki ka yi, bacci ki ke yi"

"A'a ta yakushe ni a hannuna, idonta haya?i ma yake yi" ta nuna musu hannunta, in da aka karta mata farata.

Ade ta ce "yarinya na jego kun barta tana yawo ko ina, gashi ba ta son Wan kwali, idonta ne ya buWe take gane-gane ai". Aka samu dai ruma ta farfaWo, sai dai ba ta magana sosai.

A yammacin ranar su Ade har gida suka je, suka gaida mama, dan a washegari suke son komawa.

Mai sunan baba ya tabattar musu da yardar Allah, zai kawo musu iman, ta ga dangin ta.

Har gida suka sake bin mai girma wambai, suka sake yi masa godiya, turaki kuma a lokacin yana Germany.

Hajiya Lubabatu wani irin ciwon kai ta din ga fama da shi, mai tsananin gaske, da har ta kai ba ta gane mutane sosai, kuma ba ta son haske sai duhu, tayi ta surutai na fita hayyaci, haka aka kaita asibiti aka ajiye.

Ranar da su Ade suka koma, ranar mai sunan baba ya koma lagos shi ma, sai dai mahmud ya rasa sukuni, amma bai gayawa kowa abun da yake damunsa ba, iman ta yi wa mahmud godiya, daga shi har mijinta, bisa ga namijin ?o?arin da suka yi mata

Still a yammacin ranar, wani tashin hankalin ya sake afkuwa, Allah ya yi wa galadima rasuwa, wato mahaifin jabir, Senator wakili kuma ya hau jirgi domin zuwa Mexico, sun samu plane crash, da shi da wasu manya-manyan ?usoshi a Nijeriya, wanda galibin su tare suke har?allar smoke duk suka mutu.

Duk mutuwa mutuwa ce, takawa yana jimamin rashin Wan uwan mahaifinsa, gefe guda kuma yana farincikin hukuncin lokaci Waya, da Ubangiji Allah ya haWa azzalumai yayi musu.

Ahalin masarautar kuwa suka shiga taradaddi da damuwar gagarumin rashin da aka yi, turaki ne ya yi clearing komai, ya taho da gawar Kano.
Ga matarsa na can kwance a asibiti, Wan sa kuma aka kawo shi cikin sar?a, sai a lokacin mutane hankalin su ya koma kan cewa matar galadima ba su suka yi jinyarsa ba, baro shi suka yi a can, aka din ga Allah wadai da ita.

Kwanaki uku da rasuwar galadima, ba a ga Mummy ba, mutane suna ta tambayar Ammi, wai ba su ga Mummy ba.

Kwana na huWu mahmud ya je ya samu ammi, ya ro?eta dan Allah ta kira takawa da rumaisa da iman, su haWu a sashin Mummy.

Ammi ta ce masa ba damuwa, dan kuwa yanzu ba ta ?aunar duk wani abu da zai sanya mahmud Win damuwa.

Hankalinsu ba ?aramin tashi yayi ba, da suka ga Mummy, gaba Waya jikinta a ?one, sai ihu take tana kiran sunan rumaisa, ruma kawai ta fashe da kuka ta rirri?e takawa saboda tsoron da Mummy ta bata.

Wambai ya kalli Mummy ya ce "Jamila, ya aka yi ki ka ?one haka?".

Cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali, ta din ga faWar miyagun abubuwan da ta aikata ita da Hajiya Lubabatu, babu wanda yafi Waga musu hankali, irin yadda ta kai Adam wurin boka a ka zu?i jininsa, kuma duk shekara irin bala'in da yake shiga saboda asirin da tayi masa.

Kasancewar sa da runaisa ne, ya sau?a?a masa wasu abubuwan, kuma a wannan karon ma, aljanar ce ta zo shan jini da take duk shekara, ta kasa ta sanya ruma na?udar dole ta kashe Wan, still ta cigaba da bin adam ta sha jinin da ta saba, saboda ba zata iya cigaba da aikin da aka bata ba, sai da jininsa, shi ne take ta dambe da rumaisa, ta fito a suffar mage, rumaisa ta jefata a murhu. Shi ne ta shiga jikin Mummy, ta ce sai dai tayi jinyar a jikinta, idan mutuwa ce su mutu tare tun da tsayin shekaru ita take yi wa aiki.
Wannan matar da rumaisa take gani, da haya?in da idonsa ke yi, aljanar take gani. LA ILA HA ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINA ZALIMIN, da rumaisa ta ri?a, tun da lokacin da ta san falalarta, take ganin fa'idarta a rayuwar ta.

Wambai ya ce "Anya ba surutan ciwo ne ya sanya take maganganun nan ba".

