Masarautar Qamar Complete Hausa Novel

Author :  Khadija KMU Category :  Love

Chapter   7 / 13

18K to 21K   out of 36.4K words

gashinta wani Abu ba don sai idan abun ya kadota
sosai .shine take rufe gashinta don a shekara baifi ta rufe gashinta ba sau hudu akwai lokacin da har
shekarar ta kare bata damu da rufe gashinta ba idan ba wurin sallah ba 
Cikin kyankyami take rike da hular da sam bata wanke ta ba don duk kayan gwanjon duk hasken su
sai ta sanya hannunta ta wanke su tas kafin ta sanya.
Warware gashinta tayi wanda ya zubo mata har bayanta sosai don ma akai akai take rage gashin
kanta da batasan yadda zai rinka takura mata ba kuma data rage nan da nan yake fitowa har yafi
wanda ta rage din tsawo da cika da yawa 
Taba gashin tayi sannan ta dan shinshina ko yana wari kamshin coconut oil din da taji ya sanya ta
dan saki ajiyar zuciya 
Daure gashinta tayi Sosai yadda duk bala'inka baka iya hango tukar don ta linketa ta sanya ta cikin
gashin yadda ba mai iya gane yawan gashin ko tsawonshi ko yawanshi 

Bintu da ta bude idonta masu kyau ta kalli Hurriya tace kindawo daga mata kai Hurriya tayi tanabin
ko ina na jikinta da kallo alamar rama kuma da yar damuwa tattare da ita 
Ganin Hurriya nabin ta da kallon minene matsalar ki ya sanya ta washe baki yan hakoranta suka fito
tace Hurriya jiya nazo in ganki na kawo maki abinci Amman Saita kasa ida maganar alamar kamar
tana kuka ta hade kafafunta da gwiwarta Hurriya ta duko tace Bintu miye ya faru waye ya taba ki
fadamin shi. Daga muryar ta zakaji alamar kulawa duk da yadda take kokarin boye emotions a cikin
maganarta ,duk wani mai tsantsar fahimta zai iya fahimtar damuwa a maganar ta Amman a yadda
take maganar kadai sai mutum yace bata damu ba 
Hurriya kara matsowa tayi kusa da Bintu kamar tanajin tsoronta tana tambayar wai lafiyar ki kuwa ki
fadamani manah itama maganar ta kubce mata da alamun shagwaba Wata irin kyakyawar runguma
Bintu tayi mata sannan ta fashe da matsinacin kuka Hurriya dan ture ta tayi ta zame jikinta Bintu
dagowa tayi ta kalleta da idanun ta da sukayi jajir ta kalli Hurriya da take bata fuska kamar kashi ya
tabata kuka ta kara fashewa dashi Hurriya dafe kanta tayi tace ki daina kuka ki fadamin abinda ya
faru shiru Bintu tayi kamar daman abinda ta jira ta fada mata kenan don haka tayi shiru kafin a
hankali tace cikin muryarta mai rauni tace nayi kewar ummanah Hurriya inajin tsoro tana maganar
hawaye na zubo mata shiru tayi sannan ta goge hawayenta tana kallon Hurriya data tsura mata ido
tashi tayi zata mike Hurriya tace Bintu yadda ta fadi sunanta saida ya sanya tsigar jikin Bintu ta tashi
don da wata irin kulawa ta fadi sunan Bintu kallonta takeyi da mamaki tace Hurriya tana zare ido 
dan murmushi Hurriya tayi kadan wanda duka dimples dinta saida suka lotsa sakin baki Bintu tayi
tana kallonta don tunda take a duniya bata taba ganin wanda murmushi yayi ma kyau ba irin Hurriya
itakanta har goosebumps saida taji itada take ma mace kenan inaga ta fito tana murmushi bama
dariya ba murmushi kawai tabb akwai matsala don ta tabatta duk inda ta matsa mazane zasu rinka
binta kamar sleeves Dogs inaga tayi dariya ita kanta Bintu tunda take bata taba ganin mace mai
kyaun Hurriya babu ta inda Allah ya rageta a fuskarta ko jikinta 
Gyaran murya Tayi ta kalli Hurriya da kamar tana cikin good mood a hankali Hurriya cikin muryar ta
mai dadi da sanyi tace Mai kike tunani Bintu ke nake tunani yar dariya tayi wadda har saida
hakoranta saida suka fito shiru Bintu tayi tana kallon ratsin gold din dake tsakankanin hakoranta
wanda bata taba lura dasu ba sai yau tunda take da Hurriya idonta har wani sparkling sukeyi dimples
dinta kam duk sun lotsa Bintu cewa tayi Hurriya daman kina dariya dan gyara fuskarta Hurriya tayi ta
koma yadda take da sannan ta juya ba tare da tace komai ba Bintu kiran sunanta tayi Hurriya
tsayawa tayi bata juya ba kuma batayi gaba ba Bintu matsowa tayi cikin rauni da sanyi tace Hurriya ki
zama yar uwata wadda zan rinka fuskantar ta da matsala ako dayaushe don Allah kada ki Rabu dani
ko ki juya min baya ni ko baza kiyi fira dani ba nizan yi maki fira .
Inajin kadaici sosai wanda kwata kwata banda kwanciyar hankali ke kadai nike gani inji dama dama a
raina don ni kallon yar uwa nike maki cikin muryar ta mai dadi Hurriya tace Bintu kin zama kanwata
daga yau Bintu bata fuska tayi ta bayan Hurriya tace na girme ki Hurriya shiru tayi batace komai ba ta
fita don tasan kilan ta makara dage kafadarta tayi sannan tace who cares
Tana tafiya taji ana nunata saidai ta saba sosai safiya ce ga kuma sanyin da akeyi mai shiga kasusuwa
Hurriya idan ka kalleta zakayi tunanin batajin sanyin don ba dankwali A kanta amman akwai hula a
hannunta tafiya tayi Mai nisa kafin tazo bangaren daza tayi aiki Ma'aikata ne ta gani tun abakin kofar
chamber sunata aikinsu a hankali ta shiga bangaren kallon parlon takeyi wanda komai na ciki ya
burgeta tun daga ceiling din dakin har zuwa painting komai fari ne kallon chandeliers din dasuke jere
a saman popn tayi wanda yake bada wani irin mahaukacin haske wanda yake neman tarwatse mata
idanu kujerun parlon royals ne masu matukar tsada kuma very light saboda at first glance ba Lallai
ka kirasu royal ba fa sai ka san furnitures Sosai zaka iya ganewa kallon dogayen labulen da aka jerasu

