Author : BATUL MAMMAN Category : African Stories & Novels
kiyaye bakin shi yafi akan fadar magana mara alkhairi. Ki sani a dangina ko naki, makota ko abokan arziki dole watarana sai anyi miki gori a gabanki ko bayan idonki wannan bani da haufi akansa. To ina so duk lokacin da aka fada miki maganar da ta shafi rayuwarki ta baya kuma bana wurin bare na kare miki ki sani cewa Ishaq yana son Asmau. Ki sakawa ranki akwai wanda zaki zo kiyi kuka a gabansa ya rarrasheki, akwai wanda yake kaunarki saboda Allah yake fatan kasancewa abokin rayuwarki har a aljannah."
Ba sai na fada ba Asmau kuka take yi sosai saboda yadda kalaman Jikamshi ke ratsata. Shi kanshi a raunane yake idan ya tuna cewa duk su biyun suna da abin fada a rayuwarsu.
"Abu na karshe Matar Jikamshi ina so don Allah kiyi hakurin zama dani. A duk lokacin da kika ji anyi haihuwa zuciyarki ta kwadaitu da son ina ma kece maijegon to ki tuna cewa samu da rashi na Allah ne. Da kudi na bayar da haihuwa da wasunmu sun sayar da komai nasu don suji kukan jariri a gidajensu. Ki godewa Allah kina da wadda zaki kalla a matsayin tsatsonki. Ni bani da wannan kuma na yarda na karbi kaddarata. Ina fatan hakurin da nake da wanda zaki zo ki tayani muyi ya zama silar samun rahmarmu a wajen Allah"
Da gaske Asmau take kuka. Abinda ake gudu ya riga ya faru. Allah Ya kara kare sauran 'yan uwa musulmi. Ji take duk duniya idan ba da Jikamshi ba bazata taba iya rayuwar aure da wani ba. Shi kanshi idonsa yayi ja amma sai ya daure yace "kinsan dai ba'a daura mana aure ba don Allah ki dena kukan nan. Nafi so ki tara shi sai ranar da idan kinyi zan daukeki na...."
Da kukan nata da jikakkiyar fuska ta dago kanta tana murmushi tare da dora hannunta irin yadda yayi a lebenta "shhhhh Jikamshina kada ka karasa ko na gudu"
Yayi murmushi "ina sane na turaki cikin motar don kada kice zaki gudu. Share hawayenki kinji Matar Jikamshi. Kada Umma ta hanani aurenki, kullum nazo sai kinyi kuka."
Tissue din gaban motar ta zara tana goge hawayen yana fada mata wuraren da kwalli ya bata. Tace zata duba madubin motar yaki yarda. Haka ta goge suna kallon juna suna dariya.
Sun danyi hira yake ce mata sunyi magana da Umma yana ganin nan da wata uku za'a saka musu rana. Umma tace akwai bikin Dijan Anti Bintu wata biyu masu zuwa wanda shima lokacin yaso ayi aurensu. Yasan kafin nan ya gama gyaran gidansa.
"yanzu da Umma kayi zancen saka rana?"
"Na lura kin mayar dani mara kunyan karshen zamani. To Ismail ne ya fada musu. Ni shiru nayi ina ta sunkuyar da kai irin yadda kike yi"
Dariya take yi wanda hakan yake sanyaya masa zuciya. Yana jindadin ganin ya faranta mata. Sun fi awa daya a wurin batare da sun san lokaci ya wuce ba. Ismail ne ya fito da Amatullah a bayansa. Haka nan Allah Ya dora masa son yarinyar nan. Shi bai ki ba wallahi Asmau tace ta bar masa ita.
Suna zuwa gaban motar Amatullah tace "Ummi kinga sabon Baba ya goyani."
Col. Ishaq ya tashi tsaye ya sauko da ita daga bayan Ismail sannan ya dorata a cinyarsa.
"Idan banyi da gaske ba naga alama zaka yi min kwacen 'ya"
"Colonel ai na gama da kai. Ka taho nan sace zuciyar Umminta da dadadan kalamai ni kuma ina nawa yakin a kanta da kayan kwadayi. A takaice dai yanzu nine baban"
Asmau ta rufe ido tace "Yaya Ismail kada muyi haka da kai"
Jikamshi yace "gara ki kira Musaddiq yaya da wannan. Shifa bai san ya girma ba. 'ya'ya biyar amma idan yana barkwanci kamar mara iyali."
