Chapter 7 Reading GA IRINTA NAN!!! Fitinar Zuciya by Bintu Umar Abbale READ HAUSA Novels

GA IRINTA NAN!!! Fitinar Zuciya by Bintu Umar Abbale

Author :  Bintu Umar Abbale Category :  African Stories & Novels

Chapter   7 / 12

18K to 21K   out of 35.5K words

kamar ta sani ta dauka ta bawa Ummatu ta 'boye mata....Kawu Iro yace "Gwaggo wannan wace irin rayuwa ce dan Allah ya kike nema ki furgita yarinya kina cewa tana da aljanu a ina suke? Gwaggo na fad'a miki ki daina yarda da surutan mutane akan yarinyar nan shi aure lokaci ne dashi idan lokacinta yayi za tayi aure amma dan Allah ki daina d'ora mata lalura yanzu ina amfanin abinda kikayi Gwaggo da sassafe kin bunka a haya'ki a gida kin firgita yarinya tunda tace bata so ba sai ki k'yaleta ba."


"Kai Ibrahim ba fa zanyi asarar kudina ba dole sai nayi haya'kin nan tunda d'akina ne kuma idan ba aljanun ne da ita ba me yasa take guduwa mu da muke shak'ar haya'kin me yayi mana saboda haka ba zan fasa abinda nayi niyya ba idan tana da inda za taje ta tafi."


Khalid ya fito daga dakin fuska a murtuke yace."Gwaggo ina haya'kin naga irinsa." Kallonsa tayi lokaci guda ta fahimci abinda yake da akwai tace." Babu sauransa kenan nasa a wuta."

Kawu Iro yace."Gwaggo jiya ma fa haka kika ce sai gashi kuma yau da safe kin kuma kunnawa." Kuka ta fashe dashi tace."Yanzu dai kunyi min taron dangi kenan kuna kokarin 'karyata ni ko."?

Kawu Iro hankalinsa ya tashi ya dinga rarrashinta tace."Oh!oh! Ibrahim ai 'yar d'an uwanka ta fini a gurinka tunda gashinan a kanta kana nema ka 'kure ni."

Yace."Aa Gwaggo wallahi ba haka bane ina ni ina 'kure ki nayi laifi ki yafe mun." Ba tare da tace komai ba ta shiga dakinta ta bar mu a tsaye.

Kallonsa nayi naga duk hankalinsa ya tashi nace."Kawu ka kwantar da hankalin ka insha Allahu zan cigaba da hakuri da halinta." Yace."Yawwa Sa'ida dama abinda nake so kenan naji daga gurinki kiyi ta addua kinji ko komai mai wuce wa ne." Cikin dauriya nace."To Kawu nagode." Gurinsu ya nufa ya barmu nida Khalid a tsaye.....Yace."Aunty Sa'ida kada ki damu duk inda ta 'boye haya'kin zan bincika a dakin."

Nace."Khalid kyaleta dakinta ne fa tayi duk abinda take so da abunta." "Eh d'akina ne Sa'ida idan kinyi zuciya kada ki sake shigowa." Tana daga cikin dakin take magana.

Yace."Gwaggo wace irin magana ce wannan."?

"Haba Jarumi ai dole raina ya 'baci akan al'amarin nan ranar da naje 'karbo maganin nan sai da na yini banci ba bansha ba salloli na ma sai had'asu nayi amma saboda wukalancin Sa'ida ta dinga kokarin watsa min 'kasa a ido.


Yace." To wai waye ya saki ne? sai fa da nace dake kada kije okey to zanje har gidan ita Uwalen da take janki yawon gurin masu magani na gargad'eta akan hakan ni idan kinyi min baki ba zai kamani ba tunda dai ni ba Baba Iro ba ne."

Kuka tasa daga cikin dakin take fad'in "Khalid kada kaje kaci mutuncin Uwale bata cancanci hakaba." Ya d'aga labulan d'akin da fad'in."To idan bakya so naje gidan Uwale dauko min haya'kin."

Tace."Shigo ka kar'ba." da sauri ya shiga dakin nima naji wani sanyi a cikin raina.......Wani tsohon magani ta d'auko masa a 'karkashin gadonta a daure a wata tsuhowar leda ta mika masa da fad'in"Gashinan wannan jaraba ta isheni haka."
Kar'ba yayi ba tare da ya tanka mata ba ya fito daga dakin.