tayi komai na parlon is rich and elegant carpet din wanda ya cinye katon parlon da kusan set of
chairs guda hudu kuma dukan su luxury royal chairs ne 
Sai dining table dake cin kujeru guda shidda saida ta gama kallon komai magana taji daga bayanta
don haka tajuya yar budurwa wadda bazata wuce sa'arta ce tagani sai kallonta takeyi kamar zata
cinye ta baiwar Allah Amman ke ba yar najeriya bace shiru Hurriya tayi fuskar ta a hade bata ko amsa
mata ba gyara tsayuwarta tayi sannan tayi murmushi tace hala kece sabuwar ma'aikaciya to muje In
kaiki wurin mama rabi nan ma Hurriya batace mata komai ba don ganin irin kaudinta ta katon
kitchen suka bi wanda Hurriya ke biye da ita har suka zo inda mama RaBI take 
Matar yar dattijuwa ce tsaye tana kallon sabbin ma'aikatan da aka kawo 
Zubaida tace mama rabi ga sabuwar Mai aikin da aka kawo saitin kunnen mama rabi tazo tayi mata
rada tace kinga kyaunta sai tayi dariya tace akwai kallo a masarautar nan Amman fa shegiyat akwai
miskilanci kamar jikar Qamar wata dariyar tayi tace itada tazo masarautar Qamar ai komai ta ajiyeshi
tana dariya mai cike da zallar munafunci da makirci kuma da mugunta 
Duk abinda suke cewa Hurriya tana jinsu saidai basuyi tunanin don babu ko alamar hakan a fuskarta
mama rabi tazo Daidai saitin Hurriya saida ta kare mata kallo sannan ta washe baki tace sannu yan
mata Hurriya daga mata kai kawai tayi 
Mama RaBI abun ya bata haushi Amman da yake yar duniya ce sai ta share ba bata lokaci ta fara
lissafo mata dokikin Imad shiru tayi tana saurare har tagama Hurriya batace kala ba Amman ga
dukkan alamu ta dauka 
Mama RaBI ta kalleta tace ki gwada mata hanyar dakin zubaida tace muje ko tare suka koma itada
zubaida har zuwa inda zai sada ka da dayan parlonshi kallon Hurriya zubaida tayi tace ki shiga idan
kika wuce parlo na biyu zakiga dakinda yayi hanyar da tayi kasa Tohm sai ki shiga kasa din da kin
wuce parlon to dakin dake kallon ki sai daki na hagu da na dama daga mata kai kawai Hurriya tayi
sannan ta bude kofa ta shiga parlon wanda yake dauke da set of turkey chairs parlon ya hadu don
har batasan wanda yafi kyau tsakanin na farko dana biyu ba 
Bata tsaya kallon parlon ba don ganin lokacinta ya tafi don ayyuka ne gareta da yawa don haka ta
hau steps din da zasu kaita dakin kasa wanda kamar underground 
Parlon da tagani akasa saida kam ta tsaya ta gama kallo da yabonshi saboda komai da aka sanya a
parlon zata iya cewa abinda ta fiso kenan kamar ita aka tambaya mi takeso ta fadi aka bi zabinta 
Cikin tafiyar ta mai kama da catwalk ta shiga dakin kallon dakin tayi wanda yake da matukar burgewa
ba bata lokaci ta shiga gyarawa da sauri take komai bayan tagama ne ta shiga toilet din ta wanke
komai tass 
Sannan ta fito ta kara shiga dayan dakin shima ta gyara komai da sauri takeyinshi kuma cikin rashin
ha’inci don ko ina tayi mashi kalkal 