"Kada ka zubar min da girma mana soja. Yanzu dai gaskiya Madam ta damu ban koma gida ba tun fitar safe. Ummin Amatullah taimaka ki sallame shi mu tafi. Don ma na fada mata Yayanta na rako zance yau da an hanani tuwon dare"
Ta fuskanci da gaske Ismail mutum ne mai barkwanci. Jikamshi ya katse mata tunani da cewa "haka suke daga shi har matar tasa. Gidansu kamar gidan wasan yara"
"Allah Sarki kace ina gaisheta"
"Fada mata da kanki dai" Ismail ya ciro wayarsa ya kira Aisha matarsa. Da gaskiyar Jikamshi kuwa don da gaske Aisha tayi ta janta da hira da wasa kamar ta santa. Karshe tayi ta jaddada mata ta rike amanar yayansu. Ita dai Asmau sai dariya kawai. Bayan sun gama wayar sukayi sallama dasu. Jikamshi kamar kada ya tafi. Ba don dare yayi ba kuma dai yakamata Ismail ya tafi gida yau da Umma sai ta koreshi da kanta.
A hanya ne ya dubi kaninsa yace "nagode Ismail da yadda kake yiwa Asmau da Amatullah "
Idonsa na kan titi yace "Colonel nine da godiya da ka yafe min maganar da nayi maka rannan. Duk da bana ganinsa amma na tabbatar shaidan ne irin masu hada fada tsakanin 'yan uwa ya murde min harshe na fadi abinda banyi niyya ba"
Murmushi dan uwan nasa yayi "zaka fara ko, kada ka damu komai ya wuce a wurina in sha Allah. Ka fadawa su Dahiru idan zasu sami lokaci karshen sati sai muje Jikamshi ayi magana dasu Kawu"
*****
Ranar Juma'a da yawancin ma'aikata ke tashi da wuri Col. Ishaq da kannensa maza suka tafi garinsu, Jikamshi a Katsina garin Dikko...Katsinawa kunya gareku ba tsoro ba. Kafin tafiyarsu dama Hajiya ta riga ta fadawa Yayanta da kuma kanin mijinta komai game da Asmau a waya. Kamar yadda yayi tsammani bai sami goyon baya sosai daga garesu ba. Wani kawunsa ma cewa yayi indai saboda rashin haihuwa ne yasa zai auri karuwa, karuwar ma mai 'ya to akwai zawarawa a gari masu yara ya zaba a cikinsu don Allah Ya aura amma kada ya gurbata musu dangi. Su da suka je yin kwana biyu basu sami dawowa ba sai litinin. Col. Ishaq sai da ya taba rashin kunya aka sami daidaito tsakaninsa da Kawunan nasa da manyan Gwaggoninsu. Daga karshe ma dai harda wa'azi da nasiha ya hada. To anyi sa'a da yake ana ganin girmanshi gashi kuma da dan abin hannunsa sai suka gama fadansu suka amince zasu taho Kano nan da sati biyu. Kamar yadda ya saba ya hadasu da alkhairi kafin ya tafi. Wannan karon harda kari don kada su bashi kunya ma.
*****
A bangaren su Asmau kuma washegarin da Jikamshi yaje gidansu Qasim yazo. Ya nuna mata ya janye batun aurensu kuma yana mata fatan alkairi a zamansu da Col. Ishaq. Taji kunya sosai tace "Yaya Qasim kayi hakuri da hukuncin da na yanke a matsayin zabin Allah. Bazan taba mantawa da abinda kayi mana ba. Duk da kaine babban abokin Yaya Abubakar amma hakan ba shine yake nufin sauran su gujemu ba. Tun ranar da ya rasu ban kara jin duriyar kowa ba sai taka. Nagode Allah Ya baka mace tagari kamilalliya."
Yayi mata murmushi "babu wata godiya mata zaki nemo min kawai."
Itama tayi murmshin ga dan hawayenta "to In sha Allahu zan nema maka kuwa"
"Kada ki dauka wannan abin zai shafi zumuncinmu Asmau. I am always here for you. Ki daukeni dan uwanki wanda zaki iya fadawa matsalolinki. Shi kuma soja tunda yayi min fin karfi ki fada masa aure bazai yiwu ba sai ya kama kafa dani."
