Author : BATUL MAMMAN Category : African Stories & Novels
rasuwa yayi ko sakinta yayi. Wasu ma suyi ta cewa mai zai sa Qasim ya fara da auren bazawara. Babu yadda za'ayi su boye gaskiyar lamari. Wasu ma sun dade da sanin rasuwar abokin Qasim da cikin da yayiwa budurwarsa. Gulma da kananan maganganu sai yawo suke. Ko kadan Inna bata jin dadin hakan duk da tana kokarin yiwa Malam biyayya ta nuna ta amince da auren.
"Sai anyi magana kayi ta murmushi kamar wani bazawari. Ya dai kamata kafin komai ya kankama kuje ayi mata gwajin 'yan cututtukan nan na zamani musamman kanjamau"
"Inna ba fa karuwanci taje tayi ba. Aikin asibiti tayi duk tsahon lokacin nan"
Tabe baki tayi "haka dai ta fada muku ku kuma kuka hau kuka zauna. Mace babu mai kwabarta ai sai ta mike kafa. Ni dai ba wani abu nace ba. Ayi mata gwaji ko don taka lafiyar. Gurbacewa ce dai ka gama gurbata mana dangi. Ko me kuka haifa nan gaba sai ance yayarsu shegiya ce"
Har ransa Qasim baiji dadi ba. Innarsa ta lura da yadda ya hade rai tayi murmushi "Baba kenan, kada ka daukeni muguwar uwa wadda bata son danta yayi aikin neman lada. Duk wata uwa komai shedancin danta tana son ya auri mace tagari. Abubuwan da kaga suna ta faruwa da yarinyar nab kadan ne daga *abinda ake gudu* a zina. Bana muku fata amma wata rana idan kunyi aure zata iya yin abu da zuciya daya amma saboda sanin da kayi na rayuwarta ta baya kawai sai shaidan ya kitsa maka zargi ka hau kai ka zauna. Karuwai da yawa sun yi aure. Wasu ma a gidan mijin suke sheke ayarsu. An sani amma da yake aure rai gareshi sai kaga ba'a sake su ba. Kasan halina bana boye abinda yake raina. Idan ka auri Asmau kayi mata halacci kuma ka rike amanar abokinka. Ka gyara abinda ya bata. Sai dai bazan fasa nanata maka ba ina so ka kara aure a gaba."
Duk maganar Inna yasan gaskiya ne. Idan Asmau zata taba mantawa da juyin da rayuwarta ta samu sai dai idan an goge wannan bakar ranar da tayi sanadiyar tarwatsa mata rayuwa.
"Akwai wadda kike so na aura ne? Da niyata bazan kara aure ba bayanta."
"Yo dan nan kasan me gobe zata haifar ne da zaka ce haka? Zabin wata matar yana daga gareka don kada ma a sami matsala nan gaba kace nice na zabo matar. Bari na shiga wurin Malam naga la'asar ta kusa"
Da Inna ta tashi Qasim dogon tunani ya zauna yi game da auren Asmau da ya takurawa kansa lallai sai yayi. Burinsa ya kyautata rayuwarta ba ya zama sanadiyar kunci da bacin ranta ba. A yadda ya fahimci hirarta da Col. Ishaq kwanakin baya ba karamin so suke yiwa juna ba. Addua ya rinka karantowa a zuciyarsa
"Ya Allah, na sani ina daga cikin mutanen da suka batawa Asmau da Abubakar rayuwa. Allah Ka yafe mana baki daya. Ka zaba mata miji nagari tsakanina da Ishaq. Idan aurenta ba alkhairi bane garemu Ka kaita gidan da za'a so ta dominKa."
Tashi yayi yayi shirin masallaci. Yana ganin janyewa kawai zaiyi amma zai tsaya mata sosai idan ta tashi aure. Dole mijin da zata aura ya kasance mutum da za'a iya yarda dashi. Mai amana. Shi kadai yayi murmushi da ya tuno irin kalaman da Col.Ishaq yake fadawa Asmau. Hmmm dole ta so shi ma. Shi kam ya manta rabonsa da tsara mace irin haka. Tun zamanin yana Qasim mai shafe 'yan mata. Rasuwar Abubakar tasa duk tunanin soyayya ya fice masa a rai. Kila harda rashin wannan yasa Asmau bata sauraron shi sosai. Mata da son soyayya kuma....