Sannan ta shiga dakin karshe tana bude kofar ta lumshe idonta ta dan tsotsi bakinta bude idonta tayi
tana kallon ko ina banda kamshin turaren wuta ba abinda mini falon yakeyi 
Shiga tayi ta fara kakabe komai ba wani bata lokaci tagama sannan tayi mopping ta goge ko ina tass 
A hankali ta nufi kofar dakin da take kallonta ta bude kallon Komi take na dakin wanda yake fari
subahanallah dakin ya hadu kowaye yake da dakin ta jinjina ma fashion sense dinshi Komi is
extremely expensive and superb a dakin tun daga wall decors din dake a bango dakin hadaddun
paintings ne da canvas masu matukar kyau da tsada wanda ko wani zane is worthing millions ba
wani tarkace Sosai a dakin wanda alama ta nuna mata mai dakin bai son hayaniya 
Tsarin dakin ya taimaka mata wurin reading personality din young master dinta 
Kallon katon gadon tayi wanda bedsheets din da duvet din duka farare ne saidai daga inda take tana
hangen irin laushin da Eskimon yake badawa 
Lura tayi da Akwai mutum dukunkune cikin duvet din don haka ta shiga toilet dinshi banda kamshi
ba abinda yakeyi ta hada komai na wankin ta wankeshi kalkal .
Kallon gadon Hurriya tayi tunanin yadda zata gyara wurin take cikin ranta tace why not ki tadashi
idan kingama sai ya cigaba da baccin shi 
A hankali ta nufo saman gadon tunani yadda zata tadashi takeyi saboda batasan sunanshi ba vanity
table ta kalla wanda ta hango brush na gashi dauko brush din tayi tazo Daidai saitin kanshi ta dan
janye bargon inda taci karo da fuskar Imad yana baccin shi peacefully he looks so cute and
handsome kallo daya tayi mashi tasan dan gayune don ko sumar kanshi wadda take acike irin ta
gayu tasha gyara don banda salki ba abinda takeyi kallon dogon hancin shi tayi zuwa bakinshi wanda
yake pink dan lumshe ido tayi sannan ta bude .
brush din dake hannunta ta sanya a saman gashin kanshi tana heyy ka tashi
 bata fuska yayi sannan ya kara gyara kwanciya 
Hurriya kam da taga alamar ma dadi yakeji don haka ta maida brush din saitin kunnenshi tana mashi
kamar tafiyar tsutsa 
Imad cikin baccin shi mai dadi yaji alamar Abu na yawo a kunnenshi babu abinda yazo mashi arai irin
kyankyaso don shine abinda yafi tsana da tsoro a duniya a mugun firgice ya tashi yana cewa
innalillahi wa’ina ilaihi raji’un ya diro yana tsalle yana kallon jikinshi yana dube dube kamar sabon
shigar hauka 