"An gama ranka ya dade" ta fada zuciyarta wasai. Alhamdulillah dama bata so su rabu ana jin haushin juna.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽50
Batul Mamman💖
Tun daga wannan lokacin tsakanin Matar Jikamshi da Jikamshinta wata sabuwar soyayya ke tashi da shakuwa. Duk wani labarin rayuwarsu da basu sani ba a da yanzu sun fayyacewa juna. Komai nasu abin shaawa sannan suna soyayya a tsaftace. Irin hirar nan da zata jawo budurwa da saurayi su fara sakin layi har a kai ga jin sha'awar kusantar juna sun nesanta kansu da ita. Kuma duk da haka idan kaga yadda suke sai sun burgeka. Wannan ita ce soyayya ta gaskiya. Duk wata hira mai tado sha'awa sunanta batsa kuma tana cikin jerin abubuwan da suka kusanci zina indai ba ga ma'aurata ba wanda Allah SWT Ya umarcemu da mu nisanta kawunanmu da ita. Allah Ya kara shige mana gaba.
*****
Bayan sati biyu kamar yadda suka yi alkawari kawunnan Col. Ishaq suka zo daga Jikamshi. Haj Lubabatu ta shirya musu tarba mai kyau sai da suka ci suka koshi sannan sauran kannensa maza suka yi musu jagora zuwa gidan Umma. A nan din ma tun safe ake shirin zuwan nasu. 'Yan uwa da abokan arziki sun taro. Alh Adamu ma da tasa gayyar duk don a taru a rufawa juna asiri. Baki kam sun ga karamci kuma sun yaba. Matsalar dai itace haihuwar Asmau kafin aure. Amma tunda dan nasu yace yaji ya gani dole su bi yarima su sha kida. Dubu dari suka bada wanda yasa su Baba nuna a rage. Wani cikinsu dan tsoho yace ko kwandala bazasu rage ba. Dansu yace lallai abinda zaa bayar kenan ko sama da haka. Kawu Garzali sai murna yake. Allah Yayi Asmau zatayi aure kuma zata auri wanda yake matukar sonta. Adduarsu Allah Yasa soyayyar ta zarce har gidan aure. Taro ya tashi cikin mutunta juna aka yi sallama suka tafi.
*****
Asmau kuwa da wuri ta fita amma ta bar Amatullah a gida. Hankalinta a kwance wannan karon kana ganinta zaka san amarya ce mai murna da dokin lokacin aurenta. Da kwatance saboda sababbin gine gine ta isa gidansu Walida tsohuwar aminiyarta. Har kofar gidan adaidaita ya kawota. Tana sauka a kofar gidan Walida ta fito daga makotansu. Hada ido suka yi sai suka tsaya kallon kallo kowacce tana zubar da hawaye. Duk su biyun abubuwa da dama suke tunawa wanda suka wargaza musu rayuwa. Asmau ce ta fara yunkurawa kafin ta karasa itama Walida ta taho cikin sauri suka rungume juna. A bakin kofar gidan suka fashe da kuka sosai suka rike da juna. Mutane kuwa sai kallonsu suke yi. Sai da suka dan nutsu Walida ta ja hannunta suka shiga ciki. Antin Walida matar babansu na zaune tana yankan farce suka shigo. Murna ganin juna suke sosai. A firgice ta tashi tana nuna Asmau.
"Wa nake gani kamar Asmau?"
Walida tace "ita ce Anti"
Ta karewa Asmau kallo sannan ta tabe baki "to ina abinda kika haifa. Ai na jima da jin labarin kin dawo Kano da dane ko 'ya ni ban rike ba. An gama yawon ta zubar an dawo gida."