Yana fitowa yace." Ki kwantar da hankalinki ga maganin nan a hannuna zan fita dashi na zubar."

Hannunsa na kalla a take na gane ba maganin bane domin wancan a k'ulle yake b'akar leda wannan kuwa ledarsa yaluwa ce.....girgiza kaina kawai nayi na wuce na barshi a gurin, dakin na shiga na sameta tana murd'a redion ta ta dago kanta ta kalleni ta dauke kai tana cigaba da abinda take......gurin dana kwanta na nufa na dauki wayata na nemi gefan gado na zauna wayar na kunna na fara dube dube a ciki.......Ummatu ce ta shigo da jug d'in kunu da mai daidaiciyar silba da 'kosai a ciki.

Abin mamaki cikin mutuncin Gwaggo ta kar'ba "Sannu 'yar albarka ai Ibrahim yayi sa'ar mata Rabi wallahi ina jin dadin zama dake sabida kina mutunta ni Allah yayi miki albarka."


Ita kanta Ummatu sai da tayi mamaki da yake tasan halin Gwaggo sai tayi dariya kawai ta girgiza kanta ta fita daga dakin....Nima dana san dani take ban tanka mata ba na cigaba da duba text d'in da Alhaji Nura ya turo ina mamakin al'amarin.....Kiran wayarsa ne ya katseni da sauri na d'aga nasa a kunnena.

Yanda ya amsa gaisuwata yasa naji jikina yayi sanyi nace."Alhaji naga text dinka amma kuma ban fahimci abinda kake nufi ba."

A d'an fusace! yace."Sa'ida kada ki mayar dani 'karamin yaro mana, jiya kin turo min text din daya hanani bacci amma yanzu kina wata magana."

A nutse nace."Alhaji kayi hakuri kayi min bayanin da zan fahimta na dai ga text d'inka amma ban mayar maka da replay ba."

Ajiyar zuciya ya sauke yace."Haba Sa'ida kada kiyi wasa da hankalina mana, nifa ba yaro bane ballanatana kizo min da wasa da gaske nake auranki zanyi amma me yasa kin san akwai al'kawarin aure a tsakaninki da yaron nan Khalid kikayi wasa da hankalina."


Jikina yayi sanyi nace."Wace irin magana ce wannan waye kuma Khalid."? Lokacin da nayi maganar tayi daidai da lokacin daya shigo dakin shida Gwaggon suka zuba min ido....na cigaba da cewa."Alhaji ina tambayarka kayi shuru waye Khalid da har kake wata magana akansa yanzu a duniya na rasa mijin aure sai Khalid dan Allah ka daina wannan maganar sannan kuma text d'in daka gani mybe shine ya dauki wayata a bayan idona ya turo maka amma ni da hannuna wallahi ban tura maka wani text ba."


Ajiyar zuciya ya sauke yace."Okey to har naji dadi a cikin zuciyata yanzu a'ina maganarmu ta kwana."? nace."Insha Allahu yau ko gobe zan yanke shawara.'' Yace."Haba Sa'ida wace irin shawara ce wannan da har yanzu ba'ai yanke ba."?
Nace."Alhaji ka 'kara hakuri dan Allah." Yace."Shikkenan tom ina sauraranki." Sallama mukayi na kashe wayata rai a 'bace na kalleshi yana tsaye idonsa ya kad'a yayi jajazur!! sai wani irin kallo yake min.

"Khalid waye ya baka izinin d'aukar min waya."? Kai tsaye yace." Ni ne na bawa kaina izini ko kina da abinda zakiyi ne."? Cike da mamaki! nake kallonsa.

Ya zare min manyan idonsa da suka rine da 'bacin rai da 'bakin kishi yace."Ni kike ciwa fuska ko."? Nace."Meye abin cin fuska sarkin tsaurin ido ina kai ina Alhaji Nura da har zaka dauki wayata ka rubuta masa text kasan dai ya kusa haifarka ko."?

Yana 'kokarin magana Gwaggo tace."To daya kusa haifarsa mai zai nuna masa? namiji yake shima namiji yake sannan duk abinda yake dashi shima yana dashi sai me kuma."?

Kallonta nayi tace."Mara mutunci wacce bata san mai sonta ba, dame Alhaji Nuran yafi Khalid da har zaki dinga ci masa fuska."