*****
Haj Lubabatu ke faman fifita an dauke wuta saboda hadarin da ya hado. Ta kira Bilkisu da ke zaune wurin taga tana ganin haske tana karanta littafinta na makaranta saboda test da zatayi washegari.
"Bilkisu ina babanki ne? Na zata ya dawo amma naji shi shiru tun dazu."
"Ya dawo Hajiya, na kai masa abinci ma"
"Duba min kiga me yake yi a ciki tun dazu. Kwanakin nan sai kace wata amarya bashi da aiki sai zaman daki"
Dariya Bilkisu tayi "Hajiya ita amarya zaman daki take yi?"
"Ban sani ba. Wuce ki duba ga magariba ta kawo kai."
Da sallama Bilkisu ta shiga dakin. Duhu ta gani duk labulayen a sauke ga zafi. Daga kan gadon ta hango shi a kwance ya rike kansa. Saurin karasawa tayi bakin gadon
"Uncle Ishaq" ta kira shi a hankali.
Da kyar Col. Ishaq ya iya bude idanunsa. Kansa ke masa wani azababben ciwo kamar zai tsage. Kwana uku kenan yana fama amma na yau yafi tsanani.
"Uncle baka da lafiya ne, bari na fadawa Hajiya."
Ta tashi zata fita wayarsa tayi ringing. Bata yi niyar dauka ba sai da yace "dauki wayar nan Safiyya ce take kira tun dazu. Idan kin amsa ki kasheta kawai. Ga dayar can a kusa da tv itama ki kashe"
Muryarsa da kyar take fita. Hankalin Bilkisu a tashe ta dauki wayar ta fita. Karawa tayi a kunnenta tace "Anti Safiyya bashi da lafiya Uncle din. Kamar ciwon kan nan da yake na bari..."
Gaban Asmau ne yayi mugun faduwa. Baki na rawa tace "Bilkisu nice Asmau. Tun yaushe ne bashi da lafiyar?"
Dan sauke wayar Bilkisu tayi daga kunnenta ta duba sunan. MJ ta gani wanda ta gane yana nufin Matar Jikamshi saboda ta taba ji Uncle din nata ya fada.
"Anti Asmau yi hakuri ban san kece ba. Yanzu na shiga dakinsa na ganshi a kwance. Zan fadawa Hajiya ne ko za'a kai shi asibiti. Dama yana yi idan baya samun hutu sosai."
Idanunta har sun ciko da kwalla , duk abinda tayi niyar fada masa na bacin rai tuni ta manta. Sake rike wayar tayi da kyau tace " Bilkisu don Allah ki kai masa wayar kinji."
Ta san baya son komai idan yana wannan ciwon musamman surutu. Amma kuma bazata iya cewa Asmau a'a ba. Juyawa tayi ta koma dakin. Yana nan inda ta barshi a kwance ta dan kara masa wayar a kunnensa tayi saurin fita kafin yayi mata fada.
Asmau ji tayi kamar tayi tsuntsuwa ta ganta tare dashi. Allah sarki Jikamshinta. Ashe bashi da lafiya shiyasa kwana biyu ta dena jinsa. Haushin kanta taji da har da tayi niyar nuna masa fushinta saboda baya kiranta kuma baije gidansu ba.
Yanayin canjin numfashin da take iya ji yasa ta gane an bashi wayar. Mamakin karfin halin Bilkisu yake da ta kawo masa a halin da yake ciki. Bari ya warke zata fada musu. Rashin Asmau yasa shi shiga damuwa sai yayi ta dadewa wurin aiki. Hakan ya tayar masa da ciwon kai. Sai kuma ga text da tayi tana fada masa yadda suka yi da Qasim akan zasu sake turowa. Tsabar kishi ne da rashin sanin me ya kamata yayi ya kara kwantar dashi. Kamar ba soja ba ya kasa daurewa zuciyarsa yaje ya fada mata ya janye. Dena kiranta a waya din ma ba karamin juriya yayi ba.
Muryarta mai sanyi yaji tace "Jikamshina me ya sameka?"
Bugawa zuciyarsa tayi da karfi da yaji muryarta babu zato babu tsammani. Ba karamin dadi yaji ba ya ratsa shi har ya dan manta da ciwon kan na 'yan dakiku. Bai iya ce mata komai ba sai manna wayar da ya sake yi a kunnensa. Ita kuma ta sake rudewa ko ciwon yayi tsanani ne
"Jikamshina nice, matarka ce, kayi min magana don Allah."