Murmushi Asmau tayi, irin wadannan maganganun 'yan uwa da yawa da Jikamshinta sun fada mata dole ko taki ko taso sai tayi hakuri dasu. Kuma sanin halin Antin na kwarewa wurin rashin mutunci yasa bata dauki abin da zafi ba. Walida ma da a da tasan cewa bata shiru, idan matar nan tayi mata ramawa take suyi ta cacar baki kamar kishiyoyi shiru Asmau taga tayi. Ta kama hannunta suka shiga dakinta. Kan wata kujera suka zauna Walida tace
"Ashe rai kan ga rai 'yar uwa? Na fidda rai da sake haduwa dake wallahi"
"Kiyi hakuri Walida. Na dan jima da dawowa amma na rasa me zamu cewa juna idan muka hadu. Har ga Allah abinda ya faru dani shekarun baya kika gujeni yasa ban kara nemanki ba"
Walida ta share kwalla "ki yafe min Asmau, na cutar dake da na zama sanadiyar koya miki dabi'un da ba naki ba. Ba haka kawai na gujeki ba amma..."
Asmau tace "kada ki damu. Yaya Qasim ya fada min kema duk abinda ya faru dake. Mu kuma haka Allah Ya rubutu mana tama jarabawar" da kuka ta karashe maganar. Suka taru su biyu suna yi babu mai rarrashi. Asmau na tuna rasuwar Abubakar da cikin da aka gane tare da ita a ranar da ya rasu. Ita kuma Walida tana tuno ranar da mahaifinta ya kamata da saurayi ya zura hannuwansa cikin rigarta. Wa'iyazu billah wadannan 'yan mata bazasu manta da sharrin social media ba.
Da suka gama kukan ne suka bawa juna labarin irin gwagwarmayar da suka sha. Walida tayi murna da jin zancen auren Asmau sannan tayi ta kallon hotunan Amatullah a waya tana mita ba'a zo mata da ita ba. Itama ta bawa Asmau labarin irin takunkunmin da babanta ya saka mata saboda jin labarin cikin Asmau. Karshe ma ko karatun jami'ar bai bari ta kammala ba yace sai tayi aure. To gashi shekaru shida babu auren babu karatun sai zaman gida da zuwa islamiyya. Matar gidan ta sami yadda take so wurin fadawa Walida maganganu sai dai ta dena ramawa saboda yanzu babanta bai damu da lamarinta ba. Indai ba aure tayi ba shi baiga amfaninta ba. A wannan zaman gidan kannenta biyu 'ya'yan Anti sunyi aure har sun haihu. Bata yawo daga islamiyya sai gida sai kuma abinda ya zama dole. Samari kuwa kamar anyi ruwa an dauke. Babu mai zuwa yanzu.
Asmau tace "dukkanmu munga irin abinda ake gudu a waya da social media. Allah kara rufa mana asiri duniya da lahira."
"Amin Asmau, amma ai kinfini ganin tashin hankali. Kullum ina miki addua Allah Yasa kada rayuwarki ta lalace da kika bar gida. Da farko a social media na fara watsa hotunanki cigiya kafin Baba ya karbe wayar. Rabona da wayar arziki na manta"
Yini suka yi suna hira sai bayan laasar lokacin da Asmau ta tabbatar an gama taron gidansu tayi haramar tafiya. Jikamshi yayi mata waya yace to ta fara shiri sauran kadan fa ta karasa zama matarsa yana fatan za tayi shiri mai kyau kafin zuwan lokacin. Yaso zuwa daukarta ma da kansa amma kamar yadda suka faro da bin komai yadda ya kamata sai ya hakura. Wani lokacin ko babu social media idan budurwa da saurayi suka kebe su kadai a mota sanyin AC yana dan ratsasu sai shaidan ya fara kawo musu hari. Ko kadan babu burgewa kice wai duk inda zaki saurayinki shine yake kaiki ya dauko ki. Ki duba da kyau kiyiwa kanki adalci watarana ko dan yaya sai anyi abinda bai dace ba ko da kuwa taba hannu ne. Yau da gobe ai tafi karfin wasa.
******
A cikin wata daya Col. Ishaq ya dage sosai ana ta gyaran gidansa. Duk inda yake bukatar canji kamar kayan cikin toilet irinsu baho da sink an canza an saka komai sabo. Haka ma a kitchen da su kofa. Ga fenti sai da ya kira Asmau ta fadi irin kalar da take so. A bangarensu ma Umma ta tashi tsaye sosai. Daga Asmau yanzu babu kowa a gabanta sai Yassar. Su Shemau ne suka je suka gano gidan aka zo aka fara siyayya. Dole ita ma ta dage ta fito da 'yarta ta. Gado ma ready made ta siya guda biyu tare da sauran kayan gida. Shemau, Jafar, Kawu Garzali da gidan Mama duk ba'a barsu a baya ba. Kowa akwai abinda ya dauki nauyi don ganin cewa Asmau ta sami nutsuwa a rayuwarta. Ita kam sai son barka da yi musu addua.