Nace."Kinga Gwaggo ki cire kanki daga cikin wannan maganarki babu ruwanki ni babu wanda ya isa yayi min dole a gidan nan wanda nake so zan aura bana auran 'karamin yaro a kyaleni."


Gwaggo ta fashe da kuka had'e da fad'in "Zagi na Zakiyi ne naga kina zaburowa ko kuma dukana zakiyi butulu kawai."

Hawaye suka shararo min nace."Me nayi na butulci kuma? ina zaune a gado na mahaifina ina ciyar da kaina sai me? me nayi na butulci da har kike kirana da kalmar."

Jikinta ne kuma yayi sanyi ganin ina kuka.....Girgiza kansa yayi ya fita daga d'akin zuciyarsa kamar ta babbake saboda 'bacin rai.

Bayan fitarsa na share hawaye mi'kewa nayi na fara had'a kayan wanki, sai naga tana satar kallona cigaba nayi da abinda nake tace."Sa'ida kinga yau 'kosan yayi kyau gashi da zafinsa ki zuba kunun kisha sai kiyi wanki."

Nace."Aa Gwaggo ba zan sha kunu ba kisha kawai.'' Shuru tai tana kallona tsaf na gama had'a wankin na fita dashi can bakin rijiya na zubesu komawa dakin nayi na dauko indomee biyu 'karamin gas d'ina na kunna na d'ora tukunya da ruwa akai na zuba indomee a ciki.....ina zaune a gurin ta dahu na juye a plate kana na kashe gas d'in. Nan tsakar gidan na zauna a nutse naci na fara ci ina Nazarin rayuwa wai ni Gwaggo take kira da Butulu hummm! rayuwa kenan.



*Masoya a taimaka da sharing👏🏼*



*IDAN KINA BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN GA YANDA ABIN YAKE.....VIP GRUOP#600 NORMAL GROUP #300 ACCOUNT... 0542382124.....BINTA UMAR GTBANK....IDAN KATI ZAKI TURO #400 NE SAI KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER*
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/6, 8:46 AM] 💜: *GA IRINTA NAN!!!🙆🏼‍♀️*
_(LOVE STORY🌺)_
*NA*
_BINTU UMAR ABBALE🍒_
*MANAZARTA WRITES ASSO🖊️📚*



*12*
Cikin ikon Allah ina tsayuwa a bakin titin wani adaidaita sahu ya tsaya a gabana. "Hajiya ina zakije."? Ya fad'a yana dan le'ko da kansa. Da sauri nace."Hotoro zaka kai ni." Jim yayi kafin yace."Okey to nawa zaki biya."? 'Kugin da naji a bayana yasa nai saurin juyawa Khalid ne da Salim cikin a daidaita sahu suna kokarin shiga layin....Da sauri na dauki jakata na fad'a babur da fad'in "Muje ko nawa ne zan baka." babur din ya buga da sauri muka bar gurin....Sai da naga munyi nisa sosai hankalina ya kwanta a nutse na fito da wayata daga cikin jaka number ta na shiga nema inaso na sanar da ita cewa gani nan a kan hanya.

A tsanake muka gaisa nace."Umma gani nan a kan hanyar zuwa." Tace."Da daddare nan Sa'ida ina fata dai lafiya."? Cikin rauni nace."Lafiya Umma." Ta amsa da to "Alhamdulillahi sai kin 'karaso." Kashe wayar nayi nasa a jaka kana nayi saurin sa gefan hijabina na goge hawayen da ya fara zuba a fuskata.


Cikin magagin bacci ta tashi tana lalu'ben torchlight d'inta ta kunna tana haske d'akin da fad'in "Sa'ida Ibrahim din be shigo bane."? Shurun da taji yasa tayi saurin kallon inda take kwanciya taga wayam! sai tai zargin ko tana bandaki redion ta ta dauka ta fara kokarin kunnawa wasu tashoshin sun rufe da kyar ta lalubi freedom redio lokacin suma daf suke da rufewa. kimanin minti goma tana zaune ba taji motsinta ba sai ta mike ta fito bakin band'akin ta tsaya tana kiran sunanta. shurun da taji yasa gabanta fad'uwa tana kokarin barin gurin ya shigo gidan ganinta a tsaye a bakin bandaki yasa yace." Gwaggo lafiya me kike anan gurin."?