Shiru da ta cigaba da ji ne ya sakata kuka. Dama kullum haka take kamar tana jiran kiris.
Kukan nata murmushi ya saka shi babu shiru. Idon kuka kenan ya fada a ransa kamar yadda yaji a gidansu.
"Its ok ki dena kukan"
Cikin shagwaba tace "Kaji sauki? Ina da ina ke yi maka ciwo? Me yasa baka fada min ba kawai naji ka shiru"
Ta so saka shi dariya yadda yake jin muryarta a hankali amma tana rawa alamun kukan nata bai kare ba
"I miss you too" taji yace a wahale saboda ciwo.
"Uhmm?"
"Duk wannan tambayoyin nan nasan abinda kike son cewa kenan. Kinyi missing dina. But I miss you more Matar Jikamshi. Kin hana Ishaq sukuni."
Jin kanta take kamar anyi mata wani babban albishir da taji muryarsa har ya fara tsokana yadda ya saba. Ta kara kashe murya
"Nima ka hana ni. Har dan wuya nayi. Kasa naji ina kara ....uhmm....na fasa fada"
Sautin dariyarsa taji. Dama Asmau ce ciwon kuma ita ce maganin. Ajiyar zuciya yayi yana gyara kwanciya
"Yanzu ina kwance babu lafiya ma sai kinja min rai. Ki tausayawa patient."
"Kasha magani ne?"
"No, muryarki kadai ta isheni magani. Yau ki shirya zamuyi ta waya har sai kunnenki ya gaji"
Kamar yana gabanta tayi dan fari da ido "bana fatan gajiya da kai Jikamshina. Baban Ama _da kannenta_"
Yaji dadin furucinta amma kalmar karshe ta dawo masa da tunanin da yake addabar zuciyarsa.
"Matar Jikamshi ina son ganinki. Akwai magana mai mahimmanci da zamuyi kinji"
Tunanin maganar aurensu ne yazo mata tace "to Allah Ya kaimu. Ka bari sai kaji sauki sosai. Dama duk na damu ne da naji ka shiru."
"Ki kular min da kanki." Ya iya cewa zuciyarsa babu dadi ya ajiye wayar.
Motsi yaji a wurin kofa ya juya. Hajiya ce a tsaye bai san tun yaushe take a wurin ba. Abin mamaki sai yaji 'yar kunya kadan ba da yawa ba. Itama basarwa tayi ta shigo ciki kamar bata ji komai ba.
"Zaka je asibitin ko kaji sauki? Ni a yadda Bilkisu ta fada min na zata ciwon sosai ya kamaka"
"Sosai ne mana Hajiya. Kamar kan zai tsage haka nake ji"
Tayi dan murmushi kawai "ai naga kamar ka sami magani."
Dariya ta bashi ya tashi zaiyi alwala. Fita tayi tace idan anyi magriba lallai yaje asibiti don tasan ciwon kan baya masa da wasa.
*****
Bayan isha Asmau da Amatullah suna gwada sabon dinkinsu da Yassar ya karbo musu taji waya. Ringtone din Jikamshi daban yake shiyasa ta gane shi. Da fara'a ta dauka don tun wayarsu ta dazu hatta su Umma sun ga canji a tare da ita. Kafin tayi magana yace "fito ina jiranki"
Har wani faduwar gaba taji. Tayi kewarsa sosai amma tana jin kunyar hada ido dashi kuma. A waya ta iya nuna masa soyayya sai an hadu bakin ya mutu. Ga mamakin zuwansa shi da bashi da lafiya. Amatullah ta tura wurin Yassar tace ta fada masa suje babanta ya zo. Ita kuma ta zauna ta gyara fuskarta ta sami mayafi ta yafa sannan taje ta fadawa Umma. Addua tayi mata tace ta gaishe shi. Da ta fita Umma tace ashe ga dalilin sauyin da ta gani a tare da ita. Allah Yayi mata zabi mafi alkhairi. Mai son naka dole ka so shi.
Tunda ta fito daga cikin gidan yake kallonta. Samun kansa yayi da yin godiya ga Allah da ya hada jininsa da Asmau. Yarinyar akwai nutsuwa da kamala. Tana bukatar miji nagari saboda samin ingantacciyar rayuwa da nutsuwar zuciya idan aka yi laakari da kaddarar da ta fada mata. Kuma tana burge shi saboda ta karbi jarabawarta hannu biyu. Har ta iso wurin da yake zaune a gefen mota shi da Yassar da Amatullah kanta na kasa tana murmushi.