Mahmud ya girgiza kai ya ce "Ba zafin ciwo bane, muna bibiyar duk wayar da Mummy take yi, kuma tun asali na san wasu abubuwan, ba abun da zan iya yi a kai ne"

Kuka ammi take kamar ta fita a hayyacinta ta ce "Jamila me nayi miki haka a rayuwa ne? Haba Jamila shikenan bawa ba zai Wau ?addara ba, duk saboda marigayi ya fara aure na?"

Mahmud ya zube a gaban Ammi ya ce "Ammi, dan girman Allah ki yafewa Mummy, na sam ta cutar da mu, amma ta ri?e ni kamar ita ta haifeni, dan Allah ki yafe mata"

Ruma ta ce "Wallahi ba zata yafe ba, nima ban yafe ba, dukkanin mu bamu yafe mata ba, dare na din ga bi, ina kai ?arar ku wurin Allah, sunayenku na din ga gaya wa Allah, kuma yayi mana maganinku, yau na cika al?awarin da na Wauka".

Su Fauziyya sai kuka suke yi, wambai ya ce "Jamila baku yi wa kanku adalci ba, ki ka saka na din ga ganin baiken Binta, ina goyon bayanki, kanki ki ka yi wa. Binta ki Wauki yaranki ki tafi da su, Allah ya haWa miki kansu, mun yi magana da mai martaba da ?an majalisar sarki ma, Adam ne zai gaji kujerar galadima.
Binta ki yafe mini abubuwan da suka din ga faruwa, ke kuma wannan yarinya rumaisa Allah ya ?ara haskaka rayuwarki, kin kawo sauye-sauye da tarin alkhairi a wannan gida".

Ammi ta rungume Mahmud tana rarrashinsa, sosai yake kuka yana Ammi ta yafe musu baki Waya.

Su Fauziyya sai kuka suke yi, ru?ayya na gefe ba ta iya magana, dan tun da Mummy ta fara rashin lafiya abun ya shafeta, take abu kamar taSaSSiya.

Kwanaki uku aka yi bikin naWin sarautar takawa zuwa galadima, shi kuma ya yi wa rumaisa sarautar garkuwar galadiman kano.

Kwananta arba'in da haihuwa, ya biya musu umara, shi da ita da ammi da mama, suka tafi domin nuna Godiyar su ga Allah.

Kamar yadda mai sunan baba yayi al?awari, Iman ta je ta ga danginta, mutane masu karamci da tarin dukiya.

Kamar yadda ammi ta yi al?awari, sabir na isa shiga makaranta, ta basu Wan su, lokacin ruma ta kammala secondary school, sai dai da laulayin wani cikin ta shiga makaranta, take karantar criminology. Kamar yadda suka yanke shawarar hakan ita da takawa.

Cike da tausayawa mai sunan baba yake kallon iman, ta shirya ranar graduation Win su, cikin ta kamar yayi magana saboda girma, scaninc ya nuna tagwaye ne a cikinta.

Mai sunan baba in dai yazo baya bari ta yi aikin komai, manyan mutane sun halarci bikin kammala karatun su iman.

Hajiya Lubabatu brain cancer ta samu, kanta ya din ga Wurar ruwa, aka fita da ita ?asashen ?etare, sai dai duk da an saki Jabir, bai iya zuwa yayi jinyarta ba, sai ?an uwanta.

Mahmud ya koma aiki, idan ya zo kuwa, kullum sai ya je duba Mummy, sai dai abun nata babu cigaba, kullum ciwo ?ara jagwalewa yake yi, an kai ta asibiti dressing ake yi, amma ?una sake jagwalgwalewa take yi, tana wani irin wari.

Turaki ya tattara iyalin sa yayi watsi da su, duk wani abu na kyautatawa tsakanin su, ya daina yi musu, Jamil aka din ga i?rarin ya mutu a hannun DSS saboda babu wanda ya san a in da yake.

Mai sunan baba kan Iman ta haihu, ya canza musu gida, gida mai kyau sosai da sosai, daga Lagos yake sayo kaya yana aiko wa da Usman da Aliyu kayan takalma, computer da yadiddika da lesuna da ga Aba yana aiko musu da shi, iman da ruma da nusaiba suka haWa kuWi, suke tura masa suma suna karSar takalma da laces.

Yaya Abubakar da yayi aure, jigawa ya koma, saboda a can yayi karatu ya saba da mutane, kuma cikin ikon Allah ya samu aiki a can.

Alhaji Aminu ya din ga jan mai sunan baba a jiki, yana koya masa yadda ake importing kaya daga ?asashen ?etare, mai sunan baba ya ce a koyawa su Aliyu, sune suka fi ga harkar kasuwanci, kar son rai ya shiga lamarin tun da yana aiki da hukumar hana fasa ?wauri.

Tagwayen mata aka yi wa Iman aka ciro mata, masha Allah

126 / 128