Murya na rawa tace."Khalid Sa'ida bata gidan nan.'' gabansa ya fad'i da sauri yace."Gwaggo bangane bata gidan nan ba." ? Ajiyar zuciya ta sauke tana kokarin barin gurin tace."Jeka kira min babanka idan ma yayi bacci ka taso shi.''

Khalid da sauri ya nufi gurin nasu itama ta nufi dakinta tana haske haske da torchlight nan taga babu jakar kayanta sai ta sake karaya a sanyaye ta zauna kan shimfid'arta tana fad'in "Wannan yarinya bata da hankali ashe."

Baba Iro da Khalid suka shiga dakin a tare......Tace."Ibrahim matarka ta tunzura Sa'ida ta had'a kayanta ta gudu."

Kawu Iro yace."Gwaggo wace irin magana ce wannan."? Fashewa tayi da kuka tace."Iro d'azu Rabi ta zauna ta 'karewa Sa'ida cin mutunci tana kiranta da Karuwa tsohuwar guzuma saboda kawai ina maganar auransu da Khalid shine fa ta fito tayi mata wannan cin mutuncin a cewarta wai d'anta ba zai auri lalatacciya ba wannan dalilin ya fusata zuciyarta ta had'a kayanta ta gudu."

Baba Iro yayi shuru yana jimanta al'amarin! tace."Yanzu ni babban tashin hankalina da damuwa ta inda ta nufa a cikin daran nan."


Yace."Gwaggo hakika raina ya 'baci da wannan al'amarin kuma duk irin hukuncin dana dauka akan Rabi kada kice don me ta riga ta gama fusata ni ace wai 'yar d'an uwana na jini take kira da Karuwa."

Gwaggo tace."Ibrahim ba zan hana ka ka dauki mataki akan Rabi ba domin ko baka dauka ba ni zan dauka ba zata dinga la'antar zuria ta ba."

Yana kokarin fita daga d'akin Khalid ya dafa kafad'arsa a tausashe yace."Baba kada ka yanke hukunci cikin fushi Annabi ya hana."


Rai a 'bace! yace."Saboda mahaifiyarka ce ko? yanzu kai a tunaninka abinda ta aikata tayi daidai."?

Kansa ya girgiza a sanyaye yace."Nima banji dadin al'amarin ba amma dan Allah kayi hakuri." Ba tare da yace masa komai ba ya bar gurun.


Khalid dakin ya shiga jikinsa duk a mace babu shakka yasan wannan hargitsin dake faruwa shine sila da baya shiga sabgar auntyn nasa da mahaifiyartasa ba zata samu hanyar zaginta ba.

Number ya nemo a wayarsa ya fara kira, Gwaggo tace."Yawwa dama yanzu zance ka kira ta a waya mu ta fad'a mana inda ta nufa duk da dai nasan watakila tana can gurin uwarta mai hure mata kunne."


Jin wayar tana shiga yasa da sauri ya d'aga mata hannu. shuru tayi tana kallonsa, wayar ta 'karaci ringing ta katse bata dauka ba.

Hannu na rawa ya sake kira nan ma babu amsa Khalid ya dinga kiran wayar tana katsewa ya kai sai goma, jiki a sanyaye ya kalleta da fad'in "Gwaggo aunty Sa'ida tayi zuciya taki daukar wayar."

A sanyaye tace."Khalid dole tayi fushi! bayan fitarka Uwarka sata tayi a gaba taci mutuncinta ta dinga zaginta tana kiranta karuwa." Tana share hawaye take maganar ta cigaba da cewa"Wai yau zuria ta Rabi takewa wannan cin mutuncin."

Yace."Gwaggo idan Ummatu tana da laifi kema kina dashi kada fa ki manta irin takura mata da kikeyi Gwaggo keda Ummatu kune kuka kori auntyna Sa'ida daga gidan nan."

Shuru tayi tana share hawaye tace."Dan Allah sake kiran wayar ko zata dauka idan kuma bata daga ba ka kira wayar uwartata idan kana da number ta."


Yace."Ni bani da Number Ummah Habiba amma bari na sake kira naji ko zata dauka...sake kiran wayar yayi har sau biyu babu amsa, ya sauke nannauyan ajiyar zuciya yana tunanin yanda za'ayi......."Khalid ka fito kaje gidansu abokinka ka kar'bo mukkulin adaidaita sahunsa ka kai ni babban gida.'' Muryar mahaifiyarsa ta katse masa tunani.