Saura kwanaki biyar su tafi Zaria bikin Dijah. Umma da Anti Bintu basa zama kullum sai an fita siyayya saboda ana gama na Dijah da sati hudu za'ayi na Asmau.
Jikamshi yazo yiwa Asmau sallama tafiya ta kamashi Warri zaiyi sati uku. Zaune yake ya dora hannuwansa akan cinyarsa sannan ya tallabi fuskarsa dasu yana kallon Asmau. Kallon ya takurata tace "Jikamshina zan tashi fa idan baka dena kallona na ba"
"Tashi ki tafi ban hanaki ba. Amma ki sani zan je na sami 'yan matan Warri na kalla son raina"
A shagwabe tace "don Allah ko da wasa ka dena fadin haka. Kada kasa na kasa bacci yau"
"Shine kike son hanani baccin? Daga gobe fa zanyi sati uku ban sakaki a ido ba. Ji nake kamar a daura auren nan na tafi dake. Idan mun dawo sai ayi bikin, kada kice wani abu nasan kema haka kike so ko Matar Jikamshi" wannan lumshe idon yake mata. Ita kuwa ta soma dariya.
"Wane irin aure ne amarya da ango zasuyi tafiya bayan an dawo ayi biki."
Yace "to kawai idan mun dawo mu wuce gidanmu ko. Tsayawa bikin duk bata lokaci ne."
Dariya Asmau take yi kawai. Jikamshinta yau sai wani marairaicewa yake.
"Kada ka damu ni dama ba wani biki nake so ba. Zuwa za'ayi ayi ta kallona. Na fadawa Umma ayi komai a rana daya. Bayan daurin aure mata kadan su zo a kaini."
Col. Ishaq ya gane sarai dalilinta na yin haka. Yadda mata ke son biki amma tace bazatayi komai ba saboda surutun jamaa. Dena wasan yayi yace "Matar Jikamshi ko me kika yi na fada miki dole za'a sami masu magana. Bakiji ance Dan Adam mai wuyar gane hali ba. Idan kinyi biki ace baki da kunya ko makamancin haka, idan kin ki biki ace ko dan bikin nan batayi ba don kada mutane su je. A wurin Dan Adam bazaka taba fita ba. Saboda haka biki da akeyi abu na lokaci daya zukatan masoya suji dadi na makiya su fashe...."
Da har ta fara kwalla sai yanzu tayi dariya. Shima biye mata yayi.
"I am a soldier Matar Jikamshi. Dole nayi aure irin na sojoji. Su Safiyya suna can suna tsare tsare kamar yadda su Ainau suke yi. Zamuyi aure da biki kamar kowa kinji ko. Duk wanda ya fada miki mara dadi ki rinka tuna ranar asabar din da zaki tare a gidana. Ranar da Jikamshinki zai nuna miki matsayinki a rayuwarsa. Wannan ya isheki maganin duk wani bacin rai. Look forward to being Mrs Jikamshi a zahiri." Gyara zama yayi bayan ya gama maganar yana son ganin yanayinta. Kasa take kallo tana wannan murmushin da ta saba idan tana jin kunyarsa. Bai barta haka ba sai da ya tabbatar mata lallai bikinsu za'ayi taro kamar na kowa. Masu farinciki da 'yan saka ido kowa ana gayyatarsa. Addua zasu cigaba Allah Ya kare duk wani tashin hankali da abin ki har ayi a gama lafiya.
Da zai tafi Asmau harda kuka. Tana ta cika masa baki sati uku ba komai bane zata iya jurewa ko basu hadu ba akwai waya. Hoto ya rinka daukarta fuska a kumbure saboda kuka. Da ya shiga mota ya tayar tace "Jikamshina don Allah kada ka kalli kowace mace. Ai ni kadai na isheka ko?"
Ya murmusa "anya kuwa? A haka kinsan bazan tabbatar ba sai nan gaba. Idan rabon na hadu