Da sallama ta karaso ta dan rissina ta gaishe shi. Ya amsa yana kare mata kallo. Tayi kyau sosai. Shi kuma ta lura ya dan fada.
"Yassar ka shigo dashi falo"
Yace "kiji min mata, ni gurgu ne?"
Ita da Yassar suka yi dariya sannan suka koma falon. Da kyar Yassar ya yiwa Amatullah wayo suka shige ciki.
Daga inda take zaune Asmau ta dan dago kai suka hada ido da Jikamshi. Karuwa sonta yake a zuciyarsa amma dole yayi abinda ya kawo shi. Tattaro duk nutsuwarsa yayi yace......
ABINDA AKE GUDU🙆🏽48
Batul Mamman💖
Ta kagu sosai taji abinda zai fada shi kuma nauyin maganar yake ji. Idan ya fada shikenan yayi musu katanga daga wannan lokacin. Ganin babu amfani yayi ta jan abin yasa yace
"Banda sunan sunan matata ta fari baki san komai game da ita ba ko"?
Asmau ta dan turo baki kishi na cinta duk da bata san matar ba.
"Ni sunan nata ma na manta. Kawai kazo bayan sama da sati daya ka fara min da hirarta"
Yadda take hade rai ya bashi dariya. Ya gyada kai "kishi gareki haka, mun dade da rabuwa fa har ma tayi aure".
"To ai kaine sai ka rasa hirar da zaka yi sai tata"
Ya gyara zama tare da harde kafafunsa "saboda abinda zan fada miki yana da alaka da ita. Ina so ki saurareni da kyau ki fahimci abinda zan fada miki."
Hankalin Asmau ya fara tashi. Wani abu ne ya darsu a zuciyarta ta soma hawaye babu shiri tace cikin murya mai nuna rauni "ba ma sai kace komai ba na gane abinda kake son fada. Aurenta ya mutu zaka mayar da ita ko. Babu komai zan iya zama da kishiya. Don Allah Ka kwatanta adalci a tsakaninmu" ta kare tana jan hanci.
Col. Ishaq bai san lokacin da dariya ta subuce masa ba. Ita kuwa Asmau tayi kicin kicin da fuska. Hankici ya dauko daga aljihun wandonsa ya bata "kinci sunanki Idon kuka. Daga fara magana ji yadda fuskarki ta kumbura. Ai dai kya bari na fadi abinda ya kawoni kafin ki soma zubar da hawaye. Mata na gidan mijinta zaki kashe mata aure da baki"
Dan sanyi taji a ranta kila ba abinda zai fada ba kenan. Har tayi murmushi sai kuma wani tunanin yazo mata "maganar aurenmu ne?"
Ya daga kai yana kallonta. Tausayinta yake ji sosai a ransa.
Murmushi tayi mai ciwo "Hajiya bata amince ka aureni ba ko? Dama nayi tunanin haka zata faru. Ba kowace uwa bace zata iya daure zuciyarta ta bari danta ya auri mace irina. Ko nice kila nayi sama da haka ma. Abinda kayi mana na kyautatawa Allah Ya saka da alkhairi. Nagode sosai wallahi. Ko a haka ma nagodewa Allah da Ya hadani da kai har ka nuna min so ka zama cikin masu nuna min na kara hakuri da kaddarar rayuwa"
Hawaye ke zubo mata tana magana bata ko tunanin tare shi. Dago kansa yayi daga cikin kujerar ya dan matso gaba.
"Ya Salaam, Matar Jikamshi haka kike? Lokaci daya duk kin rikita kanki. Kada ki dauki alhakin Hajiyata wallahi ta amince da aurenmu"
Jikinta duk da haka a sanyaye yake tace "sauran 'yan uwanka ne basu amince ba?"
"A duniyar nan Hajiya ce kadai zata hanani aurenki na hanu. Banda ita babu wanda ya isa. Yara kanana akeyiwa haka ba ni ba. Kamata kowa yasan ina da hankalin da zan san abinda ya dace da rayuwata. Ki saurareni da kyau kiji abinda zan fada. Kamar yadda na fara magana kafin ki katseni da dan bakin nan naki mai bani shaawa..." ya fada yana kashe mata ido.