Hurriya kam saura kadan tayi Dariya Amman ta dake yadda ta saba tayi gyaran murya don
kwatakwata bai lura da ita ba zaro fararen idanunshi yayi yana kallonta sannan yace who are you Do
you want to die  banza tayi dashi tamkar yana magana da dutse 
Don har ta fara cire pillows din domin gyara gadon 
Ammar da tun dazu ya shigo domin neman tsokana wurin twin brother dinshi Amman wata marar
Sa’a ta riga shi he’s enjoying their little drama saidai yana mamakin irin zeal din yarinya how dared
she play with a prince dariya ke cinshi Amman yaki barin  dariyar tafito saida ya gama kallon komai 
Amman ya gama jin tausayin ko wacece don yasan halin Imad Sarai don halinsu su uku to daban
yake da subira da Imad kuma da Khalifa Qamar to Khalifa ai ba’a sanya shi ma a layi don nashi abun
is too much kuma ya dade baya palace din so he can’t say much about him don he can’t remember
when last ya ganshi to daman idan anaso Ayi maka hukunci a palace din to dama either akaika
chamber din subira ko kuma Imad chamber su biyu nan suna da matsaloli 
Hurriya kam banza tayi dashi ta cigaba da aikinta don a wurin ta baida amsa ita dama she hate
useless talks ta gama gyara gadon tass Imad da yake tsaye yana fuming don bacin ran da yake ciki zai
iya karyata idan har batai wasa ba ba’a taba yi mashi irin abinda akayi mashi ba yau tun kam daga
yarintar shi 
Ta shigo mashi daki ba tare da izininshi ba sannan ta tadashi daga baccin da yake mai matukar dadi
don ta raina mashi wayau wai kuma da brush ta tadashi sannan bata gaishe shi ba and again yana
mata magana tayi banza dashi ko bata iya turanci ba bata iya durkusawa ta fara bashi hakuri tana
kuka tana rike mashi kafa 
Amman shine takeyin kamar ma batasan dashi a wurin ba gaskiya yarinyar nan must have a dead
wish because she’s playing with fire 
Wata tsawa ya buga mata yace ke bakiji ana maki magana ba ko kurma ce Hurriya a hankali ta juyo ta
zuba mashi idanunta masu matukar kyau da kaifi kallonta yake tundaga gashin kanta da yake a bude
har zuwa fuskarta mai matukar kyau da annuri yace Do you want to die sai kuma ya tuna ba Lallai
tanajin turanci ba magana yafaryi mata cikin muryarshi mai dadi kuma da dadin sauraro yace wacece
ke? Dan tsotsar bakinta tayi  sannan tace Hurriya Faisait  Hamood sabuwar mai aikin ka 
Kin aikata laifuka don haka zaki amshi hukunci da ya kamata yana maganar with arrogance ne and
full of himself 
Hurriya kallonshi take ba tare da ko kyaftawa ba tunda yake babu mai aikin da taba kallonshi ido
cikin ido kowa acikinsu yana shakkar shi Amman banda Hurriya wadda take kallonshi kamar yadda
Ammar ke kallonshi cikin muryar ta mai dadi da sanyi sai kuma maganar ta wanda yake nuna cewar
tana da wani yare na daban tace babu inda nayi laifi tunda nazo a dokokin ance ba ruwana dakai
kuma na kiyaye kuma ance bakasan hayaniya kuma banyi ihu ba ance idan kana Bacci kada in tadaka
da magana kuma banyi magana nayi amfani da wancan abune wurin tada ka 