Da sauri ya mike ya fita sai ya ganta a tsaye da hijabi a jikinta. agogon dake daure a hannunsa ya duba sha d'aya shaura yace."Ummatu me zakije kiyi a babban gida da daddare haka."

hawaye ta share tace."Babanka ya kore ni a gidan wai naci mutuncin 'yar d'an uwansa har ta gudu sabida haka nima ba zan kwana a gidan ba.''


Khalid jikinsa yayi bala'in mutuwa da saurin ya jingina jikin bango (garu) Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un ya shiga kira yana jimanta masifar dake kokarin kunno musu....Gwaggo kuwa tana cikin dakinta a zaune tana jin duk abinda ke faruwa ko gezau ba tayi ba tana zaune babu abinda ya dameta.

Yace."Ummatu ba zaki je ko'ina ba ina zuwa." da sauri ya nufi gurin nasu hankalinsa duk a tashe.....a kwance ya samu mahaifin nasa a tsakar gidan ya tsuguna gefansa hade da fad'in "Baba dan Allah kayi hakuri matakin daka dauka akan Ummatu bai dace ba."

Hannu ya d'aga masa rai a 'bace yace."Khalid tashi ka bani guri bana bukarar jin wata magana daga gareka, Rabi ta kaini karshe kuma dama ba tun yau ba nasan da cewar bata kaunar yarinyar nan Sa'ida alhalin abinda yayi ubanta shi yayi ni mu biyu kacal iyayenmu suka haifa muka haifeku me zai sanya ta d'orawa yarinya karan tsana akan wane dalili? ita ko tausayin maraicinta ba tayi to shikkenan yanda tayi sanadin barinta gidan itama sai ta barshi idan kaga mahaifiyarka ta dawo gidan nan to ka tabbata cewa Sa'ida ce ta dawo."


Khalid jikinsa yayi sanyi yace."To Baba dan Allah kayi hakuri dare ne yanzu ka bari da safe kome zai faru sai ya faru." cikin tsawa! yace." Khalid ba zaka tashi ka bani guri ba."?

Mikewa yayi ya fita daga gurin ransa a tsananin 'bace...Babu Ummatu a gurin da sauri ya le'ka dakin Gwaggon yana tambayarta tace itama bata san inda take ba, fita yayi da saurin gaske.

Can ya hangota tana tafiya yabi bayanta da sauri yana kiranta, tsayawa tayi ya karaso gurin yaga tana share hawaye yace."Ummatu kiyi hakuri dan Allah ki daina kukan nan bari na shiga gidansu Salim d'in na kar'bo key din."

Kanta kawai ta d'aga masa zuciyarta na tafarfasa tunda tayi aure tsayin shekara ashirin da biyar wani sa'bani mai muni bai ta'ba shiga tsakaninta da mijinta ba, sai gashi yau akan Sa'ida yarinyar tayi sanadin da mijinta ya koreta daga gidan auranta.

Khalid ya karaso gurin cikin adaidaita sahun a sanyaye ta shiga ta zauna yaja babur din suka tafi.

Sai da suka hau titi sosai ta sauke ajiyar zuciya da fad'in "Khalid kaga irin tozarcin da mahaifinka yayi min akan Sa'ida ko."?


Yace." Ummatu kiyi hakuri amma kema mai yasa kika zageta ki ka kuma yi mata kazafi na zina."

Cikin 'bacin rai tace."Ai ba sharri nayi mata ba gaskiya na fad'a me yasa kun san gaskiya amma gabad'ayanku kuke kareta ni nasan Sa'ida mazinaciya ce."

Yaji kansa ya sara! gumi na yanko masa yace." Ummatu zuciya takan dauki zafi a duk lokacin da zaki jefi Auntyn Sa'ida da wannan kalmar wallahi ita d'in kamila ce bata bin mazan banza a waje."


Tace."To shikkenan tunda kana jin zafi sai ka dauki mataki a kaina kamar yanda ubanka ya dauka wallahi Khalid mutukar ni na haifeka to ba zaka auri Sa'ida ba dan duk na gane take-taken ka."


Shuru yayi wani irin gumi! yana tsatstsafo masa .

Tace."Idan ka bijirewa umarnina ka auri yarinyar sai nayi maka baki ka lalace gwara tun wuri ka cireta daga cikin zuciyarka."


Murya na rawa yace."Ummatu me yasa kike wannan maganar me yasa kika dauki zafi da al'amarin nan kada

7 / 12