Kunya taji sosai harda rufe fuska da hannuwanta. Yayi murmushi ya cigaba da magana "na taba aure, shekarunmu shadaya da Badar babu haihuwa. Munje asibitoci da dama ana cewa bamu da matsala. Har maganin gargajiya mun sha. Daga karshe mahaifiyarta tasa na saketa kuma cikin ikon Allah a shekarar da tayi aure ta haihu"
Asmau ta dan girgiza kanta "Allah sarki, dama haihuwa ta Allah ce. Wani baya haihuwar dan wani"
Kallonta yake da mamaki kamar bata fuskanci inda ya dosa ba
"haihuwar Badar ya tabbatar min da inda matsalar take. *Matar Jikamshi, bana haihuwa*. Saboda haka kiyi hakuri da na bata miki lokaci amma na _janye maganar aure a tsakaninmu_."
Tamkar wadda aka watsawa ruwan zafi haka taji saukar maganarsa ta karshe. Shiru tayi na dan lokaci yana ta kallonta yana jiran ta fara kuka sai yaga idanunta ko alamar hawaye babu banda wanda ta zubar dazu. Shirunta tsorata shi yayi yace "kice wani abu mana."
Murmushi take yi kamar bata ji abinda ya fada ba ma.
"Jikamshina"
Jiran amsarta yake na nuna masa bacin rai da bai fada mata tun da wuri ba.
"Lokacin da ka fara sona tausayina kake ji ko kuwa sona kake fisabilillah"
"I love you Asmauna, and I will always do"
Tayi sassanyar ajiyar zuciya "duk macen arziki bata da burin da ya wuce idan zatayi aure ta kai budurcinta gidan miji. Jikamshina na rasa wannan damar har abada. Na fada tarkon shaidan har ya zamana ina da shaidar da duk wanda ya kalleta bazai manta da cewa Asmau ta taba bayar da jikinta ga mutumin da babu aure a tsakaninsu ba. Ni abar gudu ce da kyama a cikin mutanenmu. Bani da sauran daraja da kima a idon jama'a sai dai kawai ayi min kara. Da wannan ciwon nake kwana nake tashi kuma dashi zan koma ga Mahaliccina. Idan aka kallemu sai an sake. Ga wadda tayi cikin shege nan. Amma duk da wannan nakasar ta rayuwata kake sona saboda Allah. Ka rike 'yar da bata da uba na aure a matsayin taka. Ka nuna min ina da sauran darajar da zaka iya zama dani. Shine yanzu zaka ce zaka barni saboda rashin haihuwa.?"
Sai da yayi tunanin haka zata iya faruwa. Ba yanzu yake jiye musu ba. Kada ayi aure hakurinta ya kare musamman da yake tana da kuruciya.
"Matar Jikamshi, haihuwa ba abin wasa bace nakasa ce mai girma. rashinta ya kashe aure da yawa. Ya bata soyayyar shekaru da dama. Ya hana zaman lafiya tsakanin kishoyoyi"
Innalillahi wa inna ilahi rajiun take karantawa tun da ya fadi maganar don ta sami kwarin gwiwar magana. Kada tayi kuka ya tursasa mata amincewa da bukatarsa.
"Sayar da jiki a waje ko haihuwa babu aure shine babbar nakasa a rayuwar musulmi. Amma rashin haihuwa ta sunna ba nakasa bace. Jarabawa ce daga Allah Madaukakin sarki. Shi kadai Yasan ladan da Ya tanadarwa masu hakuri da rashi. Ita fa aba ce da duk kudin duniya bazai siyeta ba kuma marasa ita su kadai suka san halin da zukatansu ke ciki sai Allah. Amma mutuncina da ba fin karfi akayi min ba wurin rabani dashi kaga bani da uzuri. Taka jarabawar kenan, hakuri da ita sai yasa Allah Ya yafe maka dukkan zubunanka Ya baka aljannah. Ni kuwa fa? Ni na jawowa kaina. Bani da masaniya Allah Ya yafe min ko kuwa...."
Sai yanzu ta soma kuka mai cin rai. Wayyo Allah son zuciya. Babu wanda yayi musu dole ita da Abubakar suka biyewa shaidan. A rayuwa bazata taba manta groups da ake hira ko litattafan da ake rubutawa ba masu sanya mace budurwa taji bukatar namiji, mai aure idan mijinta na nesa