Sharrudan da aka gaya mata duka ta fada mashi shiru yayi yana kallon bakinta wanda yake da kyau
da bakin lining a kasa wanda kamar ita ta zanashi Amman haka hallitar bakinta yake 
Zama yayi saman sofa ita kuma ta fara share wurin da vacum cleaner Ammar ya shigo yana wata irin
dariya yana nuna Imad wanda ya rasa miye zaice Hurriya kallonshi tayi taga kamar su daya don suma
identical twins ne kamar Neela da liya murmushi yayi mata sannan yayi mata wink bayan tagama
komai zata fita tazo wucewa kenan Imad ya tadiyeta ta fadi goshinta da hannunta na buguwa da kyar
ta tashi.
🌚Masarautar Qamar 
By Khadija (KMU)
19&20
Da kyar ta tashi  kallonshi tayi da idanunta masu wani kaifi Dukansu kasa gane expression din
fuskarta sukayi she looks fierce and scary ta iya hiding emotion don fuskarta baka iya lura da farin
ciki ko sadness ko happiness ta kware wurin hiding emotion dinta don haka fuskarta is neutral saidai
idanunta ne suke bashi warning sannan ta sanya kafa ta tafi Because she was done ko mopping din
batayi yayi da kanshi.
Ammar dariya ke cinshi Amman ganin zallar bacin rai a fuskar shi ya sanya yace Husain waye ya
tabaka banza imad yayi dashi ya tashi yaje ya kwanta saman gado ya runtse idonshi
Ganin mulki da sarautar tashi ta matso ya sanya ammar ya fita idan ya sauko sai ya dawo 
Hurriya ranta bace yake Mai mutane suka dauki duniya ne itadai abinda ta sani a rayuwarta da mai
kudi da talaka duk Abu dayane da yaro da babba duk Abu dayane da makaho da mai ido duk abu
daya ne saboda duka suna amsa sunansu mutane batasan yawan tunani don haka ta nufi dayar
chamber din 
Chamber zinariya kowa kallonta yake kuma ba wanda tayi ma magana abinda ya kaita shi takeyi don
Allah ya taimaketa aikin kitchen ne 
Aiki sukeyi sosai don abinci akeyi kala kala wasu suna gyara inda aka bata wasu kuma  suna jera
fruits a trays 
Hurriya kam wanke wanke kawai takeyi tana kifewa 
Sun dade suna aiki a wurin kafin a kamalla  Hurriya wuri ta samu tadan zauna 

Shugabar dake a wurin ta kalli Hurriya tace ku tashi kuje kukai abinci kuma ku tsaya har agama ci
saboda idan suna bukatar wani abu 
Hurriya kallonta tayi ido cikin ido sannan tace bazanje ba daganan nagama aiki sai kuma abincin dare
zanzo Amman ba zan kai abinci ba 
Shiru kitchen din ya dauka kowa yana kallonta baki bude
Hurriya ba inda suka tsaya sai inda takeyin wanki tunawa tayi bata wanke kayanta ba don haka ta
shiga dakin ta dauko kayan saida ta cire kudinta da sarkokinta da wayarta ta adanasu sannan ta nufi
wurin wankin 
Wata yar karamar yarinya tazo wurin Hurriya kallon Hurriya tayi tace inason ki tayi dariya yan
hakoranta na fitowa yarinyar tace kinsan miyasa nike sonki Hurriya ta girgiza kai tana kallon yarinyar
tace Aa yarinyar dariya tayi sannan tace saboda kina da kyau shiru Hurriya tayi tana kallonta yarinyar
tace kinsan mi ?kinfi kowa kyau a masarautar Qamar 
Sai kuma ta bata fuska alamar tanaso tayi kuka tace amman banason in rasaki kamar yadda na rasa
fareedaa shiru Hurriya tayi don bata gane inda zancen yarinyar ya dosa ba Hurriya wadda bata iya
lallashi ba tace kiyi shiru ki daina kuka sannan ta matsa daga gefen yarinyar ta fara wankin 
Hurriya duk tafi jin dadin aikin wanki kowa hidimar gabanshi yake ba wanda ya damu da wani don
haka ba ruwanta da bata miyaun bakinta wurin magana 
Kayanta ta fara wankewa sannan  ta cigaba da wankin da ake kawo mata wanki take sosai ga sanyi 
Duk sanyi bai dameta ba kamar yunwar da ta dameta don duk yau bataci komai ba wata irin yunwa
takeji 
Imad kallon wayarshi yake wadda banda ringing ba abinda takeyi tun dazu khaleed ke kiranshi non-
stop Amman yaki dauka saboda his new Maid has ruined his entire day saidai he made a vowed to
ruined her life the way she ruined his mood she really messed with the wrong person wani kiran ne
ya kara shigo mashi cikin yanayi na mulki da kuma izza ya dauka shiru yayi batare da yace komai ba 
Khaled yace kaifa dan rainin wayau ne kaifa kadai muke jira tun dazu don Allah kayi sauri cikin yanayi
na mulki Imad yace please I will be there in the next five minutes 
Ya kashe wayar sannan ya tashi ya shiga toilet dinshi ya dade a toilet din kafin ya fito sannan ya
shirya cikin hadaddun English wears dinshi wadanda sukayi mashi kyau 
Imad na fitowa ya iske Ammar da yake zaune a

7 / 13